Showing 27001 words to 30000 words out of 235422 words

Chapter 10 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3535

anan baki dayan ku sedan wani abu dayataso dakuma wata decision dana yanke,bikin Hamida da Sulaiman yazo alhamdulillah so alokacin wannan taron inason inrada Sulaiman amatsayin Yarima wanda shine zai gaje ni bayan na sauka daga mulki dukda kuwa mahaifiyarku taso ayi hakan tun adacan baya amma naki sabida dalilin rashin ganin Dan Uwana Almustapha naso ace yadawo in yanada 'Da babba to tabbas yafi kowa cancanta abashi sabida asali shine yakamata yahau sarautarma sede Allah beyiba yanzu wurin kimanin shekaru talatin Ina nemanshi sede har yau babu labarinshi, ahankali yadubi ahalinnashi sannan yakarasa da nasare inaganin babu kaddarar sake haduwarmu sannan kilan zaman Sulaiman magaji na shine mafi alkhairi ga mutanen Zaria dama kowa baki daya shiyasa nayanke wannan shawarar kuma gobe zan tattaunata da mutanen fada in Sha Allah......

Tunda sarki yafara magana Magajiya takejin ranta yayi wani irin fes yayinda ah bangaren Sulaiman bahaka baneba sabida shi bahaka yakeson jiba,tunaninshi daya yazaiyi yahana faruwar wannan abun,sosai yan uwanshi suka shiga tayashi murna murmushi kawai yake ah fili wanda bawai yakai har zuci bane ba.......
Rufe taron akayi da addu'a yayinda kowa ya watse,tunda yaje shashinshi yarasa nazama dakuma abunyi sekai kawo yakeyi daga karshe
ya yanke shawarar zuwa yasamu Magajiya kilan ta taimaka mishi dukda kuwa hope dinshi na ta taimaka mishi is 1% out of 100% dasauri yake tafiya dogaraye nata zubewa suna mika mishi gaisuwa amma ko kallon inda suke beyiba bare ya ansa musu,sashin mahaifiyartasa yashiga inda tundaga bakin kofa yakejin muryarta tana Humaira idan ba hakan nayiba shi kanin naku babu abunda zai samu sede yazama kaman bawa ko dan kallo,muddin hakn tafaru nikuma nazama ba komaiba acikin Masarautar nan,tsayawa yayi don yakarasa jin metake fada.......
Inda Magajiya tashiga Jero ma Manyan 'Ya'yanta abubuwan ta aikata ....

Humaira nine sanadiyar barin Yayan Babanku gidan nan tunda jimawa sabida tun ina karama Allah yadauramin son mahaifinku sannan nakudurtama raina sena aureshi kota halin yaya, sede on the other hand mahaifinku ne karami and wanshi ne zezama sarki alokacin na lura Abdulrahman nason sarauta and shida kawunku suna matukar son juna don zasu iya sadaukarwa juna koma miyene adalilin kaunar dasuke ma junansu sannan abunda nakara lura shine shi kawun naku bayason sarauta dawannan makamin nashiga rayuwar mahaifinku nasashi abaya yazamanto meyawan rubuce rubuce duk abunda yafaru dashi wanda inada tabbacin shi kawun naku zai gani wanda har burina yacika nasamu nakawar dashi ah idanuna....
Sake duban Humaira da Halima Magajiya tayi sannan tace
Humaira nine sanadiyar gushewan kwakwalwar Mai Martaba harya manta dawaye Khairiya dama 'ya'yanta ah gidan nan wanda kuma inada tabbacin har abada bazai taba tuna kowacece itaba sabida wanda yayimin aiki banawasa bane ba sannan nine sanadiyar halin da Khairiya keciki sabida nagaji da ganin idanunta acikin Masarautar nan nagaji da yabata da Mai Martaba yakeyi dukda kuwa tafita ah rayuwarshi sabida ko bayan narabasu nasa yamanta da'ita namayar da Khairiya baiwa na cikin masu dafa abinci wanda aboye nayi hakan kada Waziri yasani sede kash bansan wani abun najama kainaba don tunda Mai Martaba yaci Masan da Khairiya tayi sau daya yace shifa kullum wannan Masan da miyar ganye yakeso anamishi dasafe washegari nasa wata tayi yakici dole se itan ne tacigaba dayimishi dukda bawai raina yanaso bane haryakai ga Mai Martaba yace yanason ganin wanda takeyi mishi masa yayi mata godiya Kuma yanason tanamishi duk wani abincinshi nanfa hankalina yatashi sosai shine nasa akayi mata illar da har yau tana kwance kuma bazata sake tashiba dasunan dafawa Mai Martaba masa bare har tayi tunanin ze yafe mata ko ya tuna da ita watarana,ahaka zata Kare har abada dukdama banyi tunanin zata Kai har yanzu ba...
Halima ne ta jinjina Kai sannan tace gaskiya Mama kinyi daidai sabida ah *GIDAN SARAUTA* in mutum be tashiba yama kanshi hobbasa ba to sede yazama dan kallo ko bawa,gwanda ace Kaine shugaba shiyasa kikaga nima tunda nasamu 'da namiji nadaina ragama sauran kishiyoyina....
Murmushin mugunta Humaira tayi sannan tace ayyayya wato shine dalilin dayasa Abba bayacin masa da miya?....
Hmmm wannan shine dalili Humaira don cemasa nayi meyimasa masar Allah yayi mata rasuwa ranar yini yayi bashida walwala sannan tundaga ranar in anyi masa baya ci sema yayita fada ko inyaci yayi amai.....

