Showing 75001 words to 78000 words out of 235422 words

Chapter 26 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3481

sannan yace
"ke atunanin ki kinkyauta?"......

Cikeda tsiwa tace"danayi meye kuma Yarima".....
riko hannunta yayi batareda yadamu da mutanen dake kallon su ba yace"fisabilillahi Zaliha tunda aka kawo Asma'u ko inda take baki nema ba bare kiso kuyi zumunci yanzu ke aganin ki yadace"...
Wabce hannunta tayi cikin sauri"aa Mallam dakata kada ma kafara,nida ita waye babba naji dai ance sa'ar su Afiya ne ahakan Kuma kake expecting dina ni innemi inda take......
Kallonta yayi da mamaki "Zaliha you're too much wallahi kuma ma inkina takama da girma ne to Itama ai mijinta ya girmeki kuma Yayana ne so you've to give her that respect"...
Kai tsaye tace"I can't inbazata iya zuwa inda nakeba kowa yayi takanshi is not as if dole semunyi zumunci tunda daman bada ita aka kawoni ba besides I don't like her tunda Matar Yayanka ce",tana karashe maganar tajuya tatafi tabarshi tsaye sororo yana binta da kallo besan yazaiyi da Zaliha tagane cewa he's not meant to be the king ba yakamata tayi putting this at the back of her mind sede takasa shikuma bayason suna samun matsala.............

Karasawa yayi bangaren su Almustapha din dakin Ummi yafara zuwa yaduba jikinta sannan yadawo parlour yazauna don yanzu ba kasafai yake shiga dakin Almustapha dinba tunda he's married yana nan zaune harya fito cikin shirin shi na kananan kaya don yau babu inda zaije yasama ranshi ko fada bazai leka ba.........
Murmushi Sulaiman yasakar mai sannan yagaida shi"Ina kwana Yaya?".....
Lafiya Lau and you?....
Alhamdulillah,samun guri Almustaphan yayi yazauna tareda dan lumshe idanunshi tunda ta doso hanyar parlourn yakejin daddadan kamshin turarenta harta karaso sa bayin tayi suka ajiye abincin sannan tagaisa da Sulaiman din..........
Amsawa yayi fuskarshi cikeda annuri yana"Uwargidana na fushi wai kinki zuwa ayi zumunci"....
Murmushi kawai Asma'u tayi "tayi hakuri zanzoni in Allah ya yarda",cewar Asma'u dukda kuwa tana mamakin wacece haka,ae itane bakuwa kamata yayi ita tafara zuwa gurinta bawae tace ita taje ba sede koma miye ne she'll go for the sake of Sulaiman.......
Haka takoma dakin don barinsu suyi breakfast donta lura kozata yi yaya Almustapha bazai taba cin abinci ah gabanta ba kam.............

Seda suka gama cin abincin sannan Sulaiman yace"result dinku is out Yaya"....
Yanda Sulaiman yayi masa maganar ah bazata seda yaji kirjinshi ya buga kafin dakyar ya iya cewa Allah yasa muji alkhairi........
Amin cewar Sulaiman din sannan yace.....

"your ID number zanje induba maka don nasan ba lallai kasamu fita ba"......

Bashi Almustapha yayi ganin yanda jikinshi yayi sanyi yasa Sulaiman din dan tapping shoulder dinshi sannan yace calm down ynzu zan duba maka so far as you wrote the exams nasan you'll surely pass dayardar Allah........
Allah yasa cewar Almustapha din sannan yatashi yakoma daki yakwanta gabadaya jiyayi duniyar ta mishi zafi bayason ace abunda yake faruwa dashi every year yafaru dashi yanzuma........
Daukar wayarshi yayi yakunna data abunda yakwana biyu beyi ba kenan nan yashiga WhatsApp kozai samu wani information daga group massages ne suka shiga shigo mishi ganin number dinta yayi asama alamar yanzu taturo massage din..........

