Showing 183001 words to 186000 words out of 235422 words

Chapter 62 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3504

irin jarabbabben likitane Na'im?".......
Dariya yayi tareda yin kasa da murya"Nima bansaniba Hamida,I don't even know when I turn to jarabbabbe. The only thing I know is ake kadai nakeyima wannan jaraban"......
Yanda yayi maganar seda yasata jin wani iri sekawai ta tsinci kanta da kallon cikinta daya fito sosai yanzu,shima kallon cikin yayi batareda yadauke kai agurin ba"how's the Baby?".......
Hararanshi tayi"You're crossing your limit fa"........
Tashi yayi tsaye tareda sa hannu ah aljihun wandonshi yana murmushi sannan yace"I'm sorry Mamin Unborn".........
Wani hararan ta wurga mishi sannan taja plate din abincin daya ajiye mata tashiga turawa batareda taso ba kawai don dai taci yabata maganin yatafi yabata guri,sede kallon da yakeyi mata harkusan sata kwarewa yayi,tsaki tayi cikeda masifa tadago"wai kai baka da respect for married women ne atleast!"........
Cire hannunshi yayi daga aljihun wandonshi tareda dan shafa kanshi yana murmushi sannan yadan sunkuyo yana tambayarta"waye married women din Hamida?".....
da mamaki take kallonshi,yar dariya yayi sannan yace.....
"as far as i know miji mai Mata kamar ki kuma kina dauke da cikinsa bazai taba barinki hakanan ah gidaba without paying you a visit koda sau dayane kuwa". .....
The first day dana ganki I thought kinada aure but not anymore,I can sense it Hamida,jikina yariga yagama bani baki da aure because the way my feelings are for you right now indai har kinada aure Allah ma bazai bani ikon yimaki wannan feelings dinba".......

Batasan sanda hawaye suka fara zuba ah idanunta ba na tuna abunda mijin nata yayimata hakanan batagane inda Na'im din yadosa ba kuma koda tagane dinma batason tayardar ma kanta abunda take tunani din kawai seta cigaba da tuttura abincin babu kakkautawa hartana neman kware kanta shine yakwace plate din dasauri sannan yace"ya'isa"......
Tana hawaye tace"bakaine kace senaciba"......
Murmushi rigimarta yasashi kafin yace"to ai bacewa nayi kikware kanki ba ko?"..........
Harara ta watsamai baidamu ba don yanzukam harya fara sabawa don haka seya balli maganin yabata tasha kafin yafice batareda yasake dawo da maganar dazunba he's just very sure batada auren and he'll not pressurize her to speak out actions dintama sunbashi ansar komai and he's certain that one day one time she'll tell him herself abunda yarabota da gidan mijin nata........
Besan dalili ba tun farkon haduwarsu yake ganin future dinshi ah tattare da'ita,there just something so special about her........

&&&
Yau sauran kwana hudu biki hakanan masarautar tacika da baki from different destinations barinma wanda sukazosu daga nesa,hakanan kowa is very busy with the preparations bangaren Zaliha kuwa gabadaya abun duniya yadameta,she really can't believe cewa abubuwa nata faruwa yanda su Sulaiman suka tsara, everyone is happy banda ita because she's really in pain from within hankalinta ma baisake tashiba seda taji Sulaiman na waya kan preparations dinsu na zuwa honeymoon dayakeyi ma su hudu wato shida Sumayya sekuma Almustapha da Asma'u dayakeson yima surprise......
She was very shocked jiya data labe tanajin zancen hakanan kasa bacci tayi ah daren jiyan, yauma tunda tatashi kasa fita ko'ina tayi dukda sunyi da Asma'un za ayimasu nasu lalle da kitson yau don anyima kowa sune ba ayimasu ba............
To ita inama taga tayin lalle?...
Intayi kenan ma tana farin ciki da auren,yanzuma Kai kawo take tayi ah dakinta itakadai hakanan gabadaya ideas sunki zuwa mata gashi yanda tayita shiga jikin Asma'un tana kisa mata karyar Sulaiman na zuwa bangarenta dawuri ma sanda suke aikin nan kamar abun be shigi Asma'un ba tunda bataga tadauki mataki ba and she never tell her anything regarding zamansu da Almustapha dukda itan tana hada karya tafada mata akan itada Sulaiman suna zaman lafiya.........

