Showing 204001 words to 207000 words out of 235422 words

Chapter 69 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3505

turaren shine yabugi hancinta wanda batamasan sanda talumshe idanunta ba, ahankali yajanyota zuwa jikinshi yayinda atare suka sauke ajiyar zuciya. Cikin cool voice dinshi yace"Mrs Sulaiman"......
Murmushi Itama tayi kafin tacemai cikin rada"Mr Sulaiman".......

Jin yanda tayi maganar seda tsikar jikinshi tatashi,besan sanda yadagota daga jikinshi ba kafin ta ankara taji bakinshi cikin nata seda ya tsotse duk gyaran da lips dinta yasha kafin yakyaleta,kaman zatayi kuka tace ka gogemin kwalliya na,Yar dariya yayi sannan ya kwaikwayi muryarta"daman kwalliyar ba ani akayi maba?" ......

Turo baki kawai tayi batacemai komai ba don tunanin ta daya yanda zataje gaban mutane ahaka,sake janta zuwa jikinshi yayi sannan yace"I'm sorry dear and I love you",likimo tayi ah jikinshi yanata yimata surutu harsuka Isa event center din,haka suka sha Dinner dinsu dukda Sulaiman da Sumayyan bahaka sukaso ba,amma yazasuyi haka Allah yatsara.............

haka akayi kwana uku ana biki sosai ah masarautar dukdama wasu bakin sun fara tafiya. Masarautar batadawo yanda take daba sebayan sati daya, yanzu komai is back to normal sede rashin ganin Asma'u yana tadama Dad da Mai Martaba hankali bakadan ba tareda tunanin halin da take ciki........
Bangaren Almustapha kuwa ba ama magana duk ya rame yazama so silent dama yaya bare yanzu dayasamu dalilin rashin maganar,baya fita ko'ina har fada ma baya zuwa. kullum yana daki tun abun baya damun Ummi harya fara damunta barinma yanzu daya zamanto baya tareda ita shikadai ne ah sashin nashi tunda ita takoma nata bangaren su Afiya ma sunkoma bangaren da Hamidan take wurin yar uwarsu kamar yanda Mai Martaba yabukata...................

Yanzuma Ummin dakanta ne tasako su Hindatu gaba da breakfast dinshi don? sunyi mata korafin bayason cin abinci yawanci insun kawo yanda suka ajiye haka suke zuwa su dauka don kozaici ma to kadan yakeci,tura kofar dakin Asma'u tayi don tajima dasanin yadawo nan dazama su Hindatu nabiye da'ita abaya seda suka ajiye tray din suka fice sannan tadubeshi. Yana zaune kan gadon laptop ne agabanshi yanata danne danne cikin ta,duk ya fada yayi wani iri dashi dukdama yakara haske sakamakon rashin fitan dayakeyi baya shiga rana........

Karasawa tayi gaban gadon sannan tasa hannu tadauke laptop din dake gabanshi kafin tazauna gefenshi tana"Imam bakaga nashigo baneba?"........
Batareda yakalleta ba yace"Ina kwana Ummi"........
Kamo hannunshi tayi cikeda damuwa sannan tace ...
"wai meke damunka Imam,why are you hurting yourself miyasa kake isolating kanka daga mutane,laifi mukayi makane fisabilillahi?"........

Se awannan karan ne yadago yadubi mahaifiyar tashi don aganinshi ko kowa zai tambayeshi miye damuwarshi itabai kamata ta tambaya ba,yakamata ace tariga tasan matsalarshi,sa hannu tayi ah habar shi murya ah raunane tace"Imam talk to Ummi please"........

Besan sanda yajanye system din daga gabanshi ba kafin yagyara zamanshi tareda kwanciya sannan ya daura kanshi akan cinyarta batareda yayi uttering koda word daya baneba, shafa gashin kanshi tashiga yi ganin baida niyar yin magana setace"akan Asma'u ne kake wannan damuwar?"........
"Why Imam?"....
"Is she that important to you?".........

