Showing 6001 words to 9000 words out of 235422 words

Chapter 3 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3537

din bakaramin kuka yayi ba ranar sabida irin son da yakema kaninshi Allah ne kadai yasani,duk wani abu dazai bata mishi rai baso yakeyiba jin yaron yake har cikin ranshi don haka ya daukar ma kanshi alkawari tun ranar babu Mai mulkar garin Zazzau bayan mahaifinsu inba Abdulrahman ba don haka sanda yagama junior secondary school dinshi yadage yanason tafiya Madina wata Islamic school karatu anyin gwagwarmaya kafin Mai martaba ya yarda aikuwa tunda Almustapha yatafi besake waiwayen gidaba seda yagama secondary school sannan ne yace yanason yakarasa karatunshi ah waje...... Mai martaba yalura Almustapha bayason karatu ah gidane kwata kwata don haka seya kyaleshi shikuma Abdulrahman duk karatunsa agida yayi kama daga primary har secondary school sannan yakanyi participating wurin taimakon mahaifinsa halarta wasu abubuwan dakuma ziyarta garuruwa dakuma solving problems na talakawansu in the absence of his Brother wannan dalilin ne yasa kowa yafi sonshi Kuma suke jida shi ahaka har yasamu gurbin karatu ah jami'ar Ahmadu Bello wanda alokacin ba'a jima da budetaba sosai yamaida hankalinshi kan karatunshi Kuma hakan behanashi cigaba da ayuukan dayasaba ba.....

Sanda Almustapha yagama kammala karatunshi yajona Masters Mai martaba har America yaje don dawo dashi amma fir yaki yanuna karara shifa bazai dawo ba indai har zaa matsa masa kan maganar sarauta......

