Showing 192001 words to 195000 words out of 235422 words

Chapter 65 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3522

shiru tayi tana kallon ikon Allah don gabadaya kanta ma ah daure yake kan wani aikine ita Zalihan keson sasu haka,bayani Zalihan tashiga yi masu kafin daga karshe tace"zaku iya?".......

Dan dukar dakai sukayi inda jiddoh ne tayi kokarin yin magana"Gimbiya ai matsalar bamusan yazamuyi mufada mata tayanda bazata gane gulma bane ba"......
"Zaku iya",Kai tsaye Zaliha tabasu answer sannan takarada tabbatarwa zakuyi tana gurin kafin kufara magana kunji....
"To", sukace mata kafin ta sallamesu inda tace kafin jibi takeson aikinta ya auku nan ta sallamesu suka fita,tunda suka fita karimatu batace komai ba bugunta Jiddo tayi cikin sauri tana "bakice komai ba Karimatu"......

Tabe baki tayi sannan tace"to mezance jiddo,nifa kinga banason matsala kuma haka kawai bazan yi abunda zaizo yana damuna daga bayaba"....
Tsaya wa da tafiya jiddo tayi tana rike kugu"me kike nufi,bazakiyi abunda akasamu bane komi?."..........
Amma kinsandai nikadai bazan iya bako.......
Kallonta Karimatu tayi sannan tace
"to ai bansaki dole ba,kina iya kinyi"......
Aa wallahi so kike zamana yakare ah masarautar nan kenan,ta'ina ma zanfara tunanin fasa abunda Gimbiya Zaliha tasakani,kinga nafarko zanzama daya daga cikin na hannun damanta,na biyu kuma zatayi Mana kyauta mai tsoka fa kikaji tace sabida haka don Allah kirufa mana asiri muyi abunda tasaka mu. Kai tsaye Karimatu tace"nikam bazanyi ba jiddoh karki manta fa Yariman Sulaiman dakanshi yanemi yafiyar mu kuma munyafe mishi tun wancan lokacin sannan Yarima Almustapha ma yazo yarokemu kan kada mufada bayason abunda zai bata kaninshi ah idon duniya,mundaukar masa alkawari Kuma ya yarda damu sekuma yanzu mucucesu sabida mune butulu?"..
Tukunnan ma mu ajiye wannan agefe, alkhairi nawa sukayi mana ah masarautar nan jiddoh,sunmaida mana rayuwarmu da ada take cikin kunci zuwa sauki da dadi yanzu,sun samo mana darajar mu amatsayin mu na mutane kaman saura,sunyi mana abubuwa da dama da ada mun fidda ran samun wannan rahamar,kawai sabida abun duniya semu juya musu baya yau?....
To kuwa tabbas damun cika butulu jiddo kuma nidai bazanyi abunda zai tsunduma ni cikin bala'i ba kindai ga inda Magajiya da Talatu suka kare yanzu sabida haka inabaki shawarar kizauna kiyi tunani",daganan karimatu tayi tafiyarta tabar Jiddo tsaye gurin kaman gunki hakanan kuma tana kissima maganganun Karimatu..........

Bayan azahar su Asiya suka iso masarautar,murna gurin Asma'u kamar tayi yaya seda takaisu suka gaisa da mutanen gidan sannan suka dawo dakinsu Amira suna hirarrakinsu,Asma'u nata korafin miyasa basu kawo mata Munira ba tunda su tasan cewa zasuyi bazasu kwana ba....
Dariya Asiya tayi sannan tace"aikuwa taso binmu Ummi tace ba'inda zataje akwai Islamiya da yanma",turo baki Asma'u tayi tana"zankira Yaya Mubaraq ko Yaya Aliyu ince susato min ita don nalura sukadai kesona".......

