Showing 156001 words to 159000 words out of 235422 words

Chapter 53 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3493

haka dinner ma sede babu wanda kataba cikin biyun".....
In a very calm voice yace...
"miyasa kika daga min waya jiya?"......
Seda kirjinta yabuga tsabar yanda yayi maganar don dukda ahankali yayi maganar jidaya zakagane akwai bitterness cikin ta........
Kame kame tafarayi....
"tana ta kiranka ne cikin dare and banason katashi shiyasa nadaga"..........
Sulaiman daya kasa daure zuciyarshi daga zugin da takeyimashi ya yakiceta daga jikinshi tareda yin wulli da'ita gefe wanda harta kusan faduwa daga gadon kafin yatashi yazauna yana nunata da yatsa sannan yace...
"kinsan halin da ta shiga bayan abunda kikayi kuwa"......
Zaliha ma da ranta ke mata kuna tace....
"ita batasan miye darajar me aure bane dazata kiraka da daddare?".......
Wani harara ya wurga mata sannan yace"dukdai rashin saninta na darajar aure batakai kiba hakanan inada yakinin tafiki sanin darajar aure because ke bakida bakin daza kiyima wani ma irin wannan maganar,I love Sumayya and I want to marry her so,you can't change that fact gwanda kidauri damara shirya zamada da'ita indai dagaske kikeyi kinyi nadaman abubuwan dakikayi sannan kije kisameta kibata hakuri don ba dagangan takirani ba a irin wannan lokacin,nan yayima Zaliha bayanin abunda yafaru kafin yakara da,inkinje kinbata hakuri only then zaki samu fuska daga gareni sabida nida kika gannin nan banason damuwa I want a peaceful and happy family inkuma ke baki shirya yin hakan ba kina iyamin magana babu takura ni me iya sallamarki ne",yakarashe maganar tareda komawa yakwanta sannan yace "kifita min ah daki I want sleep now"....
Zaliha jitake kaman ta kwallah ihu haka tatashi tafice zuwa dakinta zuciyarta nayimata wani irin kuna,wai har Sulaiman ne zaice mata zaiyi mata kishiya don ubanshi kishiyarma kuma Sumayya lallai akwai aiki agabanta haka takasa bacci ranar itakadai tana sakawa tana warwarewa hakanan zuciyarta nabata harsaitayi abunda yacedin sannan Itama zatasamu hanyar cika burinta.......
****
Around 10:30pm Asma'u se zubama Hajja hira takeyi dukdai dan karta korata dakin Almustapha hakanan aranta tanata addu'ar Allah yasa bacci yakwashi Hajjan don itama tasamu takwanta ah dakin sede da mamakinta har shadaya da rabi Hajja ko gyangyadawa bata farayiba sema cemata datayi "waike baki tafiya dakin mijinki ne?".......
Turo baki tayi kaman zatayi kuka kafin tace"Hajja hirafa mukeyi kuma ba bacci nikejiba".......

Rike baki Hajja tayi cikeda mamaki tana"ammana lallai yarinyar nan,harsai kinajin bacci tukunnan zakije dakin mijin naki wallahi Asma'u kiyima kanki fada don inkikayi wasa kinaji kina gani wata zata zo ta kwace miki miji dan ras ras dashi",Hajja takarashe maganar tareda tashi tsaye tana "baridae kigani"Asma'un kam kasa cewa komai tayi sewani kumbura bakida take tayi itakadai aranta tana itakam datasan haka Hajja take dabazata taba maraba da zuwanta ba wallahi sede kan ta ankara har Hajja tajanyo igiyar charger tana"jirana kikeyi ko,to ganinan nazo", takarashe maganar tareda yin kan Asma'un tana"yarinyar da kyaunki da komai zaki jamana kishiya don rashin hankali na damunki,to miyema auren don gidan ku?".........
Asma'u tunda taga Hajja tabiyota tafice aguje batareda tadauki wayarta bama bare hijabi tana Hajja kibarni indauki hijabi na da wayana please,wani harara Hajja ta daka mata tareda tura kofar tarufeshi gam tana"inbaki zuwa dakin nashi seki kwana anan tsaye".............
