Showing 147001 words to 150000 words out of 235422 words

Chapter 50 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3521

karamin ciki kamar yanda tafada mishi last time dasukayi waya.........
Cikeda damuwa yace"Zansa aturo mota yazo yadauke ki,Abba is sick now I can't tell him anything sekinzo gida din kawai"....
Gyada Kai kawai tamashi kamar wanda tana gabanshi kafin tayi hanging up call din ji tayi zuciyarta nayimata wani irin kuna........
Abangaren Sulaiman kuwa lumshe idanunshi yayi tareda jinginar da kanshi jikin gini tunsafe babu abunda yasama cikin shi hakanan yakasa tashi daga gun zaman makokin tun bayan da suka dawo daga jana'iza, addu'o'i kawai yakeyi Allah yakawo mashi sauki cikin lamuransu baki daya, Almustapha kuwa yayi yayi dashi yaje yaci abinci amma yaki shikuma bayason yakawo masa abinci cikin taron mutane ga Dad ma is somewhat busy bare ya hadashi dashi and Abba too haryanzu bai farfado ba dukdama likita yace su tsanmaci tashinshi zuwa dare ko safiyar gobe insha Allahu.............

****
Bangaren Magajiya kuwa tana can gidan horo gashi taki cin abinci tun safe, ciwuwwukanta ma sunyi wani iri dasu and taki yarda abata treatment dukda they're just trying to be nice to her ne kafin atashi fadan hukuncinta wanda Almustapha ne yasa ayi hakan, hakanan ba'a fada mata rasuwar Wazirin ba tun safe,bangaren Talatu kuwa ankaita clinic tun ah jiyan sannan anyi treating wonds dinta kafin akasakata cikin gidan yarin masarautar kafin afara case dinsu wanda duk jiran Mai Martaba akeyi tukun.........

****
Around 4:30pm motarsu Asiya tasauka acikin masarautar zazzau wanda yatafi da imaninta lokaci guda because dukyanda ake bata labarinta bata tsanmaci ganin har haka ba tunda bata taba zuwa ba don ko ah auren su ai ita kaduna aka wuce da'ita batareda tazo taga gidan Asma'un ba.........
Hajja ma da aka fito daga mota sewani washare baki takeyi kamar anbata gonar auduga tana"oh ni Hajja ashedai darabon zanganni cikin irin gadajen danakejinsu ah tarihi kullum kokuma ingani ah TV, Allah gatan bawa",tayi maganar kuma tana dan sharar kwallah......
Aslam ma saukowa yayi yana dan dariyan Hajja din kafin yashiga kiran layin Sulaiman don number shi kadai yakeda shima agurin daurin aurene sukayi exchanging sede unfortunately wayar ah kashe take....
"Dan rike kugu yayi sannan yace yanzu yaza ayi musan wannene bangaren Asma'u ah wannan makeken gidan kekuma kince kar ah kirata you want to surprise her",yayi maganar yana maida kallonshi ga Asiya......
Yar dariya tayi tareda dan riko hannunshi tana....
"Kai Sweetheart sekace babu mutanen dazamu tambaya"......
Jan hancinta yayi yana smiling to wakike ganin zamu tambaya nibanason raini kinsani.......
Cire hannunta tayi daga nashi tana yar dariya"to bani in tambaya mana",tayi maganar tareda nufan wani dogari dataga yana tafiya cikin sauri yarikota yana"dawo I'll ask him myself"......
"Murmushi kawai tayi tareda dawowan daman tasan za'a rina Aslam da shegen kishin tsiya wani sa'in har mamakin ya akayi ya yarda ze aureta take even after yaji batunta da Abba Dj sede kuma datayi laakari da irin sonda yake mata se tadaina mamakin".......

