Showing 99001 words to 102000 words out of 235422 words

Chapter 34 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3512

shirun sannan yace ......
"kace kana nemana nazo kuma bakace komaiba".....
Batareda ya kalleshi ba Almustaphan yace...
"do you know any good geologist dayake aikin boreholes?"......
Dan shiru Sulaiman din yayi na dakiku kafin yace sede in bincika maka dai Yaya.......
Rufe files din dake gabanshi yayi sannan yace"okay then, please kabincikamin before end of this week"daga haka yayi wucewarshi dakinshi.....
Tabe baki Sulaiman ma yayi sannan yaciro wayarshi yashiga kiran Sumayya bejima yana ringing ba tadauka...
"Babygirl bakiyi bacci ba?"...
Cikeda shagwaba tace Yaya Sulaiman nice nakoma Babygirl yaukuma?......
Yar dariya yayi sannan yace...
"audama bakisaniba you're my Sweetest Babygirl dazu shine kika gudu abunki koki bani ansa"......
Murya can kasa kasa tace...
"you know my answer already ae".......
Tashi yayi daga kujerar yafice ah parlourn don komawa bangarensu yana nidai bansani ba kifada bakini inji......
Make kafada Sumayya tayi kaman wanda tana gabanshi tace...
"naqi wayon,kasani ai kawai kanason infada ne"........
Yar dariya yayi sannan yace"okay love nakyaleki but when you feel like saying it out kifadamin kinji".......
Haka suka cigaba da wayarsu cikeda so da kaunar juna don dukansu babu wanda yalurama time yagudu harhaka don se gurin daya nadare sannan sukayi sallama su Hajiya zaliha anacan anata shatata bacci miji nanan yana soyewa da wata.......

Washegari dasafe Mai Martaba ya aika akira mashi Hajiya Muniba babu bata lokaci tasamoshi ah sashin shi bayan sungaisane yace shawara nike nema Muniba dan murmushi tasaki sannan tace inajinka Dear........

Gyara zama yayi sannan yace Magajiya tasameni maganar household kinsan ita take controlling komai daya danganci bangaren abinci dama kuma baki daya bayi Mata......
Gyada Kai Hajiya Muniba tayi cikeda gamsuwa sannan yacigaba"she's somewhat sick this days so tasameni kan tanason ta ajiye wannan responsibility din and age requested that I give this task to one of our Daughter in-laws so I'm somehow confused kungane Zaliha is the eldest but Asma'u itace Matar Almustapha Kuma yagirmi Sulaiman gabadaya narasa figuring out waye zanbamawa banason nayi rashin adalci aciki .............
Dan shiru Hajiya Muniba tayi kafin tadan numfasa"ae abun ba agirma bane Dear kaduba cikin su waye kayarda dashi wayekuma kakeda tabbacin inkata wannan damar bazata zuba ma kasa ah Ido ba,the most important thing shine wanda zaasa agurin atabbata ya cancanta,so yanzu Kai wakake ganin you trust so much"........
Shiru Mai Martaba yayi because in his heart yayarda da Asma'u dari bisa dari sede Zalihan ma bazaice wani abu akanta ba tunda tanazuwa gaida kuma tanada ladabi don haka seyace I trust them both..........
Murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tace then seka basu duka kowacce kayi mata handling responsibility daya dace da'ita and hakan ma zaifi don babu wanda zaice kayi sonkai..........
Godiya yayi mata sannan yace thank you Muniba......
You're welcome Dear barina barka kashirya yanzu nasan nanbada jimawaba zaka shiga fada ko?...

Gyada mata Kai yayi ahankali kafin tamishi sallama tafice tana tunanin Allah yasa kada yabama Zaliha aikin dazaisa tana wulakanta bayi bangarenta takoma direct.............

