Showing 45001 words to 48000 words out of 235422 words

Chapter 16 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3474

iskan yaron da kusan kowa yasanshi cikin ABU Zaria, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda yashiga maimaitawa,he really can't believe his eyes atake Kuma yaji kanshi nawani irin sarawa,Kiran number din yashigayi amma akashe yakira yafi akirga amma duka switch off ake cemishi.....
Yazaiyi yanzu,wazai tunkara dawannan maganar wata zuciyar Kuma tace babu kyau daga ganin abu kayanke hukunci yakamata ka tsawalla bincike besides Asma'u is a good girl Kuma gidansu gidan tarbiya ne dawannan tunanin ne yadanji zuciyarshi tarage zafi dukda kuwa inya tuno hoto seyaji kaman yafasa ihu, yanda Mukhtar yaga rana haka yaga dare don ko runtsawa beyiba daga karshe yayo alwala yazo yatada Sallah ko Allah zaisa yaji sauki ah zuciyarshi..........
Washegari dasafe kuwa ciwon kaine yadinga damunshi haryakejin kaman bazai iya shiga school ba sede kuma yana da important abunyi don haka yadaure yatashi yashirya cikin kananan kaya sannan yafita ....

****
Asiya kuwa tunda taturama Mukhtar sakon video da hoto ta WhatsApp ta tsiri zuwa side dinsu Asma'u don jin mezai faru amma haryau shiru,tsaki tayi tana addu'ar Allah yasa Mukhtar din yaga hoton......

***
Asma'u kuwa seda safe data tashi taga missed calls din Mukhtar sede tana sauri tashiga school wannan dalilin yahanata sake kiranshi.........

Tun 8:00am akafara yimusu tutorials se 11:00am aka gama, itada Zahra suka fito suna yar hirarsu, Zahra ne tace nikam kinga ran Monday zamuyi exams na practical aspect din chemistry sede ban iya wanda akayi last day ba kinsan ranar banshigo school ba......
Murmushi Asma'u tayi sannan tace nikam nagane sosai basai muje mugwada ba ah lab tunda bamuda abunyi kinga nima befi inkara koyaba,thank you Asma'u,muje don Allah muyi dannaji ance yana fitowa ah exams sosai......
Ware idanu Asma'u tayi tana"Allah?"...
Kinga past questions ne?....
Aa banganiba Basma kefadamin cewar Zahra din haka suka rankaya zuwa college din sannan suka shiga lab din dasuke chemistry practicals....
Babu kowa aciki sewani dasuka hango daga can gefe yana karatu abunshi,kasancewar lokacin exams ne ba ayin lecture sede dalibai su shigo suyi karatu kuma lab bawai ancika zuwa karatu gurin baneba,Zahra ne tayi gaba kafin tashiga duba musu instrument din wanda zaiyi misu anfani gurin gudanar da experiment dinsu....

