Showing 3001 words to 6000 words out of 235422 words

Chapter 2 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3540

aljihunsa yacigaba da tafiya sanda ya Isa kasuwan ma laaasar tayi likis,yasani duk duniya babu me kin kyamatarsa se Mallam Hudu agurinsa ne kawai yakesamun sauki donnhaka straight shagonsa yawuce seya samu guri abakin kofa yazauna batareda yace komai ba tundaga nesa Mallam Hudu yahangoshi se ya saki murmushi yasan halin abunshi amma shima yau tsiya yake shirin yi mishi don haka yacigaba da harkokinsa yayi kaman besan da zuwansa ba shiko Imam maganar ne bazai iyayi ba,yace yazo dinne bazaiyiba don nauyi bakin sa ke masa haka yacigaba da zama ah gurin har maghrib ah lokacin ne Mallam Hudun yafito don rufe shagon yakauda Kai kaman beganshi ba seda ya rufe har ya juya yafara tafiya se yaga ko yabar Imam ba maganan zeyiba tunda daman halinsa ne don haka yajuyo yana Yareema mekakeyi anan?.....
Murmushi kawai Imam din yayi sannan yamika ma Mallam Hudun hannu sukayi musabiha kafin dakyar yace Ina wuni...
Lafiya Lau ya jikin Hajiya?...
Seda suka fara tafiya sannan dakyar yabudi baki yace "dasauki",wanda alokacin har Mallam Hudu yafidda ran samun ansa,zanje massallaci yanzu gobe sekazo za akawomin kaya ah Daf seka saukeminsu se inbaka kudi in Allah yakaimu.....
Jijjiga Kai yayi alamar to sannan yajuya yatafi, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace zanga ranar da bakinka ze budu Yarima don kuwa rashin? maganar ka nadaya daga cikin abubuwan dasuke cutar dakai da yan uwanka sannan ahankali yakuma cewa Allah ga bayinka nan cikin wani irin hankali da bantaba ganin wani cikin sa ba,ya Allah ka duba musu ka kawo musu dauki.....
Yakarashe addu'ar da Amin sannan yawuce massallaci don kada ya rasa jam'i.......

*****

Makeken parlour ne nagaske wanda yake dauke da kayan sarauta tako Ina tundaga bakin kofar zakaji hancinka na ziyartar wani kamshi medan karen dadi sannan tundaga kofar shiga wannan bangaren zaka gane cewa me bangaren bata wasa bace dubada yanda kuyangu ke da hada hada gurin ganin sun cinma aikin su babu wanda zaka gani ah zaune kokuma ah tsaye batareda yana gudanar dawani aikiba.......

Wata dattijuwa nahango zaune kan kujera irin ta sarauta? tadan kishingida jikin kujera yayinda bayi sunkai shida suna zagaye da ita suna mata fifita yayinda biyu nazaune ah gabanta daya nagyara fruits yayinda dayan na bata tana ci ahankali daka gansu kasan ah tsorace suke baswa son suyi wani mistake ayi musu hukunci don haka kowa taka tsantsan yakeyi.....

Ana cikin hakane sega wata tashigo cikin sauri tareda zubewa gaban Matar tana takawarki lafiya Magajiya, Allah yaja da tsawon kwana....
Amin duka sauran bayin suka ansa yayinda jakadiya tacigaba da magana ..
"Ranki shi dade yau me martaba beci abinci ba haka aka dawo dashi",dasauri? Magajiya tatashi tazauna,wani abinci ne aka sarrafa mishin?".......
Shiru jakadiya tayi don tana tsoron bada ansa don tasan sauran,ba tambayar ki nikeba Jakadiya?kinyimin shiru kina zazzare idanu awani dalili?....
Cikin in ina jakadayi tace"Wainar masa ce da miyan ganye"...
Dafe Kai Magajiya tayi ranta na tafarfasa jitake kaman tarufe jakadiya da duka sede babu hali tunda dattijuwa ce duk rashin imanin ta bazata bugu wacce ta girme mata ah shekaru ba don haka tace waya girka?.....
Aliya ce sabuwar me girkin me martaba da aka canza,wani harara Magajiya ta daka mata sannan tace amma ai na fada miki kifada mata dokokin abincinsa ba koban fada Miki ba?....
Wallahi kinfada uwargijiyata akasi akasamu wai tamanta ne.....
Duba daya daga cikin bayin tayi tace Surayya je
Kikira min Sarkin gidan yari da Sarkin mazga yanzunnan,tasake duban wata daga cikinsu tace kekuma laure jeki kiramin Aliyar yanzunnan,to Magajiya nansuka fice cikin sauri don aiwatar da abunda akasakasu.....

