Showing 33001 words to 36000 words out of 235422 words

Chapter 12 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3527

this,kinsan abunda yar uwarki takeyi Amma bakizo kinfada ah gidaba?".....
Cikin kuka tace I'm sorry Yaya Mubaraq,kobi takanta beyiba yabar ta tsaye agurin......
Kuka tashigayi sannan tawuce bangarensu ranar kasa bacci tayi kwata kwata gabadaya tashiga damuwa,washegari dasafe Asiya tatashi taganta ah parlourn Daddy, mamaki ne yakamata yayinda abubuwan dasuka faru suka shiga dawo mata dafe kirji tayi tana furta yau tashiga uku sannan ta tashi cikin sauri don guduwa hartakai bakin kofa taji muryar Daddy yanacewa where do you think you're going?......
Juyowa tayi idonta yataru da kwallah,ahankali yace kidawo kizauna komawa tayi tazauna tareda gaisar dashi amma ko kallon inda take baiyiba,Kiran Mommy yayi sannan yace takira kowa ah gidan yazo,aikuwa cikin minti ishirin kowa ya hallara ah parlourn,da addu'a Daddy yabude taron kafin yadubi Asma'u yace what do you know about this,nan tashiga zayyano mishi komai sannan tafada mishi har fada tayima Asiya sanda tasani kuma tayi tunanin tabari ne sekuma tabashi labarin yanda akayi jiya......
Babu abunda kowa keyi ah parlourn se sallallami, Hajja ne tace cikin kuka menake fada miki Zainabu?,nasan wataran se matarnan tahada miki makirci keda 'ya'yanki gashi ya tabbata,inba sharri ba mezaisa yarinya mai hankali kaman Asiya tasha giya takarashe maganar tana goge kwalla da kasan zaninta,dafe Kai Daddy yayi sannan yace Hajja da idonmu munga state din da Asiya takeciki jiya saboda haka kidaina tunanin wani neyayi mata sharri....
Cikin tsawa Hajja tace kai dallah rufemn baki,Kai daman ai bakason afadi laifinta kwata kwata,shiru Daddy yayima Hajja seda tagama mitarta tatashi tatafi sannan Daddyn yadubi Asiya...
rayuwar dakika zaba ma kanki kenan,karatun dana tura ki kiyi shine laifina ko?.....
Jijjiga Kai tashiga yi tana kuka, Allah Daddy bahaka bane kuma Itama munafukar data jamin meye batayi ina ita da illigitimate son din sarki take soyayya ma,babu wanda baisaniba cikin makarantar Mubaraq ne cikin tsawa yace inbakiyi shiru ba Asiya zanzo inmiki dukan tsiya agurin,kinyi laifi accept it bawai kizo kina wa wani sharriba,Asiya bata daddara ba tace I even have the video kabarni innuna mana to prove you wrong.....
Daddy ne yace Ina video din yake?...
Tashi tayi zataje tadauko wayarta Mubaraq yace you don't have to I've it in my phone and munyi magana da ita Asma'u din dajimawa she told me everything and natambaya naji gaskiyar magana nan Mubaraq yashigama Daddy bayanin abunda yafaru sannan yace batasan wayeshiba kawai she was trying to help Kuma tun lokacin nace mata babu ruwanta dashiga harkar daba nataba tunda ba itakadai bane agurin tunda taga wani baitaimakeshiba that means something is wrong......
Jijjiga Kai Daddy yayi alamar gamsuwa sannan yace koma miyenevKuma koma wayene dalaifi dawanda yayi dakuma wanda baiyiba I've finally made my decision,dukkansu zan aurar dasu because wannan abunda yafaru yazamemin darasi sannan yakuma dubansu kushirya aurenku tareda Mubaraq zan hada,nakira Aslam da Mukhtar din anjima insunzo zanyi magana da kowannensu sannan yadubi Asiya kekuma daga yau babuke babu zuwa makaranta indai kina cikin gidan nan inshi mijin naki yaga zai barki daga baya kiyi karatun wannan tsakaninkune sannan yakalli Asma'u nabarki kije makaranta but that does not mean kiyi duk abunda kikaga dama,if anything goes wrong kema thesame punishment zanbaki,your punishment na kinfada mana abunda Yayarki tayi shine auren dazanyi miki batareda kinshiryaba and duk wata mace data ke tasowa ah gidannan tasaka ma ranta cewa babu ita babu zuwa jami'a ah gidana data gama secondary school zanyimata sure in mijinta yaga dama shiyasata ah makaranta, this's my final decision and no one can change it....
Nan Daddy yatashi yafita yabarsu da jimami,Ummi da Mommy ne suka dubi juna yayinda Ummi tace yanzu yaza ayi Anty Zainab?......
Dafe Kai Mommy tayi sannan tace addu'a shine mafita Allah yasa auren shine mafi alkhairi garesu don kuwa babu mai iya canzama Babansu ra ayi nina rigada nasani.....
Gyada Kai Ummi tayi sanin halin Mai gidan nasu sannan ta tashi don tafiya don tasan gaskiya Mommyn ke fadi,Daddy mutum ne mai tsatsaurar ra'ayi inya fadi abu yazauna kenan, Mubaraq ne yace Ummi matakin daya dauka shine daidai dasu kowa taje gidan mijinta shine mutuncinta ni inabayan Daddy they should even thank God wanda sukeso ze aura musu if I were in his shoes wasu tsofi daban zan nema inhadasu dasu yanakaiwa karshe yatashi yafice Aliyu da Musa bin Yayansu suma sukayi batareda sunce komaiba haka Mommy tafice don raka Daddyn zefita,duban Asiya Asma'u tayi Ido cikeda kwallah tamatsa kusa da ita"I'm sorry Aseey,bantaba tunanin it'll turn out this way ba"......
Daga mata hannu Asiya tayi sannan tace don't touch me,ya isheki haka you've finally succeeded kinji dadi ai tunda an rabani da abunda raina keson yi,kinji dadi ai tunda ke zaki cika burinki ke kadai daman ah gidannan kene who's always right inni nayi abu I'm always wrong,tafa hannu tayi you should celebrate now Asma'u,sannan tanunata da dan yatsanta but believe me yanda kikasa nayi bakin jini ah gidan nan senasa kema kinyi,infact senasa duka yan gidannan sunyi maki tsanar daba'a taba yimawani ah duniyar nanba, I'll make your own mother to hate you to the point that zata yafeki Asma'u,I promise you that inadani kikeja......
kuka Asma'u tashigayi metsuma rai yayinda Asiya tafita tabarta ah gurin Itama kukan takeyi.......
Innalilahi wainna ilaihir rajiun,shine kawai abunda Asma'u ke furtawa,itakam wannan wace irin jarabawa ne yasameta,kuka tadingayi kaman ranta zaifita haka ranar bata tafi school ba don bakaramin ciwo kanta yashiga yiba.....