Kusa da saurayin tasamu abubuwan don haka seta zauna,karasowa Asma'u tayi sannan tace bazamuyima lab attendant maganaba?.....
Hararanta Zahra tayi"Kai Ma'u akwaiki da tsoro wallahi,babu abunda zaice mana ai munzo yin abu mai amfanine"....
Asma'u da tunda tashigo takejin gabanta na fadi tace,toshikenan semuyin ai haka suka shiga setting abubuwansu seda suka gama setawa sannan Asma'u tace to ai babu sample anan fa.........
Nuni Zahra tayi mata da hannu inda aka ajiye samples din tashi tayi taje gurin suna jere acikin wani glass kowanne an ajiyeshi daban cikin conical flask,can ciki tahango wanda take nema din don haka tashiga kokarin ciroshi Zahra dake zaune tace wai Asmeey baki gani bane haryanzu?.....
Nagani ynzu zan dauko,karasawa gurin ta Zahra tayi sannan cikin rada tace nikam fitsari nikeji wallahi nayi tunanin bazai matsamin ba har intafi gida amma yanzukam I can't hold it anymore jinake kaman zai zubo,dariya Asma'u tayi sannan tace kije kidawo inajiranki ko in raka kine?......
Dagudu Zahra tafice tana aa nima yanzu zandawo fa mosque zani ba hostel ba.....
To sekin dawo Asma'un tabata ansa still tana kokarin ciro conical flask din seda ta ciroshi successfully harta juya zata tafi kafanta yabugu dawani kujera yayinda flask din yayi slipping ah hannunta yafadi ya fashe kafin ta ankara ta taka wani katon glass din conical flask daya fashedin wani irin Kara tasaki"wayyo Allah na" Almustapha dake gefe yana karatu yanajinsu tundazu sede yajuya musu bayane,yayi saurin juyowa jin Asma'u tayi ihu......
Babu shiri kafanta yafara bleeding dasauri yakaraso gurinta itakuwa se aikin kuka takeyi kallon kafar yayi haryanzu glass din najikinta sa hannu yayi yacire glass din tsabar zafi wani Karan takuma saki tsaki yayi tareda toshe kunnenshi,don yatsani hayaniya ah rayuwarshi,jin anyi tsaki ne yasata maida hankalinta kanshi tana shirin yin masifa ganin shine tayi saurin dauke kanta don bata manta abunda yafaru ranar ba,tashi tayi tafara tafiya nan tasake taka wata kwalbar wani karan tasake saki tana shirin taka wani kwalban ne yayi saurin janyota tadawo kusa dashi daukan seat yayi yazaunar da'ita kai sannan yace cikin kakkausar muryarshi"don't move,I'm coming"......
Yanda yayi mata maganar da command taji haushi amma se zuciyarta takasa sabama abunda yace din tana nan zaune tana ta raki yafito daga office din lab attendant din hannunshi rikeda first aid box wanda yabarmishi abude sanda zai fita saboda sunbasa......
Tsugunawa yayi gabanta bayan yabude box din....
yadauko spirit da cotton wool kafin yakamo kafar wani yar sukaji daga ita har shidin,shirin kwace kafar takeyi amma yaki saki nan yashiga yimata treatment tana kuka tsakaninta da Allah haryagama ma bata saniba don rimtse idanunta tayi,kallon fuskarta yayi tareda jijjiga kai aziciyarshi kuwa cewa yakeyi"Allah yasauwaka,wannan raki haka".....
Jisukayi an rufe kofar da karfi daga ita harshidin attention dinsu yakoma gurin sede meshi yariga yatafi,ta window ne tahango Mukhtar yana tafiya da alama ranshi abace yake cikin sauri ta tashi zatabi bayanshi don tana da tabbacin tunda yatafi ba magana yaga Almustapha ne......
Cikin sauri yakuma rikota yamaida ta tazauna kafin yace"wait for your friend",yana kaiwanan yajuya yatafi yabarta agurin kaman gunki daukan takardunshi yayi yafita bakin lab din yazauna aikuwa sega lab attendant din sallama yayi mishi yatafi..........
Tunda yafita yabarta takasa tashi ah gurin don gani take inta tashi kaman bata kyautamai ba,he cares shiyasa yace tazauna gashi tanason Kiran Mukhtar she don't know what he must be thinking,batasan miyasa mutane ke judging Almustapha ba,tarasa dalilin dayasa suka kasa ganewa shi mutumin kirki ne,yanzu miye abun bacin rai anan don Mukhtar yaga yana taimakonta,tana cikin wannan tunanin ne Zahra tashigo tana mekikeyi agurin har yanzu?....
Nuna mata kafarta tayi da hannun dayasha bandage,cikin sauri Zahra tace subhanallah ya akayi haka?....
kekam tsautsayi cewar Asma'u din kafin tace come and help me kada infame ciwon........
Cikeda damuwa Zahra tazo tadagata,tana wayamiki treating gurin?...

