Showing 114001 words to 117000 words out of 235422 words

Chapter 39 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3497

Mai Martaba yayi ahankali tareda kallon dan uwannashi kafin yace...
"Nima da nawa laifin Yaya,inada nauyi me yawa akaina amma bantaba tunanin cewa they might need me ba bntaba tunanin inje dakaina inji matsalolinsu ba sannan bantaba zuwa don ganin aikin danasa ayi masu yanakyau ko baya kyau ba I trusted the people I shouldn't have".......
Dan dafa shoulder dinshi Dad yayi in a comforting manner yace"abunda yasa baka dubawan sabida kayarda dasu kayi tunanin they're doing the right thing",su kuma sun yaudareka they're the one to be punished Abdul yanzu mutanenka na bukatar ka you need to put things in their right places........
Gyada kai Mai Martaba yayi kafin yace Galadima will be under house arrest for three months and Magajiya for two 2 month sabida ita nata laifin baikai nashi ba dukda yana ikirarin itata saka shi amma I consider him to be a Coward ya zaayi mace tace kayi abu sannan kayi fisabilillahi so, that's his punshment and dole yafi nata........
Gyada kai Dad kawai yayi kafin yace..
"hakan ma yayi atleast they will learn their lessons"......
Haka kuwa akayi Mai Martaba yafita fada sannan yasa aka kira masa Galadima da Magajiya inda yafadi laiffuffukansu gaban kowa wanda sukansu sun kasa denying sannan yabasu punishment dinsu kaman yanda yafada ma Dad..........

Magajiya kaman tayi hauka takeji tsabar bakin ciki wato yanzu dai she has to go back to that place datayi tunanin bata kara komawa ah rayuwarta babu abunda yafi damunta irin yanda Mai Martaba ya dizgata gaban kowa Galadima kuwa kowa yayi mamakin abunda yayi dubada yanda suke kusanci da Mai Martaba gakuma yarda dayayi mashi wanda ko Waziri mahaifin Magajiya baisamu wannan matsayinba haka ranar masarautar ta kaure da gulmace gulmace da kuma maganganu duk na abunda yafaru yaudin hakanan bangaren Dogaraye da bayi babu mai jajantama Magajiya sema masuyi mata Allah ya kara tareda wish din Allah yasama dagacan ah aikata babban gidan yari kota girbi abubuwan data shuka wanda are not yet revealed Laure kuwa babu wanda yakaita farin ciki donkuwa kobakomai zatasamu ta yi yanda takeso na wata biyun...........
Asma'u ma farin ciki kaman tayi yaya itada Hajiya Muniba dubada yanda abun yawakana batareda sunyi tsanmani ba atleast they'll not see her cruel face for good two months now koda Ummi taji labari murmushi kawai tayi dukda bekai har zuciba don tasan Mai Martaba must be having a very hard time right now sabida ah iya saninta babu abunda ya tsana irin betrayal babu kaman daga loved ones dinshi wanda ya yarda dasu sosai bata manta how he suffered ba sanda wannan kaddara tafada musu ah baya to tabbas tasan he'll went through thesame thing yanzuma sabida tunda jimawa tasan matsayin Galadima ah idanun Mai Martaba shiyasa bata cikin wani farin ciki sosai because batason abunda zai tada mishi hankali hakanan kuma kwanan nan time to time takan tuna da danginta wanda har takejin she wants to meet them as soon as possible ko ya suke? Allah ne kadai masani,ko zasu yafe mata abubuwan dayafaru abaya wayasani?............
Washegari Mai Martaba yakira Sulaiman da Almustapha yadubesu cikeda son ya'yan nashi sannan yace....

