Showing 183001 words to 186000 words out of 257873 words
Ta maida mun da tambaya. Ƙasa na sauke kaina hawaye suka ɓalle mun Anty Labiba ta ce
"Toh Allah ya rufa asiri, daga yau zuwa gobe dai ki san me kike ciki gaskiya in za'a je kwaso kayan toh in ma ba za'a je ba dai mu sani da wuri" daga haka ta miƙe ta fita tareda Al'amin.
BILAL
Kasa zaune yayi tunda sukayi waya da Anty Amina da safe ta ce masa ta yarda zataje gidansu Halima amma tareda Yaya Aminu zasuje. Dukda ba haka ya so ba amma babu yanda ya iya, in dai Haliman zata dawo shine muradin sa a yanzu.
Sai da ya dai dai ci lokacin ya kamata ace sun isa gidan su Halimar har sun gama abinda ya kai su kafin ya kunna wayarsa dan tun farar safiya Zulaiha ta dira masa kira akan Kawunsu yana son ganinsa yau. Kasa gane wasu maganganu da take masa akan wai idan ya je duk abinda Kawun ya ce masa ya ce Eh ya sani, kawai ya katse wayar bayan ya ce mata bari zai kirata yanzu shikenan ya kasheta gaba ɗaya dan ya san kira zatayi tayi ba zata ƙyale shi ba.
Shi kam tun da aka ɗaura musu aure yake ganin sababbin halayenta da a baya bai san da su ba abun na ɗaure masa kai yana kuma bashi mamaki amma yanayin da yake ciki a yanzu ya sa baya bari abun ya dame shi a rai kawai yake mata uzuri koma menene ya san idan suka zauna zai dai daita.
Wayar na kunnuwa message ɗin Anty Amina ya shigo ya buɗe ya karanta 'wayarka a kashe, idan ka kunna ka sameni a gidan Hajja yanzun nan' abinda ta rubuta kenan.
Muƙullin mota ya ɗauka ya fita dukda bai so ta ce su haɗu a gidan Hajjan ba amma kuma ita ɗin dai dama ita zata gayawa Hajja zancen dawowar Haliman dan shi ba zai iya ba. Basu gama da Zulaiha ba ma balle ya sakw ɓallo wata rigimar.
Motar Yaya Aminu da ya gani ya saka ya ji tamkar ya juya amma ya makara dan suna tsaye a ƙofar gidan shi da Baba Sani suna magana, ya gama ƙunƙunin sa kafin ya fito ya shige cikin gidan ba tareda ya ko tsaya ya gaishe su ba. Yaya Aminu dake kallon sa ya yi ƙwafa ya ce
"Kana kallon yaron nan yanda ya wuce mu wato bamu ma ishe shi kallo ba kenan"
"Haƙuri za'a yi Aminu, yayan yau sai a barsu da halin su kawai amma ban taɓa zaton samun Bilal da irin haka ba, ni har na rasa abin cewa ma wlh gaba ɗaya" cewar Baba Sani. Yaya Aminu bai tanka ba ya juya suka shiga cikin gidan.
Daga yanda Bilal ya tarar da Anty Amina ya san cewa tafiya ba tayi yanda ake so ba. Gefe ya samu ya zauna kan kujera ya shiga gaida Hajja da tayi masa banza tamkar bata ji shigowarsa ba, ya juya kan Anty Aminan itama a ɗage ta amsa tana maka masa hararar da bai san dalili ba. Yaya Aminu da Baba Sani suka shigo kowa ya samu guri ya zauna.
Tunda Yaya Aminub ya buɗe baki ya ringa ji ina ma ƙasa ta buɗe ya shige ciki ko kuma ya ɓace ɓat daga gurin ko ya samu sauƙin tashin hankali, kunya da nadamar da suka masa rubdugu lokaci ɗaya. Zufa ta ringa keto masa, tsabar yanda ya duƙar da kai take wuyansa ya fara ciwo amma bai ko yi yunƙurin ɗagowa ya gyara zama ba balle yayi kuskuren haɗa ido da wani daga cikinsu.
