Showing 15001 words to 18000 words out of 235422 words

Chapter 6 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3532

din da 'dan yatsanshi cikin maye yana "Kai,ni sa'an ka ne?"......
Jin muryarshi ne yasa Sulaiman din saurin juyawa nanko yayi arba da 'Dan uwanshi,mutsutsuke idanunshi yakuma yi don ya tabbatar da abunda idanunsa yagane masa aikuwa shidinne cikeda tashin hankali yayi kanshi yana Yaya Almustapha meyakawo ka nan?...
Subhanallah what the hell are you doing here,yayi masa tambayar cikeda tashin hankali don inkwana wani zeyi yana fada masa yaga Almustapha ah irin wannan gurin to bazai yarda ba, Almustaphan ne cikin rashin karfi yadan ture Sulaiman din dakyar ya iyacewa "waye kai"...
Cikeda tausayawa Sulaiman din yadaga shi yana zillewa har suka isa mota sakashi yayi ciki sannan yarufe motar yakoma ciki don biyan kudin, nawane kudinka yayima Bar Man din tambaya Kai tsaye......
Dubu goma, hararanshi Sulaiman din yayi sannan yaciro kudin yabashi don baida lokacin sa insa da shi, "Allah dai ya sauwake yan gida daya da jarabar shaye shaye,niko uwarku yazataji?"......
Cikeda bacin rai Sulaiman din yadawo tareda shake wuyanshi"dawa kake?".....
Cikin jin zafi Bar Man din yace badakai nakeba wallahi,tsaki Sulaiman din yayi sannan yace"ka iya bakin ka wallahi"....
wallahi na iya baki na daga yau Bar Man din yafada yana haki sakinshi Sulaiman din yayi yafice, nankuma yarasa inazashi don kuwa bayason shiga da Almustapha gidansu cikin wannan yanayin
don haka seyaje dab da masarautar yasamu wani dan lungu yayi parking sannan ya kishingida jikinshi ah jikin kujera besan sanda bacci yayi awun gaba dashiba shima, Almustapha ne yafara tashi wuraren hudun asuba mutsutsuke idanunshi yayi yanason yagane ah Ina yake mamaki yayi sosai ganinshi acikin mota sekuma ahankali yafara tuno abunda yafaru,sa hannu yayi yashiga bude murfin motar sede kirip arufe motsinshine yatashi Sulaiman,dasauri yadube shi tareda tsallakowa bayan da Almustaphan yake"are you okay Brother?".....
Shiru Almustaphan yayi sannan bedago yakalleshiba.....
taba jikinshi Sulaiman din yayi cikeda damuwa seyaji babu zafi kuma,komawa yayi yajingina jikinshi da jikin kujerar yace
"I'm sorry naganka in that state,but I'm so disappointed Brother,innnine nayi abu haka is okay but as for you I can't believe it"..........
murda kofar Almustapha yakuma yi sede haryanzun ah rufe take, murmushi Sulaiman din yayi don yasan hakan da Almustaphan yayi yanason yabude mishi motar ne yafita......
Sorry na shiga abunda bai shafeniba,sede ba laifina bane namanta cewa Yayana bedauke ni abakin komai ba infact he never sees me as his very own Brother......shaaa I'll let you go yakarashe maganar murya ah karye sannan yabude motar babu bata lokaci Almustaphan yabude yafito dasauri Sulaiman din yashiga gabanshi tareda da rungumeshi yana furta "it's been long Bro, atleast I should get a brotherly hug mana"......
Seda yasakeshi sannan yajuya don shiga motar, Almustaphan ne batareda ya juyoba yace "wait"....
Cak Sulaiman din yatsaya yanajiran jin mezaice sekuma yaga yayi gaba abunshi batareda yace komai ba jijjiga kai Sulaiman din yayi tareda sakin murmushi"don't worry Brother I won't tell anyone,lumshe idanunshi yayi "secret!"....sannan shima yashige motar don komawa cikin masarautar......
*****
Tunda safe dayaje gaisheda Magajiya ta titsiyeshi"Sulaiman inakaje jiya da daddare?".....
'dan Sosa Kai yayi nikuma Mama,badai niba gaskiya wawan harara tasakar mai" nasan komai Sulaiman,kada ma kayarda kace zakamin karya sannan inayimaka gargadi kafita harkan yaron nan inba sokake raina ya baci ba Kuma duk wani abunda zakayi kayi shi cikin masarautar nan domin fitanda kanayi awajen yazama kaman cin mutuncin masarautar nan ne dakuma zubar da kimanta as the air to the throne.....

