Showing 63001 words to 66000 words out of 235422 words

Chapter 22 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3486

yasan labarin ta tadago tana kallon Sulaiman din,kafin tace nagode amma dababu komai in Sha Allah komai zai wuce......
Aa 'yata baza ayi haka ba,zamuje gidan dake nizanyi magana da mahaifinki......
To kawai tace mishi dukda kuwa bawai idea din tayi mata baneba,ganin kamar akwai damuwa ah fuskarta yasa Dad cewa kada kidamu nizanyi magana da mahaifin naki inmunje gidan dazamu barki nan ma don dai bamusan gidan baneba...
To kawai tace musu kafin tace barita shiga tafito,ba ajima ba tasamo su ah mota suka wuce gidansu tanayi musu kwatance, tabbas taga Almustapha amma ko kallo be isheta ba,har kofan gidansu tukunnan sukayi parking Dad ne yacema Sulaiman yaje yafada ma mai gadin ya isar cikin gida Daddy nada bako........
Sanda Sulaiman yasamu Mai gadin cemasa yayi ai Daddy yayi tafiya can kauye amma gobe zai dawo..........
Nan Sulaiman yadawo ya isar da sakon,cikeda tausayin yarinyar Dad yace yazamuyi 'yata mahaifinki bayanan.......
Idanunta dasuka ciko da kwalla tashiga gogewa sannan tace "sede inya dawo din".....
Murmushi Dad yayi sannan yace bazaku gaisa da mutanen gida ba?....
Jijjiga Kai tayi wannan Karan hawayen sun kasa tsayuwa sannan tace aa seya dawo kawai,to kawai Dad yace sannan sukayima Mai gadin sallama suka juya suna hanya ne Dad yace zamu kwana ah gida ko sabida goben semu wuce direct.......
Itadai shiru kawai tayi batareda tace komai ba sabida Dad yayi mata kwarjinin dabazata iyace masa aa ba,haka suka kama hanya suka koma masarautar........
Tunda suka sauka ah motar Amira tarike hannunta gam gam harsuka shiga cikin sashin nasu dagudu Sumayya tazo ta rungumesu jikinta sanye da doguwar riga wanda da kadan tawuce gwiwarta sede rigar bata kamata ba kuma bakaramin kyau tayi mataba,ya akayi kuka jima haka nayi kewarku............
Batakai ga rufe bakiba idanunta suka gane mata Asma'u dake tsaye abayansu tana wasa da hijabinta, ahankali tafurta "wow Yaya Sulaiman wacece wannan kyakyawar please, takarashe maganar tana karasawa gaban Asma'u......
Hararan ta yayi shi Sulaiman din yana karema kayan jikinta kallo"yanzu wannan amatsayin kaya kika daukeshi Sumayya?"......
Turo baki tayi gaba tana "Allah Daddy kashiga tsakanina da Yaya Sulaiman yasaka min ido", murmushi Daddy yayi sannan yace tsakaninku nikinga tafiyata ma,kyale Sulaiman din tayi sannan tadubi Amira,don Allah yasunanta..
Asma'u sunanta, rungume ta Sumayya tayi sannan tace I like you, will you be my friend?....
Jinjijiga Kai Sulaiman yayi yawuce su yana"unbelievable, yarinya se shegen shishigi"......
Gyada mata kai Asma'u tayi tana faking smile,itama setaji Sumayya takwanta mata arai.........
Kama hannunta Sumayya tayi suka wuce ciki dukansu tana muje kigaisa da Ummi da Mom suna cikin gida,I know they'll like you as well....
Itadai binta kawai tashigayi, Almustapha dake bakin kofar makeken parlourn yana ganin duk abunda ke wakana,seda sukabar gurin sannan yasaki tsaki"he don't actually know what she's up to,miyasama zata yarda tabiyosu,meye alakarta dasu dahar zata yarda ta kwana gidansu,wata zuciyar kuma cemasa take anya yarinyar nan ba mayya bace ba......
Yana cikin tunanin nan ne yaji ankama hannunshi, ahankali yadaga idanun shi Dad ne,ka karaso mana son banmanta kanajin yunwa bafa so let's eat I'm hungry too Dad yakarashe maganar yana dan taba cikinshi, murmushi Almustapha yayi sannan yabi bayan Dad din....

