Showing 171001 words to 174000 words out of 235422 words

Chapter 58 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3499

bayan tacema su Rukayya sukai abinci dakinta......

Almustapha ba irin tunanin dabaiyi ba don tuna maiyayi mata amma shibaiga yayi komaiba,abu dayane kemai yawo akanshi na....
"kodai don taga rabuwarsu takusa ne shiyasa tashiga cikin damuwa",dawannan yatashi yafice zuwa masallaci yana mamakin abun donshidai yasan tana sonshi hakanan in mutum na sonka bazaiso rabuwa dakaiba ya kuma fa cemata bayason rabuwa da itan shima amma yarinyar nan tadubi kwayar idanunshi tace itaba haka ba,harda yimashi kukan munafurci gashi kuma yanzu ita abun yake damu,dan murmushi yayi aranshi yana"zanyi maganinki yarinya"..............

Ummi har daki taje tasamu Asma'u nan tasata dole taci abinci agabanta tana ta janta da hira dukdan tasaki jikinta don tasan Asma'u da shegen kunyar tsiya yanzu seta fara wasan boye boye da'ita akan abunda yafaru yaudin kafin daga karshe tajata sukayi lambu bayan sunyi sallar la'asar....

****....
Daman Mai Martaba da Dad sun tsara cewa Hajiya Muniba da Matar waziri sune zasuje sayan kayan lefe dama kuma kayan daki da kitchen ah duk kasar dasukaga zaifi musu sauki ko inda suke ganin zasu samu kaya masu kyau sede koda Dad yazoma Mom da maganar jiya take fada mishi ai Hajiya Muniba batajin dadi kwanannan, she's always sick da mamaki Dad din yakecemata baiji Mai Martaba din na complain ba infact shiyace da'ita ma za'aje.. ....
Dan shiru Mom tayi kafin tace"to besani bane komi?"......
"Probably",cewar Dad din kafin yace zai tuntunbeshi yaji shiyasa ma yau dasuka hadu yake sanar dashi,da mamaki Mai Martaban yace wallahi baisani ba and tana zuwa gunshi fa baiga alamar batada lafiya ba.........