Ba ajima ba sega Aslam din yadawo tareda dogari nan dogarin yadauki kayan Hajja sannan yayi masu jagora har bangaren su Asma'u......
Asma'u dayanzu dawowansu daga bangaren waziri itada Mom, Ummi, Afiya da Amira sunje sunyima iyalansa ta'aziya sannan suka dawo don su Amira ko islamiya basujeba sakamakon rashin da akayin,ko cire hajabinta batayiba taji ana sallama kuma kamar muryar data sani,dogarin ne yafara shigowa da kayan bayan ta'ansa sallamar sannan Asiya tashigo yayinda Hajja ke bayanta Aslam kuwa tunda dogarin yasanar dashi anyi rasuwa sekawai yawuce gurin zaman makokin donyima su Sulaiman din ta'aziya..........
Wani irin ihu Asma'u tasaki sakamakon ganin Asiyan datayi yayinda taruga aguje tafada jikinta tana ihun murna Amira da Afiya dake parlourn seda suka tsorata haka Ummi ma dake daki tuni tafito tana tambayar lafiya,meya samu Asma'u din sede ganin bakin da tayi setaja bakinta tayi shiru....
Asma'u dake jikin Asiya tana murna tace"Aseey wannan zuwa babu sanarwa haka?"....
Murmushi Asiyan tayi tareda dago Asma'un daga jikinta sannan tace"bakiji dadin ganina bane inkoma,don't you like my surprise?"......
Turo baki Asma'u tayi tana karema Asiya kallo dubada yanda tayi jiki abunta tazama matar aure sak ba Asiyar datasani ah da ba sannan tace..
"I like your surprise Sis,I'm so happy bazaki gane yanda nayi kewanki bane ba"......
Cikeda damuwa Asiyan ma tace "Nima nayi kewanki sosai Asma'u"...
Hajja dake can baya ganin ba'akasa da'ita ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ba seta saki kuka harda shesheka tana....
"ni Hajja nashigesu nayi laifin da Asma'u ko kallona batason yi yau"......
Cikeda mamaki Asma'u tature Asiya don tabbatar wa kanta muryar Hajjan taji aikuwa itance dasauri takarasa gareta tana"Hajja kukan me kikeyi?".....
Hajja dake sharar kwallah tace"kiyi hakuri jikata nasan nayi maki laifin da ba lallai kiyafemin ba amma don Allah kiyafe min wayasanima kona kusa mutuwa,banason inmutu da alhakinku", Asma'u batasan sanda tarungumi Hajja tana sharar kwallarba Itama tana fadin ahankali"it's okay Hajja,kada ajimu akwai mutane ah parlourn",aikuwa tuni Hajjan tayi shiru daman kukan gulma ne.......
Asma'u kasa sakin Hajja tayi ah jikinta hakanan jitake inama agaban Ummi ne hakan tafaru don tasan zatafi kowa farin ciki ma,ashedai akwai ranar da Hajja xata rungumeta kamar yanda takeyima su Asiya, Allah buwayi me iko kuma mai canza al amuransa aduk lokacin dayaga dama.........
Ummi ne ganin oyoyon bana kare bane tace...
"Daughter bazaki shigo dasu kigaisa dakyau ba kuntsaya daga waje?".....
Cikin sauri Asma'u tashare kwallarta kafin tajuyo ga Ummin tana yanzu zamu karaso sannan takama hannun Asiya da Hajja tashigo dasu parlourn tace su zauna Itama kuma seta zauna gefen Hajjan tareda kwanciya ajikinta kadan tana cewa...
"Ummi ga Hajja na gakuma twin sis dita Asiya"......
Murmushi Ummi tayi tareda karasowa parlourn tashiga gaida Hajja din kafin Asiya ma tagaidata haka su Amira ma kafin daga karshe Amira tace dagaske ku twins ne?....
Dariya sukayi dukansu biyu tareda gyada mata kai murmushi kawai Ummi tayi don tasan sudin ba twins bane ba tunda ranar bataji Ummi ta ambaci Asiya cikin Ya'yanta ba.......

Cikeda mamaki Afiya tace"But they're not identical"......
Dan gwaliyo Asma'u tayi masu tana"ai twins badole se suna kama ba besides kune bakuga kamar ba amma mutane da dama ma suna fada".....
Cikeda tuhuma Afiya tace"bawani banyarda ba,they're not twins agreed akwai kaman jini amma ba twins baneku"....
Ummi ne tace"tomiye na binciken kosu ba twins bane what matters they're sisters and they love each other".......
Murmushi kawai Asiya da Asma'u sukayi yayinda Amira da jaraba tace zantambaya ah gidan ku duk randa najeni..........

