Showing 21001 words to 24000 words out of 235422 words

Chapter 8 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3534

don naga Mai Martaba yanzu kimanin shekaru ashirin kenan ko samada haka yana neman Dan uwansa mezaisa kihana afada mishi ansamu labarinsa bayan kinsan shine labarin da yake bege akullum"....
Yar dariya Magajiya tayi sannan tace"Talatu kenan ke bakisan me duniyar take cikiba sannan bakisan waye Almustapha agurin Mai Martaba,dolene inkawar da duk wata hanya dazata sada Mai Martaba da Dan uwansa don kuwa shima yana iya zama sanadiyar rashin zaman 'dana ah matsayin Sarkin Zaria"...
Cikeda rashin fahimta Talatun tace bangane ba Uwargijiyata nikam kinsani ah duhu....
Rankwashi Magajiyan takai mata sannan tace dakikiya kinmata Mai Martaba kanin Almustapha ne sannan shine asali yakamata yagaji sarautar amma seya gudu kinga kuwa dawowanshi hadarine agareni dakuma 'dana domin yana iya zuwa da babban 'da namiji wanda za a iya cewa shizai gaji sarautar sabida shiyafi cancanta nikuma Kinga banison haka yanzu haka banida wani buri dayawuce insa ayimin bincike akan iyalinsa wanda shine next move dina ah nashi fannin"...
Jinjina Kai Talatun tayi sannan tace lallai Uwargijiyata akwae ki da basira da hangen nesa...
Haka suka koma cikin masarautar batareda kowa ya lura daga inda suka bulloba.......
*****
Yau tun sassafe ta tashi tashiga kitchen tashiga harkar dora abinci,jollof din dankali tayi wanda yaji nama zuku zuku acikinta kuma tayishi ruwa ruwa don acewarta haka akeson abincin marar lafiya sannan tahada kunu mai rai da lafiya tasaka ah flask shima seda tagama tas sannan tasaka acikin basket ta ajiye akan dinning table kafin tashiga wanka....

Sanda Ummi tashigo taga abinci akan dinning tayi mamaki sosai dakin Asma'un tawuce dede lokacin tagama shiri kenan zata yafa gyalenta.....

Yauma kinada 8:00am dinne?...
Juyowa tayi tareda gaishe da Ummin,sannan tace aa Ummi se karfe tara....
Oh yayi kyau to abincin miyene ah basket?....
Uhm uhm setafara kame kame don tama rasa mezata ce kafin daga karshe tasamu idea, yauwa Ummi kawata ce ah hostel take zama Kuma bata girki sayan abinci take ah school shine tace tanason cin paten dankali shine namata alkawari...

Kallonta Ummin tayi tanason tagano wani abu,sekuma tace to yayi kyau amma yaushema kikafara zuwa makarantar da har kinyi wata kawaa?.

Eh Ummi tun lokacin registration muka hadu, juyawa Ummin tayi tabar dakin tana kada dai kibar mini kwanuka ah makaranta...
In Sha Allah bazan bari ba Ummi..
Bayan Ummin tafita ne talumshe idanunata tana nanata astaghfirullah don abunda batayi ma Ummi shine karya,sede yau tafarayinshi and she's regretting it sede babu yanda zatayi bazata iya fitowa tacemata wani namiji zata kaimawa ba,karasa shirinta tayi sannan tafito taci nata abincin ah dinning table kafin tafice don tun dazu Asiya ke yo mata aike itafa zata tafi....
sanda tashiga motar da basket tsaki Asiyan tayi tana don gulma da iyayi har anfara rabon abincin gidan mu ah kawaye..

Dariya Asma'un tayi sannan tace Ina kwana?..
Lafiya Asiyan ta ansa ai tsaye cikeda manyance...
Sanda suka isa school tace Aseey kikaini clinic please inason inbama marar lafiya abincin nan......
In disbelief Asiyan tace marar lafiya Kuma,waye ba lafiya Asma'u?..
Kai tsaye Asma'un tace "a friend"....
Tabune baki Asiyan tayi sannan tace gaskiya to kiyi sauri because banason inyi latti ah dizgani gaban yara,to naji cewar Asma'un haka suka karasa gaban clinic din tasauka hannunta rikeda basket din Asiyan sebinta da kallo take tana mamakin yaushe har Asma'u tayi kawa daga zuwanta jiya.sanda Asma'u tashiga clinic din thesame nurse najiya tasamu murmushi tasakan mata tareda gaisheta ...

