Showing 144001 words to 147000 words out of 235422 words

Chapter 49 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3509

cikeda sonta tasake fadawa jikinta sede wannan Karan itace tafashe da kukan dakyar Ummin ta rarrasheta Almustapha da Mom dai suna gefe suna kallon ikon Allah seda Asma'un tayi shiru sannan yakaraso ya tsuguna gaban Ummi tareda dan riko hanuna cikeda damuwa yace"Ummi are you okay?".....
Murmushi Ummi tayi dukda idanunta akwae guntu guntun hawaye sannan tace"do you think I'll never be okay if your wife is with me?".......
Batareda yabata ansaba yadaga idanu yadubi Asma'un dake kwance jikin Ummin idanunta sunyi jage jage da hawaye gashi harsunwani kumbura tsabar kukan datasha........
Turo mishi baki tayi gaba tana...
"Ummi baiyi ko sallan maghrib bafa"......
Zare idanu yayi yana mamakinta wai harma kararshi take kaiwa Ummi sekace itan tayi, ahankali yace"dakike kawo karar nawa ke kinyi ne?"...
Murkuda mai baki yayi batareda tabari Ummi tagani ba don gani take raina mata wayau ma yayi aiyasan bata sallah inba neman magana ba miyasa zaice batayiba Itama abunda batasani ba Almustapha gabadaya yama manta cewa bata sallah......
Ummi ne tace....
"tashi kaje kayi sallah joor don yafadi gaskiya shine kake neman kayi mata sharri ko?"
Murmushi yayi tareda tashi tsaye yayinda aranshi yake fadin....
"To antaba shalelen Ummi yaukuma seyanda akayi dani"........
Haka yafice don zuwa masallaci yayinda Asma'u tabishi da kallo harya bace mata da gani,jitakeyi kamar kada ranar rabuwarsu tazo dukdama yanzu kam tasan its high time tunda komai yazama normal alhamdulillah ga wayartama se kira yan gidan su ketayi tun sunacan gurin amma taki dauka sabida bayanzu takejin zata iya magana dasuba......