Lumshe idanunshi yayi sannan yace"more than important Ummi, bantaba sanin how important she's to me ba seyanzu,she's my life Ummi,I love her and It'll be difficult for me to live without her tariga taxama wani bangare na rayuwana Ummi,kunemo min ita don Allah", Imam yayi maganar ahankali wanda seda yasa idanun Ummi suka canza launi lokaci guda harma takejin kamar taje tadauko masa Asma'un takawo masa gabansa ko Allah zaisa yadawo asalin Danta data sani,sede me tariga tayi alkawari seta hora shi sosai and this's not enough, infact she's planning on going to Chad with ita Asma'u din tareda Mai Martaba wanda tafiyar tasu cikin weekend mezuwan nanne ayanda ta tsara sede tafison tafara sanar da Mai Martaba Asma'un natareda ita kafin tarokeshi maganar tafiya da'ita din.? ... dakyar tayi karfin halin cewa"Sorry son, Asma'u zata dawo gareka lokacine baiyiba kuma ko ah inatake bazata taba son ganinka haka ba"............
Haka Ummi t aayita rarrashin shi,dakyar ya'iya tashi yaci abinci wanda duk ita ke feeding dinshi kuma ba laifi yaji hankalinshi yakwanta kadan,babu abunda yakai uwa ah duniyar nan........

Honeymoon dinsu Sumayya ko anma bar maganarshi don Sulaiman cewaCewa yayi Asmau batanan baya tunanin zai iya tafiyarnan bayan tuncan dasu ya tsara tafiyar. Mai Martaba yagaji da rashin fitan Almustapha Fada don kullum sede yayita kawo mishi excuses na kanshi na ciwo kokuma baya jin dadin jikinsa wannan dalilin yasa yayita yimasa uzuri gashi Ummi tamatsa mai da batun tafiyarsu Chad inda shikuma kwata kwata baya na'am da tafiyar,tukunnan ma yatafi yaje yayi miyene acan din bayan surukarshi yau fiye da sati ba'asan inda take ba,aikuwa dayazama mutumin banza inyayi haka shiyasa ma tunda Ummi tayi maganar to kawai yace mata batareda yayi mata bayaniba don aganinshi yakamata ace itakanta tasan meya dace dawanda baidace ba dukdama yakanyi mamakin yanda Ummi bata nuna damuwarta sosai gameda batan Asma'un bayan shidin shaida ne kan cewa tafi kowa son yarinyar agidan nan............

Yana cikin wannan tunanin ne yaji sallamar Ummi ah bakin kofar sa amsawa yayi ahankali inda ta karaso cikin dakin fuskarta dauke da kayatatten murmushi gawani ado datashi cikin hadaddiyar leshin ta sewani glowing takeyi don kuwa kallo daya zakayi mata kagane cewa tana cikin hutu da kwanciyar hankali,zama tayi gefen Mai Martaban tareda riko hannunshi cikin soft hands dinta lumshe idanunshi yayi tareda sakar mata da murmushi batareda yashirya ba don kamshin jikinta ma kadai ya Isa ya kawar maida duk wani damuwa dayake tattare dashi barekuma tahada da wannan murmushin nata me tafiya da hankalin duk wani lafiyayyen namiji gakuma shi da Allah yadaura mai sonta mai tsananani......

Wasa take da hannun nashi tana tambayarshi lafiya yake zaune ah daki shikadai bayan kuma yakamata ace yana Fada yanzu........
Dubanta yayi sannan yace"tayaya kike tunanin hankalina zai kwanta Khairiya, "Asma'u is nowhere to be found har yau,babu inda ba anemeta ba amma shiru kakeji iyayenta kuma sunyi mana kawaici dayawa yakamata ace munyi wani abu wurin ganin ansamo ta cikin gaggawa but it seems like ke bakima damuba Dear".......
Sa hannu Ummi tayi ah fuskar Mai Martaba din in a comforting manner kafin tace....
"Asma'u is in a safer hands kadaina daga hankalinka please"........