Ansawa nurse din tayi sama sama tana mata kallon tara saura kwata don jiya bayan fitan Almustapha tana kiranshi yaki amsawa dayan nurse din kebata labarin Almustaphan shiyasa yanzu dataga Asma'un taki sakin fuskarta....

Jiki ah sanyaye Asma'u tace don Allah patient din jiyafa yana cikine?..
Bayanan nurse din tabata amsa Kai tsaye....
Gyara tsayuwa Asma'un tayi tana"oh ansallameshi kenan?"...
Harara nurse din ta dakamata,bakince Dan uwanki bane inaganin zaki fini sanin halin dayake ciki ah yanzu sabida haka kifita kibani guri kina destracting dina Ina aiki"...
Take idanun Asma'u yaciko da kwalla don ta tsani wulakanci ah rayuwarta, I'm sorry tafurta ahankali sannan tafice daga clinic din sanda tashiga motar se alokacin hawayen yazubo, Asiya namata magana amma taki kulata don haka se Itama tayi shiru takaita bakin faculty dinsu ta ajiyeta...
Haka tabar mata abincin acikin mota dukda Asiyan tadamu da sanin halin da Yar uwartata take ciki kota samu na gulma sede batasamu fuskaba......

****
Tunkan yagama shiryawa Magajiya ta aiko tana neman shi dan tsaki yayi don yasani daman yau se an tsigale shi seda yayi breakfast dinshi ah nutse sannan yatafi bangarenta.....
Gaisheta yakeyi amma ko kallon inda yake batayiba,menayi kuma Mama...

Wani harara ta doka mishi cikeda bacin rai sannan tace"harma tambayana kakeyi?"....
Kai wani irin bunsurune dabazaka iya hakura da mata ba,so kake kajazamin abun magana acikin Masarautarnan,dan murmushi yasaki tareda dan sosa kanshi sorry Mama shiyasa nace miki bazan dawoba sabida nasan bazan iya hakura dasuba,tsaki tayi sannan tace auren kuma fa,mezai hana kayi aure Sulaiman?....

Kamo hannunta yayi sannan yace bazan iyaba Mama, I'm too young for that don Allah kibarma maganar nan,wabce hannunta tayi sakeni tukunnan ma abar wannan maganar meyakaika gidansu yaron can jiya,ban jamaka kunne ba?miyasa baka jin maganata ne wai Sulaiman?..

Yar dariya yayi I knew it dama,yan gulma sesun kwasa sunkai tonifa Yan uwana ne Kuma babu inda nake zuwa inji dadi inba gurinsu ba Mama inkuma kika takuramin kan wannan batun se in tatttara kayana inkoma london abina daman nagaji wallahi......



Vote
Comment.
Share!
[3/23, 5:15 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*page 7*...

Cikeda takaici takai hannu zata make shi yayi saurin kaucewa yana "Wayyo Allah na"...
Kada Inkuma ji bakinka yafurta batun komawannan se na fafffasashi.....

Cikin dariya yace Allah nadaina amma nima kidaina takuramin batun Yan uwana they are my fleshy blood inbanyi hulda dasuba dawa zanyi?....
Baga Hamida ba,itan ba 'yar uwarka baneba?...
'dan sosa kai yayi yana ni Mama kindai san halinda da Bossy character dintan nan and besides she's always making phone call bama ta da time dina......

