Showing 165001 words to 168000 words out of 235422 words

Chapter 56 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3508

Allah yasa kada ta hadu da kowa don muddin wani yaga fuskarta zaigane tayi kuka... koda takoma dakin Allah yataimaketa Hajja batanan wannan dalilin yasa tasamu bakin gado tazauna tana tunanin abunyi because she's really out of option,wata zuciyar tace tasameshi suyi magana yayinda wani bangare na zuciyartata ke raya mata kan cewa yimasa maganar ma bazata anfaneta da komai ba tunda tasan shi wanene yana ma iya kin bata hadin kai kokuma ya gwasaleta hakanan 70% na zuciyarta na kuma raya mata "what if it was a frank to trap him",to amma waye zaishigo dakinshi yayi hakan bayan itakanta tasan bakowa ke shigamai dakiba,inma hakane anshiga anyi trapping dinshine to muddin tanuna mishi cewa tana zargin yanashan giya yana iya fushi da'ita wanda itakuma kwata kwata batason hakan besides tanaso su rabu lafiya ne batareda wani issue ba and yakamata tasamu concrete evidences before concluding anything now sabida zuciyar ta tafi rayamata cewa Almustapha yadaina shaye shaye don koda kuwa yayi ah baya to sede in once in a blue moon,dawannan tunanin tayi concluding yin bincike kafin tadauki wani mataki ma'ana zata saka mishi Ido fiye da da don ganin take takenshi,goge dan guntun kwallarta tayi sannan tatashi cikin sauri tafice don komawa dakin nashi.............
Koda tashiga baidawo ba wannan dalilin yasata yin hamdala tareda daukan ledar tafice da'ita zuwa dakinta can saman wardrobe dinta ta ajiye kan intasamu lokaci zataje tazubar inda babu mai gani kafin takoma dakin nashi tacigaba dayi mashi gyaran kaya dukda ma kusan rabin hankalinta baya jikinta............

Bangaren Zaliha kuwa gabadaya yau jiran zuwan Salma takeyi,sotake kawai yarinyar tazo matada labarin Almustapha da Asma'u sunsamu matsala amma shiru har azahar wannan dalilin yasa ta aika Lantana ta kiramata ita,koda tazo cemata tayi taji su Hindatu nacewa Asma'un ce zatayi gyaran dakinshi kuma kusan zatafito dinnan taga Asma'un tawuce da ledan dakin ta wanda tanada tabbacin tagani kenan.......
Da mamaki Zaliha tace"badai yarinyar nan bata yarda yana shabane ba?".......
Itadai Salma shiru tayi kanta na kasa yayinda Zaliha tayi kwafa tana "hmm Asma'u kenan inkinsan wata bakisan wataba, you've to believe it whether you like it or not because I'll surely make you believe that your husband is a drunkard".....
****
Wuraren karfe uku motocin sojoji suka kuma sauka cikin masarautar zazzau don diban su Magajiya akaisu prison kafin ashigar da maganar su kotu, Commander dinnasu ne yace ayi mashi iso gurin Mai Martaba aikuwa basuwani jima da tsayuwaba Mai Martaban yace akaraso dasu Fadan nashi cikin dan kankanin lokaci aka shigayi masu tarba ta alfarma seda suka sha ruwa suka setu kafin suka zauna magana da Sarki Abdulrahman din inda suka nuna masa dalilin zuwansu.........

