Showing 72001 words to 75000 words out of 235422 words

Chapter 25 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3475

gida tana kissima yanda zatayi handling abun"........

***
Zaliha yarinya ce kyakyawa son kowa kin wanda yarasa don bazaka ganta kace mata mummuna ba duk hassadarka,yau yan gidansu suka komai yayinda dayanma tabi duk wani bangare na gidan daya zamanto na surukanta tagaidasu cikeda ladabi,kowa seyabawa yake da halinta dakuma biyayyarta don sunji dadin mutuntasu datayi barinma Magajiya baki harnan tayi inlaw me hankali.......
Sanda taje bangarensu Mom ah parlour tazauna aka kawo mata kayan motsa baki sannan tagaisa da Mom din, Afiya ne gulma nacinta tayi daki tana kiransu Sumayya waisuzo suga Matar Sulaiman......
Oh my god kinga kyawunta ga body Afiya takarashe maganar tana yar dariya, Amira ne tace haba kinsanni bansamu naganta ba duk event din da akayi sabida mutane......
Aikuwa xoki ganta tasowa sukayi itada Sumayya suka leko ahankali suna gulma,komawa Amira tayi tareda Sumayyan...
shiyasa Yaya yaketa rawar jiki,gaskiyakam babu laifi masha Allah......
Sumayya ne tace"Ina kyau anan nikam batamin kyau ba",takarashe maganar tana yatsine fuska....
Kallonta duka sukayi suna mamaki,yayinda takoma ta kwanta Afiya ne tace wallahi ba laifi Sumayya tanada kyau kam babu hassada...
Ku dama inakukasan kyau daga ganima bakar munafuka za ayi,dariya su Afiya sukayi ah tare suna nikam Sumayya kodai son Yaya kikeyine, fadamana man please....
Cumbune baki tayi"Allah yasauwake wallahi,mezanyi da wancan abun",dariya suka dinga mata suna tsokanarta daga karshe tatashi ta tafi gurin Asma'u tana"kukam zaku iyasamin hawan jini wallahi"....

***
Talatu bayan takoma gurin Magajiya tace"Uwargijiyata nabata takarba kuma"......
Murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace, Almustapha taka takare, you'll never be successful indai ina numfashi ah doron kasan nan.......
Duban Talatu takuma yi sannan tace,banason asamu matsala kitabbatar yarinyarnan tasaka abunnan acikin shayin kinajina?....
gyada kai Talatu tayi sannan tayi godiya tafice......

Wuraren karfe takwas nadare ta daidaici dawowan Mai Martaba daga masallaci kafin yakoma fada tana wani tunaninta, ahankali kuma tatashi tafita bayi nabinta donyimata rakiya harzuwa bangaren Mai Martaba yayinda su suka tsaya daga waje......

