Showing 102001 words to 105000 words out of 235422 words

Chapter 35 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3462

Jamila tayi har zata fice Ummi tace yauwa Jamila inkin gama tace Nonon keda Hindatu zaku raka Asma'u bangaren da bayi ke rayuwa dakuma inda suke aiki cewa tayi To Aunty barina gama semuje kafin tafice don aiwatar da abunda aka saka tadin........
Asma'u kuwa tana idar da sallar laasar Talatu tafado mata arai don haka tana gama addu'o'inta tafice zuwa gurinta........
Samunta tayi zaune kan sallaya taidar da sallah itama murmushi Asma'u tayi mata kafin tace "Ya zaman kadaici?"....
Murmushi kawai Talatu tayi kafin Asma'u tace kinci abincin rana kuwa?.....
Naci Gimbiya Talatun tayi maganar ahankali kafin tace dazu muna magana bamu karasa ba kika tafi.........
Eh wallahi Abba kenema na shiyasa kinga kuma babu dadi inbarshi yana jirana tunda ke ai kinanan zamu iya karasa maganar koyaushe ma shiyasa ma yanzu nazoni tunda babu abunda nikeyi", Asma'u takarashe maganar tana gyara zamanta Talatu ne tace hakane kuma.........
Dan kallonta Asma'u tayi kafin tace nibanason ace kintonamata asiri nafison itada kanta tatona makanta asiri takuma fadama duniya abunda tayi sannan in akwai shaida dazaki bayar sekema kibayar kinji..........
Cikeda damuwa Talatu tace...
"to kina tunanin zata tona makanta asirin ne Gimbiya, lallai bakisan waye Magajiya ba".......
Cikeda confidence Asma'u tace"time will tell,babu yanda za ayi ace kacuci mutane da dama haka sannan ace asirinka bazai taba tonuwa ba Talatu nidai taimako daya zakiyimin ayanzu"...........
To Gimbiya cewar Talatun kafin tayi shiru tana sauraren Asma'un cikin sanyi Asma'u tafara magana.....
"Nasan kinada masaniya akan duk wani al amura na tsakanin Mai Martaba da Mahaifiyar Yarima,nasan kinada masaniya akan sharri akayimata koba sharri akayimata ba",cikin sauri Talatu tace"sharri ne wallahi Gimbiya ni shaidace,wayene zai aibata wannan baiwar Allahn acikin gidan nan,wayene besan halinta nagariba sede in aki fadin gaskiyar kokuma sede in kowa yayi shiru sabida tsoron kada ya tsoma kansa ah halaka amma Sarauniya Khairiya mutumiyar kirkice,macece mai kamala dasanin darajar dan Adam......
Magajiya tayi makirci dayawa don ganin taraba Mai Martaba da matarnan amma takasa sabida tsananin shakuwar dasukayi da juna gakuma yarda dasukayi da juna don duk gulmar dazaka kaima matarnan akan mijinta kowa shaidana bazata taba yarda ba hakanan shima sunsan abunda kowannensu zai iya dawanda bazai iya ba shiyasa Magajiya dataga babu halin hadasu fada tahanyar makirci yasata komawa gun boka yataimaka mata harta aiwatar da niyarta.........
Asma'u da itanunta suka canza launi lokaci guda tace...
"ikon Allah me bokan yayi don Allah?"....
Murmushin takaici Talatu tayi sannan tace"Magajiya bata zuwa gurin bokanta da kowa Gimbiya shine gaskiyar magana koni danake kusanci da'ita sede inra kata injirata daga can nesa harta gama abunda zatayi mu dawo gida kuma dai yakai sau biyar yana bata laya wanda duk bansan namenene ba kuma gaskiya ba a lokaci daya yabayar ba guda uku nasan dai awajen gari narakata ta binne su bayan wata bishiyar kuka wanda nikaina bansaniba kozan iya ganeta yanzu kokuma ma bishiyar nanan ko batanan kingadai abun yajima gaskiya..........
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'un ke fada yayinda idanunta ke zubar da kwalla babu control sannan cikin kuka tace alokaci daya ta binne laya guda ukun ne?........
Jijjiga Mata kai Talatu tayi alamun a'a kafin tace..
"akwai ratan shekaruma ah tsakani sede inada tabbacin aguri daya ta binne".....
Kinga nafarkon daya bata tacemin ah dakin Mai Martaba zata binne shi dukda bansan tawani bangare bane tunda badani tajeba........
Se dayan kuma ah fada inda yake zama karkashin kujerar dayake zama.......
To sauran ne duk take sawa ah wajen gari din karkashin bishiyar kuka to matsalar yanzu bamusan wannene na sihirin da akayiwa Mai Martaba ba tunda shine babban matsalarmu yanzu Gimbiya......