Dad dinne yace"may be she's hidding it ne,kaje kasameta kuyi magana zaifi"....
"Sure",cewar Mai Martaba din kafin yatashi atake yayo bangaren nata,tana kwance ah dakinta gabadaya batajin dadin jikinta kwananan kawai daurewa takeyi,zama yayi abakin gadon cikeda damuwa sannan yataba temperature din jikinta yana
"what's wrong with you Dear?"......
Kokarin tashi zaune tayi tana"Nothing,Ina kwana Dear,hope lafiya kayi tattaki dakanka har bangarena you should have send for me zanzo immediately", takarashe maganar cikeda karfin hali, she's just trying so hard to prove that she's okay while she's not......
da mamakinta Mai Martaba yadaura hannunshi kan lips dinta yana...
"why do you want to force yourself to be okay when you're not Muniba?",shiru tayi tana kallon shi kafin yasake matsowa kusa da'ita tareda doro kanta ah kafadunshi"I'm here to see you tunda kinkoyi boyema mijinki damuwarki",yanda yayi maganar ya tabbatar mata da baiji dadin abunda tayi din ba seta tsinci kanta da sakin murmushi kafin tace...
"I'm okay fa kawai zazzabi ne kedan damuna"...........
Shiru yayi baice mata komai ba har likita yakaraso cikin sauri tace"I'm okay really"........
Cewa yayi with serious look"You're not Muniba kibari likita yaganki,i don't like seeing you this way",yanda yayi maganar bazata iya jadashi ba wannan dalilin yasata tsayawa likitan yaduba ta,seda yagama examining dinta sannan yace"kinada ulcer ko?".........
Gyada mishi kai tayi ahankali kafin likitan yacigaba da magana"you've to avoid spicy food sannan kirage cin mai and try and be eating your meals on time inbahaka ba zaicigaba da damunki"......
Mai Martaba ne yadubi likitan kana yace"kana nufin ulcer kedamunta?"......
"Eh ranka shidade" cewar likitan kafin yakarada"but is not that chronic intana avoiding abubuwan dana lissafa she won't have any problem in Sha Allah"........
Godiya Mai Martaba yayima likitan kafin yayi mata prescribing drugs yatafi, atake Mai Martaban yasa aje ah siyo kafin yadawo dakin yana"tunda kinzama stubborn girl I'll start feeding you myself"........
Kai Dear yaushe nazama girl tsofai tsofai dani, janta yayi jikinshi cikeda so yana"you might be old to the world Muniba but not in my eyes,kaman Baby nike ganinki kullum believe me".....
Itadai dariya kawai takedanyi ahankali don tasan kawai yana fadan hakan ne don ya faranta mata,itakanta tasan she's very lucky data auri Mai Martaba,he might not have feelings for her na soyayyar aure yanda yakamata but she's sure yana respecting dinta and despite she knowing cewa Khairiya yakeso betaba nuna mata hakan ba and koyaushe in suna tare nuna mata yakeyi she's the most special being in the whole world and it makes her feel good even though tasan bawai hakan bane ba,ita tunda tafara rashin lafiya ma tayi tunanin ciki gareta shiyasa ma tayita boyemai don aganinta abun kunya ne ace tsofai tsofai da'ita tana da ciki ashema ulcer ce ke damunta ba wani abuba,yes tasan tanason yara wanda zata haifa da cikinta but at her age itakanta tasan it'll be something difficult...........
Yajima ah bangaren nata donseda yatabbatar taci abincin kaman yanda yayi alkawari sannan yabata drugs tasha kafin yafice don komawa fada kan susake sabon decision na wanda zasuje sayayyar.........
***
Kwanan nan gabadaya Magajiya batajin dadin jikinta dukda irin daurewan datakeyi wurin ganin she's strong amma ina,kaikayin jiki yadameta,ga ciwukan jikinta gaba sukeyi ba baya ba itakanta kyaman jikinta take ji ah yanzu bare wasu, she's so weak don sau uku tana suma acikin satinnan ana zuwa asamata drip ajikinta don Mai Martaba cewa yayi baza akaimasa annoba clinic dinsaba wayasani ma cutan jikinta is communicable kada taje tayada ma mutane diseases because likitan kanshi cewa yayi yarasa dalilin dayasa kurajen jikinta suka ki healing drip dinma dayake bata na taimaka mata tasamu karfin jikinta ne kawai sabida kin cin abincin da takeyi din...........
Sede yaufa jikinnata yayi tsanani sosai don yanda jikinta ke karkarwa dakuma yanda take sosa jikinta kamar mahaukaciya tsabar kaikayin dayakeyi mata seda tabama dogaraye tsoro,tana sosa jikin tana fame ciwukanta wanda hakan bakaramin azaba yakesata jiba sede gani takeyi sosawan yafi mata dadi akan barinshi yana mata kaikayi don yafi wannan din azaba.......




Vote
Comment
Share!.....
[3/23, 6:07 PM] >?p?: =?Q?=?Q? *GIDAN SARAUTA* =?Q?=?Q?


Written by *Zeeneert*=ؕ?

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 59*.....