Yana tsaye yana shirin cire riganshi na sama tayi saurin karasowa tashiga ciremishi cikeda kisisina,yagane ta don yaga zoben hannunta don haka yadan tureta,cikin sauri takuma sa hannu sannan tafada jikinshi tareda rungumeshi ta baya"kayi hakuri don Allah Mai gidana kadaina fushi dani"....
Sa hannu yayi yakuma tabuketa daga jikinshi sannan yajuyo yana kallonta"I'm not in the mood to talk to you gwandama kikwashi kafafuwanki kitafi".....
Kukan munafurci tafara sannan takwantar dakanta ah kirjinshi"don Allah fa nace,nasan nayi kuskure kuma gashi nayi nadama kayafemin don Allah bazan iya jure fushin kaba"..
Batareda yadamuba yace seyanzu kikasan bakiyi daidai ba?....
Goge kwallarta tayi tana kisisina"Allah tunranar nagane laifina sede naga you're always busy shiyasa banzo nasame kaba nace barina bari agama bikin nan dai"..
Dagata yakuma yi ajikinshi yana"kinbaridai seda kika sallami bakin ki badai niba so stop acting"....
Marairaicewa tayi"Allah dagaske nike kayi hakuri bazan kumaba",jinta dameshine yace nifa yawuce daman bam rike kida komaiba Magajiya...
sa hannu tayi takamo fuskarshi tana kallon cikin idanunshi"Amma ai gashi idanunta sunnuna bakayi farin ciki da abunda nayiba"......
Yes banyi farin cikiba because nayi tunanin keme sona ne kuma meson abunda nikeso koban fada mikiba yakamata kitayani murna ai.......
Hawayene suka shiga shatata ah fuskarta tana kallonshi tareda sake bashi hakuri wai bazata sakeba,rantane yabaci ranar and kasan in raina yabaci daman haka nikeyi but I'll correct my mistakes zaka gani and you'll be pleased with me...
Murmushi yayi sannan yashiga goge mata kwallarta"it's okay Magajiya yawuce",cikeda jin dadin tasamo kanshi ta rungumeshi tanayi mashi godiya.....
****
Tunda tashigo gida take leka kitchen minti minti kozata ga sanda za a hada tea din amma shiru don ta lura bayin ma
wasu harkokin suke baki dayansu,abunda bata saniba shine akan kawo musu abinci daga kitchen din masarauta ne sekuma sometimes insu sunaso se Mom tadafa dakanta kokuma tayi directing bayin suyi mata tana monitoring dinsu sabida wani sa'in abincin da ake kawowa baswa ci...
Yanzu zaryanta zuwa kitchen yafi saugoma, Sumayya ne tace yau lafiyarki Asma'u kinata fita kina dawowa,do you need anything?..

Jijjiga Mata kai Asma'u tayi sannan tace babu kekam,don Allah ta ina dakin Yaya Almustapha yake?....
Mischievous kallo Sumayya tayi mata tana"ehhhhhn dama abunda kikeson tambaya kenan shine tundazu kike wahalar da kanki?".....
Allah bahaka bane Sumayya, I'm just asking,dariya Sumayya tayi sannan tace yana gefen na Dad by the right.......
Godiya tayi mata sannan tasamu guri tazauna tana wasa da hannunta itakadai tana contemplating tajene ko kada taje......
Yana kwance ah dakin yadan jingina da pillown shi yana dan dube dube cikin littafin dake rike ah hannunshi dukda kuwa he's ready for the exams bayason wani abunda zaiyi going wrong this time around gashi 8:00am ne exams din........
Jiyayi anyi knocking ah jikin kofar shi seda meshi takuma knocking wajen sau uku sannan yace"come in",shima dakyar ......
Afiya ne dataketa kumbure kumbure tashigo hannunta rikeda tray dauke da black tea akai ta ajiye mai kan yar karamar table tana gashi Yaya Almustapha.....
Ko kallon inda take beyiba kuma daman batayi expecting wani serious answer daga gareshiba,seda tafita tashiga mita ita kadai"yanzu shi yanaji inata knocking daman idanunshi biyu amma yaki cewa inshigo,haushinta daya yace bayason bayi suna shigar mai daki so koma miye za akawomai abasu su sukawo yanzu they've to be enduring this tunda agidansu nadakam baya rufe kofar dakin ma don koya rufe zafi zai addabeshi tunda babu arzikin fan nanko ga AC dole yamusu kinibibi,tana cikin mitarne suka gwaru da Asma'u...

Asma'u ne tace lafiyarki Afiya?.....
turo baki tayi tana nida Yaya Almustapha ne wallahi,nakai mishi tea yanaji inata bubbuga kofa amma yaki kulani,cikeda damuwa Asma'u tace yakarbi tea dinne?.....
Gyada mata kai tayi,kekikayi tea din?...
Aa daga cikin gida akayo tanabata ansa tayi shigewarta cikin dakin Ummi,dasauri Asma'u tayi hanyar dakin cikeda damuwa batareda tayi sallama ba ta bankada cikin dakin wannan karan ah zaune yake jikinshi sanye da wando sekuma singlet fara hannunshi rikeda tea din yakai baki............
Batasan sanda hawaye suka fara bin kuncintaba...




Vote
Comment
Share!...
[3/23, 5:41 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA* ...



Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad....

*page 31*......


Ahaka harsuka isa bangaren Magajiya tun daga bakin kofa bayin keyi musu iso har suka shiga dakin da take...........

