Showing 108001 words to 111000 words out of 235422 words

Chapter 37 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3478

it was a very good idea Magajiya".......
Cikeda damuwa tace"Suma sun nuna baswa so ne kaman".......
Murmushi yayi sannan yace if baswaso dinkam bazan takurasu daga haka dubi Asma'u yace"Daughter bazaki iya aikin danasaki bane,feel free and tell me what's on your mind kinji".......
Dan sunkuyar dakanta kasa tayi kafin jin idon kowa nakanta harda na Almustapha kuwa........
Wasa da fingers dinta tashigayi kafin tace"Zan iya Abba"......
"Are sure?".....
Kai tsaye tace"I'm very sure Abba,duk abunda kasani yi nasan kayarda dani ne shiyasa and I know you'll always guide me when I'm wrong"........
Murmushin jin dadi yayi sannan yadub????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i Zaliha dakejin kamar zuciyar ta tashe yace"Daughter kefa,do you have any problem?".....
Cikin sauri ta girgiza kai don Allah yagani bazata iya bari tayi loosing gabadaya ba gashi Magajiya ta kwafsa musu she's just blaming her for everything...
Mai Martaba ne yace to alhamdulillahi kinji dukansu basuda matsala zasuyi dukyanda akace and I've full faith in them kaman yanda kikace they should practice to hakan za ayi,duban surukan nashi yayi akaro na biyu kafin yace"Allah yayi muku albarka yanzu muje inyi introducing dinku to them dakaina".......
Haka suka tashi bakidayansu suka fice Magajiya jitake kaman tasa hannu aka ta fasa ihu haka tanaji tana gani aka danka musu wannan responsibility din gashi bayin se murna sukeyi abunsu atleast they'll have some change...........

Ahaka taro ya watse Almustapha yabi bayan mahaifin nashi don fada mishi halin da ake ciki..........

Mai Martaba na sane da Almustaphan na biye dashi amma baice komai ba harsuka isa karamar parlourn shi zama yayi tareda duban dan nashi kafin yace...
"Son any problem?"......
Zama yayi kafin yace Abba daman akwae maganar danakeson muyi ne.......
Mai Martaba maida attention dinshi yayi kan Dan nashi sosai kafin yace....
"to Son inajinka".....
Cikeda ladabi yashiga masa bayanin yanda sukayi da Galadima kafin yace Abba ninasan may be has a genuine reason shiyasa bebarni nayi maka magana ba amma ninaga I've to ask you if possible ayi mekyau din sabida tahakan ne zasu samu availability of water all the time batareda ansamu matsala ba hakanan muma wani karin saukine agaremu shiyasa nace ba inzo inrokeka if possible akara amount din kudin........

Tunda yake magana Mai Martaba kebinshi da kallo don bakaramin mamakin zancen Almustapha din yayiba shidai yasan duksanda za ayi aikin boreholes kudin da Galadima ke karba sunada yawa and sunyi akan amount din da Almustapha din kefada yanzu shine mekyau to all this time kenan ba ayin aiki mekyau komi?.........
Wannan shine tambayar dayayima kanshi dukda kuwa shikanshi baida ansar tambayar because he truly trust Galadima like his very own flesh blood Brother so he can't just take action without any investigation don haka seyace ma Almustapha din kan yaje zaikirashi gobe inyayi tunani dukda seda yatambayeshi "Are you sure Son?"
Gyada kai Almustapha yayi sannan yayi godiya yafice don samun Sulaiman because yadameshi sujesu gidansu Asma'u sugaida surkanan shi dukda ma yau bashine first time dazasu je ba yau na uku kenan da Sulaiman din ke kanshi suna zuwa.........
Bangaren Asma'u kuwa tunda takoma bangarensu gurin Ummi tawuce tana fada mata yanda akayi ah fada murmushi Ummi tayi mata sannan tace"Congratulations Dear Allah yabaki ikon yin abunda yadace".....
Amin Ummi shine abunda Asma'u tace kafin tace Ummi i need to go and see Jakadiya maganan abincin bayi........
Murmushi Ummi tayi kafin tace Allah yashige miki gaba Habibty amin ta amsa da kafin tayi mata sallama tafita zuwa kitchen din masarautar anan tasamu jakadiya tanata aikin supervising masu girki tunda tashigo kuwa bayin se wani zubewa sukeyi suna mika mata gaisuwa Rukayya baiwarta data rakota ne taje tayima Jakadiya maganar isowan Gimbiya Asma'un cikeda ladabi takaraso inda Asma'un take kafin tagaida ta Asma'un ma gaisheta tayi kafin jakadiyar yace muje daga ciki muzauna mana Gimbiya.........
Babu musu Asma'u tabi bayanta harsuka shiga wani daki fes fes yake harda table da kujeru da alama office din jakadiyan ne zama sukayi kafin Asma'u tace daman nazo muyi magana ne akan abincin bayi...

