Showing 180001 words to 183000 words out of 235422 words

Chapter 61 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3472

zanyi inma baki dainaba,tukunnan ma fada min inakikeson muje Honeymoon",yayimata tambayar yana kara gyara zamanshi........
Tashi tayi dasauri tayi hanyar kofa tana mai shagwaba tahanyar bubbuga kafarta ah kasa,dariya yakeyi sosae harda dan rike ciki sannan yabita ah bayaa yana"haba Sumyna tsaya ki fadamin mana,ina kikeso muje?"......
Nan yashiga irgo mata da hannunshi dukda kuwa ba kallonshi take ba sema tafiya datacigaba dayi
"Paris?"...
"Satorini?"...
"Bali?"....
"Thailand,Phuket?"
Ko muje "British Virgin island",yayi maganar yana sake kwashewa da dariya don Allah kadai yasan abunda yake kissimawa ranshi ganin tana niyar yin dakin Mom ne yasashi saurin kamota yana"Baki fadamin ba zaki gudu?".......
Mutsu mutsu tafarayi tana"Yaya Sulaiman yaushe ka koma marar kunya newai?".......
Wara idanu yayi mischievously"yanzuke duk zamana dake me kunya kike daukana,to lallai bakisan waye Sulaiman ba Baby"..........
"Tonidai barni intafi inada abunyi"....
Kinsakinta yayi sema sake matseta dayayi ajikinshi yana"ba inda zakije harsai kin fadamin inda zamuje musamo little Sumayya"...........

Bugun kirjinshi tayi tana yar dariya cikeda kunya"Kai Yayana"........ kwaikwayon muryarta yayi shima"KaiSumyna"..
Jijjiga kai tayi da mamakinshi, kafin in a whisper yace "ko guraren dana lissafo basu miki bane ba?".....
Shiru tayi tana kallonshi so lovingly,ganin tayi shirun ne yasashi cewa"then we should make a new suggestions,we can go to Maldives if you want to,yatsina fuska tayi kamar wata karamar yarinyar hakan yasa yayi tunanin ko bai mata bane ba cewa yayi....
"Saint bartherlemy fa?",shima yatsina furkar tayi wara idanunshi yayi yana dariya"ah lallai yarnan kinada buri,shaa I like that what of "Mauritius?"........
Shima yatsina fuska tayi,turo baki yayi tareda yin fuskar tausayi don gabadaya idea ta karemai kaman zaiyi kuka yace"to ke kizaba kawai tunda basu miki ba".......
Dariya tayima expression din fuskarshi tareda barinshi tsaye gun tayi dakin Mom seda ta isa kofar dakin sannan tajuyo tana kallonshi ahankali tace"Let's go to *Fiji resort* Yaya Sulaiman,I really want to go there nan zaka kaini",daganan tayi saurin bude kofar dakin tashige da gudu jijjiga kai yayi yana murmushi aranshi yana"zanyi maganinki ne Yarinya",afili kuma seya furta kalmar "Fiji",hakanan Kuma yana tambayar kanshi "what's so special about that place donshidai baitaba zuwaba yasandai *Fiji* ah under Asia take hakanan baisan abubuwa game da gurin ba,ficewa yayi daga bangaren kaman soko yana ta murmushi tareda niyar inyazauna zaiyi bincike akan gurin data fadadin..............

