Showing 51001 words to 54000 words out of 235422 words

Chapter 18 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3471

talk like a sensible person tabbas taji dadin canjin datagani ah tattareda Yayar tata sede she don't think shawararta ko daya tayi tasiri ah zuciyar ta, Aisha dake gefene tace Asiya maganarki gaskiyar ne nima shawarar danaso bata kenan and kicigaba da addu'a, Allah yazaba muku abunda yafi alkhairi shine kawai,don Allah kikwantar da hankalinki Almustapha kuwa abu daya zakimishi "pray for him and not crying".....
Gyada musu kai kawai tayi yayinda suka cigaba da bata shawarwari daga karshe sukayi forcing nata taci abinci bawai don tanada appetite ba.......
Aisha se yanma lilis tabar gidansu Asma'u takoma gida daniyar inta huta seta shiga gidansu Amira din.....

****
Tunda Mallam Hudu yakirashi yafada mishi halin da 'Dan uwanshi yake ciki bakaramin tashin hankali yashiga ba nan yafadama Dad, Dad din yashiga tashin hankali sosai kafin yadubeshi that means yakamata mutafi before Thursday cewar Dad din, Sulaiman ne yace no Dad indai bakagama shirin tafiyaba i can go inyaso kusai kutaho ranar Thursday din......
Dad ne yace gobe Wednesday right,why not mutafi goben gabadaya girgiza kai Sulaiman yayi kafin yace Yaya Almustapha needs me now bansan me Amira take cikiba she must be worried zanbi commercial flight dayanman nan inyaso ku sai kutaho ta private plane din Abba sabida Afiya........
Dafashi Dad yayi kafin yace bazan hanaka ba, Allah yakaika lafiya muma gobe zamuhau hanya in sha Allah......
Gyadama Daddyn Kai yayi jiki ba karfi kafin yatashi yatafi dakinshi cikeda damuwa,he can go to any length in order to save his Brother,so Mamanshi tayi using abunda shi yakeyi against his Brother innalillahi wainna ilaihir rajiun,betaba regretting yin zina ba sai yau....
lumshe idanunshi yayi jiyayi anyi knocking kofar dakinshi,cikin kakkausar muryarsa yace "come in", Sumayya da Afiya ne suka shigo......
Afiya ne tace nikam zanbika Yaya Sulaiman please,sauke idanunsa yayi akanta kafin yace kiyi hakuri gobe kuma zaku taho I've to go there and handle things kafin ku iso,trust me Sis...
Goge yar kwallarta tayi kafin tace nayarda dakai dari bisa dari Yaya Sulaiman,Sumayya ne tace "nika tafi ma daman ka takuramin dayawa,hardawani cewa wai ba ashiga Nigeria da English wears".....
Murmushi yayi yana kallon yanda take magana kafin yace"oh haka ma kikace,I know you'll be the first one to miss me".....
Harara takai mai kafin ta tashi ninama fasa taya Yayanki shirya kayan nashi yabata min rai,dariya Afiya tayi kafin tace nidai baruwana dakankima zaki dawo......
Fita tayi tana bubbuga kafa,binta yayi da kallo yana murmushi.....
Kafin Afiya tashiga hada mishi kayanshi,har airport suka rakashi seda jirginsu yatashi sannan suka dawo gida suma don karasa nasu shirin zuwa Nigeria washegari.....
*****
Magajiya na zaune acikin bahon wankanta tana dan shan dumi kafin bayinta suzo su yi mata massage,bandaki ne babba wanda yake daukeda swimming pool dede gwargwado wanda Magajiyan ke wanka cikinta sewani lum lumshe idanu takeyi hankali kwance kaman ance tabude idanunta tayi arba da wata katuwar maciji daga can gefe tanata jujjuya kai,take jikin Magajiya yashiga bari kafin tasaki wani irin ihu batama san sanda tafito acikin swimming pool dinba tana ihun maciji!maciji bayinta dake daki suna hada turarrukan da ake mata wanka dashi suka shigo bandakin aguje dalewa jikin Hindatu Magajiya tayi tana ihu harda hawaye"wallahi maciji tashiga nuna musu da hannu"......
