Showing 168001 words to 171000 words out of 235422 words

Chapter 57 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3510

komai da komai inda suka karashe zancen zatazo kusan two weeks to the wedding,to jiyane ma naji suna magana da Mom kan yau zata kamo hanya"..............
Cikeda Jin dadi Afiya tace"yaeyyyy? Allah yakawota lafiya".....
Harara Amira tayi mata tana"kekuma murnar na menene?"...
Itama Afiyan maida mata hararantayi playfully tareda cewa"akan mi bazanyi murnar ba".......
"Naga kina rawar jiki ne bayan ke ba Amarya ba bakomai ba",dariya Sumayya tayi tana"kukam baku da dama. miyene in anyi matan Amira kema inkinaso basai amiki ba tunda bakudin ki bane zaiyi ciwo"......
Ahto nima dai abunda nagani kenan cewar Afiya,nidai don Allah ku taimaka kukarasa raba ankon nan laziness dinku yayi yawa ga biki se matsowa yakeyi Sumayya tayi maganar tareda tashi tsaye,sakan baki Amira tayi tana 'yar dariya....
"Amma nidai bantaba ganin marar kunyar Amarya irinki ba".......
"Lol,kifadi abunda keranki Amira don kinga bani da kawaye ne agarin nan shiyasa", Sumayya tayi maganar tareda ficewa daga dakin don leka Asma'u tatambayeta ko ta? aikamasu Aisha da Zahra ankonsu da ta bayar tunda na dinner din harda kawayen Asma'u ne ayanda suka tsara......
Aikuwa samunta tayi tafito ah wanka kenan jikinta daure da towel,murmushi tasakar ma Sumayyan sanda taga tashigo dakin kafin tace"Amarya Amarya".......
Dariya Sumayya tayi tana"kema wata amaryar ce ae".......
Zama Asma'u tayi tana goge jikinta da dan karamin towel kafin tace...
"aa kam ni ae ba sabuwa kal ah leda baceba"........
"Lol,bawani nan",inji Sumayya din kafin tace kinsamu kin aikama su Zahra ankon ne?...
Salati Asma'u tasaki tareda cewa"wallahi namanta kwata kwata Sumayya inba yanzu dakikayi maganar ba,amma ba inkira Zahra tazo gida takarbi nata inta taso daga school Aisha kuma tana kaduna I was even thinking ko inbayar mata dinkin ah garinnan ne kawai duk kinga na manta",Asma'u takarashe maganar tareda janyo wayarta don kiran Zahra din kallonta sosai Sumayya keyi kafin tasaka hannu takarbi wayar,dagowa Asma'un tayi dasauri tana"Kiran Zahra din zanyi dai"............
Batareda Sumayyan tamayar mata da wayan ba tace"wai what's wrong with you ne Sis,I've been noticing you kaman kina cikin damuwa kwanan nan"...........
Asma'u da take idanunta suka canza launi tasaki murmushi kafin tace"me kika gani?"...
"Nifa babu abunda kedamuna",no karyane Asma'u gashi kinrame duk kin canza,kinyi wani iri and tunda ake maganar bikin nan baki zama ayi dake bayan nasan ke bahaka kike ba,you always interact.......