A duk cikin maganganun babu abinda yafi ɗaga masa hankali irin cewar da Yaya Aminun yayi wai mahaifin Halima ne duk ya faɗa masa waɗannan maganganun, ya akayi Abba ya san alaƙar aa da Jalilah? Yanzu dama Halima bata rufa masa asiri ba kamar yanda yake zato duk ta faɗa musu komai?
Ya ringa share zufar dake keto masa, Yaya Aminu kuwa kamar zai aro baki tsabar masifa. Anty Amina sai ƙafa take jijjigawa dan tun a mota bayan sun baro gidansu Halima Yaya Aminun ya balbaleta da masifa akan me zata zubar masa da mutunchi ta sako shi cikin wannan maganar bayan ta san ta'asar da Bilal ɗin yake aikatawa? Ta sha mamaki har ta kasa cewa komai domin idan ba dan ta san babu wani dalili da zai saka Abban Halima yayi wa Bilal irin wannan ƙazafin ba da zata iya musawa. Ko da wasa wani ya ce mata Bilal ɗin mutumin banza ne haka zata ƙaryata domin dai duk mugun halin Hajja da son zuciyarta tayi ƙoƙari gurin basu tarbiyya ta san kuma da saninta Bilal ba zai aikata irin abun nan kuma tayi shiru ba.
Sai dai kuma Hajjan ta shayar da ita mamaki domin bata zaci irin amsar da ta ji daga bakinta bayan Aminun ya gama zazzaga masifarsa ba. Kuka Hajjan ta fashe da shi tana cewa
"Wannan yarinya Halima ban san me take nema damu ba, yanzu a duniya ta rasa sharrin d zata bibiyi Bilal da shi sai ta masa ƙazafin nema mata? Wlh Allah ya isa tsakaninmu da su kuma maganar nan ba zamu barta ba sai munyi shari'a da su ba ta isa ta ɓatawa ɗana suna a banza ba sai naga uban da ya tsaya mata".
A zuciya Yaya Aminu ya ce
"Wlh Hajja kiji tsoron Allah, ai duk abinda ya zama kece sila domin ya sani duk aje a dawo zaki san yanda zakiyi ki kare shi. Tun ba yanzu ba duk iskancin sa yakeyi da yanda ya ringa azabar da yarinyar nan kina kallo amma baki taɓa tsawatar masa ba sai ma ƙara zugashi da kike yi kin ɗauki karan tsana kin ɗora mata saboda dama ba dan Allah kuka ƙulla auren ba kin so iyayenta su zame me muku bayi sai yanda kukayi da su da dukiyar su da baki samu haka bane shine kika uzzuraqa yar su ba kalar uƙuba da jidalin da baku mata ba amma ta jure take zaune da shi.
Saboda shegen ƙwadayi da son abin duniya ya rufe miku ido baki taɓa tunanin a ina ya samu kuɗi lokaci ɗaya da yake buƙatu da suka zarce samunsa ba, ke dai kawai tunda yana kawo miki baki damu da ina yake samowa ba. Wlh da ace Mahaifin mu zai dawo doron duniya sai yayi ala wadai da irin tarbiyyar da kika ɗora yaran nan a bayan babu shi.
Abin takaici abin baƙin ciki ɗan ki ya zama karuwa, bama shi yake neman matan yana kashe musu kuɗi ba saboda mutuwar zuciya shi yake biyawa mace buƙata tana bashi kuɗi wlh tallahi kayi asara Bilal ka kuma zubar da ƙima da mutunchinka a idon duk wanda suke maka kallon mutumin kirki".