Kan kacemi ancika gabansu da kayan ciye ciye, Ummi sejan Hajja takeyi da hira tareda tambayarta mutanen gida har aka kira sallar maghrib kafin tabarsu sukayi dakin Asma'u don yin sallan anan ne Asiya tasamu zama da Asma'u bayan sunyi sallah tana fada mata sunga program and taji dadin yanda everything turn out this way sannan tadinga bama Asma'un shawarar zaman aure tareda yanayin zama acikin *GIDAN SARAUTA*, Hajja kuwa se kalle kalle takeyi ah dakin donba karamin tafiya da imaninta kyaun dakin yayi ba har bayan sallar Isha kafin Aslam yakira Asiya kan ta fito su tafi gida Asma'u kaman zatayi kuka tace "nadauka kwana zakuyi fa",dariya Asiya tayi sannan tace...
"bafa mukarasa ko gida bafa,kinga dole muje kadama Daddy yafara tambayana tunda ance mishi zamuzo".....
"Ayya am Daddyn ma nasan bazai hanaba inkincemishi zaki kwana",dariya Asiya tayi sannan tace babu ruwana sokike Yaya Musty yamin korada hali kenan besides nima bazan iya barin mijina shi kadaiba and Hajja nanan ai".....
Babu yanda Asma'u ta'iya haka itadasu Amira suka fita raka Asiya bayan tayima Ummi sallama haka Ummi tacikata da turarraruka ah leda bayan tace tagaida mata su Ummi da Mommy.....
Abakin mota suka samu Aslam,Almustapha da Sulaiman suna dan hira sama sama tunda suka iso gurin Aslam yake baxa idanu acikinsu yana"ina Sister Gimbiya Ma'un ne wai?".....
Turo baki tayi hakanan taki gaidashi sarai tasan yagane ta neman tsokana ne kawai itakuma haushi takeji don gani take kamar shine yahana Asiyan kwana......
Asiya datasan halin Asma'un ne tace"wai fushi takeyi".....
Dafe kirji yayi playfully"ni Aslam mijin Asiya menayi?"......
Cikin raha Asiya tace"kahana Asiya kwana agidan kanwarta"......
Dariya yayi tareda duban Almustapha sannan yace"Matarkan nan shagwabar ta yayi yawa,yakakeyi da'ita newai!"...
Faking smile kawai yayi don seda yaji wani irin jin ance tanada shagwaba wato bama ashikadai takeyimawa ba harda wasu katti komi?....
Asiya ne tace...
"Ina wuni Yaya Almustapha"......
Dukda baiganeta ba amma seya amsa mata fuska daukeda fara'a yayinda Sulaiman yace "itace Asiya she's her sister,matar Aslam".......
Murmushi kawai yayi yayinda suka shige mota bayan sunyi masu sallama seda ta tabbatar dagaske tafiyar zasuyi Aslam din baida niyar barin Asiyan setayi saurin karasawa side din da yake idanu cikeda kwallah tace"Ina wuni Yaya Aslam"......
Dariya yayi yana"kin hakura kenan?".....
Wannan karan hawayen seda suka zubo tana fadin...
"to ya na'iya".....
Bashi kadaiba harda su Sulaiman seda suka kwashe da dariya at her expression except Almustapha.....
Dakyar Aslam ya'iya rike dariyartasa sannan yace"sorry Ma'un Yaya Mubaraq namiki alkawari zankawo miki Asiya wataran tayi maki kwana biyu amma dai banda yanzu"......
Share kwallarta tayi sannan tace"promise?".....
Gyada mata kai yayi yana smiling sannan yace"I promise Sis"......
Haka sukayi sallama Asiya ma duk taji ba dadi kafin suka tafi,satan kallon Asma'u Almustapha yayi ganin haryanzu sharar kwallah takeyi kafin yaja hannun Sulaiman sukayi side dinsu badon yasoba,suna shiga parlourn yace da Asma'u da suka shigo abayansu takawo abincin Sulaiman din....