Tsayawa yayi kallon fuskarta because for now he's very sure something is fishy dubada yanda tayi masa maganar with full confidence,cikeda curiosity yace....

"kinsan inda take ne?"......
Gyada mishi kai tayi
ahankali don tagaji da boyemai zancen dubada yanda yabi yadamu kanshi,sede da mamakinta taga yabata rai lokaci guda tareda sake kaimata wata tambayar..
"Since when Khairiya?".........

Jitayi jikinta yayi sanyi sosai ahankali tadauke kanta kasa kafin tace...
"tun daren ranar da abun yafaru"........
Cikeda bacin rai Mai Martaba yace"why will you do such a thing,kinsan kuwa halin dakika samu aciki,kinkuwa yi tunanin damuwar da iyayenta zasu shiga kikayi wannan abun Khairiya,tashi yayi tsaye yana"unbelievable, this's not my Khairiya"......

Cikin sauri Ummi tatashi tareda kamo hannun shi pleadingly tana..

"here me out Abdulrahman ba abunda kake tunani bane ba,give me a chance I'll explain"......

Kallon ta yayi and suddenly kuma seyaji yarage jin haushinta dubada yanda tayi pity face dakuma fuskar roko, ahankali tashiga yimasa bayanin yanda talura Almustapha baya son Asma'u ada and the reason dayasa ta boye Asma'u din sannan takarada bayan Zaliha ta fallasu nasan yakamata infito da Asma'u amma inason Danmu yasan darajarta Abdul,inason yasan how important she's to his life,inason yasan cewa yana sonta bawai yayita zama da ita hakaba thinking that ita kadai keyi mishi wannan feeling din batareda yayi reciprocating ba,I want Imam to treat Asma'u with respect,I want him to value her and that will only happen se yasan amfaninta ah gareshi and I'm seeing a progress now don Allah kada ka ruguzamin wannan plan din nawa Dear".......

Kallonta yake tunda take magana,yasan maganarta gaskiya ne to amma tayi tunanin halin da dantan ze shiga kokuma tayi tunanin halin da iyayen yarinyar zasu shiga, ahankali yace her parents fa?......
Umminta tasani,tunda naga hankalinta yatashi nakaita gurinta taganta and about the Father shida kanshi yace yanaji ahjikinshi Yarshi is in a safer hands so nasan bazai wani damu sosai ba, jijjiga kai Mai Martaba yayi cikeda rashin gamsuwa kafin yace wannan ba hujja baneba Khairiya kidauko yarinyar mutane we're taking her home tonight taga iyayenta after that kuma we'll decide meye za ayi game da aurenta da Almustapha din amma boyeta bashine solution ba please and shima din zan hadu dashi wato sabida mace ne yamanta responsibilities din dake kanshi kenan yaje yana shashanci......

Ummi dai babu yanda ta'iya dole ta gyadamai kai inda yafice ranshi bace yabarta gurin,daga fitanshi Fadawan suka rufa mishi baya donyi mishi rakiya straight bangaren Almustapha suka wuce suna isa bakin kofar suka tsaya inda shikuma yakarasa cikin sashin Almustaphan baya dakinshi don haka yakoma parlour yazauna tareda ciro wayarshi nan yashiga kiran layin Almustapha din...........