Yau Asma'u tareda ita akayi karatun asuba donkuwa gani take Itama zata karu koba komai daganan tawuce Kitchen sukayi breakfast dakanta takaima Almustapha abinci daki don Sulaiman beshigo ba yau......
Yayi mamaki donshikam har yayi wanka abunsa yashirya cikin bakar hadaddiyar shadda data kara fito da kyawunsa........
Ajiye abincin tayi sannan tace...
"Good morning Yaya Almustapha"
Morning ya ansa mata ajiye abincin tayi sannan tashiga serving dinshi calmly duka baihanata ba harta gama sede yaki faraci itakuma taki tafiya..........
Ganin kamar da magana abakinta ne yasashi cewa...
"do you need anything?"......
Girgiza maikai tayi alamar aa kafin tace..
"bakacemin ka gode ba"......
Cikeda mamaki yace"name fa!"..
Turo baki tayi"for accepting your friendship mana"....
Kallonta yayi blankly aranshi yana"so we're now friends shiyasa tadawo dayimin wayannan hidimar", ahankali kuma yasakar mata
Lallausar murmushi dayayi melting heart dinta kafin yadubeta yana...
"Do friends have to thank each other?"......
Tashi tayi tafice tana "kaidai bakason cewa ka goden ne kawai"...
Jijiga kai kawai yayi sannan yafara cin abincin calmly........

Around 10:30am Asma'u taje gurin Talatu tana kince kina nemana?......
Gyada mata kai Talatu tayi ahankali sannan tace"abunda kikayimin bakowa bane zai iya yimin arayuwa dukda anfada miki cewa niba mutumiyar kirki bace amma hakan besa kinjuyamin bayaba dan zamana dake nagane cewa baku cancanci inki taimakon ku ba kamar yanda kika taimakeni Magajiya kuma ita tayi watsi dani inaganin lokaci yayi daya kamata tafuskanci gaskiya bayan duk abubuwan damukayi", folding hannu Talatu tayi hawaye nabin kuncinta tace hankalina ba akwance yakeba gabadaya nafara nadamar abubuwan danayi kifada min duk abunda kikeso inyi miki na taimako gurin tona asirin Magajiya nikuma zanyi miki bayan nan kuma inason inmika kaina ga hukuma sabida suyimin hukuncin daya dace dani"........
Asma'u har ranta taji dadin maganar Talatun yayinda afili kuma tace"niban daukoki don kutayamu tonama Magajiya asiriba munyi miki don Allah ne so basai kin takura kanki ba please"......
Jijjiga matakai Talatu tayi tana nariga nayanke shawara zan taimakeku don Allah kada kice aa,gyada Kai Asma'u tayi sannan tace"are you sure?".....
Eh cewar Talatun kafin Asma'u tace to kibari zamuyi magana anjima yanzu zanje fada ne Mai Martaba yana nemana kikwantar da hankalinki don Allah ......
Gyada mata Kai Talatu tayi yayinda Asma'u tafice zuwa bangaren Mai Martaba don fitowarta zata gun Talatu Rukayya kece mata an aikomata sakon kira koda ta'isa samun Zaliha tayi da Magajiya zaune saida zuciyar ta tabuga dakyar ta'iya daurewa tazauna can gefe tareda gaida Mai Martaba din......
Amsawa yayi yana murmushi kafin tagaida Magajiyan.....
Yitayi kamar batajiba seda Mai Martaba yace Magajiya bakiji ana gaidaki bane cikeda takaici ta ansa tana hararar Asma'u din itadai Asma'u kanta nakasa donta rasa dalilin wannan Kiran that too tareda wayannan ko me suka hada mata Allah kadai yasani....