Kwance take kan makeken royal bed dinta yayinda hannunta se sanye da drip wanda yanzu na uku kenan da aka saka mata tsakanin jiya dayau sannan likitan yace ah tsanmaci yau zata iya tashi tunda akadawo da Magajiya bangarenta Talatu ke tareda ita bini bini dukda kuwa matar bata farfado ba........
Koyanzu ma tanazaune gabanta ne ah kasa tana hawaye sosai take tausayin Uwargijiyartata jin anyi announcing shigowar su Almustapha ne yasata saurin tashi tana hawaye sannan tagaidasu tafice abunta kallo Asma'u tabita dashi na tausayi don daganinta dole kasan sunyi matukar shakuwa da Magajiya din zama sukayi ah kasa kan kaceme ancika su da kayan motsa baki.........
Duban daya daga cikin bayin Asma'u tayi tace"yamai jikin?".....
"Dasauki Gimbiya sede haryanzu bata farfadoba".....
Allah yabata lafiya cewar Asma'u din kafin tadubi Almustapha dake gefenta yayi shiru hakanan bece komai ba kuma suna cikin haka Magajiya ta bude idanunta ahankali tana karema saman dakin kallo tanason tuno maiya faru hakanan tanason sanin inda take yanzu...........

Lokaci guda kuma kwakwalwarta ketuno mata kalaman Sama'ila"Almustapha yayi aure,ya auri wancan yarinyar", bugun zuciyarta ne yakaru gawani kaikayi da takejin jikinta nayi sosawa takesonyi amma gabadaya jikinta babu kwari daya daga cikin baiwar ne takarasa gabanta cikeda damuwa tace"sannu,Ina keyi miki ciwo ko inkira likitan ne?"......
Kallonta kawai Magajiya keyi don ita haushin yarinyar ma takeji wai ace yau itane abun ayima sannu ma ganin taki takulata sekawai yarinyar tace kinama da baki takarashe maganar tareda nuna direction din da su Almustapha suke kallon wurin Magajiya tayi jiki ba kwari......
Ware idanu tayi cikin sauri hakanan bakinta na karkarwa tana son yin magana amma yakasa fitowa tsabagen shock Asma'u dake kallonta tadan ji tausayin matar seta sakar mata murmushi tareda tashi zataje wurinta don ganin yanda hankalinta yatashi lokaci guda may be she can compose her......
Jitayi anriko hannunta cikin sauri juyowa tayi tana kallonshi cikeda mamaki tashi yayi tsaye still hannunta na cikin nashi sannan yajuya yafara tafiya......
"Let me go,ba dubata mukazo yiba kabari ingaida ta mana"kin sakinta yayi sema janta dayacigaba dayi.....
Ganin tana shirin janyo mishi jama'a yasashi samun wani lungu yaturata"kabarni nikam inacewa Abba yayi muje mudubata"....
Matseta yayi jikin bango tareda daura hannunshi kan bakinta"kimin shiru!"....
Yayin maganar cikin husky voice dinshi,aikuwa lokaci guda tayi shirun tana kallon yanda idanunshi yasauya kala lokaci guda don kuwa haushinta yakeji miyasa zata damu harta tada hankalinta akan Magajiya ina tasanta,she knows how cruel she's tunda Dad yabata labari then "why is she doing all this?".....
Nayi Allah,bazan sake maganaba tayi maganar ahankali......
Sakinta yayi tareda dan ja baya, ajiyar zuciya tasauke tareda barin gurin cikin sauri shima bayanta yabi suka koma bangarensu.....
Magajiya kuwa ganin abunda Almustaphan yayi jitake kamar zuciyar ta tayi boasting "what's going on in this palace,mezata gani Almustapha nefa well dressed cikin kayan sarauta ga yarinyar da aka Kira da matarshi ma hankalinta kwance"........
Lumshe idanunta tayi wani irin kututun bakin ciki marar misaltuwa ya ziyarci zuciyar ta. .....
Aranta tadinga fadin'i can't let this happen,basu isaba wallahi babu wanda ya'isa yaja dani"....
Wayannan wune abubuwan data dinga rayama zuciyarta kenan...........