Tsaki Magajiyan tayi"Kai kasani dai koka ki kokasu sudin ba yan uwanka bane aide kana gani bayima sunfisu daraja ah gidan nan.....
Kallon Magajiyan yayi with full confidence yace "koma miyene Mama su yan uwana ne and ah idanuna sunfi bayi daraja dama mutane da dama cikin masarautar nan,bazan iya hanaki yin abunda kikaga dama ba amma nima kada kice zaki hanani hulda dasu"....
Yanzun umarni kake banine komi?.....
Karasowa yayi gabanta yana murmushi sannan yadan kwanto da kanshi jikinta "haba Mama na Isa inbaki Umarni kawai Ina neman alfarma ne".....
Tureshi tayi"dama yafi,ni inaganin mubar zancen nan ma mukoma batun aurenka Sulaiman"....
Tuni yaji duk wata fara ar fuskarshi ta gushe, haba Mama nikam bamunbar maganar nan bane tundazu....
Aa Sulaiman bamu bari ba ajiyeta mukayi gefe yanzu Kuma andawo kanta don bazai yuyu kana zubar min da mutunci cikin masarautar nan ba.....
Yar murmushi tareda lasan lips dinshi yayi ah zuciyarshi kuwa cewa yake wani mutuncine take dashi daman tunda kowa yariga yasan halin da take ciki dakuma muguntar da takema jama'a............

Abar maganar nan kawai Mama....
Dasauri tace baza abarta ba kawai kazabi daya cikin biyu,indai kanason inbarka kana ganin wayancan tsinannun to dole kayarda da maganar auren nan....
'dan shiru yayi na'yan dakiku sannan yace to nayarda amma Mama nigaskiya mace daya bazata isheniba.....
Cikeda takaici tace Allah dai yasauwaketo aidaman nibawai nahana ka bayin bane akwai concubines ai you can use them dukda kuwa awannan masarautar anhana wannan harka sede alokacinka adawo da ita kuma maganar aure munfara ta da Mai Martaba akwai 'yar Sarkin Borno Zaliha mahaifiyarta daman kawatace sosai kuma munyi magana da'ita karshen satinnan seka shirya kaje ka ganta don Mai Martaba yace bayason auren yawuce nan da wata uku....
Zare idanu Sulaiman din yayi sannan yace kai Mama wato tunkafin in amince har angama settling komai to da banyarda ba Kuma fa?....
Harararshi tayi sannan tace tunda ka yarda ai Kuma basai antaso da wancan maganar ba? ko?.....
Turobaki yayi sannan yace no need basai naganta ba tunda daman auren dole za amin....
Dubanshi tayi "ah lallai wuyan ka yayi kauri yaron nan se in hadaka damai Martaba ina ruwana....
Yar dariya yayi sannan yace Allah ya huci zuciyarki Mamana nizan fita asa Talatu takawomin baiwa daya yau da daddare ko inje rumfarsu dakaina ....wani harara ta watsa mishi yayinda tabiyo don makanshi,yana dariya yafice ah guje marar kunya kawai......

Straight Mota yawuce don fita yakeson yi nan yayi arba da jacket din da nurse tabashi na Almustapha dakuma ledan abincin daya saya jiya da daddare ahankali yafurta subhanallah don kwata kwata yamanta dama yasai musu abinci daya fita dashi sunci ai,dauka yayi yabude daman jollof din shikafa ce da naman kaji kuma da alama babu abunda tayi don haka yadauka tareda jacket din yawuce gidansu Almustaphan dashi, sanda yaje jikin Almustaphan dasauki sosai babu laifi gaisawa sukayi sannan yace ga jacket din Yaya yakarashe maganar tareda ajiyeta gefen Almustaphan sannan yafita yashiga yaduba Ummi ma sannan yabama su Afiya abinci kan su dumama suci tareda yimusu bayanin yanda yasiyo yamanta ah mota.......

Tunda? Sulaiman din ya ajiyemishi jacket din yashiga karema jacket din kallo, ahankali yadauka yarike ah hannunshi yana tuna sanda ta lulluba mai ajiki,shiyama manta kwata kwata da har wata yarinya tazo kusa dashi,dan tabe baki yayi sannan yafurta"I don't even know how her face look like bare inmayar mata"......