Baa Jima ba segasu sundawo dukansu duban Sarkin mazga tayi tace ga Aliya tayi laifi ayi Mata hukunci da bulala ishirin sannan Sarkin gidan yari yasata ah gidan yari cikin kuka Aliya tashiga bada hakuri amma ko kallon inda take Magajiya batayiba sema duban jakadiya da tayi tace kinemi wata tamaye gurbin ta sannan aka kara irin wannan kuskuren hardake zan hukunta tunda yakamata kina duba irin ayuukan dasukeyi bawai ayitayin duk abunda akaga dama ba.....
To uwargijiyata in Sha Allahu za a kiyaye nan gaba.......
nan ta tashi tafice jiki na bari.....

****..
Tunda suka tashi suka wanke yan kwanikan dasukayi anfani dashi da dare yayinda Amira tashiga shirin tafiya makaranta Afiya Kuma tafara share sharen gidan......
Seda tagama shirin sannan tayima yar uwarta sallama tanacewa seki shirya in an fito break se indawo ke kije tunda Yaya Almustapha baya gida....
To Amira,amma nikam da kinbi tanawa ma damunyi zaman mu tunda komunje dinma kusan kullum se an koro mu ance mutafi muje muyi aiki shiyasama ni Kinga nadaina damun kaina....

Afiya nasan da hakan sede kinsan makaranta nada anfani ah garemu kiduba halin da Umma take ciki yakamata muyi kokari muzama wani abu sabida mufidda mahaifiyar mu awannan halin.....
Hakane kuma to sekin dawo din Allah yadauramu akansu karsu zo yau batakai ga rufe bakinta ba sega laure jakadiya tazo tana hararar su tareda toshe hancinta waiku don jaraba kullum sai kunsa anzo wuri medan Karen kazantar nan ankiraku?.....
Afiya nashirin yin magana Amira tayi saurin rike hannunta alamun tayi shiru..
Laure wake kiranmu?.....
Tsaki Lauren tayi sannan tace shafa kiji ai tambayar rainin wayaune ma wannan wazai kiraku inba Gimbiya ba....
To muna zuwa cewar Amiran.....
Juyawa laure tayi tana yar wakokinta sannan tace kada ma mutum yazo mana yaga abunda zaifaru dashi.....
Murmushi Amiran tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tacire hijabin makarantar kamin tasamu kayanta tasaka sannan tace tashi mutafi.....
Babu inda zanje nikam don bazai yuyu mubar Umma itakadaiba yar kwafa Amiran tayi sannan tace sekace yau kika saba barinta kinsandai ko bakije ba se anbiyoki anci miki mutunci sannan ah tasa ki gaba gwanda muje Umma Kuma Allah zecigaba da Kare Mana ita kaman yanda yasaba haka Afiya na kunkuni ta tashi suka tafi side din Gimbiya Hamida wacce wai abaki sukejin Yar uwarsu ce ta jini,yayarsu mahaifi daya......
Koda suka karasa bangarenta samunta sukayi kwance kan gado tarungume pillow tana waya se wani murmushi takeyi tana yauki....