Mamaki ne yakama na massage din meyene zata turo mishi yanzu bayan bata dade da barin gurin shiba bude wa yayi picture ne yagani dauke da massage akasa wanda yadauki hankalinshi lokaci guda........
Karantawa yashiga yi batareda yyi viewing picture dinba dukda kuwa yayi downloading akready.....

_You have not only created a niche for yourself at your young age...._

_But you have also inspired many Young people to dream big,_

_Your achievement will surely be a motivation for all the young people around you So, super congrats "My Doctor" I am so very proud of you_.....

Yakaranta massage din yafi sau hudu kafin ahankali yabude result din clear pass yagani,sosa idanunshi yayi because he really can't believe it amma still thesame thing yake gani sake duba ID number da sunanshi yayi shima nashi ne lumshe idanunshi yayi tareda fadin"Alhamdulillah fa, Alhamdulillah, Alhamdulillah fa", Allah ne kadai yasan irin farin cikin dayake ciki........
Dakyar ya iya sake duban wayan seya tsinci kanshi dasake karanta sakon nata besan sanda murmushi yasubuce maiba tareda yi mata reply azuciyarshi Yana"she's so cunning,tama rainashi shinema yaro wato".....
Yaga massage dinta na kwanaki seyayi ignoring tunda ae tasan shine yanzun ba Sulaiman din bane ba ...

" _waya yaron?_"

Shine sakon daya tura mata tana zaune ah parlour itadai Sulaiman taga massage din nashi dan bata rai tayi tareda wurgar da wayar wato ma of all this write-up that's what she'll get in return"Arrogant Dr taciturn",shine abunda tafurta tana bata rai.......
Sulaiman ne yadubeta jin kaman tayi magana"lafiya?".....

Bakomai tayi maganar rai bace,dariya yayi sannan yace "kukuma naku salon soyayyar kenan?".....
Sarai taji meyace amma setayi kaman batajiba"uhmm mekace?".........

Yasan taji don haka shima seya kawar da maganar tahanyar cewa "yaga massage dinne ko inje infada masa kada yayita tada hankalinsa?".....

Yagani mana aishiyasa naketa bata rai,waifa ma ko godiya baiyimin ba takarashe maganar tana mikama sulaiman wayar yaga reply din Almustaphan dariya yayi daganin massage din sannan yace"kunfi kusa wallahi nikinga tafiyata zanje infada ma su Dad"......
Seka dawo tabashi amsa tareda tashi tana kunkuni ita kadai harta fice zuwa bangaren Mom.........

*Around 9:30pm*...

Seda tagama wankanta tsaf tayi shirinta cikin kayan bacci riga da wando sannan tafeshe jikinta da turare harzata kwanta setaga yakamata tayima Almustapha maganar karatu datayi niyar yi kan yanayimusu atleast it'll help him retain his memory Kuma shima yasamu lada tunda tanada sani inma yayi mistake seta gyara mishi dawannan tunanin tasaka soft flat shoe dinta datake yawo dashi cikin gida tafice........
Straight dakinshi tawuce knocking tayi tayi be amasaba dan tabe baki tayi "Yana ma ji ze iya kin ansa mini",takarashe maganar tareda murda handle din kofar tayi Allah yataimaketa abude kofar take shiga dakin tayi yayinda lallausar kamshin dakinshi yaziyarci hancinta ga sanyin AC ya mamaye koina karema dakin kallo tashigayi ganin baya ciki tarasa Almustapha wani irin namiji ne haka,sabida itadai bata taba ganin namiji mai tsaftarsa ba gashi kominshi anutse yakeyinshi tana cikin wannan tunanin ne taji yabude kofar bandakin don haka tamaida direction dinta gareshi wani irin kara tasaki tareda juyawa lokaci guda zuciyarta na racing shima saurin juyawa yayi sanda yaganta gabanshi sabida tunda yake betaba tsayuwa gaban wata hakaba hartasamu taga jikinshi..........
Bangaren Asma'u ma kasa taka kafanta tayi itadai tana sankare guri guda yayinda yanda taga kyakyawan jikinshi keyi mata yawo ah kwanya gawasu kwantaccen gashi dake shimfide ah kirjinshi wanda suka kasa vanishing ah idanunta......
Sa hannu tayi tarufe fuskarta cikin sauri don gani take kaman zegane abubuwan dake yawo ah kwanyarta da kwakwalwar ta jitake kaman kasa ta tsage ta shige ciki.........
Jin bata bude kofar dakin ba seya juyo kawai gani yayi tana tsaye agurin still jijjiga kai yayi cikeda mamaki sannan ya tabe bakinshi yayi wucewarshi jikin wordrop dinshi don yanada tabbacin bazata taba juyowa ba ahaka harya gama shirin shi,harya hau gado zekwanta seya tuna bai kashe wutan dakin ba don haka yaje yakashe yadawo yayi kwanciyar sa tareda lullubuwa cikin blanket batareda yadamu da existence dinta agurin ba..........