Tashi yayi ya lankayeta jikin wata kusa dake jikin bangon dakin dukda kuwa kamshin jacket din bakaramin dadi yayi mishiba ...
****
Yau kwata kwata batada lectures, Munira ne tashigo hannunta rikeda basket din jiya tace Adda Asmeey gashi Adda Asiya tace inkawo miki kinmanta ah mota,Ummi dake gefe tana kallon TV tajuyo tana karema basket din kallo karba Asma'un tayi dasauri sannan tashige kitchen don duk ah tunaninta abincin naciki batason Ummi tagani tayi mata fada......
Ajiye wa tayi akan drawer sannan tashiga bude food flask din sede to her own surprise babu komai aciki ancinye sede kwanukan ba'a wanke ba itakuwa wannan bedame taba tunda tasamu ancinye abinci ai atleast ba ayi asararshiba nan tawanke kwanukan tas sannan takifesu ah kwando,tun tana kitchen takejin kaman sunyi bako lekawa tayi nan tahango Mukhtar zaune suna gaisawa da Umminta Allah yataimaketa kanta da dan kwali don haka tafito tana yar murmushi"yau Yaya Mukhtar ne agidanmu"...
Yaron da aka Kira da Mukhtar dan kyaukyawa,dan gayu dashi da tunda Asma'un tafito yakafeta da idanu yace"tunda kinki kawoni nida na matsu ai gashi nazo"....
Sa hannu tayi ah bakinta tana yar dariya"Kai Yaya Mukhtar yaushe naki kawoka Kuma?".....

Duban Ummi yayi Adda Maryam kinji yarkin nan ko wai tambayata ma takeyi yaushe taki kawoni,tunfa suna registration nace insun gama zasu zo gida she should inform me amma shiru kake ji"....
Kyaleni da ita Mukhtar ainalura bakin cikin ganin Yan garin mu takeyimini Ummin tafada cikin zolaya,gwaliyo Mukhtar din yamata kaman zata yi Kuka tace to ai shikenan tunda kayi succeeding.....

Yi hakuri Asma'u wasa nikeyi kema kinsani Kuma Ummin nakima tasani,turo baki tayi a'a nikam ban hakura ba,cikeda zolaya yace sena saya miki ice cream kenan?...
Aa still ban hakura ba,kallon Ummin yayi yana gaskiya Adda Maryam an shagwaba min Mata yanzu inna aureta haka zanta fama?.....
Dariya Ummin tayi don duk awasa ta dauki maganar Asma'u kuwa dataji haka tashiga bubbuga kafa tana Ummi Kinga neman tsokanan nashi ko?, itadai Ummi babu abunda take se dariya don tasan halin Mukhtar da neman tsokana tun yana yaro gashi da raha....
Zare idanu yayi,wayafada miki wasa nikeyi barima kiga infara biyayya gun sirikata yakarashe maganar yana saukowa daga kan kujera cikin yar karamar muryarsa yace Adda Maryam za abani Asma'u don Allah?.....
Wannan karan Kam dagudu tashige cikin gida don bazata iya da halin Mukhtar ba, murmushi Ummi tayi sannan tace aiyanzukam katashi? tunda ta tafiko...

Kin tashin yayi sannan yace"Ina naga ta tashi Adda Maryamu bayan bakice kinbaniba, nifa dagaske nikeyi Adda Maryam,it was love at first sight... believe me inason Asma'u and my intentions are good".....
Harara takai mishi tana lallai Mukhtar ashe zuwan ka da biyune bama ziyara kaxo minba.....
Yar dariya yayi still yana tsugunen, a'a na isa wallahi daman ni inada niyan zuwa itane bata kawoni dawuri ba,kaidai fadi gaskiya cewar Ummin...
To ayafemin Maman mu nidai ace anbani Asma'u se inji dadin shan ruwa agidan nan.....

Jijjiga Kai Ummin tayi kaifa baka da kunya Mukhtar gurin uwa kake neman izini?...
Sosa Kai yashigayi,Kai Adda Maryamu kemafa Uwace agareni wani kunya zanji nidai abani izini infara zuwa zance gurin Asma'una adaina min yanga....