Tun daga ranar Sumayya tajona su Afiya suka cigaba da shirye shiryen bikin abunsu.......
*****
Angama gyaran masarautar baki dayanta,koina yayi kel kel dashi gwanin ban sha'awa hakanan babu wanda zaizo wucewa koda ta wajen masarautar ne batareda ya yaba kyaun da masarautar ta karayiba,su Sulaiman sungama rabon invitation card biki nata matsowa hakanan baki nata isowa gakuma shirye shirye da aketakan yi babu kama hannun yaro, Almustapha gabadaya ya damu da hide and sick din da Asma'un keyi dashi don ba karamin kewanta yakeyi ba,haka zaigama kwaso gajiyar shi ah waje kullum seyadawo yanemeta ya rasa inyakira layinta kuma akashe,inyaje dakinta ma samu yakeyi batanan kullum haka dakinsu Afiya ma sekawai yafara tunanin ko tareda Ummi suke kwana shiyasa ma ya hakura don Allah yagani bazai iyazuwa dakin Ummi neman matarshi ba duk kuwa irin matsuwar dayayi da ganinta,abinci kuwa bayama sanin waye yake kawomai don sai anfaki idonshi anga yashiga wanka sannan akezuwa ah ajiye,bata taba yarda su kebe su kadai ba sede in Ummi na gurin donko su Afiya batazama gurinsu indai Almustapha nacikin gida bare har yasamu damar ganinta wannan dalilin yasa yagane gudunshi takeyi kiri kiri shikuma yakasa cireta arai,he's badly missing everything about her baccima ah daddafe yakeyinshi wani sa'in har mamakin irin yanda tunaninta kedamunshi yakeyi yi hakanan yarasa wannan din wani irin feelings ne dake neman zautar dashi batareda ya shirya ba.........
Yau sauran kwana goma biki gashi haryanzu jikin Hamida babu wani progress sema abunda yayi gaba don batason cin abinci bare kuma azoga maganar shan magani,abun ya matukar damu Mai Martaba dasu Sulaiman tunda dai gashi likita yanazuwa yadubata kullum hakanan tanashan drugs dinda aka bata abunda basu saniba shine in sun bata maganin basha takeyi ba sema jefarwa da takeyi ah bayan gado,ita gabadaya gani takeyi she's going to be a budden to them daga ita har unborn child dinta tunda mijin ta saki uku yayimata babu halin komawa gakuma tunanin yanda zata fuskanci Abba da maganar ansaketa don duk ah tunaninta Mai Martaban baisaniba bayan kuma already Dad yafada mishi tunbayan rasuwan Magajiya dayaga mijinta ne kadai baizo ta'aziya ba yake tambayar ko lafiya,koda Dad din yafada mishi cewa yayi Allah yasa hakan shiyafi alkhairi dukda kuwa abun yadameshi............

Mai Martaba dayanzu shigowanshi dakin yazauna gefenta tareda taba temperature din jikinta da haryanzu jikin keda dankaren zafi kaman wuta sannan yashiga tambayarta yajiki wanda hakan yariga yazame masa al'ada akullum don tunda tafara rashin lafiyar indai yagama shirinshi da karin kumallo to ita yake fara zuwa yaduba kafin yawuce fada. Murmushi tasaki tareda cewa "Dasauki Abba"......
Cikeda tausayinta yace"kindai fadane kawai Hamida amma ga temperature din jikinki haryanzu da zafi anya bazamuje asibiti ba kuwa tunda abun ya faskara anan", yakarashe maganar tareda maida kallonshi ga Dad dakuma Sulaiman......
Sulaiman ne yace...
"Nima tunanin danayi kenan Abba don likitan yayi iya kokarin dazaiyi amma babu wani progress"............
Jijjiga kai tayi yayinda hawaye kebin gefen fuskarta kafin tace"Allah Abba dasauki"..........
Sa hannu yayi yana goge mata kwallar kafin yace"It's better akaiki candin don zama ah gidan babu anfani tunda likitocin mu nanan sunkasa yin komai besides kina dauke da ciki yakamata ayi examining naki to see if the Baby is fine",yanakai aya yatashi tsaye tareda cema Sulaiman din ashiryata atafi da'ita hospital yanzu.......

To Sulaiman din yace inda Dad da Mai Martaba din sukafice,duban Asma'u yayi sannan yace "ta taimaka mata ta gyara jikinta sesu tafi".........
"To",kawai tace aikuwa
cikin mintuna ashirin harta shiryata nan suka tafi asibitin dukda seda yabi ta bangaren Zaliha kozata bisu amma secemasa tayi tana da baki,tabe baki kawai yayi batareda yace komai........

Straight wani private hospital dake cikin Zaria sukaje wanda yaji labarin anacewa asibitin nada kyau sosai abunda Sulaiman din besani ba shine asibitin su Na'im ne.......
Vote
Comment
Share!