****
Cikin sati guda jikin Magajiya babu laifi don kuwa tasamu sauki sosai tunda har tanadan samu tafita tayi normal abubuwanta dukda bakaman da ba sede wannan kaikayin jikin bebarta ba haryanzu kuma Mai Martaba ya yafe mata yace takoma normal life dinta sede bayason takuma yimashi mistake din datayi tunda yanzu tabarshi da asara dole shine zai sake neman wani kudin ya bayar ayi aikin dashi..........

Cewa tayi to kawai don kuwa cikin ranta Allah kadai yasan abunda take kintsawa.........

Mallam Audu kuwa tuni Hajiya Muniba tasake shi ganin yanzu Magajiya ta tsaida maganar nemanshi tunda ma abun gabanta sun isheta, she's just waiting for the right time to expose Magajiya........

Bangaren Asma'u kuwa tun ranar takoma asalin dakinta bayan Almustapha yabata keys she's now living a new life with new people batada wani goal daya wuce ta farantawa Ummi dakuma ahalin Almustapha baki daya,tamayar da cinsu da shansu aikinta don kuwa bata yarda akawo musu abinci daga kitchen din masarautar ita takesa ayimusu under her guidance wanda hakan yasake janyo mata so daga surkanan nata bangaren Ummi kuwa kullum seta fitar da ita dayanma sunje garden kaman da she enjoy spending time with her tana kallonta amatsayin mahaifiyarta hakanan amatsayin companion jiyama Sulaiman kecemata Malamin dazaizo ganin Ummi yace ranar asabar zezo yadawo daga tafiyar dayayi...
Bakaramin dadin wannan labarin tajiba donkuwa tanason sanin matsalar Ummin tanason taga ranarda Ummi zata budi baki tayi magana hakanan tanason ganin ranar da zata tashi da kafafunta tayi tafiya kamar yanda kowa yakeyi.............

****
Wuraren ukun dare tafarka yau jawo wayanta tayi ahankali sannan tashiga kiranshi as usual yanda takeyi kullum..........
Ringing yayita yi bedauka ba massage tayi mashi da ..

_"katashi kayi ibada Yaya_ _Almustapha,kakai kukanka gurin ubangiji"_

Turawa tayi sannan tacigaba da kiiran nashi babu kakkautawa daga karshe ma kashe wayar yayi yar murmushi tasaki don ita daman hakan takeso because dataji ya kashe wayar hakan na tabbatar mata da idanun shi biyu kenan muddin yatashi kuma zuciyarta tariga ta amince dashi tasan zaiyi abunda tace din.......
Tsaki yabuga jin tafara kiran nashi kaman wani kayan maita dakyar ya iya bude idanunshi ya karanta massage din nata besan miyasa tun ranar datafara kwana dakin ta take mishi thesame thing dukda kuwa betaba yimata reply ba kullum sede yagaji da jin kiran nata yakashe wayar inkuma yakoma zeyi bacci seyaji yakasa yin bacci,seya tsinci kanshi da tashi yanayin abunda tafada mishi din......

Hakanan kuma kwanan nan yakejin shi wani daban,hakanan yakejin wani kwanciyar hankali Kuma yakejin kaman anasauke mishi wasu abubuwa masu nauyi ah zuciyarshi tabbas ya yarda babu abunda yafi ibada sa kwanciyar hankali dakuma kwantar da zuciya dakuma saka bawa yarda da cewa babu kaman Allah and he'll always stand by you no matter what.........
Yanzu ma baikoma baccin ba haka yatashi yadauro alwala yatada sallah bashi ya tashiba daga kan sallaya seda yaji ana kiran sallar asubahi nan yafara shirin tafiya masallaci kuma......

Seda yabi ya bubbuga masu Amira kofa as usual sede Afiya ne taiya cewa muntashi Yaya,daganan yawuce masallaci abunshi koda yadawo kofar still arufe take hakanan kuma yanada tabbacin basuyi sallar ba haryanzu bubbugawa yashigayi ranshi bace yafi 3minutes yana buga kofar kafin Amira tazo tabude wani irin harara yabita dashi wanda yasa duk baccin dake idanunta suka wartsake lokaci guda"kunyi sallah?"........

