Showing 162001 words to 165000 words out of 257873 words

Chapter 55 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

500

sheƙe ayarsu a titi ya aura? ko kuma wata daban?
Zuciya ta raya mun 'ko kuma duniyar sa ba? Ko wacce ya kaini gidansu gaisuwa. Duk a rana ɗaya na sansu ranar da na bankaɗo sirrinsa da Jalilah ƙila ɗaya daga cikinsu ya aura. Sabbin hawaye suka ɓalle mun, bai ko bani damar yi masa tambayoyi da yawa da suke cunkushe cikin zuciyata ba kafin na baro gidan sa har a yanzun kuma daya dawo daga yanda ya ɓullo na fahimci baya buƙatar warware ƙullin baya kawai so yakeyi mu ɗora sabon babi.

Da hannu biyu na rufe fuskata ina jan kuka, na rasa tunanin daya kamata nayi, mai yasa Bilal zai mun haka? Duk haƙurin da nayi duk juriyar da nayi akan lamuransa lokaci ɗaya ya rasa irin sakayyar da zaiyi mun sai wannan?
Jin ana ƙwanƙwasa ƙofa ya saka na shiga goge fuskata da sauri dan zaryar da Zainab take mun na san da wahala idan ba CID Mama ta sakata ba, kuma daga yanayinta tun jiya da yanda Abba da kansa ya ce na fita gurin Hafiz ɗin na tabbatar ma abinda na jima ina ɓoye musu ya rigada ya bayyana ma'ana ya faɗa musu komai akan Bilal da Jalilah ga kuma wata sabuwa data ɓullo yanzu.

Ɗaga murya nayi na ce ta shigo bayan da na tashi zaune na jingina da Gado. Ganin Abba ya saka zuciyata ta shiga bugawa da sauri da sauri, haka nan ban tuna sanda Abba ya shigo ɗakina ba tun ma zamanin yammatanci balle yanzun na san dole abu ne me muhimmanci ya kawo shi. Kan bedside drawer ya zauna ba yabo ba fallasa yana amsa gaisuwar da nake masa, muka yi shiru kafin can ya ce

"Kin san me yasa na biyo ki har ɗaki?" Na girgiza kai alamar aa, ya ce
"Saboda ki gane muhimmancin maganar da nake so mu tattauna dake". Bugun da zuciyata keyi ya saka tsananta har wani ɗumi numfashina ya ɗauka gaba ɗaya a tsorace nake ban san wace magana zai mun ba dukda bana raba ɗaya biyu akan Bilal ce amma me zai ce mun?

"Nasan baki manta ba ni nayi tsaye na goya miki baya kika auri yaron nan dukda yanda mahaifiyarki da yan uwanta har ma da nawa yan uwan suke ganin rashin dacewarki dashi. Ki sani, abu biyu zuwa uku na duba da har na amince da aurenku. Na farko, a iya binciken da nayi akansa ba'a same shi da wani mugun hali wanda zai saka a ƙi bashi aure ba, dai dai gwargwado ya samu shaida ta mu'amala kuma ana kyautata masa zato akan addininsa. Abu na biyu soyayyarki gare shi, yanda kike mu'amalantar sa ya tuna mun yanda muka rayu da mahaifiyarki a lokacin da ban ma kai shi ba domin ni sanda na aureta banida da ko tartibiyar sana'a amma a hakan ta ƙaunace ni har kuma Allah ya kawo mu matsayin da muke kai a yanzu.

Na kyautata masa zato kuma son da nake miki da burin ganin na samar miki da farinciki a rayuwarki ya saka na amince na bashi aurenki bisa kyakkyawan yaƙinin zai riƙe mun ke amana amma baki ɗauki dogon lokaci a gidan aurenki ba na fara dana sanin biyewa zuciya, a ƙoƙarin son samuwar farin cikinki har hakan ya rufe mun ido na kasa hasaso idan aka samu akasi wani hali rayuwarki zata shiga?

