Showing 39001 words to 42000 words out of 235422 words

Chapter 14 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3473

yayinda yawuce yatafi straight kasuwa gurin Mallam Hudu bayan sun gaisa ne Almustapha yace"zamu samu gida please?".....
Cikeda mamaki Mallam Hudun yace gida kuma,meya faru dan dafe kai Almustapha yayi yakumacewa"gidan haya nike nufi"....
Jijjiga kai Mallam Hudu yayi sannan yace ni Almustapha bangane inda ka dosaba,kana nufin gida zaku canza hakanan?.....
Jijjiga kai Almustapha yayi alamun aa, ahankali Mallam Hudu yace koranku akayi acan din?.....
Gyada Kai wannan karan Almustapha yayi,ikon Allah shine abunda Mallam Hudu yace sannan yace mutanen nan basuda imani narasa yaushene karshen wannan abun kafin Kuma yadanyi shiru yana tunanin inda zesama musu gida ah yaudin don bayason ah wulakanta su......
Tunowa dawani abokin dillali yayi,nan yashiga
kiranshi bejima yana ringing ba yadaga kiran,tambayarsa yayi koza asamu karamar gida haka bayan sun gaisa,cemishi yayi eh za a samu.....
Ayau fa muke bukatar gidan cewan Mallam Hudun...
Daga daya bangaren dillalin yace za asamu kaikam koyanzuma, godiya Mallam Hudu yayi sannan yace barinazo insameka semuje muga gidan......
Haka suka dunguma shida Almustapha don zuwa su samu mutumin yana cema Almustapha din ai gwanda ma kubar wannan masarautar don sharrin yau daban nagobe ma daban,shidai Almustapha bece komaiba harsuka isa gun mutumin yaje yanuna musu gidan,babu laifi gidane medan kyau compared to wanda suke ciki ah masarautar don kuwa wannan akwae daki da parlour gakuma kitchen sannan akwae daki ah gefe wanda zekasance na Almustapha,anguwan talakawa ne sosai don haka kudin hayan baiyi wani tsadaba,mota Mallam Hudu yasamu akaje har masarautar aka tattare kayansu da akayi watsi dasu aka kai can gidan dazasu koma din sannan sukadawo suka dauki Ummi don Amira tajima dazuwa can tana gyare gyare,dukda kuwa sanda suke duba gidan bayan tafiyar Almustapha Magajiya tazo takarashi haukanta amma taki bude kofar kamar yanda Yayanta ya umarceta....

Bayan sunkoma gidan ne Amira tagama putting komai into its right place sannan ne Mallam Hudu yace yau da dare zedawo don akwai important magana dayakeson suyi, Amira ne tace Allah yakaimu da daren .....
Amin ya amsa kafin tamasa godiya yafita,kallon Almustapha dake gefe tayi sannan tace yazamuyi da batun Afiya,yazamuyi Yaya Almustapha?...
I'll think about it shine kawai abunda Almustapha din yafada sannan yatashi yafita shima....
***
Magajiya kuwa tunda takoma bangarenta taketa banbami su Humaira ne suka shiga bata hakuri dukda haka kasa kwantar da hankalinta tayi seda daya daga cikin dogarayen yazo yace mata ai sunzo sun tattare kayansu kafin hankalinta yadan kwanta, atleast she'll now be able to sleep peacefully......

****

*INDONESIA*

Tunda jirginsu yasauka ah city na Jakarta taketa kallon kauyanci sanda sukabar harabar airport din taxxi ya tarar musu sannan yacema mai taxxi din yakaisu any suitable hotel wanda they'll be comfortable....
To mai taxi din yace kafin yakaisu hotel din wani hadadden hotel,booking two rooms yayi musu sannan aka rakasu, har daki ya rakata sannan yace tayi wanka kafin akawo abinci tomorrow morning he'll start his work,haka tayi wanka sannan tarama sallolinta kafin aka kawo abinci taci,tanaci tabi lafiyar gado dama isowan dare sukayi and she's very exhausted.....
Washegari tunda Sulaiman yatashi yayi sallar asuba bekoma bacciba kiran numbern Mallam Hudu yashigayi tasabon number din dayasaya dasuka iso amma still baya shigo don haka seyashiga wanka abunsa yashirya tsaf kafin yashiga gurin Afiya still tana bacci written note yabar mata kafin yawuce.......