Dubanta Jakadiya tayi kafin tace"To Gimbiya Kinga ni banyi miki murna bama haryanzu, Allah ubangiji yataya riko"cewar jakadiyan.....
Murmushi Asma'u tayi kafin tace"nagode Jakadiya daman inason inji quantity na abincin da ake basu kullum safe rana da dare kuma sannan ke aganinki iya yaya za akara yanda zaizama sunaci su koshi daidai misali?"....
Dan numfasawa jakadiya tayi kafin tafara lissafo mata yanayin amount na kayan abinci da suke diba kullum suyi anfani dashi kafin tace inaganin in aka ninka kayan abinci to kowa zaici ya koshi batareda anyi almobaranci ba...........

Dan jinjina kai Asma'u tayi kafin tace nagode indai akwae ishasshen kayan abinci da za'a iya yimasu anfani dashi na daren yau?....
Gyada Kai jakadiya tafi kafin takarada"akan sayi kayan abinci na wata guda ne wanda zai isa sabida haka zai isa aninka nayau harma na kwanakin gaba".......
Alhamdulillah cewar Asma'u kafin tace to ayi masu abincin yau ishasshe please Jakadiyar kafin insamu inyi magana da Mai Martaba godiya sosai Jakadiya tayi mata kafin Asma'u tayi mata sallama tafice zuwa bangarensu dukda taso zuwa gun Mai Martaba suyi magana sede balallai tasameshi ah bangarensa ba don yawanci ah irin wannan lokacin ah fada yake zama sede zuwa yanma taje gurinsa.....

Bangaren Zaliha kuwa da Magajiya tunda sukabar fada kowannensu ranshi bace yake ga abunda yafarun yayinda Zaliha ke blaming Magajiya for everything daya faru shiyasama suna zuwa bangaren Magajiya tasaki kuka tana Mama dabakiyi hakan ba gashi kingadai babu abunda yacanza...