Dariya kawai tayi dukda idanunta sunciko da kwalla kafin tatashi tsaye tareda karasawa gaban mirror tana kokarin boye hawayenta"wai meyake samun yan gidan nan ne tun wurin kwana uku kenan kowa seyana tambayata meyake damuna haka, Ummi kusan kullum seta tambayeni, Afiya da Amira shekaranjiya sunmin same tambaya, Aunty Hamida ma dazu damuke girki seda tamin tambayar nan kema gashi kina neman isata,kumafa dukdan kunga na rame ne to slimming nafara", takarashe maganar murya ah karye jijjiga kai Sumayya tayi in desbelief kafin tace....
"you can pretend to be okay but no one will believe you sabida muryarki ma kadai ya'isa yatona miki asiri".........
Asma'u kasa cewa komai tayi se jan man shafawanta datayi tafara shafawa jikin ta tana hawayen data rasa dalilinsu duk Sumayyan na kallonta tacikin mirror,ahankali tace"kunyi fada da Yaya Almustapha ne?"......
Cikin sauri Asma'un ta jijiga mata kai,to ko bakida lafiya ne, Sumayya tayi mata tambayar ah karo na biyu shima jijjiga kai tayi yayinda takife kanta agurin tana kuka me tsuma zuciya cikeda tausayinta Sumayya tataso tana rarrashinta kafin daga karshe tace"shurunki won't solve problems, you've to speak out Sis inma bazaki fadamin ba you can call Umminki kokuma kikira Asiya kuyi magana I'm very sure she'll advice you akan koma menene kinji?"......
Gyada kai kawae Asma'un tayi yayinda Sumayyan seda tayi kokarin lightening mood dinta kafin suka kira Zahra din batun ankon inda tacemusu zata biyo? takarba inta taso daga school........
Aikuwa batazo tasamu zuwanba shiyasa ma dayanma dasu Aliyu sukazo daukar Hajja dako ah lokacin suna tareda Ummi, Asma'u tabashi kayan yamika ma Zahra inzasu wuce gida tunda gidansu baida wuyan ganewa,sunjima suna hira da Asma'un don? itakadai ne duk yan matan sunfita gari hakanan Aliyun nata lura da yanayin Asma'un gakuma? raman da tayi compared to sanda tazo gida yaso su kebe suyi magana amma babu hali dubada yanda Bayi keta kai kawo kuma Musa da Sadiq ma sunanan she might not like to speak up probably ahaka harsuka tashi tafiya inda Ummi keta mitan miyasa za azo daukan Hajja bayan gashi sun saba abunsu gama kuma biki dake karado kai amma se Hajjan tace bakomai zatadawo bikin ai Itama tanason taje tadan kintsa ne... ..
To kawai Ummin tace badon ranta yasoba don bakaramin sabo sukayi da Hajjan ba shiyasa ma gabadaya taji batason tafiyar tata to amma yazatayi tunda Hajjan ma tanuna tanason zuwa gidan abunda Ummi batasani ba shine Hajja nashiga mota tashiga yimasu Aliyu surutu"Yan bakin ciki kawai,dan kayan itatuwan dana keci kullum dakuma zama danakeyi ah muhalli mekyau shine akeyimin bakin ciki".........
Dariya Aliyu yayi yana"to Hajja yanzun dawa kike?"......
Harara tabuga mishi tana"Wanda ya tsargu kuma ko anki ko anso sena dawo bikin nan".......