To Mama abunda ya iya cemata kenan sannan yafice yabar shashenta cikeda tunanin ya akayi tasani,indai haka ne dole tana da spy,spy dinma masu bin Almustapha fa, tambayar kanshi yashiga yi to mesukeso?........

Bayan fitarshine Magajiya tashiga Kiran Laure,cikin sauri tazube agabanta"gani uwargijiyata"......

Kicema talatun tafada ma Hilu yau zamu fita da dadddare.....
To in Allah ya yarda zan fada mata,tashi kitafi... to uwargijiyata .....

*******
Yau Monday Kuma yaune zasufara fita registration shiyasa tunsafe tagama ma Ummin ta aikinta sannan tashirya cikin doguwar abaya tayi veiling wanda bakaramin kyau yayi mataba babu wani make up datayi inbanda lip gloss datasaka, Asiya kuwa anyi kwalliyar nan kaman wanda za aje dinner ko wani event haka suka shige mota don tafiya inda Aliyu ne zekaisu tunda bayida abunyi yaudin.........
Tunda suka shiga makarantar suke processes na registration din haka ranar suka yini zubuk cikin makarantar koda suka dawo gida agajiye suke Kuma wai ahakan basuma gama ba,seda sukayi sati daya cir suna registration kafin suka samu suka gama, Allah yataimakesu ah first week sukayi sunada time din hutu the other week kafin afara lectures Kuma.........
Suna dan hira da Ummin ne washegari takecewa yauwa Ummin nikam nahadu dawani Mukhtar wai yasanki....
Ummi dake gyaran wake tace ah ina Kuma kika hadu dashi?...
Wani Mukhtar? Ummi tayi mata tambayoyin ajere..
Dan Gombe ne Ummi wai su makotan ku ne acan yasansu Hajiya da Baffa duka family members fa ashe shima anan yake Medicine yanama aji biyar.......
Habadai, Allah sarki Mukhtar daman anan yake karatu bansaniba,nasanshi wallahi yaron gidan Alhaji Bala neighbors din mu. kice yaro yagirma he was at his young age sanda nayi aure fa....
Dariya Asma'un tayi Kai Ummi, yanzu kan yagirma yazama dan gaye dashi wai baisan ah garin nan kike zamaba yayi azan ah kaduna muke......
Allah sarki anan mukeda zama yanzukam yazo ai,eh yace zezo wai daga kamar mu yagane ni yace duk yanda akayi wannan Yar Adda Maryam ne.....
Ayya yaron kirki don Allah kigaidaminshi kuma kice inaganin zuwan shi...
Insha Allah zanfada mishi
Haka sukacigaba da hira duk akan Mukhtar din da mutanen gidansu tana bata labarin rayuwarda sukayi abaya can tunkafin tayi aure......
...
Tunranar da Sulaiman yasamu Almustapha ah club basu sake haduwa ba hakanan befada ma kowa ba dukda kuwa atunaninshi Magajiya tasani,yauma sanye yake cikin alkyabbar shi yayi kyau sosai suna shirin fita da mai Martaba zuwa kauyikan dake yankin Zaria dukda bawai yanason zuwa bane sede bazai iya yima Mai Martaba musu ba......
Yau kwanansa biyu behadu da Yayartashiba yar murmushi yayi sannan yayi bangarenta as usual tana kwance yayinda kuyangu namata fifita se Afiyya dake yimata tausa tunda Hamida tahangoshi take washare baki,seyau kasan hanyar inda nake....
Sa hannunshi duka biyu yayi ah kunnuwanshi I'm sorry Sis,tuba nike....
Afiyya data ganshi takasa boye excitement dinta "Yaya Sulaiman".....
Kallonta yayi yanason ganeta, ahankali yace Afiya?...
Irin he's not sure dinnan, murmushi tasakar mishi yayinda ta tashi da gudu tafada jikinshi Yaya Sulaiman yaushe kadawo?....
Hugging nata back yayi sannan yace little Sis kinanan,kece kika girma haka ina little Amira yashiga jero mata tambayoyi babu kakkautawa....

