Showing 87001 words to 90000 words out of 257873 words

Chapter 30 - KURA A RUMBU HAUSA NOVEL

23 Oct 2025

477

su Abban su su zo su gani idan ya so go be kwana biyar se aje a kai musu ko?" Cewar Mama. Labiba ta taɓe baki ta ce
"Ba dai zaki haƙura da wannan al'adar ɗaukar maganar ba? Meye wani abin zuwa a gani a kayan barka se kace lefe? Kuma da zaki gayya to su suzo kai kayan kin dai san can gidan su Bilal bana zaton ko ƙyalle sun tana da da zasu gabatar a matsayin kayan da suka yiwa yaron nan. So kike a maimaita ta lefe ko a sake samun abun da za'a yi ta terere dashi a dangi, ai shikenan".

"Toh Labiba ya kike so na yi? Kin dai san haka suke al'adar su, yanzu idan ba'a kira su ba se ki ji ya zama abin magana" Maman ta faɗa. Labiban bata sake ce mata komai ba ta wuce ɗakin da suka ajiye siyayyar kayan barkar da suka yi ta shiga fito dasu. Cikin akwati set me uku da kit ɗin sa ta shiga shirya kayan. Kaya masu kyau da tsadar gaske suka siya. Kusan duk wani abu da za'a buƙata na jego sun siya mata, har da set ɗin feeding bottle da bath set komi basu manta ba duk da ana siya Anty Labiba na mitar mijin ta ya kamata ya siya mata amma kuma itan ce me sake zaƙulo wasu abubuwan a siya har da gado ta basu na minal ɗin ta a pre order ta siye shi kafin yazo har yarinyar ta fara tafiya se kawai ta ajiye shi yanzu kuma ya zama rabon su Halima.

Mama dai na tsaye tana kallon ta har ta gama jera na yaron a babbar akwati da ta uku kafin ta shiga zuba na Halima a ta biyun wanda duk an ɗinka su. Kala shida ne Atamfa uku lace biyu da shadda ɗaya se mayafi harda takalmi da jaka set bibbiyu. Sauran tarkacen undies har da body sprays da body mist duk ta zuba a kit ɗin, ta tayar da su tsaye kafin ta kalli Mama tace
"Tsakani da Allah ko mu muka mata cikin iya waɗannan kayan sun isa".

Mama tayi murmushi kawai tana kallon ta, Labiba akwai daru. Ƙarara take adawa da lamarin Bilal da Halima amma yanda ta zage ta kashe kuɗi a sabgar auren Halima zuwa haihuwar ta ba zaka yarda bata son auren ba.
Kuɗin da Abba ya bata ta ciro daga aljihun rigar jikin ta ta shiga ware su, ta miƙawa Mama wani kaso ta ce
"Gashi nan ki rage asara wannan kuma zan haɗa akwai kuɗin ta tun na barkonon da muka taɓa siya zan haɗa su na siya mata sarƙa ta samu ta fitar suna". Mama na dariya wai ta rage asara ta karɓi kuɗin tana juya su tace

"Da kika ce ba zaku yi taro ba"
"To ko babu taro ai dai zatayi kwalliya na san kuma yan uwan sa ba zasu ƙi zuwa ba ƙila su zasu yi sunan; Allah dai ya kaimu gobe muga zubin su, ko zasu mata ƙauri ma oho" cewar Anty Labiba. Sai Mama ta bata amsa da cewa

"Ke ma da neman magana kike Labiba, cewa fa tayi har account ɗin sa sun yashe komai waɗanda suka ƙwace masa waya. Idan ya samu sararin yin haƙiƙa ma ai yayi"

"Idan ma ƙarya ya ke Allah ya biya bakin sa ya sa a kwashe ɗin" Anty Labiba ta faɗa daga nan ta zura Hijabin ra tayi wa Mama sallama akan zata je kasuwar rimi ta dawo.

*******************
Cike da walwala na ƙare yinin ranar ban da ma zuwan Hajja da ta so ta ɓata mana farin cikin mu amma ban bari maganganun ta sunyi tasiri a raina ba. Dab da la'asar Abba tare da Baba Salahu da Baba Munzali suka zo duba Bilal, tun aure na zuwan Abba na farko kenan gida na. Na ji kunya ta yanda ko ruwan robar da zan basu babu a gidan balle a je ga lemo ko wani abu se pure water na juye musu a Jug duk su ukun ma babu wanda ya sha basu jima ba kuma suma tafi.

Basu jima da tafiya ba Hajja ta zo tare wasu ƙawayen ta da suka zo dubiya da kuma barka. Ina ɗaki ina shiryawa dan gama wanka na kenan Abba na kuma yana hannun Bilal yana masa wasa dan shi Anty Amina ta fara yi wa wankan kafin tayi mun.

