Showing 93001 words to 96000 words out of 257873 words

Chapter 32 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

501

mata ai matsayin su ya fi ace can wata za'a aiko ta faɗa musu kawai ta ƙyale su idan ma za'a je ɗin se gobe da safe tukunna tun da yanzu dare yayi. Har ƙarfe tara yana gidan Hajjan sai da ya ci abinci kafin yayi mata sallama ya tafi gida a bakin titi suka sake haɗuwa da Nasir ya ringa masa masifa da ya ce masa bai je asibitin ba har sannan amma ko a kwalar rigar sa ya ce shifa sai da safe sannan zai je. Sai da ya koma gida kuma gaba ɗaya ya kasa tsaye ya kasa zaune. Har ya kwanta ya ringa jin kamar hakan da ya aikata ganganci ne musamman da bai san me suka faɗa da suka je gidan ba kar wannan ƙin zuwan da zai yi ya sa a gasgata maganar su. Sha ɗaya tayi amma haka ya zura jallabiya ya fita. Bai kuma yi nisa da fita daga layin su ba wasu da bai san ko su waye ba suka tare shi, kafin ya yi ihu suka rufe masa baki su uku ne, mutum biyu suka masa dukan tsiya ɗayan ya haye mashin suna gama jibgar sa suka zare wayar sa suma suka hau mashin ɗin su ka arce.

San da aka maida shi gida a lokacin da ya haɗa ido da Halima se ya godewa Allah da abin da ya faru da shi domin da bai san da wane irin ido ze kalle ta ko ya kalli yan uwan ta ba dan haka nan ya yarda haƙƙin barin ta da wahalar naƙuda ne ya jefashi halin da ya samu kan sa a yanzun amma kuma sanadin haka ya shafe laifin sa a idon dangin ta babu wanda ze tayar da maganar ƙin zuwan sa asibiti. Amma kuma bai zata za'a dawo da Halima gida ba, ya ɗauka daga haka zata wuce gida wanka amma kuma sai gashi an maido da ita, wannan tabbas be yi masa daɗi ba saboda shi dai yana so ta tafi gida wanka ko babu komai zai samu sauƙin wasu hidimomin amma ita ya rasa dalilin ta na son dole se ta zauna a gidan ba zata tafi gidan su ba. Shi ya cewa Hajja ta yiwa su Anty Labiba magana akan su maida Halima gida shima can gidan Hajjan zai tafi amma suka ƙi, zaman kwana biyar ɗin nan tabbas ba dan Anty Amina ba da bai san yanda ze yi ba saboda shi dai bai yi wani tanadi ba.

Shi ya sa ya ci gaba da langwaɓewa yaƙi ƙarfafa jikin sa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin sun haɗo kayan barka, ko da bai kama ƙafar wanda aka kawo daga gidan su Haliman ba amma dai sun fitar da shi kunya dan da ace shi suka bari ya yi ko ya bayar da kuɗin ayi da tabbas ko rabin hakan babu lallai ya samu. Yanzu ragon suna kaɗai ya rage masa, da yayi zaton tun da Abba ya yiwa takwara ƙila cikin halin dattako irin nasa ya bashi rago kyauta a yankawa takwaran sa, amma saɓanin da suka samu da Halima akan zancen sunan ya tabbatar masa da ko da ace Abban ya ambata ze bada tabbas ba zata bari ba domin ya lura huɗubar Anty Labiba ta fara tasiri a ƙwaƙwalwarta tun da har zata iya ɓoye abu a ɗaki ta ringa ci ita kaɗai yana kwance bashi da lafiya amma bata bashi ba; ya san kuma huɗubar Anty Labiba ce.

Already kayan abincin su dama saura ne ya san kuma kafin yan barka su janye zuwa ma sun ƙarasa cinye komai sannan azo batun cefane da sauran kunji kunji, gaskiya shi ba shi da sukunin da zai iya kulawa da maijego a yanayin da ake ciki, ya mata hannun ka mai sanda taƙi ta fahimta shi yasa kawai ya yanke shawarar biyo mata ta wata sigar ya rutsata a ɗaki ko zata ji tsoro ta tafi amma duk da haka shi bai ga alamar zata tafi ba tunda ma maganar taron suna ta ke yi.