Goge kwalla Asma'u tayi kafin tace"zezama na dakin nashi ne Talatu insha Allah zan bincika"....

Cikin sauri Talatu tace ta'ina zaki fara wannan garajen dakin da anyi masa gyara yafi ah irga yanzu terazo nema akasan kuma nasan cikin kasa ta binne.........
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi kafin tace"wannan bashine damuwana ba Talatu damuwana shine inga Ummi tasamu right dinta,Inga Ummi tafita daga zargin da aka jima anayimata tunda yanzu tafara samun lafiya with time zata fara fita and that's when people will start talking gwanda ayita ta kare,gwanda mahaifiyar Yarima sunanta yawanku ah idanun jama'a wanda hakan yasa akeyima Yarima kallon mutumin dabaida da'a,mutumin da baya kallon mutuncin mata,mutumin da bedauki darajarsu abakin komaiba bayan ni in my eyes he's the best person I've ever known sabida Mijina mutum ne da namijima bai isheshi kallo ba bare azo kan mace, I'm a witness Talatu I've seen it with my very own eyes nazauna da Almustapha fiye da wata yanzu amma ni haryau banga yayi abunda mutanen Zaria ke zarginshi ba haka Ummi she's the purest soul I've ever known,cikin kuka Asma'u tace tomiyasa za a cuci mutane irin wannan?.....
Laifin me sukayi,why will they be punished for someone's mistake please?......
Magana takeyi tana kuka mai tsuma zuciya se yau take ganin bata taba ganin cruel mutum like Magajiya ba and she'll pay for her sins for sure, azuciyarta tana raya laya har biyar?....
Kenan tayima wasu asiri bayan Ummi da Abba komi hakan ke nufi?,tokomadai miyene she'll try her very best taga ta karya wayannan sihirurrukan......
Talatu dake kallon Asma'un cikeda tausayawa don seyanzu tagane sun cuci mutane da dama wanda basumayi deserving ba tsabar selfishness irin nasu da rashin tunani jitayi Asma'un tace zansamu lokaci zaki rakani bayan garin don Allah muje mucire layoyin nan sabida bamusan har mutane nawa bane suka cutu sabida hakan na dakin Mai Martaba dana fada kuma ninasan yanda zanyi insha Allah.............
Girgiza mata kai Talatu tayi ahankali sannan tace basai kinjeba Gimbiya nizan je dakaina......
Cikin sauri Asma'u tace aa Talatu bazakije kekadai ba bazansaki kidauki wannan risk dinba murya ah karye Talatu tace wannan na daya daga cikin hukuncina Gimbiya kibarni inyi don Allah nayimiki alkawari bazan dawo cikin masarautar nanba harsai nacire wayannan layoyin ........

Gyada matakai kawai Asma'u din tayi donta lura bazata hakura ba kafin Talatun takuma cewa"sede zaki taimakamin wurin fita daga masarautar nan batareda kowa yasaniba sabida Magajiya tanada wayau sosai kuma tanada mutane masukai mata duk wasu labarai sannan kema kiyi ahankali bako inazakina fadar magana ba kamar yanda nafada miki tako ina tana da mutanenta".....
Gyada kai Asma'u tayi sannan tace"nagode sede fitar nakine bansan yazaayiba?"......
'koda asubama in dogaraye sunshiga sallah zamusan yanda za ayi",cewar Talatun.......
Godiya Asma'u tayi mata kafin tace barina koma cikin gida akwai inda zanje yanzu......
"To Gimbiya",tashi Asma'un tayi tafice jiki ah sanyaye........

