Showing 60001 words to 63000 words out of 235422 words

Chapter 21 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3487

bata samu ansa me karfi ba don ansar daya ce Yarima ne yasaka su kuma basu san daliliba sekawai tayi tunanin kilan Sulaiman din nada special baki dazai saukar ah gidan shiyasa,sede fa gulmarta bata tsayanan ba sabida sanda taga Yarima yashigo da motar sa zuwa bangaren tayi tashiga leke leken suwa ye wayannan bakin,idanunta yagane mata namiji da mata dakuma kyakyawar mace datayi shigen turawa setayi tunanin bakin Sulaiman dinne sukazo daga inda yayi karatu wannan dalilin ya hanata sanar da Magajiya harda karin ma itakanta tayi mata wuyar gani don kuwa she's very busy cikin jama'a koda zataje gurin Doctor ma dakyar tasameta ta fada mata isowarshi nan tasata yin wani aikin itakuma taje dakanta don acewarta inbataje dakantaba ana iya samun matsala.......
****
Cikeda tsoro tace kiyi hakuri ranki ya dade sabida ni tsarin mu tasake rugujewa Laure takarashe maganar kanta ah kasa don kuwa tun ranar da aikinsu yakasa aikuwa takasa tunkarar Hajiyartata don tsoro takeji harsai da ita Matar da kanta tanemeta......
Sabida aikin baiyiba shine kika ki zuwa kifada min cewar matar tana kallon Laure dake zaune gabanta........
Kiyi hakuri ranki shi dade Lauren tayi magana kaman zata fashe da kuka,babu komai Laure kuma batun aiki baiyiba ninaga zaija mana cikas sabida anriga anga macijin shiyasa nayi saurin daukeshi kada kidamu,cikeda rashin fahimta Laure tace ranki shi dade kina gurin ne?........
Aa bana gurin Laure kede yanzu kitashi kikoma gida in akwai wani bayani dazanyi miki zansake neman ki......
Gyada kai Laure tayi sannan tayima matar godiya sannan tatafi cikeda mamakin yanda macijin ya bace donko taji labarin abakin sauran bayi yan uwanta.......

****
Koda yaje gidansu Almustapha din samunsu yayi ah parlour dukansu yayinda Ummi na daki,dubansu yayi sannan yace nifa bazama nazo yiba Dad yace inzo indaukeku mutafi gida,wani kallo Almustapha yayi mishi don baigane inda yadosa ba, murmushi yayi sannan yakarasa gaban Almustaphan "Yaya Almustapha insha Allah daga yau wahalarku takare, we're going home now,I mean you people are going to be like us and we're going to live as a family from now on", Sulaiman yakarashe maganar fuskarshi na nuna tsantsan farin cikin dayake ciki.......
Amira dake gefene tace dagaske kake Yaya Sulaiman,kana nufin Mai Martaba ya karbe mu ah matsayin ya'yanshi?.....
Gyada mata kai kawai yayi don ganin yanda tayi maganar with so much hope shikuma bazaiso ya ruguza mata hope dinba,wani irin dadi taji har cikin ranta kafin tashiga tsalle harda hawaye wani harara da Almustapha yayi mata shiyasakata nutsuwa kallon Almustapha Sulaiman yayi sannan yace "if you can stop her from jubilating ah fili bazaka iya hanata ba azuci Yaya Almustapha",katashi mutafi gida everyone is waiting for you, Afiya can't wait to see you......
kai tsaye Almustapha yace"I'm not going anywhere",sabida shi babu wata farin ciki dayayi da zancen don azuciyarshi cewa yake after all this years seyau ya tuna dasu,after all the humiliation seyau yasan su Ya'yansa ne,babu abunda yahanashi rayuwa da babushi dinma dukda kuwa walakanci dayadinga sha behanashi surviving ba and he believes that he'll always move on dayar dar Allah.......
Bata rai Sulaiman yayi jin kalaman Yayan nashi"haba Yaya yazakayi irin maganar nan don Allah,koma miya faru he's your Father besides inbakaje donshiba aiyakamata kaje don Uncle Almustapha.......