Gyada mai kai tayi sannan taje tazubo takawo,duban tulin abincin Sulaiman yayi yana...
"badai kunason kuce nikadai zanci abincin nan ba?"....
Wani kallo Almustapha yayi ma Sulaiman din yana"mema kaci tunsafe tukun?".....
Turo baki yayi kamar karamin yaro yana"ammadai wannan yamin yawa"......
"Kaci dai",cewar Almustapha din.......
Hakanan yafara ci ahankali babu laifi yadan ci sosai donshima bakaramin yunwa yakejiba daman kafin daga karshe yadauki glass cup din ruwan da Asma'u ta ajiye mishi yashanye tareda cewa"alhamdulillah"
Murmushi Almustapha yayi cikeda jin dadin yanda Sulaiman din yaci abincin sosai sannan yace"kokaifa"....
Yar dariya kawai Sulaiman yayi wanda baikai zuci ba sannan yatashi tsaye yana"asuba tagari nikam bacci nikeji"......
Dan kallonshi Almustapha yayi sannan yace"where is your phone?"....
da mamaki yace yana aljihun wandona,halama Almustaphan yamashi da hannu nacewa ya miko masa babu musu yacirota ah aljihun yamika masa kunna wayar Almustapha yayi kafin yamayar masa tareda cewa"kada kasake kashe wayarka".......
"To Big Bros",cewer Sulaiman din tareda yimasu saida safe kafin yafice zuwa bangarensa........

Almustapha dakinsa yawuce ganin Asma'u natareda su Afiya,bejima dashiga ba itama tabi bayanshi sede ita dakinta tayi inda tasamu Hajja na sallah da alama shafa'i da wuturi takeyi don yariga yazame mata sabo daman kullum setayi.......
Murmushi tasaki sannan tacire kayanta tashige wanka abunta...........
Bangaren Sulaiman kuwa bangarenshi yawuce direct sede tunda yashiga yakejin wani kamshin turare nadaban da alama ansaka turaren wuta ah sashin bakidayanta abunda zai iya cewa harya manta yaushe rabon dayaji anyishi dondai ah iyasaninshi tun farkon aurensu da Zaliha ahaka dai yana mamaki harya karasa dakin shi sede to his own surprise ganin Zaliha yayi sanye da wasu shegen kaya daya nuna gabadaya illahirin jikinta yayinda hannunta ke rikeda turaren wuta tana zagaya dakin ahankali gakuma sanyin AC daya hadu da special scent din Sulaiman ya gauraye dakin wannan dalilin yasashi lumshe idanunshi ahankali kafin dakyar ya iya daurewa yakarasa bakin bedside drawer tareda ajiye phone din dake hannunshi jiyayi tarungume shi ta baya wanda hakan yasashi jin wani iri lokaci guda,cikin sauri yake kokarin yakice ta daga jikin shi yana"banason irin haka Zaliha,do not try me this night I'm not ready for your stupidity" ......

Wani irin sake rungume shi tayi tareda zagayowa tagabanshi tana mishi kisisina...
"I'm sorry,I missed you so much"......
Tureta yayi da karfin hali sannan yazauna bakin gado yana ajiyar zuciya aranshi yana addu'ar kada Allah yabata ikon cin galaba akanshi don yasan bazai wuce tazo tatadamai sha'awarshi baneba bayan bakaramin kokarin fin karfin zuciyanshi yake ah kwanakinnan ba,kanya ankara harta fado jikin shi yana shirin magana tayi saurin hade bakinsu guri daya daganan tashiga yi mashi salo kan kacemai Sulaiman yabada kai haka suka cigaba da aikin lada itakanta Zaliha bakaramin kewar mijinta tayiba dukda ma yanzun tayi hakan ne sabida tasamu tanuna mishi ita ta tuba fa and she's sorry for all she did kafin kuma tasamu tayima sauran yan gidan fake tubanta sabida tasani without his support bazata iya achieving wannan dinba dukda kafin tashawo kanshi da wahala yanzunma don tasan lagonshi ne amma tanada tabbacin dasafe akwai drama tsakaninta dashi.......