Yana fita yatari taxxi yace yakaishi CIM bank,aikuwa hargaban bank din me taxxi din yakaishi biyanshi yayi sannan yawuce bank din yana duba agogon hannunshi 8:30am yawuce he hope that Uncle Almustapha yafito dukda kuwa yasan nan kam suna valueing time sosai bakamar mu Africans ba,shiga cikin bank din yayi yana kare ma gurin kallo bakidayanta, babban bank ne sosai kuma yahadu babu karya, Kai tsaye yayi ciki receptionist din yasamu bayan sun gaisa yake tambayar ta tasan wani Almustapha Sulaiman please...
Murmushi tadanyi sannan tace mai batasanshiba gaskiya,dan bubbuga hannunshi yashigayi tareda sa dayan yatsanshi abaki because he's fully sure bank dinnan yagani ah jikin paper din,tunawa yayi da yaxo ma dashi don haka yayi saurin ciro envelope din yaciro paper din dake dauke da information din Uncle Almustapha sannan yamika mata yana nuna mata passport din jiki...
Karba tayi sannan takalla,dan sakan baki tayi sannan tace"oh,you mean this Man?"....
Cikin sauri Sulaiman yagyada mata kai,dan kallonshi tayi with questioning look na miyasa yake nemanshi sekuma taga suna matukar kama don haka tamaida makaman tambayoyinta"are you his son?"....
Gyada mata kai yayi sannan yace

" _please i need to see him,can you help me?_"....

Yar dariya tayi sannan tamika mai paper din

" _I'm sorry, actually he doesn't work here anymore_"...

Dafe kai Sulaiman yayi cikeda damuwa yace" but,how could that be possible?"....
Kai tsaye tabashi amsa

" _???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?He resigned since last year,I was his secretary_"......

Da Sulaiman haryayi losing hope amma jin tace "she was his secretary" seyaji dan relief,may be tasan wani abu gamedashi.cikeda hope yace...

" _Do you know his house please,I really need your help in this,as you can see we've been separated for years now and I want to meet him that was why i came all the way from my country"_ ....

Cikeda tausayawa tace

" _I'm sorry Young Man,I don't know his current address but I know the name of the university his Daughter is studying in_"....

Cikin sauri Sulaiman yace"please tell me"
dauko pen cikin drawer tayi sannan tamika mishi karba yayi kafin tace *Bhayangkara University of Jakarta* ....
Rubutawa yayi sannan yace her name please?...
*Sumayya*,maimaita sunan yayi ahankali sannan yadan yi dariya jin yanda matar tayi pronouncing....
kallonta yayi sannan yace"thank you,but one last question please?"...
"Go ahead Young Man", murmushi yayi sannan yace "do you know what she's studying over there,I mean her department may be it could help".....
Directly tacemishi *Industrial design*......
Godiya yayi mata sosai, cewa tayi "never mind just send my regards to them",god's willing yabata amsa kafin yatafi......

