Showing 153001 words to 156000 words out of 235422 words

Chapter 52 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3489

magana ma da alama begama warwarewa sosai ba gashi dukya rame cikin kwana biyunnan din duban Sulaiman Almustapha yayi"yaushe ya farka Sulaiman?"......
Ahankali Dad yace cikin dare yafarka amma bema jimaba yakomai bacci and likitan ma yazo yadubashi da safe yace Bpn yasauka alhamdulillah amma kada abarshi yafara fita tukunnan don jikinshi begama warewa ba.......

Cikeda gamsuwa Almustapha yace"Allah yabashi lafiya"...
Amin cewar Dad da Sulaiman din kafin Dad yakarada "kozaka kirawo Khairiya ne tunda yafarka yake kiran sunanta yana akaishi yaganta dakyar muka bashi hakuri yake breakfast ma yanzu babu yanda zamuyi mubarshi yafita batareda jikinshi yayi kwariba"
Gyadakai kawai Almustaphan yayi dukda kuwa bawai maganar takai har ranshi baneba, because to be sincere bayason yayi dragging Ummi into this, it'll only hurt her feelings shikuma bayason hakan Allah yagani sede on the other hand kuma bazai iya budan baki yacema Abban bazaiyi abunda yace dinba shiyasa ma kawai yagyada masa kansa sede da mamakinsu sukaji Abban nace wa....
"you don't to, I'll go see her myself bata cancanci tazo gurina dakanta ba"..........
Cikeda damuwa Dad yace"To Abdul haryanzu jikinka baigama warwarewa ba haryaushe zaka iya fita fisabilillahi?".....
Dan murmushin dayafi kuka ciwo yayi sannan yace"you don't have to worry I'll wait harsanda naji karfin jikina,hope she's fine too?", Mai Martaba yayi maganar yana kallon Almustapha....

Gyada masa kai Almustapha din yayi,sunjima agurin Mai Martaba din kafin suka fice su ukun inda sukabarshi da Dad don baki sunfara yawa masu zuwa duba jikinshi.........

"Tunda suka fito daga bangaren Sulaiman yace nikam kwana biyu bamu gaisada Mom ba inaganin xanyi bangarenta tukunnan",yakarashe maganar tareda canza direction din da sukabi cikin sauri Asma'u tace"zanje nima Yaya Sulaiman", dariya yayi sannan yace "to Yaya Asma'u",haka tayi saurin iso Sulaiman din suka fara tafiya tare sakan baki Almustapha yayi tareda binsu da kallo cikeda mamaki wato ma shi ko oho zasuwani tafi subarshi ganin basumasan yanayiba yasashi tabe baki tareda yin hanyar bangarensu don sauya kaya yafice zuwa gun Mallam Hudu gama yakwana biyu bai lekasu ba.........

