Showing 192001 words to 195000 words out of 257873 words
son da nake miki yafi wanda kike mun yawa".
"Amsar da nake buƙata kenan kuma na sameta. Nagode da alfarmar da kayi mun ka zauna dani tsahon lokacin nan albarkacin son da nake maka, nagode da duk abinda ka mun a tsayin zamanmu.
Na san yanda zuciya takeji a lokacin da abinda bata so yake mata naci, kayi ƙoƙari daka iya kasancewa tareda ni tsayin lokacin nan, daga yau ka yantu, ba zaka sake kwanciya ka tashi da tunanin ganin wacce zuciyarka bata muradi ba.." kukan daya sarƙe ni ya hanani cigaba da magana. Biro da takardar da na taho dasu na zaro daga aljihun rigar jiki na na ɗora akan center table ina cewa
"Gashi nan, ka datse alaƙar da take tsakanina da kai ka samarwa zuciyoyinmu yanci".
"Ba zan iya sakin ki ba Halima wlh ina sonki" ya faɗa bayan daya rarrafo ya kama ƙafafu na. Haɗe kai da cinya nayi na shiga rusa kuka tamkar wacce za'a rataye, jin yana ɗagoni, lokaci ɗaya cikin wani fushi da ban san sanadinsa ba na ɗago na wanke shi da marin da ni kaina sai da naji a jikina saboda raɗaɗin da tafin hannuna har zuwa ƙasusuwan hannun suka ɗauka saboda ƙarfin marin.
Yayi baya ya zauna wanwar yana kallona cikin mamaki, takardar na nuna masa na ce
"Ka ɗauki takardar nan ka rubuta abinda na buƙata. Sanyin halin Halima ka sani, kada ka bari in nuna maka ɗaya ɓangaren domin ba lallai idanuwanka su iya jurar kallo ba".
"Ke karki ga ina lallaɓa ki ki nemi raina mun hankali, ba dai a hannuna igiyar auren take ba? To ba zan saki ba idan kina da ƙarfi ki danne ni ki ƙwata ko ki turo wani ya ƙwatar miki. Ƙaryar banza ƙaryar wofi kawai ni da ke mun sani Halima wlh ba zaki iya rayuwa babu ni ba gara ma ki rufawa kanki asiri mu koma tun lokaci bai ƙure miki ba" ya faɗa cikin fushi bayan daya miƙe tsaye.
Tashi nayi nima ina kallon sa na ce
"Ba dan kar inyi saɓo ba dana tsinewa ƙaddarar data haɗa ni da kai, wlh Bilal ko ban ce komai akanka ba da sannu sai kaga sakayyar butulcin da kayi mun, kaje Allah ya isa tsakanina da kai za kuma ka gani tunda kaƙi sakina ta lallami wahala zata sa ka saki ko baka ƙaunar Allah" na faɗa ina fashewa da kuka na juya zan bar falon dai dai lokacin da Nasir ya shigo da alama hayaniyarmu ta janyo hankalinsa.
"Tsaya Halima, kai Bilal menene haka? Mu da muka zo sulhu kuma zaka ɓige da rashin hankali?" Nasir ɗin ya faɗa. Na coge a tsaye dan ya tare hanyar ina jin Bilal na cewa
"Dallah rabu da ita aikin banza laifi na ne da na zo shiyasa har ta samu damar yi mun wata fuffuka. Na faɗa kuma ba zanyi sakin ba a saka kaina gabas a yanka. Ya ne iyayen naki basuyi su hanaki aure na ba amma kika nace, kina gidana sau nawa suna cewa ki kashe auren kika ƙi, sau nawa kika zaɓe farin ciki na akan nasu sai yanzu ne zaki zo kina wasu maganganu? To ba'a son naki kuma ba za'a sakeki ba kiyi abinda zakiyi. Idan kinga dama ki dawo in ma kin so kiyi ta zama a gidan naku har duniya ta tashi ni ba matsalata bace"
ya nufi ƙofa fuuuu ya bangaje Nasir sai ganin sa mukayi kamar an chillo shi ya dawo baya ya faɗi tim a ƙasa.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 49*
Kafin mu gana gane me ya faru Mu'azzam ya shigo ɗakin babu kuma ɓata lokaci ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukan Bilal yanda ka san Allah ya aiko shi. Gefe na ja da sauri cikin tashin hankali na ɗora hannu biyu a ka na fasa ihu ina kiran sunan Mu'azzam ɗin, abin takaici Nasir da yake namiji daya kamata ko murɗe Mu'azzam ɗin yayi ya ƙwace bulalar idan ma yana tsoron kaiwa Bilal ɗin agaji ya haɗa da shi wai sai ya tsaya daga gefe yana ce masa ya bari.