Sunanan tsaye suna kallon halin da take cikin batareda kowannensu yace komaiba,can kuma seta saki jiki tafadi sume,daya daga cikin Dogarin ne yayi karfin halin yin magana "subhanallahi ta sume fa",kafin kuma dagudu suka shiga kokarin bude kofar don dama arufe take ta raga raga suke kallonta daman.........
Shiga dakin sukayi suna toshe hanci baki dayansu tsabagen warin dake tashi agurin kafin suka karasa gareta daniyar daukanta amma ina don dukyanda sukaso taimaka mata kasawa sukayi dubada yanayin jikinnata,gabadaya ya cabe gani sukeyi dasun tabata fatan jikinnata zai sabulewa zeyi,sky blue kayan prisoners dake jikinta ma duk yafita ah hayyacinshi yatashi daga blue yakoma brown gashi daman sleeveless ne rigan shiyasa ake iya ganin ciwuwwukan dake jikinta.............
Ganin sun kasa aiwatar da komai akanta ne yasa daya daga cikinsu yace"muje mukira Doctor din mana don ko munfada ma Mai Martaba abunda zaice ayi kenan?"..........
Jinjina kai sukayi cikeda gamsuwa da maganar tashi kafin sukace toshi yaje yakira likitan mana, haka yafice cikin sauri yayi gidan likitan daya zamanto yana cikin masarautar daman sukuwa komawa waje sukayi don daman numfashima? dakyar sukeyi acikin gurin,ba afi 30 minutes ba saiga dogarin yadawo tareda likitan.......
Tsayawa yayi daga bakin kofa sannan yace sushiga su fito da'ita nan don Allah yagani shibazai iya shiga gurin ba don bemanta wa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????halar dayasha ba kwanaki dayayita zuwa yana samata drip bakaramin fama yayi da tashin zuciya ba hakanan kusan kwana biyu inyaci abinci daya tuno yanayin warin dayaji adakin da Magajiyan take seyaji amai yazo mishi lokaci guda ko inyatuna yanayin ciwon jikintan,shi babban likita ne dayajima yana aiki ah masarautar nan. kai bama ah masarautar nan ba kadai tunda yakanyi aiki ah wasu hospitals hakanan yasha encountering patients masu cuttutukan dazaisa shi jin kyama amma hakan baitaba sashi jin wani iriba kaman yanda na Magajiyan yadameshi,her situation is so worst dashikanshi yarasa wani irin cuta ne gareta dabada badan ba cewama zaiyi shibazai dubata ba sede it's part of his work,as a Doctor he can't just ignore his patients batareda wani kwakwaran hujja ba bayan yasan she really need him.......
Yana nan tsaye har suka fito da Magajiyan,sawa yayi suka kwantar da'ita kan tabarmar dake gurin kafin ahankali ya tsuguna gabanta yana mamakin rayuwa dakuma duniyar kanta baki daya,kamarfa jiyane matan nan ke Mulki acikin Masarautar nan,kaman jiyane takeji da izza take kuma wulakanta mutane yanda taga dama don babu inda zaka shiga cikin masarautar zazzau kace *MAGAJIYA* ba ace maka ansantaba kama daga kan Bayi,Yan fada, dogaraye harma Matan manyan fadan don dukansu sara mata sukeyi tareda bata daraja hakanan suke tsananin tsoronta........
Yau ina Sarautar tata,Ina izzar,Ina kuma wannan mulkin da takeji dashi ada,she's just here laying infront of him helplessly and in need of his help as a Doctor wanda shikanshi bashida tabbacin kozai iya taimaka mata ayau din dubada yanayin ciwukan jikinta because yanada tabbacin yau drip dinma dakyar inze shiga jikinta...........
