Showing 105001 words to 108000 words out of 257873 words
yi basa kama da na wanda yake fully oriented.
Ban da ma sharrin ƙwaya, na ga daga abincin da yake masifar akai har zuwa naman da ruwan da lemon babu wanda aka siya da sisin kobon sa. Cikin kuɗin da na samu na suna na yiwo cefane na, gishiri ne kawai ban siyo ba amma hatta mai da maggi sai da na siya. Komai na mu ya ƙare Macaroni ce leda shida da Taliya biyu sai shinkafa da nake zaton ba zata haura kwano ɗaya da wani abu ba shikenan abun da ya yi mana saura. Niyya ta idan ya dawo ya ci abinci muka nutsu na yi masa zancen kayan abincin ga kuma a yanda ya dawo gidan.
Ina so na je na bashi haƙuri na tambaye shi ko na dafa masa indomie ya ci kuma ina tsoron kar na je bai gama hucewa ba na sake tada wani ballin daga ƙarshe dole na haƙura na bari sai da safe zuwa lokacin duk ma abin da ya sha ya sake shi, sai da na wanke kwanukan da suka ɓata. Har na yi shirin bacci amma zuciya ta ta gagara nutsuwa, ko da ace wani abun ya sha da gaske bai kamata na barshi shi kaɗai ba. Irin fushin da na gani tattare da shi kar ya je ma ya yiwa kansa wani abun ina zaune ban sani ba. Wannan tunanin da na yi ya saka na zabura na tashi na goya Al'amin na saka Hijab na tafi ɗakin sa.
Ta window na hango shi ɗai ɗai akan kujera da waya kare a kunnen sa, duk da ya bani baya ne amma daga yanayin gefen fuskar sa na fahimci dariya ya ke yi. Wannan ya bani ƙwarin guiwar ƙarasawa na murza hannun ƙofar sai na ji ta a rufe, ƙwanƙwasawa na yi a hankali tun da ya na kusa na san zai ji amma bai amsa ba, na sake bugawa karo na biyu still yana zaune ko motsi bai yi ba hakan ya saka na ƙara ƙarfin bugun ko wayar da ya ke yi ce ta ɗauke masa hankali sai kuwa ga shi ya taso, na ɗauka buɗe mun zai yi ga mamaki na sai gani na yi ya kashe fitilun falon dan switch ɗin a kusa da ƙofar suke sannan ya koma ya yi kwanciyar sa akan kujerar.
La shakka na san ya san da tsayuwa ta hakan da ya yi kuma yana nufin kar ma dame shi ne ko kuma baya buƙata ta a gurin kenan. Na rasa me zan yi, haushi ya kamata na ji ko kuma dariya zan yi oho, haka nan na ja ƙafafu na na koma ɗaki, ina sauke Al'amin Bismillahi ya ce dawa Allah ya haɗa mu. Ashe kukan da ya yi jiya nafila ne. Yanda kasan wanda ake yankar naman jikin sa haka ya ringa zuga kuka, duk yanda zan yi na lallashe shi na yi abu ya ci tura daga ƙarshe na kwantar da shi kawai nima na fashe da kukan yana yi ina yi. Idan na tuna Bilal ya na cikin gidan yake tsala kukan da na tabbatar har maƙwafta suna jiyo shi amma bai leƙo ya tambayi ba'asi ba sai na ji duniyar ta sake yi mun zafi.
Daƙyar ya yi shiru guraren ƙarfe ɗaya bacci ya ɗauke shi, ina durƙushe gaban gadon nima a haka baccin ya ɗauke ni bana jin an yi ko minti goma cikakke ya sake farkawa da kukan da ya fi na farko.
Bani da wani zaɓi da ya wuce na ɗauki waya na kira Mama a lokacin tun da in sake komawa gurin Bilal ma ɓata lokaci ne tun da ai shi ɗin ba kurma bane balle na ce bai ji duk kukan da yake yu ba ne. Kira uku na yiwa Mama har wayar ta gama ringing bata amsa, ita kaɗai ce bata kashe wayar ta a gidan idan zata kwanta sai ni saboda raba dare da muke yi muna waya da Bilal lokacin da nake gida amma har Abba kashe ta sa yake yi su ɗin dai su zan nema su iya kawo mun agaji a kowanne irin yanayi a kuma kowanne lokaci gashi ban same su ba haka nan na aje wayar na ɗauke shi, sai na ji jikin sa ya yi zafi alamar zazzaɓi na san azababben kukan da yake yi ne ya haifar masa da shi.