Hmmm kawai yace kafin yashiga tambayar kanshi wanene Uncle Almustapha ma, kwakwalwar shi tashiga tunomishi dacan baya tun yana cikin gatansa,tun lokacin da kullum yake makale da mahaifinsa yakan ji labarinsa abakin Mai Martaba donkuwa babu ranar da zatazo ba a ambaci uncle Almustapha dinba,kallon Sulaiman din yayi yana tunanin yaushe shi uncle Almustapha din yadawo,sede besamu ansa ba sema tashida Sulaiman yayi yawuce dakin Ummi yana inbazakaje ba mukaga tafiyar mu aikoba komai kayi biyayya ga nagaba dakai,ko kula Sulaiman din baiyiba sesanda suka fitar da Ummi din zuwa mota Amira ma tadawo tadauki yar bag dinta tafice,duk yana ganinsu yariga yayi making mind dinshi and no one can change it,batun mahaifiyarsa da kannensa kuma he'll surely come for them............




Vote
Comment
Share!
[3/23, 5:28 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*


Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 18*.....


*****
Seda ya tabbatar kanin nashi yayi bacci sannan yakoma bangaren nasu,ah parlour yasamu Afiya da Sumayya suna sanye da hijabi Sumayya nata damun Afiya kan suje sugurin Mai Martaba, Afiya kuwa tsoro takeji don haka tacemata tabari se Dad yazo.......
Aikuwa ba ajima ba segashi yashigo dagudu Sumayya ta tashi tayi gurinshi tana Dad kaga Afiya ba tundazu nace ta tashi muje mugaida Uncle Abdulrahman taki, Sulaiman dayanzu shigowanshi yana turo wheel chair din da Ummi kekai yace "point of correction,Abba akecewa"....
Dariya Dad da Afiya sukayi yayinda Afiya tatashi aguje tayi gurin Ummi, Ummi dake kan kujera dataga yartata Itama zakaga canji ah fuskarta alamun she's so relieved.....
Sumayya ne tace Yaya Sulaiman ramawa kayi ko?, murmushin kawai yamata yayinda yajuya gun Amira yana miyene kike rakubewa kamar munafuka,lekowa tayi ahankali cikeda nervousness wannan karan Sumayya ne taganta dariya tayi mata yayinda takarasa gabanta tareda kamo hannunta"Amira miyena buya kuma?"....
Jijjiga ma Sumayya kai Amira tayi yayinda hawaye suka fara bin kuncinta ita kanta tarasa na menene,she just can't believe zata kwana acikin wannan makeken gidan me dauke da daular kaya kala kala,goge mata kwalla Sumayya tayi yayinda Afiya tazo ta rungumeta tana hawayen Itama"nayi kewarki Amira,I missed you so much!",takarashi maganar cikin muryarta dake rawa.........
Dad dake gefe ne yace to sad moment ya isa aidai kyabarta tazo ta gaisa da Dad ko?....
Murmushi kawai Afiya tayi kafin takamo hannun Amiran suka karaso gaban Dad, Afiya tace wannan Dad ne Amira Yayan Mai Martaba, i stayed in his house for this long and yanzu yadawo gida baki daya.........
Murmushi Amira tayi yayinda Dad yace bazakiyi hugging Dad dinki ba,dariya tashigayi cikeda jin kunyarshi shafa kanta yayi sannan yace Allah yayi miki albarka......
Amin ta amsa, Sumayya da Afiya ne suka tabuke fuska yayinda ah tare sukace Dad mufa?......
Wannan karan harda Mom dayanzu take shigowa aka yi dariyar.......
Dad ne yace to Allah yayi muku albarka dukanku.....
Atare sukace Amin, sannan yace to kuje kuhuta ko....
Gyada kai sukamai yayinda Amira taja wheel chair din Ummi sukayi ciki...

Dad da Sulaiman binsu sukayi da kallo fuskarsu dauke da murmushi seda suka bace musu da gani sannan Dad yadubi Sulaiman din...
"Ina Mai sunana?"....
