Showing 96001 words to 99000 words out of 257873 words
kamar zasu rufe ni da duka. A gadarance ta ce mun
"Da alama kin manta muna zaune a nan ko Halima?"
Duk da na fahimci in da maganar ta ta dosa dan banga ko ledar ruwa an ajiye musu ba amma na ce mata
"Na san kuna nan mana Anty"
"Iskanci ne wato ya saka aka barmu a gantale ko kuwa jira ake mu fito mu ɗibi abincin da kanmu?" Anty Hauwa, ƙanwa ce gurin Hajja abokanan wasa suke ta faɗa. Se na miƙe ina cewa
"Kuyi haƙuri, ina ga sun shafa'a ne bari na je na musu magana, yanzu za'a kawo muku" na fita daga falon ina ji suna bi na da ƙananun maganganu. Rasa ta yanda zan tunkari Anty Labiba na yi dan haka na ja Amal gefe na ce ta ɗauki manyan kuloli a kitchen ta zuzzuba abinci idan Anty Labiba ta tambaye ta ta ce ƙawaye na da zasu zo an jima za'a ajiyewa se ta kai mun ɗakin Bilal ta ajiye. Shiru shiru kusan minti goma sai gata, da sauri na tare ta ina tambayar ina abincin ta ce mun Anty Labiban ta ce ba ze ƙare ba duk wanda ze zo ma ze samu. Ban ji daɗi ba, na ringa jele tsakanin falon da ɗaki amma na kasa yi mata magana. Bana so na yiwa wani babba maganar ta ce na kai ƙarar ta ko wani abu amma kuma a take taken ta naga alamar ta shirya yi musu wulaƙanci ne kawai tun da ai taga zuwan su har gaisawa suka yi kuma ita idan ta haihu naga ai tun ma kafin a fara rabawa mutane abinci take ware na dangin mijin ta.
Hansa'u na jawo akan ta yiwa Anty Labiban magana ta ce wlh babu ruwanta. Na kasa tsaye na kasa zaune ga Ummi tsaye bakin ƙofa na san kuma ba ze wuce sake aiko ta akayi karɓar abincin ba kuma tana ji Anty Labiban na yekuwar idan da me buƙatar ƙarin wani abu ya zo ya karɓa, ina kallo ta jinjina kai irin zata je ta kai rahoto ta juya se kawai na yanke shawarar yin shahada na mata magana. Ina matsawa gurin na jiyo Mama Sa'a matar kawun su Mama tana tambayar ta an kai wa dangin miji na abinci kuwa?
Anty Labiban ta ce
"Aa ba'a kai musu ba, na manta". Na sauke ajiyar zuciya a filiz na san ba ƙaramin mutunchin Mama Sa'ar take gani ba da har ta bata amsa me daɗi haka, ina ji ta wuce tana ce mata
"To ki zuba a kai musu dan Allah ba daɗi kusan rabin awa da zuwan su kuma sun shigo sun tarar da mutane na cin abinci"
"Za'a kai yanzu" ta sake bata amsa. Ta ke na ji sanyi a raina na waske na bar gurin ba tare da na ce mata komai ba duk da a ƙasan raina na ji kamar na tsaya na ɗibarwa Bilal ban sani ba ko ze bawa su Nasir da sauran abokanan sa na unguwa amma na san zata iya saka kaina a kular abincin shiyasa na haƙura ban koma ba. Se da aka kira Magriba taro ya fara watsewa, na samu alkhairi ƙwarai da gaske Abba ma ya yi goshi daga kan riguna kuɗi da kayan amfani su diaper da omon wanki da su sabulu mun same su babu adadi zamu ja lokaci sosai kafin su ƙare mana.
Tun da naji za'a kaiwa su Fadila abinci ban sake bi ta kan su ba musamman da ƙawaye na da mu kayi poly tare suka zo duk hankali na ya tafi ga maƙwafta masu shigowa da sauran yan uwa gaba ɗaya na sha'afa da su sai da su Baby Bashir zasu tafi na fito raka su kafin ido na ya sauka kan ƙofar ɗakin Bilal ɗin da na hango yara na tsere a ciki. Gaba ɗaya se na rasa nutsuwa, get na yi niyar taka musu amma na tsaya daga in da nake na bar su da Hansa'u ta tafi raka su wajen ni kuma na wuce ɗakin Bilal. Babu kowa sai yara dake wasa da wasu yan gidan su Abban mu yammata suna ɗaukar hoto. Ce musi na yi su fita na kullo ƙofar dan key ɗin ma a jiki suka bar shi na jefa shi cikin aljihun rigata zuciya ta na bubbugawa dan na san har dai zasu tafi ba tare da sun yi mun sallama ba tabbas da wuya idan ba Anty ta musu wani abun da ya sosa musu rai ba ne. Haushin kai na ya kama ni, ko me ya sa ban tsaya na ga abincin da ta zuba musu ba ko kuma na sake komawa gurin su na tabbatar an basu komai wadatacce, bana ma zaton ta basu souvenirs ɗin da naga ta bawa ƙawaye na da suka tafi yanzu ƙila ko daga baya aka kawo su.