Muna da paracetamol wanda aka rubuta masa a asibiti na ɗauka na bashi, haka na ringa jele da shi kamar jiya sai da sanyin asuba ya fara busawa kafin bacci ya sake ɗaukar sa. Ina zaune dan baccin ma yaƙi zuwar mun saboda gajiyar da na yi na jiyo motsin buɗe ƙofar Bilal, ban kawo zai shigo gurin mu ba, to me zai yi mana? Kwatsam kuma na ji an buɗe ƙofar falon ban motsa daga in da na ke ba har ya shigo ɗakin. Na ɗaga kai na dake mun ciwo kamar me na kalle shi, shi ɗin ma ni yake kallo fuska ba yabo babu fallasa. Mayar da kai na na yi ƙasa cikin taushin da ban tsammaci ji daga muryar sa ba ya ce
"Mai ya samu Al'amin ya yi ta kuka cikin dare?"
Ɗaga kai na yi na zuba masa idanuwa na da suka ƙanƙance saboda kuka da rashin bacci. Da zan iya da na kwarara masa ashar kafin na ce masa uban sa ne ya same shi ya ke kukan, amma harshe na ya yi mun nauyi, ba zan iya zagin miji na ba, mijin ma kuma Bilal abin ƙaunata. Sake mayar da kai na nayi ba tare da na ce masa komai ba. Ina jin sa ya matso in da na ke ya dafa ni yana cewa
"Mai ya samu idon ki haka Halima?" Baƙin ciki da takaici suka tsaya mun a wuya ban san lokacin da na fashe da kuka ba.
"Dan girman Allah ka fita, idan ka tashe shi wlh Allah sai ya saka mun" na faɗa cikin kuka ina nuna masa ƙofa.
Shiru ya yi yana kallo na kafin ya ce
"Allah ya isa kika yi mun Halima?"
"Ko ban yi maka Allah ya isa ba haƙƙin kukan da ɗan ka ya ringa yi kana jin sa kayi biris ba ze barka ba. Ka fita Bilal ka fita bana son ganin ka" na sake faɗa cikin ɗaga sauti.
Kallo na ya sake yi na kusan minti ɗaya dai dai lokacin kuma aka fara tayar da Iƙama a masallaci, ina jin sa ya sauke numfashi ya ce
"Na faɗa miki zan tafi wani aiki Abuja, Jirgin ƙarfe bakwai zan bi, idan zaki iya ki sama mun abin da zan ci kafin na fita" yana gama faɗar haka ya fita daga ɗakin na rakashi da kallo idanuwa na na tsiyayar da hawaye. Wai duk waɗanda suka auri Mazan da suke so haka suke kwasar baƙin ciki kullum ko kuwa ni ce ban yi dace ba?
Ina kwance kan gado kwata kwata bacci ya ƙauracewa idanuwa na. Wani irin zafi da raɗaɗi nake ji tun daga ƙasan zuciya ta har zuwa maƙogarona. Duk da bani da tabbacin idan ya dawo daga masallacin zai sake shigowa ɗakin amma yana fita na rufe ƙofar da muƙulli. Bana buƙatar ganin sa a yanzu, ba dan na tsane shi ba se dan kawai zuciya ta cike take da fushin halin ko in kulan da ya nuna mana. Ko rashin zuwan sa asibiti lokacin da na haihu ban ji haushin sa kamar abin da ya yi mun jiya ba.
Sai da na tabbatar ya bar gidan tunda ya ce jirgin ƙarfe bakwai zai bi kafin na fito daga ɗaki. Akan center table na tarar da farar takarda a ninke na ɗauka na buɗe.
"Kiyi haƙuri, ban san abin da ya hau kaina ba jiya, bana fahimtar komai ba kuma na iya tuna komai. Ki tafi gida, sati ɗaya zan yi idan kuma na haura haka bazan wuce kwana goma ba" abinda ya rubuta a takardar kenan. Sai na ji kamar ana yayyafa mun ruwan sanyi a zuciya ta.
Bana so na yarda da gayya Bilal ya wofantar da mu jiya, na fi gasgata baya cikin hayyacin sa ne gashi kuma ya tabbatar mun yanzu, amma kuma yaushe Bilal ya fara shaye shaye? Ko kuma dama yana yi ni ce ban sani ba? Wannan tunanin sai ya kawai da yar nutsuwar da na fara samu ta kasancewar ba wai cikin hayyacin sa ya ke ba. Na zauna na buga tagumi akan kujera. Idan ta tabbata Bilal shaye shaye yake yi na shiga uku, idan ma kuma hakan halayyar sa ce nan ma ban tsira ba. Gaba ɗaya na rasa tunanin da ya kamata na yi. Ina zaune sai da na fara jiyo kukan Al'amin kafin na tashi na ɗakko shi.