****
Around 11:30pm jirginsu Sumayya yasauka ah airport din kaduna,hakanan tafito daga airport din ta tsaya tana trying number din Matar Idriss abokin Sulaiman don fada musu isowarta because babu wanda yasan dazuwanta agida bare azo tarbanta itanma batayi tsanmanin zatazo dinba sede irin yanda tayita kiran Sulaiman batasamunsa yasa hankalinta yatashi lokaci guda gashi inta tambayi su Afiya sesuce mata lafiyansa Lau,tayi tayi sukaimasa nasu wayan sesuce mata baya kusa kosu bata wani excuse wannan dalilin yasa tun jiyan tashirya tahowa don jitake ah jikinta ba lafiya ba........
Haka tadinga kiran layin Matar Idriss din akashe gashi batada number din Yaya Idriss din wannan dalilin yasata tunanin gwada sake trying number din Sulaiman may be yanzu ya kunna wayar inyaso seya turo mata na Idriss din dukdama she wanted to surprise him ne kawai sede yaganta agida.......
Kiran wayan tadingayi sede har sau biyu ba'a dauka hakanan tacigaba da kira Zaliha dake kwance jikin Sulaiman dayake bacci tayi tsaki tareda daukar wayan jin anata kira duban screen din tayi ganin Sumayya ne yasata dagawa cikin sauri kafin tatashi daga jikinshi ahankali tashige bandaki sannan cikeda bacin rai batareda ta amsa sallamar Sumayyan ba tace"waike wace irin mayyace,kokin manta cewa Yayannaki yanada da aurene haba",Zaliha tayi maganar raibace kafin takarada"inbanda jaraba acikin salasainar daren da mutum yake kasancewa da iyalinshi ma baza'abarshi ya huta ba,to bari kiji infada miki inkika yarda kikasake kiran mijina ah irin wannan lokacin to gaskiya za ajimu".......
Daganan Zaliha takatse call din tareda komawa dakin gurin Sulaiman daketa sharara bacci, Sumayya dai mutuwar tsaye tayi hakanan tarasa abunyi,wani irin kututun bakinciki ne taji ya ziyarceta lokaci guda hakanan batasan sanda hawaye sukafara bin kuncinta ba,she came all the way for him thinking that something bad is happening to him ashe yana tareda matarshi hakanan tamanta cewa yanada wanda suka fita kusanci dashi hakanan batasan ya akayi tamanta ah al amarinsu zatayi encountering rayuwa da kishiya ba indai tace zata auri Sulaiman, tamanta ma da existence din Zaliha because all she sees was Sulaiman,his love,his support and care and all she care for shidinne seyanzu da Zalihan ta tunatar da'ita babu abunda take furtawa se neman sauki azuciyarta ahaka dakyar takoma cikin airport din tasamu kan wani bench tazauna akai tareda lumshe idanunta zuciyarta nayi mata kuna hakanan hawayen basudaina gangarowa ah kuncinta ba..........
*****
Seda tagama sa kayan baccinta sannan tadubi Hajja dake kwance kan gado hartayi bacci don tunkafin tama fito ah wanka ta kwanta,sotake suyi hira if possible suma kwana sunayi amma Hajjan harta kwanta murmushi tasaki tareda gyarama Hajjan bargon sannan taje takashe wutan dakin kafin tadawo takwanta hakanan setaji tana son takwanta ajikin Hajja din shiyasa ma ta matsa kusa da ita tareda shigewa jikinta cikin sauri Hajja tatashi don daman ba nauyin bacci gareta ba tana"waye wannan?".......
Murmushi Asma'u tayi sannan tace "nine Hajja daman baccin ki beyi nisaba?".......
Hajja dake mitsike idanu tace....
"kedin badai anan kike nufin zaki kwana ba?".....
Dan turo baki tayi tareda kunna hasken wayarta tana"Gadon bazai ishemi bane Hajja,inbazai ishemuba se in kwanta kan kujerar can",tayi maganar tana pointing sofa din dake cikin dakinta.........
Wani kallo Hajjan tayi mata kafin tace"waya gaya miki ana barin turakar miji ko waya fada miki anabarin miji irin Almustapha yakwanta shikadai to inma kinayi ne donni wallahi baki burgeniba don haka kawai bazanso mijinki yazo yanacewa na hanaki zuwa dakinshiba bayan bahaka kika saba ba kibarni da irin kunyar dazanji innahadu dashima sakamakon abubuwan danayi abaya sun isheni".........
Asma'u na shirin magana Hajja tace"karki damu indai nine,tashi maza kije ga mijinki kinji".......
Gyada kai kawai Asma'u tayi amma gabadaya ranta ya jagule, tukunnan ma ta'ina zatafara kwana daki daya dashi fisabilillahi,haka tafice tana ta turobaki itakadai......






