Showing 9001 words to 12000 words out of 235422 words

Chapter 4 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3533

itatuwa yace, insha Allahu watarana komai zezama labari......inamiki fatan alkhairi.....
Jijjiga mishi Kai kawai tayi yayinda Almustapha yadubeshi yace don Allah ka kwaso mana gwala gwalan Ummina dakuma dukwasu sarkokinta tanan ne zamu samu kudin tafiya can din...
Shafa kan Almustapha yayi ahankali sannan yace to kujirani anan Allah yasa ba mutane sosai agurin...
Amin,nan suka samu gindin bishiya suka zauna yadan kwantar da kanta akan cinyar yarasa ta ina zai rarrrasheta,shibe iya rarrashiba besan ya akeyiba se sukayi shiru dukansu yayinda ita tana hawaye kadan kadan.......

Kukan nata harcikin ranshi yakeji don haka seya damke hannunshi tareda lumshe idanunshi sunkai two hours agurin kafin Mallam Hudu yadawo seda yarakasu kasuwa suka saida wasu sannan yarakasu chemist akayi mata dressing goshinta sannan suka shiga motar Maiduguri wanda daganan ne zasu wuce Chad din, alokacin da sukayi harkokinsu Allah yataimakesu labari begama baza gari ba......

Sanda suka Isa Chad mahaifin Khairiya yace bazai karbe ta ba don already yaji labarin komai taje tasayar da mutuncinta amatsayin Yar Babbar gida bakaramin kuka tasha ba sannan yace daga ranar ya yanke alaka da ita har abada sannan beyadda duk wani nashi yataimaketa ba,ahaka suka juyo Nigeria itada Almustapha don cewa tayi dole ma tasan yanda zatayi tasamu magana da Abdulrahman sede kash koda suka dawo Magajiya taki barinta kwata kwata seda tayi ta Mata magiya wanda kullum ah wajen masarautar suke kwana dukda kuwa cikin dake gareta sannan tabarta......
Bakaramin farin ciki tayiba da tasamu zataga Maimairtaba sede to her own surprise tunda tashiga gabanshi yanuna besanta ba amatsayin bakuwa yaganta tambayartama yayi damai zai taimaka mata sekawai tafara hawaye babu kakkautawa kallonta yashigayi ahankali seyaji yanason sanin miye matsalarta duk da baisanta ba seyakeji deep inside his heart yasanta kaman yanada wata alaka da ita sede besan na menene ba, Magajiya na ganin irin kallon da me martaba kema Khairiya setasa aka fitar da ita nan takaita side dinta sannan tace mata Mai Martaba yayi loosing memory dinshi due to the shock dayasamu na abunda yafaru sannan likita yace ba ason atuna mishi da abun yafaru sabida ze iya zama hadari ga rayuwarsa kuka Khairiya tashigayi tana innalillahi wainna ilaihir rajiun,wannan wace irin kaddarace ita yazatayi da rayuwarta....
Koina tashiga basauki anata hukunta ta akan laifin dabatasan dashiba......

tsaki Magajiya tayi sannan tace ke munafuka kiyi abu sannan kice ana hukuntaki akan abunda bakiyiba Mai Martaba yana cikin wannan halin ne adalilinki kinajina.....sabida haka babu ke babu zama amatsayin matarshi gwanda ma ki tattara kikoma inda kikafito zefiye miki don acikin garin babu inda zakije akarbe ki da mutunci wasuma yunkurin kasheki zasuyi.......
Sa hannu Khairiya tayi ah baki tana kuka sannan tace kitaimaka mini don Allah kada ku koreni anan banida gurin zuwa,banida inda yafi nan banason nayi nesa da Mai Martaba tsaki Magajiya tayi sannan tace bakida matsayi acikin masarautar nan sede in matsayin baiwa zaki zauna......

Cikin kuka tace wallahi nayarda,nayarda zan zauna amatsayin baiwa har lokacin da mai martaba zai gane ni ya fahimceni, murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace ko bayi sesunfiku daraja ah gidannan.....