Tundaga nesa Sulaiman yahango wata akwati ahannun dogari kaman na Sumayya amma sebaice komai ba harsuka karasa kofar bangaren sede da mamakinshi Dogarin ma nan yashiga cikin sauri yakirashi da ladabi ya juyo yana mika gaisuwa batareda ya amsa ba yace"kayan wayene wannan"....
Da ladabi Dogarin kecemishi na Sumayya ne bakaramin mamaki yayiba don haka seyace kana nufin itace tadawo?.....
Gyada mishi kai Dogarin yayi sannan yace.....
"Bejimaba taxxi yasauketa akofar masarautar nan tun dazuma tashige gida shine natahomata dakayanta"......
Cikin sauri Sulaiman yakarasa cikin parlourn sede babu kowa batareda yayi wani tunani ba yayi hanyar dakinta sede arufe gam cikin raunanniyar murya yashiga Kiran sunanta"Sumayya,kibude kofar please"......
Haka yadinga kiran sunan ta amma shiru kakeji itakuwa tanazaune bakin gadonta hawaye nata ambaliya hakanan tanajinshi amma taki tashi tabudemai,tomema zaice mata yanzu bayan ko kira yabata hakuri ma baiyi attempting yiba jin kukanta na neman tona mata asiri yasata saurin tashi tashige bandaki wanda rufo kofar bandakin da tayi ne yasashi gane tana cikin daki........
Cikeda damuwa yace"menayi mata,why is she not opening the door?", yakarashe maganar yana kallon Asma'u da damuwa......
Itama cikeda damuwan tace"kunyi fadane,ko wani abun yahadaku?"...
Haram Asma'u babu abunda yahadamu wlhy I know I've been refusing to answer her calls due to the situation I was in but I never expect her to react this way,bantaba tunanin zatayi tunanin biyowa motar haya tazo gidaba and that's the most annoying part,she must have suffered alot on her way home,I know Sumayya she's very fragile"yayi maganar ah rikide hakanan baidaina buga kofar dakin ba daga karshe ciro wayanshi yayi yashiga kiran layinta babu kakkautawa hakanan daga shi har Asma'un suna jin wayar na ringing ah dakin ammataki dauka........
Dafe kanshi yayi tareda cewa"ya ilahi,jinake kamar in balla kofarnan",wai what's wrong with you Sumayya,talk to me,kizo kisauke haushin ki akaina if you're that angry,come and hit me may be you'll be at ease after doing that", yakarashe maganar cikin tsawa tareda buga kafarshi dakarfi ajikin kofar, he's just so tired of banging the door so yake yaganta ido da Ido ya lallasheta,so yake yaji miye damuwarta why is she so angry with him don yasan wannan fushin dashi ake dondaba dashi take fushin ba yanada tabbacin she'll look for him first,yana cikin wannan tunanin sukaji tana kokarin bude kofar gabadaya suka maida hankalinsu kan kofar tunkan ta wangaleta yayi saurin bude kofar,kallonta yatsaya yi gabaki daya idanunta sun canza launi hakanan idanunta sun kumbura tsabar kuka cike da takaici takaraso gabanshi tashiga dukan kirjinshi tana"you want me to hit you right?"...
Then I'm hitting you,you want me to beat the hell out of you right?....
"Then I'll do that", takarashe maganar tareda fara bugun duk inda tasamu ajikinshi hakanan tana kuka maitsuma zuciya Asmau dake shirin hanata Sulaiman yayi saurin daga mata hannu alamar ta bari seda Sumayya tayi mai isanta kafin tasake kai mai wawan bugu ah kirji tana...
"why am I not feeling at ease,miyasa zuciyata takasa daina kuna haryanzu?"....
Sulaiman baisan sanda yajata zuwa jikinshi ba tareda rungume ta so very tightly,like his life depends on her hakanan idanunshi suka canza launi lokaci guda"I'm sorry Baby, I'm so very sorry Summyna", yakarashe maganar yana kara sakata cikin jikinshi itakuwa kukan tacigaba dayi babu kakkautawa gashidai shidin ne yabata mata rai and she ended up crying on his body hakanan kuma shine me rarrashin.......
"Asma'u saurin juya kanta tayi ganin yanayin da suke ciki tareda yin gyaran murya amma basumasan tanayiba and she trust them completely wannan dalilin yasata shigewa dakin Mom sede da mamakinta batanan,itamadai tayi mamakin ace Mom nanan anata wannan babatun bata fitoba ai abun da kamar wuya".........