Vote
Comment
Share.....
[3/23, 6:04 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad....

*Page 54*.....



Itakadai,tafi mintuna biyar tsaye wurin dinning table din da ba'ama cika anfanidashi ba hakanan yazama kaman abun kwalliya ne kawae agurin wanda kuma yake daidai setin dakin Almustapha din kafin tajuya tana karema parlourn kallo,babu kowa cikinta hakanan duk wasu nau'in kallo ankashe shi sede ba'a kashe wutan parlourn ba da alama wanda yafita last ya manta ne kokuma yanada niyar dawowa se Allah be bashi iko ba............
Dan furzar da iskan bakinta tayi aranta tana fadin da'inje dakinshi aigwanda inkwana anan inyaso da asussuba inkoma dakina batareda kowama yasaniba because I'm very sure kowa yayi bacci by now,dawannan tunanin ne takarasa gurin switch din wutan parlourn takashe sannan tahaska wayarta takarasa kan three seater tafi minti uku akwance akai amma she's not feeling comfortable wannan dalilin yasa tadauki daya daga cikin cushions din tajefa kasa kafin takwanta akai hakanan tana jin dari kadan kadan sabida rashin bargo amma hakan baisa ta daddaraba kan kacemai bacci yadauke ta dukdama atakure takeyinshi.............

Almustapha nazaune kan makeken bed dinshi yayinda kafanshi ke mike hakanan yadaura labtop akansu yana research har wuraren shabiyu da rabi na dare kafin yakashe system din ya ajiyeta can gefe kafin yayi shirin kwanciya,har ya gama addu'an bacci seyaji yanajin kishin ruwa kuma wannan dalilin yasashi tashi yakarasa ga fridge dinshi dake cikin dakin sede gabadaya ruwan sun daskare babu wanda zai iya sha ayanzu hakan yasashi sakin tsaki ahankali batareda yashiiryaba kafin yafice ah dakin don daukowa ah fridge din dake parlour because Allah yagani bazai iya zuwa na kitchen ba tunda shiba ma'abocin zuwa gurin bane ba........

Ganin parlourn da duhu gashi bai fito da wayarshi ba sekawai yasa hannunshi yana lalubar switch din wutan inda yake tsanmanin agurin yake don daman yana dab da kofar dakinshi and hasken wutan dakinshin ma yana haskowa kasancewar dakinnashi ah bude yake,bayan ya kunna wutan ne yayi inda fridge din yake sede da mamakin shi yayi arba da figure din Asma'u dake kwance kan carpet bakaramin mamaki yashaba don wallahi dabadan wuta akunne yakeba sema yatakata batareda yasani ba gashi baccin ma atakure takeyinshi kallo daya zakayi mata kagane cewa she's not really comfortable,tabe baki yayi ahankali sannan yakarasa ga fridge din yana mamakin wani dalilin ne zaisa tabaro dakinta tazo takwanta anan seda yasha ruwan me isansa sannan yadawo inda take ahankali yatsuguna gabanta kafin yashiga tabata ahankali yana"Asma'u, Asma'u wake up"...
Amma shiru sema kara juyamai baya da tayi dan tsaki yayi ahankali kafin ya ajiye goran ruwan daya dauko sabida Incase inyasake jin kishir ruwa zuwa anjima hakanan yana tunanin yadauketa ne kawai donya lura batada niyar tashi,tana sanye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login