Hardakin Mom Sumayya takaita tana Mom nayi sabuwar kawa, she's so beautiful tazo tagaida ki......
Murmushi Mom tayi yayinda Asma'u tashiga gaidata,amsa gaisuwar Mom tayi azuciyarta tana yaba kyaun yarinyar don already daman Dad yace mata sunzo da yarinya zemata bayani daga baya zata kwana anan......
Bayan sun gaisa da Mom ne Mom din tace kinkaita gurin Ummin ku?......
Aa yanzu zamuje,to kaita tagaidata sekuje daki tahuta ko kafin anjima......
Kama hannunta Sumayya tayi sukayi dakin da aka tanadar ma Ummi,dakin fes fes yake agyare gawani kamshi dake tashi sede batasan dalili ba tunda suka doshi hanyar dakin takejin zuciyarta na dukan uku uku, Ummi nakwance kan royal bed, Amira ne kezaune gefenta tana bata ruwa tana sha,karasawa Sumayya da Asma'u sukayi yayinda Asma'u ke kallon fuskar Matar setaga tanayi mata kama da Almustapha sosai,riko hannun Ummi Sumayya tayi tana dan daga dayan hannunta "hello Ummi,nakawo miki new friend dina I hope you'll like her",Sumayyan takarashe maganar idanunta sun ciko da kwallah don sosai takejin tausayin Matar ace mutum na kwance ba lafiya tsawon shekaru haka.......
Kissing hannunta Sumayya tayi sannan tace"I hope you get well soon,I cannot wait to hear your beautiful voice kaman nasu Amira"......
Amira dake gefe ne tace Asma'u she's our Mom,Ina wuni Asma'u tagaida ta,jin shiru takuma sake gaidata wannan karan Amira ne tace"Bata magana amma nasan tajiki,zan iya ansawa on her behalf?", Amiran tayi maganar cikeda zolaya yayinda idanunta na zubar da kwallah, murmushi Asma'u tayi Itama nata idanun suna shirin tara kwalla tacema Amira eh.....
To lafiya cewar Amiran tana kokarin rike hawayenta......

*****
Dayanma Anty suwaiba tadawo gida agajiye,Aisha dake zaune tana kallo tace sannu da dawowa Anty suwaiba.....
Yauwa Aisha sannu,ina Asma'un badai tana nan tana aikin kukan nataba?.....
Murmushi Aisha tayi sannan tace a'a Aunty Suwaiba aima takoma gida yanzu nikeson fita insiyo kati inkira Ummi inji inta Isa gidan....
Cikeda mamaki Anty suwaiba tace,ta tafi kuma shine batayimin sallama ba,kenan baban nasu yasauko?.....
Aa Anty suwaiba su Yaya Sulaiman ne da Uncle dinsu suka dauketa kan zasuje subama Daddy hakuri.......
Sakan baki Anty suwaiba tayi sannan tace da izinin wa,agidan nasu ansan zasuje ne.....
Aa cewar Aisha din,tsaki Anty suwaiba tayi sannan tace yanzu ke kina da tabbacin can din sukaje miyasa kuna abu ba tunanine aiko kirana kyayi Aisha kifada min.....
Riko hannun Anty suwaiba Aisha tayi sannan tace kada kidamu Anty ninasan tana hannun kirki I trust Yaya Sulaiman Kuma hardasu Amira fa...
Janye hannunta Anty suwaiba tayi sannan tace nikam tashi kisiyomin kati inkira Ummin natan ban isa ba amanan yarinya aka banifa.......
Dariya Aisha tayi sannan takarbi kudin kati tafice don zuwa siyo recharge card din..........