Wani taxxi din yatara sannan yace akaishi address din university din da Matar tafada mishi,sanda yashiga school din kallo yashiga karema makarantar, makaranta ce mekyau dukda kuwa shi kyaunta bata razanashiba tunda yaga wayanda suka fita ah komima,taku yashigayi kafin yasamu wasu students yamusu tambaya kan inane department na industriy design,kwatance sukayi mishi kafin yatafi wurin department din,tsayawa yayi yana karema gurin kallo tareda tunanin ta ina zaifara nemanta ma tukunnan,yana nan tsaye yahango wasu yanmata biyu sunfito daga department din, daya tayi dressing cikin doguwar riga yayinda tayi rolling gyale akanta sekuma dayar tana sanye da riga da wando jeans,jeans dinma tayi folding dinshi daga kasa kadan sekanta sanye yake da hula mekyau hannunta daukeda books, ahankali yakarasa gabansu tareda yimusu sallama tunda yaga dayan tayi kama da musulma dayar kuma se yayi stretening hannun shi yana mika mata alamun sugaisa sede da mamakinshi seyaji ta amsa sallamar kuma bata mika mishi hannunba, murmushi yayi tareda maida hannun nashi cikeda kunya sannan yace"please I want to ask you something, that's if you don't mind".....
Yarinyar dake sanye da English wears dinne tace "go ahead".....
Dan sosai Kai yayi sannan yace"please do you girls possibly know Sumayya Almustapha?"..
Zare idanu tayi sannan tace, are you looking for me?.....
Dariya kawartata tayi,dan duka takai mata yayinda Sulaiman yashiga sake kare mata kallo because yakasa yarda itace.....
Uhm,you said?,takuma tambayarshi.....
Cikin sauri yace,yes,yes kenake nema.....
Yar dariya tayi sannan tace danayi laifin me kuma yau takarashe maganar tanasa hannunta ah cheeks dinta alamar tana tunani,shiko cikin sauri jin tayi hausa yasake kallonta dukda kuwa shiyafara mata hausan batareda yamasan yayiba....
Composing kanshi yayi sannan yasa hannunshi cikin aljihun wandonshi yana dan murmushi,kinason sanin mekikayi?.....
Jijjiga mai kai tayi tana dan murkuda mai baki,ciro hannunshi yayi ah aljihun wandonshi sannan yasa akan bakin nata yadan murkuda shi,ihu take shirin saki yayi saurin sa hannunshi ah bakinta,be quiet now....
Ture hannunshi tayi tana haki"who the hell are you, I'll call my father right away and he won't spare you a promise"...
Dariya Sulaiman yayi sannan yace,Daddy's favourite right?.....
Kawarta dake gefentane tashiga tsakaninsu,"Sumayya why are you always looking for trouble for goodness sake,kafin tace mata go ahead, I'll apologise to him and follow you"....
Don duk ah tunanin kawar wani Sumayya ta tsokano don halinta kenan akullum neman tsokanan jamaa don taga ana shigar mata, kallon Sulaiman kawar tayi"I apologise to you on her behalf please".....
Dariya Sulaiman yayi sannan yawuce kawar yakamo hannun Sumayyan yajuyo da'ita"so my little Sister is so stubborn like this?".....
Turo baki tayi,don ita tarasa meyesa take biyemishi da bata cimishi mutunci har yanzuba.........
Shiru tayi tana Kare ma fuskarshi kallo, ahankali tace"nasanka ne?",tayi mishi tambayar cikin hausarta dabawai tazauna sosai bane....
Riko hannunta yayi sekuma taji takasa kwatan hannun,"kindai san Mai kama dani?"......
Tunani tashiga yi dawama yake kama,cikin sauri tace afili"My Dad".....
Kafin ta kalli Sulaiman din,are you by any chance from Nigeria,inanufin Kai 'Dan uwana ne?,gyada mata Kai yayi ai wani irin dalewa jikinshi tayi cikeda murna"are you really saying the truth?".....
Shafa bayanta yashigayi ahankali"I'm telling the truth Sumayya, I'm your cousin Brother Sulaiman,nidan Uncle dinki Abdulrahman ne I know you must have heard about him from your Dad".....
Kara kankameshi tayi cikeda jin dadi akullum burinta taga yan uwanta, yan uwan babannta and finally yau gata ga daya daga cikinsu.....
Sulaiman dinne yadan dago da fuskarta,take me home Sumayya I want to meet Uncle, jijjiga mishi Kai tayi tana goge yar kwallarta murna kawarta tayi mata sannan sukayi sallama....
Ah motarta suka tafi inda yace mata zebi ta hotel sister dinshi nacan......
You mean my cousin Sister?, gyada mata kai kawai yayi haka tadinga damunshi da tambayoyi duk akan yan gidansu harsuka Isa hotel din cewa yayi tajira shi amota yana zuwa,haka yashiga yasamu Afiya nakwance tana kallo da alama tamayi wanka abunta don cikin shirinta take.....
Gaishe shi tayi kamin yace mata tatashi zasuje wani gu,cikeda zumudi tatashi ta zari gyalen abayan daya sayamata ah kaduna tayafa daman ta gaji da zaman daki........
Sanda suka isa jikin motar Sumayya, dasauri Sumayyan tafito daga motar tana murmushi,kallonta Afiya tashiga yi kafin tamaida kanta wurin Sulaiman din with questioning look..
Sumayya ne tadan bugi hannun Sulaiman din sannan tace "bazakayi introducing dinaba?",kafin tasake maida kanta gun Afiya tareda mika mata hannu"I'm Sumayya budurwar Yayanki",takarashe maganar tana kanne masa ido...
Sakan baki Sulaiman yayi,yar dariya tayi tana kallon Sulaiman din"Toya zanyi I know this must be what she's thinking,Kuma kaki kamata bayani".....
Slight hug takaima Afiyan, I'm glad to meet you little Sis, I'm Sumayya your cousin sister.....
Sulaiman ne yakarada little Angel kafin mutaho banacemiki we're going to meet a family ba?..
Gyada masa kai tayi kafin yakarada "to family din Uncle Almustapha ne Yayan Abba, I mean Mai Martaba and she's his Daughter"...
Hugging nata Afiya takuma yi sannan tace sunana Afiya I'm happy to meet you as well.....dukda kuwa bawai tasansu sosai bane tunda labarinsu kawai takeji sede taji dadin haduwa da Afiya din,haka suka dunguma suka tafi gidan su Sumayya din tunda suka shigo Unguwar zaka gane cewa unguwa ce tamasu kudi Sulaiman baitashi mamaki ba seda Sumayya tayi parking ah makeken mansion din...
Fita tayi sannan tace suma sufito,dagudu tayi cikin gidan kamar wata yar yarinya tana Kiran Mum,Dad where are you......
Kallo Sulaiman din yabita dashi yana"she's unbelievable"......
Dariya Afiyan ma tayi,atarekuma suka bi bayan Sumayya sanda suka iso bakin makeken kofan already abude yake,katafaren parlour ne wanda ke dauke da furnitures masu kyau tundaga bakin kofar Sulaiman yake hango wani babban mutum zaune kan seater yayinda Sumayya din nazaune gefen shi da alaman tana fadamishi zuwansu ne sekuma can gefe wata mata Itama dabazata fi shekaru arba'in da biyarba yar kyakyawa da'ita tana shan fruits hankali kwance......