Mai Martaba ne yace"nakiraku ne sabida indaura wani nauyi wanda mahaifiyarku ta bukaci ayi hakan".......
Shiru sukayi dukansu dukda kirjin Zaliha sai dukan uku uku yake tun shigowar Asma'u domtarasa dalilin dayasa za ayi involving Asma'u cikin wannan zancen badai Mai Martaba yanason bata wani abun bane haka tayita tunane tunane ita kadai dakyar ta'iya maida attention nataga abunda yakecewa bayani yayi musu na yanda sukayi da Magajiya din sannan yace "shiyasa kukaga nataraku duka biyu kowa inbata portion din aikinta sabida befi experience ba because one day one time kune zaku zama manyan and the responsibility will be all yours"......
Gyada kai sukayi jiki ah sanyaye sannan yace ke Zaliha daga yau zakina kula da bangaren hukunci na bayi insunyi laifi kokuma ansamu sabani ah tsakaninsu kece zakina solving problems nasu inkuma yagagareki kina iya samun Magajiya she'll help you out or kizo direct kisame ni kinji........
Gyada kai kawai tayi dukda jitake kamar zuciyar ta zatayi boasting wato wannan ne kadai aikin daza abata?......
Jitayi Abban yadubi Asma'u sannan yace Daughter kezakina kula da bangaren abincin bayi dakuma suturarsawan su duk inkinada matsala kisameta kokuma just come to me directly sannan ke Asma'u kisamu jakadiya zatayi maki bayanin komai gameda abincin masarautar nan daduk wani abu dayakamata kisani sannan yadubi Zaliha itama yace kekuma ga Magajiya she'll explain everything to you inafatan ban takura wanin ku ba?....

Gyada Kai sukayi ahankali dukda ma Asma'u har ranta itakam bason abunnan takeba sede dawani bakin zata dubi Mai Martaba tace masa bataso?...
Intayi haka tayi masa adalci kuwa wayannan sune tambayoyin da takeyima kanta albarka yadinga saka musu sannan yasallamesu.........
Zaliha da Asma'u ne sukafara fita yayinda Magajiya tadubi Mai Martaba tana amma dai rankashidade baka kyau.......
Batakai ga karasawa ba yadaga mata hannu alamar ya Isa sannan yace"I did what I felt was right kuma kene kika ce ah tsakanin su biyu nikuma bazan iya hakan ba so please Magajiya just watch over them and pray Allah yasa hakan shiyafi alkhairi gobe za ayi introducing nasu to Bayin su susan cewa sune sabbin shuwagabanninsu I've somewhere to go to right now sena dawo yana karasa fadin haka yafice yabarta tsaye tanabinshi da kallo baki sake".........


Vote
Comment
Share!
[3/23, 5:47 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*



Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad....

*Page 40*




Lallai Mai Martaba wuyanshi yayi kwari bata taba tunanin zeyi taking wannan step dinba don atunaninta ai Zalihan ce babba so bazai taba bama Asma'u ba sede gashi he end up giving her some of the responsibilities wanda shine ma yafi mahimmanci da girma ah idanun bayin...........

Bin bayanshi tayi tafice fuuuu kamar wanda zata tashi sama zuwa bangarenta.........

Zaliha kuwa koda suka fice tareda Asma'u din sebinta da mugun harara takeyi ganin Asma'un batamasan tanayiba yasata saurin jawo riganta wanda har hakan yatsoratar da ita cikin sauri tajuyo tana..
"miye hakan kuma?".....
Sakin rigarta Zaliha tayi tareda daga hannu tana nunata da yatsa daya"wallahi karkiyarda kice zaki shiga harkata bawai kinga anbaki matsayin dayafi nawa ba kice zaki raina ni,don da alama ma roka kikayi don ah iya sanina Mai Martaba bazai taba daukan wannan matsayin yaba ma wanda ba jinin sarauta ba irinki,nina rasa ke wace irin mayya cema tukunnan dahar kikasamu wannan matsayin ah gidan nan".....
Asma'u daranta yagama baci dukda tanajin hawaye sun taru mata tayi kokarin makesu kadama Zalihan taga weakness dinta ahankali tace"yanzu sabida matsayi kike zubar da girmanki har kikemin magana haka?"...
Zaliha kamar zata maketa tace ..
"karki fadamin maganar banza"......
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi sannan tace"nibazan tsaya ina fada dake akan abunda baikai yakawo ba Aunty Zaliha sede inason kisani shi position din da kiketa fifiko akaima basonshi nakeyiba don gani nakeyi kamarma wani nauyi aka dauramin da'ace zakiyimin hanyar daza a saukemin ita ma bakaramin gode miki zanyiba abunda yasa kikaga nayi shiruma sabida Abba ne,bazan taba bari yabani aikiba inkiyi ince zan zuba masa kasa ah idanu shiyasa kikaga haka so do whatever you want to take it back bazan damuba... takarashe maganar tareda juyawa don tafiya sekuma tatuna wani abu tadawo"and yes,kada kisake zagina kokice zaki zagi identity na atleast I'm proud of the fact that niba Yar Gidan Sarauta baceba hakanan ban hada dangi dasuba koba komai mu bamu fada da yan uwanmu na jini sabida position,koba komai bama wargaza zumuncin mu sabida abin duniya hakanan koba komai we stays like a family and we're true to one another bamwa stabbing yan uwan mu behind their back. atleast it's prestige!, Asma'u takarashe maganar tanayima Zaliha wani irin kallo kafin tajuya tayi tafiyarta tabarta tsaye gurin kamar gunki tana hucin takaici.......