Tanajin sanda yakashe wutan setayi saurin cire hannunta ah fuskarta amma babu abunda take gani se duhu ah dakin don har bedside lamp dinma yakashe daya koma.........
Kici kicin neman kofa tashigayi kuma don tasamu tafita daga dakin amma takasa samun direction dukda kuwa tana mamakin bawai nesa tayi da kofar ba to ya akayi haka batayi giving up ba haka tacigaba da lalume amma setaji ta bugu da wani abu da karfi Yar kara tasaki don ba karamin buguwa tayiba akafarta tareda zamewa tazauna agurin tana taba kafar sekuma tasaki kuka.......
Yana jinta amma seyaki kulata dukda bason jin kukan nata yakeyiba......
Cikin kuka tace...
"Yaya Almustapha bakaji naji ciwo bane?",yanda tayi maganar harcikin kwakwalwar shi yaji sabida yanda tayi maganar ashagwaba amma seyayi kaman baijiba.......

Sautin kukan takara"naji ciwo fa! gashi gurin duk duhu nikam kazo ka kunna min wuta to......
Yar dariya yayi kasa kasa yanda bazata jiba jin yanda take maganan,kara marairaice murya tayi"don Allah mana nasan kanajina wallahi tayi maganar murya akarye"........

Gyara kwanciyanshi yayi yanadan smilling dukda tabashi tausayi aranshi yana"yarinya dani kikewasa",sannan afili yace..
"meya kawoki dakina?".....
Cikin sauri tace...
"Allah nazo in maka magana ne kanamana karin karatu da asuba,amma nafasa ma nidai ka kunna min wuta intafi dakina".......

"Bakince ni yaro bane kinemi Babba yataimake ki,har inmiki magana kikimin reply?"yakarashe maganar tareda lumshe idanun shi.....
Turo baki tayi kaman yana kallonta"Ina kaine kakiyimin godiya".....

Shiru yayi kaman baijitaba itakuwa tacigaba da sharara kuka jin ta dameshine yace in a serious tune"Allah kika sake baremin baki I'll throw out,I want to sleep for goodness sake besides nibankawo ki dakina ba so,find your way out"......
Tanajin wani sabon kukan nashirin zuwa tayi saurin sa hannu tarufe bakinta tasan Almustapha ze iya abunda yafada din haka tadinga kukan zuci har bacci yayi awun gaba da'ita akan tiles ....
Seda yadaina jin kukan nata sannan yasamu bacci yadaukeshi sede da mamakinshi yau dede time din datasaba tashin shi yatashi shima batareda yaji kirantaba..........

Da hasken wayarshi ya yi using don mugunta yayo alwala yazo ya tada sallah bashi yatashi ba seda yaji ana kiran sallar asuba kunna wutan dakin yayi tareda kallon direction din da take kwance gabadaya ta dukun kune guri daya kamar marainiya ga baccin wahala datakeyi samun kanshi yayi da daukan pillow da blanket yakarasa gabanta tsugunawa yayi yadan daga kanta yasaka pillow din tareda rufa mata blanket din sannan yatashi cikin sauri yafice jin ana shirin shiga sallah........