Cikeda damuwa Sulaiman yace "yaki zuwa Dad,daman nayi wannan tunanin wallahi Amira ma data biyomu batareda rikici ba tabani mamaki sede danayi laakari da yar uwarta nanan may be shiyasa batayi gardama ba harna samu na taho da Ummi din.......
Murmushi Dad yayi sannan yace don't worry fushi yakeyi I'll handle it gobe zanje dakaina,gyada Kai Sulaiman din yayi kafin yace sede akwai wata magana danakeson muyi ....
Dubanshi Dad yayi sannan yace muzauna seka fada minko.....
Tare suka karasa parlourn suka zauna yayinda yace akan wata yarinya ce Dad ranarda naje fito da Yaya daga gidan horon can i saw them together harda Amira that was the first time dana ganta nan yashiga bashi labarin yanda sukayi da Almustapha dakuma yanda kawarta Aisha tazo tasamesu ah daki wanda hakan yasashi son jin gaskiyar maganar don yasan bazaisamu cikakken labari gurin Almustapha ba,duban Dad yayi yadan numfasa sannan yace dakace inje indauko su Ummi Dad shine natsaya ta gidan nayi sallama da kawartata tafito shine naroketa kan tafada min meyake faruwa don Allah,I need to know dukda tanajin haushin abunda Yaya Almustapha yayi bataki fadamin ba nan take fadamin ita Asma'un ma na gidansu sannan tafadamin cewa ga dalilin dayasa tasamu matsala da iyayenta,nan yakwashe yanda Aisha tafada mishi kafin daga karshe yace yanzu haka tana gidansu Aisha din wai mahaifinta yahanata shiga gida Kuma hakan yafaru ne adalilin munafurcin masarautar nan wanda yasa Itama zata fada ciki shiyasa nace barina fada maka kozakaje har gida kabama mahaifinta hakuri don Allah kilan yajika Dad........
Murmushi Dad yayi sannan yace in Sha Allah zanjeni gobe,amma natausayama yarinyarnan matuka kuma koma miye tayi aibai kamata mahaifinta yayi hakaba,'ya mace cefa yasan inda zataje ne ko baya tunanin hakan dayayi yasake bude wani hanyar gurbacewar rayuwartane indai tana halin dayake zargi din....
Gyada kai Sulaiman yayi sannan yace hakane Dad sede kasan kowa da irin nashi tunanin.....
Murmushi Dad yayi sannan yace me kake shirya mana ne na bikin Son?...
Dariya Sulaiman yayi sannan yace Amarya na fushi dani Dad wainabar kasar banfada mataba na daya and zasuyi event naki zuwa.....
Jan hancinshi Dad yayi yana gaskiya baka kyauta ba,amma batun event naga zakuyi anan ma in ankawota akwai al adu da ake gudanarwa bana tunanin saikaje sabida yanzu lokacima yakure jibine fa daurin auren,in Sha Allah cewar Sulaiman din......

*****
Zaune yake gaban kawu kanin mahaifinsu daya tsufa jikib abunshi,kawu yajikin naka Daddy yayi tambayar fuskarshi dauke da damuwa......
Dasauki Muhammadu,yanaka iyalin kasamu zuwa kenan?.....
Gyada ma tsohon kai Daddy yayi kafin yace Allah yakara sauki duk iyalai kuma lafiyansu kalau sunama gaisheka.......
Ina amsawa cewar kawun sannan yace naga goro mutanen gida dasukaje halarta tambayar auren yara da aka kawo,Allah ubangiji yasanya alkhairi kaga nidai jiki ya hana ni zuwa, murmushi Daddy yayi sannan yace babu komai Kawu aikomai dan lafiya ne.....
Hakane kam,wata biyar akasaka ko,kawu yayi tambayar don sake tabbatarwa,eh da haka akasaka kawu amma yaran nan suna bani matsala yanzu shiyasa ma nace barinazo gurinka muyi shawara.......
Kawune yace lafiya,meyafaru kuma Muhammadu?.....
