Showing 84001 words to 87000 words out of 235422 words

Chapter 29 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3515

karfin halin cewa hakane kuma Allah baiyi zakijeba kuma ma itanma saukan dare zatayi kilan Yaya Sulaiman yace mubari sai gobe mutaho dasafe don Abba bayason ana tafiyar dare..........
Gyada musu kai kawai tayi tafice tabarsu sunata shirye shiryensu.......

*****
Dayanma wujajen karfe biyar ana yima Magajiya massage din kafa Laure tashigo dakin hannunta daukeda kwandon kayan itatuwa da alama daga lambu take........

Dubanta Magajiya tayi sannan tace kigyara min fruits dinnan yanzu kikawomin cikin sauri Laure tayi kasa da kanta sannan tace"nawanke Uwargijiyata sauran inyanka ne"......

Zokiyi to Magajiya tayi maganar tana dan sosa jikinta tarasa miyasa maganin da boka yabata befara mata anfaniba haryanzu it seems like worsening kaikayin ma yakeyi.......
Dakyar tace Laure mikomin wayana akan mirror gyada mata kai Lauren tayi kafin tadauka tamika mata duban yarinyar dake mata Massage din Magajiya tayi sannan tace
"tashi kije ya isa hakanan"..........

To Uwargijiyata yarinyar tabada ansa sannan tatashi tafice abunta.....
Maida hankalinta kan wayar tayi kafin tayi dialing wani number ta kara akunne dukda kuwa takure volume wanda harna kusa da'ita na iyaji........

Daukar wayar akayi dafari aka fara mika mata gaisuwa donkuwa Laure dake cire kwallayen cikin kankana tanazaune gaban Magajiyan tanaji......

Lafiya lau Matawalle ya aiki?...
Munata fafatawa ranki shi dade yanzuma munfito daga Funtuwan badede zamu shiga mota mu taho gidane..........

Murmushi Magajiya tayi"to yayi kyau yamaganar mu inadai fatan baka cikin mutane?".....
Ah haba ranki shi dade na'isa kinsan yan sa Ido Allah yayi yawa dasu komawa nayi gefe koda kika kirani kuma maganarcan nariga na bula tayar motar Yariman yau daga shi har drivern nashi babu wanda zaiyi rai,yau karshen sa yazo ranki shidade ki kwantar da hankali don Yarima Sulaiman seya zama Sarkin Zaria ko anki ko anso,wani irin murmushi Magajiya tasaki don bakaramin dadin maganganun Matawallen tajiba sannan tace ka tabbatar babu wanda yajine?".......

Na tabbatar rankishidade.....
To sekun iso da gawar sabida wannan shine gudumawar danakeson kukawo wa Mai Martaba nikuma nayimaka alkawarin gagarumi. Kyauta......
Dariya Matawalle yashekeda sannan yace "angama ranki shidade",nan tayi masa sallama ta katse wayar tunda Magajiya tafara maganganu Laure jikinta ke rawa gawani irin zufa datake keto mata...
Bakaramin tashin hankali tashiga ba aranta tana"nashiga uku na kaddai Yarima zai mutu".......
Kallonta Magajiya tayi tana dariya kafin tace"anjima zan baki kudi kikaima Matawalle in sun iso"......
Cikin sauri Lauren ta gyada kanta tana..
"to Uwargijiyata",dukda kuwa hankalinta baya jikinta don babu abunda tafi bege ayanzu daya wuce taganta gaban Hajiya Muniba because only she can help Yarima may be... .......
Kallon Laure Magajiya tashigayi ganin tadai na gyaran kankanan sannan tace"ke lafiyarki?".....
Lafiyata kalau takarashe maganar tana faking smile dakyar ta'iya gama gyara kankanan sannan tashiga mikama Magajiyan dai dai tanaci hankalinta kwance harta gama ta sallame ta.......
Tana fita ah dakin tashiga sauri kamar kafarta zaiyanke daga karshe ma gudu tafara ganin takusa isa gidan Hajiya Muniba din yau ko sallama batayiba bare Hajiya Muniba tayi tsanmanin zata gaidata....
Haki take sosai sega hawaye kuma "nashiga uku Ranki shi dade Magajiya zata kashe Yarima Almustapha".....
Cikin sauri Hajiya Muniba tatashi tana"Laure lafiyarki kinsan mekike fada kuwa?",tayi maganar hankali tashe itadai Laure se aikin kuka takeyi tana kije kitaimakeshi don Allah lokaci yana kurewa.....