Kicibis sukayi da jamila tafito daga kitchen hannunta rikeda robar dake dauke da Nono cikinta tagama tacewa xata saka ah fridge don yayi sanyi...........
Cewa tayi yauwa Gimbiya dama yanzu zanshiga gurin ki n?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 agama tace Nonon Aunty tace zamuyi maki rakiya nida Hindatu.........
Asma'u da idanunta suke jazur tsabar kukan datasha tayi faking smile sannan tace to Iya Jamila ba indauko mayafina semuje ko aikuwa hakan akayi bata jima ah dakin ba tadauko mayafinta tafito suma samunsu tayi ah parlour suna jiranta nan sukayi gaba seda sukayi tafiya mai nisa kafin suka iso kitchen din masarautar tundaga bakin kofa Hindatu tace barimu fara daganan Gimbiya......
Gyada musu kai kawai tayi kafin suka kutsa suka shiga kitchen din......



Vote
Comment
Share

[3/23, 5:48 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

*Written by Zeeneert*


*Zeeneert@wattpad*

*This page is for you ABASIYA SARKI. just know that Zeeneert bata manta dake bad'I love you Sis, Allah yabar kauna infact Almustapha yace afada miki Zaki zama jakadiya lokacin mulkin shi*

*NOT EDITED*

*Page 41*...



Babban guri ne wanda ke dauke da dumbin bayi da kowanne suna da fannin aikinsu wasu suna wanke wanke,wasu yankan albasa wasu gyaran kayan miya,wasu tankade gari wasu su kuma suna fannin girki............

Binsu take da kallo abun tausayi don abunda ta lura dashi kusan gabadayansu agajiye suke ga duk kayan jikinsu sun kode sunyi dikin dikin dashi mostly jitayi Hindatu nacewa"Gimbiya ga Jakadiya itake kula da duk wani harkokina abinci"......
Murmushi Asma'u tayi tareda kallon dattijuwar da Hindatu takira da Jakadiya kafin tagaida ta gaida ta Itama jadiyar gaisheda Asma'un tayi cikeda ladabi kafin takara da sannun ki dazuwa Gimbiya......

Yauwa sannu jakadiya ya ayyuka?....
Alhamdulillah tabata ansa kafin tace zamu zaga dake ne kiga kitchen din?...
Gyada kai tayi ahankali kafin suka fara tafiya tana binsu yawanci guraren yanmatan daketa aiki suka kaita suna nuna mata ayyukan dasukeyi kafin suka karasa wurin rabon abincin bayi donkuwa yanzuma aka sauke abincin daren......
Layin kwanuka ne ah ajiye sunfi ah irga yayinda masu raba abincin inkaga yanda suke difana shi kaman wanda za abaiba kaji suci ko kulwa don inzata iya rantsewa duk abincin da ake sawa mutum befi ya'iya loma ukuba inyayi tsawoma to loma biyar cikeda mamaki tace wannan ne abincin da ake basu?......