Yana kwance ah dakinta abun duniya ya isheshi,duk ya rame yarasa sukuni yayi wani curpur curpur dashi, tun randa tabarshi yakejin wannan feeling din,the feeling of loneliness bayan kuma gashidai danginshi duk suna tareda shi hakanan suna nunamai so da kauna,kowa burinshi yafaranta mai sede Kash! Komi sukayi ba burgeshi sukeyi ba,duk efforts dinsu is just going in vein sabida bashi da burin dayawuce yaga Asma'u gani yakeyi bashida babban masoyi ayanzu dayawuce wanda zaizo yakawo masa news din yaga Asma'u......
Na'im da Sulaiman sunyi rarrashin amma ah banza,kullum burinsu su kwantar Mai da hankali haka Ummi dasu Hamida ma amma abun ya faskara shikanshi so yake yasamu peace of mind amma ta'ina ma zaifara?....
Bayan Asma'u tariga ta mamaye koina na gangar jikinshi,zuciya dakuma ruhi yarinyar dako rufe Ido yayi ita yake kallo. Lumshe idanunshi yayi ahankali yanajin wani zafi ah kirjinshi tabbas indai haka so yake to lallai batayi mashi adalci ba dabata ankarar dashi alokacin daya dace ba,yana cikin wannan tunanin ne taji wayarshi tashiga ruri dan tsaki yasaki don duk ah tunaninshi su Na'im dasuka saba damunshi ne akullum, yakai sau uku call din na shigowa amma baidaga ba harsai da aka kira na hudun nanne ya hasala yajanyo wayar jiki ba kwari batareda yaduba mai kiran ba yadaga.........
Jiyayi kawai ance....
"Ina parlournka Ina jiranka kazo yanzunnan".....
Se lokacin yagane me maganar,cire wayar yayi ah kunnenshi yana karema sunan mahaifin nashi dake kan screen din wayar tashi kallo kafin ahankali yatashi yana mamakin meya kawo Mai Martaba har bangaren shi awannan lokacin bayan lokacine dayakamata ace yana can Fada tareda mutanen sa, gabadaya bayajin karfi ah jikinsa amma yazaiyi?
Ya isa ma yace ma Mai Martaban bazai fitaba barinma yanda yaji yayi maganar with seriousness,janyo wata brown jallabiyarsa yayi yasaka sannan yafice zuwa parlourn akan babban daya daga cikin royal chairs dake parlourn yayi don haka seya samu guri nesa da mahaifin nasa ah kasa yazauna yana gaidashi"Ina kwana Abba"........
Tunda yashigo Mai Martaba kebinshi da kallo yana mamakin yanda Almustaphan yakoma cikin sati daya dayan kwanakinnan,shifa wai duk yayi masa uzurine kan yana hutawa ne sabida gajiyar biki ashe bahaka baneba, batareda ya amsa gaisuwar tasaba yace ......
"sabida Macene kamaida kanka haka Imam,sabida mace ne yasa kake kin sauke hakkokin dake kanka Imam?", Mai Martaba yayi masa tambayar yana nunashi in desbelief kafin yakarada I love your Mother to the extent dabazan iya misalta makaba,Kai kanka kasan da haka ko?........
Gyada Kai Almustapha yayi kanshi na kasa still inda Mai Martaba baibar maganaba yace""dukda kuwa irin sonda nakeyi mata din hakan baitaba sa na karaya ba,haka kuma baitaba sawa namanta responsibility din dayake kaina ba, you've royal blood within you Imam! So,I expect you to be strong and do what's right tukunnanma me kakeson mutane suce?.....
Daga daura ka karagar mulki harka fara kwalo kwalo,to gaskiyar i won't tolerate this gobe inason inganka ah Fada and banason jin wani unnecessary complains, you better come back to your right senses maganar Asma'u kuwa ba kwanciyan dakake ah daki bane zaisa kaganta you've to show some effort if you do really have feelings for her..........

Almustapha dayakejin kaman ya kurma ihu yace"Abba she's no where to be found annemeta ba asameta ba"........
Dan ba aganta ba se ah tsaida neman nata,anya Imamu kanason yarinyar nan kuwa,lumshe idanu Almustapha yayi yayinda zuciyarshi keyi mashi Kuna don gani yakeyi Abban ma bakar magana yakeyi mishi,inbaha ka ba wace irin tambaya ce wannan bayan shi ganau ne ba jiyau ba kan halin da yakecikin duk ah dalilin Asma'un ne"........
Jin yayi shiru Mai Martaba yace"bakasontan kenan?"......