Ganin kaman Lauren bata cikin hankalinta yasa Hajiya Muniba tashiga jijjiga ta tana"kimin bayani Laure yanda kikeyi dinnan bashi zaisa ingane mekike nufi ba"......
Goge kwallah Laure tashigayi dukda basu daina zubowa ba sannan tace"dagaske nikeyi jinayi tana waya wai asace tayan motan Yarima kinsan sunyi tafiya dasafe"......
Cikeda tashin hankali Hajiya Muniba tace"tabbas Mai Martaba yacemin yau Almustapha zeje rabon abinci kauyika,tasaka an bula tayar mota kikace kominene?"....
Eh Ranki shi dade harma zasu kamo hanya kuma motar da Yariman ke cikine.........
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Hajiya Muniban ke furtawa cikeda tashin hankali "She need to save him but how?"......
Kallon Lauren tayi tana tunanin wani mataki zata dauka jitayi Laure na kozamu fada ma Mai Martaba yakira shi su tsayar da motar......
Hakane kuma cewar Hajiya Muniban kafin tace amma bazaki shiga cikin maganar nanba Laure your life could be in danger kinji.....

To amma..
Daga mata hannu Hajiya Muniba tayi sannan tace ninasan yanda zanyi ke kikoma gurin uwar dakin ki kadama tayi suspecting wani abu Magajiya is so cunning she can go to any length.....
Ina ah daki tayi wayar kikace?.....
Gyada mata kai Lauren tayi kafin Hajiya Muniba tace kijeki ninasan yanda zanyi da maganar nan.........
Cikin sauri Hajiya Muniban tafice batareda tasake bi takan Lauren ba koda ta'isa bangaren Mai Martaba bayanan wayarshi tashiga kira bejimaba yadaga cikeda tashin hankali tace "Ina bangarenka kazo don Allah akwai important magana",bata jira cewarsaba takatse call din bin wayar yayi da kallo yana mamakin wace irin important magana ne haka dukda kuwa daga muryarta zakasan cewa tana cikin tashin hankaline don haka yatashi daga fadar yayi bangaren nasa cikin sauri....
Ah tsaye yasameta tanata safa da marwa acikin dakin....
Muniba lafiya,meya faru kika kirani haka?...

Batajira yakaraso cikin dakin ba tayi saurin karasawa gabanshi tareda riko hannunshi cikin nata"kakira Yarima don Allah kace su tsaida motarsu"....
Cikida rashin fahima yace..
"kaman Yaya?".....
Kaman zata saki kuka tace...
"kafada mishi kaidai it's really important now,his life is in danger".......
Ware idanu yayi cikeda tashin hankali"Muniba fadamin meyake faruwa,what do you mean by his life is in danger?"......
Kaidai kakira please yanzu safety din shi shine first takarashe maganar wannan karan hawaye sunfara zuba sabida takasa controlling dinsu.......
Allah yataimakeshi wayarshi na hannunshi cikin sauri yashiga dialing number din Almustapha hannunshi na karkarwa amma not reachable yake cewa yakira yafi sau goma amma thesame thing yake cemasa.........
Hankali tashe yace"baya tafiya call din kifada min meya faru please?"......
Tana hawaye tashiga masa bayani"daya daga cikin bayi ne tazo tasameni yanzu hankalinta tashe wai taji wani yana waya kan akashe Yarima infact har ansace tayar motarsu ma...........

Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda mai Martaba yashiga maimaitawa yayinda kafarsa ma takasa daukarsa dakyar ya'iya zamewa yazauna ah tsakiyar dakin cikin sauri Hajiya Muniba tace we've to find a way out ranka shidade.........
Dagowa yayi yana kallonta da idanu jazir kafin yace"who's behind this?".......
Cikeda damuwa Hajiya Muniba tace yanzu bawannan bane damuwar Mai Martaba musan halinda Yarima yake ciki shine the most important.......
"I said who's behind this Muniba!",yayi maganar rai bace gakuma tashin hankali duk alokaci guda......
Hajiya Muniba data zabura tace I don't know yarinyar ma cewa tayi batasaniba sabida bataga fuskar wayeba.......
Lumshe idanu Mai Martaba yayi yayinda Hajiya Muniba tashiga consoling dinshi"don Allah being weak won't help mutashi musan abunyi".....

