Showing 69001 words to 72000 words out of 235422 words

Chapter 24 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3502

this way when she calms down zatadawo daidai"......
Cikeda mamaki Dad yace,is this how she behaves when she's angry,gyadama Dad kai Abba yayi for the second time kafin yakara da but bayakaiwa nayau sede ina mamakin don banfada mataba bai kamata tayi reacting this way ba and it's all her fault bata bani daman fada mataba inama naganta Abba yayi maganar rai bace sannan ahankali yadago ya kalli Dad din"amma kamata yayi ta tayani farin ciki ko tunda tasan how important you're to me bawai tayi behaving this way ba,so what if banfada mataba ai yanzu tasani",yayi maganar murya karye cikeda tausayinshi Dad yace"kahuta yanzu we'll talk about this about it after the wedding",gyada kai Mai Martaba yayi kafin yakwanta kan gadonshi nan Dad yamishi saida safe yafita yana kissima halayen Magajiya yakamata asirinta ya tonu,yakamata kaninshi yagane cewa wacece real Magajiya sede bazasu iyayin hakan ba harsai sun hada kai sun tona mata asiri yanda kowa zaisan asalinta,bama yan masarautar ba yan gari baki daya sabida tayi succeeding in her act kuma tasama ran mutane cewa Almustapha is not the real child but illigitimate sannan tasamusu wrong impression akanshi he knows that it's going to be a tough ride gashi dama ahalinshi baki daya sede no matter what,they have to expose her with Allah's help,tunowa yayi dawani abu kafin ahankali yawuce bangarensu .......

Tunda Magajiya tafito ah bangaren Mai Martaba bata wuce koina ba se bangaren su Humaira da Halima don tasan nanne kadai babu wasu baki donsu kadai ne se yaransu,tunda tashiga dakin Halima tayi saurin riko hannunta tazaunar bakin gado,Mama kiyi ahankali kada kijima kanki ciwo........
Ture hann???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?un Halima tayi sannan tace amma Allah yahadani da gabayen Ya'ya bansaniba,yanzu harkuma ayi irin wannan aika aika ni bansaniba?........
Cikeda damuwa Gimbiya Humaira tace"kiyi hakuri Mama wallahi bamusaniba Kuma ni aganina duk wannan tada hankalin dakikeyi bashine mafitaba,mafita shine mutaru munemi solution inkina behaving haka se asirin dakika jima kina boyewa ya tonu don mutane zasufara suspecting wani abu barema gida da jama'a, tabbas nasan labarin yazo miki ah bazata kamar yanda yazo mana sedefa ba hakan yana nufin gwiwar mu tasace bane don muddin su Almustapha suka samu gurbi aziciyar Mai Martaba shikenan mu zamu zama yan kallo.........
Cikeda gamsuwa Magajiya ta kalli yartata tanajin bayanin datakeyi dukda kuwa ranta na tafarfasa seda takai aya sannan tace yakikeso muyi inban nuna bacin rainaba Humaira......
Murmushi Humaira tayi sannan tace nima bansan yaxa ayiba yanzu amma inason kikwantar da hankalinki agama bikin nan lafiya jama'a su watse kafin mukoma namu gidajen semusan mezamuyi,don Allah Mama kidaure kada kice zakiyi wani abu..
Dan shiru Magajiya tayi sannan tace"toshikenan,zanyi iya kokarina"....
Yauwa cewar Humaira din kafin tace Abba ma kije kibashi hakuri inya sauko kudawo normal don inkun samu matsala kaman aikin mu yarugujene don zaifi kusanci dasu wayancan din........
To kawai Magajiya tace bawai don ranta yanasoba.......
Haka suka cigaba da tattaunawa............