Duk da haka ban sare ba, na cigaba da yi muku addu'a na kuma ringa tallafa miki a ganina raguwar ɗawainiyar zata taimaka gurin samun dai daito a zamantakewarku musamman tunda na fahimci halayya da kuma ɗabi'ar mijin da kika zaɓi rayuwa dashi. Ko da baki taɓa zuwa kin faɗi laifin sa ba amma komai a bayyane yake, kuma wannan hujjar na riƙe a duk sanda mahaifiyarki ta so yin bore ko kawo hargitsi cikin zamanki da shi na kan nusassheta da cewar a gurinta ne take ganin gazawa ko matsi a zaman da kikeyi amma ni a guri na lafiya kike zaune domin baki taɓa zuwa kin kawo ƙara ko kin faɗawa wani damuwarki ba na kuma san ba dan baki da damuwar bane sai dan halin zurfin ciki da kuma soyayyar dake wahalar dake kin kuma yarda zaki rayuwa dashi cikin kowanne irin yanayi sa'annan akwai nauyi da gudun kar ayi miki dariya sanin kowa sai da ya ce miki kar kiyi kikace kinji kin gani.

Duk da dai da fari na ɗauka rashin wadata ne sanadin abubuwan da suke wakana a tsakaninku shiyasa ban taɓa cewa komai ba nake kuma iya bakin ƙoƙari na gurin ganin na samar miki da abinda ya gagara baki sannan kuma na hana mahaifiyar ki ko wani nata duk sanda sukayi yunƙurin ɗaukar wani mataki akan zamantakewarku amma daga baya idona ya buɗe na kuma fahimci komai, tsantsar son kai da mugunta ce kawai take damun sa ba wai babu bace.

Ina so san cewa ke kike son Bilal Halimatu kuma ko da ace yana sonki to ki sani bai kai ko kwatan soyayyarki gare shi ba. Iya zamanki a gidan nan daga zuwanki zuwa rashin lafiyar da kikayi kawo yanzu ta isa hujjar da zakiyiwa kanki Hisabi ba tareda wani ya ce miki komai ba, idan ba dan na samu tabbaci daga wanda ba zai mun ƙarya ba da banzan taɓa yarda da cewar da igiyar aurensa akanki yayi miki irin wannan tozarcin ba".

Sai lokacin na ɗaga kaina na kalle shi jin kalmar tozarci daya faɗa idanuwana basa ko gani da kyau saboda hawayen da suke cikinsu, ya gyaɗa mun kai cikin tabbatarwa ya ce

"Babu wani namiji da yake ganin matarsa da ƙima da zaiyi kwatankwacin abinda Bilal ya aikata miki. Da kansa ya ɗakko ki ya kawoki gidan nan saboda ya nuna miki cewar ke bakya gabansa, a sanadin sa kika kusa rasa rayuwarki kuma har kikayi jinya kika gama shi ki wani nasa babu wanda ya tako yazo yaga ya kike sai surutu da maganganun da suka ringa yawo da su suna faɗan abubuwa marasa daɗi akanki, duk wannan bai isa ba tunda ya fahimci har yanzun kina yawo cikin duniyar mafarkinki shiyasa ya ɗaura aure abunsa da wata.

Kin san duk me yasa na tsaya ina miki wannan dogon bayanin kafin na faɗa miki ainihin abinda ya kawo ni?" Cikin kuka na ce
"Aa Abba" ya gyara zama ya ce
"Saboda na lura baki da tunanin kanki ba kuma kya gane komai sai abinda zuciyarki ta aminta dashi. Tuntuni na tsammaci ganin sauyi tattare dake amma akasin haka na lura a maimakon sauƙi kullum al'amuranki ƙara lalacewa sukeyi. A cikin zuciyarki nan na tabbatar duk lokacin nan kina jiran Bilal ya zo ya lallasheki ya faɗa miki maganganu dai dai da waɗanda kike so kiji daga nan ku shirya ku koma shiyasa kika zaɓi haɗiye baƙin cikinki ke kaɗai kika ƙi gayawa kowa dan kar hakan ya saka a baki shawarar ki haƙura dashi ko?"