Bilal kuwa kamar mace haka ya shiga birgima a ƙasa dan ya kasa kare dukan, Anty Labiba ta shigo da alama ihu na da na Bilal be ya janyo hankalin ta tana ganin abinda yake faruwa ta shiga salati tana cewa
"Babana memene haka? Ya zaka rufe shi da duka? Bari dan Allah ko ma menene ai bai kai ayi duka ba sai ayi haƙuri a sasanta da baki" ta ƙarasa ta riƙe Mu'azzam ɗin. Dakatawa yayi daga dukan Bilal ɗin ya nuna shi yana numfashi ya ce
"Ba ka ce ta ƙwata ta ƙarfi ba? Ko ta turo wanda zai ƙwatar mata? Toh wlh ko ka rubuta sakin nan yanzu ko kuma mun ɗaura da kai daga yau duk in da na ganka sai na haɗa maka jikinka har randa zaka gaji ka saketa".
"Daɗi na da kai wauta in ba haka ba meye naka na shiga tsakanin ma'aurata? Ita tace ka ƙwatar mata ko yaya? Idan Halima ce wlh zaka sha mamaki yanda zata watsa maka ƙasa a ido gara ka barta dashi. Da Allah wuce muje kayi haƙuri Bilal ka san Mu'azzam da zuciya" Anty Labiba ta faɗa tana jan Mu'azzam ɗin suka fita daga falon.
Bin su nayi da kallo, daga yanda take magana kawai a jiki na naji duk yanda akayi wannan abun shiri ne wlh da saninta. Na maida hankali kan Bilal dake kwance maganshiyyan yana jan numfashi Nasir na gefensa yana masa sannu shi ɗin ma sai na ga kamar ƙunshe dariya yakeyi yana masa sannun.
"Miƙo mun takardar can" Bilal ya faɗa daƙyar Nasir ya tashi da sauri ya ɗakko takardar ya bashi. Yana yarfe hannu saboda zafi dan ta ko ina Mu'azzam ya ringa zuga masa belt ɗin duk jikinsa ya ɗauka yayi gajeran rubutu ya jefo mun jotter yana cewa
"Na sake ki Halima, kije na sani soyayyata ba zata taɓa bari ki zauna lafiya ba kuma ko ba daɗe ko ba jima sai kin kawo mun kanki da ƙafarki" dai dai lokacin Mu'azzam ya dawo falon Anty Labiba na biye dashi tana kiransa akan ya tsaya amma yaƙi sai da ya shigo ai kuwa Bilal ya zabura ya miƙe sai kuma ya saki ƙara ya dafe bayansa Nasir ya riƙe shi ya nuna Mu'azzam yana cewa
"Shammatata kayi, kuma wlh baka daki banza ba zamu haɗu a kotu sai naga uban daya tsaya maka".
Jotter data faɗi kan ƙafafu na Mu'azzam ɗin ya tsugunna ya ɗauka kafin ya kalle shi ya ce
"Allah ya taimake ka sai kaje ka cigaba da karuwancin da hujja kuma wlh ko da wasa ka kuskura naga ƙafarka a hanyar gidanmu da sunan kazo biko sai ka gane baka da wayo"
Haka Nasir ya ja Bilal sa bakinsa bai mutu ba suka fice Mu'azzam ma ya fita ya rage ni da Anty Labiba dake ta faman mun magana amma ko kusa bana jin ta balle na gane abinda take cewa.