Bakaramin tashin hankali da bacin rai mai martaba yashiga ba sannan yace babu shi babu Almustapha sannan duk wanda yasan yana da dangantaka dashi to yatabbatar ya yanke da Almustapha tunda shida ya haifeshima ya yafeshi hankalin Zuwaira bakaramin tashi yayiba da shikanshi Abdulrahman din, yana mamakin miyasa Yayanshi zekai wannan gandun sede dukansu babu wanda ya Isa ya karya dokan Mai martaba sabida umarni ne daga gareshi sedaga bayane jakadiya take fadama Abdulrahman din Almustapha yayi sacrificing throne dinne for him tunda yalura yanaso Itama saudaya yataba fada mata wanda hakan yasamu asaline sabida irin shakuwarsu,duk wata shawara awurinta yakenema, bakaramin kuka Abdulrahman yayiba sannan yaso fadama Mai martaba amma jakadiya takisam tace amana ne Almustapha yabata shidinma don ya cancanta yasani ne shiyasa tafada mishi haka Kuma inhar Yayanshi na iya yimishi haka mezai hana yacika burinshi tunda talakawama shi sukeso ba wansa ba dakyar yabar maganar, Mai martaba kuwa tunda yadawo daga America hope dinshi kan Abdulrahman yakoma wanda shikuma Abdulrahman din be zuba mai kasa ah idoba ahaka yakarasa karatunshi sannan akafara maganar nema mishi auren Magajiya yar gidan waziri dukda dai bawai yanaso bane sede bazai iya duban mahaifinshi yace bayason zabinshiba ahaka akayi auren sannan suna zaman lafiya da Magajiya sede akwaita da mulki da isa gata dason sarauta batada sassauci ga bayinta kwatakwata bata daukesu abakin komai ba,laifi kadan bawa zaiyi ayi masa hukunci metsauri ashekarar aurensu tasamu ciki wanda akullum bata dawani buri daya wuce taga ta haifi 'Da namiji wanda zai gaji sarautar zazzau ahaka har cikin yacika wata tara akazo gandun haihuwa sekuma Allah da ikon shi yabata santa leluwar budurwa bakaramin bakin ciki taji ba don bahaka tasoba taso ace ita tahaifi air to the throne dukdama ita kadaice Matarsa sede tasan gidan sarauta yanzunnan se ah matsa ya kara aure haka ta rungumi yarta tanasonta dukda kuwa ba macen taso haihuwa ba amma ai 'da 'dane sannan wahalar haihuwar duk dayane Gimbiya HUMAIRA nada shekara uku Allah yasake bama Magajiya wani cikin wannan karan murnar tafi takowanne lokaci don kuwa kowa yana tsanmanin za ahaiho namijine sede Allah da ikon shi batasamu 'da namijin ba seta Kuma haihuwar mace Halima,tundaga wannan lokacin Magajiya tafara shige shige don aganinta zama be ganta ba inbata samu 'Da namiji ba. bayan shekara biyu se Allah yasake bata ciki wanda alokacin bokanta ya tabbatar mata cewa 'Da namiji zata haifa sede Allah dayafi komai seyabata mamaki tasake samun 'Ya mace kuka kam tayishi ranar kaman zatayi yaya sannan tacima boka mutunci don aganinta yacuceta yayi mata karya ahaka tacigaba da rainon 'Ya'yanta mata wanda tun tasowarsu takoyamusu rashin daukar Dan Adam da daraja don kuwa bayi ba ahannun Magajiya kadai suke wahala ba harma ah hannun 'ya'yan Magajiya alokacin ne kuma Allah yadauki ran sarki Sulaiman adalilin wata yar ciwo dayayi na kwana biyu wanda yazo da ajali tunda yafara rashin lafiya yakecewa anemo masa Almustapha,acemasa ya yafemasa duniya da lahira sede kash Allah beyi haduwarsuba..... tabbas anyi rashi bama agarin Zazzau ba kadai agabakidaya kasar Nigeria kowa ya jijjiga da rasuwar bawan Allan,haka aka yimashi sallah aka kaishi gidansa na gaskiya daganan aka rada Abdulrahmanu matsayin sarki wanda Ina iya cemuku harma yafi mahaifinsa aiki dakuma yin adalci tsakanin mutanensa wannan yasa kowa kesonshi da girmama shi cikin shekara uku yagama shiga ran kowa sannan babu inda baya shiga don halarta taro na sarakuna bama ah Nigeria kadai ba har neighbouring countries dinmu sannan tunda yahau mulki yake neman dan uwansa sede shiru babu labarinsu kwata kwata,awannan lokacin ne aka gaiyaceshi zuwa wata taro na sarakunan kasashe baki daya ah *Chad* nan yakama hanya yatafi inda anan ne Allah ya hada shi da Yar Sarkin Chad yagani yace yanaso inda yanemi aurenta babu bata lokaci akabashi ita dubada irin mutunci da girma irin nasa tunda Magajiya taji labarin auren Khairiya da Abdulrahman hankalinta bakaramin tashi yayiba, hankalinta bekara tashibama seda tayi ido hudu da Khairiya babu inda taragu daga kyau har mulki da kudi gashi kuwa Mai martaba yadauki son duniya yadaura mata don jida ita yake Kamar kwai banawasaba gashi Itama tazo tanashiga ran jama'a dubada hali irin nata compared to Magajiya me wulakanta bayi ita da take tasu ma,shekaranta daya dazuwa gidan tasamu ciki har Allah yasauketa lafiya tasamu santalelen 'danta namiji ranar murna agurin Maimartaba Allah ne kadai yasani daga Khairiya yayi sama yana juyi da ita cikin daki gaban kuyangu tsabar farin ciki sannan yadauki 'Dan yana karemasa kallo tareda yi masa addu'a,samun guri yayi yazauna bayan bayin sunbasu guri sannan ya janyo Khairiyan zuwa jikinsa.....
I'm very grateful for this gift Khairiya, I'll forever be thankful to you,kinbani kyautar dabansan irin godiyan dazanyi miki ba...Dan furzar da iska yayi sannan yasake dubanta
"the owner of the throne is back Khairiya, Almustapha is back!and the throne belongs to him".....