Haka dai jama'a suka ida watsewa ya rage na jiki waɗanda suka tsaya suka gyara mun gida tsaf ba zaka ce anan aka sha didimar biki ba, abincin da yayi saura da yawa masu so sun ɗiba sun tafi da shi, ta zuzzuba mun abinda ze ajiyu na saka a fridge miya kuma da nama na saka a frizeer haka sauran ruwa da lemo kusan katan goma goma duk na lode su a store, basu bar gidan ba hatta kayayyakin da muka samu na barka se da suka taya ni na ware su komai ya koma muhallin sa kafin kowa ya wuce gidan sa. Ina tsaka da shafa mai bayan na watsa ruwa saboda jiki na da ya yi mun tsami sosai Bilal ya dawo.
Da Baba Jummai na jiyo suna gaisawa be shigo ɗaki na ba bayan na gama shiryawa kamar in share shi sai kuma wata zuciyar ta ce na dai je. Dama na ware masa abinci na sake ɗumamawa na haɗa komai a try na fito Baba Jummai ta bini da kallo ta na cewa
"Ba dai ɗakin sa zaki kai masa ba" na yi murmushi kaina a ƙasa dan na san baze wuce abin da ya faru jiya ya sa tayi tambayar ba se kawai na wuce na ajiye su tsakiyar falo kan center table ina cewa
"Aa, a nan zan ajiye masa"
"Ya dai fi miki" ta faɗa tana wucewa ɗaki. Fita na yi na tafi ɗakin Bilal, a falo na same shi yana waya bakin nan kamar ze tsage saboda farin ciki ina shiga ya yafito ni da hannu, ban matsa kusa da shi sosai ba na tsaya daga gefe ya miƙo mun wayar na karɓa duk da ban san waye ba sai da na kara a kunne na kafin na gane Hafiz ne.
Muka gaisa yana tambayar ina Dadyn sa tare da bani haƙuri akan rashin zuwan su wai uzuri ya taso musu basa ƙasar, ya ce Shahida ta ce idan ta kira ni bata samu na faɗa masa na yi setting layi na private ne idan ba ni da number kiran ba ze shigo ba se dai na ga missed call kuma tabbas na ga an kikkira ni da number waje amma ban san ita ba ce shiyasa ban bi baya ba. Jin muna yin sallama Bilal ya raɗa mun a kunne wai na yi masa godiya, ban san godiyar ta me ce ce ba amma haka na yi ya ce ba komai daga nan na mayar masa da wayar sa na fita bayan na sanar masa ga abinci can yana jiran sa.
Na zata ba ze zo ya ci ba ganin kusan minti goma har na fara gyangyaɗi kafin ya shigo. Farat farat ba zaka ce shi ya gama gasa mun maganganu jiya da daddare ba wai har yana tambaya ta ya taro an ce masa an sha bidiri a gidan nan. Na yi murmushi kawai ina kallon sa yana cin abincin yana soko mun hira, a raina na raya kenan su Fadila ba wani abu ya sa suka tafi ba tare da mun yi sallama ba ko kuma dai labarin bai iso kunnen sa ba ne. Da ya gama ci naga alamar yana so ya ja hirar da tsayi na ce masa bacci nake ji, na ringa kallon sa da mamaki jin ya ce na karanto masa account number na ya samu wasu kuɗi ni ma zai tura mun wani abu.
Na gama karanta masa ya saka muka yi sallama yana shirin rungume ni na zille na shige ɗaki, na goge ido na ya fi sau nawa a son na tabbatar da gaske kuɗin da na gani haka suke ko kuwa dai ban ga ni da kyau bane ba. Dubu ɗari Bilal ya aika mun, dubu ɗari dai a tarihin rayuwa ta da shi tun da muke dunƙulalliyar dubu goma bai taɓa ɗauka ya bani ba idan ba ta siyan kayan barka ba.
Duk baccin da nake ji sai na ji na wartsake, na rasa ma wacce kalar murna zanyi. Screenshot na yi na turawa Anty Labiba, kafin su tafi ba kalar habaicin da bata mun ba ace haihuwar fari amma abincin da za'a ci na suna se dai a dafo daga gidan ubana a kawo mun kuma a haka dan bani da kunya na cigaba da yi musu kankanba ni me miji kuma yana so na ai ko auren haɗi ba za'a kwata abinda aka mun ba.