****

Washegari asabar karfe shadaya na safe aka daura auren Humaira da mijinta Sadiq wanda shima dan wata Masarauta ne,anhalarci taron daurin auren sosai don kuwa cikin masarautar babu masaka tsinke ancika makil yayinda motaci kuwa sunjeru daga waje duk na manya manyan mutane kama daga kan masu gwamnati,yan siyasa,manya manyan yan kasuwa sannan kuma sarakuna daga different masarauta sun halarci taron daurin auren...................
Yayinda acan garin Maiduguri ma andaura auren Zaliha da Sulaiman wanda suma anyi taro sosai..........
Tunda aka gama daurin auren aka tafi inda aka tanadar donyin reception wanda shima duk acikin Masarautar ne,yayinda kide kide na ganga dakuma algeta shike tashi cikin masarautar hakanan masu kirarima nayi da maroka,karkuso kuga Sulaiman yanda yahade cikin kayan sarauta bakaramin kyau yayiba don kayan daya sama na daban ne bakaramin aiki akayi akantaba sewani sheki yakeyi daka ganshi kaga ango
Dukda kirarin da morokan keyi mishi baidamuba sabida shi gabadaya hankalinshi ma ba akansu yakeba he's busy looking for his one and only Brother dazu suna tare besan ya akayi ya bace mishiba,juye juye yashigayi yana neman shi can yahango shi tsaye jikin wata mota yayi folding hannunshi ah kirji tareda dan lumshe idanunshi kadan, murmushi Sulaiman yayi sannan cikin sauri yakarasa gabanshi"Allah Yaya Matarka ta haduda aiki,innayinan seka zille kayican se gudu kakeyi kana barina nikadai and i always want you by my side"Sulaiman yakarashe maganar yana pouting bakinshi murmushi Almustapha yayi wanda yafidda white teeth dinshi tareda sa dimple dinshi lotsawa kadan"Congratulations Ango"......
Playfully Sulaiman yace "so Yaya Almustapha can tease someone, tundazu inka zille nasamoka maganarka daya"congratulations ango", Sulaiman yayi maganar yana immitating yanda Almustapha din kefadi.....
Sannan yasa hannunshi ah aljihun wandonshi yana"don't worry soon zamu nema maka mata, this's what I'll be doing on your wedding day as well"......
Jijjiga kai kawai Almustapha din yayi batareda yace komaiba yayinda Sulaiman din yakarema Almustapha din kallo from head to toe"oh my god Yaya tundazu nidanake namiji ma nakasa daina admiring kyaun da kayi barekuma ace kashiga school yanzu"I promise wasu matan sesun saki baki yawu yana zuba"........
Hmmm kawai Almustapha yace sannan yatafi yabarshi agurin binshi Sulaiman din yayi cikin sauri"I'm sorry don Allah kada kasake guduwa yanxu muje gida gurinsu Mom da Ummi".......
Kaje gurin Mama ne Almustapha yayima Sulaiman tambayar batareda ya kalli inda yakeba......
Jijjiga kai Sulaiman yayi jiki ah sanyaye sannan yace"i won't".....
shiru Almustapha yayi don har Sulaiman yafidda ran zaiyi magana yace"why?".....
Tsayawa Sulaiman yayi sannan yace"kasanta she'll start lecturing me barema nasan she's angry with me ga abunda yafaru"......
Kallonshi Almustapha yayi cikeda tausayinshi sabida ganin how different he's from his Mother kokadan bedauko halintaba,yau in akacemishi Magajiya ba mahaifiyar Sulaiman bane bazai musa ba because they're two different people with two different perspectives......
