Showing 228001 words to 231000 words out of 235422 words

Chapter 77 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3529

sa'in tayi hawayen farin ciki because she knows that she's very very lucky to have them in her life bare samun mutane irinsu azamanin yanzu sai antona gaskiya shiyasa akullum addu'ar ta Allah yacigaba da hada kawunansu baki daya Itama kuma Allah yabata ikon kyautata musu kaman yanda suke kyautata mata.....

Cikinta nada watanni kadan Hamida tahaifi Baby girl dinta kyakyawa son kowa kin wanda yarasa ranar suna akasa sunan Ummi bakaramin farin ciki Ummin tayiba tareda addu'ar Allah ya raya yarinya cikin addinin islama. Bangaren Na'im tunda Hamida tahaihu yasake dinkewa da zuwa gidan kullum sai yazo dasafe da yanma kuma inba ya tareda Hamidan to dole babyn na hannunshi tun Hamida namai bakin hali harta bari akwai ranar data faki idanun su Afiya tahanashi daukar Islam(sunan da suke Kiran yarinyar dashi kenan) amma seya rankafo kusa da'ita cikin rada yace"wai kintaba ganin inda ake hana Uba Danshi ne?".....
Batarai tayi tareda hararanshi sannan tace"as far as I know bakai kayimin ciki ba bare kayi claiming 'Yata as naka so kama daina yimin irin shishigin nan"...
Ranshi yabaci matuka gajin kalamanta aiko bakomai tayi mishi kara dukda ma shima daman awasa yafadi maganar amma seyaga tadauki zafi don haka yace"indan nayi claiming 'yarki amatsayin nawa ne kike batarai kiyi hakuri ba laifin ki baneba laifina ne da na kamu da sonki harma nakeson abunda kika haifa",daganan yajuya yafice ranshi nayi mishi kuna Hamida binshi tayi da idanu setaji duk bata kyauta mai ba amma sebata wani damuba thinking that he'll come back soon tunda talura bawai yanada wani zuciya baneba. Nanne nanne har sati guda babu labarin Na'im kwata kwata gidan ma yadaina shigowa hankalinta yatashi fiyeda yanda take zato,she don't want to admit it but she surely miss him,sau tari seta dauki wayarta zata kirashi seta fasa sabida batason zubar da ajinta akwana na goman ne takasa hakuri takira layin nashi seda yakusa tsinkewa sannan yadaga dukansu se sukayi shiru kuma ganin bayida niyar magana seta sakinmai kuka Islam ma dake kan cinyarta jin tasaki kuka itama tafara nata series of kukan atake ya rude yana tambayarta ko lafiya cikin kuka tace"Ina kaine ka gujemu".....

Yanda tayi maganar seda ta kusan sakashi dariya amma seya gimtse ta cikin sigar lallashi yace"I'm sorry to,kiyi hakuri ki lallashi Islam i don't like her crying, I'll be on my way",gyada mishi kai tayi ahankali kafin ta ajiye wayar ba'ajima ba segashi yazoshi a parlour yasamu su Afiya bayan sun gaisa Amira da neman tsokana tace"lovers fight din yakare kenan Yaya Na'im?"...