Jinjina kai yayi ahankali yana nazarin zancen nasu kafin yace"Suyi hakuri bazai iya daukan Magajiya yabasu ba sabida duk abubuwan datayi ah masarautar tayishi hakanan he want her to be punished for her deeds agaban duk wanda tayi niyar gurbata ma rayuwarsu sannan yayi musu godiya sosai na goyon baya dasuka basu dakuma taimako dasuke niyar musu amatsayinsu na jami'an tsaro"........
Commander dinne yace bakomai ai aikinsu ne kuma yanda yafada din shima wani hikima ne sannan sunyarda da facilities dinsu,they can handle Magajiya very well tunda tariga tashiga hannu and if they need any help they shouldn't hesitate to call them sukuma insha Allah zasuzo"........
Bakaramin dadin kalaman Commander din Mai Martaba yajiba kafin sukayima juna sallama suka tafi,kokadan bejin zemika ma hukuma ita sabida yafison ta horu ah gabanshi horuwar dawani baitabayiba,she'll live all her life in prison that's his promise dukdama yasani muddin tashiga hannun hukuma aka kuma shiga kotu to tabbas hukuncin kisa za ayimata daga karshe tunda itama ta kashe wasu", she'll die when her time comes but he want her to suffer kamar yanda tasa iyalinshi suka wahala.seda aka kira sallar? la'asar sannan yawuce masallaci......
Wuraren karfe biyar da rabi Mai Martaba da Dad suka isa Gidan Horon inda Magajiya take yayinda suka sa ah fito da'ita because bazama su iya shiga wannan kazamammen gurin ba Allah yagani....
Tana kwance kan kasa dan bazance cement ba tunda duk ya gur gur je gurin wanda hakan yasa yakoma kaman yashi medauke da pebbles acikin shi,bude kofar dataji anyine yasata dagowa ahankali cikin sanyin jiki don ganin wanene gabadaya tayi baki ta rame, tazama kamar ba'ita ba don wallahi nikam dabadan nasan Magajiya agurin takeba ina iya cewa wata ce ba'ita ba......
Wani harara dogarin ya wurga mata tareda toshe hancinshi sabida wani irin doyi dayaji yana tashi agurin sakamakon warin da ciwuwwukan jikinta keyi because sunki healing kwata kwata sema cabewa dasuke sakeyi a kullum, sunwani zama abun kyama babu kyaun gani wanda hakan yakuma faruwane dalilin sosa jikinta datake yawanyi sabida masifar kaikayin dayake mata,wani sa'in intana kaikaya jikin nata zakayi tunanin ko tabin hankali ne da'ita,takicin abinci takuma ki karban treatment duk ita kadai,yananan tsaye hancin shi toshe wasu dogaraye biyun suka shigo suna toshe hancinsu suma don wallahi dabadan yazame musu dole bama babu abunda zaishigo dasu wurinnan,abincima yawanci daga bakin kofa suke garo mata shi wanda shidinma baci takeyi ba sema ball datakeyi dashi wanda inada yakinin hakan nadaya daga cikin abunda ke karasa dakin yin doyi tunda duk ga rubabbun abinci ah zube su basu kwashewa Itama kuma bata gajiya da zubarwa in an kawo din,zuwa sukayi suka kamata fuska ba walwala sannan sukayi waje da ita harzuwa inda Mai Martaban ke tsaye da dogarayensa abaya sekuma Dad dayayo mishi rakiya............
Kallon tsana da kyama yabita dashi hakanan yana mamakin yanda ta lalace cikin kwana uku,he never thought she could do all that she has done hakanan yana mamakin anya akwai wani abu waishi zuciyar Imani ah tattareda da kirjinta kaman yanda kowani dan uwa musulmi kedashi?...........
Ajiyeta sukayi ah gabanshi yayinda hannunta dake sakele ah bayanta yana daure da handcuff Mai Martaba yafi minti biyu baiyi magana ba hakanan be kalleta ba itakuwa dukda azaban datakeji ajikinta hakan behana ta wurga masa wawan harara ba,ayanzu ah duniyar nan babu wanda ta tsana irinshi hakanan tana ganin intasamu dama babu abunda zaihanata kasheshi kowama ya huta..............
Cikin kakkausar muryarsa yace"kincuceni da iyalina Magajiya cutar da ni kaina bazan iya misaltata ba,kin wahalarda ni kamar yanda kika wahalar da mutane na,me mukayi maki, have I ever wrong you in anyway or the other?",Mai Martaba yayi mata maganar murya ah raunane..............
Ganin batada amsar bashi sema mugun harara datakebinshi dashi yace"hmmm ni nasan banmiki komai ba hakanan ban yaudareki ba aduk zaman damukayi,akullum banida burin daya wuce incika miki hakkokin ki dake kaina but you,bakiyi ko daya ba and that's why you're like this and I promise you you'll end like this, aedaman Allah ba azzalimin bawansa bane se wanda ya zalinci kanshi", Mai Martaba yayi maganar ranshi na kuna kafin yayi mata wani irin kallon kyama yana nunata da hannu"sanda zanzo gurin nan I wanted to give you the punishment of your life, punishment dinda babu wanda nataba yiwa irinshi ah masarautar nan but by just looking at you nasan cewa you're already on punshment innabarki da wannan ma kadai ya isheki and kisani aurena dake babu nasake ki saki uku Kuma kisani duk cutana da kikayi nabarki da Allah, because it's unforgivable ko inason yafemiki ma zuciyata bazata barni ba infact I don't even want to think of that",daganan yacema dogarayen sudauketa sumaida gidan horon,karkuma suyarda susake wahalan nemo likita yadubata tunda ita tanuna bataso don tun zuwanshi suka sanar dashi kan Magajiya batason ganin likita sannan yace anabata abinci sabida shibazai yima mutum horo da yunwa ba dukdama yaso yasa adunga mata mugun bugu kullum wanda seta fita ah hayyacinta but by just looking at her wonds duk rashin imaninsa bazaice ayi mata wani illar akan wannan ba but it's a promise dasunyi healing za acigaba daga inda aka tsaya...........
Haka dogarayen suka dauketa zasu koma da'ita se mutsu mutsu takeyi tanama Mai Martaba wani irin kallo seda suka kai bakin kofa sannan cikin murya mai karfi tace...
"Don't even think this's the end, I'll make sure I destroy you and your family Abdulrahman"......
Yanda take maganar cikeda zafin rai harcikin dodon kunnensa yakeji hakanan besan sanda yatsaya cak ba daga tafiyan dayasomayi kafin yajuyo yana kallonta? dogarayen ma ayanzu sun tsaya,gyada mashi kai tayi yayinda tasaki wani mahaukacin dariya kuma tafi 3 minutes tanayi duk suna kallonta kafin tace...
Na kashe yan gidan Galadima baki daya seme?......
Nina rabaka da Khairiya nakumasa kamanta ko ita wacece hakanan nine dalilin dayasa Danka yashiga yanayin da ban taba ganin wani ya shigaba sabida kadaura son duniya akanshi,you wanted him to be the king bayan kamanta nine first wife dinka,I've a Son too and I wanted him to be the king not your filty Son,kaso ko kaki I rule this kingdom Abdulrahman for more than 20years now!"takarashe maganar tana nuna masarautar da hannunta sannan? tasake kwashewa dawani irin dariya,lokaci daya kuma tadaina dariya tareda bata rai tana"I might not achieve my goal of making him the King but still I'm proud na ajiye record,nayi abunda baza a manta dani ba ko bananan and i assure you I'll make all your lives miserable,I'll never let you live in peace ni Magajiya idan Dana bazaiyi rulling kingdom dinnan ba then I'll destroy it kowama ya huta", Mai Martaba daya zuciya hanyar inda take yayi yana huci cikin sauri Dad yarikoshi yana"Calm yourself Abdul inaganin haukane yafara damunta koso kake kabiyeta kuzama daya?".............
Mai Martaba na huci yace"bakaji metake fada bane, who is she,kakyaleni inkarasa ta kowama yahuta",cikin rarrashi Dad yace"babu abunda zata iyayi mana Abdul just look at her situation kawai frustration ne kedamunta bawani abu ba",daganan Dad yajuya yace ma dogarayen sutafi da'ita kafin ya lallabi Mai Martaban suka koma cikin masarautar yanata huci shikadai hakanan maganganun Magajiya nayi mashi yawo ah kwanyar shi.......