Gashi tasa Lantana ta bubbugi cikin Laure ma if zata iya samun wani labari dazai taimaka mata wurin executing next plan dinta amma Lantanan cemata tayi Lauren bata bata wannan fuskar ba shiyasama kawai tace taje takira mata Salma may be zata iya samun wani idea daga gurinta.........

Atare Lantana da Salma suka shigo batareda tabari sunkaraso bama tayi saurin isa inda suke,sukuwa dukawa sukayi suna gaidata cikeda girmamawa yatsina fuska tayi kafin tace"Tundazu nace kikiramin ita Ina kuka tsaya?"..........
Lantana ne tace"nasamu tana aikine Gimbiya"..........
Da damuwa Zaliha tadubi Salman kafin tace.......
"wai kin tabbatar kinga Asma'u tafita da kwalbar giyarnan ranan?"..........
Cikeda assurance Salma tace"wallahi nagani da idanuna Gimbiya sede in tanada irin ledar ne amma tabbas nagani kuma ranar ita tayi gyaran dakinshi ma don naji Iya Hindatu nacewa tace subari ita zata gyara"......
Tsaki Zaliha tayi tareda cize dan yatsanta because abun na matukar bata mamaki haryanzu, ahankali tace"I've no idea at all,narasa mezanyi inruguza bikin nan,narasa mezanyi in bakanta musu yanzu yes Sumayya da Sulaiman I can't do anything now wirun ganin na rabasu but Asma'u and Almustapha it's high time indai kuma nasamu naraba Almustapha da Asma'u before auren to tabbas zanruguza plan din Sulaiman na zuwa honeymoon ko wannan dinma ya wadatar for now",tayi maganar ranta ah matukar bace, she's just so confused........
Suma shiru sukayi suna tunanin ko Allah zaisa su iya taimakon ta,can Salma tace Gimbiya nasan wani abu guda daya.....
Dasauri Zaliha tace"meyene fadamin?"........
Gani tayi Salman kuma tayi shiru tana kokwanton tafada matane ko kada tafada din tunda it might implicate her and batason abunda zaijamata duka wurin Zalihan,infact batamasan meye yasa bakinta ya subuceba,cikeda bacin rai Zaliha tace"kiyi magana mana".....
Salma kamar zatayi kuka ta kekashe guridaya alamar tsoro kafin tace"na manta Gimbiya",wani irin cakumo wuyarta Zaliha tayi tana huci"Don ubanki kinmanta kamar yaya?"......
Hawaye tafara tsabar tsoro"Allah namanta",wallahi baki isaba koki tuno ko in yanka ki yanzunnan Zalihan tafada don ta tsoratata aikuwa ta tsoratan don cikin sauri tace"Allah zanfada amma karki dukeni don Allah".......
Sakinta Zaliha tayi kafin tace"inajinki".....
Jikin Salma na rawa tace"Daman zance miki ne lokacin da akabada shaidar sharrin da Magajiya tayima Yarima su Gimbiya sunyi niyar harda shaidar lalata da yan mata da ake zargin Yarima kan yatabayi zasu fada karyane, harma alokacin sun nemo Bayin da akayi masu fyade to amma sai Yariman ya tara Yan matan ya hanasu bada shaidar.........
"Kaman ya yahanasu?"....
"Miyasa ya hanasu?, Zaliha tayi tambayar cikeda zakuwa,kai tsaye
Salma tace"sabida wai bayason atona asirin ainahin wanda yayi laifin"............
"Waye yayi laifin?" Zaliha tayi ma Salma tambayar budan baki tayi zatace"bansani ba", cikin sauri Zaliha ta daga mata hannu"banace karki yarda kiyimin karya ba?".....
Baki na rawa Salma tace"tsoro nakeji karki dakeni",bazan dakekiba nace ai....
Gyada kai Salma tayi kafin tace"Yarima Sulaiman ne amma bayayi yanzu"......
Zaliha seda taji kamar numfashinta zedauke lokaci guda hakanan tana mamakin abunda Salma din tafada sede datayi wani tunani kuma setaga babu karya ah lamarin Salman hakanan tana mamakin miyasa Magajiya taboye mata wannan big secret din,yes she's jeolous kan mijinta yayi hulda da wasu matan but this will surely help, it'll help her ah yanda batayi zato bama tunda she can kill two birds at the same time with one stone......
Murmushi tadanyi Jin ideas sunfara kwararo mata kala kala kafin tadubi Salma tace"tashi kijeki zan nemeki"........