Wuraren bakwai da rabi Almustapha yafito ah masallaci don har Isha seda yayi sannan yafito ah masjid din,jiyayi kaman ana hayaniya ga commotion tako ina wannan dalilin yasashi juyawa ya kalli wani dogari dake shirin fara alwala abakin pampunan dake harabar masallacin yace"ihun mena keji anayi?"......
Cikin sauri Dogarin yazo kusa dashi jin muryar Almustapha dinne don baima fara alwalan ba daman,cikeda ladabi yace"Yarima Allah yaja da tsawon rai mutanen garine suka shigo waisai sundauka muku fansa agurin Magajiya,so suke abasu ita"...
Cikeda damuwa yace"bangane ba,gate din masarautar ba'a rufe take ba daman miyasa aka barsu suka shigo to "......
"Bansani ba wallahi donnidai nasan Yarima Almustapha yace kada abude bansan ya akayi suka bude daga bayaba",cewar dogarin donshima bawai yasan abunda yafaru bane daga baya cikeda damuwa Almustapha yabar gurin,gurin hayaniyar ya nufa cikin takunshi na kasaita sede cikin sauri wasu dogaraye suka bi bayanshi suna rokonshi kada yaje gurin sabida crowd din yayi yawa suna iya jimasa ciwoma batareda sukansu sun saniba so, it's better yakoma cikin gida kawai su zasusan yanda zasuyi.....
Cikeda damuwa yace....
"kuje kusamomin loudspeaker".......
To sukace kafin wasu daga cikin su suka juya don aiwatar da abunda yasaka su yidin yayinda sauran ke tsaye ah bayanshi don yimashi tsaro hakanan batareda ya dubesuba yacanza hanya tafiya yadinga yi har yakai kan wasu dakali wanda daganan yana iya kallon duk abubuwan da mutanen sukeyi ba ajima ba kuwa sega dogarayen sunzo da loudspeaker,karba yayi yana kallon jama'an dake zagayeda motocin sojojin cikin calm voice dinshi yasa loudspeaker din ah bakinshi tareda yin sallama amma ina basuma kulashiba dukda kuwa wasunsu sunji,yayi sallaman yafi saubiyar amma hakan baisa sundaina abunda sukeyiba............
Cikeda bacin rai yace dakuma muryardabaisan yanada ita ba cikin tsawa yace"Stop,i said all of you should stop!".......
Kankace mai gurin yayi tsit babu motsin ko mutum daya sema juyowa dasukayi suna ganin bangaren da Almustapha din yake,aikuwa sosai suke ganinshi sakamakon hasken wutan da aka zagaye masarautar dashi baki daya.....
Cikeda bacin rai yace"haka ake daukan fansa,koko ance muku abunda kukeyi din shine daidai?"........
Adalilin hakan dakukeyi din kuna iya jima junanku ciwo batareda kunsani ba hakanan Kuna iya jima innocent sojoji ciwo suda suke matsayin masu taimakon mu dakuma tsaron aduk lokacin da muke cikin matsala,adalilin mutum daya seku bari mutum dari suji ciwo ah musali?....
Tsakaninku da Allah kunyi mana adalci?...
I'm very sure some of you were here since before maghrib hakanan inada tabbacin cewa most of you bakuyi sallar maghrib ba bare isha da akayita bada jimawaba,inwani yafadi ya mutu anan tawannan dalilin do you think I'll be able to forgive myself kokuma dawani idanu zeje ya kalli ubangijinmu mahalliccin mu?.....
Nam numfasawa Almustapha yayi sannan yacigaba"indai kunayin hakane don ku burgeni to tell you the truth nibaku burgeni ba infact batamin raima kukayi,I don't want a situation whereby my people will suffer because of me hakanan ni banason tashin hankali inkuka zauna ah inda kuke inada tabbacin zakuga hukuncin daza ayima mai laifi,dubansu yakumayi sannan yayi folding hands dinshi"in abunda nafada yabata ma wani daga cikin ku rai then, I'm very sorry nina fadi abunda yake raina ne hakanan banason ku cuci kanku tahanyar faranta min indon kunason kuyi repaying dina for accusations dakukayi tayimin ne ah baya to nikam tunba yauba nayafe muku hakanan banrike ku ah raina ba so,Allah ubangiji ya yafe mana baki daya and to tell you the truth I'm very grateful for all your love and support, Almustapha nasonku From the bottom of his heart shiyasa banason abunda zaicuce ku baki daya and finally I request you all to go back home safely insha Allah zamuyi handling komai dakanmu", yakarashe maganar still both hands dinshi are folded.......
Bakaramin sanyi jikinsu yayi ba da kalaman Almustapha din hakanan sun tabbata gaskiya yake fada musu shiyasa ma suka juya suna fita ah gidan ahankali yayinda suke hailing sunanshi"Yarima Almustapha!", "Yarima Almustapha!"....

Yana nan tsaye gurin har suka gama ficewa kafin yasa dogarayen da gudu sukayi gurin motocin sojojin inda wasu daga cikin dogarayen duk sunji ciwuwwuka ah jikinsu hakanan sojojin cikin sauri suka shiga taimaka musu yayinda dakyar akasamu aka fito da waziri dake motar farkon gabadaya yayi jina jina dashi don ba karamin duka yashaba,ko motsi bayayi jini ta baki tahanci se zuba yakeyi haka aka dibeshi akayi clinic din masarautar dasauri,haka Talatu da Magajiya ma duk sunji ciwowwuka gwanda Talatun ma ba sosaiba kaman na Magajiya din don ita abunda yahanata guduwa ma kenan cikin crowd dinnan don babu abunda zaisa tazauna tana ganin wahala.......
Daza akaita clinic Almustapha yace baza akaitaba sukaita gidan horo shi likitan yabita can yayi treating dinta he knows how cunning she's,she might think of escaping and he'll never let that happen..........