Gyada Kai Jakadiya tayi sannan tace sau uku ah rana ake basu ai Gimbiya.........
Shiru kawae tayi batace komai ba kafin jakadiyan tarakata bangaren abincin manyan masarautar inda taga bama mutane dayawa ke girkataba gakuma abinci da akeyi kala kala agurin haka tana ganin wayanda aka fara zubawa ma ancika kuloli makil bakaman na bayin data gani ana difana musuba seda jakadiya tagama mata bayani tareda zagata koina kafin tarakasu bakin kofa tadawo kitchen din tafiya suka cigaba dayi don zasu kaita wani bangaren kuma itadai cike take da curiosity don haka takasa shiru tabudi baki tace"nikam Iya Hindatu iya Quantityn abincin da ake baiwa bayi kenan sau biyu ah rana?......
Gyada kai Hindatu tayi kafin tace"eh Gimbiya wani ahakan ma bazai samuba don inbaka kawo kwanonka dawuri ba aka gama rabo babukai babu samu kwata kwata sede ka kwana da yunwa don ba kowani bangaren da kake aiki bane za abaka abinci kaci don baka isama kace zakaci abincin da manyan masarauta keci ba cewama akeyi raini ne.........
Cikeda damuwa Asma'u tace"to ba akawo kayan abincin ishasshene komi?".......
Hummm shine abunda Jamila tace kafin tadubi Asma'u tana"Gimbiya abun masarautar nan se ahankali nibansan ranar da bayi zasu samu yancin kansu ba",Yar dariya Hindatu tayi kafin tace"kilan se randa Magajiya tabar duniya".......
Mehakan ke nufi Iya Hindatu dasa hannunta ah rashin bada abinci ishasshe komi kikeson fadi?....
Aikomai ma dasa hannunta Gimbiya, Magajiya babba ce ah masarautar nan da babu wanda yakejadaita duk abunda tace ayi shi akeyi ko anaso ko ba aso, tsarin abincin dakikaga anabama bayima ita ta gindaya shi don kayan abinci ishasshe anakawo amma setace baza'a dafa iya yawan dazai isaba kadan za adafa sabida in bayi suka ci abinci dayawa bazasu iya aiki mekyau ba yandama naji anacewa raba sauran kudin sukeyi da wanda keda dawainiyar kawo kayan abinci haka na sutura ma Gimbiya ance ana raba mana kaya set bibbiyu bayan shekara shekara Kuma ana bada kudi amma baswa bamu sesucinye kudin ah tsakaninsu wani sa'in bayan shekara uku abamu inmunyi sa'a kenan inko bamuyiba yana iyakaiwa tsawo shekaru biyar ma ba abamu wasu kayan ba shiyasa inkika lura zakiga duk kayan bayi wasu sun barke wasu sunyi baci wasu kuma kodewa yayi.........
Shiru Asma'u tayi tana Al ajabin wannan wulakancin wato Magajiya bata tsaya akan mutanen marasautar bama harda bayi takeyi ma mugunta lallai she's so cruel and tasamu dama dayawa ah masarautar nan donkuwa talura anbata power mai karfi jin kaman ana dukan mutum d bulala ne yasata dagowa cikin sauri daga tunanin datakeyi........
Fili ne gurin babba sede an siminte koina da cement yayinda gurin ke dauke da taps ta bangare bangare gakuma thanks takoina wanda inada tabbacin suke supplying ruwa to d tap bayan anyi pumping ruwa gakuma kayan wanki zube takowani direction bayi se zuba wanki sukeyi..........
Idanunta ne suka sauka kan wanda taji anata duka dan sakannin da suka wuce jitayi yarinyar na kuka helplessely tana"Yaya Hafsatu banida lafiya wallahi hajijiya nikeji bazan iya wankinnan ba"........
Wani irin katon bulala wanda aka Kira da hafsatun takuma yarfa mata tana zare idanu"don ubanki kitashi bawani lafiyar ki kallo zakizo kina karya tosekin yi wankinnan kokin ki kokin so"........
Hindatu ne tadubi Asma'u tana"Gimbiya nanne fannin da bayi ke wanke kayayyakin manyan masarauta kusan koyaushe kikazo wanki akeyi harta tsakiyan dare sabida kowa da lokacin dayakezuwa yayi wasu sanda yan uwansu keyi su suna wani aikin haka sauranma kuma indai kazonan dole kayi abunda yakawoka babu zama batun hutawa Kinga wancan Hafsatun?.....
Gyada Kai Asma'u tayi ahankali Hindatu tace....

"itace shugabansu,inmutum yayi kuskure itake hukuntasu kafin akai gaban Magajiya".......