*****
Tunda yadawo daga masallacin sallar asuba yawuce prison din masarautar, dogarayen nazubewa kasa suna mika mishi gaisuwa suka mishi iso,cell din da akarufe Afiya aciki yakarasa sannan yasa suka bude mashi...
Tana kwance jikin gini ta rakube kanta dakaganta kasan ah tsorace take baccin,karasawa yayi gabanta wanda jin motsinsa yasata firgita ta tashi cikin sauri"don Allah kada ku dukeni wallahi banyi komai ba"tayi maganar cikin firgita tareda folding two hands dinta guri daya alamar roko takeyi.......
Cikeda tausayawa Sulaiman din idanunshi yaciko da kwallah,kamo hannun nata yayi sannan yace little Angel it's me kidaina tsorata Sulaiman ne,your Brother.....
Dagowa tayi ta kalleshi idanunta jage jage da hawaye harsun kumbura gawani baki datayi kwana biyun datayi ah prison din,cikin kuka tace Yaya Sulaiman!kafin tafada jikinshi cikin sauri kuma tajanye tana auchhhh tana dan taba jikinta,cikin sauri Sulaiman yace what's wrong?.....
cikin kuka tace don Allah kataimakeni ka fidda ni agurin nan kullum dukana sukeyi,'yar goge kwallarsa yayi sannan yace stop crying my dearest Sis,I promise I'll get you out of here as soon as possible kidaina kuka......
Dan shiru tayi tana shesheka tareda ajiyar zuciya seda yatabbatar tadaina kukan sannan yatashi yatafi cewa guards din yayi sukira mishi Sarkin yari, sanda yazo yace adaina dukanta and anabata abinci mekyau,gyada kai Sarkin yari yayi yayinda Sulaiman yafice agurin yana tunanin mafita, straight gurin Mai Martaba yawuce yana dakin shi bai fito fadaba don haka yazauna ah parlour yana jiranshi yafito,sanda yafita karasawa yayi gabanshu ya zauna sannan cikin girmamawa yagaidashi..........
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace,Babana Kaine da safennan?.
Eh Abba nazo infada maka ana nemana ah makarantar mu ne urgently......
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace auren naka bayazoba kabari in anyi sekatafi mana,sauran sati biyu kuma ga shirye shiryen da akeyi......
Dan gyara zama Sulaiman din yayi sannan yace bajimawa zanyiba nafada musu amma sunmatsamin intafi ne....
Dan shiru Mai Martaba yayi sannan yace toshikenan, Allah yakaika lafiya yadawo dakai lafiya.....
Amin ya Allah, godiya yayima Mai Martaban sannan yace da daddare in Allah ya yarda zamu tashi.....
Safe journey cewar Mai Martaban godiya yakuma yi sannan yafice ah parlourn........