Murmushi tayi tareda Kara shigewa jikinshi don tasan irin son dayake ma Yayanshi kullum maganarsa shine Allah yabashi 'Da namiji yasamishi suna Almustapha sannan yadaurashi akan kujerar Almustapha dayabari......
Allah ya rayamana shi Abban Almustapha....
Kissing forehead dinta yayi ahankali sannan yace ...
"Amin Ummin Almustapha,kinfara koyon yarenmu sosai yanzu, you're a great learner"....
Murmushi tasakar Mai me melting heart dinshi sannan tace....
And the credit goes to you....
Murmushi kawai yayi yana karema yaron kallo kwata kwata baya gajiya da kallon yaron hakanan bayason barin yaro seyake ganin kaman inyasakeshi ze sake guduwa kaman yanda Yayanshi yagudu yabarshi......

Kallon ta yayi sannan yakalli yaron "he look exactly like his mother, I'm jeolous Khairiya"...
Dan Jan hancinshi tayi "don't be jeolous because he'll be like you one day"....
Yar dariya yayi "anyi one one kenan"......
Uhmm Mana....

ahaka akayi suna akasama yaro Almustapha anyi bikin suna sosai,anyi sadaka anci ansha awannan ranar sannan ba ataba yin taro agarin zazzauba irin na ranar sunan Almustapha.......

Magajiya kuwa ko barka bataje tayima Khairiya ba kowa yaganta yasan tana bakin ciki da wannan haihuwar haka 'ya'yanta ma tabi tasamusu tsanar 'Dan uwansu tun yana yaronshi sannan tundaga wannan lokacin tashiga makirci yau tahada ma Khairiya wannan gobe tahada mata wancan sede babu wanda tayi succeeding aciki, Almustapha nada shekara hudu Magajiya tasamu ciki shima haihuwar Mace tasake samu inda sukasamata Hamida bayan shekara biyu sega wani cikin Kuma wannan karan se Allah yabata 'Da namiji inda suka sa maisunan marigayi sarki Sulaiman Maimartaba yayi farin ciki da haihuwar acewarsa Almustapha yasamu abokin wasa dukdama duk haihuwar da Magajiya takeyi yakan nuna farin cikinsa don kuwa Mata ma 'ya'ya ne Kuma yana kula dasu dede gwargwado and duk abunda sukeso anayi musu......

Tunda Magajiya tasamu Sulaiman tasaka ma ranta cewa shine zai gaji sarautar Zazzau dukyanda za ayi setayi yanda zatayi tahana Almustapha mulkan garin zazzau koda kuwa hakan na nufin ta kaudashi daga duniya ne sede she won't go directly by doing that sede inhar the other way din yaki tafiya yanda tasone.....

Sulaiman yataso yanason dan uwanshi Almustapha, he's just a free boy baya dason bin maganar mahaifiyarshi se abunda ranshi keso yakeyi Sulaiman nada shekara biyar Almustapha nada goma shabiyu duk wani harkansu tare sukeyi sannan Almustapha nakula dashi yanda yakamata sede Almustapha mutum ne dabaya magana miskiline gashi da shariya becika damuwa da alamuran mutaneba ga sarauta da jinkai ga kyau duk wanda yasaka ido akan yaron seyaji yaburgeshi manya da yara kowa girmama shi yakeyi acikin masarautar dama garin baki daya awannan lokacin ne Magajiya tafara shirin gudanar da aikinta don kuwa ta lura sam Almustapha baya kama da Mai Martaba ko kadan uwarsa yadauko don kuwa daka ganshi kaga ba jinin Nigeria bane ba dukda kuwa bawai wani haske ne dashi ba amma yanayin fatarshi da gashin shi kadai ze baka amsa......
ranar Almustapha yadawo daga lambu kenan dayanma yashiga dakin mahaifiyarshi yasamu guri yazauna....
Kallonshi tayi sannan tace harka dawo daga lambun ne yau?.....
Uhm kawai yace Mata, murmushi tayi sannan tace Mallam Hudu bebaka unripe mango ka kawomin ba?....
"Bebaniba Ummi"..
Kuyangun dake mata fifitane sukace kilan yamanta ne Aunty....
Nima tunanina kenan Hindatu Kuma wallahi yau inbanci mangoron nanba zan iya zazzabi,Yar dariya Hindatun tayi sannan tace ba akai ga haka ba bari zanje inkarbo miki yanzunnan inyaso Jamila tafara miki tausan kafin nadawo.....