Murmushi Asma'u tayi sannan tace "Mr Taciturn",dasauri Zahra tadago tadubeta wayeshi Kuma?....
Dan bugun kafadanta Asma'u tayi cikeda wayincewa"just someone",kidaukomin bag dina acan mutafi i need to call Yaya Mukhtar......
Cikeda damuwa Zahra tace shikenan nibazan koyi abunnan ba?.....
Kiyi hakuri Zahra Monday din ai se 2:00pm zamushiga so zanshigo dawuri semuzo muyi Kinga da inason bin gidan Antyn Aisha ma amma yanzu bazai yuyu ba,toshikenan Allah yakaimu cewar Zahra din kafin tadaukoma Asma'u jakanta har mota tarakata sannan tatafi,Kiran Mukhtar Asma'u tashigayi amma yaki dagawa kwata kwata daga karshema kashe wayar yayi.....
*****
Mukhtar kuwa duk abunda yafaru yagani,zafin da kirjinshi keyi mishine yasashi kasa tsayuwa ah gurin yatafi abunshi,seda ya isa gida sannan tadinga kiranshi,tsaki yayi tareda wurgi da wayar"what is she going to tell me now that she's calling,so take tacemin it was a mistake ne ko wasu karyayyaki zata hadamin"....
Innalilahi wainna ilaihir rajiun,shine abunda yake maimaitawa jin tadameshi da Kiran ne non stop yasashi kashe wayarma baki dayanta......


Tirkashi!
Mekuke tunanin zai faru da Asma'u,shin wani mataki Mukhtar zai dauka yanzu,sannan wanene ke son ganin bayan Magajiya?..

*Kucigaba da bin Zeeneert cikin littafin Gidan sarauta, zaku ji yanda za akaya dayardar ubangiji*.....

*In Sha Allah zakujini gobe dasafe and sorry for making you guys wait yesterday*....

Inasonku sosai masoyanad'd'...



Vote
Comment
Share!...
[3/23, 5:25 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 14*....

***
Jin yakashe wayar jiki ah sanyaye taja motarta zuwa gida da dingishi tashiga bangarensu Sadiq ne yafara ganinta cikin sauri yakaraso inda take kamin yakama hannunta yana "Adda Asmeey ciwo kikaji?"....
Gyadamishi kai kawai tayi,garin yaya hakan tafaru cewar Ummi dake fitowa daga kitchen......
Nan Asma'u tabasu labari,sannu Ummi tashiga yi mata kafin tace you should be more careful next time kinji......
To tacewa Ummi kafin tace Sadiq kaimin jakana ciki,dauka yayi yatafi mata dashi.....
Haka ranar takwana tana tunanin yaushe Mukhtar ze bude wayanshi don takira shi times without number amma koyaushe takira kuma se acemata switchoff dakyar tasamu bacci yayi awun gaba da'ita.......

Tun cikin dare Mukhtar yasaka ma ranshi cewa yakamata ya rabu da Asma'u,he has to free himself from this relationship tunda ita ga wanda takeso da Sagir ma yazo mishi dasafe yatambayeshi meyafaru nan yafadamishi, shiru Sagir din yayi nadan dakiku kafin yace"I'm sorry Man,but tunda daman naso infada maka abunda yafaru da sister dinta sede alokacin banason inyi discouraging dinka daga neman aurenta and besides nayi laakari da kowa daban yake hakana
kowa da irin halinsa sabida zaka samu ah gida iyaye sunyima 'ya'yansu tarbiya mekyau amma sekaga daya daga cikin ya'yan bayajin magana kuma bawai iyayen basuyi kokaribane akanshi aa kowa da irin nashi kaddarar dakuma halin shiyasa wallahi banfada maka ba nabar maganar araina.......
Murmushin dayafi kuka ciwo Mukhtar yayi kafin yace now"it's over Sagir,da ace tanasona I won't mind amma duka behaviors dinta yanuna clearly cewa basona takeyiba, it's better i just free her from this relationship shine mafita kawai because ko anyi auren we might not be happy", gyadamai kai Sagir yayi kafin yace Allah yasa hakan shiyafi alkhairi amma mezaka cema iyayenta?.....
Dafe kai Mukhtar yayi cikeda damuwa kafin yace"Nima shine bansaniba because banason nuna ma iyayenta abunda tayi sede wata zuciyar nacemin kuma innayi shiru nabarta kaman na cucesu ne gwanda sudauki mataki akanta"..........
Jijjiga Kai Sagir yayi kafin yace keep it to yourself kada kanuna musu,besides kaima bakasan waya tura makaba,with time indai dagaskene zasu sani,gyadama abokin nashi kai yayi tareda yimashi godiya kafin yatashi yashiga bandaki yin wanka because bayason yabata lokaci gurin zuwa ganin Daddy........