****
tana kwance wuraren la'asar Ummi tashigo tana kallonta kafin tasamu zama gefen gado sannan tadubi 'yartata"yanzu ke anfada miki kuka shizaisa Babanku yacanza ra'ayinshi komi?".....
Jijjiga ma Ummin Kai tayi alamun aa batareda tace komaiba,fada Ummi tashigayi mata,inma zaki tashi gwanda kitashi kidaina wannan langabewar don ba sawa zaiyi acanza abunda akayi niyaba kinadai gani jarabawa ne agabanki gwanda kikwantar da hankalinki kiyi karatunki banason Ina ganinki haka......
To Ummi in sha Allah,taba jikinta Ummi tayi sannan tace ko kefa,bakida abunda yafi addu'a kilan wannan shine mafi alkhairi gareki,kicigaba da addu'a nima zantayaki kuma ma tunda Mukhtar ne nibana wani fargaba besides kunason junanku,so nibanga abun tada hankaliba.....
Ummi ni damuwa na Asiya she's blaming me for everything and on the other hand Yaya Mubaraq ma haushina yakeji sabida wai banfada ah gidaba....
Cikin rarrashi Ummi tace kada kidamu Mubaraq ze sauko Asiyan ma haushin naki for the mean time ne she'll calm down,kuma tayi laifi ai dole kifada ko?.....
Hakane cewar Asma'u din yayinda Ummin tace kitashi kiyi sallan laasar kifito kici abinci banason kunshewan dakike ah dakinnan don gobe dolenki kishiga makaranta.....
To Ummi,ta ansama Ummi din yayinda Ummi tafita itakuma tashige bandaki don dauro alwala,tun tana bandaki phone dinta ke ringing seda ta idar da alwalan sannan tafito tadauka Allah yataimaketa be katseba call din.Zahra ce ahankali tace"Zahra yakike?"...
Ah daya bangaren Zahra tace I'm fine,hope lafiya naga baki shigo school bayau.....
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi sannan tace kaina ke ciwo Zahra amma naji sauki in sha Allah gobe zanshigo....
Cikeda damuwa Zahra tace"alright then, Allah yabaki lafiya Asma'u sekin shigo goben".....
Thank you Zahra...
You're welcome,take care kigaidamin su Ummi....
Murmushi Asma'u takumayi tana dan goge ruwan fuskarta tace zasuji in Sha Allah kafin tayi hanging up call din,she wants to share her problems with someone sede batajin zata iya fadama Zahra bawai don bata yarda da itabane kawai dai she just don't feel like it's okay, lumshe idanunta tayi tana tuno kalaman Ummi data kecewa "besides kunama son junanku", tambayar kanta tashiga yi does she really love Mukhtar,kodai kawai she's just giving him a chance ne?....
She just know that she respect him very much and she trust him kuma tadaukeshi ah matsayin wanda yan gidan su sukeso besides she always feel okay and happy when she's around him,may be this's the feeling da mutane ke Kira da love din, ahankali tafurta"that means I love Yaya Mukhtar?"....
Kasa bama kanta ansa tayi don haka seta tashi tadauki hijab dinta tashimfida sallaya ta tada sallah......

