Showing 42001 words to 45000 words out of 235422 words

Chapter 15 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3469

ganin mutum me amana irin Mallam Hudu ba Amira ne takasa hakuri tace lallai Mallam Hudu kafita daban cikin Al umma Allah yasaka makada alkhairi..
Mallam Hudu ya amsa sannan yace bazan taba iya cutan mahaifiyarkuba sabida irin halaccin datamin ah rayuwa bakowa zeyimakaba...
Nidai ga komai na shagon nan sannan akwai ATM aciki wanda nike tara muku duk ribar da aka samu aciki sannan pin din na ciki...
Murmushi Almustapha yayi sannan yamaida ma Mallam Hudu takardar yace"kacigaba da ajiyewa agurinka Mallam Hudu,Kai ubane garemu it should be with you"...
Maida mishi Mallam Hudu yakuyi yana baza ayi hakaba, Amira ne tace gaskiyarshine Mallam Hudu komun rikedin aiba iya cigaba da rike shagon zamuyiba tunda kasan yanda aka tsanemu kilan shagon ta durkushe inaganin kai kacigaba da tafiyar da al amarin inbadai takuraka zamuyiba...
Gyada Kai Mallam Hudu yayi sannan yace to amma ATM Kam ku ajiye agurinku don babu abunda zanyi dashi, murmushi sukayi sannan sukayi mishi godiya yajima yana musu bayanin komai kafin yatafi gida......
Amira ne tace inama Afiya nanan datayi mamakin wannan abun Al ajabin yau......
Almustapha dake gefenta ne yace shiyafita, Mallam Hudu kuwa tun fitar shi ah gidan sega international number takirashi cikeda mamaki yadauka ashe Sulaiman ne bayansun gaisane yake fada mishi yana tareda Afiya yayita neman number dinshi bayasamu......
Cikeda farin ciki Mallam Hudu yace zefadama su Almustapha din donkuwa hankalinsu kwata kwata ba akwanceba daman, juyawa yayi yakoma gidan ah bakin kofa suka hadu da Almustapha din nan yake labarta masa wani irin ajiyar zuciya yayi don daman yanzu ma yana niyan zuwa masarautar ne batun Afiya din...

****

Talatu ne tazo tasamu Magajiya kan bakonta yazo,kallonta Magajiya tayi sannan tace yana Ina?......
Kan Talatu ah kasa tace yana inda kukasaba haduwa,tashi Magajiya tayi sannan tace sutafi haka suka tafi bayan sun tabbatar babu wanda yasa musu ido sanda suka isa har kasa mutumin ya tsuguna yana mika gaisuwa,batareda Magajiya ta ansaba tace kayi aikin danasaka kane?.....
Eh Uwargijiyata yayi maganan cikin sauri,nayi bincike akan gidan su yarinyar yar gidan Alhaji Muhammad ne yanada mata biyu sannan dan kasuwa ne sosai kafin yakarada itada yar uwarta suke karatu acikin makarantar ABU sede kaman yar uwar tasamu matsala da ita Asma'u din sabida Asma'u taje gida tafadi abubuwan datakeyi.....
Yatsina fuska Magajiya tayi sannan tace me Yar uwar takeyi?.....
Nan mutumin yakwashe labarin komai yabata nan yace yanzu haka anamaganar ma kaman aurar da Yar uwar za ayi Kuma tanajin haushin Asma'u don gani take ita taja mata.....
Yar dariya Magajiya tayi sannan tace"anzo gurin,fadamin yarinyar tadaina ganin Almustapha dinne itada take pretending to be pious?"...
Dan sosa Kai mutumin yayi yana washare baki, Uwargijiyata inafa ae duk kanwar ja ce don ranar dare dare naganta jikinshi,ciro waya yayi ah aljihunshi yakai kan hotuna sannan yanunama Magajiya din yasake shiga video yanunamata,shekewa da dariya Magajiya tayi sannan tace "kayi aiki mekyau yau dole inyimaka kyauta me tsoka sede bakayimin abu dayaba".....
Cikin sauri yace Uwargijiyata nasan menene zaki bukata Kuma nariga danayi miki shi kallonshi Magajiya tayi sannan yamika mata wata number,number din Asiya yar uwartata....
Murmushi Magajiya tayi sannan tace "ashedai kwakwalwarka naja".....
Washare baki yashigayi yana"awurinki na koya Uwargijiyata".....
Ganin number din tayi sannan tasake mika mishi"sauran aikin kai zaka karasa,nan tashiga yimishi bayanin yanda zaiyi"..
Daga karshe tace inafatan kagane?....

