Showing 234001 words to 237000 words out of 257873 words
nan zuciyarsa ta raya masa wani abu take kuma yayi na'am da hakan nan da nan ya shiga haɗa abinda zai buƙata a yar jaka, yana haɗa kayan yaji tsayuwar mota a ƙofar gidan, yanda kasan mara gaskiya ya fita da sauri ya leƙa.
A ƙofar gidan motar ta tsaya, ganin an buɗe ƙofa kuma ya saka mai motar yayi gaba, tsaki ya koma ciki amma bai rufe ƙofa ba yana kallon motar dake kunne har sannan. Kusan minti uku yana tsaye kafin ya koma ciki ya ɗauko jakar ya saka a mota ya buɗe Get ya fice.
A daren ya kama hanyar Minjibir, sai da ya nemi abinci yaci dan yunwa yake ji sosai kafin ya karɓi key ɗin ɗaki ya shiga. Wayarsa ya fara kashewa ya saka a cikin drawer bayan ya turawa da Zulaiha saƙo akan tafiyar gaggawa ta sameshi ta tafi gida idan ya dawo zaizo ya ɗauketa sannan yayi wanka ya kwanta bacci.
JALILAH
Tun daga sanda ta tabbatar da yayi blocking ɗin ta ta gasgata abinda zuciyarta ta daɗe tana raya mata akan Bilal yana so yayi amfani da ita ne kawai ya cimma burinsa sannan ya watsar da ita kamar yanda ya yiwa matarsa Halima. Harga Allah da aure take son Bilal dukda banbancin matsayi da yake tsakaninsu amma da yake shi So babu ruwansa da wannan tunda ta ganshi taji yayi mata, tayi masa uzuri a lokacin daya nuna mata cewar ba zai iya aurenta ba wannan dalilin ya saka ta buɗe masa bakin aljihunta a ganinta rashin wadatace ta saka yace ba zai aureta ɗin a lokacin ba amma a maimakon aure sai ya bijiro mata da abinda take ƙoƙarin bari harta yanke hukuncin auren nasa.
Tabbas Bilal shi ya fara nemar su ƙulla alaƙa ba kuma tayi musu ba ta biye masa, irin yanda kuma yake tafi da ita da jin daɗin da yake bata ya saka bata ƙyashi yi masa komai dashi da mahaifiyarsa da tun haɗuwar farko ta fahimci ƙwadayyace kuma a gurinta Bilal ɗin yayi gadon ƙwadayi.
Sau tari zuciyarta ta kan raya mata tarayyarsu bata gaskiya bace yana binta ne domin cikar buri tamkar yanda ya yiwa matarsa Halima har wasu lokutan ta kan yi yunƙurin datse alaƙar amma sai ta kasa, daga ƙarshe ta yaƙi kanta ta kuma tilastawa kanta yarda dashi da amincewa da duk zancen daya zo mata dashi wanda sau da yawa ta kan tuhumin kanta akan hakan, abinda ta yarda dashi Bilal ɗin yana da wata baiwa ta iya yaudara da asirce zuciyar mace shiyasa ko da ace tayi niyyar yaƙar zuciyarta ta rabu dashi sai ta kasa.
A karo na biyu ta sake bijiro masa da maganar aure wanda wani babban dalili ya janyo hakan ta kuma bashi sharaɗin idan har zai aureta toh fa sai dai ya rabu da matarsa wanda bai musa hakan ba kuma ya amince har suka fara shirye-shirye.
Ta siyi gida wanda tayi niyyar mallaka masa ya sakata a ciki idan sunyi aure, shagunan da Mamanta ta siya mata su kansu shi taso ta mallakawa domin tana so ya tsaya da ƙafarsa idan sunyi aure bata so ya zamana ita zata cigaba da ɗaukar ɗawainiyarsa.