Tashi Ummin tayi sannan tace nikam kaje kanemi yardarta banida matsala da wannan fatana Allah yazaba muku abinda yafi alkhairi,cikeda dajin dadi yace nagode? Adda Maryam, I'm so happy today......
yadubi Sadiq dake dinning table yanacin abincin karya wanda duk gulma yatsaya ji don tun dazu yagama cin abincin....
Kanina kawomin abincin nima naci banason cin abinci akan dinning table, dariya Sadiq din yayi sannan yashiga zuba mishi yana auren likitoci zamusha kenan Uncle....
Ai kaidai bari har Doctors night se anyi dayardar ubangiji, Allah yanuna mana cewar Sadiq din sannan yakarasa zuba mishi yamikamai don sauri yake har jikinshi bari yakeyi tsabar gulma soyake yaje ya guntsama yayunsa Asma'u tayi saurayi finally.....
Aikuwa dukansu ukun yasamesu ah parlour suna kallon football, cikeda zumudi yace albishirinku!...

Musa ne kawai ya amsa da goro,don haka Sadiq yace tunda kai kadai ka ansa kai kadai zan fadamawa, harararshi Aliyun yayi yana kai labarin ka har wata tsiyace da mutum ze so ji......
Turo baki Sadiq din yayi sannan yace toshikenan, Musa kuwa daya kosa yaji miyene cikeda kalaman yaudara yace zo 'dan kani na,zo kafada min kaji, murmushi Sadiq din yayi sannan yakarasa gun Musa acikin kunnensa yace Adda Asmeey tayi saurayi yanama cikin gidan nan yanzu. .....
Wani tsalle Musa yayi tareda zare idanu,dagaske kake ko wasa?.....
Allah dagaske Yaya Musa kaje kagani in karyane aikuwa nan gogunanku suka juyo suma sunason jin zance cikeda manyance Mubaraq yace ku bamason haukafa miyene zakuwani zo Kuna mana ihu muna kallo miyene yafaru?....
Dariya Musa yayi sannan yace a'a badamunku mukeyiba kuyi hakuri yanzuma zamu fita nan yakama hannun Sadiq din yace muje Sadiq, Aliyu ne yace"kut kudawo nan, miyene yafaru kufada mana,zaku wani tafi don munafurci"....
Yayinda Mubaraq yace kyale yan rainin wayau mana banason rainifa,dariya Sadiq yashiga yi yayinda Musa yace nawa zaku biya?...
Dakuwa Mubaraq din yamishi yayinda Aliyu yataso afusace zeyi kansu cikeda tsoro Sadiq din yace yi hakuri don Allah karka tabani Adda Asma'u ne tayi saurayi bawani abu bane ba... sololo Aliyu yatsaya baki sake,sekuma yasaki dariya wai dagaske?..
Yana Ina, Mubaraq ne yace wai wace Asma'un?, Ma'u dai danasani ...
Eh Yaya Mubaraq mujema kaganshi dan gayu dashi wallahi cewar Sadiq din, a'a baza ayi hakaba badadi muje kanshi tunda yana nan za a hadu ai wataran nidai Ma'ulelen nikeson gani inzolaye ta cewar Mubaraq...

****
Yana kwance ah daki yaji sallamar Mallam hudu,Afiya ne taje ta amsa shi sannan suka shigo har dakin Almustaphan yashiga yaduba jikinshi sannan yace"naji mummunar labari Yarima amma banji dadin abunda kayiba,fisabilillahi Allah ya horema bakin magana don miyene?"...
Badon kayi magana bane,kasan bakayi abu ba miyasa bazakace baka yinba nina baka kudi da hannu na kaje kasayi maganin nan amma sukayi maka sharri Kuma kayi shiru"....
Tunda yake magana kan Almustaphan akasa yake,seda yakai aya sannan yakara da nikam wannan bayibane ba ranar litinin din zanzo inbada shaida tunda ninasan gaskiya ....
Ajiyar zuciya Almustaphan yayi sannan yace "karka damu Mallam Hudu".....
Cikeda bacin rai Mallam Hudu yace"Ya kar indamu Yarima,sokake inyi shiru inga ana wulakanta ka...
Jijjiga Kai Almustaphan yayi alamun a'a kaman Kuma bazaiyi magana ba seyace"banason rikici ne I'll just pay them back".....
Dukda Mallam Hudun bawai yana wani jin turanci bane amma tabbas yagane meyake cewa don haka yace"Allah yayi mutum inagani ikon Allah nikam,toh!tunda haka kace bazan takurakaba haka kawai mutum ya anshi laifin da banashiba gaskiya Allah yazuba ma ruwan hakuri".....
Murmushi kawai Almustaphan yayi yayinda Mallam Hudun yace zanbaka kudin seka basu kawai inaganin shine mafita.....
"Nagode"shine abunda Almustaphan yafadama Mallam Hudu,nan yayi masa sallama kan ze tafi dukda seda yabi yaduba Ummi kamin ya wuce gida abunsa......