Nayarda Magajiya,nayarda daduk sharrudan ki......

Hindatu najin duk abunda yafaru taje tasamu Waziri tafadamishi ga hukuncin da Magajiya ta yanke don haka yazo yasamu Magajiya yanuna mata abunda tayi bata kyauta ba Kuma indai yana ubanta baza ah mayar da Khairiya baiwa ba tunda Mai Martaba bashi ya yanke hukuncinnnan ba ana iya barinsu subar masarautar sunemi gun zuwa kokuma inzasu zauna se abasu Yar karamar gida cikin nan tunda ita ta bukata......

Dahaka aka yanke hukunci aka bama Khairiya wata Yar karamar gida acikin masarautar wanda ko talaka akabashi wannan gidan kyauta seyayi mita amma bata damuba fatanta kullum Maimairtaba yazo nemanta batada wani addu'a daya wuce wannan har Allah yasauketa lafiya tasamu yan biyu mata inda tasamusu Amira da Afiya....

Almustapha kuwa tunda haka tafaru aka haramtamishi zuwa duk wata makaranta ah garin don koyaje kullum cikin tsangwamarsa akeyi shi shegene,agida be hutaba haka ma ah school hakan kuma besa yataba fadawa mahaifiyarsa halin da akecikiba don aganinshi ze Kara mata wani damuwar ne bayan wanda take ciki ayanzu......

Haka rayuwa tacigaba harma daga karshe yadawo makarantar da aka gina ma 'ya'yan bayin na cikin masarautar inda nan yakarasa secondary school dinshi,su Amira ma sunfara wayau alokacin sede suma gurinsu babu wata sassauci kullum cikin tsangwamarsu da zaginsu ake gakuma bayi da aka maida su na karfi da yaji......

Abinci ba abasu ah masarautar hakanan babu wani tallafi da akeyi musu, Mallam Hudu dai shine me taimakonsu da abinci sekuma dan dakon da Almustapha keyi mishi seyadan samu wani abu dahaka Almustaphan ya yanke shawarar shiga jami'ar Ahmadu Bello University koda kuwa cin namansa za anayi kullum acikin makarantar he needs to study,he need to be something better in life,he need to be independent shiyasa ya zana jamb and yafita da score mekyau inda babu bata lokaci
Suka bashi admission, MBBS daman abunda yayi applying kenan, Mallam Hudu ne yataimaka mishi gurin biyan kudin makaranta nan yafara, the first year dayayi ne smoothly with great result dukda kuwa yazama abun kyama ga kowa don rumor ake agari shi dan iskane Kamar uwarsa bashida aiki se lalata 'ya'yan mutane da shaye shaye wanda duk wannan maganganun daga tushen Magajiya yafito, abun baya damun shi inda sabo yasaba yana living life dinshi all alone ne,gashi da kyau da aji ga Kuma ilimi uwa uba amma hakan besa mata suna xuwa kusa dashiba sabida kowa tsoronshi takeyi......
Ah second year dinne Ummin su tafara rashin lafiya har yakai ga tasamu stroke, bakaramin tashin hankali yashiga ba awannan lokacin haka suka kaita asibity anma babu kudin yi mata treatment don haka akayi dismissing dinsu wannan shine dalilin fara shaye shayen Almustapha sabida abubuwa sunmishi yawa,zafi yamishi yawa right from his childhood he experience alot and now it's the matter of his Mother's health he can't bear loosing her,he want to protect her she's all that yakedashi sede ta Ina zefara samo kudin?...
Babu,bashi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da abokin dazai tambaya,bashikuma da dan uwan dazai tambaya sannan be Isa yatambayi wani babban mutum agaribama sede awulakantashi don haka yashiga damuwa sosai wanda inbayasha kayan maye ba bayajin sassauci ah ranshi,anacikin hakane Sulaiman dake London bejima da tafiya ba yaji labarin rashin lafiyar Ummin don haka yasa akanemai number Mallam Hudu don Almustapha bashida waya(aganinshi inya rike wayar ma wazai Kira,wayane dashi dahar zeso jin muryar sa bayan kowa kyamatarsa yakeyi),bayan Sulaiman yayi magana da Mallam Hudu ne yaji matsalar komai sannan yace ze turo masa kudi amma kada yace ma Almustapha shiyaturo don bazai karba ba domin Sulaiman yalura Almustapha ja baya yake dashi sabida mahaifiyarshi shikuma har cikin ransa yakejin dan uwanshi Kuma yakeson shi tsakani da Allah.......