Tunda Sumayya takiran sunan tilon kanin nashi yaji wani irin feelings na taba zuciyarshi bama kaman sanda tace danshi yazo, ahankali yadaga kanshi yana kallon bakin kofar datake mishi pointing.....
Tashi yayi cikin sauri yayi gurinsu Sulaiman din idanunshi sun ciko da kwallah,ko shakka babu wa'yannan jinin Abdulrahman ne barinma Sulaiman dayake matukar kama dashi.....
Janyo Sulaiman da Afiyan yayi ah tare sannan yahada ah jikinshi yarungume"ashedai darabon zai sake ganin wani nasa,ashedai da rabon zai sake gamo da dan uwansa after so many years".....
Dagowa yayi yana kallonsu sannan yace"Ina mahaifinku,babu shakka ku jinin Dan Uwana ne".....
Murmushi Sulaiman yayi sannan yace mukadai mukazo Uncle, Sumayya dake gefenshine tadan harari Sulaiman din"Dad akecewa ba uncle ba"....
Dariya dukansu sukayi yayinda Uncle Almustapha din yakama hannun both Afiya da Sulaiman yakarasa dasu cikin parlour Mum din Sumayya dinne ta taresu da murmushi ah fuskarta...........
Yayinda Dad din yace"yau Allah yayi Hadiza Kinga 'ya'ya na sunbiyoni har inda nike"..
Gaisar da Mum din sukayi se alokacin Sulaiman yaga ashe Sumayya kamar uwarta tadauko,Mum dinne tace sutashi su shiga suyi wanka se suci abinci....
Haka aka sa masu aiki suka tafi da Sulaiman din yayinda Sumayya takama hannun Afiya sukayi sama, murmushi uncle Almustapha yabisu dashi yanaji wani irin dadi aranshi.......
Seda suka ci abinci suka huta sannan Dad din yanemesu,tambayarsu yasakeyi ya hanya dakuma tambayar mutanen gida....
Nan Sulaiman yace duk lafiyansu kalau,kafin Dad din yace Abdulrahman yasamu address dina kenan?.....
Murmushi kawai Sulaiman yayi sannan yace tun tafiyarka yake nemanka Dad,for all this year babu ranar da Abba baya tunaka hakanan babu irin effort din dabaiyi wajen neman ka ba sede makiya sukan shiga tsakani su hana yin hakan,cikeda mamaki Dad din yace banganeba ....