A hannun Hafiz ta siyi gidan kuma a lokacin ta faɗa masa alaƙar da take tsakaninta da Bilal harda matsayin da suke kai a lokacin, batayi mamaki yanda Hafiz ɗin yace mata ya sani ba domin alaƙarta da Bilal a bayyane take. A lokacin ya ce mata
"Ki kula dai domin KURA A RUMBU, ABAR TSORO CE" bata damu ba dan bata ma san ma'anar karin maganar ba, sanda ya bata takardun gidan data shaida masa Bilal ta siyawa, a lokacin ne ya ce mata
"Yanzu bakya tsoron duk bayan kin gama kyautata masa ya guje ki tamkar yanda yayiwa matarsa? Jalilah Bilal ba mutumin kirki bane na shaida hakan, ta silata kika sanshi, daga sanda kika buɗe masa ido da kuɗi na zama mara amfani a gurinsa kamar yanda ya wulaƙanta matarsa, ina baki tabbacin kema haka zai watsar da ke da zarar ya samu wadda ta fiki dan haka kiyiwa kanki tunani. Bance mutum baya canzawa ba, ta yuwu dagaske yake sonki kuma ba zai butulce miki ba amma kada ki zura jiki domin duk alkhairin da kikayi masa ba zai kai wanda matarsa tayi masa ba kuma daga ƙarshe ya saka ƙafa ya tankwaɓe"
Ganin da Halima tayi musu a gidansa ya sakw tabbatar mata da tabbas Bilal ɗin ba mutum bane domin bata tsammaci bayan hakan kunya da nauyin matarsa zai bari ya cigaba da wata alaƙa da ita ba sai gashi a daren ranar ma sai da yaje gurinta, ta ringa hasaso ace ita ce Haliman a lokacin tabbas babu abinda zai hana ta kulle ƙofa ta kunna musu wuta sai dai duk abinda zai faru ya faru amma a maimakon haka sai kawai ta juya ta fita tana kuka wannan al'amarin ya saka ta canza niyyarta ta aurensa domin kuwa ta tabbatarwa da kanta Bilal ɗin ba miji bane kamar kuma yanda Hafiz ya sha faɗa zai iya aikata komai akan kuɗi.
Da wannan ta wuce Dubai a lokacin kuma har ranta ta yanke rabuwa dashi ta gaske. Ita sam bata ma ankare da yayi blocking ɗinta ba dan bata nemeshi ba sai da aka kwana biyu kawai Hafiz ya kirata yana gaya mata wai Bilal ya siyar da gida. A lokacin ta sake tsinkewa da lamarinsa, dukda kafin ta taho dama ta fara zargin wani abu akan zancen renovation data bashi kuɗi ayi amma da yake ta mata hanya-hanya tunaninta sai ya tafi akan ya kashe kuɗin ne kawai ba'ayi aikin ba ashe shi mai ɗungurungun yayi ya siyar da gidan.
Ta jinjinawa basirar Hafiz daya shaida mata takardun hannun Bilal fake ne, yayi zargin haka kuma ya sani idan ya gaya mata ba zata yarda ba shiyasa yayi shiru ya barta taga abinda yake haska mata da kanta.
A lokacin dukda Hafiz ya ce karta nuna masa komai amma ta kasa, ta ringa nemansa ta duk wata kafa amma ta gagara samunsa, ya rufe layinta kuma idan ta kira da wata number suma basa shiga alamar nan ma ya toshe kira ba zai shiga wayarsa da lambar da bai yi saving ba.
A haka labarin sakin Halima da auren da yayi tun tana Nigeria ya sake riskarta. Da kuɗinta ya auro wata ya siyi gida da kuɗin gidanta zai sakata a ciki, bata gama warkewa daga wannan shock ɗin ba Hafiz ya sake kiranta wai Bilal ya kai masa tallan shagunanta, ta shiga tambayar kanta a ina ya samu takardun shagunan? Domin dai bata bashi ba. Ta birkice ƙaramar akwatinta wacce takaddun suke ciki nan suka ce ta ɗauke su in da ta ajiye hakan kuma ya ankarar da ita tabbas ɗauka yayi, yanzu da ba Hafiz ɗin ya kaiwa ba shikenan ya dirata da ka bata ci ba bata sha ba.