Ahaka akafara treatment din Ummi har aka rubuta mata drugs takesha, sannan yacigaba da zuwa school watanta uku ah asibity aka sallame ta haka suka dawo da ita gida sede adaga akwantar tun su Amira na shekara takwas suke wahala da mahaifiyarsu yayinda shikuma yake zuwa makaranta......

Suma Kuma sukanje nacikin masarautar ahaka rayuwa tacigaba, Almustapha nada kwazo wanda harsu kansu malaman sukanyi mamakin baiwar da Allah yayima yaron he never fails any course nor any practicals har final year dinsa wanda suna shirin gamawa,sede ranar da zasuyi final practical exams dinsu jikin Ummin shi yamatsa sosai suka koma asibity inda yayi missing exams din wanda hakan yayi leading to se yayi spill na karatunshi haka the following year din Kuma thesame exams dazaiyi ranar anbata masa rai seyasha giya yakwanta bacci beje yayi exams dinba se wannan shekarar dayasake yin registration yana fatan Allah yabashi ikon yin jarabawar yasamu yarabu da makarantar dama Kuma tsangwamar dayake sha acikinta wanda yayi almost 8years yanzun yana enduring.......yanason ya huta dana makarantar atleast amma abun yamishi yawa ga Magajiya ma bata barshi ba sharrin yau daban na gobe daban,mutanen gari ma insun debo talaucinsu suzo sumishi sharrin sata ahukuntashi sannan abiyasu.....
Sulaiman kuwa tunda yatafi yaki zuwa gida sabida wani manufa da Magajiya tasa agaba wanda shi anashi ganin bazai iya cika mata burinta ba abu daya yasani babu wanda throne dinnan ya cancanta da kaman Almustapha sabida duk wani rumor da akeyi daduk wani magan gane magan gane da akeyi betaba sama ranshi Almustapha ba dan uwanshi na jini bane Kuma har abada babu mai ciremishi wannan raayi shiyasa yadaukar ma kanshi alkawari no matter how hard it may be shibazai karbi sarautan Zazzau ba face Yayanshi Almustapha wannan kenan.....

*&*&

Yana zaune akan wani fancy chair, yanzu yafito daga practicals jikin shi sanye da labcoat yayinda idanunshi kesanye da eye glasses,lumshe idanunshi yayi ahankali yana tunanin duniyar baki dayanta dama abubuwan dake cikinta dakuma irin rayuwar dayayi tun sanda yayi wayau,yasandai 12years of his life shidan gata ne babu abunda yanema yarasa,kowa sonshi yakeyi hakanan kowa nan nan yake yi dayi he never thought for once his life will turn out to be this way tunda yake betaba sama ranshi zeyi wahala irin wanda yakeyi ayanzu ba,shiyasa akace never be too proud of who you're because everything can change,inma kudi kake ji dashi ze iya karewa hakanan inma mulki kake ji dashi shima karshenta na iya zuwa tunda akwai mutuwa,akwai rashin lafiya akwai Kuma fin karfi,sannan duk mulkin ka ko arzikinka kada ka wulakanta nakasa dakai because you might end up being like them,ya yarda dawannan maganar tunda gashi shi akaran kanshi yafaru bama akan wani ba....from sanda yake da shekaru 12 zuwa yau dayake da shekaru 29 yana neman talatin, meaning shekaru 17 kenan rabonshi dasamun farin ciki he has been in this situation for good 17 years yana iyacewa acikin shekarun babu ranar dayayi murmushi wanda yakai har cikin zuci sedai yayi na yake ahankali yafurta "when will all this come to an end"kafin ya furzar da iska ahankali....
Sekuma dayar bangaren zuciyarshi tace"very soon Imamu Almustapha,very soon in Sha Allah".........