[3/23, 6:07 PM] >?p?: =?Q?=?Q? *GIDAN SARAUTA* =?Q?=?Q?



Written by *Zeeneert*=ؕ?


*Zeeneert*@wattpad....



*Page 61~62*


Koda suka shiga harabar asibitin dasauri aka karbesu ganin daga *GIDAN SARAUTA* suka zo haka nan akawuce dasu office din Na'im don yayi attending to them tunda yana asibitin and he's free......
Bakaramin mamaki Dr Na'im din yayiba ganin Sulaiman ah office dinshi haka yamika masa hannu sukayi musabiha yana cewa...
"You didn't tell me you were coming Bro".......
Murmushi Sulaiman yayi yanadan shafa kanshi sannan yace"Nima bansan anan kake aikiba ai naji ance hospital din is good shiyasa ma mukazo nan".....
"I work here,asibitin mahaifina ne ai",Dr Na'im din yayi mashi bayani dede nan kuma Asma'u suka shigo da Hamidan binsu yayi da kallo yana tambayar wayene ba lafiya..........
Seda Asma'u tazo tataimaka ma Hamida tazauna kan daya daga cikin kujerun dake kusa da table din Na'im din kafin tagaida shi.......
Amsawa yayi yana zolayarta da "Amaryarmu yakike"
"lafiya Lau Doctor ya aiki,ka buya abunka"
Murmushi yayi yana dan jujjuya pen din dake hannunshi sannan yace"bawani niban buya ba mijinki dai yahana ni ganinki dukwai dan kar ince kiyimin wannan hadaddiyar jollof din naki".......
Dariya Asma'u tayi inda shida Sulaiman ma sukayi dariyan yayinda yamaida hankalinshi kan Hamidan daketa faman hararanshi don bakaramin haushi yabata ba,batada lafiya ma amma shi surutu ma yatsaya yi abunsa aranta tana fadin"irin su ne basu san aikinsu ba,ahaka yana hira da mata harya yima patients illah",jitayi yace"kece baki da lafiya?",yanda yayi maganar ahankali seda yasata jin wani iri gashi ya kafeta da idanunshi yana jiran jin ansa daga gareta,kin kulashi tayi hakanan ita ciwon jikinta ma ya'isheta,Sulaiman ne yashiga yi masa bayanin tun farin rashin lafiyartata dakuma drugs datayi tasha......

Still idanunshi nakan Hamidan sannan yace"Ina prescribed drugs din suke?"......
Allah yataimaka Asma'u tazo dasu don haka tafito dashi tamika mishi,dudduba magungunan yashigayi sannan yasake kallon Hamidan cikeda tuhuma...
"Anya kinashan magungunan nan kuwa?"....
Wutsi wutsi tayi da idanu wanda hakan yasa yagane something is fishy,cikeda damuwa Asma'u tace"tana sha Doctor,we always make sure tasha on time".........
Ajiye maganin yayi akan desk tareda maida kanshi jikin kurerar ya jingina yana kallon Hamidan sannan yace"kunadai bata but I don't think she's taking those drugs don magungunan daya rubuta mata drugs ne masu kyau and if I were to prescribe drugs for her indai ah condition dinda take yanzu ne to thesame drugs zanrubuta mata".......
Daga Sulaiman har Asma'u suka maida kallonsu kan Hamidan cikeda tuhuma kawai seta sakin masu kuka wai ai Na'im na neman hadata dasu ne itakam tanashan magani kuma suma shaidane......
Dariya yayi cikeda mamakin katuwa da'ita amma tana kuka akan karya,itakuwa ganin dariyama yake mata yasata kara sautin kukan cikeda takaicinshi dakyar ya'iya tsagaitawa yana"tsaya tsaya, I'm sorry to Adda Hamida".........
Itadai kukan tacigaba dayi wanda inada tabbacin harda na zafin zazzabin datakeji,dakyar Sulaiman ya lallasheta tayi shiru yayinda Dr. Na'im yace"Ina kince kina shan drugs dinki on time?"........
Gyada mishi kai tayi ahankali, murmushi yayi cikeda mamakin stubbornness dinta kafin yace"okay then,nayarda kinasha but wannan drugs din zamuyi cancelling dinsu za afara sabon shane yanzu tunda sudin basuyi wani aiki ah jikinki ba and I'll be the one to be giving you those drugs in order to make sure that assumption dina na bakya shadin karyane".............
Shiru tayi batacemai komai ba, ahankali yace "Kinyarda?"......
Gyada kai kawai tayi badon tanasoba don kawai kada su Sulaiman su zargeta and shikuma she'll handle him tunda sudinma ai agabansu take zubarwa batareda sun sani ba.......
Rubuta magunguna Na'im din yashigayi yana mamakin meya ke hanata shan wadancan din don yanada tabbacin datasha din daza asamu improvement ajikinta gashi she's carying someone's Baby shi yana ina hartake kokarin risking life dinta haka?........
Seda yagama rubuta drugs din sannan yadago yadubi Hamidan
"My patient Adda Hamida".......
Ko kallonshi batayiba don gani take yama rainamata wayau,itace ma Addan don wulakanci baidamu da kin kulashi datayiba yace"kinason inyi admitting dinki anan ne ko you prefer staying at home inyaso se inzo ina dubaki?"..........
Aibatasan sanda tadago tace"gida zani"........
Murmushi yayi sannan yadubi bangaren da Sulaiman yake"take her Home nima yanzu zanzo ni".......