"nakiraku ne sabida muyi magana akan ayyukan dayakamata ayi yakamata mugyara abubuwan da mutanen da muka yarda dasu suka bata and as of now i trust no one but you two sekuma Yaya daga abunda yafaru jiya it's really going to be hard for me to trust any one anymore"........
Gyada kai sukayi duka cikeda tausayin mahaifin nasu don daga yanda yake maganar ma zaka gane akwai bitterness sosai acikinta cikin nutsuwa yace"Almustapha"....
Dagowa Almustapha yayi tareda kallon mahaifinnashi ahankali.....
"na'am Abba"....
nadanka maka project ah hannunka na boreholes i want you to go ahead with it and kudi da komai zan baka sekuma you need to go to that hospital after that kaga ya ayyukan ke ciki..............
Gyada Kai Almustapha yayi kafin Mai Martaba yadubi bangaren da Sulaiman yake sannan yace"about maganan renovation na bangaren bayi dakuma katifu da pillows and everything they'll need zanbari ah hannunka Babana because aikin zaiyima Imam yawa"......
Cikeda ladabi Sulaiman yace to Abba ammadai I've something to say.....
"Go ahead Son inajinka" mai Martaba yayi maganar yana kallon Sulaiman din sunkuyar dakai Sulaiman yayi kafin yace"ni anawa ganin Abba,Yaya should be the one to take over komai daza ayi sabida karka manta anbashi nanda wata biyar yayi proving kanshi as the best person to be the crown prince Abba and only tawannan hanyoyin ne zai cinma burinsa kuma tawannan hanyar ne mutanen gari zasu yarda dashi sukuma san shine yacancanta ba wani ba,agreed I'll help him out amma aboye something like zuwa sayan katifu da pillows dakuma nemo masuyin aiki sede he'll be the to supervise all the time daman boreholes kam aikinshi ne shi kadai but wannan dinma shi ne za ace yayi".....

Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace "thank you Son, Allah yayimuku albarka hakan ma yayi, Allah yacigaba da hada kayukanku kuma, Almustapha shidai se kallon Sulaiman yakeyi cikeda sonshi he don't know how to pay him,he's indeed the best Brother he could ever ask for...........
Sulaiman ganin yanda Almustapha ke kallonshi ne yasashi yin murmushi tareda cewa"you've to work hard for your people Bro they really need you,make us proud please I can't wait to see your turbaning ceremony"......
Almustapha besan sanda yaja Sulaiman yarungumeshi cikin jikinshi ba cikeda son shi.....
Mai Martaba da Dad ne suka kalli juna tareda sakin murmushi because seeing both the two sons together hakan yatuna musu da sanda suke samari kaman su yayinda kowannensu yake fatan Allah yasa zumuncin dake tsakanin su ya dore harzuwa karshen rayuwarsu ........

bangaren Zaliha kuwa bakaramin tashin hankali tashiga ba jin abunda yafaru da Magajiya din because koda tayi fushi da'ita she really need her sabida itakadai tasan bazata taba executing plan dinsu ba don hakane ma bayan kwana biyu da faruwar abun taje tasamu Magajiya din ah house arrest din don ba ahanata ganinta ba because wannan din bekai nada tsanani ba...........
Allah yataimaketa Magajiya ta sauko daga gandun fushin da takeyi zama tayi gefenta tareda cewa "Mama I'm really sorry"takarashe maganar murya akarye kallonta Magajiya tayi wanda cikin kwana biyu harta sake ramewa ga duhu data karayi sannan tace...
"we're still together karki damu because komiye zasuyi I can never let them win!"......
Cikedajin dadi Zaliha tace...
"me too Mama sedai yanzu yazamuyi sun rufeki tayaya zamu cika burinmu?".....
Murmushin mugunta Magajiya tayi kafin tace Almustapha yanada sauran wata uku kafin yacika burinshi nikuma wata biyu zanyi anan suyi duk abunda zasuyi when I'm out I promise you acikin wata dayan nan zan ruguza komai karki damu banason nayi wani abu yafaru inacikin nan sabida kada hakan yajaza mana karaya sedai inason kinemi wata baiwa Salma she's one of my people tana bangarensu Almustaphan I asked her to keep an eye on them and last week tafada min babu abunda yataba shiga tsakanin Almustapha da Asma'u infact baswa kwana daki daya and it seems that they're not on good terms kawai duniya ne take ganin suna tare kamar masu son juna but in reality that's not the truth kiinga wannan wata hanya ce dazai taimakemu but still kinemeta tacigaba dasaka musu ido tana kawo miki information nikuma duk yanda ake ciki just let me know in akwai abunda zamuyi semuyi kafin nafito din dukda I hope nothing works out between the two of them.........
Jinjina kai Zaliha tayi kafin Magajiya tace and yes kiyi aiki akan position din da Mai Martaba yabaki just act like nothing happens and you're okay with it....
Gyada kai Zaliha tayi ahankali sannan tayima Magajiya godiya tafice babu abunda yafi damunta ayanzu ma dayawuce yanda Sulaiman yarage mata maitan son su shirya and baicika shigowa bama se tayi bacci wataran she really don't know what's going on with him amma koma miyene bazata biyeshiba she's sure in the future zegane sonshi takeyi shiyasa takeyin hakan................