Gyada mata kai yayi cikeda gamsuwa kafin tasa Talatu ta sallameshi nan suka juya cikin masarautar,suna cikin tafiya Magajiya tace"Talatu nayi tunanin mutum irin Almustapha mace bazata taba tafiya da imaninshiba,ashedai shima yanada feelings!ikon Allah kitsaya kiga yanda zanyi raga raga da rayuwarsu wannan kadai zaisa insamu kwanciyar hankali......
Talatu ne tace Uwargijiyata dukda sunbar masarautar bazakibarsuba,tsaki Magajiya tayi sannan tace inason inbatashi ah idon Mai Martaba ne tukunnan yanda koda ansamu akasi bazai taba koda iya kallonshiba....
Murmushi Talatu tayi sannan tace mezakiyi to,mekuma yasako yarinyarnan cikin al amarinki......
Dariya kawai Magajiya tayi tayi gaba tabar Talatu da jimami.....
***
Auren Asma'u da Asiya duka ansaka shi lokaci daya dana Yayansu Mubaraq,don haka bangaren Ummi da Mommy tuni suka fara shirye shirye abunsu,Asiya kuwa tana nan kullum ah kunshe ah daki tana kuka wai ita yanzu batason Aslam, Mommy kuwa cewa tayi ko mutuwa zakiyi se ankaiki gidan Aslam inma zaki dawo cikin hankalinki gwanda kidawo babu abunda za acanza ...

Hajja ne kadai ke lallashin Asiya,tanabata hakuri don kuwa itamafa bata goyi bayan Asiyan nakin Aslam din da takeyiba.....

Bangaren Asma'u kuwa tamaida hankalinta kan karatunta don sunfara exams ma sannan tayi kokari gurin hana kanta zuwa gun da Almustapha kezama dukda kuwa wata zuciyar na ingizata akoda yaushe....
Yanzu ma Asiya takunshe kanta acikin daki tana chat cikin wayarta da friends dinta,nan taga sabuwar number taturo mata hoto,seda tagama replying massages nata sannan tabude massage din hoto ne kawai tagani yayinda tashiga downloading dinshi tana gama downloading sega kuma video yashigo nan shima yafara downloading viewing hoton tayi, zare idanu tayi ganin Asma'u kwance jikin Almustapha because she couldn't believe her eyes,sekuma ahankali tasaki murmushi......






Vote
Comment
Share!

*Zeeneert*
[3/23, 5:24 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*page 13*.....

Kafin tace"indai Asma'u na abunda idanunta suka gane mata to tabbas itan silent killer ce, ahankali tafita daga hoton sannan tashiga video din shima thesame thing ne da hoton sede wannan din video aka musu, murmushi takuma saki sannan tadaura yatsanta daya kan lips dinta tana tunanin taya zata nuna ma 'yan gidan su abunnan"will they believe her?",shine tambayar datayima kanta sabida tasan halinsu suna iya ganin abunnan suce editing akayi because they trust Asma'u so much,dan tsaki tayi kuma"she's a bitch! atleast ni ah fili nakeyi banji tsoro ba amma itakuma ah boye,she's busy pretending to be pious all this time Allah dai ya sauwaka to amma abu daya ne nasani tunda har tatonamin asiri to nima I'll make her life miserable............
Tana wannan tunanin ne seta rasa tawani hanya zatasamu tarama abunda Asma'u tayi mata sabida ita ba burinta tayi exposing dinta sabida tagyara halintaba aa sedan daukan revenge,yar dariya tayi sanda taji wani idea yafado mata lokaci daya, ahankali tafurta"Mukhtar",yes "Mukhtar" I'll send him the video and nasan for sure ze nuna ah gida wata zuciyar kuma tace mata "Amma dai bazaki tura masa ta number dinkiba ko,what will he think of you inkika tura abunda kanwarki takeyi"....
Dawannan tunanin tayi deciding sayan sabuwar Sim don aiwatar da abunda tayi niya sede inazata samu Sim din tunda ba bari ake tafita ah gidan ba kuma ko tace yayunta su suyo mata bazasu suyoba,idea ne yafado mata kan tabama mai gadi yasiyo mata dawannan tunanin tazari hijab da kudi ah hannunta tafita.....