Godiya Sulaiman din yayi mashi yayinda Asma'u takamata sukakoma gida abunsu,Dr Na'im dinma atake yabi bayansu dukda shi seda yabi chemist yasayi drugs din dakuma drips da allurai dazaiyi mata sannan yawuce masarautar........
Koda yaje firstly cewa Asma'u yayi tazubo ma Hamidan abinci ah plate,aikuwa ba ajima ba takawo tareda mika mata karba gani tayi yakafeta da idanu shi alan dole setaci,aikuwa seda taci yafi rabi sannan yakyaleta hakanan dakanshi yaballi magungunan yabata babu yanda ta'iya seda tasha don dukyanda taso ta faki idanunshi tazubar takasa don idanunshi nakanta kuru kuru,seda yatashi tafiya sannan yasamata drip inda yacema Asma'un zaidawo da dare in takoma tace ma Almustapha he's in a hurry shiyasa bai tsaya sun gaisa ba.......
To kawai tace mishi bawai don zata isar da sakon nashi bane ba tunda Itama ba ganinshi takeyi yanzuba..........

*Around 8:00pm...*

Tunda yashigo masarautar da dare Almustapha yafara kira awaya yana tambayarsa inda yake cemasa yayi yana bangaren Mai Martaba wannan dalilin yasashi katse call din batareda ya amsashi ba kafin yawuce bangaren Mai Martaba din direct,gaisarda su yayi cikeda ladabi inda Abban ke tambayanshi mutanen gida dakuma yimashi godiya kan kula da Hamidan dayakeyi dan Sulaiman yazo yamasa bayanin komai....
Cewa yayi bakomai Abba, Allah dai yabata lafiya.....