*10 days later*......
Shiri akeyi sosae ah masarautar zazzau wanda inka shigo cikinta dole kagane hakan domin tuni akafara gyare gyaren bangarurruka wanda ayanzu anyi nisa sosai hakanan koda akazo gyaran bangaren Mai Martaba Asma'u bata manta tuna ma Sulaiman batun layoyincan ba and alhamdulillah ancirosu tundaga lokacin Mai Martaba yaji rayuwarsu da Khairiya sun shiga dawomai daidai acikin kwanyarsa hakanan yana karajin wani irin sonta na ratsashi don ranar kasa runtsawa yayi seda yakira number? wayarta suka sha hira yana tuna mata each and every moment dasukayi spending ah baya sannan yake sake bata hakuri kan abubuwan dasuka faru tareda yimata alkawararruka dadama wanda akan zaicika rayuwarsu da farinciki daga ita har ya'yanta dakuma maganar zaikaita har chad washegarin aurensu gurin iyayenta da danginta,zaije yayimasu bayanin komai sannan yabasu hakuri kan abubuwan dasuka faru,bakaramin dadin kalamanshi taji ba haka Ummi takwana ranar tana kukan farin ciki tareda gode ma? Allah ........
Haka Mai Martaba yasaka agyara wani shashi ma Ummi acewarshi bekamata tazauna bangare daya da surukarta ba sannan yace su Afiya ma bayan auren sukoma bangaren da Hamida take don dama sashine babba da akayi na yaran shi 'ya'ya mata sannan haryau kowa tanada nata dakin da parlour da intazo anan zata sauka? shiyasa ma yace suma ah ware musu nasu daga cikin dakuna da parlourn na wannan sashin dukdama Ummi tanuna bataso dayazo mata da zancen because tafison Ya'yanta su zamanto suna kusa da'ita akoda yaushe amma seya dage kan hakkinsu ne dole yayimasu tunda sauran ya'yan ma anyi masu,in angama gyarawa anbasu sukuma suna iya deciding cewa gun mahaifiyar su zasu zauna to wannan shikuma bashida ja akai........