Cikin sauri Asma'u tace to Amma yarinyar can da alama ba karya takeyiba miyasa za ayita bugunta?....
Murmushin takaici Jamila tayi kafin tace"Babu wanda yake yarda in bawa yace baida lafiya daukan hakan sukeyi amatsayin karya dakuma neman hanyar dojema aiki shiyasa bayi da dama suke rasa rayukansu sabida wannan muguntan,babu wanda yadamu da al amarinsu barekuma lafiyar su".......
Mai Martaba fa?, Asma'u tayi tambayar cikeda curiosity........
Kallonta Jamila tayi kafin tace"baisan komai dake faruwa ba don daga bangarenshi yana iya kokarinshi ae yadankama Magajiya kula da bangaren nan shiyasa kikaga hakan na faruwa shikuma duk ah tunaninshi tana akwatar da abunda yadace ko ankira mutum bada shaidama bazai iya budan baki yafadi gaskiya ba sabida tsoron abunda zai biyo ba..........

Hmmm shine abunda Asma'u tace kafin tayi hanyar inda taga yarinyar da tace bata lafiya take tana tsugune gaban kayan tacigaba da wankin kaman yanda akasakata tayi amma se hawaye takeyi ga jikinta na wani irin karkarwa don kallo daya zakamata kagane batada ishashen lafiya..............

Ahankali Asma'u ta dan duka takamo hannunta tareda cewa tashi kinji......
Tashi baiwar tayi jikina karkarwa ga jikinta wani irin zafi kaman ruwan zafi kallon Asma'un tayi hawaye nabin kuncinta tareda cewa"wallahi banida lafiya"....
Bakaramin tausayin ta Asma'u tajiba ahankali ta janyota zuwa jikinta tana dan taba temperature din jikinta"sannu kinji?"......
Duban bangaren dasu Jamila suke tayi sannan tace ta inane clinic din masarautar yake cikeda girmamawa Hindatu da Jamila sukazo suka rike yarinyar suna......
"zamu kaita Gimbiya basai munje dukan mu ba"......
Kallonsu tayi sannan tace aa muje dai duka inyaso makwarasa daga baya haka kuwa akayi sukakai yarinyar clinic akayimata treatment tareda bata drugs kafin sukace gobe tadawo takarbi maganin again taimaka mata sukayi harzuwa bangaren bayi tareda Asma'u din dakuna da dama suka wuce amma babu katifa ko daya abun yabama Asma'u mamaki amma sebatayi maganaba harsuka Isa dakin da yarinyar take zama karema dakin kallo Asma'u tashigayi kafin tace anan kuke kwana ne?..............
Gyadamata kai yarinyar tayi kafin Asma'u tace to ai babu katifa badai kasa kuke kwanciya ba,sake jijjiga matakai yarinyar tayi alamar eh kafin Hindatu ta taimaka ma yarinyar takwanta kan wani tsumma datagani ah shimfide sannan tace Allah yakara sauki dukwanda yaxo yaganki kwance kice Gimbiya Asma'u ne tace kizo ki kwanta bakida lafiya kinji?.....

Cewa tayi to kafin tasake yima Asma'u din godiya kafin suka fice kasa boye mamakinta tayi tadubi su Jamila sannan tace"wai nikam baswa kwana kan katifa ne ko ince Ina katifun suke?".........
Hmmmm Gimbiya basudashi don tunwanda aka bayar wajen shekaru ashirin dasuka wuce ba asake bada katifa ba kuma dama can katifun bawani karfine dasuba ahaka harsuka lallace toma wai Gimbiya inama sukesamu suyi wani baccin kirki koyaushe bayin nan cikin aiki suke kaman jakai haka babu ilimin addini don bazan hada da boko ba tunda wannan bezame musu doleba anbude islamiya sabida su amma tunda jimawa suka daina zuwa sabida basuma da wannan lokacin sunriga sun sadaukar da rayuwarsu akan bauta ne kawai mudakike gani muke taredaku mune kadai kesamun sauki..
Hindatu tadan numfasa tana inama zanga ranar da Yan uwana bayi zasu samu yancin kansu,inama zanga ranar da za ace suma zasuyi rayuwa kaman Yan uwansu Mata har suyi sure su hayayyafa ta hanyar sunna na ma aiki ba ta hanyar zina ba....
Asma'u ne tace bangane ba Hindatu kimin bayani kina nufin bayin baswa aurene?......
Sunayi ada Gimbiya tun zamanin sarki Sulaiman dama kuma farkon da sarki Abdulrahman yahau mulki amma daga bayannan ba ayi gaskiya sabida Magajiya takan nuna rashin goyon bayanta kuma takan muzguna ma dukwanda sukazo mata da maganar sunason junansu Kuma daman ta hannunta akebi itane yakamata tana kaiwa sarki labari dadai sauransu shiyasa ma yanzu lalata yafara yawa don kuwa mata bayi sukanyi hulda da dogaraye ah boye batareda ansaniba.........