****
Mukhtar! Mukhtar ! Mukhtar abokin nashi yakira sunanshi yafi sau uku amma bemasan yanayiba sabida irin duniyar tunanin daya shiga seda Sagir yakai hannu yatabashi sannan yayi saurin juyowa gareshi......
What,mekace Sagir?....
Jijjiga kai Sagir din yayi sannan yace"ikon Allah, Mukhtar wani irin tunani kakeyi haka kwanan nan se ayita yimaka magana bakaji".....
Hmmmm shine kawai abunda Mukhtar din yafada kafin yatashi yana shirin tafiya,riko hannunshi Sagir yayi kafin yadawo dashi yazauna"inamaka magana zaka tafi,don Allah kafadamin matsalar ka meyake damunka kwana biyun nan?"....
Kallon abokin nashi Mukhtar yayi sannan yace"Asma'u ce Sagir,itakebani tough time dinnan bansan mena mata ba tunda akasaka bikinmu take behaving strangely, she no longer give me her time and attention".....
Gyada Kai Sagir din yayi kafin yace"ka tambayeta ne, you should have asked her mekayimata"....
Wallahi na tambayeta yafi ah kirga Sagir kullum setace min babu abunda nayimata,nikuma senake ganin kaman bataso aka sa auren kwana kusa bane tunda bawai munjima da haduwa bane.....
kamo hannun Mukhtar Sagir yayi kafin yace"I don't think wannan zaisa tacanza maka indai har tana sonka may be kawai stress din exams ne kabata time zuwa lokacinda za agama may be she'll come back to her normal self",don Sagir duk ah tunaninshi hakane tunda yasan Mukhtar dason sama ranshi damuwa akan abunda baikai yakawoba dakyar yayi convincing dinshi ya yarda da hakan ne kafin yace mishi"kadaina sama ranka irin abubuwan nan please it might affect your studies"..
Murmushi Mukhtar yayi sannan yace"thank you Sagir,zankiyaye in Sha Allah"....
Dahaka suka tashi suka fita....

****
Tunda tafita da mayafinta abakin gate tasamu Baba mai gadi nan tagaida shi tareda rokonshi tanason yasiyo mata sabon sim card ne babu gardama yakarbi kudi tareda tambayar ta wani layi sabida shima adan waye yake"MTN" tabashi amsa harzai tafi tace yauwa Baba Adamu layin yazamanto anyi registernta....
To 'yata nan tajuya takoma gida bayan tacemishi inya dawo ya ajiye agurinshi kawai anjima zatazo takarba dakanta basai yashigo ciki ba.......
Bayan kaman awa daya taje takarbi sim din komawa daki tayi tareda sa key akofar dakin, murmushi tayi sannan ta 'dale kan gado abunta,saka Sim din tayi ah wayarta kafin tasayi recharge card from her account through mobile banking,unisntalling WhatsApp dinta tayi kafin tasake installing wani tashiga yin register da sabuwar number din......
Batasamu wahalar ganin numbern Mukhtar ah whatsapp dinba don already number nakan phone dinta,nanfa tatura mishi hoto da video din tareda yin yar massage akasa.....