Tashi Asiya tayi tana oh haka ma zakice ko,to suda sukeson naki suzo su yini mikin mana, Asma'u na dariya tariko hannun Asiya tana"I'm sorry Sis kinsandai wasa nakeyi maki ko".........
Haka suka cigaba da hirarsu Asma'u ne tafara tashi tayi dakinta inda Asiya tabi bayanta daga baya,samunta tayi zaune bakin gado Itama zaman tayi tareda dafa hannunta, Asma'u dagowa tayi tana kallon Asiya kafin tasaki murmushi, ahankali Asiya tace....
"kince zamuyi magana jiya".......

Gyada mata kai Asma'u tayi kafin tace"Eh Asiya,akwai abunda ya kulle min kaine. I'm confused, I really need a helping hand Sis,i need someone with whom i can confide in and may be you're the best option", Asma'u takarashe maganar ah raunane kamo hannunta Asiya tayi in a soothing manner kafin tace"Don't worry Asma'u. I'm here for you kifada min matsalar ki kinji".........

Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi kafin tacigaba da magana"Narasa gane kan mijina Aseey, he's behaving so strangely. He claims that he don't love me while inyayi wani abun se Inga kamar so na yakeyi sekuma wasu abubuwa dana gani ah dakinshi dasuka rikitani Aseey", takarashe maganar wannan karan har hawayenta nazuba cikeda damuwa Asiya tasa hannu tashare mata hawayenta kafin tace kiyimin bayani dallah dallah yanda zangane Asma'u only then za muzo ga gandun neman mafita kinji......
Gyada mata kai Asma'u tayi seda tayi kusan 3 minutes tana composing kanta kafin tacigaba da magana,nan tashiga bata labarin tun farkon aurensu da Almustapha yanda yayi ta yimata harzuwa gandun yau bata boye mata komai ba kafin daga karshe tace"aganin ki haryanzu Yaya Almustapha na nashan giya kokuma aganin ki matakin dana dauka ayanzun shine daidai?"........
Still hannun Asiya nacikin na Asma'u cikeda tausayin kanwartata tace"kikwantar da hankalinki Asma'u everything will be fine Sis".....

Murya araunane Asma'u tace"How Asiya, ta'ina komai zai zama normal?".......
Gyara zama Asiya tayi kafin tamaida attention dinta kan Asma'u din baki daya tace ..
"mufara da maganar shan giya first".........
Gyadamata kai Asma'u tayi kafin taci gaba da magana...
"You clearly know that Yaya Almustapha is a victim,Magajiya ce tasashi yafara shan giya bawai shida kanshi yazaba ma kanshi wannan rayuwar ba,I can't convince you and I can't tell you koyana sha har yanzu ko ba yasha tunda kince baya zama and kinsamu bottles ah dakin shi but what matters is kece zaki gyara mijin ki Asma'u,you know his situation kamata yayi kija ajiki,know his problems, show him the way bawai kiyi shiru kina daura ma kanki damuwa ba kuma the best thing is that he's willing to accept you as his wife for the rest of his life,namiji yarone ah hannun mace Asma'u kece zakijashi jikinki you've to make sure he stop all those bad habits inma yanayi not only for your benefit for shikanshi,your children and his subjects"..........
Kai cunkushe Asma'u tace"baya sona fa,tayaya zanja shi jiki tayaya kuma zansan matsalanshi bayan shidin mutum ne dabaicika son magana ba"......

Murmushi Asiya tayi sannan tace"ikon Allah Asma'u me bama mutane shawara akullum yau takasa bama kanta, it's really simple Dear"....
Murmushin yake Asma'u tayi"bazaki gane bane ba Aseey Yaya Almustapha yawuce yanda kike tunani"........
Dariya Asiya tayi sannan tace duk miskilancinshi tunda yafada tarkon sonki ai angama komai,yanzu seyanda kikayi dashi",cikin sauri Asma'u ta ware idanu da mamaki sannan tace.....
"So Kuma?"....
Gyada matakai Asiya tayi sannan tace"Yes My Dear. Your husband is in love with you sede shikanshi baiganeba".....
Asma'u na murmushi at thesame time hawaye na zuba tace"Dagaske kikeyi Aseey?"....
"Are you sure Yaya Almustapha na nasona?",yanda tayi maganar cikeda hope dakuma excitement seta baka tausayi.......