Ahankali yadanyi tapping shoulder din Sulaiman din sannan yace"you've to go and see her,you need her blessings",yana karasa fadi yayi gaba yabar Sulaiman tsaye gurin cikin sauri Sulaiman din yakamo shi yana"okay zanjeni amma first muje gunsu Ummi,shidai Almustapha bece masa komaiba har suka Isa sashin nasu wanda yanzu take kewaye da dogaraye yayinda bayi kuma aciki sunata harkokinsu don daga Sumayya zuwa Afiya kowa ankawo mata baiwa biyu wanda zata kula da needs dinta haka Ummi ma Sulaiman yasa ankawo Uku masu kula da lafiyarta haka Mom sunkai hudu wanda zasuna kula da harkokin cikin gidan........
Tundaga bakin parlourn yake kwala ma Sumayya kira,tanajinshi taki ansawa dan murmushi yayi sannan yabar Almustapha ah parlour yawuce dakinta tana kwance kan bed tana chatting abunta,tunda yashigo kamshi turarenshi tadingaji medan karen dadi tareda kwantar mata da hankali.......
Gaban gadon yakarasa ta inda take kallo,inata kiranshi shine kika ki ansani Sumayya?......
Dagowa tayi takalleshi sannan tamaida kanta kan wayar banji baneba......
Wabce wayar yayi yawurgar kan gadon sannan yakamota tatashi tsaye"meye damuwanki Baby girl yayi maganar yana kanne mata Ido daya,kokarin kwace kanta takeyi amma takasa,sassauta rikon dayayi mata yayi sannan yace ahankali"why are you behaving so strange this days,yes nasan we always tease each other still muna hira ai ko but now abu kadan sekiyi fushi dani I don't know why"......
Feel free Sumayya,nayimiki wani abune yayi maganar yana kallon kwayar idonta,dan rufe idanunta tayi don Itama batasan daliliba ahankali tace babu komai....
cikin sigar lallashi yace kalleni to,bude idanunta tayi tadaurasu akanshi don ta damu yatafi yabarta sabida kamshin turaren shi firgitata yakeyi and his presence as well....
"Are you sure?".....
Gyada masa kai tayi, murmushi yayi sannan yace "to daga yau adaina min rashin kunya inbahakaba zan ballah bakin",dariya kawai tayi yayinda yasaketa sannan shi ya kwanta kan gadon nata tana tsaye"washhh nagaji wallahi,yau tun safe banzauna ba infact tun jiyama"......
Cikeda damuwa tace"sorry"..
"Thanks",zokimin massage yayi maganar cikeda zolaya,hararanshi tayi tana"Anty Zaliha tayi maka badainiba"......
Yatsina fuska yayi sannan yace wannan ashe zan mutu in ita zatamin massage Sumayya"Yar *Gidan sarauta* cefa gaba da baya,kinga kuwa tako ina tadebo"......
To ai nima Yar sarautarce cewar Sumayya tana yatsina fuska,dariya yayi yana kinga expression din fuskarki kuwa kaman wanda na yabi kishiyarki,shaaa nasan ke yar sarauta ce amma ai baki tashi cikinsu ba dukda ma cikin gata kika tashi sede zakiyi abunda ita bazatayiba".......
Nidai katashimin agado bacci nikeji,zare idanu yayi tareda tashi yazauna tsakiyar gadon seyanzu ma talura da takalmi yadale mata gado.......
"Bacci fa kikace Sis,aibaki isaba yau auren yayankine tukunnan ma inasauran suke yakarashe maganar yana tashi daga kan gadon sannan yakama hannunta yana muje waje inmuku assembly ma........
Ah parlour yasaki hannunta yana kiransu Afiya da Amira ba ajima ba segasu sunfito daga kitchen tareda Mom,sakan baki Sulaiman yayi ganin kayan dake jikinsu"lallai yaran nan aurena guda kitchen ma kuka shige abunku ko,kallon Mom yayi sannan yace Mom kigansu kayan bacci ne fa ajikinsu".......
Dariya Mom tayi sannan tace koyan girkin Indonesia sukeyi,wai sena koya musu tunda zun nikebinsu suje suyi wanka sunki......