Babu yanda Asma'u ta'iya haka tawuce dakin Almustapha don yaukam ko tsayuwa ah parlourn ma batayiba,yanajinta tatura kofar dakin amma yayi kamar bejiba sema sake jan blanket dayayi yarufe kanshi dashi donshikam harya kwanta tundazu dukdama yakasa bacci,he was just feeling as if something is missing hakanan minti minti yakeji tana fado mishi arai dukda yakasa yarda cewa itace dalilin hanashi baccin yau,koda tashigo wutan dakin ah kashe yake se bedside lamp dake kunne ganin hakan ne yasa tayi tunanin yayi bacci...
Karema gadon nashi kallo tayi tareda maida kanta ga sofa din dake gabanta dan gajeren tsaki tayi tareda komawa ta kunna wutan dakin sannan tawuce gurin wardrobe dinshi bude wanda take tsanmanin samun bargo aciki tayi sannan tadauka takoma takashe wutan sannan tadawo takwanta kan sofa din tareda lullube jikinta bakidaya sede har wajen mintuna talatin bacci yakasa daukanta bata ankara ba kawai taji an yaye bargon wani irin bude idanunta tayi cikin sauri amma kanma tace wani abu harya kwanto jikinta tareda maida musu bargon ya lullube su kaman zatayi kuka tace"Yaya Imam!".............
Batareda ya kulata ba yasa hannunshi ah waist dinta ya rungume yana sake gyara kwanciyar shi,shikanshi yarasa dalilin dayasa yakasa bacci yaudin shikadai hakanan zuciyarshi tabashi dayaje gareta may be he'll be able to sleep peacefully,jin yayi shiru ne yasata kara cewa"Yaya imam dai?"......
In a very cool voice yace"Uhmmm"......
Turo baki tayi ah wuyanshi wanda kesashi jin wani yaaar kafin tace"ammadai kasan gurin nan bazai ishemu bako?".........
Yar murmushi yayi yana"dakin wayene?"......
Kaman wata karamar yarinya tace"naka"....
Dago da fuskarta yayi yana kallo kafin yace"Better,so kinga I've the right to sleep wherever I want to ko?"...
Kaman zata fashe da kuka tace"gori zakayimin to?".......
Dan zare hulan dake kanta yayi still yana kallon kyakyawar fuskarta tareda shafa gashin kanta kafin yace"nidai bance ba".....
To ka barni inkoma gadon ni don nan yayi mana kadan, kawai jitayi yamaida kanta kirjinshi tareda kai bakinshi kunnenta yana"shhhhhhh,and I've the right to decide on where my visitor will sleep tunda dakina ne remember!,so, go to sleep now".........
Batasan sanda tayi shiruba jin yanda yayi maganar yayinda ahankali yakuma dago da fuskarta tareda kissing forehead dinta calmly sannan yace"Good night Wife"........
Itadai batace mishi komai ba harta fara jin saukar numfashin shi ajikinta da alama bacci yadauke shi dagowa tayi tana kallon fuskar shi so cute,gashi yana baccinshi peacefully cikeda rashin damuwa batasan sanda murmushi ya subuce mataba hakanan ta tsinci kanta da pecking forehead dinshi Itama sannan tamaida kanta jikinshi tana mamakin shi din wani irin mutum ne,ba ajimaba Itama baccin yayi awun gaba da'ita..........

*****
Washegari jikin Mai Martaba yayi sauki sosai don yaukam har parlour yafito yayi breakfast dinshi tareda Dad seda suka gama sannan yadubi tilon Dan uwan nashi yana"I'm feeling okay now".....
Murmushin Dad yayi sannan yace" And I should take you to your Darling Khairiya".......
Dariya Mai Martaba yayi kawai sannan yagyada mishi kai tareda cewa"Ya akayi kasan abunda yake raina"......