Tashi yayi ahankali jiki sanyaye don haka kawai yakejin tsoron Allah yana kara shiganshi sakamakon abunda yake ganin kafin yadubi dogarayen yace"bana tunanin zan iya taimaka mata yau Kam inaganin zaifi akaita asibiti don jikinta tsanani yake karayi"............
Jiki ah sanyaye daya daga cikinsu yace"to kafada ma Mai Martaba din mana"....
Gyada mishi kai kawai yayi kafin yafice,straight fada yawuce koda yasamu Mai Martaba din cewa yayi shiba ruwanshi kuma baiyarda kowa yafitar da'ita daga masarautar nan ba duk abunda za ayi mata ayishi within nan",to kawai likitan yace kafin yayi ficewarsa donshima yanayine don Mai Martaba din anma tunda yanuna yacire al amuranshi cikin maganar to shima miye nashi?...
Shiyasa ma yana fita ah fadan yayi wucewarsa gidansa batareda yasake waiwayar inda Magajiyan take ba..........
Dad dake zaune tareda Mai Martaban ne yadubeshi bayan Doctor din yafita sannan yace"bekamata kace hakaba Abdulrahman",dasauri Mai Martaban yakalli Dad din yana mamakin jin haka daga gareshi kafin yace"Yaya badai kanason kacemin inji tausayin wannan matar baneba?".........
Jijjiga kai Dad yayi sannan yace"nibance kaji tausayinta ba Abdul but", Mai Martaba baibari Dad din yakarasa ba yace"But what Yaya,ah tunanina kafi kowa sanin who she's and kafi sanin abubuwan da tayimana inanan dakai mukaje gurinta kwanan nan after abubuwan dasuka faru batada sign of regret ko kadan ah tattare da'ita sema zuciyar ta dake cikeda bakin hali dakuma neman hanyar daukan vengeance akanmu",jinjina kai Dad din yayi cikeda gamsuwa da maganar kanin nashi,ajiyar zuciya Mai Martaba yayi sannan yace"then why do you expect me to pity such a person,why do you want me to care Yaya!bayan mutumin dakakeson intaimaka ma din babu abunda takawo ma family na inbanda badluck dakuma tragedies", yakarashe maganar ranshi ah bace ahankali Dad yadaura hannunshi kan kafadun Mai Martaban sannan yace"Calm down Abdulrahman,ba abunda tada hankali baneba,I know Magajiya has wronged you in everyway sede kaida ita akwai banbanci you're a Muslim Brother and a leader as well besides she's in a situation datake tsananin bukatar taimako so baikamata kajuya mata baya ba,kai don Allah zakayi badon halinta ba kuma aidon ka taimaka mata bahakan na nufin anyafe matabane ba, when she gets better zata cigaba da zama ah prison din ina........
Shidai Mai Martaba maganar Dad ko kadan bai shigeshiba don wallahi ko kadan bayajin zai ji tausayin Magajiya,tariga ta cuce shi and he cannot forget that shine kawai,ganin baice komai ba sekawai Dad din yaja bakinshi yayi shiru sunanan zaune har wani daga cikin Dogarin yasake zuwa yana sake fadama Dad din halin da Magajiya ke ciki,don harcemasa yayi yanzu ko motsi batayi cikeda tashin hankali Dad din yatashi yafice zuwa gidan horon nan yaga halin da take ciki sawa yayi aka sake kira mishi Doctor din daga gidanshi,koda yazo cewa yayi he cannot do anything kaman yanda yafada ma Mai Martaba dazun advisebely sukaita hospital shine kawai shawarar dazai iya basu atake Dad din yasa akawo ambulance ............