Gyara zama Daddy yayi sannan yace Kawu kasan Asiya daman akwai rawan kai ga Itama Asma'u narasa mai ya shiga kanta gabadaya abun yadameni.......
Nan yashiga bama kawu labarin duk abubuwan dayake faruwa dakuma matakin daya dauka akansu baki daya......
Kai!kai Muhammadu kayi babban kuskure,wani irin danyen hukuncine wannan don Allah?.....
Shidai Daddy shiru yayi yana sauraren Kawun nashi kafin kawun yadan numfasa sannan yace gaskiya matakin daka dauka kan Asma'u yayi tsauri kuma bai kamataba amatsayinka na mahaifinta ai duk lalacewar yaro bazaka bada gudumawa gurin sake lalatashiba......
Cikin sauri Daddy yace nayi hakan ne don ta horu tunda itabatajin maganata,kawu ne cikeda bacin rai yace badai horata kake niyan yiba sema sake gurbata rayuwar yarka dakake shirin yi Muhammadu,tundakaga tafara bijirewa nidai anawa ganin kamata yayi kakirata kaji miye damuwarta sannan kayanke hukuncin daya dace,tunda tanuna gawanda takeso miyasa baxaka batashiba,ina nufin miyasa baxaka aura mata wanda takesoba,Daddy ne yace Kawu baka ganeba sotake tamaidani mutumin banza tunda dafari tayi naam dashi daya saurayin nata....
Murmushi kawu yayi irin tasu ta manya sannan yace amma wayene yace yafasa auren, Asma'u dakanta tazo tace maka bataso?......
Jijjiga kai Daddy yayi alamar aa,to ai shikenan tunda shi yaron dakanshi yace yafasa abunma yazo dasauki atleast danginsa baza suce an wulakanta suba da dakasamu labarin kakira Asma'u kaji ta bakinta sannan kayanke hukuncin daya dace inta dage wancan yaron takeso kace mata tace masa yaturo iyayensa ai wanda beji bariba bayaji hoho ba,tunda tadage seshidin seka aura mata shidin aidai jama'a bazasuje waje suce yarka na iskanci ba ko ta zubar da mutuncinta iyakaci ace ta auri yaron dabai dace da'ita ba wannan Kuma ita tasani sabida ita dakanta zatayi nadamar kin zabin ka datayi domin zama da irin wannan yaron amatsayin namiji indai yana abunda ka lissafo to zama dashima kadai horo ne,itadakanta zata dawo tana nadama lokacin ne kuma zatasan anfanin naka shawarar,Sabida haka ninawa shawarar Inka koma kabarta ah gida sannan kayi mata abunda takeso shine mafita tunda taki bin yanda akeso din,inkayi hakan kaima hankalinka zaifi kwanciya dakuma kimarka ah idon mutane ma .......
Shiru Daddyn yayi yana nazarin shawaran kawun kafin yace nagode sosai Kawu in Sha Allah zangwada yanda kace din.......
Allah yacigaba da shirya mana yaranmu,Amin ya Allah cewar Daddyn sannan yace muma gobe zamu koma da Hajja in Allah ya yarda.....au to to dawuri haka, murmushi Daddy yayi sannan yace eh wallahi akwai ayyukan dazanje in gabatar innakoma ne,naso tafiya yauma sede zuwa yanma inason inje indubo Alhaji Adamu acan malumfashi wai shima Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa bansamu nazo janaiza ba.....
Gyara zama Kawu yayi sannan yace tabbas anyi haka,naji kallamu na maganar(Dan kawu),don sun halarci janaizan nan,ayya cewar Daddy yayinda suka ajiye wannan zancen suka koma na kasuwanci kuma........
***
Tun bayan da Sulaiman da Dad suka fito ah massallaci suka rankaya gurin Mai Martaba don duba jikinshi ba laifi yaji sauki sosai dukda baisamu yafita massallaci ba agida yayi sallah seda gari ya waye sannan Dad yace ma Sulaiman suje maganar DNA TEST dinnan bayason ah bata lokaci kada wani abu yashiga tsakani aikuwa tare suka fito already Afiya da Amira sunshirya don Dad tun dare yasanar dasu fitan nasu,aikuwa haka suka shiga mota suka kama hanyar asibity, Dad ne yadubi Sulaiman sannan yace yazamuyi da rigimammen yaron nan?.....