"Wato kinga gurin zama har da kafa murhu" Hajja ta faɗa bayan da na fito ba tare da ta ko amsa gaisuwar da nake musu ba. Lanti, ƙawar ta ta ce
"Zancen da na ke yi a raina kenan na ce ita haihuwar farin ma ba zata tafi gida tayi wanka ba?"
"Ke ko jaraba irin ta yayan zamani mana. Nan na ke gaya miki jikar Saude ba yanda uwar ba tayi akan ta tafi gida tayi wanka ba taƙi wai da wa zata bar mijin ta? Na ce Allah ya yafe mana mu da zamanin mu ake arba'in biyu" ɗayar ƙawar ta ta da ban san ta ba ta faɗa. Shikenan ta samu fili ta fara zazzaga har tana cewa tsabar mugun ta tasa naƙi tafiya.

"Duk ibtila'in daya faɗawa yaron nan amma saboda rashin tausayi ace ki zauna ki yi jego a gidan nan; ai se ki zauna kici uwar da zaki ci" take ta maimaitawa. Ni se ta bani dariya ma na koma ɗaki na barsu ina jiyo Bilal na mata magana akan ta yi shiru amma se ƙara volume ta ke Lanti tana taya ta. To wace uwa kuwa zanci wadda ban saba ci ba? Tun ma da na dawo ɗin me Bilal ɗin ya yi mun da har zata ce ba'a jin tausayin sa? Ni yanda yayi mirsisi be tambaye ni in da aka samo kayan da ake sakawa yaron ba ma shi ya fi bani mamaki tun da dai dubu goma ce ta gifta tsakani na dashi akan sabgar haihuwa haka ko da wasa be yi zancen asibiti ba balle ya tambayi waye ya biya kuɗin.

Basu jima sosai ba suka tafi, ina ɗakin Anty Amina ta leƙo ta ce mun zasu tafi itama zata bi su taje gida ta dawo, a da ina ganin kamar tafi kowa zafi cikin yan gidan su Bilal amma a yanzu kam na tabbata duk ta fisu kirki domin tayi mun abun da ko jini na ce iya kaci kenan. Daga bakin ƙofa nayi musu sallama na koma ciki, se da na ji Bilal na kira na kafin na fita na koma falon.

"Ki bani aron wayar ki zan yi kira" ya faɗa se na koma ɗaki na ɗakko masa wayar na bashi sannan ya ce na ɗakko masa wani littafi a can ɗakin sa. Numbobin abokanan sa waɗan da ya rubuta ya ringa sakawa yana kira ya sanar musu da an masa haihuwa. Hafiz ya kira a ƙarshe bayan sun gama magana ya bani muka gaisa yayi mun barka tare da ƙorafin me yasa ban kira Matar sa na gaya mata ba? Haƙuri kawai na bashi kafin na mayar wa da Bilal wayar na tashi saboda Abba na daya fara ƙananan kuka.

"Kin ji me oga Hafiz yake cewa?" Bilal ya faɗa bayan daya gama bige bigen wayar, na girgiza masa kai ya yi yar dariya ya ce
"Wai amma shi za'a yi wa takwara".
"Se kace masa me?" Na faɗa ina kallon sa tare da tuno maganganun da suka yi,
"Nace masa Dady aka saka, kin san surname ɗin ku ɗaya. Baki ji yanda ya ringa murna ba ina ga ma yau zasu zo duk da yace suna Abuja ama jirgin 6 zasu biyo zuwa Kano dama".

Kallon sa kawai na ringa yi, yanzu shi Hafiz ɗin idan ba soko ba ne da ze yarda a wace dangantakar Bilal ze yi masa takwara balle har ya saka sunan mahaifin sa ma?
"Kin san ya so ya sakawa yaron sa sunan Dadyn ne amma matar ta ce sunan mahaifin ta za'a saka shi yasa yaji daɗi sosai yanzu dana ce masa sunan Dadyn na saka" Bilal ya sake faɗa yana ruƙo hannu na.

Duk yan da na so na ci gaba da murmushin da nake yi amma na kasa, ina ɗaki ɗazun na tsinci maganar Hajja sanda take Lanti take tambayar sunan yaron ta ce mata Aminu, ina ji ta ce "lallai, baban ta aka wa takwara kenan?" Ita kuma Hajjan ta ce mata
"Baban uban gidan sa dai". Dake nesa nake jiyo maganar se na ji kamar ta ce "Babban ubangidan sa" har ina dariya na ce wato Abban ne kuma ya zama uban gidan Bilal ashe Baban ubangidan sa ta ce.