Karar siren din ambulance dinne yajawo attention din mutane da dama dake cikin masarautar,nan aka shiga neman ba'asin abunda yafaru don duk randa akaji abu irin haka to tabbas rashin lafiyar me tsanani ne da likitocin masarautar kansu bazasu iya handling ba se anfitar da marar lafiyar asibitin gari...........
Kan kaceme rashin lafiyar Magajiya ya gama karada masarautar barin ma tsakanin Bayi da Dogaraye dasuka fi kowa iya gutsiri tsoma da gulma, Zaliha ganin masu aikinta sunata kus kus yasata kiran Lantana tana tambayarta lafiya,jikina bari lantana tashiga fada mata rashin lafiyar Magajiya din don daman Itama neman hanyar fadan take tun dazu sede tsoron karta fada ba atambayeta ba yazama wani laifin yasata yin shiru.........
Cikeda tashin hankali Zaliha tace"kikace antafi da Mama asibiti?"......
Gyada kai Lantana tayi sannan tace"Gimbiya harcewa fa akayi naman jikinta fita sukeyi dakansu",wani maka Zaliha takai mata tana"hankalinki daya kuwa,matsala na daku Bayi kunada jahilci wallahi tayaya naman mutum zena fita",cewar Zalihan ranta ah matukar bace itadai Lantana yin kasa dakai tayi kamar munafuka tana karacewa"Allah kau haka naji anacewa Gimbiya" ........
"Yimin shiru dallah inkuma bahaka ba kitashi kifitar min ah dakin",cewar Zalihan hakuri Lantana tashiga bata sannan Zalihan take tambayarta ko Sulaiman din nada labari........
Nan tace mata gaskiya dakyar in yasani,cikeda tashin hankali tafice zuwa bangaren su Asma'u don tanada tabbacin anan zatasamo Hamida don ta fada mata at thesame time kuma tashiga trying number din Sulaiman din............
Sede kwata kwata baya dagawa,yarfa hannunta take tana sauri har kaman zata fadi yayinda tacigaba da kiran number nashi tana fadin"pick the call Sulaiman, pick up the call please!".....
Ana biyar dinne yadauka batareda ta amsa sallamar dayayiba tace"where are you Dear?".......
Jin muryarta wani iri yasashi cewa"what's wrong Zaliha,wani abunne yafaru?"........
Rasa abunda zatace masa tayi kawai seta saki kuka tana fadin...
"Mama Sulaiman,come home now please", bakaramin bugawa kirjinshi yashiga yiba tunda har Zaliha takirashi da Sulaiman ayaudin yasan tabbas ba lafiya ba hakanan yanda yaji muryarta ma kadai ya'isa yafada mishi cewa something is very wrong.........
Yanason ya tambayeta meya samu Mama sede gabadaya yakasa ma sabida tsoron ansar dazata bashima yakeji cikin sauri yabar site din da ake gyaran donkuwa yana cikin masarautar daman ba nisa yayi ba hakanan yataho bangaren shi hankali tashe sede batanan,clinic din masarautar yaje nan ma baswanan cikeda tashin hankali yaciro wayarshi da niyar kiranta sega call dinta yashigo kuma dagawa yayi cikin sauri yana tambayar ta inatake,murya araunane Hamida tace suna bangaren su Almustapha amma zasu tafi asibiti yanzu don ance antafi da Magajiya din asibiti already........
Goge zufan dake keto mai yayi sannan ya katsewayar. ah parking lord suka hadu harda Asma'u donsu Afiya kinzuwa sukayi wanda hakan bakaramin kona ran Zaliha yayiba itakuma Sumayya ana mata gyaran jiki babu yanda ta'iya dukda koda ta biyosun ma ba sabida Magajiya bane ba but for her Yaya Sulaiman,she wants to be with him and console him..........
Sharara gudu Sulaiman din yadingayi harsuka isa asibitin shika wanda Allah ne kadai yakaisu lafiya, ahaka harsuka Isa emergency sede da mamakinsu haryanzu ba'a karbi Magajiya dinba, tana nan kwance akan gadon da ake tura marasa lafiya da mamaki yadubi driver da nurse din da suka kawota yana"why are you still here ko basu ganin ankawo patient ne?".......
Jiki ah sanyaye nurse din tace"sunce bazasu karbeta ba", Sulaiman da ranshi keyi mashi kuna yace"why?"......
Shiru sukayi dukansu,buga table din yayi cikeda bacin rai yana kallon nurse da driver din sannan yace"I'm asking you something for goodness sake?".....
Jikina bari nurse din? tace"Because she's Magajiya".......
Wani irin look Sulaiman yamata sannan ahankali yakuma furta kalmar wai"because she's Magajiya?"......