Cikeda damuwa Asma'u takefa furta innalillahi wainna ilaihir rajiun don abun sunyi yawa,so many things are not in control ahaka harsuka iso bangarensu batareda ta iya cewa komai ba because she's really out of words batamasan mezata yiba tasan dai Ummi tace taje ta ga ya suke rayuwa and tabbas taje tagani kuma taji tausayinsu hakanan taga kuma suna bukatan taimako sede how will she help them?....
Ta'ina ma zatafara taimakonsu,ita awa,nawama take she's just too young to think of anything that can help to meyesa Ummi zatace taje taga rayuwarsu tabbas there must be a reason behind it amma koma miyene zataje tasamu Ummin su tattauna bayan sallar isha don ko yanzu dasuka dawo anata kiraye kirayen sallar maghrib don haka tawuce dakinta direct son yin sallah............

**&**
Bayan taidar da sallar Isha tashiga tayi wanka kafin tasauya kayanta zuwa kayan bacci hijab dinta tasaka se wani asirtaccen kamshi takeyi ita kadai kafin tawuce dakin Ummi dukda kuwa batada walwala don abubuwan data gani yaudin sungama tada mata hankali tareda sata tunani kala kala samun Ummi tayi zaune tana kan gado tana dama fura hankali kwance yayinda kyakyawar fuskarta ke daukeda annuri wanda yasa Asma'un ma smilling Allah yagani matar kyau takeyi mata bana Wasa ba gawani haiba da kwarjini datake dashi wanda tanada tabbacin hakan yasamu asali ne daga addininta dakuma hali nagari irin nata karasawa tayi cikin dakin tana"Ummi Ina wuni".....
Aaa Habibty kene nadaukama kin kwantafa har inacewa wa zaikaima maigidan naki furar tasa Ummi tayi maganar still fuskar ta dauke da murmushi,cikeda kunya Asma'u tace kawo intayaki damawa Ummi........

Murmushi Ummi tayi sannan tace kibarshi kawae Dear inason inyi masa yaune amma I promise I'll teach you yanda ake dama mishi fura nangaba kezakina mishi tunda yayi mata nima na huta.......
Murmushi Asma'u tayi kafin tasamu guri tazauna Ummi na dama fura at thesame time tana examining fuskar Asma'un kafin tace...
"Habibty kunje side din Bayin ne?".....
gyada ma Ummin kai tayi kafin tace eh Ummi munje.....
Murmushi Ummi tayi kafin tace"and what's your decision,do you still want to quit?".....
Take idanun Asma'u suka ciko da kwalla don hakanan abubuwan data gani yaudin sukeyi mata gezau ah idanuwanta.........
Cikin muryar tausayi tace"Ummi dukyanda kikace inyi znyi don nikam narasa wani mataki zan daukaba but I definitely want help them,sede tayaya Ummi,who am I to do that?"......
Ummi ajiye bowl din fura da Nono tayi gefe sannan tadubi Asma'u dakyau cikin sigar lallashi tace zo Habibty......
Jiki ah sanyaye takarasa gefen Ummin tazauna riko hannunta Ummi tayi sannan tace"Baki yarda da kanki bane Daughter?"....
Jijjiga kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login