Sunfi minti arbain ah tsaye still tana wayan seda tagama sannan tayi wurgi da wayan tareda tashi tazauna,harara tazuba musu
"tun yaushe kuke dakin nan?"...
Tun dazu cewar Amira....
Ku bakusan mutum nawaya ku fita bane ko gulma da munafurcine yasaku tsayawa don jin abunda nike fada?....
To duk iskancina bekai na matsiyacin? Yayanku ba me lalata da 'ya'yan mutane.....
Ran Afiya ya baci tanashirin magana Amira tadamke hannunta kamin Amiran tace kiyi hakuri Gimbiya bazamu sakeba...
"Better"...
To your normal work as usual Kuma daga yau kada kuyarda insake sawa ah kiraku don na lahira seyafiku jin dadi wallahi.......

Dasauri Amira tashiga bandaki don hada mata ruwan wanka yayinda Afiya na yamutsa fuska ta isa ga wurin kayan Gimibiyan tamika mata towel seda ta daura sannan tashiga bayi lokacin har Amiran tagama hada mata ruwan wanka don haka tazo tajona yar uwarta suka kama gyaran dakin Gimbiya Hameedan saida suka gama tas kowa ranshi ba dadi sannan Afiya tafita zuwa bangaren kitchen don karbo breakfast din Gimbiya yayinda Amiran tashiga taimakawa Gimbiya wurin gyara jikinta bayan tafito haka aikin kenan kullum su suke mata komai harta tausa da bata abinci sannan suyita mata fiffita har saitace ya Isa........
*****
*London*

Kwance yake kan makeken gadonshi yayinda 'yan mata biyu ke kwance jikinshi kowa da irin harkar da take yimishi hankali kwance shikuma se karban sakwwnni yakeyi suna cikin badalar su ne wayarsa tashiga ringing jiki ba kwari yace

Can someone disconnect that call for goodness sake!ynda yayi maganar seda ya tsorata duka matan turawa biyun Justina dake kusa da bedside drawer da wayan ke kai tayi saurin daukan wayar yayinda dayar tacigaba da yamutsashi yana ta surutai, tunkan tayi disconnecting har ya katse call din sekawae ta mayar kafin tasake ankara wayar tasake daukar ruri ture joy yayi daga jikinshi yana huci tareda jan gashin justina"didn't I ask you to disconnect that damn call?"....
Kokarin kwace kanta tashigayi tana"I'm sorry Prince"...
Wurgi yayi da ita Itama yana"get out of my room now!"....

Jikina bari suka tashi sukafice dukansu still wayar na ringing se sake Kira akeyi Kamar kayan jaraba,tsaki yasaki tareda shafa kanshi sannan yadauki wayar tareda picking call din......
Yarima inaka shigane inata kiranka baka dauka?....
Wani kululun bakin ciki yakeji because he's busy enjoying with those girls amma Magajiya ta bata mishi budget cikeda bacin rai yace Mama darene fa kinsan by this time yakamata Ina bacci amma kika kirani ko awani dalili oho!.....
Cikin sauke murya Magajiya tace haba autana shikenan ban isa inkira Baby boy dina ba inason jin muryarsa,kasan dai nayi kewarka ko?....
Turo baki yayi kaman wanda yana gabanta, I'm sorry Mama just that kinbata min budget dina ne,sorry to Son,ya kake,yaya London da makaranta inafatan komai na tafiya smoothly....

Gyara kwanciya yayi kan makeken bed dinshi don ya lura yasamu opportunity yanzu because he's running out of cash daman yanata tunanin taya zai tunkari Mai martaba da maganar tunda ko sati biyu baiyiba daya turomasa 2million ah account dinshi itakuma uwartasa bayason kiranta sabida kullum inyakiradin maganar yadawo gida takeyimishi......
shagwabe murya yayi inafa smoothly Mama babu cash and you know kudi is everything right, I'm nothing without money.....