Dakyar yasamu ta tsagaita kukan nata kafin yakama hannunta ahankali suka shige dakin nata zaunar da ita yayi bakin gado kafin yatsuguna gabanta tareda hade hannunsu guri guda cikin sigar lallashi yace.....
"kiyi hakuri Sumayya nasan na bata miki rai but believe me that was never my intention,I thought recieving your calls ze iya tada miki hankali inkika jini cikin damuwa shiyasa naki daga calls dinki infact daga karshema kashe wayar nayi sejiya da Yaya Almustapha yakunnata da dare sabida yasha nemana baya samuna, I'm extremely sorry,had it been nasan hakan zaisa hankalinki yatashi dabanyiba yakarashe maganar muryarshi ah raunane"..........
Sumayya daharyanzu hawaye na zuba ah idanunta tace"I think this day will be the end of our relationship Yaya Sulaiman,kadaina ganina amatsayin wanda kakeso please just consider me as your sister,kafara ganina amatsayin su Amira kamar yanda kakeyi ada I think this will be the best for both of us",takarashe maganar tana goge kwallarta bakaramin jijjigashi maganar Sumayya tayima Sulaiman ba hakanan lokaci guda idanunshi suka kada sukayi jazir,he really can't believe it,badai Sumayya is trying to leave him because of his Mother ba,badai laifin mahaifiyar sa nason shafan relationship dinsu da Sumayya bane ba tokodai intayi mashi haka batayimashi adalciba hakanan intayi mashi haka tacuce takuma cuci zuciyarshi donkuwa bayatunanin zai iyayima wata irin soyayyar dayakeyimata muryarshi na cracking hakanan idanunshi sunyi jazir yace"are you by any chance leaving me because of my Mother's deeds?",wannan karan he couldn't hold back his tears don zuba sukafarayi ahankali Sumayya da is very shock jin abundama yake tunani tace"haka nace maka?"....
"Why are you trying to blame me,why are you making it as it's my fault,miyasa kake zargina",tayi maganar cikin tsawa akan abunda bashike raina ba?".....
Shima cikin tsawan yace"yakikeso inyi to Sumayya,why will you change all of a sudden hakanan nasan sabida naki daga wayarki be isheki hujjan dazaki furta irin wayannan kalaman ba,if you're not leaving me because of my mother then kifada min,akan me zakice muyi ending up this relationship!?"....
"Why don't you go and ask your wife".........
Cikida mamaki yace"kina nufin Zaliha?"...

Wannan karan wani irin harara ta watsa mishi kafin tace"kanada wata matar bayan itane",in a very confused look yace"me Zaliha tayi maki Sumayya?",yayi tambayar cikeda damuwa,sakin wani kukan tayi sannan tace"kaje katambayeta mana zata fadama,har ita takeda bakin fadamin magana donna kira cikin dare da ace tasan the situation I was in she wouldn't have done that besides tama fini gaskiya miyasa zankira married Man so late in the night bayan yana iya kasancewa tareda iyalinshi,miyasa zan takura muku tayi maganar tana kallonshi da idanunta dake cike da tsantsar kishinsa kafin tace"you love your wife don't you?".........
Damamaki yake kallonta, he's just speechless and out of words yama rasa maizai cemata hakanan zuciyar shi nayi mashi wani irin kuna da ace Zaliha na gabanshi yanzu da babu abunda zai hanashi kai mata duka Sumayya Jin yayi shiru yasata cewa"she can have you all I've no problem with that takarashe maganar tareda juyamai baya"........
Cikin sauri yatashi yadawo setin inda fuskarta yake kafin yace"kina kokwanton irin sonda nike miki ne Sumayya?".........
Cikin kuka tace"to yazanyi Yaya Sulaiman?".....

Jinjina kai yayimata ahankali sannan yatashi tsaye yana"I'll prove you wrong Sumayya",yayi maganar tareda fita yabar dakin hakanan belurama da Asma'u dake tsaye bakin kofar dakin ba tsabar ranshi na matukar bace barinma masarautar yayi baki daya don yasan muddin yanufi Zaliha yanzu bakaramin maka zatasha agurinshi ba shikuma bayason yazamo daya daga cikin mazajen dasuke dukan matayensu,he don't want to be a coword like them....

