Showing 108001 words to 111000 words out of 257873 words
zai yi a can ba" Mama ta sake faɗa sai Abba ya ce
"Gara da kika tuna mun, Halimatu maza ki shirya ki tashi Ibrahim ya kaiku asibiti, bari na kira Dr Lawal kafin ku isa kukan da yaron nan ya ke yi bai yi kama da na lafiya ba".
"Mantawa dai kayi, ita sanda aka haife ta ba haka ta ringa kukan ba sai da muka kusan yada wanka kafin ta daina shima na lokaci ne zai dai na" Mama ta faɗa. Bai saurareta ba ya zaro wayar sa yana cewa
"Duk kukan da ta ke yi jikin ta baya ɗaukar zafi irin yanda na sa ya yi kuma har ƙaƙƙafewa idanuwan sa na ga suna yi kamar wanda zai suma". Sum sum na fice ina jin wani iri a zuciya ta. Daren jiya hatta da Mu'azzam da ke bacci kamar gawa Al'amin na fara kuka ya farka haka suka ringa karɓa karɓa dan cewa Mama ta yi na kwanta amma na kasa yin baccin. Na tuna yanda shi Bilal ko a jikin sa amma su duk hankalin su ya tashi ba su samu nutsuwa ba sai da ya samu bacci dagaske dai ita soyayyar jini ba ta da mahaɗi.
Haka muka tafi asibitin a raina ina tunanin yanzu Mama zata yarda na zauna a gidan ko kuwa dai korata za ta yi?
Dr da muka gani ya gama jagwalgwala shi ya ce lafiyar sa ƙalau babu wani abu da yake damun sa ciki da kunne da cibiya da kai da duk sauran guraren da zasu iya masa ciwo ya duba amma bai ga komai ba. Har ƙafafun sa da hannaye da su baya ya duba wai ko da a garin ɗauka an gurɗe masa wani guri still dai komi lafiya. Paracetamol ya rubuta mana kawai ya ce a ringa bashi sau biyu safe da dare ko gajiya ce ta ke saka shi koke koken.
Muna hanyar komawa gida Suhaila matar Hafiz ta kira ni wai su na ta bugun ƙofa ko bacci na ke yi na sanar mata ina gidan mu ai, address ta ce na tura mata, bayan na tura ta sake kira na akan na yi mata sharing location kawai zai fi sauƙi basu gane kwatancen a rubuce ba. Da ke muna dab da gida ina shiga na hau WhatsApp na tura mata sannan na shiga kitchen bayan na gayawa Mama zuwan na su. Frozen snacks da Mama bata rabo da su na fitar da samosa na ce Zainab ta soya musu, sai dubulan da dambun nama. Na zuba dambun shinkafar da ta gama na abincin rana da peppered chicken a warmers masu kyau duk da bana zaton za su ci amma dai na aje mata komai yanda kawowa kawai za tayi idan sun zo.
Ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba kuwa suka ƙaraso, babyn ta ya girma masha Allah jikin nan luhu luhu kamar an hura masa iska, tare suka shigo da Hafiz ɗin suka gaisa da Mama ya wuce akan zai je ya dawo ita kuma ya barta. Kusan awan ta uku sai bayan la'asar kafin ya dawo suka tafi bayan sun sauke mana tulin kayan tsaraba manyan ledoji guda uku cike da designers kayan jarirai da ko ba'a faɗa ba kana gani kasan ba ƙananun kuɗi suka lashe ba ga kuma atamfofi super wax turmi biyu da wani arnen lace da ta ce sirikarta ce ta bayar a kawo mun.
Haka Mama ta cika mata bokiti da dubulan da dambun naman da ta ce sun yi mata daɗi, dambun ma tafiya ta yi da shi kamar yanda ta ce Hafiz na son Dambu ita kuma bata iya ba. Bayan tafiyar su Mama ta tsare ni da tambayar ina na samo su? Na ce mata abokin Bilal ne ɗan gurin aikin su.