Cikeda takaici Magajiya tace" au laifina kike gani Kuma bakene kikace yarinyar tace bataso ba,I should be the one to blame you for everything badai ke kiyi blaming dinaba",takarashe maganar tana nuna Zaliha da yatsa itadai Zaliha tsabar takaici ma kasa cewa komai tayi sema ficewa datayi takoma bangarenta because she's not in the mood in Magajiya tayi wasa tana iya fada mata maganganu ma..........
Laure dake gyara wordrobe din Magajiya tanajin yanda sukayi da Zaliha amma batace komaiba har Zalihan tafice Magajiyan masifa takeyi taredayin mita wanda daga karshema aka huce kan Lauren don hanata tafiya tayi wae saitayi mata massage sannan ta tsefe mata kitson kanta haka tashigayin abunda tasata din badon ranta yaso ba itakam tafara gajiya da ayyukan Magajiya dinnan gashi dai bawani evidence take samuba yanzu because it seems like idea sunfara karema Magajiya dinnan sabida bataga tana yunkurin yin wani abuba ayanzu kam shiyasa tayi deciding intasamu fitama kawai zataje tacema Hajiya Muniba itakam tagaji da aikin nan tanason takoma gunta......
Dayanma Asma'u taje gurin Mai Martaba Allah yataimaketa yana parlourn shi gaidashi tayi sannan yace
"Zauna mana Daughter".....
Murmushi tayi kafin tazauna can nesa dashi tana wasa da hannunta cikeda kulawa yace...
"any problem Daughter?"
Sunkuyar da kanta kasa tayi kafin tace"Daman Abba tunjiya daka bani wannan nauyin na zagaya cikin bayi don gano matsalolinsu dakuma wanda ake bukatan agyara and alhamdulillah nagano abubuwa da dama dayake faruwa cikeda lumana tashiga yimasa bayanin komai daga wanda tagani da idanunta harzuwa wanda su Hindatu suka fada mata sede bata fadi wanda baishafi aikinta ba dakuma wayanda take ganin ita yakamata tadauki mataki bashiba shima bata fadaba jinjina kai Martaba yayi cikeda gamsuwa sannan tace"Abba inbabu damuwa inason akara quantity na abincin da ake basu sabida only insun ci abinci mekyau dakuma wanda zai rikesu ne shine zaisa susamu strength din yin aiki,sannan rashin abun kwanciya ma wani abune barinma lokacin sanyin nan yana iya kawo musu cuta batareda an ankareba sekuma batun sutura amma shima suna fama da rashin sutura mai kyau wani ma sekaga kayan shi duk ya babbarke amma ahaka suke shiga mutane dasu batareda sun damuba tunda basuda halin dinka wanin ne".........
Seda takai aya kafin Abba yace kin tabbatar da abubuwan dakikayi discovering kenan Daughter?....
Eh Abba tabashi answer cikeda confidence mamakine sosai yakeyi donshidai from his side yana iya bakin kokarin shi wurin ganin ya biya ma bayin nan bukatunsu hakanan yana bada ishsshen kudi yanda yakamata to amma miyasa hakan tafaru,kenan duk wannan tsawom shekarun abunda ke faruwa da masarautar tasa kenan batareda yasani ba and who's responsible for this?ko yanzun ma so ake acemishi Galadima is at fault tunda shine ke rike da responsible na kudi ah masarautar nan because duk wata harka ta kudi ake bama takuma hannunshi kudin ke shiga yake kuma fita.....
He really can't believe this sede ance there is no smoke without fire shiyasa yakira daya daga cikin dogarayen shi atake cikeda ladabi saurayin yashigo dubanshi Mai Martaba yayi kafin yace kaje kakiramin Jakadiya.........
Cikeda ladabi yace to....
Ko minti goma ba ayiba sega Jakadiya da dogarin sundawo zubewa tayi kasa tana gaida Mai Martaba din kafin yace kimin bayanin ya quantity din abinci dakuke bama bayi yake babu bata lokaci Jakadiya tashiga yimasa bayani kaman yanda Asma'u tafada masa......
Jiki ah sanyaye yace tun yaushe hakan yake faruwa acikin Masarautar nan?....
Kan Jakadiya ah kasa tace"ranka shidade yanzu yakai kimanin shekaru goma sha uku ko fiye da hakan ma......
Mai Martaba dayaji ranshi nayi mashi wani irin kuna yace"waye yace kiyi hakan kodai tsarinki ne ki bar mutanena sa yunwa"....
Cikin sauri da rudani Jakadiya tace"wallahi bahaka bane Rankashidade nibazan taba yanke hukunci akan abunda ba asakaniba Magajiya ce tabada wannan tsarin tunda jimawa nikuma amatsayina na wanda take kasa da'ita yasa nabi hukuncinta tunda itace babba awurin sannan kabar komai ah hannunta........
Tunda jakadiya ke magana yake kallonta he can clearly see that she's telling the truth gabadaya kanshi ah daure yace kitashi kitafi shikenan....
Tashi tayi jikinta na bari tabar fadan don bakaramin kidumuwa tayiba tadauka ita za adaurama laifin ma bakidaya.Mai Martaba dake zaune yasake duban Asma'u sannan yace tashi kije insha Allah zandauki mataki Daughter and thank you for calling my attention........
Jiki ah sanyaye tatashi tafice zuwa bangarensu Mai Martaba kuwa yanzu target dinshi mutane biyu ne Magajiya and Galadima ne tunda dukwani list na abinci daza asaya magajiya ce zata rubuta ta aika ma Galadima shikuma zesa asayo ah kawo gida gakuma maganar Almustapha na building dinnan gabadaya yadaure masa kai don haka yakuma sakawa akira masa Galadima dakuma Magajiya at thesame time ba ajimaba segasu sunzo dukdama ba atare suka shigo parlourn nashi ba.....