Asma'u karasawa tayi cikin dakin sannan tadafa kafatun Sumayya ahankali tana"Sis kidaina kuka?"........
Dago kumburarrun idanunta Sumayya tayi sannan tace"inbanyi kuka ba maizanyi Sis Asma'u,i love him so much and I can't live without him sede it seems like shi son da yakeyimin din bana kwarai bane tunda har ya cuceni"......

Cikeda mamakin kalaman Sumayya Asma'u tace"yacuce ki kuma Sumayya,meye yayi maki?"......
Cikin kuka tace"bakiji conversation dinmu bane nayi tunanin kina bakin kofa ai tunda har kikashigo yanzudin".......

Sa hannu Asma'u tayi tana goge ma Sumayya hawayenta kafin tace"as far as i know Sulaiman ba cutan ki yayi ba indai har akan abunda naji kuna magana ne",cikeda Jin haushin Asmau ganin tana kokarin goya ma Sulaiman baya tace"isowar dare nayi fa and it's all because baya daukan calls dina,I thought something bad yafaru dashi ne shiyasa hankalina yatashi but all I could get was her harsh words after calling his number don ya turomin number Yaya Idriss, haka nakwana ah airport jiya and on top of that nabiyo motar kasuwan daban taba hawaba",cikeda tausayinta Asma'u tace"sorry on his behalf dukdama aganina aishi babu laifinshi Sumayya"....
Yasan kintaho ne?....
Girgiza mata kai tayi alamar aa,kafin Asma'u takarada"shiyadaga wayar dakika Kira?"....
Nanma aa Sumayya tace kafin Asma'u tace"fine,he didn't know Zaliha picked your call Sumayya kuma indai kikace zaki biyema wannan matar you'll end up regretting batada wani buri daya wuce ta batawa mutane rayuwarsu, Yaya Sulaiman abun tausayine hakanan shi mutum ne dayakamata kiyi mishi uziri ah irin abubuwan dayake going through,atunanina babu wanda yakamata yayi understanding pain dinshi kaman ke inkuma kina fushi don ya kwana da matarshi ne gwandama kidaina,kima gode Allah dashiba me neman mata awaje bane Sumayya sannan atunaninki kinyi mishi adalci inkikace bazai kasance da Matarsa ba bayan yanada bukatarta,I really think this's absolutely not fair Sumayya inanan agabana kwanaki kafin kikoma yayi miki maganar zeyima su Abba maganar kunason juna ayi maku aure amma kika ki,ke kinason ki karasa karatun ki kuma hakan dakikayi baisa yadaina miki sonda yake miki ba,he fully support you and he's willing to wait despite all the wahala dayakesha gurin matarsa dukda baifadaba but one mere look zakayi masu kagane hakan", Asma'u takarashe maganar tareda tashi sannan tace"I trust Yaya Sulaiman, he'll surely prove you wrong, he'll prove to you that he's best husband that you could ever ask for kede kicigaba da addu'a kawai",hakanan Asma'u tafice tabar Sumayyan nata tunane tunane itakadai.....
******
Dayanma Salma taje bangaren Zaliha tareda gaidata batareda Zalihan ta amsaba tace...
"nikam kwanaki danabaki abu kisa ah dakin Yarima kinsaka ne?".......
Cikeda ladabi Salma tace"nasaka Gimbiya".....
"To ita Asma'un bata gani bane?",Zaliha tayi maganar ranta ah bace cikin in ina Salma tace....
"inaganin bata ganiba don inasaka musu ido sosai"..........
Zungurinta Zaliha tayi kafin tace badai kinsa ah inda shizai gani harya daukeba batareda tasaniba,cikin sauri Salma tace"...aa Gimbiya acikin drawer din da yakesa takardunsa nasaka kuma yakan rufe gurin ne sannan su Hindatu bayan wata dai dai akace suna shiga suna kadewa to jibi zasu yi inada tabbacin zasu gani suna kuma iya nunama Gimbiya din tunda ba lallai susan kwalban giya bane"

Jinjina kai Zaliha tayi kafin tace"tashi kije bari mujira zuwa jibin muga inma akwai abunda zakiyimin zan aika ah kiraki"........