"Idan baka daina jifan ɗana da mugayen kalamai ba Aminu wlh idan na tashi kai ƙara harda kai zan haɗa, dama ai ba ƙaunar mu kukeyi ba. Tunda ubanku ya mutu aka raba gado a cikinku waye ya sake waiwayarmu sai yau da yake sharri ne shine zaka zo kana tada jijiyoyin wuya kana faɗar maganganu son ranka toh wlh ka kiyaye ni" Hajja ta taso masa. Sai lokacin Baba Sani ya ce
"Wannan shine babbar matsalarki Hajara ƙin gaskiya kuma ban san lokacin da kika zama haka ba"
"Eh ai dama zaka faɗi haka tunda ka gama lasa a nan yanzu ka koma gindinsu zaka cigaba da maula a haka dai zaka ƙare karen farauta kawai" ta zaburowa Baba Sanin.
Aminu ya miƙe yana cewa
"Tun da sauran mutunchi ka rubuta takarda ka aika musu da ita dan mahaifinta ya ce idan ka bari satin nan ya wuce baka sakar masa yar sa ba ƙarar ka zaiyi, wlh kayi asara, kuma haƙƙin wannan yarinyar kaɗai idan kayi wasa ba zai barka ka zauna lafiya ba domin karamchi ba kalar wanda ita da iyayenta basu maka ba amma ka butulche musu ka zaɓi hanyar banza ta saɓawa ubangiji" daga haka ya sa kai ya fice daga falon ba tareda ya saurari Hajja dake zaginsa ba.
Baba Sani ma tashi yayi ya bi bayansa ba tareda ya sake cewa komai ba. Suna fita Hajja ta miƙe ta rufe ƙofa harda saka sakata kafin ta koma ta zauna tana kallon Bilal da yake nan zaune kamar mara rai ta ce
"Menene gaskiyar abinda suka faɗa?"
Sai lokacin ya ɗaga kai amma ba duka ba ba tareda ya kalleta ba ya ce
"Kiyi haƙuri Hajja"
"Ba haƙuri zaka bani ba Bilal cewa nayi ka gaya mun gaskiya akan maganar da suka faɗa, da gaske ne matan banza kake bi a waje ko sharri sukayi maka?"
Sai da ya rintse ido kafin ya ce
"Guda ɗaya ce, Jalilah. Kuma wlh ba abinda suke zato bane kawai yan ƙananan abubuw....." Bai kai ƙarshen maganar ba ta katse shi ta hanyar sharara masa marin da sai da yayi baya saboda bai shirya masa ba. Kuka mai haɗe da gunji ta fashe da shi tana cewa
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 47*
"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?"
Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce
"Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce
"Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa a gabansa baka ce ƙaryar aka maka ba?
Karka ɗauke ni shashasha, ko da kaga a gabansu na kareka ina sane, na kuma san uban Halima ba zai maka ƙarya ba idan ma ƙaryar yake babu yanda za'a yi Aminu ya yarda da maganar nan ba tareda ya samu hujja ba dan ni na raba ku da su suna ƙaunar ku ba yanda za'ayi kuma a haɗa baki da shi ayi maka irin wannan ƙazafin" sai ta rushe da kuka tana cewa
"Ba yanda banyi akan ka auri yarinyar nan ba amma duk in na tayar da maganar sai ka kawo wani uzurin ka kauce alhalin ita burinta kenan kuyi aure yanzu da ace tun farko auren kukayi wane ɗan iska ne zai samu abun faɗa akanmu?
Amma yanzu ka lalata mana zuri'a ka kuma janyo mana abin gori a gari wannan wane irin tozarci ne? Tsabar lalacewa kuma har gidanka na aure kake kai macen banza ai dole Halima ta bar gidan baiwar Allah muna nan muna ɗaukar haƙƙin ta ashe ita kaɗai ta san baƙin cikin da take ƙunsa bayan gallazawa da azabtarwar da kake mata".
Yanda ta dage tana masa faɗa ba shi ba hatta Anty Amina ta sha mamaki domin ba zaka taɓa zaton Hajjan da take ɗaure masa ƙugu yana duk iyashegen daya ga dama bace wannan yanzu ta shiga tashin hankali har da kuka akan maganar da ta ji ba.