Ko naman ƙaurin da aka kai gidan su da farko ya ji daɗin abun amma da ya je gidan Hajja se abub ya juye masa zuwa ɓacin rai. Hajja ta ce masa wulaƙanci ne ya sa zasu aika musu da ɗanye nama saboda su ja a zage su a gari bayan kowa ya san yanzu an dena wani ƙauri se su sarakan iyayi, idan dan Allah ne kuma ai da gidan Bilal ɗin ya kamata a kai San a yanka idan so ake a siya masa mutunchi ba wai a wani sako musu ƙafar baya ɗaya da rabin ƙirji a buhu a kai musu gida ba. Ta ringa masifa, hatta da kayan barka sai da tayi ƙorafin saboda nan ma a nuna musu iyakar su ya sa zasu haɗo kaya kamar zasu buɗe kanti, ai ba gwaninta suka yi ba, taƙamar mace ai ta gidan miji ce ba ta gidan uba ba idan so suke suyi bajin ta se su buɗa masa Abba ya saka shi a harkokin sa shima ya samu kuɗi ta yanda ze ringa musu abu na bajin ta yanda suke so. Maganganu dai ba kai ba ƙafa wanda shi kuma ya ji su kamar fami a ran sa dan daman abinda ya daɗe yana ci masa tuwo a ƙwarya ne ya dai rasa da wa zai tattauna da zai fahimce shi shi yasa yake yin shiru.

Yanzu tunanin ta in da ragon suna zai fito ya ke dan dagaske ba shi da wasu kuɗi a hannun sa kuma bai yi yunkurin nema ba. Hafiz ya saka ran ze iya masa wannan rufin asirin tun da ya iya bashi na layya ma balle wannan da ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ya ce masa Dad ɗin sa ya yiwa takwara, to kuma tafiyar gaggawa ta kama shi ranar da ya ce masa zasu dawo Kano se dare ya sake kira a wayar Haliman ya ce masa ba ze samu shigowa Kano ba tafiya ta kama su zasu tafi Finland amma ze tura masa da saƙo har yanzu kuma saƙon bai iso ba bai kuma san ta yanda zai same shi ya tuna masa ba. Kuɗaɗe da suke haɗawa na abokanan su na unguwa ko karɓar su a hannu bai yi ba ya ce a bawa Kabir dama akwai shaddojin da ya siya a gurin sa har an ɗinka bai ƙarasa biyan kuɗin ba da ya san Hafiz zai masa haka da ragon ya siya da su idan ya so in akayi albashi sai ya cikawa Kabir ɗin. Da wannan fushin ya komada niyyar karɓar wayar ta ya duba Hafiz ɗin ko ta Whatsapp ne amma ta tare shi da zancen shirme ta sake ɓata masa rai.

Haka ya kwana yana juyi da tunanin ta in da rago zai fito, wani tunani ya yi, ya tashi da sauri ya shiga laluba rigar da ya cire. Shaf ya manta da ya yo swapping na layukan sa. Rashin azanci ya sa ya manta bai siyi ko ƙaramar waya me touch light ba, ta yuwu ma Hafiz ɗin ya tura masa kuɗi ta account bai sani ba. Ɗan dama dama ya ji, duk da dai ko ya tura ɗin dole se ya je banki saboda ba asalin account ɗin sa wanda aka ya she shi ya tura masa ba wanda ya ke saving a ciki ya bashi shi kuma dama bai yi activating USSD transafer ba dole se ya je banki rufin asirin da Allah ya masa kenan da tuni nan ma sun yashe shi. Da wannan murnar ya yi bacci, washe gari kuwa daga sallar asuba bai dawo gidan ba ya wuce gidan su in da za'a raɗin suna daga can kuma bayan gari ya waye sosai ya wuce banki.

HALIMA
A makare na tashi saboda baccin da ban samu na yi da wuri ba. Kallo ɗaya za'a mun a karanci damuwar da ke cunkushe cikin zuciya ta wadda fuskata ta gaza ɓoyewa. Ko da na yi wanka gado na sake komawa na kwanta dan bani da kuzarin da zan iya yin wata kwalliya. Ina kallon Baba Jummai har ta gama shirya Alameen ya yi kyau sosai ta ringa masa rawa kafin ta saka shi cikin gadon sa ta fita ta bar mu bayan da ta sake jaddadamun akan na tashi na shirya kafin mutane su fara zuwa.
Ina saka kayan ina tunanin yanzu idan muka yi baƙin me zan basu? Sai lokacin na jinjinawa wautata, da na sani kawai na cewa Anty Labiba ya bani kuɗin, har ga Allah ba zan so aga gazawar Bilal ba musamman a irin wannan lokacin.