***
Daddy kuwa tunda yakira Mukhtar ajiya da daddare hankalin Mukhtar bakaramin tashi yayi ba don besan me Daddyn zece mishiba don haka tunda gari ya waye yashirya kan daya fito ah test zewuce office din Daddyn Asma'u din yasameshi,aikuwa yana fita ah test din yawuce gurin Daddy din,bayan sun gaisane Daddy yacemishi kaga nakiraka ko?...
Kan Mukhtar nakasa yace eh Daddy, murmushi Daddy yayi yace I'm sorry to announce this nayi deciding zan hada auren Asma'u da Asiya dana Yayansu sabida wani dalilina shiyasa nace barina kiraka infada maka if you're ready katuro parents dinka tunda naga kun fahimci juna and you've something doing......

Wani dadi ne yakama Mukhtar don kuwa yajima yana jiran wannan ranar, eh Kam he's not ready for the wedding as in betaba tunanin abun will be this soon ba hakana Kuma bashida matsala koda kuwa za ayi kwana kusanne tunda ba aikinyi yarasa ba because bawai karatun kadai yasaka ah gabansa ba yana business sosai.....
Murmushi yayi sannan yace babu komai in sha Allah zanyi magana da mutanen gida...??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????.
Dan numfasawa Daddyn yayi sannan yace hope dai ban takuramaka ba? ...
Eh Daddy babu takura wallahi, Allah yasanya alkhairi aciki, nagode kwarai.....
Murmushi Daddyn yayi sannan tace to Masha Allah,yayi kyau,sundan yi hira duk akan business dakuma karatun Mukhtar din kafin yayi ma Daddyn sallama yatafi...
Aslam kuwa dake ah kaduna yake besamu shigowaba se yanma don haka ah gida yasamu Daddyn yanda sukayi da Mukhtar haka yayima Aslam din sede yafadamishi duk abubuwan da Asiya tayi amma dukda haka Aslam yace ya yarda zeyiwa mahaifinsa magana don bakaramin so yakema Asiya ba tunda daman yakeson turo iyayenshi itanedai tahanashi, mahaifin Aslam da Daddy business partners ne wanda tsabar shakuwarsu sunzama kaman family.........
***
Tunda safe dayabar parlourn Mai Martaba yakoma bangarenshi yasaka kuyangunsa suka shiga hada mishi kaya,seda aka hada tas aka ajiye gefe daya sannan yafice yabar gidan bashi yadawoba se karfe tara na dare,shima saka dogarinshi Isah yayi wanda sun saba yafitar mishi da kaya zuwa mota shikuma yashiiga wanka,seda yayi wanka yashirya tsaf cikin kananan kayanshi sannan yaci abincin da aka kawo mishi,duba time yayi karfe goma darabi,lumshe idanunshi yayi sannan yafice straight gidan yari yawuce nan yasa guards din suka bude masa cell din da Afiyan ke ciki idanunta biyu bakaman dasafe daya sameta tana bacciba, murmushi yasakar mata wanda bawai yakai har zuci bane kawai dai just to give her courage,gaidashi tayi ahankali sekuma ga hawaye,kama hannunta yayi sannan yace taso zaman ki anan yakare Afiya...
Cikin sauri ta tashi tasa hannunta cikin nashi tarike kakam haka suka fito daga cell din,duban guards din sukayi du kansu ah kasa dukda kuwa wani irin tsoro ne ah tattare dasu sede babu halin magana don basu Isa suyi questioning din Yarima guda ba,cikin sauri yace kibiyoni nan sukabi tawata kofa inda ba mutane sosai harsuka isa Mota cewa yayi tashiga,kallonshi tayi sannan tace "where are we going daman bagurin su Ummi zaka kainiba?"....
Ahankali yace,"I'm sorry you can't meet them now, I've to take you somewhere far kafin musamu solution Afiya just trust me.....
Goge kwallarta tayi sannan tashige motar,driving yafarayi har suka bar masarautar fatanshi daya Allah yasa har yabar garin Zaria kada Magajiya tasamu labari...