Kai na girgiza masa alamar Aa, ya sake cewa
"Eh mana, Tunaninki kenan saboda har yanzu ƙwaƙwalwarki bata hasko miki illar rayuwar da kike ciki ba. Halima babu iyayen da zasu so yar su tayi aure ta dawo sai dai idan abun yafi ƙarfin su domin burin kowanne iyaye ne yayansu suyi aure a inda zasu rayu cikin aminci da walwala da kuma mutuntaka wanda gaba ɗaya kika rasa. Ko wanda bai sanki ba kuka haɗu a hanya ya kalle ki in dai maganar nutsuwa akeyi ta bayyana ƙarara baki da ita. Ko shekara talatin baki cika ba kin ɗorawa kanki hawan jini harda kumburin zuciya akan namijin da kina raye ma ya wofantar dake ya auri wata balle kuma ki kashe kanki saboda dashi bana zaton ko a addu'a zai ringa tunaki.

Ba shawara nazo baki ba, kamar yanda na tsaya tsayin daka na haɗa ki da shi haka yanzu nake so ki rama mun nima ki faranta mun zuciya ta hanyar rabuwa dashi. Da na so na kira shi da kaina ya bani takardar sakin sai dai kuma na tuna bani da sauran mutunchi a idon sa ko na kira shi ma ba zuwa zai yi ba tunda mun sha haɗuwa a ƙofar gidana ma ya kalle ni na kalle shi ya wuce ba tareda ko ci kanka ya ce mun ba balle kuma in ɗaga waya na kirashi ai sai abunda kuma na gani. Dan haka ko ki kirashi ko ma duk ta yanda kika san saƙo zai fi saurin isa ki gaya masa kada ki kurkura satin nan ya ƙare kina cigaba da amsa sunan matar sa a cikin gidan nan".

Tunda ya fara maganar kuka na ya tsaya tsak, yanda kasan zuciyata zatayi tsalle ta fito haka naji sanda ya ce wai Bilal ya rubuto takardar saki ya kawo mun, ganin ya miƙe tsaye alamar ya gama magana daƙyar na lalubo yawu na jiƙa maƙoshi na kafin na samu na fizgo maganar data tsaya mun a wuya na ce
"Abba amma da wasa kake yi?" Murmushin takaici yayi kafin ya ce
"Dama ina wasa dake ne Halima?" Daga haka ya saka kai ya fita ba tareda ya sake ce mun komai ba.

Zumbur na miƙe kamar wacce aka tsikarawa Allura na shiga zagaye ɗakin ina nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, nayi zagaye ya kai hamsin kafin na zube gefen gado lokaci ɗaya na fashe da kukan rashin mafita. Ya Abba zaiyi mun haka? Na ɗauki tsayin lokaci ina kukan kafin na fahimci hakan ba zai sama mun mafita ba, falo na fito, Mama, Mu'azzam da Imam suna zaune gabansu ƙaton tray da gasasshen kifi suna ci suna hira cikin nishaɗi irin su basu da wata matsala a rayuwarsu. A gaban Maman na zube na kama guiwarta lokaci ɗaya na fashe da kuka har jikina yana jijjiga tsabar yanda nake janyo kukan tun daga can ƙasan raina, ta sauke Sharifa daga kan cinyarta jiki na tsuma itama ta kamoni tana cewa

"Menene?" Ban iya ce mata komai ba in banda kukan dana ƙara ta hanyar ɗaga murya, Mu'azzam ya ce
"Wlh sai Allah ya saka mata wannan faɗuwar gaban da kike sakata, banda tsabar iskanci kawai idan kika bushi iska sai ki hau kuka duk ki ɗagawa mutane hankali ke ko shekarunsu bakya dubawa? Ai gasu nan kema kin haifa idan da daɗi abinda kikeyi zaki ji wata rana" yayi tsaki ya miƙe zai bar gurin dai dai nan Abba ya shigo falon, ban yarda na kalle shi ba ina jin sa yana cewa Mu'azzam ɗin
"In sha Allahu yaranta ba zasu mata haka ba ita ma ɗin da takeyi mun yafe". Ya ƙarasa ya zauna kan kujera ban saki Mama ba haka ban daina kukan ba sai da ya daka mun tsawar da tunda nake ban taɓa jin ko wani can a waje yayiwa ba balle mu ɗin, cikin tsawa yace

"Saketa ki tashi daga nan sakaryar banza kawai wacce bata san ciwon kanta ba" ba shiri na saketa na mataa gefe na haɗe kai da guiwa kamar marainiya na cigaba da kuka, Mama ta ce
"Wai me ya faru ne Abba wlh duk ta tsinkar mun da zuciya".