Tunani na yi ko na bawa Baba Jummai ta je tayi cefane idan ya so na kira maƙwafta na su Maman Yusuf su yi abincin tun da ko jiya da rana sai da ta aiko ta tambaye ni akwai aikin da za'a yi na ce mata babu, ni duk na manta ma ko ba'ayi abinci dan kowa ba ai na yi saboda maƙwafta na tun da dai ban gaya musu ba zanyi taro ba kuma a cikim layin ko ba zasuyi taron suna ba su kan yi wani abu a aika gida gida.
"To ko snacks zan yi order?" Wata zuciyar ta raya mun, na zauna gefe gado haɗi da rafka tagumi. Ko ban bawa Anty Labiba komai ba na san da na faɗa mata gaskiyar Bilal ya ce bashi da kuɗi ƙarƙari ta zage shi amma za'a yi komai a kawo mun daga gida amma yanzu na ce mata ni ce bana son yin taron sunan ko dai kawai na haɗa kaya na na tafi can gidan tun da su zasu yi taron a can? Amma kuma Bilal zai yarda? Duk na ringa jerwa kaina tambayar da bani da mai amsa mun. Sanda na fito daga ɗaki tara har ta gota amma kamar ba gidan suna ba babu wanda ya ƙwanƙwasawa mana ƙofa balle mutane su fara taruwa. Har raina na ji babu daɗi na tabbatar kuma Mama ta faɗawa yan Galadanci kar su zo saboda bada haka ba tun sassafe nasan tsofafin gidan mu zasu zo karɓar suna su kuma yan gidan su Bilal ba na ce ga abinda ya hana su zuwa ba.

Da ƙyar na tura shayi da ƙwan da Baba Jummai ta soya mun, ina zaune zugui ni kaɗai dan Baba Jumman ta shiga wanka, get na ji ana bugawa. Se da na dan zabura a raina na shiga addu'ar Allah ya sa kona wanene ba daga ɓangare na bane. Mayafi na ɗakko a ɗaki kafin na fita na buɗe bayan da na tambayi wanene. Maman Yusuf ce da surukar ta inna da kuma Maman Aliyu. Ina murmushin yaƙe na basu hanya suka shigo, bayan sun zauna muka shiga gaisawa,
"Tun sassafe na cewa Sidi idan ya ga kun buɗe ƙofa ya gaya mun shiru shiru dai na ce bari mu shigo yanzu" Maman Yusuf ta faɗa. Na yi murmushi kawai ba tare da na ce mata komai ba kafin na miƙe na shige kitchen na samu jikin cabinet kawai na jingina ina tunanin me zan basu.

To dai ko bamu da dangi daga ni har Bilal ɗin ace yau ana suna a gidan mu ya ci a ce mun tattaro maƙwafta sun rufa mana asiri balle daga ni har shi babu wanda za'a yiwa gorin yawan zuri'a amma ace ko ƙuda babu da sunan ya zo taya mu murna. Muryar Baba Jummai da na ji ta sa na shiga share hawayen da suka fara saukar mun da sauri, ta wuce ni, tukunyar da ke kan gas ta buɗe bayan ta ɗebo kwanuka ta shiga zuba miya, na ringa kallon ta da mamaki ita dai bata ko kalle ni ba har ta gama zuba miyar ta jera a try ta fita da su kafin ta dawo ta zuba tuwo shima ta haɗa da ruwa ta fitar musu da shi. Tabbas da na farka na ji gidan na ƙamshin miya amma ban gasgata ba. Bayan tafiyar su Maman Yusuf dan basu ci tuwon ba juye musu tayi suka tafi da shi ta ce na lissafa mata gidajen da za'a aika da tuwon. Baki na kamar ze tsage dan farin ciki na ce

"Baba yaushe kika yi tuwon nan?"
"Ba dai ke sakarya ba ce a garin ki rufawa miji asiri zaki tonawa kanki asiri banda haka a ina kika taɓa ganin irin wannan rashin lissafin na ki? Yanzu ba dan nayi dabarar tashi da duku duku na yi tuwon nan ba yanda mutanen nan suka shigo da me zasu fita su bada labari? Dama salin alin da an gama kai abincin nan ki saka kayanki da na yaron nan a yar jaka mu tafi can gidan in ya so ma dawo da dare dan ni dai tunda uwata ta haife ni ban taɓa ganin irin wannan kalan tsiya ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 24*

A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce
"Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu shigo yinin suna".

