Showing 120001 words to 123000 words out of 235422 words

Chapter 41 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3528

sanarda ita halin da ake ciki........
***
Da dare Asma'u dasu Afiya nazaune ah parlour Amira tace nikam Masa nike kwadayi wallahi......
Dariya Asma'u tayi kafin tace"to basai ayiba nima nakwana biyu banci ba gashi baya time table dinmu na abinci".......
Turo baki Afiya tayi don ita masa baidametaba kafin tace...
"ba anayi ah can cikin gida ba kusa akawo muku mana?"....
Cikin sauri Asma'u tace a'a muma zamuyi anan barima infada masu iya Jamila ko za ajika shinkafar yanzu gyadamata kai Afiya tayi yayinda Amira cikeda murna tace"you're the best Sister In-law wallahi"......
Murmushi kawae Asma'u tayi yayinda Afiya tace Sis kije kidawo kiji favour din da zakiyimin nikam don Allah.....
To kawai Asma'u tace mata kafin tawuce dakin su Jamila harsun fara shirin kwanciya da dan damuwa tace zantakura ku ko?...
Cikin sauri Jamila, Salma,Hindatu da rukayya suka tashi cikeda ladabi suna"habadai Gimbiya wani irin takurane wai?"...
"Wani abun za ayine?"wannan karan Jamila ne tayi magana......
Asma'u bakaramin jin dadin respect dinda suke bata takejiba tasan dae she's far young and she's also free with them har wasa da dariya sunayi amma hakan baihanasu bata girma amatsayin ta na Matar Almustapha ba, murmushi tasaki sannan tace...
"Daman Masa nikeson muyi na karin kumallo ze yuyu kuwa?".....
Zeyi mana Gimbiya indae kince ayi se ayi din yanzuma semu wanke shikafar mujikata cewar Rukayya..........
Tashi Jamila da Hindatu sukayi yayinda sukace ku yarannan kuyi kwanciyar ku zamu wanke mudawo......
Rukayya ne tace
"a'a iya Jamila muyakamata muyi ae bakuba".....
Salma dataji haushin Rukayya na iyayin da takeyi masu tace"eh wallahi kuzauna kawai zamuyi",dukda maganar tata batakai har zuci ba,cewa sukayi karku damu munyi niyane haka sukafice sukabarsu Salma na hamdala da ba'a bi zancen Rukayya ba don Allah yagani tagaji bacci takeson yi kuma.......
Haka sukayi kitchen harda Asma'u nanne Jamila kecewa dakikayi maganar masa senatuna masar Aunty, ta'iya masa kamar mi inba Masartaba mai Martaba bayacin nakowa......
Cikin sauri Asma'u tace"dagaske Iya Jamila?"....
Gyada mata kai tayi sannan tace haka Yariman ma yanason na Aunty sosai dukda shi yanacin nawasun ma kinga gobe dole muyima mai Martaba abincin shi daban sabida kada asamu matsala..........
Murmushi Asma'u tayi kafin tace...
"Mai Martaba zaici Masa gobe iya Jamila and that too na wanda Ummi tayi da hannunta".....
Cikeda damuwa Iya Jamila tace...
"Anya zata yarda tayi?" ....
Murmushi Asma'u tayi kafin tace kuwanke shinkafar kawae kujika zanje inyi mata magana she'll do it I'm sure,gyada kai kawai sukayi sannan sukacigaba da aiyukansu Asma'u kuwa ficewa tayi tayi hanyar dakin Ummi tana sake sake aranta tasan tabbas Ummi will be hurt intayi mata maganar yin masa sede yazatayi?....
She want to help her out,Itama tanason ganin matar tanacikin farin ciki da jin dadi like she always want her to be happy as well,tunda haryau Talatu bata dawo ba atleast she should try her luck also wurin ganin tayi reuniting dinsu though she knows it'll be difficult bare anhada abu da asiri ahaka harta karasa dakin Ummin.....
Ummi nazaune kan gado idanunta dauke da eye glasses tana karanta news paper tajuyo takalli Asma'un tareda sakar mata wani kayataccen murmushi.......