Dukda ciwo da radadin da jikinta keyi hakan behanata wurgama Almustapha harara ba sannan tace"Daman anfada maka I'll accept any treatment from you ne,nagwammace na mutu da'in karbi taimako daga gurinka,kayi kadan wallahi Dan shegiya".......
Murmushi kawai Almustapha yayi tareda shrugging shoulder dinshi in an I don't care manner sannan yadubi dogarayen yace"Do as I say",kafin yawuce batareda ya kalli ko bangaren da take ba.....
Haka suka kaita gidan horon sannan aka tsagaye gurin da matakan tsaro tako'ina dukdama wasu sojojin dabasuji ciwo ba suntafi da polisawa, wanda sukaji ciwon kuma anyi rushing nasu to clinic din cikin masarautar don basu taimakon gaggawa......
Magajiya se huci take itakadai,wai inda takesa ah hora mutane nan aka kawo ta yau lallai Almustapha yadebo ruwan dafa kanshi she'll makesure she succeed no matter what,tana cikin tunanin nan ne taji anbude gurin likita ne da wani dogari suka shigo hannunshi dauke da first aid box,wani harara ta watsa musu sannan tace"bana bukatar treatment dinku".......
Lallaba ta likitan yashigayi amma gabadaya taki seda kokarin bibbige likitan da ankwan hannunta datake shirin yi wannan dalilin yasa yace"shi bazai iyaba koda akaje aka fadama Almustapha cewa yayi subarta kawai,ita tasani"....

Bangaren Mai Martaba yafara zuwa yaduba shi sede haryanzu bai tashiba sakamakon drip da akasaka mishi dakuma allura da akayi mishi na bacci sabida tsoron kada Bp dinshi yakai stage din da ba aso,yajima azaaune gun Mai Martaba din kafin daga karshe yatashi yafice zuciyar shi fal da tunanin halin da Sulaiman yake ciki batareda yayi wata tunani ba yawuce bangarenshi ahankali yatura kofar parlourn bayan several knocks dayayi ba a amsa ba..........
Duhu yagani ah parlourn gawani irin shiru kaman wani graveyard wannan dalilin yasashi kunna hasken wayarshi yanemi switch din wutan ya kunna kan kace me haske ya haskaka koina na harabar parlourn arba yayi da figure din Sulaiman din dake kwance jikin wata kujera ah kasa gabadaya ya dukun kune kanshi kaman wani maraya hakanan Almustapha yadinga jin zuciyar shi na dukan uku uku lokaci guda dakyar ya'iya yakarasa gaban Dan uwannashi tareda zama ah gabanshi gani yayi hawaye nazuba daga idanun Sulaiman din non stop hakan yakara idanunshi yana kallon bangare daya da alama kukan zuci yakeyi don ko sautin kuka bakaji se hawaye daketa ambaliya.........
Take Almustapha yaji shima hawayen suntaru ah nashi idanun in a very calm voice yace"I'm sorry Sulaiman"............


Vote
Comment
Share!
[3/23, 6:03 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad..

*page 53*....