Tana gurin Ummin mu,munyi kewanka Yaya Sulaiman,dan shafa kanta yayi nima nayi kewarku sosai I missed those days danake zuwa gunku ah boye.....
Dan goge kwallarta tayi don bakaramin farin cikin dawowanshi taji ba he's indeed a caring Brother kwata kwata tama manta ah dakin Hamida take shima Sulaiman din haka seda tayi musu magana cikin masifa, Sulaiman hankalinka daya kuwa kekuma mahaukaciyar wace garice?...
Kinamin tausa zaki tashi?....
Dasauri Afiya tajuya gareta cikeda nadama don duk tsiwarta tana tsoron Hamida don ba karamin aikinta bane ta hada ta da Magajiya don haka tashiga magiyar bada hakuri.......

Kama hannunta Sulaiman din yayi sannan yakarasa gaban gadon da Hamidan take yazauna Itama yazaunar da ita wani ihu Hamidan tayi yazaka barta tazauna min kan gado banason shashanci Sulaiman, murmushi yayi sannan yace ma sauran bayin sufita seda suka fice sannan yadubi yayarta shin yanzu Sis abunda kikeyi kin kyauta kenan?...

Harararshi tayi danayi mefa?...
dakika mayar da kannen ki bayinki,cikin tsawa tace niba kanne na bane wayannan yan iskan inkuma maganar dazakayimin kenan katashi kafita kabani guri,kallonta yayi cikeda disbelief sannan ya girgiza kanshi Allah yasauwake,yakawo ranar dazaki gane Adda Hamida.....

Tsaki tayi batareda tace komai ba yayinda yakama hannun Afiyan, ahankali tacire hannunta cikin nashi don seyanzu talura zata iya jazama kanta magana dama shi Sulaiman din juyowa yayi yana kallonta,gyada mishi Kai tayi alamun yatafi she'll handle everything....
Are you sure?...
Kuma gyadamai kan tayi,duba wristwatch din hannunshi yayi ganin time nakurewa kuma yace zamu fita da Mai Martaba anjima zanzo ingaida Ummi in Allah ya yarda......
Allah ya kiyaye...
Amin little Sis....
Nan ya fice yabarta tsaye ah gurin... Hamida ko bakaramin bata mata rai yayiba sannan tadauki alwashin seta fadama Magajiya abunda idonta yagane mata.......

*****
Gabadaya yarasa nayi yaudin don kuwa maganin Umminsu yakare batasha na daren jiya ba gashi babu kudi agurinshi kwata kwata bare yasayi koda guda dayane,daya rasa abunyi kawai seya wuce direct shagon Mallam Hudu kilan yasamu abunyi koya dan samu wani abu yasayamata maganin koda nayau ne kadai kafin asan abunda Allah zeyi kuma nangaba sede to his own surprise yanazuwa shagon Mallam Hudun bayan sun gaisa se yake cemishi ai mutumin dayasaba bada kudin taimako na magani ah asibity yaji yasake zuwa gari Kuma yana bada kudi ah asibity shiyasa jiya dayatashi daga kasuwa yaje kuma ya karba musu, lumshe idanu Almustaphan yayi cikeda jin dadi koma waye wannan mutumin Allah yayi mishi albarka shine kawai abunda zai iya fada,dakyar yabudi bakin shi yace "Nagode Mallam Hudu"...