Ƙarfe sha biyu na gama komai na zuge jakunkunan da na zuba mana kayan da zamu yi amfani da su. Har na goya Al'amin sai kuma na koma na zauna na yi tagumi. Baba Jummai ta tafi tun shekaran jiya, babu wanda ya kira ni ya ji ba'asin me ya faru? Ke nan bata faɗa musu abin da ya faru ba ne ko yaya kenan?
Da kamar wuya, kai ko da ace bata faɗi gaskiyar abinda ya saka ta barin gidan ba dole wani abun daban ta faɗa ƙila kuma ya fi asalin laifin zafi shiyasa kowa yai shiru bai ce mun komai ba.
Har ƙarfe biyu ina zaune ina lissafin na tafi ko na zauna? Ban san me ta je ta faɗa ba, ƙila shi ne dalilin da ya saka da na kira Mama cikin dare bata amsa ba kuma har zuwa yanzu bata biyo bayan kiran ba Allah kaɗai ya san mai ta je ta faɗa ta haɗani da iyaye na. Idan na ce zan zauna, tashin hankalin kukan Al'amin kaɗai ya isa ya zautani, ina buƙatar wanda zai tallafa mun, ƙila ma wani abun ne yake damun sa cikin daren ni ban sani ba. Ni kai na ina buƙatar mai kulawa da ni dan ciwo nake ji ta ko ina gaba ɗaya bani da nutsuwa a jiki na da zuciya ta gaba ɗaya.
Haka nan na shafawa ido na toka na tafi gida, kafin na sauka daga Adaidaitan da ya kaini ma na fi minti biyar sai da ya gaji ya mun magana Allah ya so ni kamar an kori kowa babu mutane a layin na mu balle a samu munafukan da zasu ce na zo gida daga nan a ƙulla mun munafunci. Ɗakin Mama na wuce kai tsaye dan babu kowa a falo, bacci na tarar da ita tana yi, baccin rana ba ɗabi'ar ta ba ce sai dai idan bata da lafiya ko kuma tsananin gajiya. Na kwance Al'amin da ke bacci shima na kwantar da shi a bayan ta sannan na fita kitchen dan yunwa nake ji kamar me ga baccin da ban yi ba sai yanzu na ke jin sa.
Zainab na tarar a kitchen ɗin tana ganina ta ce
"Yanzu Mama ta ce na yi sauri na gama abinda na ke yi zata aike ni gidanki, ashe kuna tafe". Murmushin yaƙe na mata kawai dan bani da ƙarfin yin surutu yanzu, shayi na fara haɗawa na shanye daga tsayen da nake Zainab dai sai kallo na take yi sai bayan na shanye kafin na ce mata taje bakin get ta ƙaraso mun da akwati na ta wuce ni kuma na shiga buɗe kulolin da na gani na ɗebi abinci. A kan kujerar da na gama cin abincin na kishingiɗa bacci ya kwashe ni ban farka ba sai ana kiran sallar magriba.
Kaso hamsin na abinda yake damuna ya saukar mun, na miƙe daƙyar saboda kwanciyar da nayi duk jikina ya ɗaɗɗaure, ɗakin Mama na shiga in duba Al'amin na tarar da ita tana sallah sai na fito na wuce kitchen in da na jiyo motsi na samu Zainab goye da shi ta ce
"Kin tashi Anty?"
"Na tashi Zainab, tun yaushe ya farka Al'amin ɗin?"
"Dama na cewa Mama magagin bacci kike yi, ya farka tun la'asar har ma na tashe ki kika bashi nono kika ce na duba jakar ki na ɗakko paracetamol na bashi amma Mama ta hana" cewar Zainab.
"Hmmm" kawai na ce na juya na fita. Sai da na yi wanka na sake cin abinci lokacin Mama ta idar da lazumin ta kafin muka gaisa. Irin kallon da ta ringa mun ya sa na ji duk na tsargu, na faɗa mata Bilal ya yi tafiya shine na taho gida yanda ta amsa da Tohh kamar bata yarda ba ya sa na fara mata rantse rantsen da gaske na ke yi ba wata matsalaba ce tafiya ya yi.