Ta daɗe tana lissafa ta inda ya kamata ta rama, yana ɗaukar kansa mai wayau ya kamata ta koya masa hankali ta muna masa wayon banza gareshi lissafinsa kuma ba daidai yake tafiya ba. Akan haka ta shirya dawowa, ta hillaceshi da abinda ta san ba zai kaucewa ba wato kuɗi sai gashi kuwa yayi unblocking ɗinta da kansa.
Abu na farko data farayi shine siyar da gidan daya rigada ya ci kuɗinsa ga tsohon abokin harkarta Ahlan. Abinda ya rabasu shi ɗin ya fiya tsalle-tsalle sannan kuma yana shan giya, ita kuma duk namijin da zata kula ta fi so ya zama ita take da iko dashi shiyasa tafi harka da waɗanda tafi kuɗi a yanda zata ringa juyasu yanda take so. Ahlan matashi ne da yake cikin late thirties ɗin sa, yana da kuɗi sosai yana kuma kashewa mata su tamkar a bishiya yake tsinkosu. Tantiri ne na gaske, ko bunsuru albarka a neman mata.
A hanyar dawowa suka haɗu a jirgi hira tayi hira yake bata labarin wata yarinya mai shegen taurin kai daya haɗu da ita yayi yayi taƙi bashi haɗin kai shi kuma ya rantse tunda yawunsa ya tsinke sai ya ɗanɗana dan haka yanzu ya yanke shawara zai aureta daya samu biyan buƙatarsa ya saita mata hanya. Tana jin haka tace masa ai kuwa tana da gida na siyarwa, da farko ya ce mata Aa, auren da ba zai wuce na kwana ɗaya ba da an ɗaura zai fanshe kuɗinsa ya saita mata hanya sai kuma bayan kwana biyu da yin haka ya kira wai yana son gidan ba wani ja in ja ya tura mata kuɗinta ya karɓi Original takardu a hannun Hafiz.
Wani abin al'ajabi kuma bayan sun bar gidan Bilal ɗin tana duba status taci karo dana ɗaurin auren Ahlan, kawai ta fashe da dariya ba shiri ganin wacece Amaryar, Fadila fa ƙanwar Bilal lallai sata ta saci sata.
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 58*
HALIMA
Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida.
Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje duba Khalil ɗin tace mata yanzu sai tace toh mu biya mata mu tafi tare kawai.
Mun tarar da yan uwan Anty Ummi matarsa sunzo su da yawa dubiyar sun cika falon dan haka tace mu shiga can falon Uncle Mudassir yana nan dama, tun daga bakin ƙofa na fara jin ƙamshin turarensa, ina son turare shiyasa duk inda naji wanda yayi mun daɗe nake riƙe ƙamshin duk kuma idan na ji irinsa a wani guri sai na tuna da asalin inda na fara saninsa.
Suna zaune kan two sitter dining dake gefe a cikin falon da farantan abinci a gabansu, Uncle Mudassir har ya ci fin rabin nasa amma shi bai ko taɓa ba yana danna waya sallamarmu ta saka ya ɗago kai caraf muka haɗa ido. Sake ƙanƙance ƙananun idanuwansa yayi yana kallona nayi ƙasa da kaina na wuce ina gyara riƙon Sharifa a jikina har kuma na zauna ina jin alamun har sannan kallona yakeyi. Ba tareda na bari mun sake haɗa ido ba na yi musu gaisuwar haɗaka shida Uncle Mudassir ɗin daya taso ya dawo cikin falon yana mana sannu da zuwa.