Vote
Comment
Share!

[3/23, 5:23 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert* @wattpad

*Page 11*

Acan gidan yari kuwa su Sulaiman na fita daya daga cikin dogareyen yayi saurin zuwa yasamu Sarkin gidan yari yake fada masa sannan yake tambayar shi yaje yafada ma Magajiya ne!....
Cikeda tashin hankali Sarkin gidan yari yace babu ruwanka kakoma bakin aikinka harsai inta zo dakanta ko ta tambaya se ace mundauka ita taturo Sulaiman din don kuwa banshirya fita yawon banza da daren nan ba kasan muddin akafada mata zatace se annemosu kuma dai ninasan ba samunsu zamuyiba tayuyuma shi Yariman barin garin zeyi da'ita......
Gyada Kai dogarin yayi yakoma bakin aikinsa dukda kuwa zuciyarshi bugu takeyi don yasan daga karshe shine ah ruwa kuma dai bai isa yayima Sarkin gidan yari musuba.......
*****
Kanada tabbacin kana ganinshi da mace kwanan nan Magajiya tayi tambayar cikeda mamaki.......
Cikeda assurance mutumin yace tabbas Uwargijiyata don sau biyu inaganin su tare sede kaman ita yarinyar ne kebinshi don ranar har tureta yayi tafadi sekuma akwai ranarda nagansu harda kanwarshima dakuma yarinyar,gyada kai Magajiya tayi sannan tace kayimin bincike akan ita yarinyar kaji?...
kanshi na ah kasa cikeda biyayya yace to uwargijiyata, murmushi tayi sannan tace ina nufin komai game da yarinyar tundaga gidansu har zuwa rayuwarta na makaranta zuwa jibi ka tabbatar kazomin da komai,gyada mata Kai yayi sannan yayi godiya yatafi.....
Talatu dake gefen Magajiya ta washare baki cikeda gulma tace "Uwargijiyata kinji yaro yagirma har budurwa yayi,ai dama mun tambaya ko kyakyawa ce mai aji don kuwa irin matan dasuka dace hadadden yaron can kenan" .....
Cikeda takaici Magajiya takai hannu zata maki Talatu,cikin sauri Talatu ta gauce sannan tashiga neman gafara"wallahi tallahi Uwargijiyata subutar bakine, Allah kuwa".....
Harara Magajiyan takai mata"inbaki iya bakinki ba I can't help it wataran senayi rugu rugu dake wallahi"....
Za agyara Uwargijiyata tayi maganar kaman zatayi kuka,tsaki Magajiya tayi don bakaramin bata mata rai Talatun tayiba sannan tawuce tabarta agurin.......
***
Kusan 12:00am ya Isa cikin garin kaduna straight gidansu abokinshi yawuce wanda already daman yakirashi yafada mishi yana hanya da kanwarsa.........
Bayan sun gaisa da Matar Idriss dinne wanda itama batakai gayin bacci ba yayi musu sallama yawuce hotel abunsa dukda kuwa sunyi sunyi yakwana tunda sunada extra room amma yaki, washegari wuraren goma yazo yadauki Afiya yakaita shopping don kuwa batazo da kaya ko dayaba dadai sauransu se kusan azahar suka dawo gida inda yake cemata da la'asar zasu wuce Abuja....
Itadai mamakine yakamata don tayi tunanin ah kaduna ze barta tazaune tareda Matar Idriss din don harta fara jin dadin zama da'ita sabida Matar akwai kirki kuma koda zata girmeta ma to befi da irin shekaru biyu ko daya ba,amma se bata tambayeshi ba tunda yace mata she should trust him to tayarda dashidin tabbas.....