Dariya yayi yanadan sosa kai sannan yace"tana Ina?".....
Daki ta nuna mishi jijjiga matakai yayi alamar a'a ita tashiga takiramai ita don koda dinma inkaga yashiga dakin to da jamaa aciki kokuma ace yaje duba lafiyarta ne. To Amira tace kafin suka shige ciki sudin sannan suka fada mata zuwanshi saka hijabinta tayi tanaji kamar taruga taje inda yake tsabar kewarshi da tayi,samunshi tayi ah parlournsu yana zaune kan daya daga cikin royal chairs din duk ya rame,ya fada yayi wani iri dashi kamar wanda yatashi daga jinya karasawa tayi kusa dashi yayinda haryanzu Islam batabar kukan ba tashi yayi yamika mata hannu alamar tabashi ita babu musu tamika mai Babyn abun mamaki segashi tayi shiru murmushi yayi yana jijiga ta tareda yimata wasa yayinda Hamida kezaune gefe tana kallonsu adoringly har Islam din tayi bacci ahannunshi still be ajiyeta ba tana hannunshi yana kallon innocent face dinta. Hamida ganin bayida niyar magana yasata dubanshi ahankali tace"I'm sorry Yaya Na'im".......
Dagowa yayi yana dubanta sannan yace"yawuce"ahankali cewa tayi"thank you" ........
Tashi yayi tsaye sannan Itama tatashi tahowa yayi inda take tareda mika mata Babyn yana"kikwantarda ita ah daki tayi bacci",gyada mishi kai tayi tareda kai hannunta daniyar karbanta amma da mamakinta setaji yajayota yahada su itada Babyn yarungume ajikinshi Hamida samun kanta tayi da kasa tureshi ahankali yace"I love you Hamida,don Allah kiyarda in aureki I want to spend the rest of my life with you and this little angel".......

Shiru tayi tanajin wani irin feeling nadaban gamedashi don tasani tabbas ba kowanne namiji bane zaiyi tolerating dinta kaman yanda Na'im keyi ayanzu,nafarko itaba budurwaba shi saurayi nabiyu kuma gata da babynta wanda ba fleshy blood dinsa ba amma hakan baitasa yanuna mata wani negative impact ba to in sonda yake Mata ba genuine baneba na menene to?".....
Tana cikin tunanin nan ne taji yakuma cewa"uhmm Ummu Khairiya say something please"......

Murmushi tayi kawai tareda dagowa batareda ta kalleshiba sannan takarbi Islam ah hannunshi tajuya daniyar tafiya cewa yayi"all these attitudes serves as yes kenan?'.....

Gyada mishi K
Kai tayi batareda ta juyo ba wani genuine murmushi yayi sannan yafurta kalmar alhamdulillah kafin yajuya yayi tafiyarsa. Haihuwan Hamida dayan wattanni Asiya ma tahaifi Baby girl dinta kyakyawa inda akasaka sunan mahaifiyar Mijinta Aslam Asma'u da Almustapha yaso hanata zuwa sabida yanayin jikinta amma sam taki tarikicemai harsaida Ummi tashiga maganar sannan yabari shima da sharadin tare zasujesu cewa tayi"to tayarda",haka sukaje sunan suka dawo ranar don ya hanata kwana sam.

*9 Months later*......