Godiya Salma tayi mata kafin tatashi tayi tafiyarta........
Kallon Lantana Zaliha tayi sannan tace"kina iya tuna koda daya daga cikin yan matan da Sulaiman yayima fyade ne?".............
Cikin sauri Lantana tace nasan har biyu ma Jiddoh da kaltume,to kinemo minsu yaudinnan kinajina.......
To tace mata kafin tatashi tafice cikin sauri,har Zaliha zatazauna setaji kuma tanason tayi lallen tsabar ganin plan dinta will go according to yanda takeson tsarashi,bangaren su Asma'un tajeta inda tasamu har angama ma Asma'un kitso anakan yi mata lalle.......
Dubanta Asma'u tayi da murmushi tana"harfa zancema mai kitson taje bangaren ki tayi maki may be you're busy ne shiyasa bakizoba"......
Yar murmushi Zaliha tayi tana shafa kitson kan Asma'u daba karamin tafiya da imaninta yayi ba tsabar kyau tana"kekam wani aikine yatsaidani,kitson ki yayi kyau sosai".......
"Nagode",cewar Asma'u din Amira dake gefe tadan yatsina fuska don Allah yagani batason Zaliha ko kadan aranta gashi sunkasa canza ma Asma'u raayin kan Zalihan ba canzawa tayi ba bangaren Afiya kuma tadan fara saukowa don hartakanyi mata magana cikin lumana tunda talura Zaliha is trying to be friendly with them and badadi suyita ignoring dinta koda sama sama ne suna gaisawa is okay ai koba komai itan matar Sulaiman ne.....
Anacikin yima Asma'u kitso Zahra tazota murna suka shigayi sosai Asma'un na seyau ma kikaga daman zuwa ko .....

Kama kunne Zahra tayi tana"I'm sorry Dear kinsan yanayin karatun mu sai ahankali" ......
Murmushi Asma'u tayi sannan tashiga tambayarta ya karatun dakuma course mates dinta databari dukda bawani sabawa tayi dasu sosai ba alokacin tunda basu jima dazuwa makarantar ba tabari,"duk lafiyansu kalau Dear sunata gaidaki Basma harda cewa infada miki tayi fushi wai taji za ayi bikin nadi ah town shine suko gayyatar su bazakiyiba"......

Dan dafe Kai Asma'u tayi tana"don Allah kibata hakuri ni kingama inbanda ku babu wanda na gayyata, believe me and she's highly welcome indai zatazo kice musu duk na gayyacesu".........
Afiya ne tace"bawani seda suka roka"....

Hararanta Asma'u tayi"banason hada guri kekamu",dariya Zahra tayi tana aigaskiyane fadi abunda keranki sis,dariya Afiyan tayi tana"Allah Zahra kiyima kawarki fada bikin sarautan mijinta guda komai se an takura mata takeyinshi, she's not even interested I don't know why kinga muma takura mata mukayitayi kafin ta aika muku ankon",wara baki Zahra tayi tana kallon Asma'un"are you okay Asma'u?"........
Dariyan yake Asma'u tayi kafin tace"kidai tsaya biyema Afiya kina ruwane"........
Bawani nan,nidai yanzu inkinason inji dadi kuma kema kifita daga kallon dasukeyi maki na kin auri babban mutum kina neman ki manta dasu to kidauko wayarki ki tura musu invitation card.....
Da mamaki Asma'u tace"au tunanin da sukeyi kenan?"...