"No Abba inasonta wallahi,I love her so very much",yanda yayi maganar kadai yagamsar da Mai Martaba amma seyace....
"then fight for your love Son,go out and look for her,make her feel that she's special and then bring her back home yourself bawai kakwanta kana ciwo kamar rago ba, you're a leader and you've royal blood running within you so,act like a king not like a coward",daganan Mai Martaba yatashi tsaye daniyar tafiya bin bayanshi Almustaphan yayi yana kissima maganganun mahaifin nashi dukdama bayajin ko kadan yanada courage din yin yanda yace din.
To Amma yazaiyi?.....
Ya Isa yaja da maganar mahaifin nashi ne,har bakin kofa yaraka shi kafin yakoma dakin Asma'un daya dawo nashi ayanzu da batanan din..........


Adaren ranar Mai Martaba yasaka Ummi gaba batareda kowa yasani ba sukayi gidan kanin Mallam Hudu din inda nanne Asma'un ke zaune. Tunda taji kofar na kara tadubi Rukayya tace"tashi kije kibude kofar naji kamar ana sallama"......

Cikeda ladabi Rukayya tatashi tayi hanyar kofa don aiwatar da abunda Asma'un tasakata inda tayi arba da Ummi da Mai Martaba sekuma Mallam Hudu dake biye dasu abaya, murmushi Ummi tasakar mata sannan tace Ina Uwar dakin naki Rukayya?.......

"Tana ciki", Rukayyan taba ma Ummi amsa cikeda ladabi,to kije kice mata tayi baki kinji....
Gyada Kai Rukayya tayi sannan tayi ciki da gudu don tabbas batamanta yanayin databar Asma'un ah parlourn ba,bawasu suturar kirki bane ah jikinta dahar zata iya ganin surukanta awannan yanayin.....

Jin gudun Rukayyan ne yasa Asma'un tashi daga zaunen da take tana tambayar ta ko Lafiya, Rukayya na haki tace Mai Martaba da Ummi sunzo sunce acemiki kinyi baki ware idanu Asma'u tayi sannan tayi daki aguje Itama tana kice sushigo mana, Ummi dake gaba wanda har sun iso cikin parlourn tadan saki dariya tana gamu munshigo Daughter inda Mai Martaba da Mallam Hudu suka samu gu suka zauna Ummi kuwa tabi bayan Asma'un tanacewa Rukayya taje takawoma su Mai Martaba ruwa susha. Samunta tayi ah dakin harta burma katon hijabinta tana shirin fitowa murmushi Ummi tayi tana wannan zumudin dukna ganin Mai Martaba ne kokuma kokuma na.......... ne don nidai duk zuwana ba'a wannan dokin", Ummi takarashe maganar cikeda zolayar Asma'u, lokaci daya kunya ta lullube Asma'u seta samu kanta da jan lufayanta tana lullube fuskarta yayinda cikin siririyar muryarta tace"Ina wuni Ummi".......

Dariya Ummi tayi tareda kamo hannun Asma'un tana"Lafiya lau Daughter,how have you been doing?"......
"Fine Ummi".....
To Masha Allah cewar Ummi kafin tajata sukayi parlour Asma'u zuciyarta se racing yakeyi don duk ah tunaninta da Almustaphan akazo tunda har Ummi tayi mata zolaya,she's yearning to see his beautiful face,sede da mamakinta babu shi acikin ahalin parlourn hakanan kobayan data gaidasu tayita saka tsanmanin ganin kozai shigo daga baya amma shiru,haka Rukayya takawo musu kayan motsa baki wanda duk Mallam Hudu ke musu wannan dawainiyar tunbayan zuwansu gidan,basu wani shaba sema duban Asma'u da Mai Martaba yayi cikin zolaya"Daughter kika buya abunki ko?".......
Cikeda kunya tace aa Abba,dariya yayi kafin yace zamu tafi gida yanzu kam ko,seta kasa bashi amsa dukda kuwa babu abunda tafi so ayanzu dayawuce taganta ah gidan Jin tayi shirune yasa yace"ko gurin Daddy da Ummi kikeson zuwa?"....