Sulaiman da tunda Zaliha tashigo bangaren tagama babatun duniyarnan amma be kulataba daga karshe Itama hakura tayi tawuce daki don ji da nata damuwar.......
Bayan tashiga dakin ne yatashi yakashe wutan parlourn sannan yadawo yakwanta guri daya, gabadaya duniyar tayi mashi zafi dukyanda yaso yadaure beji wani iriba yaka sa,shiwayene dabazaijima mahaifiyar shi takaicin abubuwan da tayiba,shiwayene dabazai ji zafin wahalar dazata shigaba acikin zuciyar shi, she's his Mother no matter what hakanan tadauki cikin shi for 9months and the most annoying thing she's doing all this to make him powerful dukdama yasan tanayine for her own interest and benefits,jiyake inama inama,inama ana iya canza identity,inama ana iya canza mahaifiya da wallahi babu abunda zai hanashi canza Magajiya tunda jimawa........
Hakanan yananan kwance ah parlourn har Sumayya tayita kiran layin shi amma baidaukaba,takira times without number amma yaki dauka can yaji Afiya tashigo tana waya da Sumayya din,jiyayi tanacewa...
"bayanan bangaren su ma,kinga wutan ma ah kashe yake baki dayanta alamun bakowa ni inaganin yana Fada tareda su Yaya Almustapha"......
Besan me Sumayyan tace mataba seji yayi Afiyan nacewa"kada kidamu,I trust Yaya Sulaiman he's a very strong Man and besides shikanshi yasan wacece Magajiya so bazai wani damu ba", takarashe maganar tareda juyawa tafice tabarshi besan sanda hawaye sukafara running cheeks dinshi ba hakanan yana maimaita kalaman Afiya"he's a very strong Man",sekuma yatambayi kanshi","is he really that strong?",kaman yanda Afiyan tafada,yasani he always hide his pain but today the situation is different,yau yaji abubuwan dabai taba tunanin wani dan Adam zaiyi bama balle kuma Uwar data haifeshi.. ......
Allah sarki Sumayya haka tacigaba da kiran layin nashi amma yakasa dauka daga karshe ma kashe wayar yayi gabadaya don yasan indai taji muryarshi her mind will never be at ease dama tananan gida ne yasani she'll always be with him, she'll hug him and comfort him hakanan she'll makesure that she makes him feel better and she'll tell him that"everything will be alright",yana cikin wannan yanayin ne har Almustapha din yashigo yasameshi ahaka.......
Jin yace mishi "he's sorry dinne",yasashi dago da idanunshi yana kallonshi da mamaki donshi aganinshi he should be the one to say sorry,if not for anything but for his Mother's sake...........

Almustapha dinne cikin raunanniyar murya yace...
"i can't see you like this katashi kazauna please".......
Ganin yanda Yayan nashi yadamu yasashi tashi yazauna din yana kallon Almustapha din muryarshi na cracking yace...
"I sh...o..u..ld be the one to say sor..r..y Yaya"Almustapha besan sanda yajanyo Sulaiman din zuwa jikinshiba hakanan yashiga rarrashinshi yana...
"why will you say sorry you fool?"........
Cikin kuka Sulaiman din yace"on behalf of Mama,she did many things,she hurt you guys way too much"yakarashe maganar yana kuka harda shashsheka...
Tapping bayanshi Almustapha yashigayi yana"it's okay,you're not at fault,Mama ne tayi bakai ba then why are you punishing yourself for her deeds,tell me?", Almustapha yayi maganar yana dagoshi daga jikinshi kallonshi Sulaiman yayi batareda yace komai ba.....
In a very calm voice Almustapha yace"if we punishing her is giving you a very hard time zanyiwa Abba magana,we should just forgive her,let her go and we can move on in our lives I promise zan iya yimaka haka Sulaiman kawai so nake Inga ka kwantar da hankalin ka,I want you to be the Sulaiman I used to know".......
Murmushin dayafi kuka ciwo Sulaiman yayi sannan yace...
"you don't have to do that,l'll be okay".......
Kallonshi Almustapha keyi kafin yace"Are you sure?".....
Gyada masa kai kawai Sulaiman din yayi kafin Almustapha ya mikar da kafansa yace "kwanta to" musubabu Sulaiman din yakwantarda kansa akan kafafun Almustapha din tareda lumshe idanunsa ahankali yayinda Almustapha yashiga shafa kan Sulaiman din in a comforting manner tareda yimasa addu'o'i ahaka har Sulaiman din besan sanda bacci menauyi yadaukeshi ba........
Shidai Almustapha idanunshi biyu se kallon tilon kanin nashi dayakeyi hakanan yana kissima yanda abubuwa suke tafiya acikin rayuwarsu baki daya.yana cikin haka yaji text yashigo mai awaya dubawa yayi as he expected Asma'u ce budewa yayi yashiga karantawa......