" _Assalamu alaikum Mukhtar inafatan kana lafiya,yakuma karatu da alamura, Allah yabamu sa'a baki daya.nasan kana da tambayoyi aranka nakan cewa ni wanene sede abinda nakeson kasani shine ni masoyinka ne mesonka da alkhairi shiyasa naturo maka wannan sakon sabida nasamu labari kan kana neman auren yarinyar nan Asma'u yar gidan Alhaji Muhammad,inason kasani cewa ba yarinya ce data dace da nagartaccen namiji irinka ba bata kuma dace dazama uwar yayankaba tunda dai ga abunda takeyi ah zahiri,basai kanemeni ba nina maka taimakone inkuma baka yarda daniba kana iyayin bincike dakanka_"

Takaranta massage din yafi sau uku kafin ta tura mishi dukda kuwa baya online amma yatafi, murmushi tayi sannan tacire simcard din tamaida nata because batason asamu matsala yace zeyi tracing haka WhatsApp dinma tamaida ainahin number dinta because the important thing is for him to get the massage tunda yatafi to ai shikenan sauran game din Kuma zatagani ah zahiri in Mukhtar yazo gida....
****
Tafiya takeyi cikin sauri daka ganta kasan ah tsorace take,tana tafiya tana dan juye juye sabida batasan kowa yaganta seda ta tabbatar babu mai ganinta sannan tashige gidan. makeken gidane acikin Masarautar wanda ina iyacewa yana daya daga cikin tsararrun gidaje dake cikin masarautar........
Bayan tashiga ne tayi sallama awata kofa,matar dake cikin dakin ne dabana ganin fuskarta sabida yarinyar ta tareta tamata nuni data shigo da hannu......
Karasawa yarinyar tayi yayinda ta tsuguna har kasa tana mika gaisuwa"in wuni ranki shi dade?"....
Lafiya Lau Matar ta amsa ah yatsine kafin tace babu dai wanda yaganki ko?.....
Babu tabama Matar amsa, murmushi tayi sannan tace "Kinga tun ranar ban nemekiba ko seyau"....
Eh wallahi ranki shidade senayi tunanin kintsorata da abunda yafaru ne kika fasa cinma burinki,wani irin dariya Matar tayi kafin tace"haba Laure sede wata badai niba,babu abunda zaihana ni kawar da Magajiya ah doran kasan nan najima ina shirin yin haka Kuma yanzu ne lokacin da zan aiwatar da niyana(Niko dake bakin kofa inadaukan rahoto nadafe kirjina tareda fadin innalillahi wainna ilaihir rajiun, Laure,so Laure is behind all this,kafin ahankali nayi karfin halin lekawa Inga ko wacece Matar sede bani iya ganinta se shadow dinsu sabida dakin akwai duhu don haka nahakura nacigaba dajin zantukan dasukeyi)....
Laurene tace hakane Ranki shi dade nima inabayanki Kuma zangoya miki baya akoda yaushe tahanyar jiyo mana dukwani sirri nasu kuma zanyi iya kokarina gurin ganin ba akama muba har mu kai ga cinma burinmu........
Dan shafa kanta Matar tayi kafin tace yauwa Laure nagode sosai kema tahakan ne zaki cinma naki burin nazama ta hannun damar Matar sarki....
Washare baki Laure tayi sannan tace,nagode Ranki shi dade nagaji da bautawa Magajiya da 'ya'yanta kullum sede zagi da tsangwama sannan bata daukeni abakin komai ba kamar yanda tadauki Talatu,nima inason wannan matsayin.....
Indai wannan ne kinsamu Laure,yanzu yanda zamu hada next move dinne matsala banason asake samun matsala kamar nada kinga nafarkon Allah yataimakemu akayi tunanin wancan yarinyar Afiyace,nabiyun kuma da ankamani ah dalilin Talatun nan amma Allah yataimakeni nasan wata kofa shiyasa nabi tanan nafita.......
Gyada kai Laure tayi kafin tace hakane Ranki shidade in Sha Allah zamu kiyayena gaba.....
Cikin sauri Matar tashiga yimata bayanin abunda zatayi,gyada Kai tayi cikeda gamsuwa kafin Matar ta sallameta tatafi.......