"Ikon Allah, abokin ma na gurin aiki ne amma ya yi masa wannan hidimar?" Ta faɗa. Na taɓe baki na ce
"Kuma basu wani daɗe tare ba, bayan auren mu aka kawo Hafiz ɗin ma kawai dai Allah ne ya haɗa jinin su, shima sanda ta haihu baki ga kayan da ya siya musu da zamu je barka ba. Da babbar sallama fa Hafiz ɗin har rago ya bashi da ke an ce Baban sa mai kuɗi ne sosai nasan Abba ma zai iya sanin sa dan shima tsohon ɗan kwangila ne" na bata amsa. Ta yi jum kafin ta ce
"Ku dai kiyaye, duk dai a yanyin su babu kalar rashin gaskiya ko makamancin haka amma dai ku kama kanku ku kuma guji abin hannun su ko dan saboda mutunchin ku"
"Shi dai, ni ina ruwa na da su? Ita ce ma take nacin sai mun yi mu'amala amma ni wlh idan ma ba ta kira ni a waya ba mantawa nake yi da ita shine dai bini bini ya ke zuwa gidan su" na faɗa ina taɓe baki, Mu'azzam da ya shigo ya ce
"Dama ai dole ya bi su tun da suna da kuɗi. Shi fa mijin nan na ki kwaɗayayye ne kawai, idan kika duba circle ɗin abokanan sa kaf sun fi shi wadata, kowa a unguwar su ma ya sani an masa tambari baya abota da talaka, idan kuwa kika ganshi da wanda ya fi rufin asiri to wlh aboki ne irin tun na ƙuruciya da ba yanda ya iya da shi irin su Nura Tela, su ɗin ma da ta in da yake morar su shi ya sa yake tare da su".
"Kai kuma na hanaka magana akan yaron nan in dai ba alkhairin za zaka faɗa ba amma ka ƙi ji ko Mu'azzam? Ai shikenan" Mama ta faɗa.
Ya wuce yana cewa
"Ni fa gaskiya na ke faɗi ba wani abu ba ko tun da na ke na taɓa yi masa sharri? Duk abin da zan faɗa halin sa ne idan kuma ƙarya aka masa ai ga ta nan ta faɗo abokanan sa guda biyu da suke ƙasa da shi".
Ni dai shiru na yi kawai ina bin sa da kallo can ƙasan raina kuma ina ƙoƙarin lissafo abokanan Bilal ɗin da ya ce wanda suke ƙasa da shi a wadata amma na gaza samo ko guda ɗaya a waɗanda na sani.
Abokanan sa da na yiwa farin sani mutum huɗu ne. Nasir chemist ɗin sa uku kuma na cikin unguwar mu ma shi ne ƙarami a cikin su banda gidan gona da ya ke da shi yana siyar da kaji da ƙwai sai Abduljabbar su maƙwaftan mu ne a da kafin suka koma Abuja da zama yanzu haka a CBN yake aiki, sai Nura Tela shi ma kuma ni dai ba zan saka shi a layin marasa wadata ba domin a shaidar gani da ido ma a guri na ya fi Bilal tun da matar sa ko makaho ya shafa jikin ta ya san tana cikin jin daɗi, gi da ne kawai za'a ce na Bilal ya fi na sa kyau da tsari baya ga haka banga ta in da ya fishi ba sai kuma Aliko, shi kam ko a kantin Kwari ma oga ne. Su ne kusan abokanan sa da duk wanda ya san shi ya san su, sauran ma kuma duk daga na gurin aikin har na gari kowa da sabgogin sa, gaskiyar Mu'azzam Billa ba shi da abokanai talakawa. Amma kuma wannan ba hujja ba ce da za'a ce masa kwaɗayayye ko mai son zuciya.
Sai da Anty Labiba ta zo ta ringa fitar da kayan tana faɗar kuɗin su jiki na ya sake sanyi da lamarin Hafiz, a wata akwati ta zuba kayan dan rigunan duk manya ne ƙananan ciki ba su da yawa ta haɗe su da sauran na barkar mu data ware ta ɓoye bayan ta gama ta ce
"Na san a ranki zagi na kike kina cewa na tattare muku kaya na ɓoye ko? Duk idan lokacin amfanin su ya kai da kaina zan fito da su na kawo miki dan wlh ba za'a tattara kaya ki kaisu gidan na san ki sarai yanda kika ringa kwasar suturun ki kina rabawa ƙannen sa suma haka zaki kwashe ki basu tun da ba sanin zafin su kika yi ba. Ranar suna ina kallon Lace ɗin da figaggiyar ƙanwar nan ta sa ta saka ko kin zata ban gane shi ba? Tun ranar ɗaurin auren ki bana jin kin sake sakawa shine kika bata, zanin da ta yi goyo da shi ma na super da aka kai ki da ita a jikin ki ne".
Ƙasa na yi da kai dan bani da bakin kare kai na ina jin Mama ta na cewa
"Au da kika ce idan aka miki zani bayar da kayan zaki yi ashe da gaske kike yi? To yanzu ina sauran ko su ma duk kin bayar da su?"