invitation cards ma jiya Sulaiman yakarbo daga gurin bugawa yakawo su Dad sugani,bakaramin kyau design din yayiba hakanan Dad da Abban sukayi ta yabawa sannan aka fara maganar yanda za ayi distributing nasu kaman yankin su katsina,kano,kaduna, Abuja,sokkoto,jigawa za'a iya kaimusu har gida sauran garuruwan kuma sede aturamusu sako tawaya inda Dad kecewa barema yanzu damuke cikin zamanin social media,shi Sulaiman yaso duka ma ayi hakan amma su Dad din sukace aa wayannan dindai akai musu kuma suma zasufi ganin ankarramasu, dawannan sukayi concluding washegari Sulaiman din zefara wannan aikin cikin ikon Allah yayinda Almustapha dinkuma zaicigaba sa gudanar dana cikin masarautar.......
Misalin karfe goma da rabi na dare Asma'u nakwance kan sofa din dake dakin Almustapha,daga kanta tayi ahankali tareda dorashi kan agogon dake jikin bangon dakin hakanan tana mamakin meyake tsayar dashi ah waje har tsawon lokacinnan haka don tun ranar da tasamu ledar giyan nan adakinshi bazata iya cewa ga ranar dayashigo yasameta idanunta biyu ba sede su hadu dasafe dukdama takan tashi taganta ah jikinshi kamar yanda yake mata kwanaki,inya dawo daga masallaci kuwa,da yayima su Amira karatu shima sama sama to shikenan kuma seyakoma daki yahau shiri,dayayi wanka yaci abinci yashirya yake fita shida dawowa kuma se Allah tunda itadai dasafen suke haduwa,gabadaya tarame tasama ranta damuwa da tunane tunane hakanan tarasa dawa zatayi sharing problems dinta gashi shi ba budan baki zaiyiba yace mata ga abunda yake tsaidashi itakuma batason tambayarshi don rasama mezata ce mishi takeyi, shin cemishi zatayi"miyasa baka dawowa da wuri?",kokuma "mekakeyi ah waje haryake sakayin dare haka!",gani takeyi intayi mashi irin wannan tambayar kamar zaiyi tunanin tana zarginshi ne bayan kuma zargin nashi takeyi tunda har tana son yin bincike akanshi dukdama haryau bata samu wani clue ba, lumshe idanunta tayi ahankali hakanan tanaji hawaye nason zubowa amma tayi kokarin rikesu, tasandai ana aiki acikin masarautar amma batasan cewa suke kan aikin ba se kwana uku da suka wuce da Sulaiman yashigo take mishi magana kan ya rage shigowa sashinsu shine yake cemata ayyuka ne yamasa yawa Mai Martaba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yadanka musu duk wasu ayyuka na bikin akansu shiyasa tarage ganinshi,to jinwannan yasa tadanyi mashi uzuri to amma atleast? tana matsayin matarshi koba komai ae seyace mata"Asma'u kwanan nan ina da ayyuka sosai shiyasa kika ga bana dawowa dawuri",ko dai yayi mata wani bayani dazaisa ta gamsu amma baiyi ba infact he's acting normal as if nothing is happening bayan itakuma aranta abubuwa da dama suna faruwa besides ita batama tunanin aikin masarautace ke tsaidashi har dare haka tunda kullum insuna tareda da? Zaliha duk inda Isha tayi zatace mata zata koma bangarenta kar Sulaiman yadawo batanan,to tambayarta anan shine indai tare suke aiki da Sulaiman miyasa shi yake dawowa dawuri?(niidai azuciyata nace kinmanta waye Almustapha ne,katambayama Yaya bare kuma baka tambaya ba).........
Tananan kwance tana ta saka da warwara har bacci yayi awun gaba da'ita batareda tasani ba,wuraren shadaya da rabi? Almustapha da Sulaiman suka fito daga bangaren Mai Martaba bayan sungama lissafe lissafensu yayinda Sulaiman yayi sashin shi inda shima Almustaphan yayo nasu sashin dakinshi yawuto direct donkuwa kowa yayi bacci by that time. Samunta yayi kwance kan sofa kamar kullum amma se bebi takanta ba yau sema wucewa bandaki dayayi yayo wankanshi sannan yashirya cikin kayan baccinshi ahankali yakarasa jikin sofa din tareda tsugunawa agabanta yana karema kyakyawar fuskarta kallo cikeda tausaya wa,shikanshi yasan son da yarinyar takeyi mashi bana wasa bane ba hakanan akullum yanajin inama shima yana da urge din yimata irin wannan son because she deserve more from him............
Sa hannu yayi ahankali cikin nutsuwa yadaga ta kamar Baby dukdan kada yatada ta daga baccin da takeyi,zuwa yayi yakwantar da'ita tareda zama gefenta yana tsuramata manyan idanunsa gani yayi tayi rama tayi wani iri within 10days dinnan,she has changed so much bakamar Asma'un daya sani ada ba,bata mishi shagwaba yanzun inyayi mata abu, bata mai korafi sannan duksanda suke tare yakan lura da'ita tana yawan shiga duniyar tunani. Yanada labarai da dama dayakeson bata nakan ayyukan dayakeyi dakuma irin gajiyar dayake kwasowa but she never ask him on why he's coming late hakanan bata taba tambayarshi batun nadin sarautarshi ba dakuma bikinsu Ummi da akasaka danasu Sumayya bayan kuma yasan tanada masaniya akai tunda tana gani anata shirye shirye sannan yasa ran zata tambaya din tunda shi mutum ne da tasan baya fadan abu se an tambayeshi,in antambayeshin ma yaya tunda bakowa yake bude ma abunda keranshi ba. He's just very sure something is bothering her because she's not really Asma'un dayasani,he want to ask her meyake damunta but baisan ta'ina zai fara ba?..
Bai saba ba,baikuma taba yima wani irin wannan tambayar ba hakanan baya tunanin zaifara akanta he just hope that she'll open up soon because shirunta is really Killing him inside.........
Dan shafa kanta yayi ahankali yanayimata addu'ar bacci kafin daga karshe yayi bending kanshi tareda pecking cheeks dinta sannan yatashi yakoma ta dayan bangaren yahawo gadon tareda janyota jikinshi........