Around 10:30am ya isa gidan tarba akayi mishi sosai kafin Sadiq yace bari yaje yayima Asma'u magana, jijjiga Kai Mukhtar yayi kafin yace kyaleta inason ganin Daddy tukunnan inna fito zamu hadu, murmushi kawai Sadiq din yayi don bedauka abakin komai ba sannan yace bari yaje yafada ma Daddy din dama Sunday ne weekend,ba ajimaba kuwa Daddyn yace ashigo da Mukhtar ahankali yakarasa cikin katafaren parlourn don bakaramin nauyin Daddyn yakejiba.....

Gaisawa sukayi kan Mukhtar din akasa, Daddy yatambayeshi ya exams yace masa alhamdulillah,nan kowa yayi shiru cikinsu babu mai magana don shikanshi Daddyn bejima da recieving shocking news of his life ba sannan daganin Mukhtar din seyakejin 90% na zuciyarshi naraya mishi abunda yakawo Mukhtar din kenan..........

Daddy ne yayi karfin halin cewa Mukhtar lafiya,akwai wata damuwa ne??...
Jiki ah sanyaye Mukhtar yace eh Daddy yayinda take idanunshi suka kada sukayi jazur,to Mukhtar fadamin mana inafatan dai lafiya?.....
Jijjiga kai Mukhtar yayi kafin yayi karfin halin cewa Daddy maganar auren mu da Asma'u ne yakawo ni, I'm sorry to say this ina inaganin afasa shi kawai sabida ko anyi ba lallai muji dadin zaman ba......
Murmushin dayafi kuka ciwo Daddy yayi kafin yace da akayi yaya, Asma'un ne tace maka tafasa?.....
Cikin sauri Mukhtar yajjijiga kai alamun a'a yayinda yakarada batafada min ba amma inaganin tanada wanda takesone bayan ni nikuma banason in tauye mata hakkinta,kafin yayi folding hannunshi alamar roko yace Daddy don Allah ku tuntunbe ta kuyimata abunda ranta keso kada tafada wani hali......
Gyada kai Daddyn yayi kafin yace,I regret the fact that you cannot be my son in law sabida kai yaro ne me hankali da sanin yakamata,ko gobe katashi neman aure indai ah gidan nan ne inkuma inada halin baka zanbaka Mukhtar Kuma inason kasani rabuwarku da Asma'u bawai yananufin kayanke zumunta damu bane please.......

To Daddy insha Allah, murmushi Daddyn yayi sannan yace bazan takuraka ba,may be your decision is the best sede inason kafada ma iyayenka tun wuri kada sunacan basu saniba,gyada Kai yayi sannan yace zanfada musu dayardar ubangiji nagode Daddy,nan yayima Daddy sallama yatashi yatafi batareda yanemi Asma'u dinba don Allah kadai yasan yanda yakeji ah yanzun...
....

Daddy kuwa tun fitan Mukhtar yadafe kanshi cikeda damuwa,yarasa meke damun 'ya'yanshi mata,yayi musu tarbiya maikyau,yasosu iyaso amma abunda zasu sakamishi dashi kenan,isa daki yayi yadauki wayanshi yakira Ummi yace tazo itada Asma'u,kafin yakira su Mommy da Asiya dakuma yayunta.......
In no time suka hallara ah parlourn, Asma'u kuwa tunda Sadiq yazo yacemata Mukhtar yazo yashiga gurin Daddy hankalinta yatashi zuciyarta tashiga bugu .......