"Aa suna nan wlh duk ban ma taɓa sakawa ba, shima wancan ɗin ba fa bata na yi ba iya zanin ne shi ma zuwa ta yi ta manto zanin goyo a gida shi ne na bata aro kuma ban san da shi ta tafi ba" na faɗa jin Mama zata balbaleni da faɗa, ashe da na yi shiru ya fiye mun alkhairi ma nan kuwa ta shiga faɗan ta na cewa
"Saboda ba da kuɗin ki kika siya ba ai dole ki ce baki san ta tafi da shi ba, meye amfanin rigar da ɗankwalin toh yanzu? Da kin haɗa kin bata ko banza ta mora tun da sun fi ki sanin darajar sutura. Shashsha, naga uban da zai sake siya miki kayan balle har ki wulaƙanta su" ta tattare waɗanda su Hafiz suka kawo ta ce
"Waɗannan zan riƙe kuwa" na fashe da dariya ina cewa
"Wlh bari na gidan nan duk yan uba sun shiga sun fita sun gurɓata mun ke Mama gaba ɗaya kin koyi faɗa bayan ba halin ki ba ne" bata kula ni ba ta wuce ɗaki ta bar mu da Anty Labiba. Sai bayan isha'i da Anty Labiban zata ta fi ta ke cemun
"Yau ɗin zamu tafi ko se daga baya zaki zo?"
Na bi ta da kallon rashin fahimta, Mama da ta shigo ɗakin ta ce
"Gidan ta zaki je ki zauna kafin mu dawo tun da kin ce ba zaki koma gidan ki ba". Na yi rau da ido na ce
"Amma Abba ya ce na zauna a nan ai"
"To ba zaki zauna ba idan kuma kika cika mun ciki wlh yanzu zaki tattara ki koma gidan ki. Ina dama kin zaɓe shi sama da nan ɗin? Da ya kore ki ya ce ki taho ba share guri kika yi kika zauna ba? Tun da haka kika zaɓawa kan ki ai shikenan, shi dai mutunchi mutum shi yake siyawa kan sa tunda ke kin saryar da naki ai shikenan" Mama ta faɗa cikin fushi tana gamawa kuma ta fice daga ɗakin ta barmu.
Anty Labiba da ke tsaye ta koma ta zauna kusa da ni haɗi da dafa kafaɗa ta, kamar ina jira na fashe da kuka na faɗa jikin ta, ta ce
"Bazan ɓoye miki ba ran Mama a ɓace ya ke da ke Halima amma na lura rashin hankali sam bai bari kin fahimci haka ba"
"Toh ai bata faɗa mun ba" na faɗa cikin kuka. Ta ɗago ni daga jikin ta ta ce
"Ke baki da tunani kenan, baki san abinda kika yi zai ɓata mata rai ba sai ta buɗe baki ta gaya miki? Halima har sai yaushe zaki fara tunani daidai da shekarunki ne?
Yanzu bayan duk rashin mutunchin da Mijinki ya yi kin san kuma labari ya zo kunnuwan su, baki yi tunanin ya kamata ko a waya ne ki kira ki bada haƙuri ba sannan sai yanzu ki iya ɗakko ƙafa ki zo gidan ki ce zaki zauna. Na jinjinawa ƙarfin hali irin naki".
"Ke fa kika ce ko me zai yi mun na yi haƙuri na shanye, kuma na san idan na zo na faɗi wani abu akan Bilal ke zaki fara cewa dama ai kin faɗa" na sake faɗa ina ƙoƙarin tsaida kuka na. Ta yi murmushin da kana kallo zaka san na takaici ne kafin ta ce
"Yanzu ai kin gani da idon ki abin da na faɗa ɗin ko? Kuma saboda kar muyi magana shiyasa kika zaɓi ki nuna masa iyayen ki ba su da mutunchi a idonki zai iya zagin su kuma ki iya cigaba da zama da shi ko?"
"Bilal bai zage ni ba Hajjan su ce, kuma wlh bayan sun tafi ya dawo ya bani haƙuri kuma ko cewa da yayi na taho gida ya gaya mun saboda Hajja ne amma ba har ransa yayi maganar ba" na faɗa, sai ta sake ni ta ce
"Ni wlh yanzu abubuwan da kike yi sun daina bani haushi tausayi kawai kike bani saboda baki san me kike yi ba. Wannan haukan da kike yi ya wuce So Halima you are obsessed with him idan kuma baki yiwa kanki faɗa kin fahimci zahiri ba zaki haukace a banza ranar da kika fahimci Son ma So wani kike yi. Yanzu ke kin yarda da wasan da miji zai fututtuke ya ci miki mutunchi sannan ya dawo daga baya ya ce miki wasa ya ke yi wasan ma kuma ya haɗa har da iyaye a ina ake haka?
Ke ki gwada yi masa irin wasan ki gani idan zaku kwashe lafiya, ba zagi ba, ki gwada ɗaga masa murya ko kuma cikin wasan ki ce masa BANZA kawai ki gani a ranar idan bai sauya miki kamanni kafin ya kawo mana ke ba.