Wani abu naji ya tsaya mun a wuya, na buɗe baki amma na kasa ce masa komai se kawai na zame hannu na daya riƙe na wuce ɗaki ina jin sa yana kira na amma ban tsaya ba. Kwanciya nayi akan gado ina kokawa da abin da ya tsaya mun a wuya, amma ko har idan ta tabbata uban Hafiz Bilal ya yiwa takwara tabbas ya gama raina mun hankali ya kuma mayar da ni shashasha da ban san abun da na ke yi ba. Ina jin sa ya shigo ɗakin na rufe ido na, duk yanda ya ringa kira na da tambayar menene na yi masa banza har ya yi fushi ya fi ce ya barni. Kuka na fashe da shi mara sauti.

Bayan magriba Nasir da matar sa suka zo, ina ɗaki har sannan duk shige da ficen da Bilal yake ta yi duk be sake mun magana ba ni ma ban kula shi ba se da suka zo sannan ya shiga ya mun magana. A hannun kujera na zauna muka gaisa da Nasir ɗin kafin na cewa Aisha mu je ciki taga babyn. Kusan ƙawata ce tare muka yi islamiyya duk da dai ƙawancen namu bai wuce na gaisuwa ba idan ta kama ayi hirar duniya ko yanzun da na auri Bilal aminin mijin ta zumunchin mu be sauya daga yan da yake a da ba dan ya fi maraba da alaƙa ta da matar Hafiz akan Aishar Nasir da suka tashi tare.

Ina zaune na jingina kaina da gado na yi zurfi cikin tunani sam ban ji duk maganar da take ta mun ba har se da ta taɓa ni sannan na farga.
"Tunanin me kike yi haka Halima?" Ta faɗa ta na kallo na. Na ƙirƙiri murmushi ina gyara zama na na ce
"Ba tunani na ke yi ba bacci nake ji wlh".

"Ai fa se a hankali zaki saba hala yana muku kukan dare?" Da kai na amsa mata alamar eh se ta ce
"Yaya Bilal ne ya ke kiran ki". Hijabin da na cire na mayar sannan na fita. Daga gefe na tsaya ba tare da na kalle shi ba na ce "gani".
Nasir ya ce
"Hajiya Halima wai me ya faru ne tun da muka shigo na lura akwai yar damuwa a gidan".
"Babu komai Yaya Nasir" na bashi amsa ba tare da na ɗaga kai na ba, Bilal ya ce
"Wai yanzu kamar Halima bata san wasa ba? Daga fa munyi waya da Oga Hafiz na ce masa Dadyn sa na yiwa takwara bayan mun gama na gaya mata shikenan fa ta fara kumburi har da shiga ɗaki tayi kuka".

Sauti a sama na ce
"Ai tun jiya ya kamata ka gaya mun sunan Baban abokin ka ka saka ba na mahaifi na ba kaga da be sha wahalar takowa har gidan nan ya duba ka ba"

"Au dama ba dan Allah ya zo duba ni ba saboda na yi masa takwara ne?" Ya taso mun shi ma. Se Nasir ya yi saurin katse shi ya na cewa
"Meye haka Bilal? Wace irin maganar shirme ka ke yi?" Ya juyo kaina ganin na miƙe ya ce
"Dawo ki zauna Halima". Kai dan kar ya ce na masa rashin mutunchi ya sa na koma na zauna na ja hijabi na rufe fuska ta.
"Yanzu saboda Allah abun da be kai ya kawo ba kuke so ku bawa shaiɗan ƙofa ya hadda sa saɓani a tsakanin ku. Yanzu kai menene na cewa sunan wani can baban abokin ka ka saka masa?"

"Ni fa ba haka na ce mata ba; waya muka yi da Hafiz ya ce amma shi zan yi wa takwara ni kuma na ce masa aa sunan Dady aka saka saboda nasan sunan su ɗaya da Abban Halima. Shi kan sa ai yasan wasa ne ba wai dagaske Dadyn nasa ma saka ba amma ai ze ji daɗi ita kuma dan na bata labari meye abin ɗaukar zafi a ciki saboda Allah?" Bilal ya faɗa se na ce

"Saboda na san halin ka ne kuma ba abun mamaki ba ne dan ka saka sunan Baban Hafiz ɗin. Tun da na ɗauki ciki safa baka taɓa siya ka kawo gidan nan ka ce na ajiye ba har zuwa yanzun dana haihu kallon ka kawai na ke yi amma da matar Hafiz ɗin ta haihu ka kashe kuɗi ka cika leda da kaya ka kai musu kaga ko ai sun fi ni muhimmanci dan haka ba wani abun mamaki bane idan ka saka sunan Baban sa tun da kuna da wata alaƙa da bani da masaniya".