Duban Galadiman yayi kafin yace...
"yakukayi da Yarima batun boreholes?"....
Dariya Galadima yayi kaman wani mutumin kirki kafin yace..
"aimun gama magana dashi yallabai"........
Cikin dakewa Mai Martaba yace "I know still kafada min yanda kukayi nace",atake Galadima yashiga fadamishi karya da gaskiya kafin daga karshe yace harmun samo mesuyin aikin ma nace mishi cikin sati zasuje su fara......

Bakaramin mamakin karyar da Galadiman ke shararawa Mai Martaba yayiba don haka seya daga wayarsa yakira Yarima Almustapha yana"kana inane Son?"......
Cikeda ladabi Almustapha yace yanzu shigowa na Abba,anutse Mai Martaba yace kazo kasameni ah parlour na yanzunnan........
To kawai Almustapha din yace yayinda Mai Martaba yakatse call din Almustapha kuwa yanzu shigowansu daga gidansu Asma'u harda Munira da Ikram suka taho wai sunzo zasuyima Asma'u weekend......

Duban Sulaiman din yayi kafin yace"Abba nakirana kukarasa cikin gida dasu"....
Gyada masa kai Sulaiman yayi yayinda Almustapha yayi bangaren Mai Martaba din gaishesu yayi kafin yasamu guri yazauna dubanshi Mai Martaba yayi ahankali kafin yace ka maimaita min yanda kukayi da Galadima batun aikin boreholes......
Cikin nutsuwa Almustapha yashiga bayanin yanda sukayi har karshe duban su duka biyu Mai Martaba yayi sannan yace"I don't know who to believe between you two dukanku Kuna bani different story I don't know why?"........
Galadima dayayi tsuru tsuru kasa cewa komaima yayi because betaba tunanin Almustapha zezo yasamu Mai Martaba ba........
Mai Martaba ne yafito dashi daga trance dinshi tahanyar cewa...
"Galadima kace kungama magana da Son shikuma yace baku gama ba?".......
Cikin in inaaa Galadima yace"to ni madai bansan meyesa yace hakaba?".....
Almustapha dai mamakin mutumin yakeyi haka Mai Martaba ma daga ganin fuskar Galadima zaka gane karya yakeyi don gabadaya reactions dinsa yanuna.........
Dan ajiyar zuciya Mai Martaba yayi kafin yace i gave you enough Money for this work miyasa zaka yimin haka Galadima?......
I trust you for years now Ashe you've been betraying me and all the time cewa kakeyi aiki mekyau akeyi ba marar kyau dinba but I never intend to investigate sabida nayarda dakai you're one of my close friends atunanina you'll never do something like that but you prove me wrong today because daga reaction dinka nariga nasan komai Galadima...