Koda yadawo baccinta take peacefully wannan karan lallai ma yarinyar nan shine abunda yafada sannan yakarasa gaban gadonshi yadauko glass cup da ruwa aciki yadawo gabanta diban kadan yayi yadan yayyafa mata motsi tayi kadan ganin tana shirin komawa baccin ne yasashi sake yayyafa mata ruwan wannan karan cikin sauri tatashi tazauna komawa yayi ya ajiye cup din sannan yafice daga dakin zuwa dakin Ummi.....
Binshi tayi da kallo harya fita daga dakin sannan tamaida hankalinta kan wall clock din subhanallahi shine abunda ta furta ganin har 5:40am yayi cikin sauri ta yaye bargon dukda tana mamakin waye ya lulluba mata jinda tayi kafarta tayi wani irin zafi ne yasata saurin komawa tazauna sega hawaye kuma zululu,dakyar ta'iya daurewa tamike tana"itakam Allah yahadata da mutum"........
Dakinta tawuce tayi sallah abunta sannan takoma takwanta don yaukam bacci be isheta ba koda su Hindatu basu ganta ah kitchen ba sunsan kilan bata tashi baneba don haka sukayi girkin dakansu tunda tayi time table na abinci already daman..........

Su Afiya ma anfara tashi dawuri don kuwa sundauki shawarar Asma'u din sannan tun jiya sukayima Sulaiman maganar Islamiyar su yace in sha inyasamu time zekaisu ayi masu interview awata islamiya dake kusa dasu...........

****
Yau kin gyaramishi daki tayi kwata kwata sabida fushin da takeyi dashi har azahar hakan yasa shima yagyara dakanshi batareda yaneme taba tunda koda dinma bashi yasakata ba ita tasaka kanta daman......
Sosai Dad da Abba sukayi mishi murna na kyaun da result dinshi yayi sannan Abba yac he should expect his gift soon........
Ranar wuni yayi cikin farin ciki don kowa tayashi murna yakeyi cikin yan uwan nasa dakuma iyaye baki daya har hawaye yayi dayaje gaban Ummi inama inama,inama zata iya magana he know for sure she'll be more than happy to hear this news, she'll be the first person to hug him and congratulate him...........

Washegari da asuba Asma'u tasha mamaki dataga Almustapha nayima su Afiya karin karatu sede taji dadi bakadan ba aranta dukda tana mamakin ya akayi ya yarda dabadan fushi take dashiba babu abunda zai hanata jonawa sede dukda haka batabar gurin ba don samun wani spot tayi tazauna tanajin yanda yake karatu cikin kira'arshi me dan karen dadi har yagama sannan ta lallaba tagudu don kada ma yaganta yafada mata ba dadi.........

******

Tana sanye cikin wata atamfa hadaddiya data amshi jikinta se katuwar gyale data yafa hnyar bangaren Zaliha tayi don zuwa sugaisa tunda tace setaje mata sannan ita tazo tundaga nesa take hango yanda bayi suka taru guri daya da alama wani abu ke faruwa suka tsaya kallo..........
Duban bayinta biyu dake binta abaya tayi"hafsat meyake faruwa acan?"........

Sunkuyar dakai yarinyar da aka kirada hafsat tayi sannan tace"bansaniba wallahi Gimbiya amma barina duba",cikin sauri Asma'u tace no need zanje dakaina takarashe maganar tareda yin gaba wurin suka Isa inda bayin suka shiga bata hanya harta Isa ta gaba gaba.....

Magajiya ce ke dungurin Talatu tana"don ubanki banace kifita harkataba,ko anfada miki ana dolene?".......