Gyada matakai Zahra tayi kafin tace"kinsan mutane ba ayi musu Asma'u daman neman abun fada sukeyi kuma sunsamu,just show them komai ba komai bane ba and prove them wrong"......
To kawai Asma'un tace kafin takarada "I'll give you the invitation cards seki kai masu".........
Gyada mata kai tayi sannan suka canza hirar tana tambayarta Asiya,barni da Aseey yanzu kwananta uku agarin nan amma takasa lekoni ni fushi ma nikeyi da'ita ...........
Dariya Zahra tayi tana kunfi kusaa ai
babu wanda ma zaisan sanda zaku shirya,dan dundun Asma'un takai mata playfully tana"bawani nan"............

Sunanan zaune sega Rukayya tazota tsuguna wa tayi tana gaidasu cikeda ladabi kafin tadubi Asma'u tace"Gimbiya Yarima yace inkiraki"......
Seda taji zuciyarta tayi wani bum don rabon da taji sunanshi ma harta manta hakanan rabon data ganshi ma tun ranarda yaje duba jikin Hamida,dakyar takalli kafafunta da ake sakama lalle sannan tace"bakice mishi anamin lalle bane ba?"........
"Banfada ba cewar Rukayya din"......
"To kije kice mishi anayimata lalle akafa,bazai yuyu tatashi ba",wannan Karan Zahra ne tayi magana sekuma tadubi Asma'un to kema kikirashi kifadamai mana zefi......
"Kawai taje tafada mishi din,I don't even know where my phone is".........
Jijjiga kai Zahra tayi
In desbelief don Itama tasha kira akashe........