Ni dai abin da na ke raya wa a zuciya ta Bilal na so na, duk kuma abin da a ke ganin ba ya mun da ma ce ba shi da ita ina kuma da yaƙinin wata rana zai mun ninkin abin da ma ba'a taɓa tsammata ba gashi kuwa ya fara tabbatar da hasashe na. Bacci ma kusan rabi da rabi na yi, bini bini zan farka na ja waya na duna dan in tabbatar kuɗin na nan ba su gudu ba.
GIDAN HAJJA
Tun safe suka ta shi da kacaniyar taron sunan da suka shirya zasu yi a can gidan. Ita ta ƙarfafawa Bilal akan ba wani taron suna da Halima za tayi in dai ba can gidan su zata tafi suyi a can ba, daga baya kuma ta rikiɗa ta ce ita zata yi taro a nan gidan ta, jikan ta na farko na ɗa namiji bai kamata ace ba a yi taron suna ba. Da Anty Amina ta ce mata in dai ba Halima za'a bawa kuɗi ta yi taro ba se dai a haƙura haka ta ringa faɗa ta na cewa ita ta kasa ganewa Amina, gaba ɗaya ta canza yi ta ke ma yanzu kamar Halima ce yar uwar ta ba Bilal ba to ba za'a bata ɗin ba idan ta na so ta fitar da kuɗin ta tayi taron nan itama da Fadila ta haihu ai babu ƙwandalar kowa su suka yi taron sunan su.
Da Bilal ɗin ya ce mata ba shi da kuɗi yanzu na Rago ya ke ƙoƙarin haɗawa ma ce masa ta yi ita ba damuwar ta ba ne wannan idan ya so ma ya bari se ranar sati biyu sannan ya yi musu yankan. Haka nan se da ya basu kuɗin kafin ya samu lafiya a hannun Hajjan. Da safe kuma bayan an gama raɗin suna bayan da ya je banki ya tarar da Hafiz ya aika masa saƙon da ya girgiza masa lissafi. Ya san tabbas ze yi masa abu na bajinta domin Hafiz akwai harkar girma amma be zata abun ze kai har haka ba. Babu bata lokaci ya Abubakar ya ce ya zo ya karɓi kuɗi ya siyo Ragon shi kuma ya wuce wani uzuri.
A gurin da ya siya ya yanka aka feɗe masa kamar yan da Bilal ɗin ya ce ayi sannan ya wuce ya kai can gidan ya na komawa gida marin sa ne kawai Hajja ba ta yi ba dan a yanda ta ce ta ɗauka yana da hankali idan ya siyo zai yi tunanin ya fara kaiwa gidan ta ba wai ya wuce ya kaiwa Halima ba. Ta ringa sababi, se kace wacce aka kai musu garke guda hatta da yayan ta sai da abin ya ba su haushi ga mutane duk suna zaune suna jin ta take wannan abun. Suna tsaka da sabgogin su Fainusa ta je ta ke basu labarin yanzu aka kira ta ana can ana bidiri a gidan Bilal, kuma wai duk se ransu ya ɓaci akan me ba'a gaya musu Halima za ta yi taro ba, har Bilal ɗin Hajja ta kira ya ce shi bai san zata yi ba dan be bata ko sisi ba se dai idan yan gidan su ne suka shirya abun su, haka suka zari jiki suka tafi har Hajjan da ta ce zata bisu suka hana ta ta ringa jaddada musu akan duk abin da aka yi su taho mata da shi se gasu yanda suka je haka suka dawo hannu na dukan cinye se ma asarar kuɗin mota da suka yi dan dai ko ruwa ba'a basu ba a yanda suka ce. Suka ringa zagin Halima da yan uwan ta suna wassafawa Hajja irin liyafar da suka tarar ana yi tun daga kwanukan almajiran da suke ƙofar gidan zaka san ana harkar girma a ciki amma tsabar an raina su ba'a kuma daraja su ba haka nan aka bar su kamar wasu almajirai babu wanda ya bi ta kan su suka gaji da zama suka taho.
Saboda yan da abin ya harzuƙa Hajja bata iya cewa komai ba, ta ringa kiran layin Bilal wayar na ringing amma yaƙi ya amsa wannan ya sake ɓata mata rai, duk yan da aka yi da sanin sa shi ya sa ya zagaye ya sa aka kai musu Rago ba tareda ya yi shawara da ita ba.