"Nace miki banason kara cudanya dake miyasa bazaki gane hakan ba, you're a betrayer kin cuceni Kuma kinason in karbe ki don ubanki, Magajiya takarashe maganar tareda kaiwa Talatu Mari wannan Karan"innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'u ke furtawa don tayi mamakin yanda matar ke bugun mace da tayi kusan sa'arta wannan wane irin wulakanci ne haka besides if she could remember kaman itace ke tareda Magajiyar lokacin da bata da lafiya she was very worried for her and now itakuma tahaka zatayi repaying dinta tana wannan tunanin ne taji Talatun na"Uwargijiyata wallahi babu abunda nayi akomai ina bayanki,bantaba cutarki ba hakanan bantaba yimaki karyaba kiyarda dani please takarashe maganar tana hawaye tareda foldung hannunta alamun roko".
Takaici ne ya ishi Magajiya azuciye tayi ball da Talatun tana"Zan hallaka ki inbaki bace min da ganiba",still Talatu bata daddara ba ball da'ita Magajiya tashigayi tana huci cikin sauri Asma'u ta'isa wurin tareda shiga gaban Magajiyar da har take shirin ball da ita Itama cikin kuka tace"kibari don Allah,haba sekace wanda kika samu dabba, she's busy pleading with you amma ko ajikin ki sekace wanda bakida zuciyar imani Asma'u takarashe maganar tana hawaye...........

Magajiya ta saki baki tana kallonta donkuwa waye ya isa yayi interrupting dinta intana abu lallai Matar Almustapha taga gadon baccinta,lallai taganta amatsayin marar lafiya ne ba a matsayin magajiyarta ba, lallai batasan wacece itaba don taga tayi musu shiru tunda tazo gidan batace komaiba azuciye tace "who do you think you're dazaki shiga gabana inama slave dina hukunci?"...
Cikin kuka Asma'u tace"kiyi hakuri don Allah kibarta hakanan,she can be your slave but she's also a human being like you bekamata kina treating dinta kamar dabba ba".....
Wani irin kukan zaki Magajiya tayi kafin tadaga hannu daniyar kaima Asma'u mari cikin sauri taji anriko hannunta daga ita har Asma'un juyawa sukayi don ganin wanene wannan cikin husky voice dinshi yace...
"Don't you dare touch my wife!"....
Wani irin huci Magajiya tayi tana shirin kwatar hannunta amma yaki saki wani irin kallo yakeyimata dayasata rikicewa lokaci guda Asma'u kuwa dasauri tayi kan Talatu tana riko hannunta"sannu baiwar Allah"....


*sorry for the typing errors nayi editing yagoge and I can't keep you guys waiting anymore*

Vote
Comment
Share?
[3/23, 5:41 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


*Written by Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad..

*Page 32*......



Dukda kukan da Talatu takeyi behanata dagowa don ganin wanene yazo ceton ta ba arba tayi da kyakyawar fuskar Asma'u mika mata hannu Asma'un tayi tana"kitashi kinji,sannu"......

Batasan dalili ba seta kasa rejecting offer din dukda kuwa yanda take tsoron Magajiya din haka Asma'u takama hannunta sukayi bangarensu............

Bangaren Almustapha kuwa seda yaga Magajiya tarage hucin da take sannan yasaki hannunta yana kara jaddada mata"babuke babu family na stop messing around with us",yakarashe maganar yana nunata da yatsa cikin sauri tayo gaba tana neman shakareshi amma tuni ya juya yatafi yabarta da takaici jitake kaman tadora hannu aka ta fasa ihu cikin gurnani tace"Don ubanka da ni kake wasa Almustapha, harni zaka fadama magana akan wata filthy Matarka I'll make sure you regret this", Almustapha kuwa yiyayi kaman baima jitaba harya Isa bangarensu......

Tana nan tsaye tanata fadan maganganu kamar wata me tabin hankali harta gaji juyawa tayi taga bayin suna kallonta wani irin tsawa tamusu"meyekuke kallo,ni kuke kallo don baku da hankali" takarashe maganar tana nuna kanta da yatsa cikin sauri kowa ta juya takoma bakin aikinta cikeda tsoron Magajiyan Itama bangaren ta takoma tanata huci itakadai............