Kalmar "Na sake ki Halima" da Bilal ya ambata ce kaɗai take mun amsa kuwwa a kunnuwana. Da ƙarfi ta jijjigani abinda ya maido ni hayyaci na na kalleta ina zare ido ta ce
"Tunanin me kikeyi Halima?"
"Bacci nakeyi ko Anty?" Na tambayeta cike da fatan hakan ta kasance.
"Bacci? Aa mutuwa kikayi kika dawo" ta mun ba'a. Kallon falon na shiga yi komai yana nan a yanda yake, hular Bilal da na hango a gefe ta saka na fahimci dagaske abinda ya faru a zahiri bane ba mafarki nakeyi ba. Hannu biyu na ɗora a kai sai dai kamar an sace mun murya ihun da nayi niyyar yi yaƙi fitowa sai hawayene suka shiga wanke mun fuska tamkar an buɗe famfo.
Anty Labiba ta buɗe baki tana kallo na ta ce
"Wai kuka kike saboda ya sake ki? Toh Allah ya duba miki, ki wuce ciki ki samu guri mai kyau kiyi kukan nan za'a gyara Baban Amir zai yi baƙi yanzu" ta wuce ta barni a gurin.
A kan gadonta na zube na shiga kuka kamar wacce aka gama jana'izar iyayenta, na kasa yarda wai Bilal ya sake ni dukda ga takardar sakin da rubutunsa ɓaro ɓaro akai Mu'azzam ya ajiye mun bayan da yayi snapping a wayarsa sannan ya wuce gida.
Anty Labiba ta shigo ɗakin tana kallo na fuskarta fes yanda kasan babu wani abu daya faru ta kama baki tana cewa
"Wai har yanzu kukan kike?"
"Aure na ne fa ya mutu Anty ba zanyi kuka ba?" Na faɗa cikin kukan ina tashi zaune. Ta gyara fuska da gani dariya ce ta taso mata kafin ta matsa gaban mudubi tana cewa
"Gaskiya dai abin kuka ne ya sameki gara kiyi". Sai na haɗe kai da guiwa ina cigaba da kukan na ce
"Ban taɓa zaton akwai tsananin da zai saka Bilal ya iya sakina ba"
"Ai yanzu gashi kin gani da idon ki ba wai tunani ba, kuka kuma ba zai miki maganin komai ba kamata yayi ki tashi kiyi alwala kiyi sallah ki roƙi ubangiji Allah ya sa hakan ya zame miki alkhairi a rayuwarki ba koke koke ba" ta sake faɗa sai na miƙe na faɗa jikinta ina cewa
"Wlh ina son sa ba zan iya rayuwa babu Bilal ba Anty ki taimaka mun"
"Ai kuwa sai dai ki mutu dan ubanki dan wlh ko zakiyi hauka ba zaki koma gidansa ba" ta faɗa tana tureni daga jikinta. A ƙasa na zauna na cigaba da sheƙa kuka sai da naji na fara jin jiri daga zaunen da nake alamar Bp na yayi high kafin na lallashi kaina na koma sauke ajiyar zuciya. Takardar na janyo na saka karanta abinda ya rubuta a ciki.
"Ni Bilal na saki matata Halima saki biyu bisa tirsasawar iyayenta".
Sabbin hawaye suka ɓalle mun sai na cukuikuye takardar na jefa ƙasan gadon Anty Labiba dai dai lokacin ta turo ƙofa ta shigo
"Bata ko kalle ni ba ta wuce ta zauna gaban mudubi ta fara cire sarƙa da ɗankunnen da tayi kwalliya da su. Murya a dashe na tambayeta ta paracetamol saboda ciwon da kaina ya ɗauka ta buɗe drawer ta janyo ta wullo mun na ɗauka na miƙe daƙyar ina dafe bango na fita kitchen. A can na tsinci wayata da na bari sanda nake shiryawa su Bilal abinci na ɗauka bayan da na sha maganin na zauna na buɗe ganin alamar message akan screen ɗin
"Wlh Halima sai kinyi dana sanin cewa na sakeki, kuma ki haɗa kayan yarana gobe za'a zo a ɗauke su ba kuma zaki sake ganinsu ba har abada" abinda saƙon ya ƙunsa kenan.