Lallai kam,Anya wannan matar Itama ba tsafin tayima Abba ba Mama,cewar Humaira din,oho mata koma shi tayi to tasamu wanda tafita don aduniyarnan bana tunanin akwai mehana ni cinma burina,shiyasa koda nasamu labarin kawun ku naboyema mahaifinku batun.......
Cikeda mamaki Humaira tace Mama kinsamu labarinshi yana Ina?....
Indonesia Humaira,najima dasamun labarinshi sede bansan taka maimai inda yakeba sejiya me aikin nawa yazo yakefadamin,wai yana Indonesia da iyalinsa.....
Hmmm yakarata can basai yadawoba kilan ma yanada 'da namiji cewar Gimbiya Humaira.
nima abunda nagani kenan,shiyasa duk abunda nafada muku kuyi Kim da bakinku kada kowa yaji koda kuwa Sulaiman ne don yaroncan bashida hankali da tunani wataran innazauna inatunani se ince anya 'Dana ne Sulaiman don gaskiya beyi gadoba.....

Dariya Humaira tayi sannan tace kyale Dan banza anayi sabida shi amma bayagani in sha Allah bazamu fada masaba,haka suka cigaba da hirarsu duk akan makircinsu harda batun ah yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Martaba yatsani Almustapha,tsana irin sosai dinnan domin matakin daya dauka kan abunda yafaru wata biyu dasuka wuce baiyimata ba kuma bahaka tasoba. .. Sulaiman kuwa kafarsa kasa daukarsa tayi don kuwa bakaramin mamaki yaji ba,yasan Mamanshi is someone who is not nice at all sede betaba tunanin muguntan nata yakai har hakaba,tunda yafita ah shashinta yasamu guri yazauna tunanin duniya ya isheshi,mezaiyi, *MENENE MAFITA*,ta ina zaifara neman uncle din ah Indonesia tunda shibawai yasan address din bane kuma ah iya tunanin shi kawo kawunsan ne kadai zai tsayarda rada shi as the crown prince da ake niyar yi din sannan daga nan ne Kuma zasu fara tunanin neman mafita gameda rashin lafiyar Ummin,Dafe kanshi yayi all he knows is bazai taba tonawa uwarsa asiriba sede he can do whatever he can to stop her from doing all the evil things datakeyi......
Yana cikin wannan tunanin ne yaji kamar magana kasa kasa,se yayi shiru yana saurare to his own surprise seyaji muryar Magajiya tana"kasamu duk wani bayani?"...
Bawan ne yace eh Uwargijiyata a adireshin shine anan dakuma duk wani bayani akan ahalinsa.....