"Lol, I'm your One and only Brother remember?",cewar Dad din murmushi Abba yayi dukdama shikam bawai yatuna komai bane na rayuwar soyayyar dasukayi ammadai he's quite sure komai da akafada din gaskiyane tunda gashi harda shaidu and she has suffered alot because of him sabida haka yakeson yadawo mata da happiness dinta by asking for her forgiveness itada Ya'yanshi and yanason ya roketa kan ta aureshi so that they can start afresh sumanta baya su fuskanci future hakanan sucigaba da addu'ar Allah yabashi ikon tuno memories din baya don he really want to remember each and everything that happened back then atleast it'll help him to build a better future dukdama yana ganin shikam yanda suka tsufan nan wani rayuwa ne zasuyi na jimawa?...
Sede koma miye ne hakanan koma shekaru nawane suka ragemai he want to spend his remaining time with his loved one's ba,ba masu yaudararsa ba dason ganin downfall dinsa...........

Dad dakanshi yataimaka mishi yatashi kafin suka fita daga bangaren nashi hakanan dogaraye nabinsu ah baya har suka isa bangaren su Almustapha inda dogarayen suka tsaye daga waje yayinda su Dad din suka karasa ciki da sallama.........
Parlourn babu kowa hakanan ko'ina agyare yake fes fes yayinda babu abunda ke tashi agurin se kamshin turaren wuta medan karen dadi wanda ke tafiya da zuciyar me shaka wanda wannan din duk aikin Asma'u ne sabida shirin tarban abokin mijinta Dr Na'im da Almustapha yafada mata yauda safe kan cewa yace zaizo lunch gurin amarya ayanzu hakama tana kitchen tana karema kayan abincin kallo, gabadaya tarasa mezata dafa masa wannan dalilin yasa tashiga kiran Almustapha din,aikuwa seda wayar takusa tsinkewa sannan yadaga sallama tayimai kafin ya ansa....
Ashagwabe tace"Yaya Imam narasa mai zan dafama abokin ka".......
Dan sosa kanshi yayi tareda kallon Na'im dake gefenshi sannan yace"komiye ma kiyi, it'll be okay.....
Sake turo baki tayi kaman tana gabanshi"ayya am to katambayeshi mana miye favourite dinshi",cikeda takaici yace "I can't",sabida shi haushima tabashi bata taba tambayarshi mezaici ba komai taga dama girkamai takeyi amma dayake abokinshi zaizo harwani special abu takeson dafamai,lallai ma yarinyar nan"........
Itama rai bace ta katse wayar tana mita"ba laifinkabane ba laifina ne dana kira miskili irinka"......
Hindatu dake gefe dariya tayi sede kafinma tayi wani magana sukaji Rukayya tashigo aguje tana haki kallonta sukayi dukansu biyu yayinda tace"Mai Martaba yazo,cikeda kidima Hindatu tace kina nufin bangaren nan?"........
Gyada mata kai tayi, Hindatu da damuwa tace shine ba afadama bare agyara guri sabida tarbansa fisabilillahi itadai Asma'u dariya ma suka bata yanda duk sukabi sukawani rude kafin taraba tagefensu tafice tana ku kawo musu kayan motsa baki.........
To kawai sukace yayinda takarasa parlourn fuskarta daukeda murmushi ta tsuguna tareda gaidasu Abba din.....
Shine yafara cewa"Daughter yakike?".....
Lafiya Lau Abba ya karfin jiki?...
"Alhamdulillah"???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yabata amsa yayinda Dad yace Almustapha yafita ko?....
Kanta nakasa tace eh Dad anma Ummi naciki, murmushi Dad yayi sannan yace kicemata tanada baki cikeda jin dadi Asma'u tatashi tawuce dakin Ummi inda tabar Abba kirjinshi nata dukan uku uku haka su Hindatu suka kawo kayan motsa baki suka koma kitchen...........

Asma'u kuwa koda tashiga dakin Ummin samu tayi tana shafa mai da alama ma daga wanka tafito,harta juya don fita tabata guri taji Ummin nacewa"yazaki koma kuma?"....