Zaliha jitakeyi kaman tabita ta bugi yarbanza amma tayi controlling anger dinta tawuce bangaren Magajiya aranta tana"harni yarinyar nan zata fada ma magana,aiko zanyi maganinta"
Asma'u ma tayi nasu bangaren ah parlour tasamu Ummi tana kallon CNN jingine jikin kujera da alama ma taimaka mata akayi tazauna din......
Fake smile tasaki don gabadaya ranta ajagule yake game da wannan babban nauyi da aka daura mata gashi har Zaliha naneman tafada mata magana tunma ba aje koina ba abun bakaramin damunta yayiba.......
Zama tayi gefen Ummi tareda gaisheta sannan tace yajikin Ummi?.......
"Dasauki alhamdulillah Habibty yanaganki wani iri,Is everything alright?",Ummi takarashe maganar tana observing fuskar Asma'u din gyada mata kai Asma'u tayi tana kokarin danne damuwarta kafin tace...
"babu komai Ummi everything is fine"......
Cikin sauri Ummi tace a'a kam kifada min damuwarki please it's evident on your face that kinada damuwa, inbaki yi sharing damuwarki daniba dawa zakiyi sharing Asma'u?.........
Hakanan se Asma'u taji she's free with Ummi din and she can share her problems with her indai tawannan fannin ne ahankali tafada mata yanda sukayi da Mai Martaba din dakuma yanda sukayi da Zaliha awaje kafin daga karshe tace"Ummi I'm too young for that ta'ina zan iya rike wannan nauyin banason inzo inyi failing Abba and kinga sabida haka ma munfara samun matsala da Zaliha koba komai Matar Yaya Sulaiman ce bazanso fada irin haka yashiga tsakanin mu ba kumama kaman zatafi dacewa da aikin tunda ita ranta naso", takarashe maganar cikeda damuwa.......
Murmushi Ummi tayi sannan tace...
"wannan shine damuwarki Asma'u?".....
Gyada mata kai tayi ahankali kafin Ummin tace bazan ki taimaka miki wurin sawa adauke miki wannan matsayin ba indai kina ganin bazaki iyaba but before that Dear inason kizagaya cikin bayin nan fannin inda suke zama,abincin dasukeci dakuma suturun dasuke sakawa dama sauransu kiga yanda suke rayuwa seki dawo kifada min opinion dinki"......
Dagowa Asma'u tayi tana kallon Ummin murmushi Ummi takumayi mata encouragingly tana"I'll support you whatever your decision might be kinji"......
Gyadama Ummi kai tayi don hakanan taji hankalinta yadan kwanta sannan tace zanjeni da dayanma Ummi.........
Allah yakaimu Ummin tabata ansa ahankali nan tazauna gefen Ummi tana tayi mata hira don ganin tayi Lightening mood dinta cankuwa sega Asma'u se dariya takeyi har Almustapha da Sulaiman suka shigo gaidasu tayi suka amsa tananan zaune.........
Sulaiman ne yadubi Almustapha din sannan yace...
"nasama maka maiyin aikin and he's willing to do it yacemin ma zaka iya zuwa kasameshi da yanma kokuma shizaizo gida dakansa kuyi magana"......
"Thank you shine abunda Almustapha din yace"......
"You're welcome Bro amma zakaje kasameshi ne koshi zaizo don yace I should get back to him on time Sulaiman yayima Almustapha maganar yana kallonshi?".....