Yananan tsaye ah Corridor din dakinshi Rukayyan tazo mishi da ansar Asma'u din,gyada matakai kawai yayi ahankali inda tajuya tayi tafiyarta. Kallon screen din wayarshi yayi yana tsurama number din Mubaraq ido don shine daman yakeson magana da ita wai sunyi ta kiran layinta akashe always,for a moment yayi tunanin zaisamu yaganta yau hakanan yayi tunanin he'll embrace her and tell her how much he missed her, lumshe idanunshi yayi ahankali kafin yajuya yashige dakin nashi "the feeling is just so unbearable,he's just trying to be okay but truely it kills him inside"...........
Zama tayi ahbakin gadon shi hakanan yafi awa biyu yana tunane tunane shikadai,yana tunaninta yana kuma kara karanta massages dinda yayi ta tura mata batayi responding ba seda Mubaraq din yakirashi sannan yatuna ma cewa yakamata ace yafada mishi anayimata lallen tundazu wata zuciyar kuma tashiga raya mishi "to ai yanzukam angama",sekawai yaki picking call din, tashi yayi yafita ah dakin ah parlour yahadu da Salma don bangaren nasu babu wasu mutane ah zazzaune kasancewar bakin da sukazo daga wasu masarautar yawanci ah bangararruka daban aka saukesu relatives dinda sukazo kuma na Asma'u ne mostly se tsirarrun kawayen su Afiya da suka zo kuma suma duk ah daki suke zama shiyasa ma sashin baicika ba.........
Alama yayi matada hannu kan tazota,cikeda ladabi takaraso kanta ah kasa hakanan tana mamakin wai yau Yarima ne zai kirata da kanshi.....
Mika mata wayar yayi sannan yace"kikaima Asma'u".......
Karba tayi sannan tace"to",hakanan ranta nayimata kal wai itace yau da rike wayar Yarima guda lallai takwashi sa'a,sanda takaima Asma'u wayar har ancire lallen don ita kadai ce adakin da alama ma daga wanka tafito don tana daure da towel ne.......
"Karban wayar tayi da mamaki sekuma ga kiran Mubaraq yashigo".........
Murmushi tayi sannan tadaga,"Ina wuni Yaya Mubaraq"......
"Lafiya Lau Ma'u,wai meyasamu wayarki ne ayita nemanki ba'asamunki",dan sosa kanta tayi sannan tace"wallahi bansan inda najefata baneba shiyasa amma zanyi kokari induba yau"........
"Kiduba dinkam mutanen batagarawa gobe zasu taho karsuzo suna kiran layinki ah kashe".......
Da mamakin waya gayyace su tace"dagaske Yaya Mubaraq?".....
Dariya yayi jin how excited she's kafin yace"har batagarawa Sulaiman da Yariman dakansu suka kaimusu invitation shine Baffa yace aikuwa zasuzo kodan karamcin da akanuna musu"........
Murmushi tayi sannan tace"Allah yakawosu lafiya, Aunty(matar Mubaraq din) da Asiya fa?"......
Kai tsaye yacemata gobe zasuzo su.......
Allah yakaimu tace mishi inda sukadan taba hira sannan yakara tuna mata da tanemo wayarta please kafin sukayi sallama,ajiye wayartayi dukda kuwa tana iya shakar kamshin me wayar ajikinta......
Salma kam already harta tafi tun bayan data bata wayar bare tabata ta mayar mishi itakuma batason haduwarsu Allah yagani sekawai tayi deciding bata shirya inta koma dakinsu Amiran setaba daya daga cikinsu yakai masa.........
Tana cikin tunanin nan ne taji anbude kofar dakin wannan dalilin yasata juyawa don ganin wanene wara idanunta tayi ganin shine kafin dasauri tatashi tayi bandaki aguje tareda rufo kofar ta ciki tana sauke nishi,shikuwa haryanzu yana bakin kofar dakin nata yana mamakin abun nata,dodo tamaida shine komi?........
Ahankali yadinga takawa zuwa bedside drawer dinta inda yahango wayarshi,sa hannu yayi yadauki wayar sannan yadubi bangaren da bandakin yake. Kallo daya zakayima Almustapha ya baka tausayi shikanshi yarasa mezaiyi yakuma rasa meyake addabar rayuwarshi game da'ita karasawa yayi bakin kofar bandakin sannan yadora hannunshi jiki kaman wanda inyayi hakan kofar zata budune cikin raunanniyar murya yace"Asma'u ghost nakoma mikine dakike guduna?".........
Tananan jingine da jikin kofar hakanan batasan sanda hawaye suka fara running cheeks dintaba,she's missing him so badly gashi kodan kallon tsoro tayimishi ah dazun setaga yakara yimata kyau dukda kamar ah firgice yake ga kayan dayasa sun amshi jikinshi bakar shadda ne dayasha aiki ba laifi......
Jin sautin kukanta ne yasashi lumshe idanunshi ahankali, she's so stubborn tukunnanma shida ita waya kamata yayi kuka fisabillahi?,Kara kasa da murya yayi"I'm not going to force you to talk to me inbaki so hakanan bazan sake damunki da kizo gareni ba so kidaina ma bata hawayenki kinji sede inason kisani in guduna dakikeyi kina tunanin will make me divorce you then you're very wrong Asma'u. Aure na dake babu zancen rabuwa acikin sa",daganan yafice ah dakin jiki sanyaye........
Zamewa tayi kasa tana kuka me tsuma zuciya wanda tana da tabbacin na tausayin daga ita harshi dinne don from his voice tagane he's in pain too,to anma pain din na menene?........