Yar dariya tayi sannan tace to nagode,nan tacema Talatun tasallameshi sannan suka juya zasu tafi jin suna tahowa ta direction dinshine yasashi saurin tashi yadan buya abayan wani katanga seda ya tabbatar sunbar gurin sannan yafito yana hamdala sannan yawuce sashinshi atleast yanzu yanada hope he'll surely come and look for the details.......

****

Tunda takoma gida tashige daki tarufo kofarta,koda Mukhtar yazo cewa Munira tayi tace masa tana bacci don yau batajin hiran shima Kuma dashike yasan batajin dadi yaudin seyace kada su tasheta hira yayi dasu Mubaraq sannan yawuce gidansa dake cikin garin Zaria din don ba a hostel yake zamaba.....

Juyi tadingayi akan gadon ta tarasa meyake mata dadi,batasan yazatayi da Asiya ba tabar abunda takeyi din,daukar wayarta tayi takunna data dinta tana dudduba chats kozata danji Dadi aranta aikuwa sega friend dinta Aisha online,mamaki tasha kawarai don tajima bata chat fita tayi ah whatsapp din sannan tashiga dialling number dinta aikuwa yayi ringing nan ta daga, Asma'u tafara haba Aisha miye duniya?.....
Dariya Aisha tayi sannan tace kwalin cabin Asmeey,kadama kifara mitar dazu aka kawomin wayar hawana WhatsApp kenan don nasan korafin dazakiyi kenan dariya Asma'un tayi sannan tace "tona maida wukar kawata,yakike it's been long nayi kewarki sosai wallahi"....
Nima nayi kewarki Asma'u,tunfa damuka gama school bamuyi communication ba gashi ba halin ziyartar juna ba gari daya muke ba but I'm back now harsai kingaji dani cewar Aishan......
Hahaha,yanmata kozan gaji dakowa bazan gaji da keba, you're special to me you know that,ya mutanen gida?..
Duk lafiyansu kalau wallahi,tokigaida minsu please kuma namiki murna Allah yasa akashe waya lafiya....
Aisha tace Amin Asma'u nagode sosai semun hadu ta chat,to shikenan nan sukayi sallama Aisha nashirin katsewa Asma'un tace yauwa nikam Aisha yama full name din Sarkin Zaria?....
Yar dariya Aisha tayi sannan tace kinji kunya wallahi Sarkin garin kuma bakisan sunanshiba,pity face Asma'u tayi kaman tana gabanta sannan tace sorry mana kifadamin please naga ke bakya manta irin sunayen nan ne and besides abunda yayi Zaria shiyayi kaduna ai so yakamata kinsani....
To uwar iyayi sunan shi sarki Abdulrahman Sulaiman i guess.....
cikeda jin dadi Asma'u tace nagode to kigaida su Mama,nan ta katse call din lumshe idanunta tayi ahankali sannan tasake bude su duban wayartata tayi kafin tashiga Facebook if she could remember ranar Zahra cemata tayi sunan gayen Almustapha and he's the illigitimate son of the king,tokoma illigitimate son ne yakamata yana bearing sunan mahaifinshi ne donhaka tashiga searching Almustapha Abdulrahman setaga babu don duk sunayen dayake nuna mata is not exact sede similar names,dan tsaki tayi sannan tace"what name could he be using?"....
Can wata idea tafado mata nan tasa Almustapha A Sulaiman suma duk babu wasu sufficient names haushi ne yakamata tayi wulli da wayar sannan tace"he's different from the others,so sunan dayake using ma might be different,komadai miyene I need to apologise to him",dawannan tunanin takwanta bacci...




Vote
Comment
Share!

*Zeeneert*
[3/23, 5:21 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*Page 9*...