Shi dai Bilal kansa na sunkuye yana tsiyayar hawaye ya kasa sake cewa komai, Anty Amina ta kalli Hajja ta ce
"Duk wannan maganganun da kikeyi ihu ne bayan hari Hajja domin ke kika bashi ƙofa tun farko kika bashi goyon baya akan duk abinda yake aikatawa. Tun farkon ganina da yarinyar sai da na ce bata mun ba,
Zubin ta da wayewarta tafi ƙarfin kula namiji irinsa ga uban hidimar da take masa sai dai idan tana da wata manufa akan hakan. Amma me kika ce? Ɗan ki ya isa kowacce mace ta so shi ta kuma yi sha'awar aurensa, babu tunanin komai ke da shi kuka mayar da ita saniyar tatsa tayi ta kashe muku kuɗi, kin san ba shi da wani dalili na zuwa Abuja amma kullum yana hanyar can idan anyi ƙoƙarin nusar dake ki ce muma hassada zamu masa.
Ko sau ɗaya baki taɓa tunanin ita ɗin a ina take samun kuɗin da take bashi sannan aikin me yake mata da zata ringa masa irin wannan wadaƙar kamar a bishiya take tsinko kuɗin.
Na sha miki magana Hajja, babu inda son zuciya zai kaiki ƙarshe sai dai ya janyo miki ɓacin rai amma baki ji ba tun akan Hafiz, yanda kika ringa biye masa kina zubar da girman ki kuna roƙon yaron nan har sai da kuka ƙure shi ya janye jikinsa sannan ya sake kamo muku wani kifin kuka juya kanta. Ki godewa Allah ma da ya zama ƙwadayin nasa iya bin mata ya kai shi ba maza ba da..."
"A'uzubillahi wace irin magana ce wannan mara daɗi Amina? In sha Allahu ba zanga wannan baƙin cikin a zuri'ata ba" Hajja ta katseta. Anty Amina ta taɓe baki ta ce
"Ƙwadayi da son duniya su suke kai mutane ga halaka sai daga baya su zo suna dana sani mara amfani, yanzu dai ƙwai ya fasu kowa ya ji warin, Halima kuma da a kullum baku da abin zagi da aibatawa sai ita kinga irin abinda ta shanye ta rufawa ɗanki asiri.
Ita kuma wacce kike haƙilon ya auro mikin ku cigaba da shan romo anyi walƙiya yanzu kun san wacece ita. Kuma na san harda haƙƙin Halima da ya fara bibiyarku, Fatana ɗaya ubangiji ya rufa maka asiri ya sa ita wacce ka wulaƙanta uwargidanka akanta ka kashe duk kuɗin haram ɗin da ka samu akanta da iyayenta karta zame maka kara da kiyashi dan wlh jiki na bai bani kayi dacen mace ba" ta ƙarasa tana miƙewa tsaye da alama ta gama abinda ya kawota.
Daga Hajja har Bilal ɗin kallonta kawai suka ringayi har ta nufi ƙofa kafin ta tsaya ta waiga ta kalle shi ta ce
"Karka ɓatawa kanka lokaci kace zaka koma ka bawa Halima haƙuri ko iyayenta domin ba zasu saurareka ba. Ka kuma fi kowa sanin mahaifinta kaifi ɗaya ne, yanda ya toshe kunnensa a sanda kowa yake faɗin baka dace da yarsa ba ya ɗauke ta ya baka haka a yanzu da ya buƙaci ka sakar masa ita bana zaton ko duniya zata taru akansa akwai wanda zai saka ya haƙura ya barka da ita. Yanda ya ce ka kai masa takardar sakinta salin alin kayi idan kuma ka shirya tonuqar asirinka wa duniya baki ɗaya ne toh kayi gardama" daga haka ta buɗe ƙofar ta fita ta barsu.