Murmushi Mallam Hudun yayi sannan yamika masa dubu hamsin din yace ga kudin nan sekuma yakara mishi dubu
goma seka cika kasayi maganin na wata daya kaman yanda akasaba,wannan karan Almustapha rungume Mallam Hudun yayi he's just out of words, Allah yakawo mishi mafita batareda yawani wahalaba,abunda Almustaphan besaniba Sulaiman ne yabawa Mallam Hudu kudin don kuwa yaje yaduba Ummi Kuma yatambayi su Afiya maganin Ummin sesukace masa yama kusan karewa gudun kada yasiyo yabasu Almustaphan yatambayesu ina sukasamu shine yabama Mallam Hudun kaman yanda yasaba yi ada can baya.....
Tunda Almustapha yafita chemist din da suka saba sayan maganin yawuce yasaya sannan yawuce gida don Kai maganin....
******
Yau Monday Kuma yaune zasu fara fita makaranta dukansu sunada 8:00am don haka suka shirya dawuri,sannan Daddy bayan yakuma dawowa daga tafiya yakawo musu tsarabar mota wanda zasuna tafiya makaranta da ita tare bakaramin murna sukayi ba already daman duk sun iya driving don su Aliyu kan koya musu yanzuma sungama yima kowa sallama ne yayinda Asiya ce rikeda key sewani kaudi takeyi haka tayi driving nasu zuwa school seda tayi dropping Asma'un sannan tawuce nata faculty din akan tajirata inta gama nata lectures din zatazo su tafi gida......
Tunda tashiga GST din tamaida hankalinta ga abunda malamin keyi kuma babu laifi tana gane wa sosai don kuwa malamin nada method of teaching sosai koda Malamin yafita seta kasa tashi tana ganin yanda 'yan uwanta keta fita jitayi anmata sallama ansawa tayi tareda kallon yarinyar wacce take kusan sa arta ko ace saartace ma.....

With a beautiful smile yarinya tamika mata hannu "I'm Zahra and you?"....
Murmushi Asma'un tamata tareda mika mata nata hannun "Asma'u, I'm Asma'u Muhammad"....
nice name cewar Zahra din,can we be friends nima sabuwar zuwace and it seems like thesame course mukeyi ko?....
Kallon Zahran tayi sannan tace Okay bakomai,may be we can confide with each other ma amma sede ni MBBS aka bani bansan keba....

Dariya Zahran tayi wanda har seda hushiryarta ya bayyana,nasani nima shidinne ai duk wanda kikaga munyi GST tare yau MBBS yakeyi bakiga bamu da yawa ba?..
Hakane kam Asma'un tabata ansa yayinda Zahra tace se 2:00pm mukeda lectures kuma yanzu 9:30am kinga malamin ma yafita dawuri kozamu dan bikan abunda Malamin yayi mudanyi refreshing kwakwalwarmu.....
Yar dariya Asma'un tayi,kumafa haka ne go ahead....
Nan suka shiga yima juna bayani inwannan batagane nan ba seta fada ma yar uwarta hakadai,kafin kace mai har sun saba kaman wasu kawayen dasuka jima tare...
****
Yau tun asuba talatu tazo gurin Magajiya tana haki,harararta Magajiya tayi miyene kikazomin da sassafen nan?......
Kiyi hakuri Uwargijiyata amma yazaman min dolene inzo infada miki,to miyene kifada mana kinata wani nuku nuku Magajiya tayi maganar rai bace sabida antasheta daga daddadan baccin datakeyi.....

Talatu na haki sabida uban gudun datasha tace Uwargijiyata naso fada miki tun ranar amma nayi shiru ina tsoro sede yau abun yakai inda bazan iya boyemiki ba Yarima Sulaiman ne yayima bayi fyade yau baiwa na hudu kenan da abun yafaru dasu kuma iyayensu sunyi maganar kaiwa Kara gurin Mai Maitaba dukda yaran basu fada musu wayene yayi musu ba shine naji inason in fada miki....