"Kar ki kuskura ki ce zaki zage ni ko ki mun rashin kunya Halima" ya faɗa cikin hasala yana miƙewa tsaye duk da Nasir na riƙe shi amma be fasa cewa
"Na kai musu kayan da kuɗin ki na siya balle kiyi baƙin ciki? Ban siya miki ɗin ba kuma ba zan siya ba idan ki na da ƙarfi se ki ƙwata mu ga ni"
"Wlh na fi ƙarfin na yi baƙin ciki akan abin duniya Bilal duk abin da kake zaton zaka yi ko ka yiwa wani nafi ƙarfin sa, idan da na ina saka ido na akan abubuwan da kake yi da bamu kawo yanzu ba. Kuma ko ka siya wa ɗan ka ko karka siya kai ta shafa dan idan da ina tsammatar kayi mun wani abu da ban ɗauki cikin ba ma. Idan ka ga dama ka sauke haƙƙi kan ka ka taimaka ba wani ba" na ƙarasa ina shigewa ɗaki har ina ture Aisha da hayaniyar mu ta fito da ita.

Ina jiyo yan da ya kw bambami kamar ze kama da wuta Nasir na tare shi da alama ɗakin ze biyo ni, a yanda raina yake suya duk abin da Bilal ya ke ji da shi yau ni ma daidai na ke da shi wlh. Aisha ta biyo ni ta na cewa
"Wai duk me ya yi zafi haka Halima?"
"Babu ruwan ki" na faɗa ina miƙewa. Wardrobe na buɗe na fara fito da kaya na ina ajiye wa a kan gado, ta riƙe hannu na ta na ce wa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wai gida ki ke tunanin tafiya Halima? To kije ki ce musu me ya haɗa ku?"

Kamar ta zare mun kuzari haka jiki na ya yi sanyi na gagara ci gaba da ciro kayan se na koma na zauna akan gado zuciya ta na bugawa da ƙarfi, da gaskiyar Aisha, yanzu na je gida na ce musu me?
Ba wani sauraron maganganun da take yi na ke ba daga ƙarshe na tashi na shige banɗaki na barta. Ka fin su tafi se da Nasir ya sake ƙoƙarin sasanta mu. Ban san me ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga da na fito jikin sa a sanyaye ba kamar ɗazu da yake fizga kamar ze rufe ni da duka ba. Ya ringa mana nasiha da ban baki Bilal ma ya ce na yi haƙuri shi wlh ba abinda yake nufi na kenan shaiɗan ne kawai ya ke so so ya yi wasa da zukatan mu. Sun tafiya na koma ɗaki na kulle ƙofa ta da muƙulli dan na ƙudurce a raina a wannan gaɓar ba zan wa Bilal da sauƙi ba rantsuwar sa akan sunan Abba ya sa ba zata sa nayi saurin yarda da shi ba.

Ina jin sa yana bugu da roƙon na buɗe na masa banza daga ƙarshe ya ce na miƙo masa Abba idan ma ni ba zan fito ba. Ina jin yunwa amma haka nan na zauna har se da Anty Amina ta dawo cikin sa'a har sa tsarabar farfesun jelar sa ta taho da shi, shi na ci da tea na kwanta raina babu daɗi. Har ga Allah ina so na matsa daga kusa da Bilal na tafi gida amma ban san ya zasu karɓe ni ba musamman ace matsala ce tsaka ni na da Bilal ta dawo da ni. Haka na raba dare na kasa bacci.

Washe gari guraren goma na safe Anty Amina ta ce na yi waya gidan mu na ce musu yau za'a kawo kayan barka a turo waɗanda zasu karɓa. Anty Labiba na kira na gaya mata ta ce
"Se kace wani abin kirki zasu kawo har da yin gayya; to se mun zo. Dama muma yau zamu kawo miki na nan gidan ai. Sun yanka abin ƙauri ne ko kuwa?" Ta ƙarasa da tambaya.
"Ni ma ban sani ba ƙila ko a can gidan su zasu yi" na bata amsa se ta yi tsaki kawai ta kashe wayar. Bayan la'asar kuwa se ga yan gidan su Bilal ɗin yan uwan Hajja da matan yayyen sa da suke uba ɗaya dama babu wacce ta zo barkar da su Farisa kusan su ashirin suka zo kawo kayan. Babbar akwati guda ɗaya se leda baƙa me dan girma itama da kuma saitin bawo da net ɗin jarirai.

Bayan mun gaisa na koma ɗaki in da na bar su Hansa'u da suka zo mun katsahan ba zato. Ko jiya da muka yi magana ta ce mun se bayan suna zata samu shigowa Kano kuma yau se gata. Naji daɗi sosai na riƙe yar ta da tayi kuɓulɓul gwanin sha'awa irin goyon da na ke so na yi kana kallon ta kasan tana samun kulawa me kyau.

"Anty Halima tsakani da Allah ya zaki mana haka?" Farisa da ta shigo ɗakin ta faɗa. Na mata kallo ɗaya na ɗauke kai dan nasan ba ze wuce halin na ta na tsugudidi zata yi ba kuma ba zan so ta faɗi wani abu da zata zubarwa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login