Cikin sanyin murya Mai Martaba yace anfada miki since tayar mota wasa ne Muniba is not as if nayi giving up kawaidai narasa abunyine I'm not my self now yakarashe maganar tareda dora kanshi kan kafafunshi Allah ne kadai yasan halin dayake ciki yanzu, Allah ne kadai yasan irin abubuwan dayajeji aranshi yanzu gawani juyi dayake jin kanshi nayi mishi lokaci guda....
Fuskar Almustapha ne kemishi gezau ah idanu tun yana little boy with that his charming smile......
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine kalmomin da Mai Martaban ke maimaitawa ko Allah zaisa yasamu sauki aranshi ya iyayin wani abun......
Hajiya Muniba ganin Mai Martaba baya cikin his normal self yasata saurin daukar wayar nashi tashiga kiran Dad cikeda damuwa tace"Yaya don Allah kaxo bangaren Mai Martaba"....

Batajira amsar saba tacigaba da kiran layin Almustapha ko Allah zaisa yashiga amma still not recheable gashi ita basanin number wani tayiba dasukayi tafiyar tare bare ta kira anacikin hakane Dad yashigo nan take fada mishi halin da akaciki......

Cikin sauri yace let me call him right now....
Wayarshi bata shiga tabashi amsa,still daukar wayarshi yayi yashiga kiran layin wasu daga cikin fadawan dasuka tafi tare amma duka daga me waya ah kashe se me not recharge.......

Subhanallah cewar Dad hankali tashe kafin yashiga kiran layin Sulaiman ba ajimaba yadauka......
"Kuna inane?"....
Muna kaduna Dad wani abu yafaru ne Sulaiman yayi tambayar cikeda curiosity jin yanayin muryar Dad din.......

Sabida kada ya tada masada hankali yace"kunyi waya da Yayanka recently ne?"......
Eh munyi Dad yacemin zasu fita ah Funtuwan Badede.........
Alright shikenan daman nakirashi wayar bata shigane se anjima.......
Shikeda rashin damuwa da zancen Sulaiman yace may be network problem ne Sulaiman din yabama Dad din ansa....
Yea probably cewar Dad din kafin ya katse wayar....

Duban Muniba da Mai Martaba yayi hankali tashe sannan yafice daga dakin atake yasa akamishi arranging mota yace daya fito sallar maghrib zasuje police station sukai report sannan sukama hanyar Funtuwan badede.......
Mai Martaba dakyar ya iya tashi yayi sallar maghrib shima adaki don yakasa fita kwata kwata......

Koda Dad din yatashi tafiya bebi takan Mai Martaban ba don yasan zai iyacewa zai bishi sede he's not in a state to follow him........
Kan kaceme labari yagama karada masarautar cewa ga abunda yake faruwa daga bayin har dogaraye dama sauransu kowa yashiga tashin hankali tareda addu'ar Allah yasa kada wani abun yasamu Yariman........

Bangaren Magajiya kuwa dataji labarin bakaramin tashin hankali tashiga ba don haka tayi saurin yin bangaren Mai Martaba don babu abunda yafi damunta kaman taji shin an ambaci sunanta ne ko yaya........
Koda taje samun Mai Martaba tayi zaune kan sallaya yana addu'o'i yayinda Hajiya Muniba kezaune bakin gado don tana fashin sallah Itakam.......

Dagudu takarasa cikin dakin tareda rungume Mai Martaba tabaya tana kukan munafurci"nashiga uku na wai maiyake faruwa damune acikin Masarautar nan,miyasa za ace Yarima yamutu
"...........

Hajiya Muniba dake gefe tana hararan Magajiya tace"cemiki akayi mutuwa yayi?", takarashe maganar tana hararta......