Cikeda kunya tace"Ummi inkingama shiri zandawo".....

Dariya Ummi tayi sannan tace zo zauna abunki nagama ai kaya kawai znsaka,hakanan babu yanda Asma'u ta'iya dole takoma tazauna sede wasa tashigayi da hannunta har Ummin tagama sa kayanta kafin tace"I'm done,hope I'm safe Habibty?".....
Dariya Asma'u tayi sannan tace"laa Ummi bakine fa kikayi ah parlour","Baki kuma,daga Ina", Ummi tayi tambayar cikeda curiosity.....
Ahankali Asma'u tace...
"Su Abba ne da Dad"...........
Take Ummi taji gabanta yashiga bugawa dakyar ta'iya cewa"kice musu bananan don Allah Habibty",jiki asanyaye Asma'u takarasa ga Ummin tareda riko hannunta sannan tace"Ummin mu".......
Dagowa Ummin tayi tana kallon surukartata nervously,kallo daya zakayimata kagane cewa bakaramin tashi hankalinta yayiba lokaci guda in a very calm voice Asma'u tace...
"what will you gain by running away from him Ummi?"........
Shiru Ummi tayi yayinda idanunta suka ciko da kwallah lokaci guda,magana Asma'u tacigaba dayi"it'll only bring you pain Ummi,you need to be happy as well,it's high time you forget about your past and move on besides miye laifin Abba,shima cutanshi akayi he was never at fault"......
Ummi batasan sandama tafara kukaba secewa datake"I know Habibty,he was never at fault I'm just too nervous it's been long bamu haduba banshirya ganinshi yanzuba kigane Dear,banshiryaba"Ummi tayi maganar tana kuka murmushi Asma'u tayi tareda kwantar da Ummin ajikinta tana"to Ummi tunda baki shiryaba no one will force you kikwantar da hankalinki I'll go tell them that you're sleeping"........
Gyadakai kawai Ummin tayi dakyar Asma'u ta lallashi Ummin hartayi shiru kafin tatashi tafita jiki ah sanyaye Allah yagani batason yimasu Mai Martaba karya sede yazatayi?......
Karasawa tayi garesu kafin tace"tana bacci"....

Dad ne yayi murmushi irin nasu na manya kafin yace"tadai ki fitowa ko Daughter ?".......
Asma'u dai kunya kamar zatayi yaya yayinda Dad yadubi kanin nashi sannan yace"let's go we'll come back later semuji shidinma wani excuse za ayimana,mudai munsan bazamu gajiba"..........
Abba dake gefe yace"I'm not going anywhere zanjira harta tashi"......
Dad baiyi mamakiba hakanan yasan Mai Martaba da kafiya don haka seya sallami Asma'u sannan yashiga kiran layin Almustapha yace masa yazo gida yanzunnan haka yafadama Mom, Hajiya Muniba,Sumayya Sulaiman da Hamida da tuni Sulaiman yafada masa tazo gida and he told him everything about her,yafison ayita takare yau din tunda Mai Martaba dinma is being stubborn.........

Wuraren karfe daya kowa yagama hallaruwa except Afiya da Amira dake school wanda suma anje daukosu yanzu don haka Dad yace su mazan suje suyi sallah kafin isowan su Afiyan aikuwa hakan akayi zuwa karfe biyu kowa is ready hakanan Almustapha dakanshi yashiga ya yi convincing Ummi tafito dukda shima he's against it sede yazaiyi.........
Yana rike da hannunta suka shigo parlourn hakanan tunda suka fito daga dakinta Mai Martaba yazuba mata narkakkun idanunshi yayinda zuciyarshi ke raya mishi anya wannan mahaifiyar Almustapha ce?.....
She still looks very young da in ancemaka ita tahaifeshi zaka iyacewa bahaka baneba sede irin masifar kaman dasukeyi ne kadai zai iyasawa kayarda don wanda yacika musuma cewa zaiyi yayarsa ce,yasan Khairiya dajimawa he knows her face sede rayuwar dasukayi na dadi ne yakasa tunawa baki daya,karasowa sukayi cikin parlourn tareda zama yayinda Dad yayi gyaran murya tareda bude taron da addu'a kafin yace ma Mai Martaba yayi magana.........