Vote
Comment
Share!
[3/23, 6:06 PM] >?p?: =?Q?=?Q? *GIDAN SARAUTA* =?Q?=?Q?

Written by *Zeeneert*=ؕ?

*Zeeneert*@wattpad.....

*I've seen all your comments.....*
*And to tell you the truth,i really feel honored and blessed to have you all in my life,thank you so much Allah yabar kauna*=ؕ?d'......

Insha Allah option dinda mutane suka fi yawa akai shizan dauka...


*Page 58*


Shidai Aliyu dariya kawai yayi don yasan inya biyema Hajja se suyitayi ne babu tsayawa and daga karshe shine ah ruwa don zuwa zatayi tahada mishi bomb gurin Daddynsu,koda suka koma gida maghrib ta gabato shiyasa ma baiyi tunanin kiran Asma'un ba seda yazo kwanciya aranshi yana addu'ar Allah yasa batayi bacci ba kokuma baswa tareda Almustapha don dukyanda yaso yabari se washegari kasawa yayi don gabadaya gani yakeyi kanwar tashi nacikin tsananin damuwa........
Asma'u nakan sallaya ta'idar da sallar isha wayarta tayi kara,tashi tayi tadauko cikin sauri don kada call din ya yanke ganin Aliyu yasata dagawa cikin sauri.....
"Ina wuni Yaya Aliyu?"......
"Dazuba mun gaisaba Sis",yayi maganar ahankali yar dariya tayi sannan tace "aiyanzu da dazu ba daya bane ba Yaya Aliyu sannan tashiga tambayarshi yanda suka isa gida"yakun isa gida lafiya yakuma kuka samu su Mommy da Ummi,I hope kowa lafya?"......
Kowa alhamdulillah Sis except one person,cikeda damuwa tace"subhanallah waye ba lafiya?".......
Gyara zama shi yayi sannan yace"tsaya kada kitada hankalinki kuma,kowa lafiya ah gida I'm talking about you Asma'u, what's wrong with Sis,bakida lafiya ne ko akwai wani me takura miki acan din?"............
Cikin tsananin damuwa Asma'u taji gabanta yashiga faduwa itakam tashigesu wai miyake faruwa ne,miyasa kowa yake gane halin da take ciki so easily while she's trying so hard to hide it,jin tayi shiru ne yasa Aliyun cewa"Asma'u,are you there?"....
Gyada mishi kai tayi kaman wanda tana gabanshi kafin dakyar ta'iya cewa....
"Eh Yaya nifa babu abunda yake damuna believe me",bebari tarufe baki bama yace"karya kikeyi Sis you better tell me what's bothering you inbaki fadamin ba wazaki fadamawa,are you going to let it disturb your peace of mind?",sannan yayi kasa da murya "Feel free Sis,Yaya Aliyu is here for you",ah take taji zuciyarta ta karye hakanan idanunta suka ciko da kwallah lokaci guda ita kanta tasan she really need someone to talk to kozata dan ji sauki aranta and surely tasan Aliyu is the right person,shi mutum ne dabaidamu da baza sirrin wasu ba and most importantly akwai shakuwa sosai ah tsakaninsu,he might understand her and may be yabata shawara ma sede tasan maganar bana waya baneba don haka tace"we cannot talk on phone dole semun zauna Yaya".........
Cikin sauri yace"okay then I'll come home tomorrow evening semuyi maganar kinji,but before that kikwantar da hankalinki please"....
Gyada kai tayi kamar wanda tana gabanshi jin tayi shirune yasashi sake cewa"kinji sis?"....
Sa hannun tayi tashiga goge yar kwallarta kafin tace"To Yaya Aliyuna", murmushi yake yayi yana"that's my girl, I'm hanging up now kigaida mijinki kinji".......
To kawai tace mishi kafin ta ajiye wayarta ah gefenta,haka tacigaba dazama agurin tana hawaye ita kadai har wuraren shadaya kafin dakyar tatashi tasauya kayanta zuwa na bacci kafin tahau gadonta ta kwanta sede gabadaya bacci yaki daukanta........
Yau Almustapha da wuri yadawo gida, shiyasa ma dabai samu Asma'u kwance ah dakin ba seyayi tunanin ko agaba zatazo ta wannan dalilin yasashi yin wanka yashirya cikin kayan baccinshi sannan yadauki laptop dinshi yana dube dube dukdama rabin hankalinshi nakan kofa ko Allah zaisa tashigo amma shiru har shadaya da rabi,dan tsaki yayi sannan yakashe laptop din tareda rufeta yana mamakin rashin zuwan nata tunda bawai sunyi sallama da Hajjan baneba bare yasan tatafi........

