Showing 42001 words to 45000 words out of 257873 words

Chapter 15 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

462

ransa ya ɓaci yasa na bar maganar, har ya rage saura kwana biyu a rufe registration be sake ce mun komai ba tun da na tuna masa wancan ranar dama ya fara wasu attitudes se kawai na rabu dashi da yamma ranar nace masa zan je gida be kuma hanani ba na tafi.

Cikin sa'a na tarar da Uncle Mudassir ƙanin Mama a gidan, ina faɗa musu abin da ya faru ya hau faɗa yana cewa da uban me na zauna yi ga waɗan da muka gama karatun tare har sun ci ƙarfin service ɗin su? Tare muka je dashi aka mun registration ɗin as single, ya karɓi details ɗin yace ze bawa wani abokin sa dake aiki a NYSC ɗin ayi mun ƙoƙari a barni a Kano. Yanda Bilal be ce mun ba nima na masa shiru se sa aka kwana uku muna zaune da dare yana danna waya ya kalle ni yace
"Wai ashe an rufe registration din NYSC, amma ɗan iskan mutumin nan be kyauta mun ba dole naje naci uwarsa gobe. Kullum na kira shi ya ce mun yau gobe gashi har an rufe beyi abun nan ba" ya wani fututtuke kamar gaske. Kallon sa kawai nayi na maida kai naci gaba da danna wayata.

Sosai naji zafin ko in kular daya gwada mun tun akan zuwa karɓan result da kuma zancen service ɗin nan yanzu. Se na tuna da wata magana da ya taɓa faɗa a gaba na tun ina diploma, lokacin da Nasir ze auri matar sa tana karatu yace ze ci gaba da ɗaukar nauyin ta. A gaba na yake cewa Nasir ɗin bashi da hankali.
"Kai ka sakata a makarantar balle ka ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ta? Ai wlh nan da ka ganni idan iyayen yarinya sun ga zasu bani auren ta tana karatu to su san duk lalurar ta tasu ce ko kuɗin fensir ba za'a ɗora mun ba tun da ba ni na sakata a makarantar ba". A lokacin kwata kwata ban nazarci maganar sa ba a rashin hankali na ma gani nayi daidai ne tun da ina jin Abba na yawan cewa ko ze mun aure se na gama makaranta dan babu dalilin da ze saka ka ɗorawa miji hidimar da bashi yayi niyyar kansa ya saka maka yar a makarantar ba. Tuna wannan abun yasa naji raina ya sake ɓaci kawai na tashi na bar masa gurin nayi kwanciya ta a ɗaki be kuma damu ba balle ya biyo ni yaji ba'a si dan dama ni ce nake kasa zaune na kasa tsaye idan ransa ya ɓaci shi kuwa ko a jikin sa duk fushin da zanyi se dai ya jira na gama hawa na sakko.

An yi posting cikin rashin sa'a aka cilla ni Bauchi, uzurin da abokin Uncle Mudassir ya bashi na cewa state of origin ɗina Kano ce kuma banyi registration da wuri ba dan haka list ɗin yan Kano ya cika da daga wata jahar ne ma ya iya cucu cuku a jefani amma yanzun ma babu damuwa registration kawai zan je nayi se a mun relocation. Sanda ya kira yana mun wannan baya nin duk se na rikice na rasa ta in da zan fara. Kwana biyu da suka wuce Bilal ya tsare ni da masifar akan me naje nayi registration a matsayin mara aure kuma ba da umarnin sa ba? Yayi rantsuwa akan muddin aka kai ni wata jahar se dai nasan yanda ze yi amma har idan da yawun sa ne ba zan je ba tun da na raina shi na fara yankewa kaina hukunci ba tare da sanin sa ba. Yanzu haka bama magana, tsaka ni na dashi kallon banza ko abinci na baya ci in ya fita tun safe se nayi bacci yake dawowa ɗazu har Hajjan su ce ta kira bin ba'asin me ya faru? Bata kuma tsaya taji uzuri ma ba ta ringa surfamun faɗa wai dama taji ƙishin ƙishin ɗin na raina shi bana jin maganar sa to wlh na shiga hankali na kuma taka a sannu idan ta juyo kai na ba zan ji da daɗi ba.