" _Where are you Yaya Imam?_ ".....
Dan murmushi yasaki tareda farayimata reply.....

_"Ina ruwanki?_"

Asma'u dake kwance kan three seater ah parlour tareda su Afiya daketa maida yanda akayi tsakanin su takaranta reply din nashi......
Turo baki tayi aranta tana"oh hakama zaice".....
Kafin tatura mai...

" _Ayya am Yaya Imam, it's so late in the night shiyasa kuma Ummi ma nata tambayarka_ ".....

Yana ganin massage dinnata yashiga karantawa hakanan yana karantawa yana imagining yanda zatayi da fuskarta in agabansa zata fadi maganar,dan hargitsa gashin kansa yayi kawai sekuma ya shiga kiranta damamaki ta kalli screen din phone dinta ganin shike kira kafin ta saci jiki tawuce dakinta harya kusa tsinkewa sannan tadaga.........
Batareda yajira tayi magana ba yace...
"I'm with Sulaiman so,you don't have to worry zanshigo dasafe".......
Gyada mishi kai tayi kamar wanda tana kallonshi,jin tayi shiru ne yasashi cewa...
"are you there?"
Cikin cool voice dinta tace"uhmmm,hope he's alright?",don hakanan taji ba dadi don seyan zunema Sulaiman din yafado mata kan cewa shi Dan Magajiya ne....
"Yea, he's asleep now", Almustapha yabata ansa sannan yace"seda safe kifadama Ummi"......
Gyada mishi kai kawai takumayi kafin ya katse call din..........

&&&.....

Hajja tunda ta'idar da sallar Isha tashiga hada kayanta ah akwati koda Asiya tashigo da cikinta dayafito sosai da mamaki tadubi Hajjan tana...
"Hajja da kaya Zaki tafi?".......
Batareda Hajjan ta dubeta ba tace...
"eh daso kike inbarmiki kidinga sawa komi?".....
Zama Asiya tayi abakin gadon sannan tace...
"a'a Hajja bahaka nike nufi ba nayi tunanin zamuje mudawo tarene fa kumadai naga akwai kayanki acan gida".......
Budan bakin Hajja cewa tayi....
"cabdi aini daganan babu inda zaku saukeni se gidan Asma'u ko gida bazaniba kuma kimaji ba dawowa zanyi ba ainayi maki kokari Itama Asma'un wayasani ko tanada karamin cikin ma dole inje inkula da ita kekuma zancema Babanku ah dauko miki Jiddo tazauna dake harzuwa lokacin dazaki sauka"........
Itadai Asiya dariya kawai tayi don daman sungaji da Hajja da shegen mitanta ga takura in ankunna generator tace kara yadameta ita dai akashe haka abinci ma tadinga sa Asiya tanacin tuwon dawa dana hatsi waishi zaisa Danta yataso da kwarin jikibawai tayita cin abincin turawan nan da basu da karko ajikiba and on the other hand she's very Happy for her Sister atleast she'll get along with Hajja don da alama tagama saukowa baki daya in anci sa'a ma tana iya daina fushi da Ummin ma tahakura hakanan.....
Haka ta taya Hajjan suka karasa gyara kayan kafin suka kwanta bacci washegari tun sassafe tadingayi masu jaraba se su tafi dakyar Asiya tasamu takora Aslam yatafi aiki tace yabari inya gama ayyukansa seyazo suwuce kaduna da Zaria aiba wani nisa banedashi dahar saisunyi sanmako donda shima Aslam biyema Hajjan yayi............

