Showing 90001 words to 93000 words out of 257873 words

Chapter 31 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

475

Bilal mutunchi a gaban ƙawaye na da dama duk ba son sa suke ba. Gefe na ta zauna tana cewa
"Ni wlh duk se naji kunya, muna murna mun haɗo sha tara ta arziƙi mu taho tsaka ni da Allah a fito mana da kaya kamar za'a buɗe shago wai na ɓangaren uwa ai da se ki ce kawai kin ya fe ba se mun kawo namu ba ko kuma a saɓa rana". Kafin na bata amsa Khausar yar ƙanwar Abba ce ta ce mata

"Ke kuwa takwaran Abba guda ai bama ayi komai ba wannan somin taɓi ne, ki jira ranar suna sannan zaki tabbatar da yaro ɗan gata ne kuma ɗan dangin ya kuma ci sunan babban mutum"
"Ai hakan ma mun gani dan wasu kayan har ya shakara biyu ma ba lallai su masa daidai ba" ta sake faɗa. Ni dai tafi ki mutu ban ce ba, ba ta haƙura ba ta sake cewa
"Kuma a hakan ma fa mu karo karo muka yi kowa abin da tayi niyyar bayar wa ne Hajja ta ce a haɗa". Wannan karon Hansa'u ce ta bata amsa ta ce

"Dama ai haka ake yi, da abin da uban ɗan ya bayar da na yan uwan sa ake haɗewa a yi abin da za'a yi ai ba ku kaɗai kuke haka ba"
"Au, lallai" ta faɗa daga nan ta tashi ta fita tun da gulmarta ba tayi tasiri ba. Tana fita Baby Bashir ta ce
"Amma duk yanda akayi wannan yar uba ce" na yi dariya na ce
"Me kika ga?"
"Ai it's obvious munafunci take so ta haɗa, irin waɗannan fa ba'a basu fuska Halima yanda zata kwaso gulmar wasu ta kawo miki kema haka zata ringa kwasar ta ki ta kai wani gurin se kin iya takun ki wlh" shikenan hira ta koma kan munafukan dangi masu irin Halin Farisa.

Se bayan magriba gidan ya sarara da mutane, Anty Maimuna matar yayan su Bilal na biyu da zasu tafi ta shigo ɗaki ta saka mun envelope a hannu na ta ce in ji mijin ta a siya wa takwaran sa turare. Dake da Alhaji Balarabe na san shi ban ma taɓa sanin sunan Abba na ne da shi ba, na mata godiya sosai, ina kallon Fadila da ta biyo ta tana ta leƙen hannu na dake rigar jiki na me aljihu ce se kawai na zura envelope ɗin a ciki a raina ina raya ko nawa ne a ciki dan na ji da tudu ba laifi.

Raina ƙal ina cin gasasshen nama da aka baɗe da yajin daddawa ina kallon Anty Labiba da ke ta faman ware kayan data hargitsa. Allah sarki Abba. Sa guda ya sa aka yanka da yammar da Baba Salamatu ta kira shi ta ce masa ba'a yi mun abun ƙauri ba, a al'adar gidan mu kuma har yanzu suna yi kuma suna cin sa'a mata da ake aurar wa suma in da suka zuwa ana musu dan haka sun mayar da shi kamar wani dole shi ake rabawa mutanen da suka kai kayan barka da masu karɓa naman suna kuma ba'a taɓawa suya me kyau ake masa a aje wa maijego tayi ta cin abun ta ta bawa wanda taga dama ƙaurin shi ake haɗawa da yaji a rabawa dangi.

Dake yamma tayi sanda aka yi yankan se kawai ya ce a ɗiba wani kaso a kai can gidan su Bilal ɗin su soya su rabawa mutanen su sauran kuma aka cire ɗanye na sadaka da wanda za'a gasa mun ragowar Mama ta kira masu yi mata aikin sallah su ka hau aika ce shi.

Se da ta gama ware kayan tsaf ta nuna mun wanda ta zuba a bakko ta ce
"Waɗannan duk ba na amfanin yansu bane can gidan Mama za'a kai su a ajiye idan lokacin buƙatar su ya yi se ku ɗakko ba za'a bar su a nan ya bi dare ya kwashe ba". Ɓata fuska na yi ita kuwa ko a jikin ta ta tattare atamfofi guda biyu da lace ɗaya da suka sako mun ta ce
"Waɗannan ma dai ki ɗinke su kya ƙara na jego". Wato tsabar ta raina kayan ne shine ta ke cewa wai na ƙara na jego da su, Allah ya yafewa Anty Labiba kawai. Har kusan goma sannan ta tafi tana jaddada mun har idan ina so na yi taron suna toh fa na karɓi kuɗin duk abin da zan yi a hannun Bilal dan ko pure water ba sake kawo mun za'a yi daga gida ba sun yi iya bakin yin su.