To Hindatu Allah yamiki albarka, nan kuwa Hindatu tafice aguje don karbowa Jamila nashirin barin yin fifitar Almustaphan yadaga mata hannu alamun tabari sannan yataso ahankali cikin takunshi na kasaita yazauna kusa da kafafun Maman nashi yana yimata tausan ahankali sannan yana dan satan kallon cikin ta don yaga Kamar yadan kumbura murmushi tayi lura da kallon cikin dataga yanayi sannan tariko hannunshi ahankali tadaura akan cikinta "you'll be a Brother soon Yarima"....
Lumshe idanunshi yayi ahankali don bakaramin dadin news din yajiba sannan yadan saki murmushi,yanason kanne yanaso ace shima yanada kannenshi uwa daya uba daya it feels good sabida yagaji da wulakancin Magajiya da Yayanta duksanda taganshi da Sulaiman seta cimishi mutunci wurin yayyunsa matakam baya samun sauki har humaira da Halima sukayi aure baya tunanin maganar kirkita taba hadasu .......

Cire hannunshi yayi acikin nata sannan yarungumeta batareda yace komaiba,tasan rungumar na nuna farin cikinshi ne,tasan halinshi sarai bazai taba magana ba ko shakka babu Almustapha mahaifinta yadauko wurin miskilanci da sarauta dakuma mahaifin shi dan ko sarki Abdulrahman ma ba bayaba wajen kasaita suna nan zaune ahaka har Hindatu tadawo da unripe mango ah yanke karban plate din yayi yanabama Ummin nashi ah baki tanaci suna haka ne wata baiwa tashigo wai ai tayi bako daga Chad tayi mamaki sosai don ah iya saninta babu wani dan gidansu datasani dayace zaizo mata amma seta zari mayafinta tafita anan ne tayi arba da bakon dabatasanshi bama kwata kwata gaisuwa sukayi cikin yarensu na Chad sannan yace mata daga Chad yazo aikine ah Zaria baida gurin sauka Kuma yajima dasanin cewa tayi aure anan shine yace bari yazo su gaisa....

Godiya tamishi sosai da ziyara sannan ta tambayeshi mutanen Chad duk yace mata kalau suke sannan tace akarasadashi gurin Mai martaba sugaisa ace bakontane daga Chad zedan kwana biyu anan.......

Aikuwa Maimartaba yaji dadin ganinshi sannan aka bashi masauki mekyau abunda Khairiya batasaniba he was hired by Magajiya sabida suyi conspiracy against her kwanan shi biyu ah gidan kullum inyadawo daga inda yake karyar yaje aiki seyaxo gurin Khairiya sudan gaisa sudan taba hira Kuma wannan abun yafara jan yan magance magance cikin masarautar wanda bayin Magajiya ne sukafara kintsata wai ai ba dan uwan Khairiya bane to miyasa zena zuwa gunta hira,wasu suce kode tsohon saurayinta dai hakadai magana tafara nisa har Magajiya taje gun Mai Martaba tafara mashi abunda taji anafadi gwanda yayima Khairiya magana ta sallami bakonta karya jamata matsala.....

Tsaki Mai Martaba yayi sannan yace "nifa Magajiya Kinga bana son gulmace gulmace da kananan magana,wani sa'in kuke bama bayinnan daman suna fadan wasu abubuwan dababu Kai babu gindi don haka kar inkara jin zancen banzan nan abakin ki"......