WASHE GARI
Tun da na yi wankan safe na ci abinci na sake komawa bacci ban farka ba se azahar lokacin har Baba Jummai ta gama soya naman tas ta gyara gidan, ban yi mamakin ganin babu wanda ya zo taya ta suyar naman ba. Se da na sake watsa ruwa sannan na fito, tambayar ta na yi ko Bilal ya shigo ina bacci ta ce be fito ba ba ta ji motsin sa ba. Abinci na fara haɗa masa, sauran sinasir da waina na ɗumama na ɗibi nawa na haɗa komai a try na faki idon Baba Jummai na tafi ɗakin. Sallah na tarar ya na yi, bayan ya idar ya kalle ni da murmushi ya ce
"Kin ta shi kenan?"
Murmushin na mayar masa na ce
"Ashe ka leƙa na tambayi Baba ta ce bata ji motsin ka ba"
"Sanda na shiga tana can tana soya nama, da kamar na yi mata magana na ga ta goya Al'amin ga hayaƙi ga kuma zafin wuta kar su dame shi". Na zare ido ina dariya na ce
"Lallai, ka ce ka so ka siya mana magana ta ce ka mata rashin kunya. Ka san mitar Baba kuwa? Ɗazu fa daga ta masa wanka ta ajiye shi taje zubar da ruwan naga towel ɗin ya buɗe ga farka a kunne na gyara masa ta na zuwa ta fara mun taratsi wai me na ke dubawa a jikin sa kar na mata sharri na ce ta masa wani abun" muka yi dariya tare kafin ya ce
"Amma tana da kirki sosai ga aiki, na lura sam bata son ƙazanta itama ko ina fes fes ɗakin ku yana ƙamshi kamar ba na masu jego ba gaki kema ta na kula mun da ke sosai" ya faɗa ya na jana jikin sa. Ban musa ba na je, yana shafa fuska ta ya ce
"Jegon nan ya karɓe ki My Halims, wani kyau kullum kike ƙarawa haƙuri na fa ya fara ƙarewa". Zabura na yi na bar jikin sa da sauri ya fashe da dariya kafin ya ja try ɗin gaban sa ya buɗe ya na cewa
"Kamar kin san yunwa na ke ji sosai, ɗan ɗebo mun naman nan na taɓa. Idan kuma akwai sauran peppered chicken ɗin jiya ki kawo mun". Zuwa na yi na ɗebo masa naman na haɗo da kazar da ya ce na ji daɗi da na tarar Baba Jummai a garin lallaɓa Al'amin ta bi shi sun yi baccin tare se na ɗauki abinci na na wuce da shi muka ci tare muna hira kamar lokacin ya dawwama.
"Akwai tafiya da zan yi, zamu je wani aiki Abuja daga office. Tun shekaran jiya waɗan da zamu tafi tare suka yi gaba na bari ne dama se an yi suna nima jiki na ya sake warwarewa kafin na bi bayan su cikin kuɗin aikin da aka bamu ne ma na tura miki wani abu daga ciki jiya" Bilal ya faɗa bayan da muka gama cin abinci,
"Toh, yaushe kenan kuma zaka tafi?" Na tambaye shi. Ya ɗan ɓata fuska ya ce
"Gobe nake tunani dan suna ta mun waya akan na taho ni suke jira mu fara aikin".
"Amma fa har yanzu jikin ka da saura, na fa lura da kana sallah ƙafar ka daƙyar ka ke lanƙwasata a haka kuma zaka tafi wani aiki ba zasu canza ka da wani ba?" Na faɗa cikin marairaicewa. Se ya miƙe ƙafar yana cewa
"No na samu sauƙi fa, rashin yawan motsa jikin ne ma ya sa har yanzu nake ɗan jin ciwo amma babu wata damuwa zan iya. Kuma ban da abin ki bayan har an bani kuɗi na kashe se na ce kuma ba zani ba kenan zan mayar musu da kuɗin su".
"Kuma aikin na menene?"
"Bari na zo na je gidan Hajja, naga ta kira ni tun jiya ashe ban lura ba se ɗazu tukunna" ya faɗa ba tare da ya bani amsar tambayar da na masa ba. Tattare kwanukan na shiga yi ina cewa
"Bari to na yiwa Baba magana ta raba naman se ka tafi musu da nasu kawai" na fice daga ɗakin. Ina shiga kitchen na jiyo ana buga get, shi ya fita ya buɗe, gaba na ya faɗi jin muryar Hajja ta na cewa
"Bacci kuke ko me da za'a yi ta bugu ba zaku buɗe ba". Sauri na yi na kashe famfo na bar ɗauraye kwanukan da na yi niyya da gudu gudu na wuce ɗaki na na shige banɗaki.
Kamar na fasa kuka sanda