Amira ne takaraso parlourn tana"Yaya Sulaiman Allah bamuda kayane,kasa karashe maganar tayi ganin Almustapha datayi zaune sanye cikin sabuwar shadda fara kal wanda bakaramin kyau yayi mashiba gashi gashinnan yasha gyara ga wata hadaddiyar hula dayasaka,tsalle tayi tana Afiya zokiga Yaya Almustapha don Allah,dagudu Sumayya da Afiya suka karaso suna gamu,woow shine abunda Sumayya tace"Allah Yaya me shiru shiru dukda bakason min magana yaukam semunyi hoto",dariya sukayi dukansu harda Mom dake tsaye ah can baya........
Zama Sumayya tayi gefenshi sannan tace Yaya Sulaiman daukemu,babu musu ya daukesu,another one please tayi maganar tana canza style kafin tadubi Almustapha din Yaya don Allah kayi smiling.......
Murmushi yayi don yarinyar dariya take bashi, she's so open minded seda akamusu yakai biyar yaga batada niyar tsayawa yaja karan hancinta ahankali fuskarshi daukeda annuri"it's okay naughty girl",sannan yatashi yabarta gurin zaune binshi tayi da kallo tana"Ya Allah, Afiya yayankun nan baya kasheniba, he's so lovely ah swear".......
Hararanta Sulaiman yayi"zoki tura hotunan ko in goge yanzunnan", dagudu tayi gurinshi tana bashi hakuri riko ta yayi sannan yace"I need a selfie too",sannan yayi whispering ah kunnenta"with you"......
Daukarsu yayi sannan su Afiya ma akayi dasu hotuna sunyi kyau yanata mita waishi yazaiyi yadaura hotunan shi da kannenshi with sleeping dress Kuma ranar aurenshi for that matter..........
Alkawari yayi musu kan zai bada dinkinsu ma wani tailor din friend dinshi inyasamu fita and yasan zaiyi musu express kona gobe susamu kafin agama sauran don already yasiyo kayan dajimawa ya ajiye don specifically na aurensa yasaya musu sebezo yasamu yabada dinki ba kuma ma babu na Sumayya ciki so zai squeezing ayi musu duka susamu nasawa ah events din daza ayi agaba............
Seda yakarasa gun Mom suka gaisa sosai tanata tsokanan shi ango ango sannan yakarasa dakin Ummi don duba jikinta,samun Asma'u yayi kwance jikin gadon Ummin tayi shiru alamun tunani takeyi, murmushi yayi sannan yace Asma'u kekam tunda kikazo kina kunshe ah daki abunki,yar dariya tayi tareda tashi daga kwancen datake tana Ina wuni Yaya Sulaiman......
Amsawa yayi sannan yace"memakon kije parlour ko dakinsu Amira kuyi hira abunku",nafi jin dadin hakan nedai.........
Toshikenan kinga banji Daddy yana maganar zamuje gidan kunba yau ma kodai se gobe ne.....
Cikeda damuwa tace he's busy ko?....
Gyada mata kai yayi ahankali sannan yace,kozaki kira kifada ma Ummi kilan tayi understanding.....
Jijjiga Kai tayi cikin sauri alamun a'a don batasan ta inama zata farama Ummi bayaniba don haka tace kozaka maidani gidansu Aisha din kawai inyaso inkum tashi sekubi tacan kudaukeni........
Dan shiru yayi nawasu dakiku sannan yace"to amma kibari se anjima don yanzu inada gurin zuwa koma inshi Dad din baya komai inna tambayeshi basai mujeba kawai".......
Godiya tayi mashi sannan yaduba jikin Ummi yafita ah dakin don zuwa gurin Magajiya........
Ah daki yasameta ya gaggaisa da baki se Allah sanya alkhairi akeyi mishi yayinda wasu ke guda,harkasa ya tsuguna ya gaida Magajiya dukda kuwa yanda takejin haushin shi haka ta daure zuciyarta bata nunaba suka gaisa lafiya lau........
Yasha mamaki sosai dabata bata rai koyimai fada ba sekuma dayayi la'akari da gurin akwai dumbin jama'a sannan no matter what yasan yau is a special day for her.......