****
Sulaiman tundasuka idar da sallah yawuce hospital don karban DNA report din kaman yanda akace sudawo dayanma, addu'ar shi daya Allah yasa komai yatafi daidai kada asamu matsala dukda kuwa yanada tabbacin haryanzu Magajiya bata da labarin komai sabida biki yashige mata gaba,he just don't want her to know everything se aikin gama yagama because he fully know his mother she can go to any length ganin ta ruguza komai.......
Sanda ya Isa hospital din yakarbi DNA report din yafito yashiga mota yayi gida,bangaren Mai Martaba yawuce nan yasamu Dad zaune gefen Abban, gaishe da Abban yayi da jiki sannan ya dauko envelope din yamika ma Dad,kallon envelope din Dad yayi kafin yashiga ciro result din.........





Vote
Comment
Share!.....
[3/23, 5:29 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*..

*Zeeneert*@wattpad....

*page 19*


Dubawa yashigayi cikin nutsuwa yayinda lokaci daya fuskarshi tacika da annuri yana kuma hamdala azuciyarshi, Sulaiman dake gefe ganin Dad din yayi murmushi seyaji hankalinshi ya kwanta don shima daman beduba ba yafison yakawoma su Abban tukunnan ayi komai agabansu, Dad ne yamika ma Abba envelope din sannan yace it's now clearly written that su 'ya'yanka ne so,anawa tunanin wannan enough prove ne basai ankuma wani bincike ba.......
Karba Abba yayi yagani sannan yayi shiru nawasu dakiku don bemasan wani irin feelings yakeji aranshiba bare har yasama abun fadama su Dad din,abu dayane yasani ya yarda da Sulaiman da Yayanshi bazasu taba yimasa karya akan abu mai mahimmanci hakaba..........