Hajja ta kalle shi ta ce
"Ko me za'ayi karka kuskura ka saketa kaji na gaya maka". Sai ya ɗaga kai da sauri ya kalleta, sai kace ba Hajjan da bata da wani buri illah na ta rabashi da Haliman ba amma kuma bai san dalilin ta na canza ra'ayi a yanzun ba dan haka ya ce
"Amma me yasa kika ce haka Hajja bayan baki da wani buri illah na ganin na rabu da Halima a yanzu?"
"Ko a da ina so ku rabu yanzu na canza shawara. Ba zaka saketa ba, saboda idan suka samu abinda suke so zasu tona maka asiri ne su watsa labarin a duniya, idan kuwa kuna tare dole su yi shiru domin sirrinka sirrin yar su ne idan kuma suka fitar ba iya kai kaɗai zasu zubarwa da mutunchi ba" Hajjan ta faɗa. Ya buɗe baki da niyyar magana dai dai lokacin Abubakar ya shigo daga tsayen da yake ya ce
"Tamkar ba ke kika gama kuka yanzu kina masa faɗa ba Hajja. Wai menene jin daɗin ki akan rayuwar ƙunci da baƙin cikin da Halima takeyi a gidan sa? Me yarinyar nan ta tsare miki?"
"Ai duk ita ce sila, idan da ya samu abinda yake buri daya aureta a ina zai je ya haɗu da wannan tsinanniyar yarinyar harta koya masa abinda ba halinsa ba? Dan haka yanda ta zama silar ɓacin sunan sa haka zasu zauna tare su kwashi baƙin ciki ba ta isa ta rabu da shi ba wlh" Hajjan ta bashi amsa sai Abubakar ya watsa hannu irin ko oho ɗin nan ya ce
"Ai kuwa sai ku shirya kwasar baƙin ciki ke da shi domin ko yaƙi Allah sai ya sakar musu yar su, kuma tun yanzu ku fara tattara duk abinda kuka san kunci na waccen matar dan wlh ba zata barka ba, kada ka ɗauka ka fita wayo, ka yaudareta kayi aure sannan ka salwantar mata da dukiya kaci banza na san kallonka kawai take kuma zata yi lokacinka nan ba da daɗewa ba".
Sai da cikin Bilal ya juya ya zurawa Abubakar ido zuciyarsa na bugawa fat fat kamar zata huda ƙirjinsa ta fito. Yanda Abubakar ɗin yake magana kamar yana da masaniya akan gidan Jalilah daya siyar da shagon ta da yake shirin siyarwa a yanzu.
Ya sadda kai ƙasa yana jin Hajja na cewa
"Idan ta fasa yin lokacinsa bata ƙaunar iyayenta, roƙon ta yayi ko me? Dan Allah karta fasa ta kuskura ta zo nan ta ce zata yi mana wani hauka taga yanda akeyi shegiya karuwa mai lalata yaran mutane" ta cigaba da sababi.
Abubakar dai fita yayi ya basu guri Bilal ɗin ma jiki a mace kamar wanda ya sakko daga iskokai ya miƙe da niyyar barin falon. Hajja ta ce
"Ka dai ji abinda na gaya maka ko kotun ƙoli zasu kaika kada ka kuskura ka saki Halima, sannan itama waccen ta tare a satin nan dan karma tsautsayi ya saka magana ta fita su ce wani abu dan wlh basu isa ka gama wahalta musu wani abu ya gifta su ce za'a warware auren nan ba ko zaka saketa sai mun fanshe wahalar da ka musu sun maido maka da komai tukunna".
Shi dai ya fita mamakin Hajja na neman kashe shi. Sai kace wahainiya. Kwantar da sit yayi bayan da ya shiga mota ya kwanta haɗi da rufe idonsa yana jin ina ma yana da damar maido da lokaci?
Ya daɗe yana hasashen irin