Tunda Sulaiman yafita yakoma gun abokanshi dakuma wasu hidindimu yama manta da batun maida Asma'u don gabadaya ya shafa'a......

Aranar ana gama daurin aure mutanen Borno suka dauko Amarya suka taho da'ita aikuwa sunyi isowar dare sosai don kusan dayan dare suka iso cikin masarautar dukda kuwa irin daren daya tsala hakan behana anyimisu tarba mai kyau ba don already angyara bangaren Sulaiman din dayake makeke ne don yanzu zezama nasu shida ita,sosai suka yaba da karamci irinna masarautar Mai Martaba Abdulrahman.....
Hakanan washegari akafara events da aka shirya komai yatafi cikin tsari hakan su Amira ma baa barsu abayaba sunyi sunyi suja Asma'u amma taki zuwa don ko ajiyan dayanma seda tafita da Ummi wanda ayanzu tafi jin dadin zama da'ita fiyeda kowama dukda kuwa bawai magana sukeba........
Itama she's lonely,gani take bataga ta murna da farin cikiba tafison zama guri shiruma gashi damuwarta yanzu shine har yau Sulaiman bedubeta ba hakanan Dad don sanda suke shigowa ma tayi bacci damuwarta daya kada hankalinsu Ummi yatashi.....

Ranar litinin angama biki yayinda baki sunfara watsewa sannan duk wasu programs daza ayi angama shi don Gimbiya Hamida ma antafi da ita gidan mijinta.........

****
Fitowanshi daga wanka kenan zama yayi gaban madubi yana kallon bruises na jikinshi dahar yanzu basu gama warkewa sosaiba,sede sundanyi healing ba laifi shafa mai yashigayi ahankali yayinda yake sake karema kwalin wayar dake gabanshi wanda Dad ne yabashi ita yau dasafe yakuma bama su Afiya ma nasu sede model din ba dayaba sedaya bashin ma yatunada Sulaiman ma yataba bashi wani phone,tabe baki yayi ahankali sannan yadauka yasa ah drawern dake gabanshi donshi bega meye zaiyi dawayaba ma tukunnan,he has no one to call insune ai kullum yana taredasu,cigaba da shirinshi yayi don yau zeshiga school tunda yakwana biyu beshigaba and yanada exams gobe,paper daya daya rikeshi for some years now, addu'a yadingayi aranshi yana fatan Allah yasa yasamu ya rubuta ta bana.........