Dukda kukan da Magajiya keyi seda ta dago tana karema Matar kallo donkuwa yaune first encounter dinsu koda suka hada Ido seda taji gabanta yafadi donji tayi kaman tasan idanun nan amma seta daure tacigaba da act dinta"nibacewa nayi yamutuba amma dai kinsan in ansace tayar motar babu abunda zai hana accident faruwa kuma irin wayannan hatsarin dakyar mutane ke rayuwa dukdama muna fatan shidin ya rayu sede nasan ba lallai yadawo kalauba",takarashe maganar tana kukan munafurci..
....
"Mai Martaba tureta yayi ta baya ranshi bace yayinda Hajiya Muniba tace"Amma kinbani mamaki wallahi amatsayinki namai hankali dakuma shekaru irin naki banyi tsanmanin irin wayannan magan ganun daga garekiba, inbazaki fadi alkhairi ba kiyi shiru please"......
Kuma maganar cewa dakikayi babu abunda zai hana accident kuwa akwai tunda Allah nanan kuma shine meyin komai hakanan yana iyacanza al amarinsa aduk lokacin dayaso........

Wani kallo Magajiya tayi mata tana shirin yin magana Mai Martaba yace dukansu su fita su bashi waje he wants to be alone don shi maganarsuma haushi yake bashi he's worried about his Son sukuma argument ma sukeyi...........
Koda suka fitan harara Magajiya tabi Muniba dashi tana kifita idanuna banason shishigi bakisan wacece niba ah to......
Murmushin takaici Hajiya Muniba tayi sannan tace"banida lokacin ki yanzu sabida halin da ake ciki"takarashe maganar tareda wucewa bangaren ta......

Koda su Dad sukaje police station sukayi report cemusu akayi zasu kira mutanensu nacan ah bincika ko anyi accident ah hanyarnan so there is no need for them to go there sukoma gida kawai insha Allah zasu bincika musu adaren nan......
Babu yanda Dad ya'iya haka yadawo gida gurin dan uwansa yana keeping nashi company........

******
Fitowarta daga wanka kenan shiryawa tayi tsaf cikin simple doguwar riga na material kafin tafeshe koina najikinta da turare

shimfida sallaya tayi ta tada sallah haka kawai setakejin gaban ta na wani irin mugun faduwa ahaka dai harta idar da sallah duba time tayi ganin Isha yakusa kawai setace bari tajira tayi sallar Isha din......
Seda tayi Isha sannan taninke sallayar ta maidashi ma ajiyinsa fita tayi ah dakin gabadaya yau setakejin gidan shiru sabida su Amira ma baswa nan daga ita se bayin ne kira tashiga kwalama Salma baiwarta........

Cikin sauri tazo kanta akasa tace"gani Gimbiya".....
Ankai abincin su Abba ne dana Mom.....
Jijjiga kai Salma tayi alamun a'a cikeda mamaki Asma'u tace to me ake jira tunkan nashiga wanka nace azuzzuba abincin su iya Hindatu baswa gurin ne?......
Suna gurin yanzu za akai Salma tabata amsa ahankali tabe baki Asma'u tayi sannan tace daukomin na Yarima inkai dakinshi nasan by now ya'iso gida.......
To kawai Salman tace kafin tajuya takoma kitchen din........

Asma'u nanan tsaye har kusan minti biyar ba akawo abincin ba aranta tana yau meke damun mutanen nan ne gabadaya they're not active at all...
Gajiya tayi da tsayuwar tawuce kitchen din don daukowa dakanta sede to her own surprise lokacin ne ma rukayya ke kokarin sauko da coolers din daza asa abincin.........