Maganganun ta suka kulle mun kai na kasa gane in da ta dosa, ni ce na raina Bilal? Kuma waye yake kai mata tsogumin? Matar da sa albarka ne tsakanin mu idan naje ko yayanta suka zo ko mukayi waya bakin ta baya gajiyawa da gode mun da yi mun addu'a ita ce zata kira tana mun wasu maganganu da ban ma gane kan su ba. Ina cikin wannan jimamin kiran Uncle Mudassir ya same ni, kai na ya sake kullewa na rasa ina zan kama. Haƙura zanyi da service ɗin nabi yanda Bilal ke so ko kuwa na barshi na bi son rai na? Ina buƙatar me bani shawara.

[5/18, 14:39] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*Page 12*

"Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets da bargo ya koma can.

Kwanan mu uku bana sanin fitar sa bana sanin dawowar sa. Hankali na ya tashi matuƙa, har ƙasan raina ina jin na masa laifi kuma ya cancanci yayi fushi tunda matar sa nake ya kamata ace duk wani abu daya shafe ni yana da masaniya a ciki musamman irin wannan abun da tilas nake da buƙatar sahalewar sa. 'Amma kuma na bashi damar sa', zuciya ta ke raya mun. Daga ƙarshe dai ɓangaren da yake ganin abin da nayi ba daidai bane ya rinjayi wanda yake ganin ina kan daidai. Ranar laraba daya kama washe gari Alhamis za'a fara shiga Camp da sassafe Uncle Mudassir ya kira ni. Bayan mun gaisa yake ce mun

"Tun jiya naso na kira ki, ina ganin idan da hali ki shirya kawai ki tafi yau tun da gobe za'a buɗe camp ɗin. Kin ga idan kika kwana can zaki fi fita da wuri kije ki gama abin da zakiyi a goben ba tare da cunkoso yayi yawa ba jibi kiyi juyowar ki".

Shiru nayi, se da naji yana ta hello hello kafin na sauke ajiyar zuciya nace
"Dama tun da na gaya masa zancen tafiyar ne yake ta fushi, kuma yace in har da yawun sa ne be amince ba" na ƙarasa muryata na rawa. Se yayi shiru kusan minti ɗaya kafin ya ce mun
"Shikenan, kiyi yanda kika ga ya miki Halima" be ko saurari abin da zan sake faɗa ba ya kashe wayar sa. Duk se na sake shiga ruɗani. Na ɗauka shi da yake namiji ze fahimce ni ya kuma ƙarfafa mun da nabi umarnin miji na amma daga amsar sa na gane ransa ne ya ɓaci har ya rasa amsar bani shi yasa ya kashe wayar. Na zabga tagumi gaba ɗaya ma ƙwaƙwalwa ta ta cushe na kasa tuna ni. Na sauke tagumin jin wayata ta ɗauki ƙara na ɗago ta daga cinyata, Abba ne yake kira se naji wani rauni ya saukar mun nan da nan hawaye ya tarar mun a ido.

Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son ƙwace mun na gaishe shi ya amsa sannan yace
"Mudassir ya kira ni yanzu, wani abu kika yiwa Bilal ɗin da har ya yanke miki wannan hukuncin?" Se kawai na fashe masa da kuka. Be hana ni ba nayi me isa ta har naji na samu ƙwarin guiwar yin magana sannan nace

"Ban masa komai ba wlh Abba. Kawai dai tun da aka buɗe registration ɗin da naje suka ce se na kawo marriage certificate da sauran takardu na shaidar ina da aure na gaya masa yace ze je ayi, har aka kusa rufewa beyi ba da na sake masa magana shine ya fara faɗa wai na dame shi ranar na zo mukayi magana da Mama Uncle Mudassir yana nan shine yace kawai muje nayi ai ba za'a tsaya jiran sa ba. Ina ga wannan ne yasa yayi fushi ya kuma ƙi tsayawa muyi magana ma balle ya fahimce ni, ni kawai na haƙura Abba tun da dai be yarda ba" na ƙarasa ina sake fashewa da kuka.

Shiru Abba yayi na yan sakanni kafin yace
"Kin haƙura da service ɗin Halima?"
"Toh Abba ya zanyi? Yace be yarda ba kuma ai ba zan tafi ba tare da izinin sa ba" na faɗa cikin kuka, se Abba yace
"Haka ne, toh Allah ya taimaka ya kawo sauƙi cikin al'amarin. Se a ci gaba da haƙuri Allah yayi miki albarka" daga nan ya kashe wayar sa. Kuka sosai na sha bayan mun gama wayar har se da naji kaina ya fara ciwo kafin na rarrashi kaina nayi shiru.