Satinsu Munira daya Sulaiman yamaidasu gida Asma'u harda hawayenta don bakaramin jin dadin zuwansu tayiba sabida suna debe mata kewan gida bakadan ba.......

*TWO MONTHS LATER*......

Around 9:20pm
Zaune take ah parlour tana kallon ZeeTV taji wayarta tayi kara dubawa tayi Sulaiman ne batareda tayi wata wataba tadaga......
"Sister in-law"shine abunda yace...
Yar dariya tayi sannan Itama tace"Brother in-law"don kwanan nan tagama gane Sulaiman akwae son tsokana shiyasa Itama karfi da yaji ta koya inyace Sister Inlaw tace brother in-law inko yace Aunty Asma'u Itama Uncle Sulaiman inma Yaya Asma'u yace Itama Yaya Sulaiman haka suketa fama dai......

"Lol kindai dage sekin rama duk tsokanar danayi miki", murmushi tayi to yazanyi dakai Yaya Sulaiman....
"Hhhh toshikenan tunda haka kikace daman nakiraki ne incemiki ki kunna TV za'afara network news akwai abunda nikeson ki kalla"...
"To shikenan",tabashi amsa kafin tamaida Chanel din zuwa netwrk news din gani tayi ana nuna abubuwan da Almustapha yayi cikin watanni hudun da aka bashi acting crown prince,acewar me bada labaran he has achieved many things wanda yataimaki talakawa dadama kama daga kan availability of wata acikin garin Zaria wanda yaduba areas dasuka fi tsananin wahalar ruwa yakuma taimaka musu wurin dauke wannan wahalar hakan kuma bakaramin taimaka musu yayiba Mai bada labarin yafadi yayinda aka shiga hasko unguwannnin acikin talabijin tareda nuna yanda akayi musu boreholes da panpuna gakuma jama'ar unguwar na ta diban ruwa cikeda farin ciki ah fuskokin su....
Samun wasu daga cikin mutanen unguwar akayi yayinda medauko rahoto yashiga yi ma daya daga cikinsu interview....
Yaya sunanka?.....
Dattijon da aka tambaya yasa bakinshi ah mike din tareda cewa...
"Sunana Hashimu Ibrahim".....
To barka da rana Mallam Hashimu Ibrahim meye zakece gameda wannan cigaba dakukasamu ah unguwannin talakawa da dama?........
Dan murmushi dattijon yayi kafin yace"Babu abunda zanfara yi se godema Allah daya aikomana da mutumin kirki kaman Yarima Almustapha sabida mu mungani munkuma yarda without him duk wayannan abubuwan will never be possible tunda kusan shekara na ishirin cikin garin Zaria bantaba ganin anyi mana aikin da shi yayi mana ba kama daga kan gwamnati har ma sauran shuwagabannin dasukayi mulki abaya,shiyaduba matsalolin damuke ciki yamangance mana ita ah matsayin mu na talakawa babu abunda zamu ce masa sede Allah ubangiji yasaka mishi da alkhairi kuma Allah yakuma sake bashi hakurin duk wasu accusations dayayi tasha abaya dukdama haryanzu wasu akwai tambayoyi da dama ah zukatansu gameda shidin nidai yasani ina alfahari dashi nagode kwarai haka talakawan garin Zaria infact bama su kadai ba na yankin kaduna state baki daya".....
Murmushi mekawo rahoton yayi sannan yace muma mungode da bamu lokacinka dakayi sede inada tambayar karshe inbazaka damuba?...
Yar dariya Mallam Hashimu yayi sannan yace"feel free kayimin duk tambayar daka ga dama tunda ninayi representing duka talakawan garin nan ne don nuna appreciation dinmu ga Yarima Almustapha".......
"Ah to to ai shikenan tunda abun hakane",cewar mai kawo rahoton kafin yace"daman naji kayi maganar accusations da ake ma Yarima ada kuma kayi maganar haryanzu dadaman ku kunada tambayoyi dadama aranku shine nikeson inji wasu irin tambayoyine may be kaga hakan ya'iya kaiwa kunnen Yariman shikuma inyaga dama zai iya zai ansa muku ita daidai gwargwado"........