Ahankali Asiya tagyada mata kai tace"and you'll be the one to make him realize that he's in love with you, you'll be the one to make him confess Sis", Asma'u batasan sanda tafada jikin Asiya tana kuka ba ashedai akwae ranar dazataji wani yafurta mata cewa Almustapha nasonta from his actions because hakan datajin ma ya isheta farin ciki atleast Asiya din tasaka mata hope dukda badaga bakin wanda takeso taji dinba,rarrashin ta Asiya tadingayi harsaida ta tsagaita kukan.......

Sannan tace"yanzu dai ayi hakuri asauko daga fushin da akeyi da Yariman mu", Asiya tayi maganar playfully,Dan dukanta Asma'u tayi tana"Kai Aseey cemiki nayi fushi nakeyi dashi".........
Dariya Asiyan ma tayi tana"inba fushi ba menene to"....
Lol nidai fada min yanda zanyi mashi please,I've no idea....
Lol tonidai aganina tunda shida bakinshi yanuna yanason zama dake to kisamu time kiyi mashi magana kan cewa kema kinyarda yanzu you want him to be your life partner daganan sekina janshi ajiki always ask him his problems,show him you love him and care for him always and I'm very sure sooner or later he'll confess his feelings Asma'u, kobai fadaba inaganin yakamata kigane cewa yana sonki inbahaka ba miyasa yadage sekun zauna tare,miyasa yadage dazuwa gareki dukda kina gudunshi, it's a sign of love Asma'u miskilancin mijin ki ne yahanashi fada but the more you two are closer the more he'll be attached to you,inma yana shaye shayen you can change him tunda bashine yadaura ma kanshi ba kinji?"...
Gyada matakai Asma'u tayi sannan tace"Thank you Aseey zanyi yanda kikace,I'll change him insha Allah bama inkirashi yanzu Asma'u tayi maganar cikeda zumudi",dariya Asiya tayi tana"a'a kekuma make it in a special way mana".......

Kyabe fuska Asma'u tayi tareda maido hannunta baya datake shirin janyo wayarta ah dazun sannan tace"how?".....
Kai tsaye Asiya tace"in a more romantic way"........
Sa hannu Asma'u tayi tareda lullube fuskarta wai ita kunya,dariya Asiya tayi sannan tace nikinga tafiyata tundama kunya ta kikeji nasan you can plan it yourself",nan Asiya tafice abunta don komawa gun su Amira.........
Zaliha dake bakin kofa tundazu tanajin zancensu dataga Asiya zata fito setayi saurin buya seda taga tatafi sannan tafito tashigo dakin Asma'un tana hamdala da Allah yakorota dakin Asma'un ah dazu hartasamu taji conversation dinsu..........

Asma'u nazaune itakadai se smiling takeyi dukdama haryanzu takasa deciding wani irin romantic plan zatama Almustapha din dazai sashi jin dadi,jitayi kaman motsin mutum abayanta cikin sauri tajuya,Zaliha ce ke tsaye tana mata Smilling mayar matada murmushin tayi sannan tace zauna mana Yaya Zaliha.......

Yar dariya Zaliha tayi sannan tace"tunanin me kikeyi haka naga harna bude kofa nashigo bakisani ba?"......