Lokaci guda hankalinta yatashi tace dagaske baka da kudi shine baka Kira ka fadamini ba Sulaiman....
To ai kedinne Mama dana kiraki seki fara maganar dawowana gida shiyasa banson Kira amma wallahi banida kudi. ..
Dan kwafa tayi sannan tace zanturoma kudi amma maganar zuwa gida yazama dole Yarima rabonka da gida kusan shekaru biyar ahaka kakeson abaka sarautar kodanma Kai daman wan Babanka ka dauko bakason abun kwata kwata toka rufamin asiri Kaine hope dina Yarima babu wanda nakeson yagaji sarauta Kamar ka inkuma baka dawo kusa damu kafara gudanar da duties dinkaba bana tunanin Mai martaba zeji dadin haka......
Yamutsa fuska Yarima yayi,to ai Kinga matsalar ni Mama banason sarautarnan kema kinsani bama nina cancanta ba tunda I'm the Youngest son,no one deserves the throne other than Brother Almustapha yakarashe maganar yana magiya....

Kai! Magajiya tayi wata irin tsawa wanda saida Yarima Sulaiman ya tsorata harcikin dodon kunnensa sannan ahankali yatashi daga kwance yazauna akan gadonshi.....
Cikin bacin rai Magajiya tace idan har nasake jin irin wannan maganar ah bakin ka ranka bazai maka dadi ba wallahi ko sunan yaron nan nasake ji abakinka ranka inyayi dubu seya baci and I warn you for the last time kafin satinnan yakare ka tattaro naka ya naka kadawo Nigeria inbahaka ba nidakai ne acikin gidannan sannan takatse wayar tana hucin takaici.....
Furzar da iska yayi ah hankali sannan yayi wulli da wayar"Damn it,I told her I'm not after the throne meyasa baza abarni in huta ba miyasa baza a bar mutum ya shakata ma rayuwarsa ba,I don't want to be caged in there.i want to be a free Man,I mean a free Man!"yakarashe maganar yana tsakin takaici yasan Magajiya she will not take her words back tunda tace yatafin as a command dole yatafin if not shikanshi bazai ji da dadinba don haka yasama ranshi dole yakoma Nigeria cikin satinnan din......

****
Yau tunsafe bayan tagama taya Ummi ayyuka tashige daki ta dale gado don karanta wani littafi da Aisha tadameta takaranta wai ya hadu sosai,aikuwa littafin bakaramin tafiya da hankalinta yayi ba waishi *ALKAWARI BAYAN RAI* na *SUMAYYA ABDULKADIR*? tana ganin masu karanta Hausa novel amatsayin marasa aikin yi dakuma bata lokaci seyau ta tabbatar ba bata lokacinsu sukeba tunda gashi tunda tafara da safe bata iya ajiyewa sallah ne kadai ke tadata daga kan gadon sekuma in Ummi tai Kiranta each and every page takaranta she'll be yearning to know what will happen next se yanzu Allah yabata ikon gamawa....
Lumshe idanunta tayi ahankali tana tunano abubuwan dasuka faru cikin littafin,towai daman haka soyayya yake?
haka mutum yakeji when he's in love,haka yake reacting dakuma sacrificing...
dan shiru tayi nadan dakiku sannan ta lumshe idanunta,when will?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? she fall in love and who will she fall for,ya yake? will she be lucky to get the love in return kokuma son maso wani zatayi,ya gayen ze zama dogo ne ko guntu, fari ko Baki, kyaukyawa ko mummuni duka babu wanda tasani dan ware hannun ta tayi ahankali sannan tafurta "only God knows,but I hope he'll? be dashingly handsome in everyway"......

Murmushi ne yasubuce mata sekuma taji kunyar kanta, ahankali tadan bugi kanta"Ya Allah what am I thinking?"....

Jitayi Munir namata sallama ah kofar dakinta don haka ta ansa sannan yace Mommy na kiranki....