Dan numfasawa Sulaiman yayi sannan yashiga bama Dad labarin abubuwan dasukai ta faruwa bayan tafiyar shi ah masarautar,daga wanda labari aka bashi harzuwa wanda yayi witnessing da idanunshi harzuwa yanzu daga karshe yace"Dad Masarautar mu yanzu ta lalace ba kaman yanda kasanta ah da ba, it's surrounded by people who are so selfish,many things are going on over there that nikaina nakasa fahimtar komai besides i don't want to be the crown prince,inason insama ma yan uwana yanci, Almustapha deserves to be the next king that's if bakada 'da namiji Uncle,duban Afiya Sulaiman yayi sannan yace yan uwana suna going through injustice amma banida halin taimakonsu,Uncle yan uwana acikin Masarautar nan ko bawa yafisu daraja nikuma nakasayin komai akai shiyasa nataso all the way from Nigeria nazo insameka sannan abu nakarshe inason Abba yahadu da Dan uwanshi daya dade yana burin haduwa dashi,I want to be the reason for his happiness don ina iya cemaka tun rabuwar Daddy da Kai dakuma Ummi yadaina walwala ah rayuwarsa daman ita tadawo masa da hope din sake ganinka bayan kunrabu..........
Daga karshe Sulaiman yayi folding hannunshi"don Allah Dad kataimaka mukoma gida,meet everyone and then we can work as a team sabida mugyara ahalinmu dama komai"...
Dad,Mum, Sumayya da Afiya duk sukayi shiru suna sauraren Sulaiman yana bayani har yakai karshe,Afiya da Sumayya kuwa kankame juna sukayi suna kuka,Dad kuwa da Sulaiman yakai karshe seyadan sa hannu tacikin eye glasses dinsa yagoge kwallarsa sannan yace "Son nikaina nayi mamakin rashin samuna da Abdulrahman baiyi ba sabida irin naci irin nashi inyasa abu agaba to seya cinma shi dukda kuwa inajin labarin komai dayake wakana ah gida daga kan mutuwar mahaifinmu,auren mahaifinka to Magajiya dama sake aure dayayi sede bansan meyake faruwa acikin gidan ba all I thought was that my brother is now happy and Kuma mutanensa ma suna farin ciki dashi don yana musu aiki mekyau da kwatanta adalci shiyasa nadaina bincike gamedasu da jimawa,wallahi bansan abu kamar haka yafaru ba da tun da jimawa nakoma gida don ceton dan uwana, amma tunda yanzu kafada min I'll do whatever it takes to put things into places.....
Murmushi Sulaiman yayi tareda tashi ya rungume Uncle Almustapha din,thank you Uncle...
Shafa kanshi Uncle din yayi sannan yace kadaina min godiya, Sumayya dake gefe tana goge kwalla tace"didn't I tell you to stop calling him uncle"....
Dariya Dad din yayi sannan yace "Sweetheart miyena bata rai Kuma,talk to him politely"....
Yar Turo baki tayi"Dad I'm jeolous of him Kanata embracing dinshi after all I'm the only one da ake pampering agidan nan amma yanzu naga kaman kafi sonshi".....
Dariya duka sukayi yayinda Mum tace to Babana kashirya shan mita gurin Sumayya....
Kanne mata ido daya Sulaiman yayi sannan yadubi Mum din"inadaidai da ita ai Mum karki damu".....
Bubbuga kafa tashigayi akasa yayinda Afiya tace"don't mind them Sis I'm with you tashi mutafi ciki"....
Nan suka fice dariya Dad din yayi sannan yacema Sulaiman"she's my only Daughter,itakadai Allah yabani kaga dole in shagwabata"....
Murmushi Sulaiman yayi"she's so lovely Dad".......
Dariya kawai uncle Almustaphan yayi sannan yace I'll plan on when we're leaving for Nigeria.....
Okay,cewar Sulaiman din yayinda yashiga yima Dad din massage akafa sunadan hira abunsu....