Bin su Jamila da Hindatu tayi da kallo ganin duk fuskarsu badadi da alamar suna cikin damuwa...
Cikeda mamaki tace"subhanallah wani abunne yafaru naganku kunyi tsage tsage kaman wasu marayu?".......
Hindatu ne tayi karfin halin cewa babu komai Gimbiya.....
Dukda bata yarda dame tacedinba setace to meya hanaku zuba abincin tun dazu?......
Kame kame suka farayi batareda tabi takansu ba takarasa cikin kitchen din takarbi ludayin tashiga zuba masa abincin nasa tana...
"ayya yau Yaya Almustapha shikadai zaiyi dinner Yaya Sulaiman bayanan".......
Jamila kasa controlling tears dinta tayi don hakama tafice ah kitchen din cikin sauri Asma'u kuwa gama zuba abincin tayi tasaka ah tray sannan tafice abunta dakinshi tawuce straight tayita knocking amma shiru turo baki tayi tana"he likes being so arrogant ana zakal kale namishi girkin ma"........
Tura kofar tayi ahankali sannan tashiga dakin nashi sede to her own surprise wuta akashe Allah yataima keta wayarta na hannunta don haka takunna haske kafin tanemi switch na wutan dakin takunna koina na dakin fes yake agyare kaman yanda yake tunsafe da alama ma babu wanda yashigo......

Ajiye tray din tayi kan stool kafin taduba toilet nanma shiru babu kowa fitowa tayi ah dakin tana kiran Hindatu.....
Cikin sauri takaraso tana gaidata...
"Yarima bai shigo bane daman?"....
Gyada mata kai Hindatu tayi jiki ah sanyaye,ikon Allah tokodai yatsaya gurinsu Mai Martaba ne kafin yashigo don anjima da idar da sallar Isha yanzu to 9:00pm fa........

"Inagani hakan ne Gimbiya Hindatu takarashe maganar idanunta sunciko da kwalla",cikin sauri Asma'u takaraso gabanta tana meyake faruwa ne naga fuskokin ku duk babu walwala batakai ga rufe bakiba taga hawaye nazuba idanun Hindatu....
Subhanallahi why are you crying Iya Hindatu,wani abunne yafaru?.....

Hindatu kasa holding tears dinta tayi gawani tausayin Asma'u datake ji yasata juyawa zata tafi lokaci daya bugun zuciyar Asma'u yakaru shan gaban Hindatu tayi tana kallon ta"meya faru,kifadamin meya faru please wani abunne yasamu Yaya Almustapha kosu Amira tayi mata tambayar cikeda tuhuma?....
Shiru Hindatu tayi tana hawaye still,wani irin tsawa Asma'u tayi hankali tashe"kifada min mana,meya samesu?......
Murya na stammering Hindatu tace"babu Gimbiya"......

Jijjiga ta Asma'u tashiga yi tana"karyane kifadamin,su Amira ne?".....
Jijjiga kai Hindatu tayi alamar aa,cikeda tashin hankali murya na karkarwa tace"Ya..ya almus...ta..pha ne?"......
Yanda tayi maganar bakaramin tausayi tabama Hindatun ba hakan yasa kukanta yakaru harta kasa bata ansa...
"kifadamin mana meya sameshi Iya Hindatu?".......
Takarashe maganar tana hawaye maganan datayi da karfine yajanyo hankalin sauran bayin sukayo parloun dasauri.....

Jamila ne takaraso Itama tana kuka tace"Gimbiya don Allah kikwantar da hankalinki babu abunda zaisameshi"......
Wani irin kallo Asma'u tayi mata sannan tasaki Hindatu tadawo kanta tana kuka me tsuma zuciya"nayarda dake Iya Jamila nasan ke bazakimin karyaba,kifadamin don Allah meyasamu mijina takarashe maganar tana folding hannunta alamar roko".......
Babu abunda Hindatu da Jamila keyi se hawaye haka wasu daga cikin bayinmma...
"Don Allah kifada min amma karkicemin yamutu please i can't bear it,zuciyata bazata iya daukaba he can't just leave me like this we've a long way to go,our journey has not been completed yet don Allah kifadamin ina Yaya Almustapha Asma'u takarashe maganar tana damke da rigar Jamila duk ta cukwiwuyeta".........
Kuka Jamilan take Itama tareda rungume Asma'u din janyewa Asma'u tayi daga jikin Jamila tana bazaki fadamin ba?....
Kema dana yarda dakedin yau bakida bakin sa zuciyata tayi sanyi?.....
Yanda Asma'un keyi dukwanda ke gurin seya tausaya mata suna cikin hakane sukaji anbude kofa cikin sauri tace"kingaba nacemiki bazai taba barina ba", takarashe maganar tareda juyawa tayi hanyar kofar da gudu da zummar ganin Almustapha din sede to her own surprise Dad da Abba dakuma Mom tagani.............
Tsayawa tayi cak kafarta takasa daukarta don ganin yanda fuskokin su yake yasa bugun zuciyarta kara karuwa Mom ne takaraso gabanta cikin sauri tana"Daughter"......