Karasawa daya daga cikinsu tayi cikeda tsoro amma itabataga komaiba,hango wata baiwar sukayi cikin bandakin tana haki cikin sauri suka karasa gurinta suna lafiya....
Cikeda rudani tace nashiga na dauko kasko acikin wancan dakin nafito kenan nahango maciji yanashirin kai ma Uwargijiya hari shine nayi kokarin jefa mishi kasko kawai senaga ya bace......
Magajiya dake jikin Hindatu daga ita sedan karamin rigar wanka ajikinta tace nidai ince naga maciji sannan cikin rudani tashiga kalle kallen gefenta tareda taba jikinta don ji takeyi kaman macijin ze bullo ajikinta tunda ance bacewa yayi,mehakan ke nufi?.....
Macijin daga inayake tayi maganar cikeda rudani,bayin kuwa ganin yanda Magajiya ta rude sunason yin dariya amma babu halinyi don suma sunsan sauran......
Hindatu ne tayi karfin halin cewa Uwargijiyata mukoma daki inyaso se akira azo ah duba ko Ina,cikeda tsoro Magajiya tace hakan za ayi nan suka fice tanemi kaya tasaka kafin akaje aka kira dogaraye,zuwa sukayi suka duba koina amma basu ga komai ba....
Cikeda tashin hankali da al ajabi tasamu gefen gado tazauna Allah yataimaketa babu baki ah dakin, Talatu ne takaraso kusa da ita tana Uwargijiyata kinfasa yin wankan ne?...
Wani irin harara takaima Talatun kafin tace wankan yaci ubanshi dan uwarki,Kai ah kasa Talatu tashiga bada hakuri Magajiya ko kallon inda take batayiba ita tunanin ta daya waye zaikawo mata macijin cikin daki don takowani fanni na daki babu tainda maciji ze iya shigowa, tabbas wani ne yashigo dashi,to wanene shine tunaninta tunda wanda take zargin ma baswa cikin masarautar tariga da ta koresu,cikin sauri tazabura ta tsaya zuciyarta nawani irin bugawa"badai wani na shirin illata ta bane acikin masarautar?".........
Talatu ne tace waye zeyi miki haka Uwargijiyata?....
Bansaniba Talatu, Talatu ne takuma cewa nagadai baki da makiyane,cikeda bacin rai Magajiya ta nuna kanta kafin tace ina Matar sarki zakice banida makiya tsabar kwakwalwar taki yanzu juyewa tayi komi?......
Yi hakuri Uwargijiyata cewar Talatu kafin tafice tabar dakin don talura ran Magajiyan ah bace yake sosai........

****

Tunda ta idar da sallar isha'i takwanta kan sallayar tana juye juye hartasamu bacci yadauketa sede abun mamaki mafarkin Almustapha tayi ansaka shi cikin wani kogo anata bugunshi yana ihu asking for help gashi kogon duhu ne dashi baka iya ganin komai,ah zabure tatashi tana furta innalillahi wainna ilaihir rajiun taba fuskarta tayi taji wani irin gumi na keto mata gabadaya jikinta yajike da gumi,dakyar ta iya tashi ta kunna wutan dakin agogon jikin bango takalla karfe uku da mintuna shida bandaki tashige tadauro alwala tadawo ta tada sallah tana kai ma Allah kukan ta har lokacin sallar asubahi tayi seda tayi sallar asuba sannan ta nade sallayar komawa bakin gado tayi tazauna tana tuno mafarkin datayi, what if it's true,what if mafarkinta gaskiya ne,what if Almustapha nashan wahala kamar yanda tagani jin hawaye tayi sunabin kuncinta she need to save him tunda babu mai taimakonshi,she need to protect him and take him far away from them may be yasamu sauki acikin al amurarshi wata zuciyar ne tace tayaya Asma'u,tayaya zaki taimakeshi