*****
Koda dare yayi Mallam Hudu bemanta da alkawarin dayama su Almustapha ba hargida yazo yaduba jikin Ummi din sannan yatara Almustapha da Amiran yace suzauna akwai maganar dazaiyi agaban Ummi din...
Shiru sukayi duka kafin yafara magana"naso ace Afiya nanan sede Allah baiyi ba najima ina rikeda nauyin nan akaina Allah bai bani ikon saukeshiba sabida mahaifiyarku batason kusani sede nagaji da ajiyeshi araina kuma ayanzu danaga rashin lafiyarta yaki ci yaki cinyewa naji inason fadamuku gashi nima tsufa yazo baasan sanda rai zaiyi halinsaba...
Amira ne tace kadaina irin maganar nan Mallam Hudu don Allah,dubanta yayi ahankali sannan yace Amira indaina zancen mutuwa kikeson cewa?.....
Gyada mishi Kai tayi ahankali, murmushi yayi sannan yace kona fada koban fada ba mutuwa tazama dole don tana kan kowa don haka kikwantar da hankalinki sannan muzamanto muna cikin shirin tarbarta akowani lokaci don bata sallama bare ankarar da mutum,inlokacin mutum yayi daukan ran kawai takeyi batareda tayi la akari da shekaru,hali,kudi kowani abu nakaba...
Almustapha da jikinshi yayi sanyi ya gyada Kai, Mallam Hudu ne yamika masa wata takarda sannan yace "hungo wannan rike kagani"....
Karba Almustaphan yayi yayinda Mallam Hudu yacigaba da magana"wannan bayanai ne aciki na duk wani kaya damuka saya dakuma wanda muka sayar ma mutane ah shagon ku,daga Almustapha har Amira dagowa sukayi suna kallon Mallam Hudu din don basu gane inda yadosa ba....
Murmushi yayi sannan yace"shagon dakaga ina kasuwanci aciki banawa bane Almustapha nakune kaida kannenka wanda mahaifiyarka ne tasani nabude mata shi da kudinta tun lokacin da tarabu da mahaifinku,alokacin duk wasu kadaranta aka sayar aka bude wannan shagon sannan cangin muka sayi fili wanda filin sanda tayi rashin lafiya ne nasayar dashi mukayi harkan asibitin ta dukda kuwa Sulaiman ma yaturomin kudi awancan lokacin batareda saninkuba sabida shiyabukaci hakan ...

Dan numfasawa yakuma yi sannan yace abunda yasa banfada muku ba sabida irin tsanar da mutane sukayi muku ne nasan muddin akasan shagon ku ne ze durkushene cikin kankanin lokaci amma ah yanzu kam nafison infidda abun araina infada muku kusani Kuma tunda yanzu kunbar masarautar inaganin kunada right din sani din kilan kunason ku bukaci kudi mai yawa sabida samun cigaban rayuwa....

Tunda yake maganar Almustapha da Amira shiru sukayi suna mamaki don basu taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login