Kwanciya yayi tareda jan bargonshi amma gabadaya yakasa bacci duk rufe idon dazaiyi ita yake gani hakanan kawai soyake yaga,"her very beautiful soul sleeping next to him as usual",yacanza position din kwanciya yafi ah irga amma babu alamar zai iya baccin wannan dalilin yasashi tashi cidok yafice zuwa parlour da tunanin ko anan tayi bacci sede koda yaje nanma batanan jiki ah sanyaye yakoma dakinshi yakwanta don bayason zuwa dakinta kuma Hajja nanan,bashi yasamu yayi bacci ba se wuraren biyun dare hakanan asuba nayi yafarka feeling as if some part of him is missing ahaka yatafi masallaci yayi sallah yadawo,samun su Amira yayi suna zazzaune suna jiran yazo yayi masu karatu,wucesu yayi batareda ya amsa gaisuwar subama don gabadaya mamakin rashin ganinta agurin yakeyi bayan kuma da'ita ake karatun, ah hanyar dinning? suka ci karo dan kara tasaki sakamakon gwaruwan da goshinsu yayi wanda hakan yajanyo attention dinsu Amira dake parlour harda yar dariyarsu shikuwa kallonta yakeyi cikeda jin dadi don bakaramin relief yajiba infact bemaji zafin buguwarba don koyajima baidamu ba kama hannunta datake sosa goshin nata dashi yayi sannan yajata sukayi daki,rufe kofar dakin yayi tareda jingunuwa jikin kofar yanajin wani kwanciyar hankalin daya rasa adaren jiya sunfara dawowa daya bayan daya, ahankali yataka zuwa inda take tsaye,rungume ta yayi hakanan lokaci guda yalumshe idanunshi tareda sauke ajiyar zuciyar dabaisan dalilin shi ba,itadai mamaki da kidima ne suka kamata lokaci guda gashi tanason kwace jikinta amma gabadaya ta kasa sabida wani irin wawan runguma yayi mata jitayi yace"Don't move please",sakamakon motsin da takeyi ajikinsa itama kuma seta tsinci kanta dadaina motsin sannan ahankali tasa hannunta ah gadon bayanshi tana lumshe idanu............
Sunfi minti biyar yanatason yayi magana amma yakasa,dakyar kuma yayi karfin halin cewa"do you know?"....
Jijjiga mai kai tayi ahankali tanajiran jin maizaice amma shiru,sema sake cewa dayayi"do you k..n..o..w that",wannan karan har muryanshi na cracking amma gabadaya yakasa karasa sentence din ahankali tazare jikinta daga nashi cikeda damuwa tasa hannunta tariko fuskarshi tana kallon cikin idanunshi"Yaya imam"........
Kallonta yakeyi kawai batareda yace komaiba, calmly tacigaba da magana"what where you saying,what do you want me to know?"..........
Cire hannunta yayi ajikin fuskarshi sannan ya sarkesu cikin nashi yana kallon hannayennasu dake sarkeda na juna kafin yace...
"I couldn't sleep early without you by my side yesternight".......
Lokaci dayi taji heart dinta yayi melting,she couldn't sleep without him too and ita tasan dalili but shifa? what's the reason behind it,has he by any chance fall for her?goge kwallar dayayi slipping agefen kuncinta tayi kafin tacanza maganarda"Su Amira najiranmu Yaya"because batason ayi furthering maganar ma she might end up getting hurt sabida tunanin Almustapha ze sota ma is a false hope,a very great one ma kuwa sede da mamakinta taji yadagata sama kamar Baby bedire ko'ina ba sekan gado,kwanciya yayi ajikinta kafin in a whisper yace...
"I want to sleep now".....?
Gyada mishi kai kawai tayi tana kokarin danne kukanta,she couldn't just say no to him besides she need it too,his warmth,his breath,his scent infact everything about him ma don Itama dakyar ta'iya tayi baccin jiya............
Yarigata yin baccin yayinda itakuma taketa sake sake aranta harma batasan sanda baccin yayi awun gaba da'ita ba.......
Bangaren su Amira kuwa haka sukayita jiran fitowarsu amma shiru,wannan dalilin yasa Afiya tashi tana tattara littafanta"tonikam kunga tafiyata".........
Sumayya ne tace "kujira mana sufito kada Yaya Almustapha yafito baisamemuba kunsan ranshi zai baci",don ita haryanzu bakaramin tsoron Almustapha takejiba shiyasa take dar dar dashi.......
"To indai jiran wayannan ma'auratan zakiyi kinada aiki,Afiya jirani mutafi daki baxan zauna bakin ciki ya kasheni ba don nasan yama manta da existence dinmu anan",wannan karan Amira ce tayi magana.....
Dariya Afiya tayi tana"ah to",daganan sukayi daki itama Sumayyan binsu tayi dukda ranta baisoba sede kuma talura maganar tasu akwai kamshin gaskiya acikinta shiyasa ma tayi giving up tareda mamakin Yaya Almustaphan,so he could be lovely like this>?t?........