Na saci kallonsa ganin shima ya taso, ya zauna a gefena kan 1 sitter kafin ya ɗan zame ya shiga gaida Mama cikin girmamawa, bayan sun gama gaisawa ya juya kan Anty Labiba Uncle Mudassir yayi saurin dakatar dashi yana cewa
"Karkaga ta kusa cika two sitter ka ɗauka wata babbace ƙanwarka ce itace autarmu" duk sukayi dariya banda ni da nake kallonsa ya wani shafa kai yana murmushi kafin suka shiga gaisawa. Har gurin goma muna gidan sunata hira, ni dai zaman Dr Salman ne ya takurani na kasa sakewa ƙarshe ma jin baƙin cikin gidan sun ragu yasa na koma can tareda Inayah da Sharifa da suka fara bacci.
Anty Ummi ce ta leƙo tace na fito mu tafi, na tada Inayah kafin na ɗauki Sharifa muka fita, nayi tsaye ina kallon Dr Salman a raina ina mamakin zaman me yakeyi da har sannan bai tafi gida ba? Tare muka fita muna gaba yana binmu a baya har muka hau babban titi kafin kowa ya kama hanyarsa. Bayan mun sauke Mama Anty Labiba ta fara mun taratsi wai dama mutumin nan Oga na ne shine na masa wata gaisuwar jeka ka mutu?
"A hakan kike so su baki aiki idan kin gama service ɗin alhalin bakya mutunta Oga? Wlh daga yanda naga yana kallonki na san yaji haushi tun wuri ma ki san ta yanda zaki fara bashi haƙuri". Ni dai ban ce mata komai ba har muka isa gida, Amir da baiyi bacci bane ya ke gaya mana Uncle Faisal ya zo ga saƙo can ma daya bayar a ajiye mun.
Sai da nayi wanka nayi shirin bacci dan munci abinci a gidan Uncle Mudassir kafin na buɗe saƙon da Faisal ɗin ya kawo mun, customized pouch ne na wayata, sai water bottle mai kyau shima da sunana a jiki da kuma jotter mai kama da diary. Na cire asalin pouch ɗin wayar na saka sabon ina murmushi. Shi da ya ce yanda yake jin Khadija a zuciyarsa (Matarsa) ba zai iya yi mata kishiya ba amma kuma na rasa dalilin zuwan da yakeyi da ƙananan kyaututtukan da yake yi mun, duk sanda zai zo gidan sai ya taho mun da wani abu amma kuma ya ce shi ba zawarci na yakeyi ba.
Gyara kwanciya nayi bayan na kashe filila na rufe ido na amma bacci ya gagara ɗaukata, tunanin haɗuwarmu da Bilal jiya ya shiga dawo mun. Tashi nayi zaune na jingina bayana da allon gadon haɗi da rungume ƙafafuwana na zubawa wardrobe ɗin dake kallona ido ta cikin duhun daya mamaye ɗakin.
Babu wata alama data nuna kewa ko damuwa a tattare da Bilal, dukda na sani shi ɗin gwani ne gurin iya ɓoye labarin zuciyarsa ta yanda yake matuƙar wahala ka iya karantar yanayinsa ta cikin ƙwayar ido ko a kan fuskarsa amma nayi tsammanin na tsinci wani abu musamman da nake yawan jin ana faɗar Maza sukan shiga wani hali idan suka rabu da matansu musamman idan ya kasance su suka zalinci matan amma ya akayi ni a kaina abin ya zama akasin haka?
Babu wata damuwa a tattare da Bilal, idan ma ba idanuwa na bane sai naga kamar har haske ya ƙara da kyau alamar bashi da wata matsala a rayuwarsa. Idanuwana suka kawo ruwa nayi saurin share su kafin su fara ɗiga sannan na koma na kwanta ina jan numfashi ta baki a ƙoƙarin kwantar da zuciyata. To wai ma mai zai dame shi ne bayan yana tareda Duniyarsa? Abar ƙaunar sa ya kuma rabu da kaskar da liƙe masa ai dole.