Cikeda tashin hankali Magajiya tace kije kikawo min yara hudun yanzunnan,tashi tayi jiki nabari tafice bayan kaman minti goma segasu sundawo tareda bayin zubewa kasa sukayi suna mika gaisuwa yayinda dayar da abun yafaru da'ita adaren jiya taketa sheshekar kuka cikeda bacin rai Magajiya tace ke dallah yimana shiru kina wani kukan munafurci,kebama abun alfahari bane agareki ace Yarima guda yakwanta dake shasha sha marar wayau,dakyar indo tahadiye kukan datakeyi kamin Magajiya tasamu guri tazauna gyaran murya tayi sannan tace"kubude kunnuwanku dakyau kuji mezan fada muku"...
Jijjiga Kai sukayi sunajinta yayinda tace Laure tamiko mata kullin data ce tadauko miko mata tayi sannan tajefa musu gashi kuje kuraba wannan sannan kurufe bakin ku banason inji shi ah kunnen wani inbahaka ba na lahira seyafiku jin dadi daga ku har iyayen naku....

Jiki na bari sukace to Magajiya zamu kiyaye,tashi kutafi,harsun tashi zasu tafi tace kudawo, dawowa sukayi dubansu tayi irin duban wulakancin nan sannan tace zan neme ku akan al amarin sannan iyayen nakuma aturomin su in rufe bakinsu haka ko akayi iyayenma dasukazo kudi tabasu sannan tace suyi shiru if not zatamusu hukunci me tsanani(innalillahi wainna ilaihir rajiun,lokaci yazo da kudi yazama abun so akoda yaushe wanda har ze rufe ma bawa ido daga ganin gaskiya,duniya inazaki da muya Allah kasa mufi karfin zukatan mu)....

Bayan sun tafine tadubi Talatu"kinshirya abubuwan danasaki yau?".....
Eh na shirya Uwargijiyata da Maimartaba yashiga fada yau da safe zeje yakai karar.....

Jinjina Kai Magajiyan tayi sannan tace to shikenn Allah yakaimu, Amin cewar Talatun yayinda Magajiya tajefa mata wani kulli kudi ne aciki jikina bari Talatu tashiga godiya sannan tafice........

Yau litinin Kuma yauce ranakun da mutanen gari dama na masarautar suke kawo kara ah fada don akarba musu hakkinsu sannan ake yanke hukunci.tun karfe takwas me martaba yashiga fadar masarautar wanda anan yake zama kowace litinin donjin matsalolin mutanensa dakuma neman hanya don magance masu ita.....

Haka duk masu Kara suka shiga kawo wa ana yanke ma masu laifi hukunci yanda yadace dasu har aka iso kan wani bawan Allah kuka yakeyi sosai kamar ranshi ze fita sannan yagaida Mai Martaba ansawa yayi sannan yace yafadi matsalarsa.....
Cikin kuka yace Allah yaja da tsawon kwana Mai Martaba ni talakane me tsoron Allah dakuma neman na kaina,bantaba cutan waniba kaman yanda banason ah cuce ni matana biyu da 'ya'yana goma banida wani hanyar ciyar dasu seta hanyar kiwon kajin danake yi,inada kaji guda talatan Kuma dukansu arana kowannensu takan zuba kwai uku wanda muke fitarwa musayar har musayi abincin dazamusa ma bakin salatinmu kwatsam shekaranjiya semuka tashi babu kaza ko guda daya wani yabiyo dare ya kwashesu bakaramin tashin hankali muka shigaba nida matana inda muka shiga cikiyarsu cikin unguwa nanne wani saurayi yace yaga sanda wani yaro yafito da kaji da daddare yatafi dasu amma beyi tunanin sato su yayiba Kuma yace zegane fuskar yaron don kuwa shima yaje saida nashi kajin jiya se suka hadu bayan yadawo ne yaji muna cikiyar namu.....
Mai martaba yadubi tsohon sannan yace inayaron yake?...

Kiranshi tsohon yayi yayinda saurayin yazo yazube gaban Mai Martaba yana mika gaisuwa, Kallon shi Mai Martaba yayi sannan yace ya akayi kasan kajin na wannan mutumin ne?.....
Ranka ya dade ta hanyar gidan naga yafito Kuma danaje saida kajin na hadu dashi tabbas kaji guda 30 ne don har rokon mai sayarwan yayi kan yasaya amatsayin dubu sittin yanason sayama mahaifiyarsa magani ne don da Mai sayan kajin dubu hamsin da biyar yaso saya.....
kuma bayan nadawo naji labarin satar munkoma da shi Mallam Audun yaga kajin yace tabbas nashine sede sunyi rigima damai saidawan yace bazai bayarba donshi saya yayi se ankawo masa kudinsa......
Maimartaba ne yadubi dogarin dake isar mai da sakon zuwa ga mutane sannan yace wayene aka kama yayi Satan?......