Vote
Comment
Share!
[3/23, 6:04 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 55*....


To Salma tacema Zaliha kafin tatashi tafita don komawa bakin aikinta.........

Dab da sallar maghrib su Hamida suka iso masarautar itada driver din da Sulaiman yatura yadaukota direct bangarenta tawuce directly hakanan ko'ina agyare yake fes fes kaman wanda ba barin gidan tayi na tsawon watanni ba gakuma bayinta dasuka saba mata aiki duk sunanan wanda tana da tabbacin aikin Sulaiman ne wannan din bana kowa ba,dakyar ta'iya zama bakin gado tareda dan dafe kanta hakanan takejin haushin kanta dakuma mijinta na miyasa zaiyi mata har saki uku lokaci guda bayan yasan she's carrying his Baby and on top of that she love him unconditionally ah dan zaman dasukayi,hakanan tana tunanin halin da uwarsu take ciki ayanzu,bata dawani buri daya wuce taje taganta amma koma miyene she'll wait for her Brother first dawannan tunanin tatashi tadauro alwala ah bandaki sannan tazo tatada sallah......

Sulaiman baishigo gidaba sai wuraren tara da rabi na dare hakanan bangaren Hamida yawuce direct don tun bayan datayi sallah takira tafada mishi isowarsu..........
Samunta yayi kwance ah dakinta yayinda Laure data kasance Baiwarta tun ada kezaune kasa tana mata massaging kafarta cikeda kulawa don daman asalin ita baiwar Hamida ne inbaku mantaba ko ada haduwarsu da Hajiya Muniba aboye ne sukeyinta don taimaka mata............

Zama yayi bakin gadon yayinda Lauren tagaida shi cikeda ladabi ansawa yayi kafin yace"bayanzu kinayima Hajiya Muniba aikiba?"......
Gyadamai kai Laure tayi kafin tace"Daman tuncan ah Gimbiya Hamida nikewa aiki kuma sabida tatafine shiyasa nakoma gun Hajiya Muniba amma tunda yanzu tananan shine Hajiya Muniban tace indawo inayimata kaman yanda nikeyi ada tunda nafada mata tafi sabo dani".......
Sulaiman yaji dadin zancen don yariga yajima dasanin yanda Hamida takeda Laure,tafi yarda da'ita hakanan dukwani aiki dayashafi harkarta tafison saka Lauren sede kuma wani bangaren na zuciyarshi na raya mishi ai Hamidan tadawo dun dun ne bawai kwanaki kadan zatayi takoma ba itakuma Hajiya Muniba tayi tunanin hutu tazota may be shiyasa tace Lauren tazo",dan kyabe baki yayi sannan yadubi yayar tasa"ya hanya?"........
Murmushin dayafi kuka ciwo tayi sannan tace alhamdulillah Bro,yakake?......
Dan shafa kanshi yayi yana murmushin yaken shima"not that bad", Laure dake zaune ganin kaman suna bukatar sirri seta tashi tafice abunta Allah yagani har ranta takeson Gimbiya Hamida amatsayin uwar dakinta hakanan tana fatan Allah yasa kada Itama tacigaba da bin halin uwarta dukda ma ita babu abunda tayi ko ah da din,she was just rude to her blood sisters and tadaura rayuwarta kan yin waya da tsohon saurayinta dakuma social media baki daya wanda hakan yasa batadamu da alamuran mutane baki daya bama..............