Washegari bayan Mai Martaba yayi magana da mutanen fada aka yi announcing bikin rada Sulaiman amatsayin the crown prince wanda za a hada tareda bikinshi dana Hamida,Yan fada damutanen gari kadai ke murna don kuwa bayi bakaramin tashin hankali suka shiga ba sabida sunada tabbacin indai Sulaiman yahau sarauta to tabbas abunda aka daina shekarun baya dasuka wuce za adawo dashi wato zamansu wulakantattu da anfani dasu batareda anbasu wata daraja ba,dukda kuwa Magajiya na tunanin bayin basu san Sulaiman ke wannan aika aikan ba iyakacin wanda yayimadin ne kawai suka sani sede abunda batasani ba labari yariga ya yadu ah tsakaninsu kawai tsoron fada akeyi sabida sanin wacece Magajiya acikin Masarautar......

Tunda aka tashi daga babbar fada yawuce dakinshi yasa dogarayensa suka fitar mishi da kayanshi don tafiya Maiduguri kaman yanda yayima Magajiya alkawari zeje yaga Zaliha....
haka yakama hanya batareda yayima kowa sallama ba.....

****

Afiya nayima Hamida tausa, Hamidan tadube ta tace ke tashi kije kicema Laure Ina Dan waken danace tayimin tundazu jiranta nikeyi.....
Cikeda takaici Afiya tafita tayi kitchen din masarautar wanda kace anguwane guda tsabar girmansa yayinda yake daukeda masu aikin girke girke kowa is busy yana portion din aikin da aka basa,masu yankan albasa dana masu gyara kayan miya daban haka masu duba wuta ma daban,sedacan gefe kuma masu wanke kwanuka nayi,masuyin tuwo ma daban wanda suke afili dayane Kuma nanne ake dafa abincin jama'ar masarautar baki dayanta......
Afiya tagefen su tazo tawuce yayinda tashige wani gu wanda shima dai kaman kitchen dinne sedai bekai wancan din girmaba sannan mutane basufi goma acikinta ba dasukeyin aikin yayinda jakadiya guda daya dake tsaye kansu tana supervising ayyukan dasukeyi da alama nanne ake dafa abincin su Magajiya dakuma Mai Martaba....
Daga can nesa tahango Laure karasawa tayi gurinta sannan tace

"kekam Gimbiya Hamida nata jiran kinzo kinyi zamanki".....
Tsaki Lauren tayi sannan tace bakiga ina jiran ruwan ya tafasa bane,tunda ma kinzo kijefa mata danwaken kawai daman Magajiya na nemana,hararanta Afiya tashigayi tana dashike aini akasaka yin danwanke ko,nidai sako ta aikoni in isar kuma nafada miki sabida haka Kinga tafiyata,dariya Lauren tayi sannan tace kitafi mana barinaje infada ma Magajiya ita zatasan yanda zatayi dake,take kuwa laure tatashi tabar Afiya tsaye gurin kamar gunki,tabe baki tayi sannan takoma tazauna tana jiran ruwan ya tafasa tajefa danwaken don already ankwaba garin danwaken.......
Seda ya tafasa sannan tajefe kwabin tas cikin ruwan, wutan naci sosai don haka tuni yafara kumfa nan tashiga neman matsami sede babushi ah gurin don Lauren bata tanadeshi kusa ba,tashi tayi dasauri don dauko matsamin data hango kan wani dan tebiri, daukan matsamin tayi harzata tafi se idanunta sukayi arba da funkasau da miyar ganye acikin cooler wanda marfinshi is transparent,jitayi ya burgeta kuma harga Allah son ci takeyi batareda tayi wani tunani ba tashiga bude coolern tadauki funkasau daya zata kai baki Talatu dayanzu shigowarta kitchen din tadaka mata wani uban tsawa.....
"Ke mekikeyi agurin abincin su Magajiya?"....
Iye mekikeyi ah gurin tsabar tsoro Afiya seda tasaki matsamin da funkasau din yafadi ah kasa she never thought this was coming kan kace me gabadaya attention yadawo kanta harma da wayanda suke waje suka fara lekowa don gulma,janta Talatun tayi sannan tace mekikeyi anan?.....
Kwace hannunta Afiya tayi sannan tace babu matsami nazo dauka zankwashe abinci.....
Wani harara Talatun ta watsa mata tareda sake damkar hannunta,nafa ganki da idanuna sabida haka kidaina min karya,mekikasa musu acikin abincin?"....
Cikeda firgita tace babu abunda nasaka musu nikam kiduba kigani mana,suna cikin wannan rikicin ne jakadiya ta karaso tana tambayar meyafaru......
Nan Talatu tashiga bayani" jakadiya tundaga can waje nake hango mutum kaman yana barbada abu acikin abinci amma ban tabbatar ba seda nashigo naga tana sake garwaya miyar shine nayi ihu"....