Maidama Dad envelope din yayi sannan yace keep it with you and alhamdulillah with you nayi realizing wasu daga cikin zuria na dasuka dade baswa taredani,yaran dasuka jima basu samu gatanaba dakuma soyayyataba,I really feel blessed to have you Yaya Almustapha and in Sha Allahu daga yau zanbasu hakkinsu kaman sauran yan uwansu bazan nuna musu banbanciba dukda kuwa abunda mahaifiyarsu tayi mini,I believe it's not their fault laifin wani baya shafan wani,don haka zanrikesu dakyau and I'll give them the love they deserve.........
Ahankali Mai Martaba yadubi Sulaiman dake gefe yana ta murmushi yarasa inazaisa kanshi don farin ciki"mobbu honduko(rufe bakin) Babana",cewar Mai Martaba yana smiling dariya Sulaiman yayi sannan yace Abba Allah kadai yasan irin farin cikin danake ciki yau.........
Murmushi kawai Mai Martaba yayi sannan yace kaje kasamu Sarkin gida kace masa inason asanar da duk wani ahali nacikin masarautar nan kama daga kan bayi har sauransu kowa asanar mishi cewa inason yin sanarwa karfe takwas nadare..........
Gyadakai Sulaiman yayi sannan yatashi yafice, Dad ne y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????adubi kanin nashi sannan yace sanarwan miyene haka?......
Gyara zama Abba yayi sannan yace batun samun ya'yana I want to ensure that sunsamu equal right like the others......
Cikeda jin dadi uncle Almustapha yace naji dadin wannan decision din naka, I'm so proud of you sede bakayi maganar crown prince ba,yanzu kaga Almustapha ne babba.....
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace ba girman muke dubawaba yanzu Yaya, capability muke dubawa tukunnan shi Almustapha din ina yasan kan gidan sarauta daduk wani aiki daya kamata ayishi,sannan na biyu Almustapha is not a good boy for my people countless times ankawomin karansa anan Yaya,taina kakeson infara zaban shi ah matsayin shugaba fisabilillahi,innayi haka banyi adalci ma mutane na ba sannan abuna karshe danake dubawa shine Sulaiman anriga anjima da kwadaita mishi sarautarnan banason abinda zaikawo gaba tsakanin Ya'yana ni kaga dalilaina,so inaga mubar maganar nan we should focus on how to make that boy a better person tukunnan sabida mahaifiyarsu tariga ta lalatasu...........
Gyara zama Dad yayi sannan yace koma miyene shine yakamata yakarbi sarauta bayan kai and believe me he's capable enough,just give him a chance batun Sulaiman kuma shidakanshi yanuna bayaso......
Dan shiru Mai Martaba yayi kafin yace to shikenan amma se bayan bikin yaran nan zamuyi zama da mutanen fada bana yanke hukunci direct senaji opinion dinsu.......
Murmushi Dad yayi sannan yace Allah yakaimu lokacin,su waziri naji suntafi Maiduguri ko?...
Eh suntafi bayan laasar dinnan sune zasu halarci daurin auren su Sulaiman acan din cewar Abba yayinda Dad yace Allah yasanya alkhairi yakaisu lafiya yakuma dawo dasu lafiya.......
Amin ya Allah, daganan Abba yace i want to meet them now, kaini gurinsu Yaya.....
Kama hannunshi yayi yatayashi tashi yana "Abdulrahman tunanin me kake sama ranka haka duk kabi ka tsofe",dariya Mai Martaba yayi sannan yace kaidin naga Saurayine ai Yaya.....
Rankwashi Dad yake niyar kaimishi Mai Martaba yayi saurin kaucewa yana yar dariya kafin Dad din yace"zancen gaskiya kafini tsufa"....