*****
Yau gabadaya hanata sakat sukayi sunbi sunsata ah gaba wai tayi saurayi,kuka tashigayima Ummi kantace musu subarta ita bahaka bane fa,dariya Ummin tayi sannan tace kinga tafiyata nikam don kunfi kusa, dariya Mubaraq yayi sannan yace ai Ummi gwanda kidawo mufara zancen biki kinga se ahada danawa tunda karshen watan nan za aje tambaya....
Itadai Asma'u haushi kaman tayi yaya,sema yanzu tagane wanda yahada abun dasauri tayi kanshi tana Allah Sadiq yau me rabani dakai cikin gidan nan seyayi dagaske....
dagudu yafita yabar parlourn yana wayyo Allah Ummi kizo kitaimakeni....
Sukuwa su Aliyu inbanda dariya babu abunda sukeyi wayarta dake gefen Musa ne yayi ringing aikuwa sunan Mukhtar ne yayi appearing ah screan din, dariya Musa ya kece da kunga har masoyin yakira yakasa hakuri yadaga wayar yana nuna musu screan din cikin sauri takarbi wayar tareda amsawa tasaka ah handsfree....
Daga can bangaren Mukhtar yace Matas laifin me nayi akaki daga wayata tundazu?.......
Ae tanajin haka dasauri tacire ah handsfree din kuma tagudu daki tanajinsu suna mata dariya, Allah Yaya Mukhtar kabari kaga kasa anata tsokana na agida,'yar dariya yayi sannan yace kice nasamu shiga har haka?...
Dole inzo in kwashi gaisuwa cikin weekend dinnan....
Turo baki tayi, Allah nikam kabar wasan nan banaso....
Ganin batadau abun da serious ba yasashi sassauta murya yace "Asma'u I'm serious bawasa nike ba,I love you"....
yanda yayi maganar seda yasa tsikan jikinta yatashi,cikin nutsuwa yacigaba da magana"tun randa naganki naji kinyimini and it was love at first sight believe me"....
Shiru tayi don tama rasa mai zata cemishi,kina jina Asma'u na?yayi maganar ahankali....
Uhm kawai ta iyacewa, murmushi yasaki sannan yace kibani dama innuna miki irin son da nike miki please,I really love you!....
Kai tsaye tace mishi I'll think about it Yaya Mukhtar....
Cikeda jindadi yace zuwa yaushe kenan?....
Murza yan yatsunta tashigayi sannan tace kaidai kabani lokaci.....
To Asma'u na, I'll wait for your answer, don't make me wait for a very long time please.....
to kawai tace mishi yayinda tayi mishi sallama ta katse wayar,lumshe idanunta tayi ahankali don batamasan nayi ba abunda kawai tasani shine she need to give him a chance atleast dubada yanda yan gidansu suka dame ta........
*****
Washegari kuwa Almustapha bakaramin dadin jikinshi yajiba don yanzu yasamu sauki sosai shiyasa yana wanka yashirya yashiga duba Ummi, yau se kallonshi takeyi wanda yakula sabida bandage din dayake kan goshin shine murmushi yasakar mata dayaga akwai alamar damuwa ah fuskarta,how are you feeling Mother?.....
Jijjiga mashi kai tayi alamar dasauki,taba goshinshi yayi yana nuna mata don yasan abunda keran ta kenan "a minor accident Mother, but I'm fine now"......
Murmushi tadanyi mai kawai sannan yadan shafa fuskar ta yanajin temperature

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login