"Ni nace matsala ce ta kawo ki gida Halima? Haka kawai ma idan mutum ya bushi iska ya kan je gida ya huta ai balle ke da dalili. An dai yi rashin sa'a mu ma tafiyar zamuyi jibi zamu tafi Umarah, in da kin yo waya kafin ki zo da sai in ce kiyi zamanki kawai tun da kin kori yar zaman wankan ta ki ko kuma ki tafi can gidan su Bilal ɗin ki zauna kafin ya dawo. Amma yanzu ma bata ɓaci ba, sai ki koma, idan kuma zaki iya zama ke kaɗai shikenan dan har da su Imamu zamu tafi Zainab kuma gida zata tafi har mu dawo dama kulle gidan zamuyi".
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 27*
Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce
"Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?"
Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun shiru ya saka duk na sha jinin jiki na.
"Baki sanar mana da wuri ba kin ga da mun ɗaga tamu tafiyar zuwa lokacin da ze dawo, ke kuma a yanayin da kike babu damar ace za'a tafi tare da ke" Abban ya sake faɗa. Da sauri na ɗago da zummar in ce masa mai zai hana daga nan har bangon duniya zan je balle kuma Saudiyya da nake ta cin burin zuwan ta har yau Allah bai kira ni ba. Duk cikin mu ni kaɗai ce ban taɓa zuwa ba, Mu'azzam har aikin Hajji ya yi Imam da Amirah sun yi Umarah sau bibbiyu ni kuwa kamar wadda aka sawa hannu duk idan tafiya ta taso ko dai na rasa visa ko wani dalili mai ƙarfi ya gifta da ina ji ina gani a tafi a barni yanzu ga wata damar ta samu ina zan yi wasa da ita?
"Zan iya mana Abba a tafi da ni kawai" na faɗa. Mama ta harare ni ta ce
"Saboda kasuwar kurmi kika ji an ce za'a je ai dole ki ce a tafi da ke. Ke matsalata da ke rashin lissafi, idan ma ƙalau ki ke ai dai kin san ba motar Zaria ba ce balle ki ce a tasha ake yankar ticket sai an nemi Visa kuma passport ɗin ki ma tun yaushe ya yi expire, ko yana nan ma da wane tsarkin zakiyi ibadar?". Hawaye na fara matsowa ina cewa
"Amma ai Abba kai ka ce in dai za'a sake yin tafiya da ni za'a je"
"Haka na ce, amma wannan tafiyar babu shiri ta zo kiyi haƙuri idan Allah ya kaimu azumi lokacin abokina yayi ƙwari sai koma tare da Maman ku kuma in sha Allahu daga bana za'a fara kiran ki Hajiya Halima, shikenan dai ko?" Abba ya faɗa yana dafa kaina. Baki na kamar ya tsage saboda murna, Mama dai ta girgiza kai kawai ta yi murmushi tare da taya ni yin godiya. Har na miƙe zan tafi na fara baza labari Abban ya dakatar da ni ya ce
"To yanzu zaki iya zama a nan gidan idan ya so a samo miki wata a Galadanci ku zauna tare ko kuma can gidan Antyn ki zaki tafi?"
Yanda Mama ta kalle shi sai na ga kamar ba haka suka tsara ba da alama ya sauka daga layin maganar da suka ƙulla kafin shigowa ta. Da sauri na ce
"Eh Abba, ko Baba Salamatu ma ko Innar su Salaha tun da babu abin da suke yi kuma ga Zainab sai mu yi zaman mu".
"Daga haka ta koma gidan ta mana sai su je can su taya ta zaman menene amfanin zaman ta a nan bama nan?" Mama ta faɗa, na marairaice fuska ina jira na ji Abban ya ce Aa sai ji na yi ya ce
"Hakan ma babu laifi ai, sai ki kira Yaya Salamatun kiji idan zata yarda taje can gidan nata, na san halin ta dai zata ce gidan siriki ba zata zauna ba shi yasa na ce ta zo nan ɗin su zauna"
"Ni fa kulle gida na zanyi na gaya maka Zainab ma garin su zata tafi dama akwai bikin yayan ta da za'a yi wani satin, Yaya Salamatu kuwa ba za'a ɗora mata hidimar Halima tana fama da kanta ba, iya kukan ɗan ta kai kanka raba dare kayi jiya kana zarya balle ita da ba cikakkiyar lafiya ba. Gara ta koma can gidan ta ta gaya masa ya samo mata wata cikin dangin sa su zauna kafin ya dawo tun da ai sati ɗaya ta ce zai yi ba wai daɗewa