Ah ido ba amma ai kafini shekaru Yaya kuma wahalar mulki ma kadai ta Isa ta tsofar dani, murmushi Dad yayi sannan yace to tsoho Abdulrahman.....
Murmushi kawai Abba yayi don yalura Yayannashi neman tsokanarshi yake son yi.......
Haka suka shiga takawa harzuwa bangaren dasu Dad din suke dukda kuwa dogaraye sunyi niyar binsu Abba yace suyi zamansu he's going alone......
Tunda ga waje Abba yalura babu dogaraye dakuma bayi ah bangaren,cikeda mamaki yadubi Yayan nashi, Yaya yahaka Sulaiman befadama bayi akwai baki anan bane ba, I'm not seeing any of the slaves here meyasa?.....
Cikeda rashin damuwa Dad yace kamanta ni ne Abdulrahman,I want a free life banason takura shiyasa nacema Sulaiman banaso koda yaturosu.....
Tsayawa Mai Martaba yayi sannan yace"to ai yanzu ah gidan nan kake wani free life ne Yaya,taya Madam ayyuka zasuyi sekuma masu gadinku tako ina for security reasons,don Allah kayarda da wannan abun in ansake turo su kada ka koresu please"......
Murmushi kawai Dad yayi sannan ya gyada ma kaninnashi kai dede nan suka isa cikin parlour din...
Guje guje sukeyi ah tsakiyar parlourn kaman wasu yara kanana,Sumayya narikeda apple ahannunta tana gutsura tana musu gwaliyo,"duk maiso yaje yadauko,ni banbadawa"......
Amira ne data gaji dabin Sumayya tace"koni mayyace na hakura wallahi,takarashe maganar tana zama kam kujera"......
Afiya ne tayi sa an kamo Sumayyan nan tashigayi mata cakulkuli suna dariya bashiri Sumayya tasaki apple din yafadi ah kasa yashiga gangarawa dagudu Afiya tasaketa tabi apple din tana tonikam yau nacika mayya dansainaci, daukar apple din tayi ahankali sakamakon ganin kafafun mutane biyu datayi gabanta wanda dayan kafanshi na sanye da takalmin sarauta me tsada da kyau wanda ko tantama babu na sarki ne inko banashiba tona Yarima Sulaiman ne sede shidin tariga da tayimishi sani inba occasionally ba baicika saka kayan sarauta ba,jitayi gabanta na dukan uku uku yayinda ahankali tatashi daga sunkuyon datake, Dad da Mai Martaba tagani dasuka tsaya kallonta suma fuskar Dad dauke da murmushi yayinda na Mai Martaba takasa fassara expression na fuskarsa,jatayi da baya ahankali sannan tashiga gaidasu cikin rudani....
Amsawa Dad yayi yayinda take idanun Mai Martaba yaciko da kwalla,koyanaso bazai iya denying cewa Afiya ba yarsa bace, she's his Daughter one single look yayi mata yagane hakan sabida kaman datakeyi da Sulaiman dama shikanshi hannunshi na shaking yariko hannunta"My Daughter?"....
Itama idanunta suncika da kwalla tashiga gyada masa kai, ahankali yarike hannunta kamkam suka karasa cikin parlourn don daga nesa yake hango twin sister dinta donkuwa ga kama nan already yasan Sumayya don dazu taje gurinshi sun jima tare,hada Amira da Afiya yayi ya rungumesu ahankali yakejin wani irin son su nashiganshi tareda tausayin yasukayi rayuwa without him,mesukayi going through without his support tunda shiba jiyau bane shi ganau ne na shari'ar da akayi da Almustapha kan yayi sata,what does that means suna rayuwar talauci kenan shiyasa yashiga harkar sata,anya ze iya forgiving kanshi for living them all alone kokuma Khairiya ne bazai yafemaba na abunda tayi mishi wanda hakan yasashi rabuwa da yayanshi.......
Sakinsu yayi ahankali cikin murya me rauni yace"forgive your Father please"........