bayan bakimasan inasuka kaishiba yayinda afili tafurta"why am i even afraid to lose you when you're not even mine Mr Taciturn?",wata zuciyar ne kuma tadinga cemata because you're in love Asma'u, because kinason shi and duk wanda kakeso bazaka tabason ganinshi cikin damuwaba dawannan tunanin ne zuciyar ta tadinga ingizata ga tadau mataki duban wall clock din tayi still karfe biyar da minti sha biyar,tashi tayi taleka window still gari da duhu kuma daman su Daddy insun fita masallaci baswa dawowa se gari ya waye in rana tadan fara fitowa bude kofan dakinta tayi bayan tadauki kudi acikin drawer dinta cikin sanda tafita har parlour duk wuta ah kashe kuma babu motsin kowa don daman Ummi keda girki probably tana bangaren Daddy,koda ta isa bakin gate din Allah yataimaketa Baba mai gadi bedawo daga masallaciba don haka tafice daga gidan tafiya tadungayi cikin sauri seda tayima unguwarsu nisa sannan ta tsaya tana dube dube ko Allah zaisa tasamu abun hawa dukda kuwa tasan bawai ancika samu bane ah irin wannan lokacin cigaba da tafiya tayi can Allah yataimaketa tasamu, tsayar dashi tayi sannan tafada masa unguwarsu Anty suwaiba har kofar gidan tayi mishi kwatance yakaita bashi kudi tayi yatafi bata tunanin zata iya zuwa gidansu Aisha ah yanzu tunda tace mata gidansu Amira nagefen nasu ta hannun dama kawai seta shiga kwakwansa kofar batareda tayi wani tunaniba Amira dayanzu ta idar da sallah taji ana buga kofa tataho tabude dukda kuwa tana mamakin wanene ze buga musu kofa da asubar Allahn nan.......
Arba tayi da fuskar Asma'u dukda kuwa gari begama haskeba tagane ta, Asma'u kece agidanmu yanzu...
Cikeda damuwa tace nazo gurin kine muje muyi saving Yayanki yanzu ne opportunity dinmu kafin gari yagama wayewa nibansan kan masarautar ba,cikeda mamaki Amira tace kaman yaya bangane ba taina kike tunanin zamu iya taimakonshi so kike ah kashemu Asma'u?......
Kiyi hakuri gaskiya zan iya Laying life dina for him but you bazan goya miki baya muje tareba inaganin sabida bakisan Magajiya bane shiyasa kike neman kisa rayuwarki acikin hadari.......
Cikeda damuwa Asma'u tariko hannun Amira tace in Sha Allah babu mai ganin mu kekam kizo muje jijjiga kai Amira tayi sannan tace"Asma'u bakisan mekike fada bane shiyasa,inbamu sa kan mu ah wahalaba muna iya kara sa Yaya Almustapha acikin wani wahalar gwanda kikoma gida kada anemeki,idon Asma'u yaciko da kwallah sannan tace wallahi bazan koma gidaba harsai kinzo munje abinda yasa nake binki sabida bansan kan gidan baneba bansan inda akasakashiba".....
Jiki ah sanyaye Amira badan ranta yasoba tace muje don ah ganinta in bare zata iya wannan jarumtakar ma Dan uwanta why not she,Ina zuwa barina fada ma Aisha tana bacci ah daki dan zare idanu Asma'u tayi kafin tace karkicemata muna tare please!kuma kema karkice mata ga inda zakije kawai kice mata yanzu zaki dawo kinji...
To kawai Amiran tace mata kafin tadauko hijab dinta tafito bayan tayima Aishan magana don yauma agidansu takwana......
Machine suka tara aka kaisu har masarautar basu samu wahalar shigaba kasancewar anfara taron biki sosai,itadai Amira secewa take itafa tsoro takeji bazata iyaba tana tsoron Magajiya....