Galadima da gabadaya yagama rikicewa yace"yanzu yarda da Danka da kasameshi ah sama saman nan kayi fiye da ni damukayi shekaru dadama tare?".......
Murmushin takaici Mai Martaba yayi kafin yadubi Almustapha yace jeka kiramin Jakadiya kace tataho da record book nata yanzun nan ...
To shine abunda Almustapha yafadi kafin yafice zuwa yin abunda akasakashi aikuwa tunda sukaji haka daga Magajiya har Galadima suka rude donsunsan yau asirinsu yakusa tonuwa amma mi se Magajiya tadaure ahaka har Almustapha da Jakadiya suka dawo mikama Mai Martaba katoton littatafai guda biyu tayi wanda ke daukeda duk wasu lissafe lissafe na kayan abinci daya ke shigowa hannunta na shekaru da dama yanzun.........
Dubawa Mai Martaba yashigayi yanda Asma'u da'ita sukayi mishi bayani dazu haka abun yake arubuce mikama Galadiman yayi sannan yace"kagani da idanunka dukda nasan kana sane da abunda kukayi kaida Magajiya don bazance babu hadin bakinta ba".....
Cikin sauri Magajiya tace nifa bansankomai ba wallahi ni kawo kayan abinci yakesawa ayi kawai nikuma nawa in sa ah ajiye ah store....
Murmushin takaici Mai Martaba yayi kafin yace"you can't lie to me Magajiya,miyasa baki taba zuwa kinsameni kinfada min ba inbabu saka hannunki aciki?"......
Cikin rashin gaskiya tace"nadauka iya kacin abunda zaka iya bayarwa kenan"......
Galadima dayaga Magajiya nashirin barinshi aciki yasashi saurin cewa...
"Karya kikeyi wallahi mutumiyar banza,sokike kibar ni aciki wato ko,to indai haka zakiyimin gwanda intona mana asiri baki dayan mu because yanda kikeson kanki haka Nima nake son kaina batareda Galadima yayi wata wata ba yace duk kudin da kake bayarwa Mai Martaba nida ita muke rabawa kama daga kan na abinci dama na suturun bayi dakuma katifu dama na aikin boreholes duk tsakanin mu muke raba canjin daya rage sannan Almustapha gaskiya yafada maganar damukayi dashi kenan Kuma babu algungumin daya kawo wannan shawaran inba itaba and yanzu tanason tabarni aciki dongata shedaniya to baki isaba yakarashe maganar ranshi bace sannan yakarada ninasan I'm selfish, nayi betraying dinka sabida abun duniya kudi sunrufe min iso har hakan yasa namanta irin yardar dakayi dani kakuma dankamin amana amma dukda haka inafatan zaka yafemin abunda nayi I know I'm very selfish bankyauta makaba yakarashe maganar muryar ah karye.........

Magajiya dai dagewa tayi tana kuka tanacewa karya yake mata,hmmm shine abunda Mai Martaba yayi kafin yace"tun bangama Samo evidence ba kafadi gaskiyar kenan"....
Kan Galadima ah kasa yace"nariga nasan kasan gaskiya so babu anfanin boye boye asirina yariga yatonu and nothing can change that but believe me I'm always your person dukda banida idanun kallonka ayanzu sabida abubuwan dana aikata",murya akarye Mai Martaba yace"it's not your fault laifina ne danayarda dakai dayawa, it's my fault dabana shiga cikin mutane na dakaina inaduba matsalolinsu sabida ahtunanina kudin kunayin abunda yakamata ashe bahaka bane,ashe my people have been suffering,ashe suna rayuwa da yunwa batareda nasani ba amma bakomai Allah zai sakamin dagani harsu tunda yaga zuciyata.........
Cikeda damuwa Galadima yace kayafe min don Allah.....
Mai Martaba ne yace"bani zakanemi yafiya aguna ba kaje kanemi yafiya gurin wayanda kacutar daganan yatashi yafice batareda yasake dubansu ba dagashi har Magajiya din don zuciyarsa takasa daukar abunda yafaru din hakanan yarasa wani irin mataki zai dauka akansu........
Galadima ma tashi yayi yafice jiki ah sanyaye Almustapha kuwa kallon Magajiya yadinga yi cikeda tsana yana mamakin yanda tadage tanata kukan munafurci kamar wata mutumiyar kirki...