****

Tun ranar asabar Anty suwaiba kafin tawuce office ma taje gidansu Asma'u din bayan sun gaisa da Ummin take tambayarta ko Asma'u tazo gida...........
Cikeda mamaki Ummi tace tazo gida kuma,basuna tareda Aisha gurinkiba?......
Cikeda damuwa Anty Suwaiba tashiga bata labarin abunda yafaru,Ummi tace ikram ce tajefamin wayar aruwa ankaita gurin gyara yabaci shiyasa baki sameni ba amma Asma'u kam batazo gida ba kwata kwata wallahi.......
Shiru Anty suwaiba tayi don tana blaming kanta for everything don ah iya saninta ita ga abunda Aisha tace mata,to in Asma'u batazo gidaba inataje kiran Aisha tayi take sannan tace tazo tasameta gidan su Asma'u din, Aisha tunjin muryar Anty suwaiba tasan babu lafiya don haka tazari hijabinta abakin kofa sega Mallam Hudu yana shirin bude gidansu Amira don Sulaiman yaje hargidansa yamasa bayanin komai sannan shima yace zezo har gida yagasu Almustapha din yamusu murna inya samu sarari don shigan shi masarauta ba abu maisauki bane tun sanda Magajiya ta kori su Almustapha din.....
Gaishe shi tayi dayake tasan fuskarshi sannan ta tambayeshi number Sulaiman nankuwa yabata take tashiga Kira amma yayita ringing ba adauka ba ahaka harta isa gidansu Asma'u agaban Ummi tatsuguna tana gaisuwa yayinda Anty suwaiba tarufe ta da fada tana"kimai maita abunda kika fada min jiya bayan na dawo?".......
Jiki ah sanyaye tashiga bayani yayinda daga karshe tace ga number Yaya Sulaiman din nakarba yanzu barina sake kira,sake kira tayi still ba a daukaba cikeda damuwa Ummi tace"ikon Allah, Allah yasadai lafiya",Amin cewar Aisha din kafin tace Allah Ummi kilan sunzo bakunan nan ne I'm sure nansukayo.....
buge bakinta Anty suwaiba tayi"dallah rufemin baki,kuna abu kaman hankalinku baya jikinku,aidakin kirani da duk hakabai faruba".......
Ummi ne tace kiyi hakuri Suwaiba kuskure anriga anyishi fatanmu inda Asma'u take yanzu shine kawai..........
Anty suwaiba sunfi awa ah gidan kafin daga karshe Ummin tace kada tadamu tatafi aikinta zasu cigaba da kiran number din itada Aisha haka suka rakota har bakin gate nanne Aisha tayi tunanin tambayar me gadi ko wasu sunzo neman Daddy......
Cikin sauri yace"tabbas sunzo harda yarinyar wurinki yayi maganar yana nuna Ummi,sede nace musu mai gidan bayanan amma zai dawo yau kuma sunce xasu dawo in Sha Allahu".....
Murmushi Ummi tayi taredayin hamdala atleast tanada hope yanzu,may be zuwa anjima suzosu nan tacema Aisha dinma takoma gida babu komai bayan tafiyansu bejimaba sega Daddy ma yadawo,zuwa sukayi tayi mishi sannu da zuwa inda yake cemata yajima da shigowa gari yatsaya daurin aurene ah masarauta da aka gayyace shi,shiyasa koda dare yayi taga basuzoba setayi musu uzuri da kilan shagalin bikin ne yahanasu zuwa.....
Hakanan har yau Monday shiru sedefa yaudin hankalinta yadan fara tashi gashi ita bata tunkari Daddy da maganar ba shima kuma beyimata ba dukda daman tasan bayi mata maganar zeyiba kozata yi yaya tunda shiya bukaci ko ambaton Asma'u din bayason ayi mashi ah gidanshi.......
*****...
Dayanma likis tana zaune cikin lambu karkashin bishiyar mangoro data saba zama kullum sede yaudin bata fito da Ummi ba sakamakon baccin databarta tanayi ah dakin,lumshe idanunta tayi ahankali yayinda hawaye suka fara zuba ah idanunta tagaji she want to go back home,tana missing gidansu dama kowa ah gida, tadaukar ma kanta alkawari yaukam in Dad ko Sulaiman basuyi mata maganar tafiyaba komawa gidansu Aisha zatayi gobe sabida koba komai zamanta acan yafi ma ana akan zamanta anan gida daba saninsu tayiba............
Sa hannu tayi tana goge kwallarta yayinda takebin bishiyoyin tangerine da kallo duk maitarta dasu yaukam batada appetite din shansu......
Tananan zaune taji kaman ana taku kadan kadan sekuma can taji ankusa isowa inda take, tsoro ne yakamata donkuwa tunda take zuwa lambun bata taba sa'an haduwa dawaniba shiyasa take zuwa kullum freely without any fair,kallon gefe da gefenta tayi yayinda take tsoron kada masu maganar su kamata,ahankali ta tashi dayake bishiyar mangoron ba irin me tsayin da mutum zesha wahalar hawa bane setayi saurin dalewa bishiyaan ahankali sannan tayi likimo jikin wata reshe jitayi mutane biyun sunsake matsowa kusada bishiyar don daga inda takema tana iya hangosu.......
Jitayi daya Matar dake tsaye gaban yar budurwa taciro wani abu ah leda tace inji Magajiya kisaka wannan acikin shayin Almustapha inzaisha da dare kafin ya kwanta ina kince yakansha shayi?...
Gyada kai yarinyar tayi,Asma'u jitayi gabanta yashiga dukan uku uku sede fatanta taga fuskar yarinya amma bata iya gani daga inda take ......
Karban ledan yar budurwar tayi sannan tace zanyi yanda akace inyi sede yana iyakin sha don yanada ra'ayi wallahi.......
Tsaki Matar tayi sannan tace kekika sani kisan yanda zakiyi yasha in bahakaba keda Uwargijiyata nidai sakone na kawo miki,tana karashe fadin haka tajuya tatafi.........
Nan budurwarma tabar gurin, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'u ke furtawa "wannan din wani irin mugunta ne,mekuma akeshirin yima Almustapha lallai wanda akabama wannan abun tabbas acikin sashin da take yake,seda ta tabbatar suntafi sannan tasauko ah bishiyar tayi cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login