Mai Martaba dake feeling nervous yadubi side din da Ummi take yace"Khairiya!"......
Yanda yakira sunanta batasan sanda hawaye suka fara zuba ba she's been waiting for this very day,ranar da Abdulrahman dinta zai budi baki yakira sunanta dawannan kakkausar muryar tashi medan karen amo da dadi,tsabar yanda takeji kasa amsa kiranma tayi sema dago idanunta datayi tasaka cikin nashi"........
Ahankali yacigaba da magana shima yana kallonnata"I don't know what you and my children went through hakanan I wasn't there with you to support you but believe me after knowing all that happens I can feel the pain Khairiya dukda nasan bazaikai nakuba hakanan nasan no matter how I try bazan taba iya gushe abubuwan daya faru daku ah baya ba but I'm still asking for your forgiveness, I'm sorry for not being a trustworthy husband and I'm sorry for leaving yourside during those harsh moments", Mai Martaba yayi maganar tareda folding hannunshi hakanan idanunshi sun canza launi lokaci guda Ummi dake gefe cikeda tausayinshi tace"it was never your fault Abdulrahman tunda jimawa nasan da haka and believe me right from that day nariga na yafemaka, Allah yayafe mana baki daya", besan sanda hawaye yayi slipping ah idanunshi ba hakanan yana mamakin"how can someone be as kind as she's,after all that happened tayafe mishi so easily,adaidai wannan lokacin yagane cewa yayi loosing mace abaya hakanan yayi loosing uwar Ya'ya tagari",dakyar ya'iya cewa thank you kafin yadubi su Almustapha din tareda sake folding hannunshi yana shirin neman yafiyansu akaro nabiyu amma dasauri Afiya da Amira suka karaso gareshi tareda shigewa jikinshi suna kukan farin ciki, Amira ne ta'iya cewa"Don Allah Abba karkace komai, we've forgiven you for a long time now and munsan ba laifin ka bane ba"......
Yayinda Afiya tace"let bygones be bygone Abba".......
Lumshe idanunshi yayi tareda shafa kansu hakanan yanajin kaunar yaran nasake ratsa cikin jikinshi babu abunda yake furtawa se alhamdulillah because he never thought it'll be this easy barinma ta bangaren Ummi......
Hamida dake gefe tana ganinsu idanunta Itama suka ciko da kwallah kafin tayi breaking silence din dake parlourn tahanyar tashi takarasa kusa da Abban sannan takira sunayen Afiya da Amira ahankali....
Dagowa sukayi suna kallonta atare yayinda tayi fuskar tausayi in a very calm voice tace"I'm a very horrible Sister,i cheated you girls,nayi making life dinku miserable back then but believe me I regret all that I've done, I'm really sorry", takarashe maganar tana kuka mai tsuma zuciya Afiya ne tashiga goge mata kwalla tareda sakin murmushi...
"what's the need to say all this Sis?"......
Yayinda Amira taje saitin kunnenta tana"kinbude little secret dinmu yanzu seda kikasa Abba yaji"...........
Hamida batasan sanda ta rungumi yan kannen nata ba tsabar kauna da nadaman abubuwan da tayi masu abaya, Abba dake gefene yace kuskus din me kukeyi?.....
Dad ne yace"kyalesu sunfi kusa inkace zaka shiga kuma kaine dajin kunya gwandama mukoma inda mukafi kauri",Dad yakarashe maganar tareda tashi tsaye dasauri Mai Martaba yace"To angama maganarne tukun?".......
Wara idanu Dad yayi tareda sake komawa yazauna yana"to ai bansaniba nadauka iyakacin maganar daza ayi kenan ah taron"........
Dariya su Sulaiman sukayi yayinda su Hamida ma duk sun juyo yanzu suna kallon Abba da Dad din.........