Cikeda tsoro tace yanzu zamuyi Yaya,tureta yayi tareda karasawa cikin dakin yana kallon Afiya dake kwance tana shatata bacci haryanzu"Afiya!"yakira sunanta cikin wani irin tsawa jikina bari tatashi zaune dabas akan gadon"bakiyi sallah bako?".....
Kame kame tafarayi.....

Ranshi bace yace"yaushe kuka fara wasa da sallah akan lokaci,when?",yayi musu tambayar cikin tsawa don kuwa shidai yasani ko ah rayuwar talaucin su suna sallah kan lokaci abu dayane baswayi shine zama suyi addu'a kokuma yin nafifilu amma kwata kwata yanzun sun canza.......

Batambayar ku nakeyi ba?......
Mu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ryar Afiya na stammering batasan sanda tace"bamu kwanta dawuri baneba?"......

Karasawa yayi gaban gadon yayi...
"meya hanaku yin baccin dawuri,danne dannen waya ko, social media ke destracting naku this days ko?"......

Girgiza kai Amira tayi alamun a'a,cikeda bacin rai yace where are your phones?.......
Hakuri suka shiga bashi cikin tsawa yace ba magana nake muku ba?....
Haka suka kawo wayoyin suka bashi jiki ah sanyaye duk tsoron shi yagama shigansu karba yayi sannan yace and the laptops?......
Kallonshi Amira tayi don da tayi tunanin laptop dinta will survive inma wayar batanan atleast zatasamu na kallo...
"Kayi hakuri Yaya",cewar Amira Afiya ne tace"please".........

Batareda ya kalli inda suke ba yakarasa gefen gadon inda yaga laptops din na ajiye daya ansaka shi ah chargi haka yacire ah charging yahada dayan yayi hanyar barin dakin ah bakin kofa yaganta tsaye dauke kanshi yayi yafice daga dakin rabonshi da ita almost three days now dukdama koya gantan ba magana sukeyima junaba daman........

Shiga dakin tayi tasamu guri tazauna tana ganinsu kowa rai jagule suka shige bandaki sukayo alwala sukazo sukayi sallah.........
Seda suka idar sannan tace"I'm sorry on his behalf dukda ma kuma kunada laifi".......

Dagowa Afiya tayi tana kallonta tace"miye laifin mu Sis,muma bayin kanmu baneba nikaina bansan miyasa nike makara sallar asuba yanzuba"......
Murmushi Asma'u tayi sannan tataso daga inda take tadawo gabansu tazauna"sanda kuke rayuwan da karfe nawa kuke bacci Amira?".......

Dan shiru Amira tayi tana tunani sannan tace wataran taran dare wataran kuma goma that's if bamu kwanta dawuri ba......
Yanzufa, Asma'u tasakeyimusu tambayar tana kallonsu.....
Wannan karan Afiya ce tace"inmunyi bacci dawuri 12:00am don wataran nakan Kai 3:00am Ina kallo ah laptop kafin na kwanta" .. ......
"Do you now see the difference", Asma'u tayi musu tambayar tana Smilling.. ..
Nidai bangane ba Sis Amira tayi maganar tana kallon Yar uwarta kafin Afiyan tace nimadai bangane metake nufiba.............