Itama maida mata da murmushin tayi kafin tace...
"Ina wuni Ummi na".....
Murmushi Ummi tayi kafin tace "lafiya Lau Habibty na se yanzu kika tuna dani,wato miji yadawo ko",tayi maganar cikeda zolaya......
Murmushi Asma'u tayi tareda dan lullube fuskarta,dariya Ummi tayi tana cire eye glasses din...
"shy shy kawai,nadauka harkun kwanta fa don banji motsin su Afiya bama".....
Muna kuma parlour fa Ummi bamukai ga kwantawa ba,"sunacan sunata asararren kallon ko bayan ga karatu ah gabansu WAEC and NECO is approaching ga uwa uba jamb ma"......
"Ummi suna karatu fa"......
Yar hararanta Ummi tayi tana"to tare musu ke me kawaye ko kanne nema zance"......
Dariya kawai Asma'u tayi kafin tace"Ummi Yaya wai zaici Masa dasafe nikuma ban iyaba",tayi maganar murya ah karye sanda ta ambaci masa seda kirjin Ummi yashiga dukan uku uku hakanan rayuwarta da Mai Martaba yashiga dawo mata lokaci guda Asma'u nalura da expression dinta amma batace komai ba.......
Dakyar Ummi ta'iya faking smile tace"kamar kinkoyi yin masa daga yau zuwa gobe, I'll help you out Dear"......
Cikeda Jin dadin maganarta tace...
"thank you Ummi".....
Dan shafan cheeks dinta Ummin tayi kafin tace kicema su Jamila sujika kaman yanda nasaba yi inkuma sun manta ne se inzo inyi"gyada ma Ummin kai tayi kafin tasake yimata godiya tafice tasamo su Jamila tafadamusu aikuwa sunyi mamaki kafin sukayi yanda tacedin don basu mantaba koda su suke wankewa su jika daman itakuma inta tashi setayi miya da hadin bayan an niko"........

Haka takoma gun Afiya fuskarta daukeda murmushi tana"maganar me zamuyi Afiya?".....
Afiya cikin sauri tataso daga kwancen da take tareda yin kasa da murya alamar roko"don Allah Aunty Asma'u taimako zakiyi mana".....
Dariya sosai Asma'u tayi don this's the first time da Afiya takirata da Aunty"lallai wannan taimakon dazanyi gagarumi ne na lura harda Aunty". .......
Amira ne tace...
"kina wasa da Afiya kenan indai gurin kalaman yaudara ne nabata award"......
"Lol",cewar Asma'un kafin tace"fadamin miye damuwarki Sis".....
Kara maraicewa Afiya tayi tana"karki biyema Amira batasan abunda nakeyi harda itabane ba shiyasa take neman hure miki kunne"............

Dariya Asma'u tayi...
"kekam fadi abunda ke ranka kawai"......
Cikeda Jin dadi Afiya tace...

"Daman inason kitaimaka mana kiyima Yaya Almustapha magana yadawo mana da system da phones dinmu kinga munshiga ss3 yanzu we really need it for assignment and other purposes dai"......

Dariya Asma'u tayi don gani take Afiya magana takeson fada mata,ganin tana dariyar ne yasa Afiya cewa...
"dariyama nabaki Sis?"....
Asma'u daharyanzu takasa daina dariyar tace"yo ba doleba of all people kice nizanyima Yaya Imam magana yadawo muku da laptop dinku ba gwanda kice Ummin bama"......
Cikeda damuwa Afiya tace"Ummi takiyi masa magana fa wai inyabamu zena distracting namu shikuma munmushi maganar yafi ah irga amma yaki dawomana dashi".........
Tashi Asma'u tayi tana"tonidai badaniba kuma kunyi trying luck dinku bebayar ba seni?"...

Wannan karan Amira ce tace"kikasani kozaiji maganar ki,just try your luck for us please"......
Yanda Amiran ta marairaice fuska yasa Asma'u cewa......