Cikin sauri yaron yace Almustapha ne sunan yaron, Mai Martaba seda yaji gabanshi yafadi amma bece komai ba sema cewa dayayi aje akawo shi nanfa dogaraye suka fice don zuwa kawoshin,nan aka cigaba da jin matsalolin wasu ana bada hukunci kafin akawo mai laifin se acigaba da nasu sunkai minti talatin kafin suka dawo tareda Almustapha don shikam takun kasaita yashiga yi musu dukda zaginshi dasukeyi ah hanya ko kallo basu isheshiba dukda yana mamakin laifin meyayi daza a nemeshi don koda wasa bazaice alkhairi ne ke kiranshiba sanda suka isa fadan seda aka gama dawanda akeyi din sannan aka cigaba da nasu yayinda Mai Martaba ya umarci da afaro daga farko don yaron yaji laifin da ake tuhumarsa dashi har aka iso inda aka tsaya kamin Mai Martaba yace Ina Mai kajin yake, nan aka fito dashi.....
daya daga cikin dogarin ne yace wannan ne yazo yasayar da kaji agurin ka?.....
Babu kunya babu tsoron Allah saurayin yadubi idanun Almustapha yace eh jiya da safe yazo har yarokeni in Kara masa kudi zesayama mahaifiyarsa magani ne.......

Shide Almustapha tunda akafara maganar ko dagowa beyiba bare ya kallesu kanshi nakasa,yariga yasani sharri akeson yi mishi and they've succeeded, wanda yake claiming anyimai satar ne yace har Mai maganin Kam nadauko nan Mai Martaba yace ashigo dashi,se awannan lokacin Almustapha yadago don ganin memaganin tabbas shine wanda yake sayan magani agurinshi,tambayar shi akayi shin Almustapha yazo yasayi magani ah gurinsa....
Jijjiga Kai yayi alamar eh sannan yace yazo yasaya jiya da safe....
Duban mai chemist din Mai Martaba yayi sannan yace nawa yakawoma?....
Dubu sittin ranka shi dade.......
Nan shima aka sallameshi,kallon Almustapha Mai Martaba yayi feeling somehow sannan yace to Almustapha kaji laifin da ake tuhumarka dashi kayarda kayi?......
Almustapha zuciyarshi wani irin Kuna take mishi dabazai iya misaltawaba,mezai ce?bayan anriga anmishi kulla kulla,ta inama zece bashi bane bayan duka ga evidence anfiddo lumshe idanunshi yayi ahankali yayinda bayamason ko kallon inda Mai Martaban yake seyau yakejin wata irin tsana ta wannan mutumin tafara shigan shi har amishi sharrin sata amma bazai iya komai akaiba,tukunnan ma bai nuna yamasanshi ba bare yace akwai alaka ah tattare dasu.kowa yayi shiru ah fadan anajiran amsar Almustapha sede shiru kakeji wurin minti biyar....
Mai Martaban ne yakuma cewa shirun dakayi na nufin ka amsa laifin dakayi kenan ko?......
Nan ma shiru awannan lokacin ran Mai Martaba ya sosu amma seyace nabaka nan da sati daya kanemo ma mai kaji kudinshi kadawo mishi dashi sannan yadubi tsohon yace ka karbi kajin ka tunda besayar ba nan da rana itayau zamu karasa daga inda aka tsaya.........

Batareda yace komaiba yajuya yafita ah fadan dan satan kallonshi Mai Martaban yayi yakasa yarda yaron zaiyi sata dukda bawai saninsa yayiba Kuma abunda yasa yayi mishi hakan yanason yagano gaskiyar al

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login