Kwarin gwiwa Asma'u tadinga bata har suka fara doson gurin lokacin gari yayi haske sosai hango dogare uku sukayi sunzagaye gurin amma dukansu akwance suke sunata shatata bacci,cikeda hope Asma'u tace kinga bacci ma sukeyi dukansu babu mai noticing dinmu cikin sanda suka cigaba da tafiya har suka shiga gurin, Asma'u hawayene sukacigaba da bin kuncinta ganin gurin wazece mutum nazaune cikin gurinnan fisabilillahi aiko dabba ba abarshi yayi rayuwa cikin gurin nanba bare mutum,rushashen gurine koina very scattered gawasu ciyayi ah gurin da sun tsiro har sun bushe guridai kaman bola and somehow Amira ne tagoge nata kwallar kafin tace muyi sauri muje gurinshi kada ah kamamu gyada mata kai Asma'u tayi kafin suka shiga wani daki ah gurin daman gidan ko roof babu,can suka hangoshi zaune fuskarshi tayi jina jina jikinshi ko riga babu yajingina kanshi guri daya idanunshi suna rufe wanda zakayi tunanin bacci yakeyi amma ba baccin yakeyiba dagudu Amira tayi gurinshi tana kuka tareda fadawa jikinshi fama mai tabobin jikinshi tayi wanda yasashi yin saurin bude idanunshi amma se baiyi magana ba Asma'u data lura da hakan ne tana hawaye takaraso kusa da ita kafin tace Amira you're hurting him .....
Cikin sauri Amira tatashi daga jikinshi kafin tashiga yimishi sannu tanabin jikin nashi da kallo,sannu Yaya Almustapha.......
Asma'u kuwa zuwa tayi ta bayanshi tashiga since igiyar hannunshi tana we need to get out of here kafin sutashi........
Amiran ne tazo ta taimaka mata suka sunce hannunshi daya kumbura tsabar irin daurin da sukayimai juya baya tayi kafin tace help him yatashi Amira......
Lumshe idanunshi yayi ahankali don bayajin ze iya tashin, ahankali Amira tace katashi mutafi Yaya Almustapha,kallonta yayi kafin yace "kubar nan gurin banason suganku"....
Cikin sauri Asma'u tace"tare zamu tafi kuma bazasu ganmuba da yardar Allah".....
Batareda ya kalletaba yace"I'm not going anywhere".....
Sakan baki tayi tana kallonshi,meyake nufi duka hardwrk dinsu abanza zai tafi....
Zuwa tayi cikin sauri ta tsuguna gabanshi"don Allah katashi baka ganin irin illar dasukayi maka ne,kumafa basuda niyar barinka you don't know when they are going to release you",takarashe maganar tana goge kwallarta kallonta ya tsaya yanayi tareda mamakin ya akayi tasan halin dayake ciki kuma mai yakawota, batareda yasan yayi magana ba yace"what are the tears for,besides why do you care?",yanda yayi maganar seda yasa tsikar jikinta yatashi don ko Amira dake tsaye bataji meyace ba,kallon cikin idanunshi tayi batareda tasan ansar dazata bashiba dakyar ta iya dauke fuskarta kafin tace"I don't know and yanzu ba lokacin argument baneba please"..
Lumshe idanunshi yayi batareda yace musu komaiba,Amira ne tace nidaman nasani bazai taba bamu hadin kaiba he don't want to be a coward bakisan Yaya Almustapha baneba damuka samu yadubemuma muji dadi,kallon Amira Asma'u tayi batareda tasan abunyiba,can kuma tasamu guri tazauna gefenshi sannan cikin kuka tace "if he's trying to be stubborn then, I'm stubborn as well idan be tashiba babu inda zanje nima".....
Bude idanunshi yayi yadaurasu akanta saurin dauke kanta tayi don batason su sake hada idanu..........
Maida kanshi yayi kan Amira,kibarnan gurin yanzunnan and keda kika kawota kidauke ta kutafi....
Cikeda damuwa tace sorry Yaya Almustapha amma bazamu iya barinka cikin wannan condition dinba,wani harara daya dakamata ne yasata saurin juyawa tana cema Asma'u ta tashi su tafi suna cikin hakane suka ji anbude kofa bakaramin rudani suka shiga ba dukansu Amira tafara salati tana shikenan nasu yakare........