"Saboda na ce ta karɓo takardar sakinta gurin wancan yaron ko?" Ya bata amsa, sai ta dafe ƙirji ta ce
"Kai wa ya aike ka?" Ya bita da kallon mamaki da kuma rashin fahimta sai ta ce
"So kake ta saka ka a bakin duniya tace kai ka kashe mata aure? Ai da kayi shawara dani da baka fara wannan ɗanyan aikin ba". Tsaki yayi ya miƙe yana cewa
"Ni dai na faɗa mata, kuma dama gobe in Allah ya kaimu ta wuce ta karɓo posting letter ta idan ba haka ba wlh Halima zakiga other side of me wanda baki sani ba tunda naga alamar sako sakon da ake miki ya saka yanda kika mayar da kanki shashasha kowa ma kike so ki mayar dashi haka" ya wuce ɓangarensa. Mama ma miƙewa tayi bayan da tace

"Allah ya rufa asiri toh" Imam ko yanda ka san baya falon kifin sa kawai yake ci yana bawa Sharifa, da yaga kukana zai cika masa kunne ma remote ya ɗauka ya ƙara volume ɗin Tv, haka na ja jiki na sake komawa ɗaki na cigaba da kuka kamar wacce aka ce za'a fillewa kai gobe. Sai da na gaji kafin nayi shiru ina jan ajiya zuciya, ciwon da kaina yake mun kuwa ba zai mislatu ba har wani ɗin ɗin nake jin ƙara kamar ta agogo a cikin kan nawa.

Dare ya tsala kowanne mai rai dake da nutsuwar zuciya yana kwance yana bacci amma banda ni ina dai kwance akan gadon ina juyi daga wannan kusurwa zuwa waccen na gagara bacci haka nan ƙwaƙwalwata ta kasa bani haɗin kan da zanyi tunani mai ma'ana da zai sama mun da mafita gashi, da ina da tsarki ne ma sai inyi sallah ko zan samu nutsuwa. Ina tunanin firgici ne ya matso mun da period dan a lissafi sai nan da kusan kwana huɗu zai zo amma ɗazu ina shiga banɗaki na ganshi.

Bansan me zanyi ba, umarnin Abba yayi mun tsauri, dukda cewar ni a karon kaina har yanzun ban yanke shawara dangane da yuwuwar cigaba ko ƙarewar zamana da Bilal ba na bar hakan ne tukunna har sai ni da shi mun zauna munyi magana ta gaskiya daga nan ne zan yanke hukunci akan abinda ya kamata nayi amma shi Abba kai tsaye ya yanke nasa hukuncin yanzu yaya ake so nayi?
Idan kuma ya zama duk abinda Hafiz ɗin ya faɗa ƙarya ne ko ma duk abinda ya faru tsakaninsa da Jalilan setup ne fa tunda ai da bakinsa ya ce basu san ya sani ba toh ta ina ya sani kenan bibiyarsu yakeyi idan kuma haka ne dama akwai abinda yake so ya cimma shiyasa har yake binsu kenan?