To fans yakuka ji labarin Almustapha,if you were in his shoes yazakuji,meye zakuce akan Magajiya Matar sarki......inajiran jin ra ayinku

Vote!
Comment
Share...

*Zeeneert*
[3/23, 5:13 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad..

*Page 4*


Bude idanunshi yayi daga lumshesun dayayi sannan yadubi wristwatch din hannunshi dasauri yatashi don tunawa dayayi lokacin shan maganin Umminsu yayi ahaka yafara tafiya don yawuce gida duk inda yawuce seyaji ana kuskus kokuma ah tsaya ana kallonsa ko wasu na nuna shi,shi abunma mamaki yakebashi dubada yanda mutane basudamu da nasu al amurarba sannan baswa duba nasu flaws din sena wani.abu dayane yasani cikin su babu mai kusantar shi da maganan duka kowani abu so far as he's in his right senses sede suzage shi ko su fadamai maganar banza wanda shikuma ko kallo basu isheshiba,the only state dasu ke ci mishi mutunci shine when he's drunk......

Ayanzu ma tafiya yakeyi yanashirin barin harabar makarantar wasu yan mata ne agabanshi suna tahowa 'dayar se kallonshi takeyi kamar wanda zata cinye shi lura da abunda takeyinne yasa tagefen nata tayi saurin rike hannunta gam tanacewa muyi sauri Aisha mudauko kayan kada tailor dinnan yagudu......
Wabce hannunta Aisha tayi sannan tace Bebe kibarni bakiga hadadden gayen dana gani bane takarashe maganar tanashirin zuwa gurin Almustapha,damkota
Muniba tayi cikin sauri sannan taje saitin kunnenta tana"don ubanki inkinaso kigama anfani ah idon duniya sekije ki ai"....
Dasauri Aisha takalli kawartata with questionable look irin bangane me kike fadi ba,cikin rada da tsoro Muniban tace shine Yarima Almustapha Aisha,aituni jikin Aisha yafara 'bari sema tayi gaba tabar Muniba agurin tana yau na shiga uku na lalace Muniba cewa fa akayi inmutum ya yarda yahada ido dashi toseyayi anfani dashi,nashigesu na Allah yasa bamu hada idanuba Aisha takarashe maganar kaman zatayi kuka tana tatttaba fuskarta......
Yar dariya Muniba tayi sannan tace keba uwar jaraban son maza ba sekin debo ma kanki ai.....

Wallahi nadaina Muniba dagayau kawai yamin kyau ne shiyasa,danasan shine Almustapha koma nasan zamu hada hanya aiko makarantar ku bazan zo ba,nikam wace irin kaddarace takawoni cikn SAMARU yau,dariya Muniba tayi harda rike ciki tana to ya isheki Kuma kina exaggerating abun kuma.....

Duka Aishan takaima Muniba din don ubanki ba dole ba dondai baki taba jin abunda ake fada akanshi baneba shiyasa and it happens I swear because har hukuntashi mahaifinsa yakeyi.......ammadai yayi asara,ga kudi,ga kyau,ga iya gayu amma yasa ma kanshi wannan jarabar wannan wace irin rayuwace kaman ancema yana tsafi ko Muniba?........

Tsaki Muniban tayi sannan tace ke matsalata dake yawan surutu nima bansani ba I just know that ko hanya banason hadawa dashi sabida halayensa danake jin labari,kede kibar zancen kawai kadama muja ma kanmu,zomuje indauko kayan mukoma gurin macucin tailor dinkin nan......
To nadaina Aishan tafada cikeda fuskar tausayi daka ganta kasan ah tsorace take baki dayanta....