Da ke da Baba Jummai me aikin Mama Fauziyya aka taho Anty Amina se ta tafi gida. Ban ga Bilal ba se washe gari da safe dan har Anty Labiba ta tafi bai shigo gidan ba ni kuma tafiyar ta ba jimawa nayi bacci sai bayan na fito daga wankan safe na tarar da shi a falo da Abba na a hannun sa. Fuska ɗauke da murmushi kamar bamu samu wani saɓani ba ya ringa kallo na ni kuma na ɗauke kai na shige ɗaki. Se da Baba Jummai ta karɓi Abba zata yi masa wanka kafin ya biyo ni, ina ƙoƙarin zage zip ɗin riga ta ya rungume ni ta baya ya ɗora kan sa a kafaɗa ta yana cewa

"Wai yaushe kika koyi fushi haka Halima. Ban za na masa ina ƙoƙarin janye hannayen sa da yake yawo da su a jiki na.
"Na fa baki haƙuri me kuma kike so na yi ki dena share ni dan Allah?" Ya faɗa a marairaice mun.
"Ni ka rabu da ni" na faɗa ina cigaba da ture shi, be sake ni ba se ma jefa ni kan gado da ya yi ya bi baya na. Yanda kasan ana kaɗa mazari haka jiki na ya ɗauki rawa saboda yanda ya birkice mun yana neman canza layi, ko da ban samu ƙaruwa ba amma karen hauka bai cije ni ba da zan yarda ya kusance ni. Saboda rikicewa na manta ai bani da tsarki, na riƙe hannayen sa ina girgiza kai lokaci ɗaya hawaye ya ɓalle mun amma na kasa buɗe baki na masa magana. Muryar Baba Jummai ta cece ni, salati ta rafka dan a buɗe ƙofar ta ke ta juya a sukwane tana sake jan dogayen salati sum sum Bilal ya ɗaga ni ya fice daga ɗakin ni ko sai da na kwashi kusan minti goma kafin nayi ƙarfin hali tashi na shiga banɗaki na gyara jiki na. Yinin ranar kasa haɗa ido na yi da Baba Jummai, me lalle da kitso Anty Labiba ta turo mun dama ta ce mun na wanka kaina da nayi wankan safe na wanke dan haka tana zuwa ta fara saka mun han lalle bayan ta gama ta hau mun kitso.

Tun da Bilal ya fita be sake dawowa ba, gashi babu waya a hannun sa balle na kira shi dan har lokacin ba muyi zancen taron suna ba, bai ce mun komai ba nima kuma da ta ce na yi masa maganar ban masa ba. Abin da ya sa ban wani damu sosai ba saboda akwai kuɗin da Yayan Bilal ya bayar aka kawo mun dana duba rafar yan dubu dubu ne sababbi dubu ɗari cif sun ishe ni nayi duk wata hidima kuma tun da na ji Anty Labiban bata sake yo waya ta tambayi yanda muka yi fa shi ba nasan a can gida ma ba zasu kasa yin wani abu ba da zasu kawo.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 23*

Se bayan sallar isha'i Bilal ya shigo gidan lokacin ina wanka saboda kitso da lallen da bamu gama da wuri ba se lokacin. Leda na ga ni da kuma ƙaramin kwalin biscuit a ajiye, sai bayan da na shafa mai na saka kaya kafinna nufi falo muka gamu a bakin ƙofa yana shirin shigiwa dan haka na juya.
"Ga shi nan na suna ne se ki bawa waɗan da za su zo da safe" ya faɗa yana nuna mun kayan daya ajiye ɗin.

"Har yanzu baka ce komai ba na ɗauka ma ai ka manta gobe ne sunan" na mayar masa da amsa ina kallon sa, se ya ce
"Kamar ya na manta go be ne suna?"
"Toh ai ban ji ka tambaye ni me zamu yi na taron sunan ba ne" na sake faɗa,
"To ni menene nawa a cikin abinda zaki yi na taron suna?" Ya faɗa, na kalle shi, da alama daga baya ya fahimci maganar da ya faɗa ba ta kamata ba se na ji ya kuma cewa
"Ina nufin ai taron ku ne na mata ni menene nawa a ciki?"