Kowa yayi shiru ah parlourn kamar babu mai rai ahankali Daddy yaciro wayarshi yamikama Ummi,jiki ah sanyaye Ummi tabi hoton da kallo wanda tun ranarda Asma'u tafada jikin Almustapha dakuma na jiya ah lab,sa hannu tayi ah bakinta tana kokarin rike kukanta maida ma Daddy wayar tayi kafin ta tashi tadauke Asma'u da wani irin wawan mari"Tarbiyar danayi miki kenan Asma'u?"......
Asma'u dake zaune batasan me Ummi tagani ba tace menayi Ummi,wani makan Ummi tasake kai mata tana innalillahi wainna ilaihir rajiun kukam wani irin yarane,miyene yashigeku iye,dan ubanki tambayana ma kikeyi Ummi takarashe maganar tana hawaye........
Mommy ne tace haba Maryam miyena dukanta Kuma,ko dukanne zeyi solving problems don already Daddy yabama Mommy hoton takalla....
Cikeda takaici Ummi tace Anty Zainab bakiga metayibane fisabilillahi,inban duketaba mezan mata yarinya tana neman bata rayuwarta......
Daddy ne yayi gyaran murya tareda cewa ya Isa haka dukkanku kuzauna,dakyar Ummi tabar Asma'u kafin takoma tazauna zuciyarta na tafarfasa miko wayar ma Daddy Mubaraq yayi jikinshi yayi sanyi because yakasa yarda da abunda yagani.......

Gyaran murya Daddy yayi kafin yace"tunranar dana taraku kan maganar
Asiya danaji Asiya tayi maganar Asma'u da yaroncan hankalina yatashi don haka nasa jibril yayi min bincike akan abun batareda kowa yasaniba,and here it's jiya da dare yakawomin hotunan nan nakan cewa yagansu tare sau biyu and dasafen nan Mukhtar yazo yace min yafasa auren Asma'u shi dukda yakifadamin directly abunda yasa ninasan wannan dalilin ne yasashi janyewa.......
Jiki ah sanyaye Daddy yace my girls are trying to ruin their lives I don't know why,yanda yayi maganar zakasan cewa akwai bitterness sosai acikinta,kallon Asma'u yayi sannan yace I thought you're more sensible than your sister ashe duk daya kuke, Asma'u mezakiyi da yaron can,yaron da bashida tarbiya yaron da ubanshima yakishi?....
Cikin kuka tace believe me Daddy there is nothing between us wallahi sharri akayimin, cikeda bacin rai Daddy yace I don't care abunda nagani shizanyi anfani dashi ko anfada miki mudin mahaukatane"this's not the first evidence Asma'u"......
Nunata da yatsa Daddy yayi,daga yau babu ke babu zuwa makaranta kuma kishirya nanda sati biyu zanyi miki aure dakoma waye naga dama Itama Asiya zan tuntubi iyayen Aslam din inbasuda matsala da hakan zanhadaku duka ko hankalina yakwanta kafin yadubi Mubaraq yace"kamin siezing wayoyinsu kakawomin yanzunnan",tashi Daddy yayi yafita yabarsu dukansu se kuka......
Karban wayoyin Mubaraq yayi kafin yakaima Daddy din yafice abunshi Mommy da Ummi ma fita sukayi haka Asiya,kuka takeyi kaman ranta zai fita yautashiga uku meyake shirin faruwa da'ita ne wai,jiki ah sanyaye tatashi tana dingishi takoma side dinsu tundaga bakin kofa Ummi tadinga janta kafin tashigar da'ita daki tashiga Kai mata duka,ihu Asma'u tadingayi amma babu mai taimakonta se kannen ta dake bakinn kofa suma suna kukan seda Ummi tadaketa son ranta kafin tafito tarufe dakin.......
Hararan Munir,ikram da Munira tayi dake tsaye bakin kofa suna kuka sannan tace"inbaku bacemin dagani ba senayi muku dukan tsiya Kuma"....
Jiki na bari suka koma parlour, Ummi kuwa daki takoma takwanta kanta nasarawa, Asma'u kuka takeyi harda shikewa gabadaya jikinta yayi rada rada,inazata saka kanta taji dadin rayuwarta gashi Daddy yakwace wayarta bare takira Mukhtar taji dalilinsa nayi mata haka don ita tsabar rikidama bataji bayanin Daddyn dakyau ba don duk ah tunaninta Mukhtar ne yanunama Daddy din.........
Bangaren Asiya kuwa tunda takoma bangarensu tashige dakinta tana hawaye don ita damuwarta Simcard dinta don tanada wani waya da Ahmad DJ yabata taboyeshi sabida kada agani ah gida ah tambayeta inatasamu,ah take kuma tatuna cewa ashe tacire Sim card dinnata dasafe tasa wanda Baba maigadi yasiyo mata don duba ko Mukhtar yaga massage dinta tunda tajishi shiru.....
Dan murmushi tayi atleast she'll now get to chat with her friends babu boring life,tunowa da halin da kanwarta tashiga tayi setaji kuma she's not happy da abunda tayi din,tsaki tayi afili tafurta"Asiya kindauki revenge amma miyasa bakyajin dadi harcikin ranki,miyasa bakyajin dadin ganin Asma'u acikin wannan halin"......
Tashi tayi cikeda damuwa tabude wardrobe dinta tadauko wayar tasaka simcard din sannan tajonata ah charging bayan tasa key akofar dakinta......
Komawa tayi takwanta tana tunanin abubuwan dasuka faru,she just want to be happy about it sede she couldn't zuciyarta takasa aminta da hakan,dakyar tasamu ta kauda tunanin aranta.......