Dariya Asma'u tayi tana"just planning something"....
Zama Zaliha tayi tana"surprise for our Brother In-law?"......
Damamaki Asma'u tace ya akayi kikasani?......
"Lol guessing kawai nayi",cewar Zaliha din,murmushi Asma'u tayi batareda takuma cewa komaiba kallonta Zaliha tayi tanason taji tace wani abu amma jin tayi shirudin itakuma tanason bugan cikinta yasata cewa"you should plan something special for him kaman kiyi masa special dish then docarate the room with flowers,dress like a princess and look good for him,I'm very sure he'll like it"....
Cikeda kunya Asma'u tace kai Yaya Zaliha kina sani jin kunyanki,dariya tayi Itama tana"miye abun kunyar kina iya yimashi gobe ko jibi ma kokuma after the turbaning ceremony"........
Cikin sauri Asma'u tace yayi nisa,dariya Zaliha tayi cikeda jin dadi don daman neman hanya takeyin hakanan tanajin dadin yanda Asma'un ke fada mata komai atleast she'll get some clue yayinda afili kuma tace"inyeee wannan so haka".........

"Kai Yaya Zaliha kibari mana",cewar Asma'u din,tona bari cewar Zaliha din inda Asma'u tace kinga daman yau su Afiya zasuyi parking zuwa bangarensu Ummi ma angama yimata jere dakomai komawa ne kawai batayiba se bayan andaura aurensu da Mai Martaba amma yawancin mutanen ta acan suke yini so gobe kamu I'll use that opportunity to do as you say tunda dayanma za ayi kamu. May be after that.....
Gyada matakai Zaliha tayi kafin tace toshikenan, I'll come and help you inkinaso......
Godiya Asma'u tayimata inda suka cigaba da hira nayanda abun zai kasance daga karshe Zaliha tafice tabarta tana planning nata plans din............

****
Tunda Zaliha tafita takoma bangarenta tunanin yanda plans dinta zasu tafi agoben takeyi don daman tafara planning but batayi tunaninta it'll work soon ba daga wayarta tayi tareda kiran wani number sunjima suna magana kafin takashe wani irin guntun murmushi tasaki kafin tazauna kan daya daga cikin seaters din dake parlourn ta aranta tana"inkunsan wata baku san wataba"....
Hope dinta bewuce bayin nan suyi abunda taceba tabangaren Sulaiman din and bangaren su Almustapha kuma she's very sure zuwa gobe she'll ruin their lives for good .....

Wuraren la'asar tasa Lantana takira mata Salma aikuwa tare suka dawo,mika mata wata envelope tayi cikin sauri Salma takarba tana tambayar meza ayi dashi.......
Cewa tayi"sonake kisashi ah dakin Yarima kafin gobe da yanma"........
Ah razane Salma tace"Dakin Yarima fa Gimbiya"...
Gyadamata kai Zalihan tayi jiki na bari Salma tace"wallahi bamu cika shigaba iya Hindatu da iya Jamila ne ke shiga dakin",batareda Zaliha tadamu batace wannan kuma keya dama nidai nafada miki kisan yanda zakiyi kisaka sakon nan kafin gobe da yanma. Salma na yunkurin yin wani maganar Zaliha ta dakatar da'ita tareda cewa tafita tabata guri,hakanan babu yanda ta'iya takoma bangarensu bayan taboye envelop din. Samunsu Rukayya tayi suna zazzaune gurin aikinsu inda Rukayya kecin abinci sekuma su Hindatu daketa hada kayan wankin sashin da alama zasu kai gurin wankau ne....
Hindatu ne tadubi Rukayya tace....
"nikam bance kije dakin Yarima kidauko sauran kayan shi ah cikin basket din kayan wankin nanba?"........
Pity face Rukayya tayi sannan tace"ayya Iya Hindatu zandauko so nake inkarasa cin abincin nan inwanke hannu na kinsan Yarima baison kazanta"....

To dai kiyi sauri cewar Hindatun yayinda take cigaba da raba kayayyakin don daman kowa nashi daban ake wankewa baswa camukawa guri daya,dede nan Salma tashigo gurin Rukayya ne tace...
"Yauwa gama Salma nan kawai taje tadauko mana kar inbata maku lokaci".....

Wani harara Salma tawatsa mata don ita abun duniya ma ya'isheta gashi tatsani yanda su Rukayyan suka samata idanu waitafiye son jiki,cikeda takaici tace"miyene kikecewa inje inyi bayan ke akasaka baniba"........
Iya Hindatu tabata ansa"aikedaman ba'a isa ace za'a aikekiba saikinyi korafi. to kuwa saikinje aidai kinga itadin cin abinci takeyi"........