Dan ware hannun yayi alamar baisaniba shima jijiga kai Sulaiman yayi in desbelief sannan yace"Allah Yaya you'll never change".....
Murmushi kawai yayi bece komaiba sema daga wayarshi dayayi yashiga danne danne Sulaiman kuwa duban Ummi yayi yace"Ummi yakamata akai Yaya hospital ko akwai aikin daza su iyayima bakinshi wanda zaisa yafarama mutane magana sosai ta hanyar basu details mekyau ba short short maganaba, hawa mulki zakayi Yaya yakamata ace kana interaction da mutane yanzun sosai"....
Dariya Ummi tayi tana"Kai Sulaiman ba a rabaka da abun dariya wallahi yanzu daman ana sa mutum yakoyi magana dole ne ah asibiti?"....
Dariya Sulaiman dinma yayi yace"ahto Ummi nagadai sune suke bada taimako inmutum nada problem na rashin lafiya may be they can help"........
Lol that's how your Brother is naturally you can't change that Ummi takarashe maganar tana yar dariya sannan takara da but kaga ni mukanyi hira sometime and he's open to me so with time inya hau mulkin dole yayi maganar ai tunda yazame masa dole.......
Shidai Almustapha yanajin su bece komaiba Asma'u kuwa se satan kallonshi take tana mamakin shi wai ace mutum magana ma wahala takeyi masa.ikon Allah kenan dan murmushi yayi jin sundameshi da same magana sannan yadubi Ummin yace...
"Ummi fura nikeson sha".....
Kallonshi Ummi tayi da mamaki tana...
"Daman haryanzu kananan da jarabar shan fura Imam?",shidai shiru yayi bece mata komaiba yayinda Ummi tadubi Asma'u tana"Daman yana yawan shan fura haryanzu?"....
cikin sauri Asma'u ta girgiza kai alamar aa don tama rasa mezata ce yar murmushi Ummi tayi"cab lokacin da Imam na karami bana iya rabuwa da fura da Nono to kullum seyasha kamar jaraba inko babu yadinga kuka kenan haka zaihanamu bacci ranar"......
Asma'u batasan sanda dariya ya kubce mata ba she's just imagining him crying like a baby yayinda dayan bangaren na zuciyarta ke tambayarta miyasa to bata taba ganin yasha fura ba tunzuwanta gidan hakanan kuma bata taba gani su Jamila na hada mishiba......
Abunda basu saniba shine Almustapha haryanzu yanason shan fura da Nono sede tunda Ummi takwanta rashin lafiya besake sha ba don duksanda yakalli fura da nono ko ah kasuwa ne seyadinga tuna yanda Ummi ke dama mai ada lovingly toko ya siya baya iya sha yadinga tunanin mahaifiyartasa kenan dukda kuwa ranshi naso toyau kuma seyaji yanason shan furar data dama da hannunta amma seya lura yajama kanshi raini ne tunda Ummi ended up gisting his wife about his childhood............
Hararar Asma'un yayi dayaga tana mai dariya sannan yayi wucewarsa daki Sulaiman ne yace"I text him zezo gida in the evening"......
To kawai Almustapha din yace mishi sannan yayi wucewarsa daki dariya Ummi tayi kafin tace"Da akwai wata mata ta'iya fura sosai harcikin masarautarnan take kawo mana kullum Nono kuma akan tatsa daga jikin shanayen masarautar ne so fresh sekin gani lokacin gwanin ban shaawa ",koina Matar take yanzu oho.....
Ummi tayi maganar ahankali......
Asma'u ne tace rayuwarkenan Ummi inda rabon kisake ganinta zaki sake ganinta insha Allah nima kakata ta'iya fura haryau bansake shan fura maidadi irin nataba.........
Kallonta Ummi tayi sannan tace"you must be missing her I know?'.....
Murmushin dayafi kuka ciwo kawae tayi don harga Allah tanason ace Itama tanada kaka mesonta me goya mata baya hakanan tana pampering dinta kaman yanda taga anayima wasu yaran sede ita Allah baibata wannan gatan ba tunda kakkaninta na bangaren Uwa duk Allah yayi musu rasuwa se Hajjan ne dama itakuma tadauki karan tsana ta daura musu gashi tayi aure ma koneman inda take batayiba........