Yau tunda tatashi cikinta keyi mata wani irin severe pain amma ahaka tadinga daurewa bata nunama kowaba Almustapha na lura da yanayinta yacanza haka yadinga tambayarta ko lafiya amma setace mishi kalau take at first kin shirin fita Fada yayi seda ta takuramai da he might be needed over there sannan yatashi yashiga wanka sanda yafito yagama shirin shi sannan yadauki hula yasaka tareda fesa turare jikinshi, zuwa yayi gabanta tareda kai mata light kiss ah cheeks dinta sannan ya tsuguna dede cikinta daya totso gaba yakai mata wani kiss din ah tumbinta adede wannan lokacin ne taji cikin yasake wani irin murdawa babu shiri tasaki kara wanda hakan bakaramin ruda shi yayi ba cikin sauri yashiga tambayarta lafiya nishi take tana nunamai cikinta ganin gabadaya tafita hayyacinta yasa yadauko mata hijab yasaka mata sannan ya sunkuceta suka fice hankalinsu Rukayya tashe sukabi bayansu haka koda yafita harabar masarautar gabadaya masu aiki da dogaraye hankalin su yatashi daga masu zuwa sufada ma uwayen dakinsu semasu Allah yasauketa Lafiya Almustapha bebi takan kowa ba yayi gurin mota seda yasata ah bayan motan sannan yama tuna ashefa bai iya driving ba duk wannan dimimin juyawa yayi rai bace atake kuma sega driver yazo kusa dashi yana mikamai hannu alamar yabashi key din mota harararshi yayi ya wurgamai key din sannan yabude bayan motar yashiga yadagata tareda kwantar da'ita ajikinshi yana aikin yimata sannu ahaka har suka isa bar masarautar suka dauki hanyar hospital daga driver har Almustapha sunmanta ma cewa akwai asibiti acikin masarautar kuma ma kosun tuna shi driver aganinshi baikamata akaita inda ake duba bayiba shiyasa yadauki wannan hukunci abunda baisaniba shine da ace Almustapha yatuna babu abunda zaisa yaki cewa akaita gurin tunda bayinma mutane ne nd doctors tawannan bangaren dasuke musu aiki ah clinic din specialists ne. Suna shiga asibitin aka karbi Asma'u akayi labour room da'ita Almustapha cire hulan kanshi yayi cikeda damuwa tareda hargitsa gashin kan yana karanto addu'o'i aranshi da fatan Allah yasauke ta Lafiya. Kan kacemai asibitin ya cika da mutanen masarautar kama daga kan fadawa zuwa manya manyan Fada, Sulaiman nazaune kusa da Almustapha yana comforting dinshi tareda bashi kwarin gwiwa su Ummi dasu Hajiya Muniba ma duk suna gurin alokacin ne kuma su Mommy da su Mubaraq sukazo daga gidansu Asma'u don Ummi dakanta takira tafada musu halin da ake ciki,duk sunyi zugum kowa da abunda yake rayawa aranshi can sukaji anbude labour room din dasauri gabadaya attention dinsu yakoma gurin dayake sunsan itakadai ake karbar haihuwar ta awannan bangaren dasauri Almustapha yayi gaban Doctor din yana tambayar ta"How's my wife?"......
Murmushi likitan tayi sannan tace "Calm down ranka yadade your wife is safe and sound. She gave birth to a Bouncing Baby boy, congratulations".....

Wani irin sanyi Almustapha yaji yana ratsa zuciyarshi slowly wallahi da ace doctor dinnan namijice kamarshi babu abunda zaihanashi hugging dinta murmushi yasaki sannan yazube kasa yayi sujjada yanayima Allah godiya kafin yataso yace"can I see her please?"...
Yanda yayi maganar cikin sigar roko seda yasa likitan dariya gyada mashi kai tayi tana Smilling"Yea,sure zaka iya ganinta",ai bebari tarufe baki bama yawuceta tareda tura kofar dakin yashiga yarufo taciki tsayawa yayi yana kallon Asma'un dake sanye da maternity gown gabadaya ta galabaita tsabar wahala hakanan yana iya hango rodi rodin hawaye ajikin idanunta da alamun tasha kukanta karasawa yayi kusa da ita yazauna sannan yakamo hannunta yayi kissing kafin yakara dubanta"Thank you so much Asma'u,nagode Allah ubangiji yayimiki albarka".
Lumshe idanunta tayi tanajin dadin kalamanshi kafin takwantar da kanta akirjinshi tace"Amin ya Allah", kissing soft gashinta yayi sannan yace"Ina Babyn namu?"....

Turo baki tayi"Nima bansani ba"......
Dariya yayi jin yanda tayi maganar kamar wanda zatayi kuka ahankali yace"ba guduwa akayi dashibadai Matar Yaya Imam may be suna gyaranshi ne",yana gama maganar kuwa segashi anbudo wata kofa dake cikin dakin Nurse ce sanye da uniform dinta tafito yayinda hannunta ke rike da Baby anyi mishi wanka ansamishi sutura maikyau karasowa kusa dasu tayi tareda mika musu Babyn fuskarta daukeda murmushi tace"Congratulations"......

Atare suka sa hannu suka karbi yaron so innocent and cute dashi gashi kuwa hargefe gefen fuskarshi ga shi fari tas dashi kaman kataba jini yafito Asma'u ne tayi kokarin cema Nurse din thank you dukda kuwa kanta nakan yaron haryanzu suna kallon little angel din da Allah yabasu. Fita Nurse din tayi tabasu guri Almustapha yadubeta yasake kallon Babyn sannan yace"badake yake kama ba hasken ki kadai yadauko"........