Dariya Sulaiman yayi yayinda yaciro wata leda fara anyi silling dinta yana nuna ma Dad din,cikeda mamaki Dad yace miye wannan din?...
Mika masa Sulaiman yayi yana"gashin Yaya Almustapha ne jiya nacira daga kanshi bayan yace bazaije ba", cikeda mamaki Dad yace bana Abban kubane?....
Sake dago wata irin ledan yayi sannan yace gana Abba nan, murmushi Dad yayi sannan yace I'm so proud of you Son.......
Haka suka wuce asibity akayi DNA TEST sannan akace zasu samu result zuwa yanma,Dad jiyake kaman yatsaya ah asibitin har result din yafito don bayason asamu matsala yariga yasan Magajiya since childhood she's so cunning, kaman Sulaiman din yasan meke ran Dad din yace"don't worry Dad, I've full trust in him dayardar Allah baza a samu matsala ba".....
Jinjiina kai Dad yayi sannan yace"I hope so",haka suka bar asibitin kan Sulaiman zai dawo yakarba da yanma............
Bayan sunbar asibitin ne Dad yace suje gidansu Aisha he'll like to talk to Asma'u and Almustapha too......
Babu musu driver din yashiga driving har inda Sulaiman din yayi masa kwatance parking motar yayi yayinda Daddy yashiga bin gidan dasu Amiran kezama da kallo gaskiya suna wahala hakanan sunsha talauci har cikin gidan Sulaiman yayi directing Dad din, Almustapha nakwance idanunshi rufe wanda zakayi tunanin bacci yakeyi amma ah zahiri ba baccin yakeyiba yunwace ke addaban cikinshi gashi shi babu abunda ya iya dafawa kuma yana kwiyan zuwa ATM yaciro kudi kawai seya kwanta batareda yasan abunyi ba, tabbas yaji anbude kofa amma baisan waneneba kuma baidamu da tashi yaga wayeneba, Sulaiman ne yace Yaya Almustapha katashi,kayi bako.....
Bude idanunsa yayi ahankali yasauke su kan tsohon dake tsaye kanshi,besanshi ba sede one look dayayi mishi yagane cewa shine Uncle Almustapha din sabida tsananin kaman da sukeyi da Mai Martaba.....
Tashi yayi cikin sauri daga kwancen dayake yazauna,take cikinshi yashiga kugi na kukan yunwa,kunya ne takama shi haryakejin kaman ya nutse kasa murmushi Dad yayi sannan yazauna gefen Almustapha din ......
Kan Almustapha ah kasa yace"Ina kwana", don bazai iya kuma kallon idanun mutumin ba sabida akwaishi da kwarjini .
Riko hannunshi Dad yayi sannan yace"Yarima so kake kanunamin kai sarautar taka ah jininka yake,wato sede ni inbiyoka ko,banga laifinka ba kuma gani mesunana nazo da kafafuna ina rokon ka katashi mutafi"..........
Gyada Kai kawai yayi sabida bazai iya kallon cikin idanun babban mutum kaman Dad ba yaki bin umarninsa dukda kuwa zuciyarsa bason zuwan yakeyiba,murmushi Dad yayi kafin ya rungume Almustapha din yana"kaikam bakayi kama damuba Son larabawan ka dauko ko shuwa zance,sede kallo daya nayimaka naji ina matukar kaunarka hakazalika naji ka kwanta min arai bawai dadin baki nike makaba I'm just telling you abunda ke zuciyata"...
Shidai Almustapha lafewa yayi jikin Dad din batareda yace komaiba sede shima din thesame feelings yakeji game da Dad din,tunda yajashi jikinshi yakejin the feelings of being home,irin feelings din da they are somehow connected......
Janye shi Dad yayi sannan yace seka tashi muje gida kaci abinci don na lura kai rago ne Dad yayi maganar cikeda zolaya ...