Cusa kaina nayi cikin pillow na saki kukan dana kasa haɗiyewa. Na yarda shi dai Bilal bai taɓa so na ba kawai ni nayi ta cusa kaina na kuma kasa gane hakan tuntuni. Nasha ji da karanta labaran mazaje sa suke cin amanar matayensu da wasu a waje amma ban taɓa cin karo da irin Bilal ba, yanzu nake ganin kamar ma da gayya ya bada ƙofar da zan fahimci abinda yake aikatawa har ma kuma ya barmun shaidar da ko na ci gaba da zama dashi to fa ba zan sake samun kwanciyar hankali ko nutsuwa a tareda shi ba.
Idan na tuna musayar kalamansu da Jalilah da kuma ganin da nayi musu a cikin gidana sai in kasa gane dalilin daya saka har yanzu nake jinsa a zuciyata. Ya kamata ace tun da daɗewa ya fita a raina irin azabar daya ganawa zuciyata har ma da gangar jikina amma dukda haka amma a koda yaushe cikin yi masa uzuri nake. Rabuwa da hawayen nayi sukayi ta shatata tsayin lokaci kafin na tashi na ɗauro alwala na shiga jera raka'oi har saida naji nauyi da ƙuncin daya tasarma mamaye zuciyata ya sauka. Na daɗe a zaune ina tasbihi da yiwa annabi salati har saida idanuwana suka fara rufewa kafin na shafa addu'a na haye gado ban ko ƙara ko minti biyu ba bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba dani.
Alhamdulillah, tunda ubangiji ya lamunce mun na durfafi kai masa kokena koda ace guguwar ƙaunar dana rasa yanda zanyi da ita akan Bilal ta taso mun dana kalli gabas zanji komai ya wuce tunanina ya saitu na dawo kan hanya.
Washe gari ta kama asabar kusan wuni nayi ina aikin yiwa Al'amin da Inaayah snacks da zasu kai makaranta a gobe Lahadi zasuyi picnic shine kowanne ɗalibi zai kai wani abu daga gidan Anty Labiba tace nayi musu cake da samosa. Sai yamma lis na gama nayi wanka, bayan sallar magriba ina azkar na kunna Data dan yinin ranar gaba ɗaya ban hau online ba, ina kallon saƙonnin da suke ta shigowa, number da na gani ta saka na ɗauki wayar da sauri ina dubawa.
Na goge duka numbobinsa amma haddarsu bata goge a ƙwaƙwalwata ba dan haka ina gani na gane shine dukda wannan layin ba sosai yake amfani dashi ba a lokutan da yake yawan tafiya Abuja ne yake kirana dashi dukda banyi saving ba amma na haddace number.
Kife wayar nayi ba tareda na karanta abinda saƙon ya ƙunsa ba, na san ba zai wuce shirmen daya fara yi mun waccen ranar da muka haɗu ba ne zai cigaba ni kuma banida lokacinsa a yanzu.
Sai da nayi sallar isha'i kafin na tashi daga gurin na zuba abinci na fara ci kenan Anty Labiba tace mun wai Abba yana ta kirana bana ɗauka in kirashi yanzu hakan ya sa na tashi na ɗakko wayar.
Abban na fara kira bayan mun gama maganar da zamuyi har zan ajiye wayar zuciya ta ƙwadaita mun son ganin saƙon daya turo dan haka na shiga Whatsapp ɗin na buɗe.
"Na san ko duk duniya zasu juya mun baya ke kaɗai ce ba zaki gujeni ba My Halims, ina cikin wani mawuyacin hali ina kuma buƙatar taimakonki. Idan kin amince zaki taimakamun ki dawo mun da amsa cikin gaggawa ki kuma shirya zan tura miki da address ɗin in da zaki sameni, na tanadar miki da amsoshin da kika daɗe kina bukatar jin su daga gareni, duk abinda ya faru shiri ne na tabbatar kuma zaki fahimci haka idan kika saurari bayani na. Bilal ɗinki." abinda ya rubuta a saƙon kenan.
Guri na samu na zauna