Ɗakin Anty Labiba na koma muka ci karo a hanya tana shirin fitowa jiki na yana rawa na bata wayar ta duba message ɗin kafin tayi tsaki ta ce
"Da uban waye ya ce masa za'a riƙe masa yaya? Ai dama ko bai faɗa ba mayar masa da su za'a yi dan ba'ayi zaman mutunchin da har za'a masa wannan karar ba" ta faɗa ai kuwa na fashe da kuka ina cewa
"Wlh babu wanda zai rabani da yarana, kun san ba zaku riƙe su ba akan me zaku kashe mun aure? Toh wlh ba zan yarda ba in dai ba za'a riƙe ni da su ba sai dai a barni in koma"
"Ki dai nemi wanda ya kashe miki aure tun dare bai miki ba kome kuma ai kina da dama wata uku cir kan kiyi iddah idan kin so ma yanzu maza ki bishi ku sasanta daga can ku wuce gobe in Allah ya kaimu sai a tattaro miki kayanki da yaran naki a biyo ki da su, ai duniya ce Halima gaki gata babu wanda zai sake ce miki kiyi ko ki bari" Anty Labiban ta faɗa cikin sautin daya nuna ranta ya fara ɓaci da al'amarin nawa. Zama nayi niyyaryi a bakin ƙofar zan fara tijara ina cewa
"Ni gidanmu zan tafi"
Uncle Saleh ya daka mun tsawa kafin ya balbaleni da masifa yana cewa
"Ke wace irin yarinya ce mai shegen taurin kai ne haka Halima? Da kika san kina son zama da mijinki da halinsa tun farko waya ce ko taho gidan? Ki kama kanki, idan ba haka ba wlh zan saɓa miki tunda naga alamar raini da iskanci ne abun naki da kunne na naji kina cewa ya sake ki ba zaki koma ba sannan yanzu zaki zo da haukan ƙarya kina cewa sun kashe miki aure to in sake ji zakiga yanda zanyi da ke kuma babu in da zaki je a nan gidan zaki zauna har ki gama iddah wawuya kawai kin girma har kin haihu amma bakiyi hankali ba" ya ƙarasa yana zare mun manyan idanuwansa irin na Nufawa.
Tsaf na haɗiye kukana dan sosai tsawar da yanda yayi maganar cikin fushi da gargaɗi suka shigeni. Uncle Saleh bashi da daɗi ba kuma shi da sakewa dan ko doguwar hira ba'ayi da shi idan ko kaji dariyarsa to da matar sa ne ita kanta kuma duk buyaginta tana shakkar sa.
Haka na raba dare ina kuka amma ba mai sauti ba dan ina jiyo magangan sama sama daga falo da alama mugayen miji da matar basuyi bacci ba kafin ya lafta mun mari da hannunsa mai kama da na maƙeri.
Gurin ƙarfe uku Anty Labiba ta sake shigowa ɗakin lokacin ina zaune a ƙasa na rafka tagumi hannu bibbiyu abin duniya duk ya taru ya mun yawa, shikenan fa na zama bazawara.
"Da wannan zaman ke ba bacci ba da tashi kikayi kika ɗauro alwala kikayi sallah sai kiji sanyi a ranki" ta faɗa tana kallona. Na haɗiye yawu daƙyar kafin na gyaɗa mata kai alamar "toh".
Kan gado ta zaune gefen in da nake cikin taushi ta ce
"Menene matsalar ki Halima? Nayi zaton ke da kanki kika ce ba zaki koma ba ya sake ki yanzu kuma akan me zaki takura kanki kiyi ta koke koke bayan kuma abinda kike muradi ne ya tabbata?"
Hawaye ya shiga zubo mun ta dakatar dani ta ce
"Ba kuka na ce ki mun ba ki buɗe baki muyi magana ta fahimta kawai nake so"
"Ina jin zafin abinda ya mun har raina Anty amma ina son sa, ji nakeyi kamar ba zan taɓa iya rayuwa da wani namiji bayan Bilal ba" na faɗa bayan da nayi ƙoƙari tsayar da kukan da na fara.