Asma'u daranta yabaci tace"is she a devil ko itan ba mutum baceba da baza aji tausayinta adubata ba ah arin wannan condition din,tukunnan ma ya akayi sukasan itace",tayi maganar ah kafule dasauri Nurse din tace munzo da file dinta ne and? Doctor din yaga sunanta, Asma'u dasauri tayi hanyar da take tsanmanin nanne office din doctor din amma sai Sulaiman yayi saurin shan gabanta cikeda bacin rai tace"kabarni Yaya Sulaiman i need to bring them back to their right senses, patients dinma harsai sunzabi wanda zasu duba don wulakanci?"..........
Jijjiga kai Sulaiman yayi jiki ah sanyaye sannan yace"inkikaje mezaki ce musu?"...

Da mamaki tace"mezan cemusu fa kace?"...
Gyada mata kai yayi sannan yace"they're right Asma'u,Mama tayi abunda is unforgivable and she's paying for what she did now, I can't blame them nor you so, it's better we just leave"......

Zatayi magana yajijiga mata kai sannann yajuya yafice ah gurin gabadaya yama rasa abunyi,to yanzu insukaje wani asibitin ma may be thesame thing za afada musu komi?.....
binshi
sukayi inda yace sumaida Magajiya din cikin mota haka sukaje wani private hospital acikin Zarian dukda yaso suwuce gida kawai amma Asma'u ta matsa sede alhamdulillahi su sunkarbeta amma fa sunkasa bata attention koda kadan ne se magun guna dasuka rubuta wai asaya abata and advisibly su fitar da ita waje kawai don su basu taba ganin cuta irin wannan ba Allah yagani............
To kawai Sulaiman din yace don dama abunda yayi planing kenan bayan anki karbansu ah dayan asibitin dasuka jedin,dukyanda kakai ga rashin imani inkaga Hamida da Sulaiman saisunbaka tausayi,dafa gadon datake yayi ahankali aranshi yana fadin to kenan ayanda take sume zasu barta har lokacin tafiyarsun yayi komi?........

Aedai koba komai ayimata taimakon gaggawa dazaisa tafarfardo daga suman datayi wanda hakan ne zebasu hope din cewa she'll wake up soon,dafashi da Hamidan tayi ne yasashi juyowa yana kallonta ahankali tace"mukoma gida kawai Sulaiman".........
Gyada mata kai yayi jiki ah sanyaye hakanan yana mamakin yaushe jikin mahaifiyar tasu yakoma haka tunda shiba zuwa ganinta yakeyi ba,anhana su kai bama shikadai bama babu wanda kezuwa mata ziyara asanda take gidan horon,he was busy preparing for his wedding while his Mother is suffering,he was busy jubilating wanda hakan yasa yamanta da al amuranta nawasu lokaci,ahaka suka kwasheta suka koma gida da'ita Sulaiman baiyi tunanin komai ba yace akaita bangarenta babu musu kuwa sukayi abunda yace din straight bandaki yashiga yadebo ruwa ah rubber sannan yazo yazauna gefenta dukda warin da jikinta yakeyi hakan baisa yadamuba sema diban ruwan dake rubber dayayi yashiga yayyafa mata ahankali aikuwa segashi tafara motsi da jikinta bashi kadai ba har Hamida wani irin wawan ajiyan zuciya sukayi tareda hamdala.......
Kuka Hamida keyi sosai harda shesheka yayinda sautin kukan nata ne yasa Magajiya tafara bude idanunta dasuke mata dishi dishi dakyar tasamu suka budu sannan tadaura su kan Hamidan, bakaramin mamakin ganin yartata tayi ba amma batada bakin magana don ayanda takejin jikinta ko A dakyar inzata iya cewa,matsowa Hamidan tayi tana sannu Mama yayinda haryanzu batabar kukan datakeyi dinba.. ..
Shima Sulaiman din sannu yashiga yimata haka Zaliha ma dake can tsaye Asma'u kuwa tunda suka dawo take bangaren su daman batareda ita sukazo bangaren Magajiya dinba......
Itadai se binsu da'idanu kawai takeyi dukda ita kadai tasan yatakeji aranta game da kowannensu ganin shirun yayi yawane yasa Zaliha cewa bari taje tasa ahado kayan abinci intaci setasha maganin may be tasamu taji dadin jikinta.....
Gyada mata Kai Sulaiman din yayi inda tafice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login