A can gida kuwa bayan da Abba ya aje waya cikin ɓacin rai Mama dake sauraron duk maganganun su tace
"Shikenan abin da zaka ce mata Abba?"
"To me kike so na faɗa bayan wannan Amina? Tace mijin ta be yi mata izini ba, so kike yi nace ta take maganar sa ta fito ko yaya? Idan aka yi haka ai ba da shi muka ja ba umarnin Allah muka take. Tun da ita bata da dabarar da zata lallaɓa shi ta kuma haƙura ba shikenan ba duk wanda ze so mata tayi service ɗin ta haɗa takardun ta guri ɗaya ai ba kamar ita da tayi karatun ba, ki bar maganar nan kawai. Ai ba cewa akayi daga wannan karon shikenan an gama ba. Akwai wani lokacin sanda ya amince mata se tayi amma yanzun a barshi kawai" Abban ya bata amsa ƙarara kuma fuskar sa da muryar sa sun nuna ransa be masa daɗi ba shima da hukuncin da Haliman ta yanke. Tashi Mama tayi daga gurin kawai saboda ranta dake suya idan ta zauna ƙarshe zata sauke fushin ne akan Abban. Tana shiga ɗakin ta ta kira Anty Labiba ta gaya mata.

"Dan girman Allah Mama ki barta. Ai bata sako kowa a ciki ba bata nemi shawarar ki ba. Tun da dai haka taga ya fi mata se mu rakata da addu'a Allah ya bata sa'a amma kar ki wani ɓata ranki akan wannan abun" Anty Labiban ta faɗa mata.

Ina ji ina gani na haƙura da tafiya service duk a son farantawa Bilal. Ranar Juma'a la'asar ina zaune jigum ni kaɗai a falo na kunna tv, ido na ne kawai akanta amma sam bana fahimtar abin da ake yi a ciki. Na zata da Bilal yaga ban tafi ba ze fahimci na haƙura ne na bi umarnin sa ya sakko mu fahimci juna amma sam banga haka ba, babu abin da ya canza se ma ƙaruwa da yayi dan tun shekaran jiyan cefanen mu ya ƙare tas be siyo ba be kuma aje mun kuɗin da zan siyo ba ban ma ganshi ba balle na gaya masa shi kuma kusan sati guda Kenan dama baya cin abinci na dan haka baze ma san menene akwai da wanda babu ba. Kwana ukun da nayi jere ina cin mai da yaji har ulcer ta ta fara motsawa, ina so na fita na yi aike ina tsoron sake yin wani lefin.

Ana kiran sallar Magriba Bilal y shigo, rabon da na saka shi a ido na kwana huɗu kenan yau. Na bishi da ido kamar wadda taga sabuwar halitta, kamar ko yaushe yasha kwalliyar Juma'a cikin shadda se tashin ƙamshi yake. A kan kujerar dake kallon wadda nake kai ya zauna, na sauke ido na ƙasa ina sakin ajiyar zuciya jin idanun sa a kaina. Minti kusan biyu ganin yana zaune har sannan kafin na tattaro yamun baki na na jiƙa maƙoshina daƙyar na furta
"Sannu da zuwa".
"Yawwa sannunki da gida" ya amsa mun, se na ɗaga kai na kalle shi jin muryar sa a sake sak ba fushi ba ɓacin rai. Hannu ya miƙa mun alamar naje gare shi, ban motsa ba se hawaye da suka ɓalle mun kamar an kunna famfo. Shi ya taso ya dawo in da nake ya ɗaga ni tare da rungume ni nan na samu dama na ringa kuka kamar wadda aka aikowa da mutuwar iyaye. Shiga sallah da akayi yasa na janye shi kuma ya wuce ciki da sauri ya yo alwala.

Be buɗe baki ya bani haƙuri akan abin da ya faru ko ƙauracewa gidan tsayin sati ɗaya da yayi ba amma ya nuna mun a aikace. Ya ringa tattali na yana ji da ni kafin kace me na manta da duk fushin sa dake zuciyata muka cigaba da zamanmu kamar wani abu be faru ba. A haka muka sake cinye watanni biyu wanda ya kama wata takwas kenan da auren mu. Shirye shiryen azumi ya kankama dan ana lissafin saura kwanaki biyar ko shida a fara azumin watan ramadan. A tsayin tashi na na saba a gidan mu muddin aka ce azumi ya gabato da wata ɗaya muke fara shirye shirye. Mama tana fitar da kayan kitchen ɗin ta a wanke komai ta ware waɗan da zata ci gaba da amfani dasu sauran a bayar sannan ta zuba sababbi wanda nasan Abba ne yake bayar da kuɗin. Kafin a ɗauki azumi kusan abin da baze ajiyu bane kaɗai ba'a siya a gidan mu a ajiye haka batun kayan sallah wani lokacin kafin a ɗauki azumi an gama mana ɗinki.