Gyara tsayuwa Mallam Hashimu yayi kafin yace"wannan ma wani dabara ne da tunani kuma sannan tambayoyine da basu wuce akan tasowarsa ba dakuma rayuwarsa nada sabida mudai ah iya jinmu da saninmu Yarima Almustapha mutumin banza ne wanda baisan darajar dan Adam ba,a'iya labaran damukeji shi mutum ne da ya dauki lalata ya'yan mutane ba abakin komai ba hakanan shi mutum ne daya dauki shan kayan maye amatsayin abincin cinshi da shan shi duban me kawo rahoton Mallam Hashimu yayi sannan yace agaskiya bantaba ganin Almustapha ba awannan lokacin labarinshi kawai nikeji sede tunda yahau mulki yafara yimana aiki sannan nakuma ganshi ah unguwanmu har muka gaisa tun ranar nafara kokwanton abunda mutane ke fada akanshi sabida nidai babu abunda idanuna suka gane min game dashi inbanda nutsuwa dakuma hankali ga sanin yakamata sannan zuciyata tana fadamin mutum mai irin wannan halayen bazai taba ma tunanin sanin halin da talakawa ke cikiba bare yamayi tunanin taimaka musu shiyasa farkon da akace anbashi acting Yarima hankalinmu yatashi gabadaya don atunanin mu daga ranar to kasar mu ta gama lalacewa ne sede ashe abunda bamusani ba shidin alkhairi ne garemu",daga yatsa daya mutumin yayi sannan yace" kaga yataimaka mana wurin samun ruwa in a very easy way tayarda kowa zaisamu batareda ya wahala ba sannan ga uwa uba lafiyar talakawa daya duba tahanyar bude asibiti for free ah local government din daya lura suna fama da rashin asibiti sannan neighboring villages ma suna samu suje su aduba lafiyar su kuma abasu magani kyauta cikeda girmamawa batareda an wulakanta suba kuma naji anacewa ma yana gina wani asibitin ah garin nan gakuma masarautar su daya duba halin da Bayi da dogaraye suke ciki ya taimaka musu wannan kadaima bakaramin cigaba bane ba sannan bakaramin kokari yayiba don bakowa bane za iya wannan ayyukan acikin wata hudu Kuma mu munyarda dashi amatsayin wanda zai mulke mu bayan Mai Martaba sarki Abdulrahman muna bayanshi dari bisa dari don kamar yanda nafada maka ina representing gabadaya talakawan mu ne because this's the way they feel about him kuma munfara doubting abubuwan da mutane sukaita fada akanshi harma muke tunanin ko munyi misunderstanding dinshi ne muna fatan zamu samu ansa daga gareshi kwana kusa Inna neman yafiyarshi ne munema don intakasance ba gaskiya bane abunda aka fada to tabbas mutane da dama sundauki alhakin mutum kamili irin Yarima Almustapha.........

Godiya Mai kawo rahoton yayima Mallam Hashimu kafin yajuya yana kallon Tvn "to masu kallonmu kundai ji hirardamukayi da Mallam Hashimu wanda ya jagoranci talakawan garin Zaria yakuma fadi abubuwan dasukeji gameda Yarima Almustapha wanda yayi fice cikin watanni kalilan sabida halinsa nagari dakuma nagartarsa gakuma tausayin talakawa da yasa agaba tahanyar taimakonsu dukdama sunce sunada tambayoyi zuwaga gwarzon namu kuma inshallah zamu gwada yi muku alkawarin gwada tuntunban shi gwarzon namu inzai yarda yayi hira damu kozamu samu muji ainahin gaskiyar al amari"
Ahaka akakoma nuna asibitin da Abba yasiyama Almustapha ah kauyen *Gangara* under *Giwa Local government*....... Dakuma yanda talakawa daga kauyika ke karban magunguna kuma akebasu treatment cikin kulawa harma akayi hira da wasu ma aikatan gurin dama wasu daga cikin patients dasuke gun wanda duk hirar bewuce appreciation dasuke nunawa bane ga Almustapha din tareda son jin asalin labarinshi suma......