Wajajen goma na safe Sulaiman yashigo bangaren su Asma'u din yana tambayar ina Almustapha amma sece mishi Afiya tayi yana bacci da mamaki yace"Bacci kuma?"....
Are you really serious.....
Yar dariya tayi sannan tace"Allah dagaske nakeyi Yaya",dan tsaki yayi sannan yayi hanyar dakin Almustapha din yana"lallai ma Yayan nan yasan munada ayyuka shine ze kwanta bacci fisabilillahi?"...........
Cikin sauri ta tare gabanshi tana dariya kafin tace"yanada kai ai you can do the work yau hutu yakeyi',wani harara ya daka mata yana"Bani hanya ni kiga I don't have your time" sannan yakarada"I was supposed to go to Kaduna tun sassafe amma natsaya jira yafito sabida banason ana aiki one of us baya gurin thinking he'll come out soon amma shiru shiyasa nabiyo baya"........
Batareda ta matsa agaban nashi ba tace"zaifito ai Yaya Sulaiman",dukdai wai tanason yagane dakanshi kan cewa yana tareda matarshi amma Ina shigabadaya ma wannan tunanin baizomai bai ganin ya matsa ne akafule tace"Yaya Sulaiman ta'ina zaka fara shiga dakin mai iyali newai tukun"........
Lokaci daya Sulaiman yaji abun yafado masa don shadaf yamanta yadaina shiga dakin Almustapha tunda yayi aure,dan shafa suman kanshi yayi yana"Damn it",kafin yadago ya kalleta"kinsan I totally forgot", sekuma yakwashe da dariya dukda takaicin dayakeji na abunda Yayan nashi yayi yana"lallai ma mutumin nan,zan rama wallahi badai inyi auren yagani...........
Afiya ma dariya tayi tana aigwanda kai ganin sa nema bakayiba kwata kwata muda ko ansa gaisuwarmu baiyiba bare musa ran za ayi karatu yau yanazuwa corridor yaja Matarsa sukayi daki...........
Dariya sosae Sulaiman keyi yana cize yatsan shi,daman he was worried ganin Asma'u kaman tanada damuwa but after hearing this today seyake tunanin they might resolve their differences,dawannan yafice yana "Shikenan yau ba batun zuwa Kaduna amma Yaya yasani ana gama biki innakwashi amaryata muka tafi honeymoon bazaku sake ganinmu semun samo muku tsarabar Baby",dariya sosai Afiya tayi tana jijjiga kai da mamakin rashin kunyar Sulaiman din.......
Asma'u kuwa itata fara farkawa ahankali ta dago kanta daga physique chest dinshi tareda daurawa kan wall clock din dake dakin ai batasan sanda ta zabura ba ganin har karfe shabiyu da mintuna arba'in da uku wanda zaburan nata ne yafarkar da Almustapha daga baccin dayakeyi yana tambayarta lafiya..........
Kaman zatayi kuka tace"kaga time fa",bedamu da abunda tace dinba hakanan baiduba wall clock din data bukata yayiba sema kallonta dayakeyi cikeda adoration,ganin kallon dayake mata yayi yawa gashi yana sata feeling wani iri seta sake pouting bakinta cikeda shagwaba tace"niwai miyene kaketa kallona?", murmushi kawai yasakar mata because he's really enjoying the moment,it's been 11 days now rabon dayaga tayi mashi shagwaba shiyasa dayaga tayi ayanzu taburgeshi hakanan yakejin kaman all his problems are gone...........
Ganin yaki magana ne yasata tashi cikeda tsarguwa,cikin sauri yatashi yazauna shima tareda janyota kan cinyarshi in a whisper yace"where are you going Wife?",harara ta buga mishi wanda hakan yasashi sake janta jikinshi cikeda zolaya yace"ko ruwan wanka baki hadamin bafa?"....
Wannan karan kan
dan bugun kirjinshi tayi sannan tatashi cikin sauri tasauka daga kan gadon tsabar tama rasa mezata cemishi,sekace daman ita take hada mishi ruwan wanka ada din,wai what's wrong with him ne yau,miyasa bai tafi inda yasaba zuwa ba ita tana tunanin yanda zata fita tabar dakin nema dakuma yanda zata fuskanci yan gidan.......
Yana ganinta tsaye tanata saka da warwara itakadai,intayi bakin kofa kaman zata fita sekuma tadawo hakadai, shidai baicemata komai ba baikuma tashi daga kwance dayake ba se yar dariya dayakeyi mata kasa kasa can kuma seyaga ta sake nufar kofan Yar dariya yakumayi yana jiran ganin tadawo amma wannan karan setayi ficewarta abunta...........
Jijjiga kai yayi yana mamakin hali irin nata sannan yatashi yashige bandaki donyin wanka, Asma'un ma tanazuwa daki wankan tashiga don gabadaya tarasa abunyi,wannan abun kunya damai yayi kama kana bangare daya da suruka kakasa tashi daga bacci sai azahar that too adakin miji fisabilillahi?....
Itadai Almustapha bai kyauta mataba yau gaskiya.........
Seda tayi wanka tashirya sannan tadauki wayarta dake kan bedside drawer tun jiya, bakaramin mamaki tayiba ganin 10 missed calls from Yaya Aliyu cikin sauri tashiga kiranshi Allah yataimaketa yashiga, ringing daya yadaga muryarshi daukeda damuwa yace"nayi ta kiranki baki daukaba,inafatan dai lafiya?".........
Dan murmushi tayi sannan tace"wayar na silent ne Yaya Aliyu seyanzu nagani, I'm sorry",shima cewa yayi "I'm sorry too baxan samu zuwa yauba munama kaduna 2 jirginmu zai tashi zuwa Lagos kinsan Daddy bayawa mutum alert inza ayi tafiya sede kajishi kwatsam, I'm really sorry innazauna I'll call you semuyi magana"......
Karka damu Yaya, Allah yasaukeku lafiya kagaida min Daddy please......
Ahankali yace"insha Allah nan sukayi sallama ya katse call din",ajiyewa tayi agefenta taredayin hamdala don itakanta daman kawai tace mishi to dinne bawai dan tasan ta'ina zatafara bashi labarin abubuwan dasuka farun ba ....