Salma jitake kaman takama Rukayya da duka amma babu yanda ta'iya,batareda Hindatu tadamu da halin da Salma take ciki ba tace"dakin Yarima zakije kibude basket dinda yake ajiye kananan kayanshi masu datti kidauko munmanta bamu hado dasuba kumadai kinsan Idi ne kadai keyi mashi wanki ah masarautar nan kuma jibi zaitafi garinsu bikinshi shiyasa ma Ummi tace abada wankin kawai"..........

To kawai Salma tace yayinda tajuya tayi hanyar dakin Yariman cikin sauri don kadama su gane halin datake ciki na farin ciki tunsanda taji an ambaci dakin Yarima zataje,lallai Allah nasonta faduwa kuma tazo daidai dazama. Koda tajeta dakin ba'a rufe yake da makulli ba don haka seta tura kawai tashige ciki abunta tarufo kofar da makulli dukdan kada akamata,ko'ina fes fes dashi straight bedside drawer tawuce tareda dauko envelope din tasaka sekuma taciro key dake dauke da room number ajiki kaman yanda Zalihan tace mata tadaura asaman envelope din sannan ta tura drawer din tarufe dukda kofar dakin arufe amma gabadaya ah tsorace take zuwa tayi tadauko kayan wankin sannan tarufo kofar dakin tafice Allah yataimaketa babu wanda yaganta wani irin ajiyan zuciya tayi tana gode ma Rukayya datasa aikinta suka tafi cikin sauki haka takaimusu kayan wankin suka cigaba da harkokin su,su Hindatu sunsan Asma'u tahana shiga dakin Yarima inba Hindatu da Jamilan ba amma kunsan Dan Adam sesuke ganin kaman Rukayya da Salman dayane dasu tunda suma ah Asma'un sukeyima aiki sannan sun zauna dasu so,basu taba tunanin akwai mai iya cutar su Almustapha acikinsu ba tunda duk wani bawa dayakema uwar dakinsa aiki always stays loyal no matter what bare salma daketa kunkuni kan aikin ma ba lallai mutum yataba tunanin she'll do something like that ba...........

Aranar taje tasanar da Zaliha tasaka sakon,murna gun Zaliha kaman zatayi yaya babu abunda take jira kaman gobe tayi dukdama haryanzu su jiddodo basu dawi gareta ba bare su fada mata halin da ake ciki......
*****
Tunda ta'idar da sallar asuba tasuri wayarta kafin tashiga neman contact dinshi,she just wants to send him something special and unique, something that will make him feel loved by her dukdama tushen sakon bewuce yagane cewa tasauko daga fushin bane ba and tanason fada mishi ya ajiye duk wasu schedules dinshi na dare,today is their day!.....

Tunani tashiga yi na mezata rubuta mishi because she's not good at writing love massages ganin batada option yasa tayi deciding rubutamai short massage kawai.......

"Can we meet tonight?"...
"I've a surprise for you"

Bayan tagama rubutawa yafi sau uku tana kara karantawa don setake ganin kaman words din basukai su isarda abunda ke zuciyar ta game dashi ba amma ganin batada wasu dabarun yasata tura mishi kawai.........