Dariya tayi tana"to ai kaima badakai yake kama ba da Yaya Sulaiman yake kama?"....
Wara idanu yayi yace"to shi Sulaiman din dawa yake kama?",shiru tayi batace komai ba don tasan Sulaiman din nadan yanayi da Almustapha dukda bacan sosai ba but sincerely speaking Babynsu ubansa yadauko kama daga hancin,idanun,bakin dama komai she just don't want to admit it ne. Suna cikin haka Ummi tashigo fuskarta dauke da murmushi sannan tace"abun rowa ne kuma?".
"Don dan nakune sekuwani kule daki kukadai Kuna kallonshi?".lokaci daya Asma'u taji kunya ta mamayeta dasauri tacire hannunta ajikin dan tabarma Almustapha dariya yayi yana fadin"daga baya kenan Yarinya"......

Karban Babyn Ummi tayi tana fadin"Masha Allah, Allah yaraya Baby boy"......
Amin Almustapha yace inda Asma'u ta ansa aranta kafin yace"yauwa Ummi dawa yake kama sincerely speaking?".....

Kallon yaron tayi tasan exact replica din Imam dinta ne amma setace"dawa zaiyi kama inba da Mamansa ba?"......

Turo baki Almustapha yayi sannan yace"mema yakaini tambayarki Ummi?"....
"Namanta kedin me goyon bayan Asma'u ne akoda yaushe"......
Dariya sukayi duka kankaceme su Mai Martaba da sauransu suka fara shigowa duba Babyn kowa na yaba irin kyawunsa aranar aka sallamesu suka koma gida kullum masarautar bata rabuwa da baki masu zuwa barka har ranar suna. Ranar suna anci,ansha ankuma taru sosai fiyeda yanda kuke zato koina farin ciki akeda murna inda akasama yaro suna *Abdulrahman* maisunan Mai Martaba kenan,da dare Almustapha yazo ganin Asma'u da 'Danta wanda haryanzu tana sanye cikin kayanta medan karen tsada daya amshi jikinta zama yayi gefenta yana rikeda Babyn kwata kwata baya gajiya da kallon kyautar da Allah yayi mishi ahankali yadubeta yace"mezamuna kiranshi".......
Tace"I don't know wallahi suggestion dinka nike jira".......

Murmushi yayi sannan yadago yaron yayi kissing forehead dinshi sannan yace"We'll call him *SULTAN*".....
Tace"nice name".....
Ummi dakanta takira Ummin Asma'u tanayi mata maganar zuwa wankan Asma'u gida tanason taji raayinsu murmushi Ummi tayi sannan tace"tayi zamanta agidan mijinta duk dayane da ace babu maikula da'ita anan dinne setazo gida amma yanzu kotazo ma Babanta zaiyi fada yace shiba yason irin wannan al adun kinga Asiya ma gwaggon tane taje tayimata zaman arba'in yahanata zuwa gida kwata kwata.......
Murmushi Ummi tayi sannan tace"toshikenan daman nakira inji raayinkune amma in acikin dangin ku ma kunason wata tazo tayi mata zaman arba'in din she's higly welcome"......
Dariya Ummi tayi tace" 'Yafa takuce kuyi yanda kukeso duk dayane", murmushi Ummin Almustapha tayi sannan tace toshikenan Allah yaraya manashi daganan sukayi sallama. Almustapha dayaji Asma'u bazataje wanka ba murna kaman yayi yaya dadinma dandai Ummi tace seyanda iyayenta sukace shiyasa ma baisaka bakiba.