Sulaiman dake gefene yace"Dad danasan Yaya zaiji maganarka aida tarema zamuzo tunjiya"....
Dariya Dad yayi sannan yace angaya maka masu suna daya suna ba ma juna kusa ne......
Ah nagani cewar Sulaiman din, murmushi Dad yayi yana rikeda hannun Almustapha din har suka fita ah gidan nan Sulaiman yarufe gidan da makulli kafin azo daukar kayansu dazasu bukata.......

Sallama Sulaiman din yayi gidan Anty suwaiba, Aisha da Asma'u na parlour suna kallo dukda kuwa kawai kallon TVn take bawai don tana gane me akeyi aciki baneba don gabadaya hankalinta yayi wani gun, Aisha ne tace niko naji kamar anyi sallama.....
Asma'u dajin maganar Aishan ne yasata dawowa cikin hayyacinta tace "uhm mekika ce?".....
Cewa nayi naji kamar ana sallama awaje,batakai ga rufe bakin nataba taji anasake doka wata sallamar ...
Aikuwa sallamar akeyi Asma'u ba inje induba wayene Aishan tatashi tazari hijab dinta tafita, Sulaiman tasamu abakin kofa yana shirin sake doka wata sallamar murmushi yayi ganinta sannan yace"nayi tunanin bakwanan ma ai"......
Munanan wallahi Ina wuni Yaya Sulaiman?....
Lafiya kalau,yagida Ina Antyn ki?...
Lafiyar ta kalau wallahi batama gida tafita asibiti...
Ayya,yar murmushi yayi sannan yace nazo daman da Uncle dina ne kamar yanda nafada miki jiya zamuje gidansu Asma'u din zeyi magana da mahaifinta.......
Dan shiru Aisha tayi sannan tace, gashi Auntyn batanan Yaya Sulaiman nima inason haka sede ba lallai bane Asma'u tayarda tabiku after what has happened dama Auntyn nanan ne kilan inkunyi magana da'ita tasanar da ita...........
No problem muna tareda Uncle dina ai kawai kice yanason magana da ita,dan jim Aisha tayi sannan tace toshikenan bari insameta kukuma kushigo parlour nan tayi masa nuni da parlour,gyada mata Kai yayi sannan yakoma mota yayima Dad magana,fitowa Dad yayi suka shiga gidan,Aisha samun Asma'u tayi sannan tace kinada baki ah parlourn waje nan Aisha tashiga hada trayn ruwa tana barina zuba musu ruwa seki tafi musu dashi.......
Cikeda mamaki Asma'u tace baki kuma daga Ina Aisha?.....
Murmushi Aisha tayi sannan tace baki yarda danibane,kede kije kikasani ko bakin alheri ke tattare dasu,jin Aisha ta ambaci hakan seta tashi cikin sauri tadauki hijabinta don abunda ranta yabata shine kilan ko su Yaya Mubaraq ne sukazo maida ta gida,karban trayn tayi tafice har kaman zatayi tun tube.........
Da sallama tashiga parlour sede datayi arba da fuskar Sulaiman setaji kaman tajuya,abu dayane yasata karasawa ganin dattijon dake zaune gefen Sulaiman din ajiye musu ruwan tayi sannan tagaida Dad din, murmushi yayi sannan yace lafiya Asma'u ko?.....
Gyada masa kai tayi,Dad ne yace Sulaiman yasameni yafadamin duk abunda yake faruwa da duk wani misunderstanding da aka samu wanda inaganin naki iyayen basu fahimci abunba kuma koda nine in their shoes i may believe everything da nagani,akasi akasamu Ina baki hakuri antuhume ki da laifin daba nakiba har akaso hadaki danaki iyayen shiya sa nataso dakaina don inkaiki har gida gaban mahaifinki inyi mishi bayani may be ya yarda ya yafe miki don bazanso amtsayina na mahaifin Almustapha ba ace kinshiga wata rayuwa ah dalilinshi batareda muntaimaka ba tunda munada hali.......
Cikeda mamakin yanda akayi Dad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login