"I'll try but in ya dizga ni akanku zanrama kuma ma kawai dai zanyine sabida karkuce naki"........
Cikin sauri Afiya tace"eh munji try your luck for us".......
Gyada musu kai tayi kafin tace"yashigo ne!".....
Gyada mata kai sukayi duka suna baijima da shigowa bama,to kawai tace musu kafin tawuce dakinshi samunshi tayi zaune kan sofa yanata aiki cikin laptop.......
Turo baki tayi kaman wanda yana ganinta kafin takarasa tazauna gefenshi yanajinta amma yaki kulata because he's so busy tafi minti talatin agurin har bacci yadauketa kawai seji yayi kan mutum ya kwanto kan kafadunshi cikeda hafula yace"Asma'u aiki nikeyi please!", yakarashe maganar tareda juyowa don kallonta sede da mamakinshi yaga ashema bacci tafarayi murmushi yasaki yana kallon kyakyawar smooth face dinta ga eye lashes dinta dake kwance zara zara dasu baitaba tunanin karema fuskarta kallo ba seyau fuskarta is so round yayinda gashin giranta ah kwance lub lub dasu gwanin ban sha'awa kaman ita tabama kanta idanunta kuwa dara dara dasu babu laifi ga kwancecciyar eye lashes dinta daya kara musu kyau bangaren hanci kuwa sede ince Masha Allah donkuwa Asma'u akwae hanci tayi gado daga Umminsu se yar karamar pink lips that is well shaped gashi da daukar hankalin jamaa ayanzu ma lips din sanye yace da wet lips wanda yakara haskaka shi don Asma'u bata taba rabuwa da shafa man baki.......
Almustapha kanshi yarasa dame zai fassarata she's just so perfect kamar yanda takeda sanyayyar hali,Masha Allah dakyar ya'iya kauda tunanin dake ranshi kafin ahankali don kar ya tasheta yadaga kan nata yamatsa sannan yakwantar da'ita kan sofa din daukar laptop din yayi yakai kan bedside drawer dinshi kafin yadauko katuwar blanket din dake kan gadonshi yazo ya lulluba mata ah jikinta yajuya zai tafine yaji anriko hannunshi juyowa yayi ahankali gani yayi idanunta ah bude tana sakar mai lallausar murmushinta...
"Thank you kuma na yafe maka kin yaba lallena dakayi",don tunsanda yadaga ta daga jikinshi tafarka kawai lamo tayi sekuma ga mamakinta taga ya lulluba mata blanket dukda batayi tsanmani ba,kallon hannunshi data rike yayi sannan yace"kitashi kije ki kwanta to"......
make mai kafada tayi...
"ni ba yanzu ba banajin bacci".....
Janye nashi yayi cikin nata"to aini inajin baccin ko?"......
Turo baki tayi ah shagwabe"Kai Yaya Imam bazai wuce 5minutes ba, please",tayi maganar tana karya wuya zama yayi ah gabanta batareda yace komai ba.......
Cikeda Jin dadi tace...
"Daman maganar laptop da phones dinsu Afiya ne please kamayar musu kaga yanzu sunshiga ss3 kuma anabasu assignments gakuma karatu dayakamata sunayi dashi"........
Kallon ta yayi yana..
"sune sukace kizo ki tambayeni".....
Cikin sauri tace...
"aa nifa banceba Yaya Imam".....
Murmushi yayi sannan yace...
"komadai miyene kije kice musu inma suna tunanin kinkai wannan matsayin dahar zaki fadi abu inyine to baki kai ba,when I decide no one can change my mind",yakarashe maganar tareda tashi daga zaunen dayake ah gabanta yanadan murmusawa kasa kasa yasan tana iya barkemai da kuka don ya lura shine abunda tafi kwarewa akai, sannan yakarasa bakin gado yazauna yana"and yes,kije dakinki kikwanta Asma'u bacci nikeji banason any disturbance please nace bazan basu ba and no one can change my mind"yakarashe maganar tareda kwanciya.....
Asma'u daranta yabaci takasayin shiru cikin karyayyar murya tace"basai ka nunamin I'm not that important to you ba nikaina najima da sanin hakan Yaya,tunda jimawa nasan I'm just an option,tunda jimawa nariga nasan relationship dinmu is just for a time being tunda you said it not even once but twice Yaya Imam,I know it already so,basai kafadamin ka sosa min zuciyata ba, basai ka fadamin ka tozartani ba,I already know that takarashe maganar tana kuka wannan karan don ta ma kasa holding tears nata...........