&&&
Watan Sultan biyar yayi bulbul abunshi,gakyau da freshness dayaketa karawa dagashi har mahaifiyar shi tsabar hutu da kulawa dasuke samu ah masarautar,yaro harya fara kokarin yin rarrafe abunshi ga farin jini kowa so yake ya dauka yanzuma Asma'u nazaune tana samishi Pampers dan ita kwata kwata bata yarda da tabarma Bayinta aikin danta ba she prefer tayimasa komai da kanta inbadai dan abunda baza a rasa ba, acewarta tarbiyar yaro inba Uwa tasa idanu ba to gaskiya akwai matsala don kuwa bakowa ne yadamu da abunda ba nashi ba wanima ah nashin ya akakare bare azo ga yayi na wani shiyasa gwanda tasaba da shi tunyanzu yanda inya fara tashi zatasan all his moves. Almustapha ne yashigo sanye da kananun kaya da alama duk agajiye yake zuwa yayi yadaga Sultan din sama yanayi mashi wasa irin na Uba da Dansa daman already tagama sakamai Pampers din murmushi tasaki sannan tace"har angama practicing koyar motar ne nayau?",don Almustapha yadage da koyon mota dukda kuwa yanada masu tukashin still he want to be independent......
Gyada mata kai yayi yana fadin I'm so tired zuwa nayi inyi wanka kona ji dadin jikina tashi tayi tsaye sannan tace"barina hada maka ruwan wanka to sekayi ka huta ko?"......
Alama yayimata da hannu kan tayi magana ahankali because Sultan din yafara Gyan gyadi da alama bacci yakesonyi dariya tayi sannan tashige bandaki tana jijjiga kai sanda tagama hada ruwan tafito already harya kwantar dashi kan gado tace"yayi baccin kenan?"....
sa hannu yayi ah lips dinshi"shhhhh,karki tasheshi".....

Tace bazai tashi bafa Yaya Imam yaronnan da shegen nauyin baccin tsiya kanta ankara taji ya sunkuceta tana shirin magana ya hade bakinsu guri daya seda yayi mai isarsa sannan yakyaleta cikin rada yace"muje muyi wanka kada kitadamin yaro"........
Kaman zatayi kuka tace"nifa banjima dayin wanka ba".....
Dariya yayi"ehdai muje second round zakiyi"........
Koda suka fito tare suka shirya dubanta yayi sannan yace"akwai maganar danakeson muyi Asma'u",cewa tayi "to Yaya Imamu na inajinka"......

Kallonta yayi fully sannan yadaga kafafunshi yadaura akan gadon tareda folding dinsu guri daya Itama thesame thing tayi tana murmushi kafin ahankali yakamo hannunta yasaka cikin nashi sannan yace...
"maganar karatu zamuyi Asma'u,tunda na aureki baki taba kwatanta yimin maganar cigaba da karatun kiba bayan nasan yana daya daga cikin manyan burikan ki?".......
Dariya tayi cikin sigar wasa tace"to incemaka miye Yaya Imam?"......
Serious face yayi sannan yace"ba maganar wasa nike mikiba Asma'u,i'm serious sannan inason kifadamin duk abunda yake ranki gameda maganar dazamuyi yanzu din",still cikin sigar wasa ta jijiiga mai kai"Yes sir"......
Murmushi yayi shima sannan ya jijiga kan"you're unbelievable you know"......
Dariya kawai tayi kafin tace"Allah dagaske to mezan cemaka Yaya Imam?"......
Tun ran gini tun ran zane. Allah yariga da yajima da kadartawa nibazanyi karatu ba bautar aure zanyi and to be sincere I'm very happy with my life now,yace aa Asma'u you still have chance inkinaso zaki iya cigaba da karatun ki babu mai hanaki besides you're still young.......
Cire hannunta tayi daga cikin nashi sannan takai fuskarshi tanadan shafawa ahankali tace"Thank you amma there is no need for that"....
Yace"why?"...
Tace"because karatun bazai yuyu ba Yaya Imam?"....
Yasake cewa"kifadamin dalilin dazaisa kice bazai yuyu ba?".....