"Baba ban gayawa Bilal ba" na faɗa ba tare da na kalle ta ba,
"Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku ɗin da zaki tafi shine kike cewa baki gaya masa ba? Me ze miki? Naga tun farar asuba ya fice ya bar miki gidan gashi har sha biyu ta taho ko ɗan tsako be leƙo gidan nan daga dangin sa ba, kar kiyi ta kanki kin ji. Ni dai idan ma ba zaki tafi ba se in yi gaba abu na in ya so ki saka ce gidan duk bugun da za'a yi karki buɗe tun da dai baki da abun bawa ma su shigo mikin" Cewar Baba Jummai. Se na miƙe na yafa mayafin jiki a sanyaye, ta nufi ƙofa tana cewa

"Jira na taro mana ɗan sahu ba ma fita haka da akwati ana kallon mu ba" ta fita. Komawa na yi na zauna na yi tagumi hannu biyu, ko a waya ba wanda ya kira ni se kace wata mara galihu. Tunanin in da Bilal ya tafi na shiga yi, gashi ba waya a hannun sa balle na kira shi kuma gaskiya zan so na tafi can gidan nima tun da zamana a nan dai a yau ba shi da wani amfani. Muryar Baba Jummai da na jiyo da wani da ban gane ko waye ba ya sa na fita tsakar gida na tarar da ita tare da Abubakar da Saleh suna ƙoƙarin saƙale Rago a jikin window ɗakin tsakar gida.

"Yanzu da ze yi yankan tun farar safiya ba'a yi ba se yanzu da rana ta take?" Na jiyo ta tana faɗa, su dai ba su tanka mata ba suka gama ɗaure shi kafin suka shigo falon muka gaisa a tsatstsaye suka wuce. A falon na zauna Baba Jummai kuma ta kwance Al'amin ta hau aikin gyara kayan ciki tana yi tana mita duk ta cika mun kunne se kawai na koma cikin ɗaki na rufo ƙofa ta. Har bacci ya fara ɗiba na sama sama hayaniya ta tashe ni, kamar na doka tsallen murna ganin su Amal da sauran cousins ɗina kusan su goma. Zuwan su ya wartsakar da ni musamman da na gansu da tulin ruwa da lemo katan katan ga wasu kuloli da suka ce saƙon Anty Labiba ne ta ce kar wanda ya taɓa se ta zo. Zuwa la'asar gida ya gama cika taf da dangi na kusa da na nesa ana ta harkokin arziƙi har sannan kuma yan cikin gidan su Bilal babu wanda ya zo.

Babu ce kawai Anty Labiba bata dafo ta kawo ba tun daga kan abinci zuwa snacks da abubuwan sha iri iri. Nan gurin dining ɗina ta sa aka tura shi gefe ta zuba kayan suka ringa serving, daga yanda taƙi matsawa ko nan da can daga kan abincin na fahimci ta shirya wani abu shi yasa har zuciya ta nayi farin ciki da rashin zuwan dangin Bilal dan dai na san koma menene saboda su ne. Biyar da wani abu na shiga canza kaya saboda me ɗaukar hoto da ya zo se ga yan gudan su Bilal zuga guda yan ɗakin su da kuma yan uwan Hajja babu dai dangin Baban su ko ɗaya ko matan yayyen sa a ciki.

Dama tun da Khausar ƙanwar Mijin Fainusa ta zo take tambayar bata ƙaraso ba ne na ce mata eh bata zauna ba kuma ta tafi dama jiki na ya bani sai ta kira Fainusan ilai kuwa se gasu manya da yara Anty Amina ce kawai babu.
Falo na suka fara shiga suka gaisa da yan uwana da ke zaune kafin Fadila da Fainusa suka iske ni ɗaki, Fadilan ta ce na basu key ɗin can falon Bilal tun da nan ɗin ya cika da mutane. Ban musa ba na ɗauka na bata dan zan fi so su ware gefen.

A can na same su muka gaisa mai hoton ya fara shiga can muka yi hotunan kafin na dawo tsakar gida muka cigaba. Na ɗauka za'a samu wanda zai yi tunanin basu abinci shi yasa na cigaba da sabgogina, Ummi yar Anty Sauda yayar su ta biyu tazo tayi kira na wai inji Maman su. Na tarar da su kowacce fuska a ɗaure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login