Duban Afiya jakadiya tayi sannan tacema Talatun tayi searching dinta,nan tashiga tattabamata jiki amma babu komai sake kallon jakadiyan tayi sannan tace wallahi jakadiya kiyarda dani naganta,kafin Talatu tarufe bakinta wata baiwa tace gacan wani leda ah karkashin teburin awurge,dasauri kowa hankalinshi yakoma kan ledar dasauri Talatu ta tsuguna tadauko ledar wani irin bakin garine aciki,karba jakadiya tayi sannan tace miye wannan?....
Tuni Afiya idanunta sukayi jage jage da hawaye tace nima bansaniba babu abunda nayi Talatu kiji tsoron Allah dakuma ranar haduwarki dashi..

Ke dallah can rufemin baki,ke yar shegiya dake har kinada bakin cewa wani yaji tsoron Allah cewar Talatun sannan ta zungure ta kibari a tabbatar da abunda kikayi mana tukunnan nan ne za aga waye baya tsoron Allah....
Jakadiya ne tadubi Talatu,ya Isa haka don Allah, Afiya kuwa se kuka takeyi tana ita wallahi batayikomai ba ah duba abincin.....
Wata cikin bayin ne tace to agwada bama mage abincin agani mana,aikuwa nan aka dauki shawararta akasamo mage cikin masarautar nan take sannan aka gutsuri funkasau da yar miya akasaka mishi nan yashiga ci,Amira dake dakin Hamida taji Laure tazo tana kawo gulma dagudu tayi hanyar kitchen,zuwa tayi tarike Afiya tanacewa kada kidamu tunda anbawa magen ai gaskiya zai bayyana ....
Cikin kuka Afiya tace Amira sekace bakisan halin mutanen nan ba ni inada tabbacin da biyu akayi abunnan.....
Goge mata hawaye Amiran tashigayi tana Allah yafisu in Allah ya yardama ba hakan bane ba .......
Jisukayi bayin na ihu ai mage tafara amai daganan kuma tafadi luuu shikenan babu rai,salati akafara da salallami...
Talatu tace aidama nafada amma anaganin kaman karya nakeyi,ga yarinya nashirin yin kisa kiri kiri,kisanma na masu gida,nan fa bayin suka fara yowa kan Afiya kaman zasu rufeta da duka,kankame yar uwarta tayi suna kuka, jakadiya ne tace duk su tsaya basuda right din yanke hukunci sabida duk wani abu daya danganci harkan bangaren bayi mata dakuma dangane da kitchen Magajiya ce zata yanke hukunci sabida haka kowa takoma bakin aikinta, hakan kuwa akayi yayinda jakadiya tasa dogaraye biyu suzo sutafi da..
ita bangaren Magajiya, Magajiya na zaune ah parlourn ta akazo kiranta kan ga wata tayi laifi,yatsuna fuska tayi sannan tace tana zuwa.....
Cikin takun kasaita tafita gaban parlourn nata Afiya ce zube kasa dogare biyu natsaye akanta.....
Kallonta Magajiya tayi sannan tace kekuma me kikayi,bana ce ko kallonki banason inayiba akusa dani?...
Cikin kuka Afiya tace don Allah Magajiya kiyimin rai wallahi nibanyi komaiba, bansan komai ba sharri akayi mini ....
Daga mata hannu Magajiyan tayi alamun batason hayaniya,shiru tayi dukda kukan zucin datakeyi Amira kuwa nacan gefe ta rakube Itama hawayen takeyi tarasa ta Ina zata taimaki Yar uwarta...
Jakadiya ne tadubi Magajiya tace Uwargijiyata kamata mukayi tazuba guba acikin abincin ku kuma har Mage munbama yamutu ah take,dafe kirji Magajiya tayi lokaci daya taji zuciyarta na dukan uku uku,kafin tazare idanu kamar wata zararriya tayi kan Afiya....