To kawai tace mishi yayinda tana fita tawuce gurin bokanta tafadamishi tanason Maimartaba ya zargi Khairiya sannan duk abunda ita tafadamishi ya yarda,aikuwa boka yace to ....
Ranar da daddare Khairiya na bacci ah dakinta se ga dan chadin yazo side dinta wai ita ke neman shi, Hindatu akafadamawa don haka tace bari ta tambayi uwargijiyanta tukunnan dakin babu haske da duhu don haka daga bakin kofa tayi sallama setaji ta ansa mata Kuma kamar muryar Khairiyan ne seta fadamata sakon nan tace ah shigo dashi ba Karamin mamaki Hindatu tayiba sede babu jaa amaganar shugabanta dole tabi abunda tace don haka seta fita don bashi ikon shiga dakin idonta yaciko da kwalla don tarasa abunyi.....
Abunda Hindatu bata saniba ba Khairiya ne tayi magana ba daya daga cikin kuyangun Magajiya ne tazo ta labe haka yashiga dakin yadale gado yakwanta gefen Khairiya can cikin masarauta kuwa anfara gulmace gulmace kan sarauniya Khairiya tashigar da kato dakinta kan kace mai magana tagama karada ko Ina duk inda ka tsuguna gulma akeyi, Almustapha na dakinsa yana duba wani littafi yaji kaman dogarayensa nadamunsa da hayaniya don haka yatashi yafita don ganin meke faruwa samun su yayi suna ta yan magance magance,tsayawa yayi yana kallonsu don kuwa ah tsarinsa daya tsaya agabansu from his reaction suke gane meyakeso amma seyaga yau basu zube kasaba don mika masa gaisuwa sannan basuyi shirun ba kaman yanda yabukata sema daya daga cikin dogarayen ne yace wayasani ma ko shima ba asalin 'Dan Sarkin bane kawai ta yaudaremu ne.....
Wani ma yadauka"ahto nidama tunda inamamaki miyasa yaron nan bedauko ubansa ba akamanni,ashe ga dalili nan ah fili".....
Lumshe idanu Almustaphan yayi don yaji zafin maganar amma seyakoma daki don saka kayansa yawuce side din mahaifiyarsa don jin meyake faruwane,yanajin wani na Kuma cewa matsalar auren nawajen kenan basuda tarbiya kwata kwata.....