*****

Magajiya kuwa ana Masarauta anata shirye shiryen biki sabida yau sauran kwana shida auren 'ya'yan nata dukda kuwa gabadaya tadamu da rashin dawowar Sulaiman din gashi Mai Martaba ma na complain tunda Sulaiman yatafi baikirashiba.....

Itadai addu'ar ta daya Allah yasa Sulaiman ba guduwa yayiba don kuwa daba karamin rusa mata plan yayi ba,layinshi na London kuwa kullum cikin kira takeyi amma amsar dayace kullum akashe ......
Yanzuma tana zaune tanata gwada layinshine amma yaki shiga,gabadaya tadamu gashi tasan daga gobe Monday baki zasu fara hallara agidan kuma za afara tambayar inayake,Talatu ne tashigo cikin kuskus tacema Magajiya tayi bako,tsaki Magajiya tayi kafin tace inazuwa seda Talatun tafita sannan Magajiya tabi bayanta ah inda suka saba haduwa tasamesu,rai bace tace lafiya?......
Kai kasa yace kiyi hakuri Uwargijiyata Inna bata mikirai.....
Kai tsaye tacemishi me ake ciki da batun yarinyar?......

Nan yashigayimata bayani, Uwargijiyata naturamata amma inaganin itan batadau matakiba, Allah yataimakeni yaron da mahaifin yarinyar yasa yayi bincike akan Asma'u din seya sa anemo mishi wani yayi aikin donshi bazai iyabin ta makaranta kullum ba yanada abubuwan yi to wanda yasa yanemo mishi meyin aikin abokina ne shine yake fadamin don yasanni da neman kudi shine nace mishi zanyi nanna gudanar dakomai nahada dawancan video da hoton farkon dana jiya natura masa shine yakai ma mahaifin yarinyar to yanzu dai bamusan matakin dazai daukaba se anshiga sati zankoma cikin makarantar in bincika, toshikenan kasan adireshin da Almustapha yakoma ko?.....
Gyada mata Kai yayi kafin tashiga yimishi bayanin aikin datakeso yayimata ....
Cikeda ladabi yace anyi angama ranki shi dade,sa Talatu tayi ta sallameshi kafin yatafi,duban Talatu tayi sannan tace Ina bayin da Yarima yayi anfani dasu?.....
Kan Talatu akasa tace sunanan Uwargijiyata akirasune?.....
Eh kice suzo su sameni yanzu,gyada mata kai sannan suka koma cikin masarautar ita Talatu tayi hanyar zuwa kiran bayin.....

Ba ajimaba segasu sunzo tareda Talatu din gaisuwa suka shiga yima Magajiya kafin tace kwanaki nace muku zakumin aiki ko,innatashi zan neme ku.....
Atare sutayika amsa da eh Uwargijiyata ...
Murmushi tayi sannan tace lokacin yayi to,gobe zaku gudanar min da aikina ah fadar yanke hukunci......
To uwargijiyaa sukayi maganar cikeda ladabi,bayani tashiga yimasu kafin daga karshe tace sutafi in aiki yayi kyau zasuji kyautarsu,jikina bari duwawu nazikiri suka fice ah dakin nata......

*****
Asma'u yini tayi tana sharbar kuka,yayinda lokaci daya wani irin ciwon kai yashigeta batayi sallar azahar ba bare laasar gashi har maghrib tagabato kai,duban agogo tayi nan taga biyar da rabi cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login