Wurgi tayi da pillow dinta sannan tace to inazuwa, Allah sarki yau Mommy tunsafe bata ganni ba dole tanemeni.. .

******

*****
Yauma kaman jiya yaje kasuwa shagon
Mallam Hudu seyasake neman guri yazauna batareda yayi magana ba murmushi Baba Hudun yayi sannan yafito yasamo shi zaune,dan dafa shi yayi sannan yace daga makaranta ka fito ne?......
"Ina wuni",yagaishe shi ciki sanyayyar muryarsa...
Lafiya Lau Yarima,yajikin Hajiyan?,murmushi kawai yama Baba Hudun batareda yace komai ba suna nan tsaye sega motar kawo Kaya ta zo nan Almustapha yashiga aiki najido kayan yana shigar dasu shagon inda sabo yasaba don wannan shine aikin da Baba Hudun kesashi yi har yadan samu abun rikewa ah hannunshi yakuma saima kannensa abunda zasu sa ma bakin salatinsu dukda ma wani sa'in yakan dauki kyautan kayan abinci yabasu,sede ba kullum za ayi maka ba dole watarana mutum ze gaji shiyasa shima Almustaphan yakeson yin aikin yasan yasamu da guminshi ne bawai yazama maroqi ba seda yagama kwashe uban kayayyakin sannan mallam Hudun yamasa sannu tareda cewa to ga kudin ka nan Yarima.....
Lumshe idanu Almustapha yayi bayason wannan sunan kwata kwata inda Mallam Hudun yasan yanda yakeji inya kirashi da wannan sunan dakoda wasa bazai taba koda kwatanta kiranshi da sunan ba sede duk yanda yakeji din bekai girman darajar Mallam Hudun dayake gani ba don haka bazai iya budan baki yace masa bayason sunan ba....

Dukar dakansa yayi kaman bazaice komai ba se can sannan yace ka ajiye kudin agunka kawai zanturo Amira, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace to amma dai katafi musu dawannan yanzun nan Mallam Hudun yajuya cikin shagon yadauko taliya da macaroni bibbiyu yasaka mishi ah leda hadeda ledan maggi da Onga roll daya se Mai kwalba daya yace to gashi ka Kai musu ko kafin Amiran tazo.....

Karba yayi batareda yace komai ba sannan yabar gurin mallam Hudun da kallon tausayi yabishi dashi sannan ya jijjiga kanshi yakoma cikin shagon nashi.....

Waishin wanene Almustapha?
Menene asalinsa,menene labarin masarautar Zazzau,meyasamu Ummi?,meye dalilin dayasa Almustapha suke cikin wannan yanayin?....

Kucigaba da bin Zeeneert don jin yaza akayata....

Vote
Comment
Share!

*Zeeneert*
[3/23, 5:12 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad!....

*Page 3*....


*ASALINSU*....