Gyadamishi Kai tayi ahankali dn kuwa tabbas tayi kewarsu suma, murmushi yayi irin nasu na manya sannan yace...
"Jeki shirya kayan ki semukaiki gida kiga su Daddy ko"........
Cewa tayi to kafin takoma dakin sede already harsu Ummi da Rukayya sunfiddo da akwatinta da yan kayayyakinsu,nan aka dibi kayan akasaka ah mota godiya Daddy yadinga ma Mallam Hudu yana Allah yabar zumunci......
Mallam Hudu yace"Babu godiya ah tsakaninmu Mai Martaba, Almustapha is like a Son to me besides Asma'u iyalinshi ce inban kulada itaba wazai kula da ita?".........
Murmushi Mai Martaba yamai kafin suka dunguma sukayi gidansu Asma'u dukda zuwan nasu is un announced amma sunsamu tarba mekyau dede misali kuma ma Allah yataimaka Daddyn na gari. Asma'u tunda tashiga bangaren su su Munira suka taho da gudu suka dale jikinta suna ihun"Ummi ga Adda Asma'u tadawo"......

Ummi dake ninke kayan Autanta da aka debo daga shanya da yanman nan batasan sanda tasaki na hannunta ba tafito da sauri tanason tabbatar da zancen su Munir din ,tsayawa tayi abakin kofar dazai sadata da parlour daga dakinta tana kallon ya'yan nata so lovingly, she's aware yarta is safe and sound with Ummi amma ganinta ah yanzun seyasata sakejin wani irin dadin da kwanciyar hankali, ahankali Asma'un tasaki kannenta kafin tayi inda mahaifiyar tata take emotionally tace "Ummi!".....
Sekuma tafa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da jikinta tareda fashewa da kuka, rungumeta Ummi tayi tana tapping bayanta"it's okay Dear,stop crying everything will be alright insha Allah"...
Kan kacemai bangaren Ummi yacika da duka yaran gidan,sewani nannan da'ita sukeyi daga mece mata"where have you been,meya faru dake and suwaye suka taimake ki"...
Seme cemata
"Miyasa baki kirani ba,kinmanta kinada Yaya Aliyun ki komi?".......
Sekuma Mubaraq me warning in the end"inkika yarda kikasake making decisions without informing any one of us I'll make sure I break your bones", murmushi take ayayinda hawaye kebin kuncinta hakanan batasan sanda tashige jikinsu dukaba tana gode ma Allah daya bata yayu masu sonta da kaunarta,atake suka Kira Asiya da tuni takoma Kaduna suna fada mata dawowan Asma'u din, ihun murna tafasa awayar tanama Allah godiya kafin Itama tashiga yin nata tambayoyin sede duk batasamu amsarsu ba don haka tashiga nata fadan Itama kan tafiya datayi batafada ma kowa ba,haka suka Kira kauyen Batagarawa ma suka sanar da baffansu kan afada ma Hajja don gabadaya tabi ta tada hankalinta Itama aikuwa ana sanar da'ita take tasa Baffa yakira wayar Aliyun sannan tace ahadata Asma'un,ana hadasu ah wayar Kuma se dukansu suka fashe da Kuka dakyar Asma'u ta'iya kokarin tsagaita nata kukan kafin tace"Hajja to miye abun kuka bagashi nadawo ba".........

Cikin kuka Hajja tace"don ubanki shine zaki tafi konema na bakiyi ba,inama laifin kice mutafi tare fisabilillahi"....

Asma'u tasoyin dariya amma seta daure tace"kiyi hakuri Hajja bazan sake ba"........
Nan Hajjan tace mata Itama gobe zata shigo Zarian in Allah ya yarda daga haka sukayi sallama....

Acan parlourn Daddy kuwa bayan ankira Ummi da Mommy suka gaggaisa kafin Mai Martaba yafada musu duk yanda akayi bai boyemusu komai ba da Ummin tayi sannan yakara da basu hakuri inda Itama Ummin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login