Hawaye Asma'u takeyi tace...
"Mom inayake don Allah?"....
Sun iso ko,hope sun iso lafiya?.....
Cikeda tausaya wa Mom tajata jikinta Itama idanunta sunciko da kwallah tana"kidaina kuka insha Allah Almustapha will be fine"........
Lamo tayi ajikin Mom din tana...
"yana Ina don Allah kikaini gurinshi Mom".......
Ganin Asma'un is not in her right senses yasa Mom cikeda rarrashi tace"zankaiki Asma'u, I'll take you to Almustapha kidaina kukadai yanzun"........
Dagowa tayi daga jikin Mom din tashiga share kukanta"Allah nadaina Mom kikaina don Allah I want to make sure he's fine by looking at your faces nasan ba lafiya ba",kama hannun Mom din tayi tana shirin janta cikin sauri Dad yace compose yourself Asma'u you can't see Almustapha now......
Muma bamusan halin dayake cikiba bincike akekanyi tukunnan.......

Sakan baki tayi tana kallon Dad din shima kallonta yakeyi cikeda tausaya wa ana cikin haka kuma se wayarshi tashiga kara dagawa yayi dasauri yana officer ansamu wani news ne please?.......

Daga daya bangaren ne officer yace"eh yallabai"....
Yanda yaji muryar officer din ya tabbatar akwai damuwa don haka yace kafadamin meyake faruwa don Allah....
Murya akarye officer din yace...
"I'm sorry ansamu motar kunce marcedese ba?".....
Cikin sauri ya gyada kai kaman wanda yana gaban officer dinne kafin dakyar ya'iya cewa eh marcedese ce....
"I'm sorry Allah yayiwa mai motar rasuwa it was a very terrible accident sundauki body dinma zasukai hospital gobe dasafe sekuzo kukarba, Allah yajikanshi sede sunce driver din is still alive anyi rushing nashi to the hospital"........
Cire wayar Dad yayi daga kunnenshi batareda ya katse call dinba yayinda yashiga furta innalillahi wainna ilaihir rajiun.......
Innalillahi wainna ilaihir rajiun...
Cikin sauri Mom tace meya faru,kafada mana mana please.......
Idanun Dad sunyi jazir dakyar ya'iya cewa"babu abunda Almustapha ke bukata irin addu'armu ayanzu".......
Daganan yakama hannun Mai Martaba dako magana baya iyayi suka fice ah bangaren Asma'u wani irin hajijiya tadinga ji yana dibanta yayinda tafadi ah sume kanta su Jamila sukayi suna kuka mai tsuma zuciya suna kiran sunanta ......
Daukanta sukayi suka kaita daki Mom nabiye dasu abaya cikeda tashin hankali......
Salma ne takawo ruwa cikin sauri aka shiga yayyafama Asma'u din aikuwa tafarfado kuka tashigayi kamar ranta zaifita Mom ne takaraso gabanta tana...
"Compose yourself Asma'u babu abunda Son ke bukata agurinki irin addu'ar ki,stop crying please"......
Murya ah dushe tace"Mom kema kinyarda yamutu?".....
Ninasan bemutuba,wallahi Yaya Almustapha baimutuba jikina yana bani he can't just leave me like this.........
Kowa saida yatausaya ma Asma'u tsabar yanda taketa sambatu..........
Mom daga karshe kasa controlling tears dinta tayi Itama tashi tayi tafita.....
Asma'u nata ita tasan Almustapha baimutuba sudaina daura mishi mutuwa......
Jamila ne tace kiyi hakuri Gimbiya yakamata kikarbi kaddararki hannu bibbiyu Yarima adduarki yake bukata.............
Sa hannu Asma'u tayi aduka kunnuwanta tana"kudaina fadamin irin wannan maganar please,kufita kubarmin dakina ninasan mijina bai mutuba takarashe maganar tana nuna kanta"mijina bai mutuba we're still on the

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login