Sarki Sulaiman babban sarki ne acikin Nigeria da babu yankin dazakaje ba asan dashiba tsabar tashen da mulkinsa yayi dama kuma adalcinshi ga talakawanshi,asalin iyayenshi nomads ne(Wanda akafi sani da fulanin daji) tun kakanni wanda basu da takaitaccen gurin zama suna yawo ne depending on the weather tayanda zasu samu su ciyar da dabobbbinsu dama su kansu ahakan ne har Allah yasauke su acikin garin Zaria wanda tun alokacin ba abakin komai take ba don mutane tsirarru ne kawai agarin.tunda sukazo garin Zaria suka ji dadin zama agarin se suka kasa yin gaba suka kafa gida da kasuwancin su wanda ahakan ya bunkasa har suka saba da mutanen gari akazama daya. with time population na karuwa ah garin har garin Zaria yafara zama babban guri alokacin da Allah yadauki ran Sarkin garin bashi da magajin daza abama sarauta don haka akanemi wanda yacancanta aka bama wanda shine mahaifin sarki Sulaiman shima bayan shekaru tsufa taxo se mulki yadawo hannun sarki sulaimanu wanda alokacinshi bakaramin taka rawar gani yayiba don ganin yayi wani abun alfahari ah yankin Zaria haka rayuwa tacigaba, Sarki Sulaiman yazama abun soyuwa ga kowa bama a zaria kadai ba ah kasar Nigeria bakidayan ta.matar shi daya kwallin kwall wanda tunda ya aureta basu samu haihuwa ba har na tsawon shekaru takwas hakan Kuma besa yakara aureba dukdama irin takuramasa da jama'a sukeyi da irin hakurinshi dama Kuma addu'a dasukeyi gakuma subjects nayimusu Allah yabama Zuwaira ciki kaman da wasa bakaramin farin ciki sukayiba lokacin har yar kwarya kwaryar walima seda akayi sanda Zuwaira tahaihu 'da namiji tasamu nanma murna sosai akayi ranar suna akasama yaro suna Almustapha wanda mutanen gari ke kiranshi da Yarima tun haihuwarshi Zuwaira da Mai martaba suka dauki son duniya suka daura ma yaron komai yace yanaso za ayimishi har tasowanshi, Almustapha yazamanto me kiriniya da son yawace yawace da freedom,tun yana shekara biyar akeson fara koya mishi swordfighting da hawan doki amma kwata kwata bayaso sabida baida passion for sarauta kwata kwata wannan abun baidamu su Sarki ba se suka barshi ah tunaninsu yarinta ne with time zefara dakanshi, Yarima Almustapha nada shekara bakwai Allah yasake bama Zuwaira ciki wannan karan anyi murna sosai don harta fidda rai ga haihuwa sede murnar batakai na lokacin haihuwar Almustapha ba

haka akayi suna lafiya akasama yaro Abdulrahman tunda aka haifi Abdulrahman yazama abun so acikin masarautar sabida yaron akwai shiga rai haka Almustapha yadauki son duniya yadaurama tilon kaninshi komai yasamu na Abdulrahman haka Abdulrahman dinma yataso yanason dan uwanshi komai tare sukeyi hakanan Almustapha bayason laifin kaninshi komai yana shigan masa sede abunda ya banbantasu Abdulrahman na matukar son sarauta tun yana shekara biyar yake koyon fada dason hawan doki daduk wani activities na sarauta,gashi da kwazo da kaifin basira gakuma son manyance alokacin ne Kuma akafara matsama Almustapha yadinga koyon abubuwa sede ranshi bayaso ko anfara koya mishi seya gudu akwae ranar da sarki Sulaiman yakirashi yayi mashi fada sosai wanda hakan betaba faruwa ba yayi kuka sosai sannan yadau alwashin fara yin abunda mahaifinshi keso don bayason bacin ransu kwata kwata don haka yafara participating dukda kuwa ranshi bayaso,bakaramin dadi Mai martaba yajiba ga canzawan 'dan nashi sekuma yawanci karfin koyon yakoma kan Almustapha aka daina bama Abdulrahman din attention sosai wanda hakan bakaramin sosa mai rai yayiba sede be nuna ba saboda shi yarone dabai cika tada hayaniya ba bekuma cika nuna damuwarshi ah fili ba sede yakebe gefe yayi kukansa me isansa yashare hawayensa, Abdulrahman yakasance yaro meson rubuce rubuce barinma akan abunda yafaru dashi dakuma abunda yakeso tunda yafara wayau yakan zauna yazana kanshi ah zaune akan kujerar sarauta kokuma yana tsaye rikeda sword jikinshi da kayan alfarma shiyasa koda yalura bazai samu sarautar ba anfison abaman Yayanshi seya rubuta cikin diary dinsa how he felt and the rest.....

Almustapha cikin yan watannin daya biyo baya yalura Abdulrahman yadaina sakewa kaman da don haka yatambayeshi amma besamu ansa daga gareshiba don haka yashiga bincike wanda ahakan ne har ya karanta diary

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login