****

*INDONESIA*

Zaune suke dukansu kan dinning table sunacin abinci banda Afiyya datake bin abinci daya bayan daya da kallo don ita gani take bazata iya cibama tarasa dalilin dayasa kullum different girki sukeyi gashi ita ah Nigerian ma bakomai tasamu takeciba bare ace wasu Indonesian foods nan,kallon Sulaiman tayi yawani dage seci yakeyi hankalinshi kwance yamutsa fuska tayi tana tunanin ina ya iya cin irin wannan abincin...
Sumayya ne data lurada abunda Afiyan keyi tashiga kwalama me musu abinci kira, " *Kiara* come here"...
Cikin saurin wanda aka Kira da Kiara tazo tana....."Yes Ma'am"....
Hararanta Sumayya tayi sannan tace"didn't i ask you to go and learn about Nigerian recipes on net?"...
Cikeda tsoron kada ah koreta Kiara tace"you told me Ma'am".....
Tsaki Sumayya tayi kafin tace then what's all this?.....
I'm sorry Ma'am Kiara tashiga bada hakuri, get lost Sumayya tabata amsa kafin tadubi Dad sannan tace....
"Dad duk masu aikin nan nalura basu san aikinsuba akoresu kawai kaga Afiya cannot eat any of this".....
Murmushi Sulaiman yayi yana kallon Sumayya din kafin yace "I was the one that asked her not to cook any Nigerian food Sis,sabida inason Afiya takoyi ci,inbata koya yanzuba when is she going to learn what if wataran tazauna da irin su kowani abu yataso that she need to eat their food,besides tunda tazo batayi tasting abincinsu kodayaba inalura daku ke kenema mata abunda zataci daga baya"......
Harara Sumayya takai mishi kafin tace, to ai batason cine dazataci,dariya kawai yayi kafin yatashi daga inda yake yakoma kujerar dake kusa dana Afiya din kafin yadauko bowl din *Nasi Goreng* dana *Ayam rica-rica* sannan yadauki plate yadubeta "Little Angel wanne zakici?"....
Yamutsa fuska tayi, murmushi yayi sannan yace"trust me Sis you will like them,da dadi fa sosai".....
Allah Yaya Sulaiman, Afiya bta tambayeshi tana fuskar tausayi..
Gyada mata Kai yayi alamar eh kafin yace barina zubamiki wannan kamar shinkafa shinkafan yana da dadi sosai,gyadamai kai tayi kawai yayinda yazuba mata sannan yamika mata plate din"try one spoon sekin gode min"....
Badan ranta nasoba ta zari spoon din tadiba tana yamutsa fuska sannan takai baki take kuma se expression na fuskarta tacanza sabida dadin abinci, nan danan tashiga ci,dariya dukansu sukayi yayinda Sumayya ta tsaya tana kallon Sulaiman din aranta tafurta"he's so caring".....
Dad ne yace, Daughter kikara da *Gado Gado* sekince bazaki sake cin abincin Nigeria ba,dariya tayi tana cin fried rice dinnasu wanda suke kiranta da Nasi Goreng tace a'a Dad se dare kuma cikina yacika yanzu sosai takarashe maganar tana taba cikinta......
murmushi Mom da Dad din sukayi kafin Dad yace Sulaiman I've arranged everything ranar Thursday zamu tafi in sha Allah, Allah yakaimu cewar Sulaiman din yayinda Sumayya tace 6 days from now kenan, can't wait namatsu inganni ah Nigeria....
Harara Sulaiman yamata cikeda wasa yace amma dai tundaga nan zaki sayi atamfofi ko don akasar mu ba abari ayi yawo da irin wayannan kayan......
Sakan baki tayi cikeda damuwa tace"dagaske?".....
Eh kawai yace mata kafin yatashi yace zeje yayi freshen up sesutafi yawo.........