Almustapha dukda zafin dayakeji ajikinshi bazai iya bari agansu ba cikin sauri yatashi yakama hannayensu sukayi cikin wani daki dake dauke da katakai ah jubge,bayan katakan suka shiga suka buya kafin yamusu alama da hannunshi kan suyi shiru Asma'u dake gefenshi ne taga kafarshi na bleeding yataka kusa,hawaye ne suka zubo mata harara yadaka mata wanda yasata hadiye kukanta,sunajinsu sunata nemansu babu inda basu shigaba ah building din kafin daya daga cikinsu yace kilan baya cikin nan yagudu don haka suka fita cikin sauri don dubawa,seda suka tabbatar dogarayen sun fita kafin yace sufita su tafi make kafada Asma'u tayi wani harara ya sake daka mata wanda yasata saurin bin bayan Amiran batareda ta shiryaba.........
Komawa yayi yazauna ah inda suka daureshi din tareda jingine kanshi jikin karfen.....
Asma'u da Amira na fita basuyi nisaba sukayi kicibis dawani dogari,ihu yayi yana calling attention nasauran yan uwansa kafin yabisu abaya ah guje suma gudun sukeyi sosai sede basu da sa'a don wasu dogarayen gabansu suka sha,ihu Amira tashigayi dasauri daya daga cikin dogarayen ya maketa,Ina munafikin Yayan naki?....
Shiru tayi batareda tace komaiba,daya daga cikin dogarayen ne yace daga gurin suka fito duk yanda akayi sunbaro shi acan cikin sauri suka kama Asma'u da Amiran suka maidasu gidan,tunda Almustapha yaji anbude kofa yaji hankalinshi yatashi ga kukan su Amira dayakeji wurgi akayi dasu kafin wani ya make Almustaphan yana tsabar kai rayuwarka ah son Mata yakare sunema zasu zo taimakonka?.....
Dariya suka kwashe dashi dukansu yayinda daya daga cikinsu yace"yarasa masu tsirar dashine ko kamanta bashida kowa?".......
Kama Asma'u da Amira sukayi suka dauresu suna ku kuka kawo kanku sannan suka daure Almustaphan wasu daga cikinsu suka tafi sanar da Magajiya abunda yafaru.....

****

Munira ne tashiga dakin Asma'u don dubata taga wayam babu ita hakanan taleka bandakin ma babu kowa cikeda tashin hankali tashigo parlour tana Kiran Ummi, cikeda bacin rai Ummi tace miyene kike kirana kamar wanda zaki tashi sama, karasowa tayi tana haki tace Ummi Adda Asma'u bata daki,cikeda damuwa da maganar Ummi tace shine kikazo kinamin wannan kiran,kinduba bandaki batanan ne?......
Batanan wallahi Ummi,hararanta Ummi tayi kafin tace kizo kici abinci kada kuyi latti banason shirme ko in zata fita daman seta sanar dakene.....
Jiki ah sanyaye Munira tanemi guri tazauna tafara cin abinci ba ajima ba sega Munir da Ummi ta aikeshi yakarbo mata abu cikin agurin Mommy yashigo yanacewa Asiya tace yakawoma Asma'u littafinta data samu cikin Jakarta.....

Ummi ne tace itan bata canne?....
Batacan Ummi,atake se Ummi taji hankalinta yatashi dakanta taje duba Asma'un batanan ta aika bangarensu Mubaraq ma batanan,dafe kanta tayi cikeda damuwa tana tunanin ina Asma'u tashiga,bangaren Daddy tawuce don fada mishi amma koda tayi mishi bayani cewa yayi bayason damuwa Asma'u is getting out of hand and she'll surely come back ko Ina ma tajeta shikuma zai dauki mataki lokacin,jiki ah sanyaye Ummi tafita.....