Kasheni kikeson yi nida 'ya'yana don ubanki?.....waya turoki,kifadamin maza waya turoki Magajiyan takarashe maganar tareda kaima Afiya naushi,kuka Afiya keyi tana"banibane wallahi,bansan ya akayiba sharri akayimini".....
wani naushin Magajiya tasake kaimata,tana bazaki fadamin ba?....
Itadai Afiya secewa take batasan wayene ba daga karshe Magajiya tace aje da ita gidan yari ayita bata kashi harsaita fada.....kuka Afiya da Amira sukeyi sosai suna Afiya batasan komaiba anma Ina babu wanda yakulasu sema hankade Amira da dogarayen sukayi sannan suka dauki Afiya sukayi gaba da ita,dagudu Amiran tayi gidansu tana kuka dakin Almustapha ta leka bayanan don haka tazari hijabinta tana faman toshe bakinta don kada Ummi taji kukan datakeyidin......
Tundaga masarautar take gudu harta isa kasuwa bata tsayaba seda ta iso gaban shagon Mallam Hudu ta tsaya tana haki gakuma hawaye dake zuba ah idanunta shabe shabe......
Mudi ne ke fadama Mallam Hudun ga kanwar Almustapha tazo tana kuka dasauri yafito don yasan bawai su Amira suncika fitowa daga masarautar bane Kuma tun da har akace tana kuka to ba lafiya ba......
Samunta yayi zube bakin kofar shagon tana kuka tsabar gudun datayi gabadaya tagaji shiyasa takasa karasawa cikima,tsugunawa yayi ah gabanta,"Amira,tashi?"...
Nan yakama hannunta suka shiga shagon dubada yanda jama'a suka fara taruwa suna kallonsu daman acikin shagon akwai wani store don haka yakaita ciki,kidaina kuka kifada min meyafaru?.....
Kasa daina kukan tayi se Afiya datake ta kira,me Afiya tayi kifadamin Amira.....
Mallam Hudu sharri akayi mata,suntafi da'ita ina Yaya Almustapha don Allah kafadamin inda yake?".....
Cikeda tausayi yace yana makaranta bezo nanba seda yanma zaizo......
Kikwantar da hankalinki kikoma gida nasan daya taso ah makaranta nan zezo daganan semuzo gida inji meya faru don na lura yanzu ko magana mekyau bakya iya yi,shikuma ba wayane dashiba bare inkirashi kinji.....
Gyada mishi Kai tayi alamar to dukda bawai maganar tashigeta bane gani takeyi inbataga Al???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?mustaphan ba tafada mishi hankalinta bazaitaba kwanciya ba gashi Sulaiman bayanan don taji Hamida namaganan ya tafi Maiduguri....

Kudin machine Mallam Hudu yabata sannan yace taje gida,haka tafita ah kasuwan ta tari machine nantace mai yakaita Samaru,aikuwa har bakin gate din main campus din ya ajiyeta nan tashiga datambayan mutane har
tasamu ta isa Medical college din,daka ga idanunta zakagane taci uban kuka agaban gurin tahango yan mata na zaune su biyu suna hira abunsu,karasawa tayi gurinsu tareda yi musu sallama, Zahra ne ta ansa yayinda Asma'u tashiga kare mata kallo dubada irin kodaddun kayan dake jikinta gata kuma kyakyawa abunta, astaghfirullah shine abunda Asma'un tafurta tareda dauke kanta gareta...
Amiran talura da kallon da Asma'u tayimata amma bata damuba don abunda yakawota shine agabanta,cikin dashashiyar muryarta tace don Allah kunsan wani yana Medicine sunanshi Almustapha.....
kai tsaye Zahra tace gaskiya bamusanshi ba,sede kitambayi wasu daga can don mu sabbin dalibai ne ah makarantar bakowa muka saniba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login