"Amma ko da taron mu ne na mata ai haƙƙin ka ne da ka bayar da abin da za'a ci da wanda za'a yi sauran hidima da shi" na faɗa ina kallon gefe.
"Halima, amma dai bakya buƙatar na sake maimaita miki abin da ya same ni ko? Ni a yanzu ba ni da wasu kuɗi da zan baki kiyi hidimar suna da su yanzu ta lafiya ta na ke yi dan ko da kika ga ina fita ba wai na gama warwarewa ba ne ba nan ƙafata kawai daurewa na ke yi ina takata jira na ke yi a yi salary na je asibiti na sosai a duba ni" ya faɗa. Na yi shiru kawai ina kallon sa, na tuna ranar da aka kai lefe na a leda, da ya zo yana lallaɓa ni har yana cewa na biyo shi bashi in sha Allahu zai biya ni da dozen ran da na haifar masa Bilal junior ko little Halims. Hannu biyu na saka na fara share hawayen da suka ɓalle mun, ya ja tsaki ya ce

"Daga magana se ki fara yi wa mutane kuka, gaskiya ta na faɗa miki, in ba sata kike sona yi na baki ba ya kike so na yi? Ni ban hana ki kiyi ba idan kina da kuɗi, amma ni dai bani da abin da zan baki. Ban da ma bakya tsoron Allah duk kuɗin da ake baki ki na ɓoye wa ni ban saka miki ido na ce ki bani ba shi ne har zaki iya buɗe baki ki tambaye ni wani abu. To ba ni da su, idan ma saboda yan uwana na da zasu zo ya sa ku dafa tsiyar ku ku cinye su ma za suyi na su a gida babu lallai ma kowa ya zo, Ni ta kuɗin ragon suna na ke yi ba wani can shirmen abinci ba" ya sa ke jan tsaki kafin ya fice daga ɗakin yana ci gaba da mita.

Haɗe kai na yi da guiwa na shiga risgar kuka na ma rasa takamaiman tunanin me zan yi? Me ya canza Bilal haka? Ko kuwa dama can haka ya ke ɓoye mun asalin halayyar sa ya yi se bayan da mu ka yi aure tukun na?

"Kiyi haƙuri uwata, wannan kukan ba ze kawo miki mafita ba sai dai ki sake jefa kanki cikin wata damuwar" Baba Jummai ta faɗa, ban san sanda ta shigo ɗakin ba amma yana yin yan da ta yi maganar a sanyaye jikina ya ba ni duk yan da akayi ta ji yan da mu ka yi da Bilal tun da ba a hankali yayi maganar ba kuma ƙofa a buɗe ta ke. Hannu na sa na shiga share hawayen amma suka ƙi tsayuwa, ta zauna gefe na tare da da fa ni ta ce,
"A kwana biyun nan na fahimci abubuwa da yawa dangane da zaman ku uwa ta. Ina yawan jin zancen mijin ki a bakin Hajiya tun ma kafin kuyi aure amma na ɗauka kawai dan basa son haɗin ku ne amma yanzu na fahimci sun fi ki gaskiya.
Magana ta domin Allah, a ɗan zaman da nayi da ku na fahimci mutumin da dangin sa duk yan da aka yi sun so ne su mayar da ke daddawar ɓurma, ke kuma So da ƙuruciya ya rufe miki ido kika kasa gane hakan".

"Kallon rashin fahimta nayi mata dan ban taɓa ji ba balle na san ma'anar kalmar da ta faɗa daga ƙarshe; ta ci gaba da cewa
"Ko a ƙauye ban taɓa ganin in da ake haka ba. Haihuwar fari dai ko mutum shi ya yankewa talauci cibiya yana hoɓɓasa da taimakon dangin sa ya yi abu na bajinta balle wannan yaron da duk wanda ya kalle shi ya san babu rashi a tattare da shi sai dai mugunta kawai ta hana ya yi miki abin da ya kamata. So ya ke yan da ya aure ki ki zame masa hannun jari komai iyayen ki su ringa ɗakkowa suna baki toh ni dai ba zuga ki na ke yi ba amma tun da sauran hasken rana duhu bai cimmiki ba ki ki farka ki kuma ƙwatarwa kan ki yan ci domin har idan kuka miƙe a haka tabbas ke zaki sha wahala musamman da ya kasan ce ya riga da ya gane son da kike masa ya fi na sa".