A soyayya akwai sanin ciwon kai Halima, a soyayya akwai sanin martabar kai, a soyayya akwai mutunta kai, akwai aji. So is not do or die affair Halima duk muna soyayya muna da waɗanda muke so amma hakan ba shi ya saka muke banzatar da kanmu duk da sunan So ba zaman ki da ni bai amfana miki komai ba domin babu abinda kika koya. Ba alfahari ba ni na yarda da kaina kuma na san na isa mace. Kin sani da ace sakarya ce ni irin ki da ban kai labari a gidan Saleh ba. Na goga da dangin miji na goga da matan bariki da na riƙe Allah na kuma yi amfani da baiwar da ubangiji ya mun a matsayi na na mace a gaban idonki komai ya zama labari. In da na bari soyayyar sa ta rufe mun ido yanda kike yi a yanzu na bishi a yanda na tarar da shi ƙila yanzu idan ban mutu da baƙin ciki ba da tuni na daɗe da zarewa sai ke akan Bilal da bai wuci jariri a makarantar tantiran Maza ba.
Yau da ace Bilal is reciprocating, yana maida miki martanin abin da kike yi masa tare kuka zauce kuke haukan ku babu mai ce miki dan me? Babu mai ganin baiken ki domin dama ai Hausawa suka ce ka gaida mai gaishe ka amma a nan, ke kaɗai kike kiɗan ki kina rawar ki. Ya mayar da ke wawiya, sai idan buƙatar sa ta tashi yana so ya cuceki ya miki wayo a lokacin ya ke gwada miki kina da amfani a gurin sa da zarar kuma ya samu biyan buƙata shikenan da ke da babu duk ɗaya kuke a wajen sa.
Kalle ki, aure kusan shekara biyu amma kullum jiya i yau babu wani canji a tattare da ke wanda za'a ce kin tsinci wani abu cikin auren soyayyar da kika na ce sai kinyi. Ki kalli ƙawayen ki da kike musu dariya kina ganin sun auri waɗanda basu da ce da su ba, hatta da Hansa'u da kike cewa zata auri sa'an Babanta idan akajera ku dake da kika auri yaro sabon jinin sai an ɗauke ta sau dubu ba'a ɗauki ki ba saboda ta fiki walwala, ta fiki kyan gani da ka kalle ta baka buƙatar a faɗa maka tana cikin farin ciki a gidan auren ta ko ita kaɗai ta ishe ki ishara da ki gane ƙuruciya ba ita bace soyayya a gidan aure, dacen abokin zama shi ne kan gaba.
Yanzu ko sati biyu baki rufa ba haihuwar fari amma tun kina gadon Asibiti yake watangaririya da ke. Mazan kirki ana roƙon su basa so ake ɗauke matan su a tafi da su gida wanka amma me tun yana miki hannun ka mai sanda har ta kai ya fito ƙiri ƙiri ya kore ki wannan wane irin rashin daraja ne?
Yanda mata muke so mu auri miji mai aji haka kowanne namiji yake son samun macen da ta san kanta, kisan kanki a sanda miji ya miki abin farin ciki haka ki san kanki a sanda ya ɓata miki rai amma ba ki zama ballagaza ke son miji duk in da ya ja ki ya watsar nan zaki yi a lissafi na hankali ma kin san dole wata rana ya ƙosa da halin ki. Wallahi idan baki shiga hankalin ba Halima akwai ranar da sai kin ɗora hannu aka kin yi ihu a sanda Bilal ze gwada miki ke ɗin ba komai ba ce a gurin sa, a kan idon ki ze ɗakko mace mai aji da ta san kanta ya riritata a sannan kowa zai zage shi ace ya wulaƙanta ki amma gaskiyar magana ke kika fara wulaƙanta kanki ba wani ba".
Maganganun ta na ƙarshe suka tsaya mun a ƙahon zuci, Bilal ya auri wata mace bayan ni, ina addu'ar idan akwai ƙaddarar auren wata mace a rayuwar sa bayan ni ubangiji ya ɗauki raina kafin na ga lokacin domin ko ban mutu ba na tabbatar sai na kamu da ciwon da zai nakasta ni. Ta yaya ma za'a yi Bilal ya so wata bayan ni? Wane irin mugun fata Anty Labiba take mun haka? Mai ya sa a koda yaushe ita bakin ta baya taɓa faɗar alkhairi sai aka sin haka?
Ita ta mun baki akan Bilal, ita ta fara faɗin ko xa na aure shi bazan samu farin cikin da nake kwaɗayi ba gashi da wasa wasa bakin ta ya na neman kamani.
Nayi juyi haɗi da ƙara toshe kunnuwana saboda yanda kukan Al'amin yake neman ya hanani yin tunani mai kyau. Yau da wuri ya fara dan yanzu haka ƙarfe goma da minti biyar na dare. Tashi na yi jin kukan na sa yana