Ta dafa kaina ta ce
"Sai kuma me?"
"Kuma ina duba makomar yarana idan mun rabu kinga gashi yanzu har ya fara cewa zai ƙwace su"
"Da kuma me?" Ta sake tambaya nayi shiru tayi murmushi ta ce
"Ki faɗa mun duk abinda yake ranki, ko da ban taɓa makauniyar soyayya irin taki ba amma nima ina son mijina ina kuma da yaya, ko bisa kuskure nayi tunanin wata rana zan iya rabuwa da shi ina jin zafi har raina dan haka zan miki uzuri har idan kina da ƙwaƙƙwarar hujja kuma na gamsu na miki alƙawarin zan wuce miki gaba in fahimtar da Mama da Abba har suma su fahimce ki".
"Ni babban abinda ya fi damuna dama kowa sanda zan aure shi sai da ya ce suna nan zan dawo, ba iya ku na cikin gida ba dangi da mutanen unguwa duka kowa idonsa da kunnuwansa na nan kawai jira ake aji aurena ya mutu a fara yi mun dariya da Allah ya ƙara" nayi ƙarfin halin sanar mata da damuwar da take cin raina.
Wani uban ranƙwashi ta sakar mun a tsakiyar kai kafin ta lailayo ashar ta maka mun kamar ma ta manta da tsakiyar dare ne ta balbaleni da faɗa tana cewa
"Dan ubanki sai munyi dariyar Allah ya ƙara kuma tun daga sanda ya fara auna miki abinci muke miki ita. Wato saboda gudun kar ayi miki dariya ya saka zaki zauna ki lalata rayuwarki ki kashe kanki ƙarshe ya ɗakko ciwo ya shafa miki ya ƙara jefaki a masifar da ta fi wacce kike ciki ko? To ki kiyaye ni, kuma wlh maganar nan ta mutu daga nan.
Na rantse da Allah kika koma gida kika ce zaki cigaba da tayarwa da su Mama hankali sai irin dukan da Mu'azzam yayiwa jakin zan saka ke ma ya miki tunda gashi nan bugu ɗaya da yaji wahala ba ja in ja ya baki takardarki to kema idan aka miki irinsa salin alin iskokan da suke taya miki kina iskanci da layla da majnun ɗin kan nako duk zasu kama gabansu".
Ni dai sosa in da ta ranƙwashe ni kawai nake hawaye ya cika mun ido amma ba damar na bari su zubo dan da alama nata mutanen suna kusa karta mun rotse. Ashe dagaske ita ta saka Mu'azzam ya daki Bilal,
Tsawa ta buga mun ta ce
"Tashi ki ɗauro alwala kiyi sallah, tunda kika auri shaiɗani ibadarki ma sai a hankali dama ta ina kike zaton zakiga dai dai a lamuranki?"
Haka na tashi na yo alwalar kuma da na fara sallar musamman dana tattara hankalina sai na ji nutsuwa ta fara saukarmun hatta ciwon kai da jirin da nake ji kafin na idar da sallolin duk sun ragu, kamar gaske lokacin da Hansa'u ta zo har addu'oi ta bani da wurudai ina yi kuma sosai na samu nutsuwa a lokacin ban san yanda akayi na watsar na sake komawa yar gidan jiya ba.
BILAL
Asibiti Nasir ya ce zai kai shi bayan sun bar gidan amma yaƙi ya ce ya kai shi gida.
"Amma dai da munje, ba fa ƙaramin duka ya maka ba wlh kar kaje ya bugeka a in da zai iya maka illah" Nasir da har ransa daɗi ya ji na dukan abokin nasa da akayi ya faɗa. Cikin sauƙi Allah ya ƙwatar mata haƙƙinta dukda yaga alamar Haliman kamar kurarin banza kawai takeyi kamar dai har yanzu tana son abokin nasa.
"Ni dai ka kaini gida, kuma wlh idan na ji maganar