Sanda ya isa gida samun su Amira yayi suna cin abinci,sannu dazuwa sukayi mishi sannan Amiran tazubo mishi abinci bedamu da kanshi ba matsawa yayi kusada Ummin sannan yajingina mata pillow ya kwantar da'ita ajikinshi sannan yayima Amiran alama data miko mishi plate din abincin haka yashiga bama Ummin abinci tanaci ahankali harseda tanuna takoshi sannan yadauki drugs din yabata tasha.......
Kallon fuskarta yayi sannan yace ahankali kaman wanda bayason magana"How are you feeling Mother?"......
Lumshe idanunta tayi alamun dasauki,bekuma cewa komai ba sema cigaba da kwanciya datayi ah jikinsa yanajin su Afiya suna hira abunsu jefi jefi kallonsu yashiga yi cikeda tausayin kannen nashi.......

*****
Sadiq da Munir na playing game agaban Tv yayinda Asma'u tana ironing school uniform dinsu Aliyu yashigo yana dariya kasa kasa"wai ina Asmeey ne".....
Turo baki tayi tanajinshi taki kula shi don tasan yaganta neman magana kawai yakeyi kara daga muryarsa yayi "Asma'u!,wai inatake ne yadubi su Sadiq dasuke game yace bakuji ina neman Ma'u bane dabazakuje ku kiramin itaba".....
Sadiq ne yace Allah Yaya Aliyu bamujiba hankalin mu baya gunka we were busy playing game.......
Eh ai daman ku inkuka fara game ba asamun hankalin ku maza kukaje kuka kiramin ita yanzu if not nakwace kayan game din Kuma bazan bakuba kwana kusa.....
Munir ne yatashi dazuman yaje yakirata don yaman tama tana guga ah parlourn nan yayi arba da ita turo baki yayi sannan yakoma mazaunin shi ashema gatanan......
Adda kinaji anata kiranki shine kikayi shiru,harara ta dalla mai sannan tace ai yaganni ....
Dariya Aliyun yayi sannan yazauna ah kujerar dake kusa da inda take gugan yace"lallai yarinyar nan kinraina ni wallahi,innaganki zanta kwalla miki kirane?,kodan Kinga muna sonki shine kike mana yanga.....
Kai Yaya Aliyu nifa bahaka bane ba.....

Ware hannu yayi sannan yace to miyene,ai na miki text cewa he'll be coming this evening amma kinayi kaman bakiga massage din ba,nakuma Kira ki several times baki dauka ba.....
recently nagani kuma Ummi tasani aiki, hararanta yayi sannan yace kiyima Ummi sharri kinji,ba laifin ki bane don Kinga abokina yanason kine.....

Yar dariya tayi sannan tace nashiga uku Yaya Aliyu kanasani inajin kunya.....
Rankwashi yakai mata,kunyar banza inzaki tashi kije kishirya gwandama kitashi don yadameni wallahi....
Kashe socket din tayi sannan tace nifa kabashi hakuri babu inda zani Allah,Inka takuramin zanfada ma Mommy wallahi......