"inyana Sonta miyasa bazai fadaba ko dai lust ne wata zuciyar tashiga raya mata ahankali?"....
Haka taci kukanta daga karshe tasake wanka tafito tashirya jiki ah sanyaye hakanan direct bangaren Hamida tawuce tadauko wayarta don daman acan yake tuntuni.......
Kunnawa tayi sannan tashiga kiran layin Asiya baijima yana ringing ba tadauka, ahankali tace....
"Asiya bazakizo baneba!"......
Dariyan yanda Asma'un tayi magana ah shagwabe Asiyan tayi kafin tace"ba Yaya Mubaraq yace miki gobe xamuzo ba"..........
Gyadakai tayi ahankali kamar wanda tana kallon Asiyan ne kafin tace"inadai zakizo goben?"......
"Sure, insha Allah zamuzo".....
"Allah yakaimu and please kuzo dawuri inatason muyi wata magana", Asma'un tayi magana murya ah raunane cikeda damuwa Asiya tace"lafiya daiko?"......
"Kekam sekinzo din Aseey, Lafiya lau"...
To kawai Asiyan tace mata dukda tadamu da sanin menene haka sukayi sallama kafin Asma'u ta katse call din..........
***
Washegari tun sassafe sega Lantana dasu jiddoh ah bangaren Zaliha........
Murmushi Zaliha tayi tana kallonsu kafin tace kuzauna mana,zama sukayi dukansu biyun cikeda tsoro don gani suke wani laifin sukayi shiyasa aka kirasu.....






Vote
Comment
Share!......
[3/23, 6:07 PM] >?p?: =?Q?=?Q? *GIDAN SARAUTA* =?Q?=?Q?


Written by *Zeeneert*=ؕ?


*Zeeneert*@wattpad....


*Page 65~66*..


Koda tashiga dakin yanda tabarshi dazun haka tasameshi,very neat and tidy gakuma decorations datayi dazun. Straight bedside drawer din datake hange tajeta bude sede duk iya dubanta babu wani abu mekama da envelope aciki wannan dalilin yasa tayi tunanin yana daya bedside drawer din shiyasa ma takarasa gaban drawern budewa tayi ahankali don haka kawai taji kirjinta na mugun bugawa lokaci guda.........

Makulli tafara arba dashi asaman wani envelope wanda ajikin kwalin da spair keys keciki anyi rubutu da manyan harrufa inda aka rubuta Organo hotels and suites gakuma room number akasan dukda kallo daya tayima key din tagane anciri wasu daga jikinsu ba complete keys din bane ba dukda bugun da zuciyarta yakeyi hakan behana takauda key din gefe ba inda tadaga envelope nasaman ko Allah zaisa taga wani akasan shi tunda Zalihan cemata tayi wanda zata dauko din yana ta kasa. Sede da mamakin ta babu wani envelope din dago nasaman tayi gabadaya don dubawa dakyau amma seya subuce ah hannunta yafadi kasa sakamakon karkarwan da jikinta keyi batareda tasan dalili ba innalillahi wainna ilaihir rajiun tashiga furtawa sannan tajuya ga envelope din daya fadi din don daukowa amma gabadaya abubuwan ciki sun zube akasa dasauri takarasa gun tareda daukan wata paper data gani don mayar wa amma da mamakin ta setasake ganin organo hotels and suites asaman paper din mamakine yakamata don itadai tasan organo hotels and suites agarin nan yake inma akwai awani gari bazatace Almustapha yataba zuwaba tunda shiba mutum bane mai yawan tafiye tafiye bare ace...........
Hankalinta baikara tashiba seda taga indication nacewa hotel din Zarian datasani dinne gakuma sunan Almustapha radam radam akai cikin sauri tashiga karantawa takardace datake nuna cewa yabiya kudin dakin for one year wanda ayanzu yaci wata shida acikin shekara daya that means tun kusan aurensu kenan hakanan bayan sun samu yancinsu amatsayinsu na ya'yan sarki Abdulrahman,mamakine yakamata na meyakeyi da dakin?....

Still jikinta na mugun karkarwa gakuma zufa datakeji yanacigaba da keto mata dukda irin sanyin ACn dake dakin haka tadaga paper din sannan tacigaba da kallon sauran duk shaida ne na mallakar dakin sekuma reciept na biyan kudin dakin dagacan kasan papers din kuma tayi arba da hotunan yan mata sunkai goma wanda duk turawa ne ga jikinsu ma babu wata kyakyawar sutura daga mai pant da bra sai mai mini skirt da best ko half vest sa hannu abakinta tayi tana kokarin rike kukan dake shirin kwace mata dukdama takasa tsaida hawayen da ah yanzu suketa kwalalala kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login