****
Tunda Asma'u tagama shirin makaranta setasamu guri tazauna kamar yanda tasaba ada intana jiran Asiya,setakejin kaman zata aiko akirata tazo su tafi seda Ummi tayi mata magana sannan ta tashi tatafi hannunta rikeda car keys.......
Tana zaune cikin motar takira wayan Zahra seda suka gaisa sannan take tambayar Zahra din kota shigo school nan Zahra kecemata a'a bata shigo ba tukunnan ai Antynta ma tahaihu adaren jiya dakyar inzata samu shigowa,cikeda farin ciki Asma'u tataya Zahra murna sannan tace tagaida Antyn inta tashi ah school may be tabiyo tayi musu barka...
Ah dayan bangaren ne Zahra tace to senaganki Asmeey,nan sukayi sallama.....
Tunda Zahra tace mata bazata shigoba setakejin batama jin shiga school library yau don dama itane me sata zuwa din, starting motar ta tayi sannan takoma hanyar gun data saba ganinshi parking motar tayi ahankali sannan tafito hannunta rikeda litattafanta tayi lungun gurin seda ta lelleka tako ina amma bayanan juyowan dazatayi kuma setayi arba dashi daga can gefe yana karatunshi hankali kwance, murmushi tadan yi sannan takarasa inda yake harta samu guri tazauna bece mata komaiba hakanan bedago yakalletaba amma bata damuba setace...
"Ina kwana Yaya Almustapha?".....
Dukda yayi mamakin ya akayi tasan sunanshi seya kyaleta be kulataba yiyayima kaman bejitaba,dan tabe baki tayi sannan tace insabida abunda nace ranar ne kake kin kulani I'm really sorry,I was just hurt by your attitude bawai yakai har zuci bane ba.tayi maganar kaman me shirin yin kuka. ...
Still bekulataba sema bude next page na takardar dake gabanshi yayi,sa hannu tayi tadauke littafin gabanshi yayinda cikin sauri yadago kanshi yadaura idanunshi kan nata seda ta tsorata amma seta dake"tunda bazaka kulaniba nima bazan barka kayi karatunba",wannan karan ah shagwabe tayi magana.....
Dauke kanshi yayi daga kallon oily eyes dinta ya kawar gefe sabida wani irin yanayi dayake ji wanda betaba jiba a rayuwarshi kafin yatashi ahankali zebar gurin don ya lura yarinyar neman fitina take dashi shikuma bashida lokacinta Itama cikin sauri tatashi tareda shan gabanshi sannan tamika mishi littafinshi"indai don nabaka hakuri ne zaka tafi, I'm sorry just stay back bazan sake damunka ba"....
Yanda tayi maganar seyaji jikinshi yayi sanyi, atleast she's being nice and hakurine yakamata yahakura tunda ko Allah ma muna mishi laifi ya yafemana ballantana mukuma bayinshi,karban littafin yayi kaman bazaiyi magana ba sekuma yace"It's okay".....
Kallonshi tayi sannan tace"hakan na nufin ka hakura?"....
Jijjiga mata kai yayi sannan yajuya zai tafi cikin sauri tace indai ka hakura basai katafiba please kazauna kayi karatunka nima zanje can inyi....
Bayason musu da takura don haka yakoma yazauna Itama godiya tayi mishi sannan ta tafi can dan nesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login