Almustapha na bangaren su Afiya dasuka koma ah jiyan(inda Hamida take) yana kara musu karatu yaji wayarsa tayi kara alamar massage yashigo amma sai bai duba ba har seda suka gama karatun har yakoma daki yakwanta yaji gabadaya he's feeling bored gashi shiba baccin yakejiba bare yakoma wannan dalilin yasashi janyo wayarshi yashiga dannata nanne yayi arba da massage dinta aibaisan sanda yatashi daga kwancen dayake ba tsabar abun yazo mishi unexpected,massage from Asma'u and that too early this morning kuma abunda yajima yana yearning for......
Bude massage din yayi yashiga karantawa ahankali harya gama. wani irin lumshe idanu yayi hakanan yanajin wani irin sanyi na ratsa shi ahankali dukda kuwa baisan haduwar tasu ta menene ba sede one thing he's sure of is yau seyaji dalilin fushin nan hakanan dolenta tasauko, yakaranta massage din yafi ah irga because he just cannot believe she wants to talk him yaudin,can he really wait har zuwa daren yau din kuwa?........
Even though bayason yayi admitting cewa yayi kewarta but that's the very clear fact, ahankali yashiga yimata reply.....

"why not now,dare yayi min nisa Asma'u.I'm yearning to see you!"........
Sanda taga massage din seda taji zuciyarta tayi melting lokaci guda hakanan wani bangaren na zuciyar ta nacemata tace mishi su hadu din amma ganin intayi hakan kaman tabata surprise din datake niyan yimashi yasa tace.......

"No se daren kawai".....

Koda yaga reply dinta dora wayar yayi kawai akan chest dinshi yana tunani kala kala hakanan yayi deciding ya kawai hakura harzuwa daren don shi tsoroma yakeji kada tace tafasa don ya lura tazama yar rigima yanzu shiyasa ma yakebinta ahankali..........
****
Tun da gari ya waye Jiddo take neman Karimatu don Lantana ita tasamu jiya da yanma tana tuna mata aikin da Zaliha tasasu din,dakyar tasamo Karimatu ah bangaren da take aiki cewa tayi"Karimatu tundazu niketa nemanki kizo muyi magana don Allah"........

Karimatu dake goge gogen furnitures tace"baki ganin ina aikine,maganar miyene dabazaki fadamin anan ba", don duk ah tunaninta Jiddon tazo matada maganar suje suyi abunda Zaliha tace suyi ne bayan itakuma Allah yagani bazata iya yiba. Kamo hannunta Jiddo tayi sannan tace"Lantana tazo tasameni ne batun wancan maganar kizo mu tattauna wani na iyajinmu anan".....
Kwace hannunta Karimatu tayi tana"nifa bazanyi ba aina fadamiki tun ranar"...
Kai tsaye Jiddo tace"Nima bayi din zanyiba shiyasa nazo gurinki minemi mafita",kallonta Karimatu tayi tanason gasgata zancenta gyadamata kai Jiddo tayi alamar she mean it,batareda wani tunaniba Karimatu ta ajiye towel din da take goge goge dashi acikin bucket kafin tayi hanyar barin sashin,bin bayanta jiddo tayi,seda suka samu wurin da babu mutane sosai kafin Karimatun taja tatsaya tana"to mezamuyi yanzu?".......
Wara hannu Jiddo tayi sannan tace.....
"nima bansaniba shiyasa ma nazo gunki munemi mafita don inmuka yarda Gimbiya Zaliha tasake kiran mu batareda munyi abunda tasamu ba zatayimana abunda bamwa zatone ninasani".......
To mizai hana musamu shi Yarima Sulaiman din mufada mishi halin da ake ciki don shi kadai ne zai iya sawa taki yimana mugunta dazata iyayi kuma kinga inmukayi hakan shizaisan matakin dazai dauka akanta yanda bazata iya zuwa tasamu wasu daga cikin mu ba tace suyimata irin abunda tasamu ba dahar zai iya hadashi da Gimbiya Sumayya",cewar Karimatu din........
Dan shiru Jiddo tayi tana kissima maganganun Karimatu din kafin tace"bakya tunanin hakan zaizama matsala?".......

"Insha Allah bazai zamaba"....
To shikenan semuje musameshin don nima nayi tunani banason abunda zai gurbata rayuwana sabida inada tabbacin indai asirin mu yatonu babu maijin tausayin mu ah masarautar nan,ah to nima abunda nagani kenan wannan karan Karimatu ne tayi magana ...

Atake suka yi deciding zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login