Wannan karan Hajiya Muniba ne tace"ah to nimadai inabayan Mai Martaba nasan dai maganar nan dasaura".......
"Lol,to ai shikenan anbarmuku kukarasa",cewar Dad din murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tadubi bangaren da Almustapha da Ummi kezaune ahankali tatashi sabida dizziness datake yawan ji kwanan nan kafin takarasa inda suke tareda zama gaban Ummin itadai Ummi kanta nakasa takasa cewa komai tundazu ahankali Hajiya Muniba takamo hannunta wanda hakan yasa Ummin dagowa tana kallonta itama murmushi Hajiya Muniba tayi kafin tace"zan ari bakin Mai Martaba inci mishi albasa dukda baifadaba nasan abunda yake ranshi kenan,don Allah Aunty Khairiya kiyi hakuri kikoma dakin ki,kiyi hakuri kimanta baya kucigaba da rayuwarku da Mai Martaba kaman da it might sound weird to hear this from me but believe me I'm saying it from the bottom of my heart,inasonki amatsayin abokiyar zama sannan Mai Martaba was a friend and a Brother kafin yazama mijina and from all labarin danaji nasan farin cikinshi lies in you Aunty.so,I want you to bring back that happiness please"...........
Dad dake gefe yayi murmushin jin dadin abunda Hajiya Muniba din tayi kafin yakarada....
"indai anyafe mana ayi hakuri akarbi kokon bararmu to"........
Ummi kam kasacewa komai tayi se hawayen farin ciki wai itane yau akecemata takoma dakin mijinta,mijintan ma Mai Martaba.......
Mai Martaba daya gaji dajiran jin ansa daga gareta yace"Khairiya kindaina so na ne?",yanda yayi maganar seya baka tausayi wani irin harara ta wurga mishi tana murmushi"ni haka nace maka"....
Dariya yan parlourn suka kece da yayinda Sulaiman yayi dungure yana"Ya Allah wanga soyayyar tsofi ta burgeni, Allah kasa Sumyna tasoni irin haka koda furfurata".........
Aikuwa gabadaya suka maida kallonsu kanshi suna dariya seda yagama dawowa daidai sannan yagane baran baramar dayayi cikeda jin kunya yashiga sosa kai Sumayya kuwa jitake kaman ta nutse kasa tsabar kunya......
Dad ne yadubi Sulaiman din cikeda tsokana donshi tuni yariga daya ganosu tunba yau ba sannan yace"naji kaman kace wani abu Son?"......
Kame kame yafarayi"uhm Abba, Dad daman wai,daman".....
Dariya sukayi duka Dad din na "oh kanason 'Yartawa bazaka iya fitowa kafada ba da nayi niyan baka amma tunda you're not sure of your feelings se inbama wani kawai"......
Ai Sulaiman baisan sanda ya'isa gaban Dad dinba yana"Wallahi Dad inasonta,I love her so much kawai banason fadane batareda nanemi izinintaba"......
Murmushin jin dadi Dad yayi sannan yace"to alhamdulillahi batunyauba nikeson hada irin wannan zumuncin sede nibamaison in takurama yara baneba shiyasa nazuba muku idanu, Allah yasanya alkhairi indai tani ne nabaka Sumayya halak malak Sulaiman because I know you'll be the best husband ever".......
Murmushi Sulaiman yayi yana"nagode Dad".....
Abba dake gefene yace"kujimin danyen hukunci ita tace tana sone?"......
Lallai Abdulrahman bakasan yaran nanba,tunyaushe suke kus kus batareda munsaniba I'm very sure sun fahimci juna besides koba ta so zamatafara so",cewar Dad din....
Aa bazaayi haka ba inji Abba kafin yajuya ga Sumayyan yana"Zonan Daughter".....
Sunne kanta tayi cikin cinyarta don hakanan setaji yau tanajin kunyar Abban sosai,dariya Dad yayi mashi sannan yace"kagani ko"....
Still Abban bai daddaraba yace....
"kinason Sulaiman Sumayya,fadamin inkinason shi inko bakyaso babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login