Goge kwallarta tashigayi because she really want to be strong sede takasa gani takeyima kaman yanzune ma aka bude ma hawayen pampo sudinga zubowa dakyar ta'iya tashi kafin takarada....
"nasan lokaci yayi dazamu rabu,may be ma in the next one week or two haka,i'm very sure za azoyimaka maganar anason hira dakai akan past dinka which is the only thing I've been waiting for Yaya Imam",dan numfasawa tayi cikeda karfin hali kafin tacigaba da magana"please kayarda this's one of the requests danake nema agurinka",tayi maganar yayinda tayi folding hands dinta kafin takarada
"They'll ask you about your past don't hide anything,tell them about everything, infact we've concrete evidences that will help us expose that woman, Mallam Audu yasan maganar kaji sharri akayi maka lokacin hakanan maganar kudin me chemist Mallam Hudu yayi min magana kwanaki sede Aunty Muniba tace mubari tukunnan shiyasa ban tunkareka ba sekuma itakanta Aunty Muniba din zata bada shaida akan abunda yafaru da Galadima da jimawa sekuma Talatu uwa uba wanda banacire ran zata dawo kwana kusa inshallah wanda inada tabbacin itakadai zata warwaremana komai wanda zaisa asirin Magajiya yatonu harma da abunda tayima su Ummi abaya kaga by doing all that Magajiya will be behind boss and zargin mutane zai tafi,she'll be punished for all her deeds you'll be free Yaya Imam tayi maganar cikeda excitement a muryarta dukda idanunta nadauke da hawaye jage jage sa hijab dinta tayi tagoge hawayen dukda basu daina zuba ba sannan tacigaba"Ummi ma will be free,she'll reunite with Abba and you all will live like a happy family", lokaci daya kuma muryartata tacanza launi daga na excitement zuwana bakin ciki tana"and i....i will also be free from this relationship",tunda I'm sure iyayena koyanzu sunfara gane gaskiya and they'll accept me wholeheartedly without any suspicious kuma zansamu incigaba da karatuna wanda yana daya daga cikin manyan burikana arayuwa",tsugunawa tayi daga tsayen datake sannan tace nasan duka kalaman da nafada will look like imagination to you but believe me it'll surely come true when you cooperate nasan bantaba neman alfarma agurinka ba anma yanzu ganinan gwiwowina ah kasa inarokon ka kayarda ayi abunnan kowa ya huta,komi yawuce because this's the best solution, I'm tired of staying in a place where I does not belong too and my second wish is dan zaman daya rage mana Yaya always smile for me because it gives me happiness ko ranka bayaso try and do that please! na lokaci kalilan ne and inkayi min wannan alfarmar i assure you my last days with you will be one of the best days of my life try and make it special please!karka fadamin maganar dazata sa zuciyana tayi kuna sabida ni mutum ce mai rauni zuciyata bazata iya kuma dauka ba",takarashe maganar tana kuka mai tsuma zuciya sannan tafice zuwa dakinta Allah yagani yanzukam tagaji gwanda data fadamishi kawai ayita takare shine the best,yaushe zasu tsaya jiran Magajiya tatona ma kanta asiri bayan suna da evidence dazazu bayar,Itama tanason takoma gidansu,tanason cirema ranta son Almustapha hakanan tanason tacirema ranta yaudarar datajima tanayima kanta nacewa shidin zai iya zama nata watarana,yanda Asma'u taga dare haka taga rana don kusan kwana tayi tana kuka se wuraren ukun darene ma ta'iya yima kanta fada tayi alwala tatada sallah tana kaima Allah kukanta na ya cire mata son Almustapha aranta sede kamar ma abun karuwa yakeyi.............