"Amma kuma wace riba zai ci idan yayi hakan?" Ni da kaina na jefawa kaina tambayar da bani da amsarta. A zahirance ma bani da wata hujja da zan jefa masa kowanne irin zargi domin Bilal bashi da wani abu da har zai saka mutum irin Hafiz yayi framing nasa. Kuma ko da ace da gaske shirin ne idan dama ba halin sa bane ko yana so ai babu yanda za'ayi ya biye mata tunda babu inda naga alamar ta masa dole a cikin hirar su duk ba wannan bama ai da ba zai haɗa ta da danginsa ba har tazo duba mahaifiyarsa da bata da lafiya.
"Ta yuwu ma ita ya aura tunda tana da kyau kuma tana da kuɗi dama kuma ai ya ce shi baya tarayya da mutumin da ba zai ƙaru da shi ba" na faɗa a fili. Sababbin hawaye ne suka ɓalle mun na koma na kwanta ina jin ƙuna a ƙirji na, na ringa tuna fuskarta haɗuwar mu a asibiti fara kyakkyawa mai diri duk hassadar mutum bai isa ya kushe halittarta ba. Ji na ringayi tamkar numfashi na zai tsaya har saida na tashi zaune, abunda na tabbatar shi ake kira da kishi ya turnuƙeni, lokaci ɗaya kuma hotunan waccen ranar suka shafe na kyakkyawar fuskar Jalilah da nake gani, muryoyin da sukayi musaya suka shiga mun amsa kuwwa a kunne, hannu biyu na saka na toshe kunnuwana na fashe da kuka mai sauti.

BILAL
Hankalinsa ya kwanta yanzu saboda ya samu nutsuwa akan kokonton dake neman hargitsa masa lissafi akan Zulaiha. Dukda dama zuciyarsa bata yarda zai samu akasin abinda yake tsammani daga Zukaihan ba sai dai canjin halayyarta na lokaci guda ne ya bashi tsoro, amma zuwan da yayi jiyan da hirar da sukayi ya kwantar masa da hankali dan har haƙuri ta bashi sosai kamar zatayi kuka akan ɗaga masa muryar da tayi a waya. Sun daɗe suna hira sosai irin yanda suka saba, da zai tafi ya shiga suka gaisa da Ummansu, har ya miƙe ta dakatar dashi tana cewa

"Dama yan uwana ne sukayi magana akan suna so suje ganin gurin da zata zauna". Kansa na ƙasa dan bala'in kunyarta yakeji har mamaki yake yanda bayajin nauyin Mamansu Halima irin yanda yakejin ma Umman Zulaihan.

"Dama zuwa wani satin nake so idan an ƙarasa gyaran gurin nayi magana je a gani" ya bata amsa, ta muskuta tana gyara hijabinta tace
"Toh madallah, kasan da yake sune jikokin ya mace na farko ni a gidanmu da za'a fara aurarwa duk yayyena matan yayayensu maza ne shine fa kowa hankalinsa yana kan bikin nan, ga zancen kawo lefe ma kasan abunka da masu ƙaramin ƙarfi sai anyi tanadi ya kamata idan za'a zo afaɗa da wuri saboda a tanadi abun tarbar baƙi, su dai na Nuratu sun ce Asabar ta sama nan da sati biyu kenan da kawo lefen da tariya duk rana ɗaya dan ya ɗauke ta ma sunje gurin tela an gwadata a ɗinke zasu kawo abunsu. To itan ma ya kamata kaga mu sani in kuma kuɗin za'a bayar ma duk kaga sai a san shirin da ake ciki" ta ƙarasa tana sosa kai kamar wata mara gaskiya.

Zama yayi sosai dan da a tsugunne yake ya ce
"Ai Umma munyi magana da ita tace kince ba sai anyi lefe ba kawai ayi mata kayan ɗaki da kuɗin". Yanda ta zaburo tace
"Inji ubanwa? Yaushe mukayi haka da ita?" Sai da abin ya bashi mamaki domin a iya saninsa da ita kullum muryarta a ƙasa take fuskarta washe da fara'a. Itan ma da sauri ta gyara zama bayan da ta fahimci abinda tayi ta shiga kame kame tana cewa

"Na rasa yaushe Zulai ta koyi magana biyu, ni bamu taɓa zancen lefe da ita ba, Mijin Nuratu dai da ya ce ko yayi mata kayan ɗaki a madadin lefen to kuma yayyina suka ce Aa ai ba'a haka, za'a mata daidai ƙarfin mu duk abinda bai masa ba daga baya ya sake mata toh ni dai iya zancen da nasan anyi kenan shine ta canza magana ashe ta gaya maka haka ni yarinyar nan ganinta nake kwana biyu ma kamar wacce iskoki suke taɓawa yanzu zata birkice ta fara masifa abunda ba halinta ba ko kuma duk zullumin auren ne ban sani ba".
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login