Komar da hannunta tayi kasa tana wasa dasu kafin ta sunkuyar dakanta kasa tace"atunanin ka Ina aure a *GIDAN SARAUTA* abu mai sauki ne ince zanyi karatu?"....
"Atunanin ka Ina aurenka amatsayin ka na crown prince zan tsallake responsibilities din dake kaina ne intafi wani karatu sabida son ra'ayin kaina,kaima kasan hakan bazai taba faruwaba",dago da kanta yayi da hannunshi yana"ki kalleni Asma'u".
Kallon cikin idanunshi tayi annanne taga how sorry he feels for her ahankali yace"kece Crown Prince din?"....
Tace"aa but I'm your wife"....
Yace"naji you're my Wife to anma fadamin miye responsibilities dina?",Dan shiru tayi kamar bazatayi maganaba kafin tace"zaka wakilci Abba aduk sanda bayanan ko in ya bukaci hakan and you'll be the next king after him"......
Yace"good", yanzudai Ina kingane inda na dosa ko?...
Still tana kallonshi tace"but still",sauri yayi yadaura yatsanshi akan lips dinta"shhhhh",tsayawa tayi tana kallon cikin idanunshi cikin rada yace"kikoma karatun ki don Allah, I'm responsible for katsewar karatun ki indai har baki cigaba da karatun ba kinzama abunda kikeson zamaba bazan taba yafewa kaina ba".....
Cikeda mamaki tace"you're not responsible for it, you're a victim too Yaya Imam so,why are you blaming yourself? ".....

Yace"nasani amma dai aida sunana akayi anfani akayi koma miyene sannan dabaki hadu daniba da babu wanda zaiyi tunanin hada mana sharri agurin iyayen mu har zuwa abunda yafaru yau",gyada mishi kai tayi sannan tace"haduwata dakai Alheri ne Yaya Imam, it's a blessing to my life sabida haka kadaina ma wannan tunanin please ".......

Janyota yayi kiiiiii kamar babyn roba tadawo dab dashi sannan yamikar da kafafunshi yajuyarda ita yasakata ah tsakankanin kafafunshi tareda sako kanshi ta wuyanta yayinda hannunshi ke zagaye da cikinta cikin rada yace"I know about that nidai kawai kiyarda zaki koma karatun ki",turo baki tayi gaba ganin yanda yadage da maganar jin tayi shiru yasa yadanyi kissing wuyanta tareda cewa"uhmmm"...
"Kiyi magana mana"....
Jin yana neman rikitata tace"to kabari muyi magana dasu Ummi tukun"......
Sake matseta yayi jikinshi tareda fadin"munriga mungama magana dasu ke kadai akejiran jin response dinki", murmushi tayi sannan tadan kalleshi tagefe"Yaya Imam kacika wayau".....
Dariya yayi"just say yes"......
Tace"okay, okay,Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi",cewa yayi "kokefa,Amin ya rabbi".......

Haka Almustapha da Sulaiman suka shiga yimata cuku cukun makaranta tareda su Amira and Afiya ah *Chicago* because suma WAEC and NECO dinsu yayi kyau matsalar jamb ne basuci ba dukansu shiyasa Mai Martaba yace akan subata lokaci suna Mata gwanda ah fitar dasu wajen suyi karatunsu acan tunda sunada halin yimasu din. sunnemi shawara gurin Na'im inda yafada musu wata institution agarin CHICAGO din yace"they're one of the best indai abangaren Medicine ne infact har other courses ma yace inbacan ba kuma to kunema musu ah India",atake Almustapha yace Chicago din yafi Allah yasa albarka aciki. cikin wata daya suka gama komai don Sulaiman dakanshi yaje har Chicago din yakarbo musu admission letter yayi musu registration da komai sannan ya nema musu gidan dazasu zauna acan din kafin yadawo gida Nigeria yafada musu sufara shirin tafiya in the next 10 days jirginsu zai tashi don haryayi musu booking flight bada private flight din Abba zasu tafiba tunda ba ranar dawowa cewa sukayi "to" nan suka shiga shiri babu kama hannun yaro, Sumayya dai gabadaya wani iri takeji don batason sutafi subarta ita kadai ah gida ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe amma babu yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login