Bangaren Almustapha tunda take magana he was just so stunned,he regret his words betaba tunanin it'll hurt her this way ba tunda shi harga Allah abunda ke ranshi yafada mata bayason a situation whereby nan gaba insunyi laifi ya hukunta su subiyo ta hannunta,she's just so fragile tanada tausayi da sanyi bazaiso yafara biyemata ba yazo yana 'bata kannenshi batareda ya ankara ba sede to his own surprise tajuye masa wayannan magan ganun dabaiyi tunanin jinsu awannan lokacinba,shima juye juyen yadingayi don gabadaya yakasa yin bacci daya rufe idanunsa crying face dinta yake kallo haka yakejin muryarta na kuka nayi masa yawo ah kwanyarsa wata zuciyar nason yaje yace mata he's sorry sede egoistic one din yahana don gani yake yafadi inyaje yabata hakuri,gani yakeyi shibaiyi laifin komai ba abunda ke zuciyarshi yafada,then meyasa zaibada hakuri?.........
Asma'u akan sallaya bayan tayi sallar asuba bacci yadauketa ba'ita tatashi ba se wuraren 8:30am haka,subhanallahi shine abunda tace ganin yanda hasken rana ya bullo tacikin dakin ta don labulayen ah bude suke........
Kokarin tashi tayi dukda ciwon da kanta yakeyi mata sannnan tashige bandaki takalli mirror Allah yataimaketa fuskarta bata nuna alamun tayi kuka sosai ba wanke fuskar tayi kafin tawuce kitchen tundaga parlour takeji kamshi hadaddiyar miyan ganye.......
Murmushi tasaki kafin takarasa cikin kitchen din tana"Ummi sannu da aiki".....
Ummi dake nan Helter skelter tana hada miya already harta gama toya masan tace"harkin tashi Habibty!"......
Cikeda kunya tace...
"Sorry Ummi bansamu nayi bacci dawuri ba shiyasa na makara" ...
Dariya Ummi tayi tana"koma kiyi kwanciyar ki nama gama nikam,jeki huta abinki kinji Habibty"(niko nace su Ummi iyayen fassaara).........
Asma'u kuwa batagane abunda Ummi ke tunani ba don haka tace"Babu abunda zanyi ai Ummi,miyarki se kamshi takeyi tundaga daki nike juyowa"....
Dariya Ummi tayi"kice nacancanci aban tukwici"......
"Kwarai kuwa Ummi ae dukwanda yaci masar nan seyabaki inbahaka ba in ansake babu mai kaimasa"....
Lol lallai Habibty wannan kasawa da tsarewa haka amma dai ba'in fara dake,ke tukwicin mezaki bani Daughter", Ummi tayi maganar tareda sauke tukunyar miyar don already yagamu.......