*I know this's the most boring chapter may be,but don't worry I'll make it up to you guys I'm really very sorry*......

Vote
Comment
Share?
[3/23, 5:49 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad



*Page 43*

Ganin bazai iya juran tsayuwa kusada itabama yasashi fita don komawa bangarensu.........

Magajiya kuwa takaici ne yaisheta nafita da kowa yayi yabarta agurin batasan sanda tayi wani irin karaba kafin tayi ball da wani table dake tsakiyar dakin mai Martaban tana huci kamar wata mahaukaciya hararan dakin tashigayi sannan tafice cikin sauri tana huci.....
Dogarayen dake bakin kofar dakin sunajin ball datayi da table din amma hakan baisa sunyi gigin leka dakin ba donsunriga sunsan hali suna iya jama kansu abunda yafi karfinsu don koda tazo fitama yi sukayi kaman basu ganta ba tsabar tsoron Matar haka tawuce bangarenta tanata huci ita kadai tarasa meke mata dadi hakanan tarasa wani mataki zata dauka gashidai komai tabar baremata yakeyi ahankali and she's not getting any new clue........

&*&
Asma'u tunda tabar parlourn takejin wani irin dadi na musamman atleast tasani Abba zedau mataki tunda yace yasan yanda zaiyi batada wani damuwa daya wuce
taga bayin nan suna rayuwa maikyau tana wannan tunane tunanen ne setaga kaman Laure nayin hanyar bangaren Hajiya Muniba bayan kuma tasan Laure baiwar Magajiya ce and it seems like yarinyar nata dube dube kamar wata marar gaskiya wanda hakan yasa Asma'u tabi bayanta cikin sauri harta isa sashin tasan babukyau lekan sirrin wasu sede yazatayi?.......
She needs to know if they're behind something kokuma kansu hade yake ah bakin kofar tasamu dogaraye gaisheta sukayi kafin tashiga ahankali sede koda tashiga parlourn samun guri tayi ta rabe don ta hango Lauren cikin parlour zaune gaban Hajiya Muniba kasa kunne tayi donjin mezasu ce........
Laure ne ke kuka kamar ranta zaifita tana"nikam Rankishi dade don Allah kitaimaka ki dawo dani amatsayin maiyi miki aiki don wallahi yanzu Magajiya batadauke ni ah bakin komaiba batama fadamin dukwani abu dazatayi"......
Hajiya Muniba da takejin tausayin Laure tace"kiyi hakuri Laure ninasan kina hakuri da matarnan amma inason kisani bazai yuyu murabaki da itaba batareda asirinta yatonu ba don inmukayi haka kaman ma muntona ma kanmu asiri ne kafin mu cika burinmu kicigaba da hakuri komai yakusa zuwa karshe in Allah ya yarda"..........
Dakyar Laure ta'iya daina kukan don tasan gaskiya Hajiya Muniba ke fadi kafin tace"tonikam abun yakici yaki cinyewa ranki shidade kodai zakiyi anfani da Mallam Audu ne dakuma ke karan kanki kitona mata asiri kawai sabida Magajiya tacuci mutane da dama wallahi kuma tana kan cutansu don banga alama tanada niyar saukar da kanta tayi abunda yadace ba"......
Murmushin takaici Hajiya Muniba tayi kafin tace"nikaina inason hakan but I want her to confess all her crimes inason tayi mugun muzanta agaban idanun mutane banason ace wannan laifin guda biyu shine kadai laifin daza a kamata dashi batareda sauran abubuwan datayi sun bayyana ba,inason Magajiya tasha wahalar da babu wani mahaluki daya taba sha ah duniyarnan yanda Hajiya Muniba ke maganar zaka gane akwai bitterness sosai acikinta har jijiyoyin jikinta tashi yakeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login