Amira dake hawayene tace"wai yau nine mahaifina yake rungumata haryana neman yafiya na,maizai hanani yafe maka Abba,i really need you bansan miye dadin uwa ba bare na uba tunda na taso,tunda nayi wayau I always have the urge of being loved by a Father and Mother sede bansamuba,goge kwallarta tayi ahankali sannan tace Abba inban yafe maka ba ta ina zansamu wannan gatan barema by Allah bantaba rikeka a raina ba ko Inyi fushi dakai kullum tunanina shine wannan jarabawa ce garemu and in Allah ya yarda watarana zezama labari, Amira takarashe maganar tareda sake rungumar Mai Martaba tapping bayanta yashigayi yana lallashinta ahankali haka Afiya ma....

Sumayya ma karasawa tayi gabansu sannan tayi pouting mouth dinta"Abba nifa baza'a rungumeniba"......
Dad dake gefene yace"when will you grow up komai ke wasa kika dauke shi?"...
Amira da Afiya ne suka dan buda mata yayinda Mai Martaba yace"dagaskiyarta kyaleta Yaya,inbata rungume niba wazata runguma?".......
Cikeda jin dadi tashiga click din rungumar tana I love you Abba.......
Shafa gashin kanta yayi sannan yace "I love you more my darling Daughters".......
Asma'u dake gefe tana zaune tun su Sumayya na wasa harzuwa yanzu tatashi ahankali dan seyanzu tagane bekamata tana zaune cikin suba, family talk sukeyi and she should not be involved tashi tayi ahankali tafita ah parlourn dukda batasan meyake faruwa ba tayima su Afiya murna atleast they're reuniting with their Father,goge kwallarta tayi yayinda ta tuna kalaman Amira na tataso batasan gatan iyayeba, atleast ita tagode Allah ma tayi nata rayuwar cikin gata da iyayenta yanzu ne kadai tasamu misunderstanding dasu and tana fatan yazo karshe in Sha Allahu wata zuciyar kuma tace mata that means Ummin su Afiya is sick for this long,meke damunta kenan dede lokacin ta iso kofar dakin Ummin jitayi ta bugu da mutum dasauri takoma baya tana subhanallahi, I'm really sorry kasa rufe bakinta tayi ganin wanda ke gabanta saurin dauke kanta tayi sannan ta raba ta gefenshi zata wuce janyota yayi yadawo da'ita gabanshi yana binta dawani mugun kallo janye hannunta tayi daga rikon dayamata cikin sauri zata sake tafiya yasake fizgota"why do you keep following me?"........
Wani harara ta daka mishi azuciyarta tana lallai wannan yacika dan rainin wayau,afili kuma tace "inma nabiyo wasu aibakai nabiyo bako?"......
Cikeda rashin damuwa yace"they're my family don't you even think of hurting them"......
Batareda tacemai komaiba tawuce tashige dakin Ummin don ita tarasa suitable answer dazata bashi taji dadi aranta,meke damunshi why will he even think that she'll hurt his family......
Shiko yaji haushin shariyar datayi masa don haka yajuya zaibita seyaji Dad yakira sunansa, ahankali yajuya bangaren Dad din sannan yace na'am,arba yayi da fuskar Mai Martaba.......
Kallonshi Mai Martaba yayi sannan ya ware mishi hannu alamun yaje gareshi,dauke kanshi yayi sannan yajuya ahankali yabi ta back door batareda yace musu komaiba cikeda defeet Mai Martaba yace"he's different from them, he's older than them daman nasan it'll be difficult for him to forgive me,sede nima I'm just trying to accept him sabida yazame min dolene amatsayina na ubanshi bawai don Ina alfahari da halawayensa bane,duban Dad Mai Martaba yayi sannan yace I'll introduce them tonight convince him to come to the venue please Yaya",yana karashe maganar yajuya yatafi, jijjiga kai Dad din yayi sannan yabi bayan kanin nashi......
Tanaganin abunda Almustapha din yayi sede kwata kwata bataji dadin abunda yayima mahaifin nasa ba koda kuwa meyamasa, ahankali takarasa jikin gadon da Ummin ke kwance idanunta bude tana kallon silling sede takan dan kyafta idanun, murmushi Asma'u tayi sannan takalli wheel chair din Ummi dake can gefe ahankali tajanyo shi sannan cikin dabara ta daga Ummi tadaurata kan wheel chair din dawowa tayi gabanta tareda cewa"Ummi zamuje musha fresh air awaje I hope you don't mind?".....
Tsayawa tayi kozata samu ansa daga Ummi din amma shiru ko motsi Ummin batayiba,jiki ah sanyaye taja wheel chair din harsuka bar dakin ta backdoor tabi don dazu taleka tahango wani guri kaman lambu daga wani bangare and gurin is so silent,tura wheel chair din tadingayi har suka isa lambun shiga sukayi sannan ta samu wani karkashin bishiya dataji yanada sanyi gakuma iska me dadi dake kadawa tsaida wheel chair din tayi sannan taciro dankwalinta tashimfida agaban Ummi tazauna tana sauraron yanda tsuntsaye ke shawagi dakuma kuka ko ina agurin fes yake,kallon fuskar Ummi tayi ahankali sannan cikin kakkausar muryarta tace"I hope you're feeling okay here Ummi,naga dakin is so silent and you were all alone shiyasa nayi deciding infito dake kisha iskan duniya,I know you're sick and can't walk on your own but we're here for you right?,kinada right din yin yanda kowa keyi,you should know what's going on in the world as well, inafatan banyi laifiba tayi maganar tana sunkuyar da kanta dukda kuwa tasan ba ansa zata samuba"...... ...
Sunfi minti goma shabiyar shiru ahaka can ta tashi tsaye tana dan karema lambun kallo daga tsaye idanunta ne suka gano mata bishiyoyin tangerine da Guava duk sun nuna wanda tundaga inda take take hango yanda suka canza kala.....
Cikeda jin dadi ta kalli Ummin"Ummi barina kawo mana abun motsa baki,batajira cewartaba tayi gaba seda taciro da dan yawa sannan tadawo tawanke bakin wani tiyo dataga ansa ma wata bishiya ruwa na zuba,zubasu tayi cikin hijabinta sannan tazauna gaban Ummin....
tashiga bare tangerine din tana bama Ummi din da tayi tunanin bazatasha ba setaga tana sha kuma,yafi rabi tabata tanasha kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login