Mayar da kai na nayi ƙasa kawai ina sauraron ta, zuciya ta na so ta kama abin da take faɗa amma kuma wani ɓangaren ya kore maganganun nata. Kullum haka suke cewa Bilal ba ya so na ni kuma ba zan taɓa yarda da hakan ba. Abin da na jaddadawa zuciya ta shine Bilal ba shi da kuɗi sannan ya na da matsalar rashin iya tantance kalmomin da ya kamata ya yi amfani da su a magana shi ya sa yake faɗar kowacce irin magana ta zo bakin sa ba tare da ya taunata ba, wannan kuma ɗabi'ar mutane da yawa ce ba shi kaɗai ne haka ba. Wannan tabbacin na bawa kai na ya kuma kore tasirin da maganganun Baba Jummai suka so suyi a ƙwaƙwalwa ta.

"Bilal ya na so na, kuma na san ba shi da shi ne shi ya sa amma babu abin da ba ze yi mun ba Baba Jummai" na bata amsa ina murmushin da be kai zuci ba, ta ƙura mun ido kafin ta ce
"Yanda ki ke kyautata masa zato Allah ya bawa maraɗa kunya a sanda zai samu wadatar yi mikin" daga haka ta miƙe tana gyara goyon Al'amin kamar yanda Abba ya ce ba za'a saka masa wani sunan iyayi ba a kira shi da hakan. Tana rufe mun ƙofar na sake fashe wa da kuka, ni ya ke cewa ba ni da tunani kuma ba ni da tsoron Allah na ɓoye kuɗi ban ba shi ba.

Ƙarar waya ta ta sa na tashi na ɗakko ta, Anty Labiba ce. Sai da kirab ya katse wani ya sake shigowa lokacin na dai dai ta kaina kafin na ɗaga.
"Bacci kika fara ne?" Ta tambaya nasan kuma murya ta da ta ji ne dalili, na samu gangara dan haka na ce mata
"Eh wlh, na ga ji ne; na ɗan kishingiɗa ban ma san ashe bacci ya ɗauke ni ba"
"Sannu, toh ya kuka yi da Bilal ɗin?" Ta sake faɗa. Sabon kuka ne ya kusa ƙwace mun amma na danne shi da ƙyar na ce mata
"Ni fa ban yi masa magana ba Anty saboda kin ga fa wayar sa da aka ƙwace sun yi amfani da ita sun kwashe masa kuɗin account duka, kuma ba'a yi albashi ba ai se yaga rashin hankali na ma idan na yi masa maganar wasu kuɗi yanzu, sannan gashi ba shi da lafiya ko fita ba ya yi a zo a tara masa hayaniya a kai a babu daɗi".

"Kuma haka ne" ta faɗa amma se na rasa har ran ta tayi maganar ko kuma baƙar magana ta faɗa mun tunda na san halin ta sarai, a sanyaye na sa ke cewa
"Kawai a bar taron ko Anty tun da dama yawancin duk waɗan da zasu zo sun je tun muna asibiti wa su kuma sun zo nan gidan".
"Shikenan se ayi hakan, amma dai kin san yan Galadanci ko an ce babu taron suna ba zasu fasa zuwa ba kuma jiya Mama duk ta sake aika musu da yaji wanda ya manta ma kin ga an tuna masa, amma dai shikenan tun da mai gida ya ce ba za'a yi taro ba ai ba a zo masa gida ba bari na kira ta yanzu se a gaya musu a can gidan ku za'a yi sunan dama ai ba wani abu bane taron sunan a haɗu ne kawai a ci abinci ba lalali sai kina gurin ba".

"Aa fa Anty shi ba cewa yayi kar ayi ba" na yi saurin katseta kafin ta ƙulla wata maganar, ba ta ja zancen da tsayi ba ta mun sallama bayan da ta ce itama ai ba cewa tayi shi ya hana ba ta fahimci maganata kawai zasu yi taron su a gidan Mama shikenan. Ranar kasa bacci na yi har guraren ƙarfe uku sannan, maganganun Bilal suka yi ta mun yawo a zuciya, se da na ji kaina yana neman tarwatsewa saboda ciwo kafin na rarrashi kai na nayi bacci.

BILAL
A fusace ya fice daga ɗakin ya koma ɓangaren sa. A falo ya kwanta ya tada kansa da hannu biyu ya tafi tunani,
Waccen ranar da ya gamu da tsautsayi bayan sun rabu da Nasir ya koma gidan Hajja ya tarar da ita ta na shirin tafiya dubo Halima ya hanata, bayan sun koma ɗaki ta ke ce masa
"Amma yanzu idan ba mu je ba kar ace mun yi rashin kyautawa, musamman da Balarabiya ce matar ƙanin uban ta ta shigo har nan ta gaya mun kaga ai ko da kai ba'a kira ka ba ni ai an gaya mun ka bari kawai na je dai". Zama yayi ya kalallame ta da zance yana nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login