****
Almustapha da Sulaiman tare suka fita sallar asuba wanda bayan an idar ne suka samu labarin rasuwan Waziri da Allah yayi masa cikawa cikin dare ah clinic din cikin masarautar sakamakon bugun dayasha jiyan don likitocin sunyi kokaro gurin ganin su ceto ranshi amma dake wa'adin yacika bbu yanda suka iya....
Babu abunda Almustapha ke furtawa se innalillahi wainna ilaihir rajiun yayinda Sulaiman dakyar ya'iya cewa Allah yayi masa rahama hakanan yana tuna irin kirkin Kakan nasu dakuma yanda yake nuna musu kauna akoda yaushe shida yayunshi Mata don koda jiya Hajiya Muniba tafadi cewa Waziri was there sanda mahaifiyar shi tayi setting fire agidan Galadima he couldn't believe it sede dayayi la'akari da Wazirin yayi hakan ne don yayi protecting Magajiya sebeyi mamakiba don yasan irin son da Wazirin keyima Magajiya wanda hakan yajamusu soyayyarda yake musu amatsayinsu na Ya'yanta..........

Babu laifi an halarci jana'izar tasa sosai donkuwa dukda abunda yayi din Waziri mutumin kirki ne gashi dason jama'a dasanin yakamata shidai kawai laifinshi yaso 'yarshi dayawa,ya lullube laifinta mafi muni ah mutanen duniya wanda aganinshi yayi hakan ne don irin sonda yake mata sede besani ba cutan ta yayi sannan yasake gurbata mata rayuwartane don dayafada tun lokacin za ahukuntata hakanan bazama tasamu chance din sake aikata laifuffukan data aikata bayan nan ba shiyasa wani sa'in iyayenmu suke babban kuskure wurin boye laifin Ya'yansu batareda sunbari an hukuntasu ba,su gani suke kaman taimakon mu sukeyi kokuma gani suke shine karshen so suke mana bayan bahakan shine daidai ba gaskiya,when your children are wrong show them the way if you can,mu ajiye batun so agefe don inson yayi yawa yana leading to gurbata rayuwar yara da dama because sonda zakayima danka baka iya tsawata mishi inyayi laifi ba so bane wallahi barema in the case of Magajiya it's so horrible,she did a very wrong thing but yet mahaifinta yaboye without thinking twice.....
Allah ubangiji yasa mudace,Allah yakuma sa mufi karfin zukata mu hakanan Allah yabamu ikon tarbiyantar da ya'yan mu tahanyar data dace,Amin ya rabbi...........
Sulaiman baimanta sanar da Yayunshi rasuwar Wazirin ba dukdama seda akakai Waziri gidanshi na gaskiya sannan yasamu yakira su sede abunda baisaniba shine suma sunacan suna fama danasu gidan mazajensu sabida abubuwan dasukayi ta aikatawa hakanan sarai anji labarin abunda mahaifiyartasu tayi wannan dalilin yasa mazajen nasu suka hanasu izinin fita daga gida don mijin Humaira kam cewa yayi intabar masa gida abakin aurenta wayasan wani halin banzan zata sake zuwa tadebo gurin uwarta tamaci albarkacin ya'yan dake tsakaninsu ne da sallamarta zaiyi ya huta shima.....
Hakuri tadinga bashi don itadai Allah yagani ta tuba kuma taga ishara akan mahaifiyarta .....
Sulaiman koda yakira Hamida kuka tasakar mai awaya lokaci guda hankalinshi yatashi yana tambayar ta ko lafiya don baya tunanin labarin rasuwan Wazirin yakai kunnenta bare ace shine dalilin kukan nata .....
Batareda ta tsaida kukan ba tace"mijinta ne yasaketa yanzu sabida tadage setazo gida sakamakon abunda yafaru da Magajiya din kuma don wulakanci ma saki uku".....
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Sulaiman yashiga maimaitawa tareda dafe kanshi hakanan yadinga jin kanshi nasarawa lokaci guda tsabar abubuwan damuwa sunyi mashi yawa ayau din dakyar ya'iya karfin halin consoling dinta hakanan yakasa fada mata rasuwar Wazirin don yasan it might affect her health in abun yamata yawa gashi tana dauke da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login