Tashi Hamida tayi tazauna yayinda Sulaiman yadaura idanu kan dan karamin cikin Hamida cikeda takaicin abunda mijin nata yayimata, ahankali yace "Dagaske sakin ki yayi Sis?"...
Gyadamishi kai tayi ahankali yayinda idanunta suka ciko da kwallar da take boyewa tundazu ahankali yajanyota jikinshi tareda rungumeta yana fadin"sorry,you don't have to worry Allah yasa hakan shiyafi alkhairi"......
Amin Hamida tace tareda karawa da"Amma aikoba komai seyayi tunanin unborn child dinmu ko?".......
Gyada mata kai Sulaiman yayi sannan yace....
"kinyi mishi wani abunne?".....
Jijjiga kai tayi alamun a'a kafin tace"from the beginning kaman auren bazai yi kyau ba amma zamana dashi I came to know he's a very simple and honest person Sulaiman,baida hayaniya and despite him being from a royal family becika girman kaiba wannan kyawawan halayen nasa sukasa nafara sonsa though I never express my feelings but I've changed my attitude from being cold to being nice to him dukdama in inason abu nadinga mishi naci kenan harsai yayimin shiyasama danaji labarin abunda yafaru da Mama nadinga mishi maganar zanzo ni gida amma yaki nikuma raina yabaci don aganina ai baikamata yayimin haka ba shiyasa mukayi kaca kaca haryakaishi gayimin saki with which i was very shocked, he's never like this hakanan baya daukan mataki batareda yayi tunani ba it's unlike him to divorce me akan silly abu haka"...........

Sulaiman dake shafa gadon bayanta yace...
"do you have any enemy over there?".....
"His Aunt,she never like me sabida taso 'yarta ya aura and the Daughter too she hates me way too much",tayi maganar ahankali and kasan GIDAN SARAUTA wani makiyin nakama backstabbing naka zainayi without you knowing,some will pretend to love you while baswa sonka harcikin zuciyar ka"......
Gyada mata kai yayi sannan yace"bazamuyi zargin kowaba ayanzu sabida zato zunubi ne koda yakasance gaskiya,koma miyene we should keep praying and shida yamiki haka he'll surely come back looking for you yanzu kikwantar da hankalinki,take very good care of my unborn niece Allah natareda mu and please don't think of doing anything stupid akan Mama komai yafaru da'ita ita taja kuma inafatan yazame maki ishara and believe me harda alhakin mutane data dauka shiyake bin mu ayanzu".......
Goge kwalla Hamida tayi tareda gyadamashi kai kawai don ita daman babu abunda tayi niyan yi damuwarta ma ayanzu sun isheta dukdama tanason kallon Magajiya din taga wani hali take ciki,dagowa tayi daga jikin Sulaiman din sannan tace bazai yuyu Inga Maman ba?....
"You can't,babu maiganinta and wannan order ne da Dad yabayar we can't change it just keep praying for her Allah yasa tagane gaskiya", Sulaiman yayi maganar murya ah raunane kafin yakuma tambayarta da"kinci abinci ne?".....
Eh kawai tace mishi kafin yatashi tsaye yana"go to sleep now and if you need anything just let me know,maganan fadama Abba batun divorce dinki kibari seyasamu sauki sosai ganinki ah gida na'iya sake tayar maida hankali kinji".......
To tace mishi kafin yayi mata saida safe sannan yafice zuwa bangarenshi yauma samun koina agyare hakanan yawuce dakinshi yayi wanka yasauya kaya zuwa na bacci kafin ya kwanta yanason jin muryan Sumayyan amma yasani komi zaiyi bazata taba picking calls dinsa ba don haka kawai seya lumshe idanunshi tareda jan bargo yarufe kanshi,yafi mintuna talatin bacci baidaukeshi ba hakanan yanaji aka bude kofar aka shigo amma baidamu da duba wayebane don yanada tabbacin Zaliha dince.....

Zuwa tayi tashige jikinshi baice mata komaiba dukda kuwa irin kunan da zuciyarshi keyi mishi,itane tafara cewa"Sweetheart inakaje tunsafe daka fita bansake ganin ka ba and na ajiye maka lunch dinka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login