****
Munira ne tashigo dakin tana Yaya Asma'u wai inji Yaya Aliyu kikai mishi ruwansha,harara ta doka mata sannan tace "can't you see I'm studying,common ruwa dinma harsai kinzo kinfadamin instead of kikai mishi direct".....
Sorry shine abunda Muniran tafada tareda fita daga dakin tana yamutsa fuska,tarasa meyake damun Yayarta kwana biyun nan she's becoming rude abu kadan setafara ma mutum fada.....
Asma'u cigaba da karatunta tayi hankali kwance,wayarta dake gefenta ne tashiga kara dan tsaki tayi don duk ah tunaninta Mukhtar ne seda takai dubanta kan screen din sannan taga ashe bashi baneba kawartane Aisha,jiki ah sanyaye tadaga call din,daga daya bangaren Aisha tace"guess what Asma'u?"....
Sekin fada Aisha inajinki,cikeda damuwa jin muryar kawartata Aisha tace "Asma'u bakida lafiya ne?"....
"Kibari kawai Aisha bansan meyake damunaba nima",tayi maganar kamar zata fashe da kuka Aishan ne tace daman zance miki ina Zaria ne nazo gidan Aunty suwaiba hutu.....
Cikeda jin dadi Asma'u tace dagaske,yaushe zakizo gida?....
Yar dariya Aisha tayi sannan tace"atleast i brightened your mood, probably inshigo gobe"....
Tabe baki Asma'u tayi kamar wanda tanagaban Aisha din kafin tace "ou ouuu gobe zanshiga school za ayi mana tutorials against exams na Monday".??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????...
Kada kidamu Asma'u basai inzo Sunday ba duk dayane ai, a'a Aisha ba ayi hakaba kawai innataso ah school zanzo gidan Anty suwaiba din intayarda indauke ki muzo gida mukwana ......
To shikenan senaga zuwanki, Kuma kikwantar da hankalinki kidaina damuwa Kinga dai kina exams ne dukdama ina fushi dake baki fadamin aurenki ba sede inji abakin wasu....
Hakuri Asma'u tashiga bata tanacewa itafa babu wanda ma tafadawa so batasan ya akayi wanda sukafada matan suka saniba.....
Kekikasani dai cewar Aisha din kafin tace sekinzo goben kawai.....
Okay Asma'u tabata ansa tareda yimata sallama,ajiye wayar tayi jiki ah sanyaye"why is she not happy about the wedding tunda tanason Yaya Mukhtar,miyasa akoda yaushe tashiga duniyar tunani se Almustapha yafado mata rai,tanajin tausayin Mukhtar ba ason ranta takemishi wasu abubuwan ba she's just following her heart without a reason,lumshe idanunta tayi kafin tafurta"Ya Allah gani gareka,help through and chose the best for me"......
Because tunda akasa ranar aurenta bata wasa da neman zabi gurin ubangiji sabida tasan bata da kamarshi.......
kasa cigaba da karatun ma tayi don haka tadibi takardunta tadorasu kan bedside drawer sannan takoma takwanta tuni bacci yayi awun gaba da'ita.....

****
Yau so late Mukhtar yadawo gida sabida yini yayi ah school,daman haka yakeyi duk lokacin exams sedare yake komawa gida tunda yashigo yajefar da jakanshi ah tsakiyar parlour tareda samun daya daga cikin seaters din dake parlour din yakwanta......
Ciro wayarshi yayi daga aljihunshi rabonshi dajin muryarta tun jiya dasafe don haka yashiga kiran layinta amma yayi ta ringing batadauka ba seda yakira sau uku duk bata dauka ba, lumshe idanunshi yayi ahankali kafin yakuma budusu sekuma yayi tunanin kunna data dinshi she might be online dukda kuwa 90% na zuciyarshi naraya mishi bata online din donkuwa Asma'u ba mutum bace meyawan chat..........
Bayan ya kunna data dinne massages suka shiga shigowa sede shi baya begen ganin kowani massage inba nata ba scrolling yashiga yi kozaiga nata amma bata turomai komaiba, inbox dinta yashiga tareda turamata sallama kafin yafita yana replying massages har ya iso kan wata sabuwar number budewa yayi inda yaga picture da video already sunfara downloading ma donkuwa wayarshi na automatic download,karanta massages din yashigayi yayinda zuciyarshi tashiga bugawa kasa karasa karantawan ma yayi don yafi damuwa yaga hoton budewa yayi yagani tabbas Asma'u ce dakuma Almustapha dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login