&*&

Koda Magajiya tashiga dakin nata samun Zaliha tayi azaune se kumbure kumbure takeyi itakanta oganniyar afusace tashigo...........
Dasauri Zaliha tatashi tana......
"Mama kinga abunda Mai Martaba yayi ko?"....

Zama Magajiyan tayi tana sosa jikinta gabadaya yanzu jikinta yadameta da kaikayi fiyeda nadama donta lura kaman abunma gaba yakeyi gawasu kuraje dake fito mata ah skin dinta yanzuma data rasa na menene kuma bawani kyaun gani Allah yataimaketa acikin jikine ma dakyar ta'iya barin susan jikin kafin tace"bantaba tunanin zeyimin hakaba wallahi all I was thinking shine ke zaibamawa tunda ke babba ce amma tunda yayi haka to bazata sabuba don bazan taba bari wata data keda dangantaka dasu tayi taking hold of this responsibility ba,tayi kadan wallahi", Magajiya takarashe maganar tana huci.......
Nima bantaba tunanin hakanba Mama amma tunda yabatan babu matsala nalura shiru shiruce kumama dabakinta tacemin bataso dazu damuka fita daga bangaren Mai Martaba din wai sabida bazata iya dubanshi tace bataso bane yasata karban responsibility din so, ni aganina zan kula da komai zannuna nafi zakewa harma shi Mai Martaban dakanshi yadawo yabani bakidaya"....
wani kallo Magajiya tayima Zaliha don itadai bata tunanin Asma'u bazatayi wani abuba donta lura Asma'u is naive and cunning tun ranar datazo takwaci Talatu ah hannunta so bazata taba bari tahada hulda da'ita bama ita abunda tayi deciding shine tafasa yarda da sharawan databama Mai Martaba din ita zatacigaba dayidin kawai har susamu mulki yadawo hannunsu baki daya seta mayar da aikin ma Zaliha din............
"Ninasan abunda zanyi goben so kada kidamu kuma dukyanda kikaga nayi kigoyamin baya because it's the best for you".......
Gyada kai Zaliha tayi dukda kuwa tana mamakin me Magajiyan zatayi kuma wani mataki zata dauka sede koma meyene she has full faith in her...........

**&**

Bayan la'asar Jamila tashigo hannunta rikeda kwaryan Nono dakuma ledan fura wanda Ummi ne tasata tasamo mata don tanason dama ma Almustapha din tunda yace ranshi naso......
Ajiyewa tayi sannnan tace Aunty ga fura da Nonon murmushi Ummi tayi kafin tace bude mugani Jamila Allah dai yasa fresh Nono ne beyi tsamiba kinsan Imam da zabe.......
Bude kwaryar Jamila tayi yayinda Ummi tasa hannu tadan taba Nonon cewa tayi"yauwa babu tsami se ah tace shi ajuye ah roba kusaka shi ah fridge indare yayi zandama mishi kafinnan yayi sanyi".......
To Aunty nima nayi kewar damunki wallahi,dariya Ummi tayi tana yau zakisha ai karki damu daukan kwaryar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login