Wannan karan waziri dakansa yaje yasamu Mai martaba yake fada masa sannan yace yazo yagani da idanunsa babu musu Mai martaba yatashi yabi bayansa sanda ya iso bangaren Khairiya acike yake da bayi da dogaraye suna ganin Mai martaba kowa yakama hanyarsa yakoma bakin aikinsa haka yashiga sashin nata yanajin kirjinshi nabugawa dukda kuwa baya tunanin ze ganta dawanin kaman yanda jama a keta fada sede kash yanashiga yayi arba da abunda idanunsa da jikinsa bazasu iya dauka ba lumshe idanunshi yayi sannan yafara furta innalillahi wainna ilaihir rajiun,kamin kace me ya yanki jiki yafadi dasauri waziri yayi kanshi yana ihun sunanshi yayinda alokacin Khairiya ta tashi sakamakon jin ihun Wazirin datayi,aikuwa 'Dan Chad din dagudu yafice don neman tsira don yasan in aka kamashi bazai ji da dadi ba, awannan yanayin ne Almustapha yazo yasamesu ganin mahaifiyarshi na kuka yakarasa gareta tareda rungumeta yayinda zuciyarshi nayi mashi zafi alokacin ne kuma aka fita da Mai martaba.....
Almustapha bansan komai ba,wallahi banyi komaiba Almustapha, believe me son.....
Sa hannu yayi yarufe mata bakinta shima idanunshi sun ciko da kwallah"I trust you Mother,basai kinyi magana ba".......
Haka suka kusan shide awa daya shi kuka ita kuka daga karshe ta tashi don zuwa dubo jikin Mai Martaba amma tundaga waje tagane ba lallai abarta tashiga ba dukda haka takarasa shashin nashi don trying luck dinta sede tundaga bakin kofa tahadu da Magajiya,"ke dakata!"....
Ina zakije,munafuka algungunma kodai so kike kikarasamin mijine bayan abubuwan dakikayi duk basu isheki ba?.....
So kike kikarasa shi har lahira?,to baki isa ba Khairiya don kin asirceshi yafita acikin tunaninshi awancan lokacin toyanzu baki isaba!...
Kuka Khairiya tashigayi tana nibansan komai ba,wallahi banyi komaiba Magajiya don Allah kibarni inga Mai Martaba innayi mishi bayani zai gane......
Dariya Magajiya tayi harda shewa sannan tazare mata idanu"da tsafin naki ba?"...
Jijjiga Kai Khairiya tashigayi yayinda Magajiya tace"Yo inbada tsafin kiba damai zai gane,bayan kowa yaganki kiri kiri da kwarto ah gado daya wani bayani ne kuma zakiyi wanda yafi wannan?kifada mini wani bayani zakiyi.inma zaki tashi kibarnan tun cikin ruwan sanyi gwanda kitashi inbahaka ba insa dogaraye sumiki dan banzan duka dake da 'Ya'yan shegun dake cikin ki"......
Tsugunawa Khairiya tayi gaban Magajiya tana rokon ta tayi hakuri tana kuka kaman ranta zai fita duk wanda yaganta seyaji tausayinta amma Magajiya fir taki sema sawa datayi dogarayen suzo suyi waje da ita,haka sukazo sunajanta tana kuka tana tutturjewa hargaban shashenta Almustapha dake ciki yaji kaman kukan mahaifiyarshi don haka yayi saurin fitowa hango walakancin da dogaraye keyimata ne yasashi saurin tafiya aguje nan yashiga dukansu ai tuni suka koma kanshi kuma sede shima ba baya ba he's well trained seda yamusu likis duka sannan yadawo kusa da Ummin shi yadagata yana hawaye suka karasa gaban shashen nata sede Magajiya da dogaraye na tsaye agurin anata wulli da kayan mahaifiyarsa lumshe idanunshi yayi ahankali yanajin wani irin zafi a ranshi yayinda Ummin tasake hannunshi takuma tafiya da gudu tana bama Magajiya hakuri harda rike kafafunta ball Magajiya tayi da'ita wannan karan seda ta gwaru dawani dutse dakarfi Almustapha yashiga Kiran Ummin nashi *Ummi!Ummi* sannan yaruga aguje zuwa gurinta Magajiya tana iyacewa tunda yaron yazo duniya yaune tafara jin muryarshi don magana betaba hadasuba.....

Ahankali yadaga mahaifiyartashi sannan ya yagi rigan jikinshi yashiga goge mata goshinta inda yafara jini still tana shirin kwatar jikinta ne don taga mai martaba sede wannan karon yarike hannunta ka Kam,kamata yayi suka tsaya sannan yayi hanyar barin masarautar duk inda suka wuce anakallonsu kowa na tofa albarkacin bakinsa sede daga ita harshi babu wanda yadaga ya kallesu seda suka bar masarautar sukayi nisa sosai sega Mallam Hudu yazo yana kuka shabe shabe yana kigafarce ni uwargijiyata abu irin haka yafaru dake bazan iya komai akai ba......

Murmushin dayafi kuka ciwo Khairiya tayi sannan tace Mallam Hudu kaima Ka yarda dani ko?,kayarda bazan iya aikata abunda ake zargina dashiba ko?....
Jijjiga Kai yayi cikin kuka yanacewa nayarda dake ko kowa ze juya maki baya nina yarda dake nikuma na tabbatar me martaba ya yarda dake sede in wata kulla kullar akayi.....
Fatana Allah ya kubutar dake daga wannan al amarin don magana duk ta baza gari,cikin kuka tace bana tunanin zan iya warware kaina daga zargin nan zankoma kasata wurin iyaye na inada tabbacin me martaba dakanshi zezo nemana.....
Cikin kuka Mallam Hudu daya kasance mutumin ta me kula Mata da lambu dakuma kawo mata ya'yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login