***
*Same night*

Daddy ne yadubi Mommy dake serving nashi dinner yace"Hajjan bata dawo ba haryanzu?".......
Batareda Mommyn tabar zuba abincin datakeyi din ba tace"Bata dawo ba Dear".......
Dan tsaki yayi kafin yace"Daman kucema su Aliyu suje sudauko ta gobe ina anfanin zuwa tazauna ah gidan surukai ba haihuwa Asma'un tayi ba bakomai ba dama ace bamwa gari ne mu is understandable".......
Jinjina kai Mommy tayi don Itama abun yajima yana damunta kawai shiru tayi bare abunka da uwar miji kada kayi magana yazama wani laifin kuma,to amma? tunda shi yasan rashin dacewar hakan dasukayi hakuri daga ita har Ummin ai yau yabudi baki yayi magana dukdama Ummin bata fito fili tayi complain ba amma tabbas tasan abun naranta kawai fadane batayiba,ahaka dai takarasa zuba mishi abincin yashiga ci kafin daga karshe tatashi tayi bangarenta don fada ma su Aliyun sakon Daddynsu because batason ma tazo tamanta goben,koda tafada musu cewa sukayi to don kuwa daman sunjima suna planning zasuje gidan Asma'un Allah nedai baiyiba to yanzu sunsamu great opportunity.........
Sadiq ne yace"Nima zanbiku Yaya Aliyu",wani harara Aliyun yayi mashi tareda cewa"Babu inda zakaje yanzu seyaje yanamana kauyanci",Aliyu yakarashe maganar yana kallon Musa.....
Mommy ne tace"Uwar kauyanci zaiyi muku kubar yaro yaje yaga yar uwarsa shine zakuwani ce zaije yamuku kauyanci dan iskanci".......
To Mommy inaga Nadin Yaya Almustaphan ma yakusa zuwa zaije ai,tashi Mommy tayi don komawa bangaren mijinta tana"nidai nace seyaje goben kuma inga uban dazai hanashi",daganan tayi ficewarta Sadiq dayasan yana iya samun rabonsa yayi saurin tashi don wucewa Boysqusters dinsu don dama ah bangaren Mommy suke tun dazu binshi Musa yayi yana"matsoraci kawai daka tsayamana".............

*****
*Early morning*.....

"Sis kinkira matar ne?",Afiya tayima Sumayya tambayar tana kallonta gyada matakai Sumayyan tayi tareda cewa"Amma bani nakirata ba da Mom ne zasuyi magana daman ai",Sumayya tayi maganar tana karawa da"Ummin Asma'u ne tahada su da matar,ita tayi masu Asma'un gyaran jiki lokacin bikinsu inda tace ta'iya sosai don haka tabama Mom contact dinta sukayi communicating daita kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login