Asma'u dake zaune tana kallon TVn cikeda amazement haka batamasan tana hawayen farin cikiba ashedai rayuwarnan Inka barma Allah komai he'll never let you down koita datake tareda Almustapha bata taba tunanin things will turn out this way ba she's really very proud of him hakanan akullum sonshi kara ruruwa yakeyi azuciyarta sede ganin yanda abubuwa ke tafiya gani take rabuwarsu takusa zuwa tunda shidakanshi yace"when everything comes to an end and when everything is back to normal hakanan in iyayenta suka cire zargin da suke mata akanshi to tabbas he'll free her from this relationship",and ko kafin yatafi Gangara seda yasake fada Mata,the time has come may be because tanada tabbacin da Almustapha yayi hira da gidan talabijin yafada musu gaskiyar al amari to tabbas komai yazo karshe don ko ayanzu tasani Almustapha da'ita sunfara
fita ah zargin da akayi musu abaya daga idanun yan gidansu,to mema yarage indai batun masarauta ne everything is back to normal because angama renovation na bangaren bayi hakanan ansaka musu katifu da pillows,fans da duk wasu facilities dazasu bukata hakanan kuma tayi make sure yanzu basuda wata damuwa regarding wahala kamar jakkai don Almustapha dakanshi yayi setting rules as the acting crown prince after 11:00pm bayason yaga kowacce baiwa awaje dasunan tana aiki she should be in their hostel resting sekuma biyar din asuba wanda Asma'u ce tabashi wannan shawarar dubada yanda problems na raping bayi dakuma lalata da ake dasu yayi yawa wanda tanada tabbacin fitan daren nan ne kesawa hakan yafaru kuma yasa ana rufe bangaren nasu 11:00pm dot sekuma biyar na asuba za'a bude wanda Sulaiman ne yadauki nauyinyin patrol akan batun har abun yadaure sannan Almustapha yayi setting rules akan batun karatunsu na addini every Saturdays and Sundays 8:00~10:00am time na islamiya dinsu ne kuma babu wanda ya'isa ya hanasu zuwa don Mai Martaba kanshi yayimagana akan hakan very strictly insunada aikin dazasuyi ma mutum suyi before that time or after sannan sunbama dukwani dogari da bayin daman insuna son auren junan su su fito su fada sukuma zasu goya masu baya dari bisa dari kada su boye sede bazasu bar masarautar ba they'll remain over there as slaves but zasu samu nasu gidan cikin masarautar hakan kuma bazai hanasu yin aikinsu ba they're humans too suma sunada needs din dakowacce mace da namiji sukedashi so,bazasu tauye musu wannan hakkin ba haka batun kayama cikin satinnan aka gama dinka musu aka raba musu set bibbiyu abinci kuwa tuni suka fara samun mekyau kuma ishashe sannan hakan bakaramin taimaka musu yayiba gurin samun karfin yin ayyukansu mekyau batareda gajiyawa ba kumadai haryau ba asake samun wani problem ba kuma anabin doka alhamdulillah gawani respect da akebama Asma'u dakuma Almustapha din because sukansu sunsani without them all this will not be possible hakanan baswa gajiya daba Almustapha hakurin abubuwan dasukayi mashi abaya barinma wanda sukasan suntaba fada mishi maganar banza dadai sauransu.......
Asma'u kuwa rashin dawowar Talatu haryanzu damunta yakeyi gashi ita ba wayaba bare ta kirata fatanta daya Allah ubangiji yasa ba guduwa tayi ba dukda 89% na zuciyar ta nafada mata ba guduwan tayiba tunda alokacin she can see that Talatu is telling the truth and she was willing to help adduarta daya Allah yasa she's fine dai ga haryanzu ba afara renovation na gida baki daya ba bare Sulaiman yasamu yacire wayannan layoyin don Abba cewa yayi abar renovation din tukunnan se angama dawanda is important tunda su nasun kowani two two years akeyi na mutane masu bukata yafi mahimmanci yanzu daga baya ayi nasun tundama it's not that necessary..............
Goge yar kwallarta tayi tareda canza Chanel don dama abunda tazauna kallo kenan kuma angama don ita ba gwanar kallon news bace daman....
Kallon screen din wayarta tayi"she's badly missing him yau kwananshi goma kenan da tafiya kauyen *Gangara* kuma ko kiranta baiyiba itakuma duksanda tadaga waya zata kirashi seta kasa sabida gani take he should be the first to call dukdama cikijn watanni biyun relationship dinnasi yadanyi improving tunda sukan zauna suji matsalolin juna and subama juna shawara hakanan sometimes sukandanyi hirar da baza arasaba dukdama itace mesurutun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login