Tun da watan sha'aban ya kama nake yiwa Bilal zancen shirin azumi se ya ce mun se kace wani sabon abu kamar bamu taɓa yin azumi ba shirin me za'ayi? Dake muna da kayan abinci, buhun shinkafar dafawa uku aka mun ta gara data tuwo biyu, haka dangin su taliya zuwa mai komai uku har carton ɗin maggi da gishiri ban da ma dangin Bilal dake yawan zuwa dan dai cikin mutum biyu zamu iya fiye da shekara ma ƙila be fara siyan abinci ba. Duk kuwa sanda wani ze zo na dafa abinci na bayar ko be yi magana ba se naga ɓacin rai a kan fuskar sa, na rasa irin wannan hali da Bilal ya tsira akan abinci.

Sanda na buɗe buhu na biyu haka ya ringa bala'i wai na ɓarnatar da buhun shinkafa a wata shida a haka ma wai dan ba ita ake ci kullum ba da kenan a wata ɗaya zata ƙare. Yanzun shinkafa buhu ɗaya ta rage mana da saura kaɗan a buhun da be ida ƙarewa ba, ina so cikin azumi ko ba kullum ba na ringa dafa abinci ana yin sadaka amma ban san ko Bilal ze amince ba.

Na rigada nayi list na duk abinda zan iya buƙata da azumi se wanda ba a rasa ba jira kawai nakeyi ayi albashi na bashi ya siyo mana. Ranar alhamis aka fara yin albashi, a kunne na naji yana waya da wani ɗan gurin aikin su ya gaya masa sun samu ƙarin albashi. Har raina nayi murna saboda ina tunanin ƙarin da suka samu ze saka mu ƙara samun walwala tunda kusan cefanen gidansu a kansa yake dukda yayyen sa mata biyu suna auren masu wadata kuma ba laifi suna hidimtawa mahaifiyar su haka ƙanin sa Abubakar matashi ne me zuciya sosai amma kullum Hajja cikin kiran sa ya bata kaza ya kawo musu kaza abu kaza ya ƙare take be kuma gajiyawa ze ɗauka ya kai mata hakan yasa nake ɗauke kai ga yanayin yanda yake tafiyar da namu cefanen na ke kuma yin abin da naji ina so in har ina da kuɗi a hannu na. To Abban da yake bani kuɗin tun zancen NYSC na shima na fuskanci chanji a gurin sa, da wuya in je gida na tashi tafiya ya bani ƙasa da dubu biyar kuma se yace na ɗauki duk abin da nake da buƙata a gidan tun lokacin kuwa yanzu idan naje dubu biyu uku har dubu ɗaya bani yake yace na hau mota. Kasancewar na saba da ɗan riƙe kuɗi a hannu na yanzu kuma me banin ya fara janye mun tallafi yasa duk nake ji na a takure.

Ban bashi list ɗin da nayi a ranar alhamis ɗin ba se na bari washe gari juma'a gurin ƙarfe goma bayan ya gama shiryawa ze fita sannan na ɗakko masa takardar. Kwata kwata abubuwan dana lissafa a ciki basu haura na dubu goma sha biyar ba zuwa ashirin wanda kuma ina da yaƙinin zasu kaimu har bayan sallah da nisa ma. Ina murmushi cikin raina ina yaba zati da haiba irin ta Bilal. Kullum ƙara kyau da kwarjini yake a idanu na musamman da yayi yar kiɓa jikin sa ya cike ya zama cikakken magidanci yanzu, kullum ya fita cike nake da zullumin kar mata su bibiyar mun shi. Amma na yarda dashi na kuma san bashi da kwashe kwashe.

Jin yana mun sallama yasa na miƙa masa takardar ya karɓa yana juyata.
"List ne na abubuwan da zamu buƙata kaga yau za'a fara duba wata" na faɗa ganin yana kallona da sigar neman ƙarin bayani. Se ya buɗe takardar ya shiga bitar abubuwan dana rubuta

"Ke yanzu ana ta abinda za a ci a ƙoshi lissafin ƙwai da dankali dasu doya kike har da plantain?" Ya faɗa yana kallo na bayan daya ninke takardar. Murmushi na saka dan na ɗauki maganar tasa ne a sigar wasa nayi far da ido nace
"Eh mana, kasan a gida na saba da su nake karya azumi. Idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login