*****...
Saukar dare yayi don wuraren karfe shadayan dare jirginsu yasauka ah Abuja straight yawuce yadauki motar sa yakamo hanyar Zaria dukda kuwa yasan irin risk din dake hanyar na yan fashi dadai sauransu......
Sanda ya iso masarautar tayi shiru duk kowa yakwanta bacci se guards wanda suma bakowane yasan da isowarsa ba, straight bangarenshi yawuce yasamu guri yazauna yana tunanin matakin dazai dauka don saving dan uwan nashi daga wannan masifar.........
Aikuwa garina wayewa yayi wanka yayi shirinshi cikin kayan sarauta,he knows what he's going to do is very risky sede bashida wani option ah yanzu daya wuce yayi hakan only then his Mother will stop all the accusations......
Straight bangaren Mai Martaba yawuce batareda ko breakfast yayiba,tundaga hanya da bayi suka ganshi suka shiga rige rigen zuwa fadama Magajiya donkuwa kowa burinta ta isarma Magajiya sakon isowar 'Danta don su samu kyauta.....
Aikuwa lantana ne tayi sa'ar zuwa sanar da Magajiya, murmushi Magajiya tayi dukda kuwa irin damuwar datake ciki na ganin maciji jiya ah dakinta seda taji zuciyarta tayi wasai atleast Sulaiman is back koba komai zecika mata daddaden burinta......
Kyautan zoben gwal akabama lantana tana godiya cikedajin dadi tafice yayinda Magajiya tafice don zuwa bangaren Mai Martaba taga 'Dan nata don bazata iya jiran har yazoba.....
Sulaiman kuwa tunda ya'isa bangaren Mai Martaba aka shiga yimashi iso ah parlour yasamu mahaifin nashi cikeda jin dadi sede bangaren Mai Martaban bahaka baneba........
Tsugunawa yayi yana mika gaisuwa kin amsawa Mai Martaban yayi sannan yace Baba na kasan irin tashin hankalin dakasani aciki kuwa?...
Cikeda damuwa Sulaiman yace kayi hakuri Abba,i wanted to surprise you shiyasa naki communication dakowa agida....
Bata rai Mai Martaba yayi yana"wane irin surprise ne haka dahar zaisa kasaka family dinka cikin damuwa,munata nemanka bamwa samunka.....
Murmushi yayi tareda karasawa kusada mahaifin nashi sannan yakama both kunnuwanshi...
"I'm really sorry Abba,bazan sakeba"....
Murmushi Abban yayi kafin yace nayafemaka tunda kadawo gida safe and sound...
Cire hannunshi yayi ah kunnuwanshi kafin yace"nagode Abbana"..
Gyada Kai Mai Martaba yayi kafin yace isowar dare kayi kenan?...
Eh Abba Sulaiman din yabashi ansa kafin Mai Martaba yace to Ina surprise din.....
Cikeda damuwa Sulaiman yace bansamu nazo dashi ba amma insha Allah yau zaka ga surprise din Abba zuwa anjima da dare, dukda kuwa bahaka nasoba tahowar dole ne takamani Abba......
Ganin yanda fuskar Sulaiman din tacanza lokaci guda yasa shi cewa,lafiya Sulaiman,meke damunka?..
Dago idanunshi dasukayi jazur yayi yace,Abba naji labarin kana hukunta wani ah dalilina shiyasa hankalina yatashi nadawo gida,naji labarin kana hukunta wani akan laifin dabashi yayiba bayan nine nayi laifin wannan karan hawayene suka zubo ah fuskar tashi,cikeda damuwa Mai Martaba yadubi Sulaiman din yace bangane inda ka dosaba......
Goge yar kwallarshi yayi kafin yace Abba inamagana ne akan Almustapha, yaron dakasa amishi hukunci ranar Monday sabida ankamashi da laifin yima bayi fyade ah masarautar nan, folding hannu Sulaiman yayi kafin yace believe me Abba he did nothing duk abunda yafaru ninayi bashiba bansan ya akayi akayi turning abun kanshi ba bansan miyasa bayin suka ce shineba,tunda yafara magana Mai Martaba kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login