Asma'u tace..
"kifadi mekikeso Ummi"....
Lol anya zakiyi Habibty keda kikemin rowar ganin Umminki ma....
Cikeda damuwa Asma'u tace...
"kiyi hakuri Ummi bazanmiki rowartaba dadinma don kafarki begama warkewa bane shiyasa bamujeba".......
Juyowa Ummi tayi tana sakar mata murmushi ganin yanda tadamu lokaci guda sannan tace...
"I'm just kidding, though daman zanyima Imam magana kan zamuje gida dake kema yakamata kije gida kigasu Ummi nasan kina kewarsu"......
Cikeda Jin dadi Asma'u tace"thank you Ummi"....

Murmushi Ummi tayi kafin tace gashi seku zuzzuba abincin ko nidai nagama nawa dukdama bakiga yanda nayiba but I'll teach you next time ...




*kuyi hakuri from Friday zakuna samun update kullum inshallah*

d'

Vote
Comment
Share!
[3/23, 5:51 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*



Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad....

*Start with this,the other page is on the way in Sha Allah*

*NOT EDITED,so avoid typing errors please*

*Page 46*


Haka Asma'u tazuzzuba abincin ah kulolin daya dace kafin tambayar a kakkai daukan na Almustapha tayi don kaimishi dakanta don tanason tanuna mishi yes she wants them to stay happy together like she requested kafin lokacin barinta gidan....
Knocking tayi ah kofar dakin cewa yayi"come in",hakan yasa tatura kofar tareda yin sallama ah sanyaye amsawa yayi azuciyarshi yayinda yake mamakin zuwanta after abunda yafaru jiyan yasani on normal basis inwani abu yafaru takanyi fushi dashi koda na awanni kadan ne takuma sauko dakanta batareda yabata hakuri bama sede yanzu yasha mamaki don she's acting as if nothing has happened......
Ajiye tray din tayi kan stool kafin tace..
"Ina kwana Yaya Imam"......
"Lafiya lau",ya amsa mata ahankali dubanshi tayi fuskarta daukeda murmushi kafin tace...
"kaman ma yanzu ka tashi badai bakayi bacci ba?",takarashe maganar tareda tashi daga tsugunen da take sannan tadawo saman gadon gefenshi tana duba temperature najikinshi cikeda damuwa sede everything is normal ajiyar zuwaciya tayi tareda hamdala ah zuciyarta shikuma kallonta yatsaya yi babu ko kiftawa, ahankali tadaga idanunta tasaka cikin nashi kafin dakyar ta'iya cewa...
"katashi kayi brush kaci abinci, special food ne yau Ummi tayi",takarashe maganar tareda tashi don tafiya cikin sauri ya riko hannunta wanda dukansu seda sukaji wani irin electrification shock kafin yyi magana can kasa kasa kaman meyin rada"meyene abincin?"........
Murmushi tasakar mai dakyar don bakaramin affecting nata muryarshi takeyiba barinma wayanda inyayita ah hankalinnan..
"you'll see for yourself Yaya Imam, it's a surprise from Ummi".....
Sakin hannunta yayi ahankali tatashi tafice yanabinta da kallo hakanan seya kasa bude abincin yawuce bandaki yayi brush yayi wanka yashirya kafin yazauna cin abincin bude cooler din yayi wanda yaji kamshin miyar dabazai taba mantawa ah rayuwarshi ba,miyar Ummi a very special soup dayake ganin babu wanda yakaita iyawa murmushi yasaki tareda zubawa harzai faraci seyatuna da tilon kaninshi Sulaiman daga wayarshi yayi yashiga kiranshi baajima ba kuwa yadauka.........
"Kana Ina ne?",cewar Almustapha din

Daga daya bangaren Sulaiman yace"Ina bangaren Dad naje mugaisa da Mom ne"....
To kagaidata please inkagama kazo muyi breakfast,dan murmushi Sulaiman yayi kafin yace kaci abincinka nima naci da Mom din katse wayar Almustapha yayi don yasan definately Masan ne yaci tunda daga nan akekaima su Mom dinma abinci fara cinnashi yayi cikeda nutsuwa........
Bangaren Abba kuwa koda akakaimishi nashi abincin yana tareda Hajiya Muniba ne don haka saitace ma bayin suyi tafiyarsu kawai zatayi serving dinsa dakanta.....
Tunda tabude kulolin abincin yakejin wani irin long lost kamshi atattare da abincin besan sanda ya lumshe idanunshi ba aranshi yanason tuna ah ina yasan wannan abincin,ah inane yasan girkin nan amma gabadaya yakasa tunawa dakyar yabude idanunsa yadaura kan masar lokaci guda kuma zuciyarshi tashiga dukan uku uku yayinda wasu flashes ke mai yawo ah idanunsa amma baya g????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
aninsu very clearly dakyar yace...
"I don't eat Masa Muniba",ganin Hajiya Muniba nashirin serving dinshi.........
Cikin sauri ta dago sannan tace"dagaske bakaci?"..
Gyada mata kai yayi ahankali yayinda tace"to miyasa zasu kawo maka bayansunsan bakaci".......
Murmushin karfin hali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login