Rike baki yayi yana kallonta sannan yace ke ai bantaba ganin bakauye irinki ba wallahi dama Asiya yace yanaso dukda rashin kunyarta bazan ji haushi ba because bazata watsamin kasa ah idanu ba....
Murmushi tayi sannan taninke sallayar datayi gugan kai tana naji bakomai yanzuma se inkirata taje be baciba, tashi yayi yana banaso nima inada baki da kafafuna kekuma kiyita zama kina koran samari naga ranar aurenki ....
Dariya kawai tayi batareda tace mishi komai ba har ya isa bakin kofa yajuyo yana Darling Sisto tsayamana....
Juyowa tayi tana kallonshi 'dan marairaice fuska yayi yana taba cikinshi...
"Allah tunsafe cikin nan bega komaiba".....
Dariya tayi"kaje Asiya tanema ma abinci mana"...
Sake marairaice murya yayi kaman Karamin yaro"haba Yar kanwata shalelen Daddy,Ummi da Mommy kitaimaka mana"....
Toshe kunnuwanta tayi tana dariya"Kai Yaya Aliyu Matarka tashiga uku da zakin baki",kanne mata ido daya yayi sannan yace"ance miki nidin nawasa ne.......
to naji barina ajiye kayan nan zanzuba insa akawoma don bazan yarda inhadu ma da abokin ka ba inma wayau kakemin.....
Dafe Kai yayi don ya lura plan dinshi couldn't work se kawai yayi gaba abunshi.....
****
Kuka take sosai wanda tundazu Laure kanta takasa lallashinta don haka tatashi don zuwa ta sanar ma Magajiya ah bangarenta,tana shiga ta zube kasa tana mika gaisuwa sannan tace Uwargijiyata akwai matsala....
Kallonta Magajiyan tayi cikeda damuwa sannan tace inajinki....
Kai tsaye Laure tace Gimbiya Hamida ke kuka tun dazun nakasa lallashinta,tashi Magajiyan tayi sannan Lauren tabi bayanta nansuka fice zuwa side din Hamidan duk inda suka wuce bayi nazubewa kasa suna mika gaisuwa koda suka isa Laure daga waje ta tsaya yayinda sauran ma suka fito don basu guri........
Zama Magajiyan tayi gefen Hamidan yayinda tayi saurin fadawa jikinta tana kuka Mama yadaina sona,wai yafasa aurena bansan yazanyi ba bazan iya rayuwa babushiba.......
Bubbuga bayanta Magajiya tadingayi ahankali tana comforting dinta seda tayi shiru sannan tace dago ki kalleni Hamida, ahankali tadago tana duban mahaifiyar tata"yanzukam inaganin yakamata kihakura da Sa'id dinnan tunda shi bainuna dagaske yakeyiba daman tunda mun zuba miki ido ne kuma bawai daman munasonki dashi ne ba,kina Yar gidan sarauta Yar babban gida kyaunta kishiga irin wannan gidan,Hamida 'ya'yan sarakuna nawa sukazo neman auren ki amma kika bujure...
tukunnan kinaduba shekarunki kuwa,kina neman ashirin da shida yanzu babu maganar dabamaji ah gari amma ahaka muka toshe kunnenmu mukayi kaman bamuji ba to ya Isa hakanan Hamida, you've to think twice yakamata kiyima kanki fada zanbaki nan da sati biyu kiyi tunani inbaki samu mafita ba nikuma zanyi ma Maimartaba magana yabama daya daga cikin masu neman auren ki izini su turo......
Kuka sosai Hamidan keyi "Mama karkimin haka shikadai nikeso bazan iya rayuwa inbabu Shiba"....
Lumshe idanu Magajiya tayi sannan tace munmiki kokari ai,Kuma bana ganin Sa'id nada niyar aurenki sabida haka kiyi hakuri kawai 'yata haka tacigaba da rarrashinta hartayi shiru tasan inbahaka tayima Hamidan ba bazata dawo cikin hankalinta ba yanzu kusan shekara goma suna tareda Sa'id amma kullum akayi maganar aure seya kauce gashidai shiba dan kowa......

****

Koda Magajiya takoma sashinta sega talatu tazo nan tazube gabanta tana mika gaisuwa kafin Magajiya tabata izinin zama.....
Kallonta Magajiyan tayi sannan tace wani labari kika kawomin?.....
Numfasawa talatu tayi sannan tace Uwargijiyata yau sati biyu kenan rabon da Yarima Almustapha yasha kayan maye.....
wani tsawa Magajiya ta daka mata"don ubanki waye Yariman?"....
Jiki na 'bari tace yi hakuri ranki shi dade subutar bakine......
tsaki Magajiyan tayi sannan tace "naji tashi ki tafi sannan kifada ma Hilun yacigaba dasamin idanu aduk wani al amuransa banason yabata komai".....
In Sha Allah zan fada masa nagode!...
Tsaki Magajiya takumayi sannan tace tashi kitafi yau kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login