Almustapha kuwa yana gama shirinshi gun Ummi yayi suka sha hiransu don cewa yayi yau hutawa zaiyi babu inda zashi awurin Ummin nema yakejin Hajja tatafi, murmushi yayi aranshi yace"so that old woman was helpful"........
Ganin har 3 Asma'u bata fito ba Ummi tadubi Almustapha da tuhuma"Anya Imam kana damuwa da al amuran matarka yanda yadace kuwa?".....
Da mamakin meya kawo maganar yace"wani abunne yafaru Ummi?"......
Ajiyar zuciya Ummi tayi sannan tariko hannunshi cikin nata"I'm not sure if kaine cause din damuwarta but I'm sure something is bothering her for the past two weeks I guess,nayi nayi tafada min bata fadaba she always says that she's okay while she's not,kai bakaga yanda tarame bane ko bakasan yanda ake kula da Mata bane sena koya maka?",yanda Ummi keyi mai maganar seyake ganin kaman tamaidashi wani karamin yaro ne,dan cire hannunshi yayi cikin nata sannan yashafa suman kanshi gabadaya yarasa mema zaice ma Ummin,da ace tasan yanda yadamu yaji matsalar yarinyar shima dabazama tafara mai maganar ba yanzu........
Jin yayi shiru yasata cewa"Did you ask her?"....
Ahankali ya jijjiga mata kai alamar a'a,jiki ah sanyaye Ummi tace tokodai kasan mekayi mata ne kakeyimin shiru inatada magana nikadai.....
Cikin sauri yace...
"I did nothing Ummi".......
Try and ask her dukdama ba lallai tafada ma ba kokuma kazauna kayi tunanin abunda kasan kayi mata yabata mata rai ko abunda kasan zai iyasata cikin damuwa because I've the feelings that it's something connected to you Imam......
Gyadama Ummin Kai kawai yayi yayinda tatashi tafice don zuwa gun Asma'un

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login