Tafi minti talatin ahaka kafin daga karshe takira daya daga cikin bayinta tace anemo mata Laure,cikin sauri yarinyar tafita don zuwa takirata ba ajimaba kuwa segasu sundawo.....
Zubewa Laure tayi gaban Magajiya tareda mika gaisuwa dukda kuwa yanda zuciyarta ke bugu don gani take kaman ankamata da laifine(kunsan mutum marar gaskiyar).......
Kare mata kallo Magajiya tayi"kedin miyene kike abu kamar wata munafuka?"......
Wallahi babu Uwargijiyata cewar Lauren muryarta na stammering.........

Dan sosa jiki Magajiya tayi tareda gyara zama sannan tace"dago ki kalleni daman nakiraki ne infada miki daga yau kezakinamin duk wasu aikace aikacena na kusa dani sabida bayan Talatu babu wanda nayarda da irinki Itama kuma kinga ta yaudareni".....
Kiyi hakuri cewar Lauren.......
Harara Magajiya takaimata tana"bawai hakuriba kika yarda kika cuceni gunduwa gunduwa zanyi dake infada miki".......
Gyada kai Laure tayi cikeda tsoro don itakam yanda tasamu Hajiya Muniba batason ace tacuceta, sallamanta Magajiya tayi sannan tatashi cikin sauri tafice bata tsaya koina ba se bangaren Hajiya Muniba zama tayi gabanta tana gaisheta lura da yanayinta Hajiya Muniba tayi sannan tace lafiya laure,meke damunki naganki duk ah birkice?...............
Cikeda tsoro laure tace ranki shi dade inacikin hali mai wuya wallahi....
Fadamin meke damunki yata Hajiya Muniba tayi maganar cikeda damuwa....
Nan Laure takwashe mata yanda sukayi da Magajiya sannan tasaki kuka tana wallahi ni banason inzama baiwar ta ninasan Matar nan nakuma san halinta bakiga abunda tayima Talatu ba yau Rankishi dade kuma wallahi babu wanda ya'isa yaje yafada ma Mai Martaba wannan zancen............
Cikeda tausayawa Hajiya Muniba tace....
"kiyi hakuri Laure insha Allah babu abunda ta'isa tayimiki I'm with you kuma wannan wani chance ne muka samu na bayyana wannan matar kikwantar da hankalinki kada kibari tama gane you're not loyal to her",dagowa Laure tayi tana kallon Hajiya Muniban murmushi tasakar mata tareda kara bata kwarin gwiwa kafin sukayi sallama................

*
Adakinta ta taimakama Talatun tazauna batareda taji kyamartaba koda kuwa kadan ne sa Salma tayi takawo ruwa ah kofi kafin tazauna gefenta tana"baiwar Allah ga ruwa Kisha"......

Girgiza kai Talatu tayi alamun takoshi Asma'u bata takura mata ba ta ajiye ruwan gefenta dede lokacin Jamila baiwar Ummi tashigo zare idanu tayi ganin Talatun.......
Asma'u ne tace iya Jamila kikaraso mana.....
Dan jijjiga kai tayi sannan tace...
"bazama nazoyiba Gimbiya daman Yarima ne yace inkiraki"......
Tashi Asma'u tayi tafice don zuwa gun Almustapha din tareda murtuke fuska don haryanzu batasauko daga fushin da takeyiba....

Jamila kuwa karasawa tayi cikin dakin tana hararan Talatu"kekuma hatsabibiya dame kikazo kuma yanzun?....

Cikin kuka Talatu tace kiyi hakuri don Allah banina kawo kainaba Gimbiya dakanta takawoni dakinnan batareda Jamila tajira sake jin me Talatun zatace ba tajawo hannunta tana "kizo kibar dakinnnan don inada tabbacin datasan wacece ke ko hanyar bangaren nan bazaki taba ganiba bare harkisamu daman zuwa kizauna mata ah daki".....
Haka Jamila tadinga jan Talatu hartakaita ta back door tasaketa ah kasa tana wallahi baki isa kizo ki sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login