Kamo hannunsu tayi su duka biyun sannan tace kuyi hakuri in abunda xan fada zai bata muku rai but atleast I feel it's right to remind you people inajinku kaman yan uwana na jinine wallahi.......
Cikin sauri Amira tace"shhh don Allah kifadi abunda yake ranki we're now families,in mu ba yan uwa bane ada yanzu Yaya Almustapha yayi strengthening bond dinmu"..........
Nagode da fahimtata dakikayi Amira,ni anawa ganin rashin baccin ku dawuri ne yake hanaku tashi sallar asuba tunda ada kunayi din bawai bakwayiba sannan inaganin yakamata kurage kallon nan sabida bashine gabanku ba you two have alot of things dayafi kallon nan besides what will you gain by doing that?......
Inma chats kukeyi mezakuyi gaining ayin chat din,nibance karkuyi chat ba hakanan bance kada kuyi kallo ba tunda nima inayi sede you people have to use your time wisely abunda nake nufi anan shine indai kallo zaiyi destracting naku daga addinin ku to miye anfaninshi?......
Set your time wisely,kowani aspect na life dinku kubashi time dinshi daban yakamata ace ibadan ku yakaru ne bawai yaraguba dubada halin da kuke ciki dakuma halin da Ummi take ciki, she's so sick yakamata kunayi mata addu'a ne,yakamata kudinga addu'a Allah yasa hankalinta mahaifin ku yadawo kan mahaifiyarku, Allah kuma yasa asirin wanda yacuce ku yatonu,I think this's what you people have to focus on sede nalura ku abunda yazama muku dole kukeyi we've to change please tayi maganar tana hawaye.......
Cikin sauri Afiya take kuka ta rungumeta tace"mungode da shawarar ki Asma'u in Sha Allah zamu gyara,sede kisani bawai munada ilimin addinin sosai bane muntaso cikin wahala tabbas ansaka mu ah islamiyar sede babu wanda yadamu da munje ne ko bamujeba,inmunje dinma wataran koromu akeyi muzo muyi aiki daga boko har islamiyar sanin damukayi din kadan kadan ne Asma'u sannan munfi bada kwari gurin bokon don ah tunanin mu shine zai taimakemu har muzama wani abu daban ah rayuwa mutaimaki Ummin mu,babu maice mana abunda mukeyidin badaidai bane,babu kuma wanda yadauramu akan hanya besides wama mukedashi? Afiya tayi maganar tana goge kwallart sannan takara da shi wanda mukedashi din shima bawai yanada lokacin mu sosai bane sannan koyi muke dashi don abunda yayi shi mukeyi Kuma shima kada kiga laifinsa yatashi cikin rashin gata,yakuma tashi cikin kuncin rayuwa Wanda yasashi manta menene daidai dakuma wanda badaidaiba,abubuwa sunyima kwakwalwar sa yawa sake damke hannun Asma'u Afiya tayi"Yaya Almustapha yanada sanin addini sabida tunyana karami yayi sauka hakanan yakaranta litattafai dadama at his young age ayanda naji,kawai kuncin rayuwa dakuma rashin sanin yakamata ne yamaida shi haka and he was so young to know what was right and wrong harma yafada ma wasu shiyasa yatashi ahaka,ajiyar zuciya takumayi but now Yaya is getting what he deserve,yadawo cikin daular mulki sede baya cikin farin ciki he need some love,he need to be happy and only you can bring happiness to his life Sis,I trust you"........

Tapping bayan Afiyan Asma'u tashigayi cikeda tausayawa tace"I'll make him happy Afiya, I'll make him the happiest man on Earth I promise takarashe maganar Itama tana hawaye me tsuma zuciya,sede inason kuma kuyimin alkawari zaku gyara halayenku sannan zaku nemi ilimin addinin ku sabida shi ilima bakana zaune ne zaisamoka ba kaine zaka fita ka nema....

Insha Allah suka amsa mata atare sannan Amira tace zamuyima Yaya Sulaiman magana yanema mana Malami Yana zuwa gida yana mana karatu kawai,kuma yanema mana Islamiya.......
Murmushi Asma'u tayi"zannema muku Malami wanda xenayi muku karatu agida inyaso Yaya Sulaiman din seya sama muku islamiyan"......
Godiya suka shiga yimata cikeda jin dadi kafin tafita tawuce kitchen don gari yayi haske already tasan su Hindatu sunfara aiki............
****
Tare suka fito daga bangaren Magajiya babu laifi yaudin tadan sakarmai fuska tunda harta ta'iya ta ansa gaisuwar sa duban Zaliha yayi sannan yace"zanje gun Yaya Almustapha i heard that result dinsu is out inason infada mishi"....
"To Allah yakiyaye".
Da Amin ya amsa mata haryajuya zaiwuce sekuma yadawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login