Amsawa sukayi da Amin dukansu,seda Almustapha da Na'im suka fita yake tambayar shi yaushe Hamidan tafara rashin lafiya don shidai Allah yagani baisai ni ba hana rantsuwa dai lokacin rasuwar Magajiya yaji Sulaiman nafadin tana zazzabi tunda yaje yadubata kuma baisake komawa ba............
Dan bugunshi Na'im yayi playfully Yana"amma dai anji kunya wallahi kuna gida daya kanwarka ma bakasan batada lafiya ba fisabilillahi?"...
Tsaki Almustapha yayi"to anfadamin ne","se anfada maka tukunnan zakasan halin da Yar uwarka take ciki,da ace kana interaction dasu babu abunda zaihanaka sanin halin da sukeciki Yarima".....
Shidai Almustapha bekuma cewa komai ba harsuka isa bangaren Hamidan Na'im din baidaina mishi babatuba kan yana shiga mutane dakuma yin hulda dasu only then zaiji dadin rayuwa....
Su Afiya,Amira, Sumayya da Asma'u nazaune suna dan hiransu sama sama yayinda Hamida kebinsu da idanu kawai,na daraw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ta dara haka na murmushi ma tayi Zaliha kuwa tunda Sumayya tashigo bangaren ta fice don Allah yagani zama kusa da'ita basonyi takeyi ba sabida wani irin bakin ciki takeji su Asma'un ma yaya barekuma yarinyar datake ganin tagama saye mata miji...........
Da sallama su Na'im din suka shigo inda yanmatan suka maida attention dinsu kansu baki daya,sakan baki Na'im yayi yana"Dakin patient din nawa aka maida dandalin hira?".........
Dariya sukayi duka suna gaisheshi inda ya amsa su duka kafin yakaraso gaban gadon yana tambayar Hamidan yajiki.....
Dasauki tace mishi inda su Amira suka tashi suka fice don bama Na'im din guri yaduba Hamidan, Asma'u kam kasa tashi tayi sakamakon kallon da Almustapha din yakeyi mata, shikanshi bazai iya misalta how much he missed her ba dukdama yadan ji dadin ganin tarage ramar datayi kwanaki ganin kallon yayi yawane yasata cewa"Ina wuni" .........
Be ansata ba hakanan baidaina kallon nataba kuma irin kallon nan ne na tuhuma,na"why do you leave me all alone?".

don haka seta tashi jiki sanyaye tashige bandaki tareda rufowa tabbas indai har tacigaba da zama akusa dashi tana kallon fuskar tausayin dayayi zata iya manta komai taje gareshi,dan ajiyan zuciya tayi tareda jingunuwa da kofar bandakin tanata kissima abubuwa aranta.......
"Kinci abinci ne?"......
Gyada masa kai tayi,"Anya Adda Hamida kinci?"

Murkudamai baki tayi"niba Adda bace ba,i'm Hamida so call me with my name"......
Murmushi yayi yanadan shafa suman kanshi"to sorry,Hamida are you sure kinci abinci kinga bazaiyi anashan magani batareda anci abinci ba".........
Cikeda kafula tace"Allah naci"......

"To tunda kince Allah nayarda Hamida,sekuma yatashi daga zaunen dayake yadauko ruwa ah fridge sannan yazo yana balla mata maganin seda ya tabbatar tasha sannan yakyaleta",yajiki Almustapha yayi mata inda tasakar mai murmushi tareda yi masa godiya. Da Na'im yatashi tafiya tare suka fice da Almustapha din don cewa yayi seya rakashi har mota shikuma damuwan shi bewauce yaga fitowan Asma'un daga bandaki ba amma taki fitowa.........
Seda ta tabbatar suntafi sannan tafito kamar munafuka tana tambayar Hamidan ya jiki, murmushi Hamidan tayi tareda cewa"Dasauki",dukdama tun tuni tagane akwai matsala tsakanin dan uwantan da Asma'u sede Allah baibata ikon yin magana bane ba besides couples do fight and ah tunaninta they'll catch up soon babu anfanin shiga abunsu............

Kwanciya tayi gefen Hamidan zuciyar ta na racing kafin dakyar tajanyo wayarta tareda kunnawa don kullum akashe take se intanason anfani da'ita take kunnawa data gama kuma zata kasheta ta ajiye. Kamar wanda yake jiran takunna wayar sega call dinshi yashigo bakaramin bugawa kirjinta yayiba hakanan tasa wayar ah silent don kadama ta dami Hamidan,haka yayita kira yakai sau biyar amma taki dauka bayan kusan mintuna goma kuma sega text dinshi..........

"Why aren't you
Picking my calls?"........
Lumshe idanunta tayi ahankali tanajin bugun zuciyarta na karuwa akai akai sede takasa yimasa reply dukda 85% na part of her nason yi mashi din amma tadanne zuciyar ta,game tashiga tanayi dukwai don kozata samu zuciyarta tadaina tunanin sa amma takasa,she's very sure he's in his room now.........

Almustapha dake kwance kan gadonshi ko canza kaya yau yakasayi tsabar damuwa tayi masa yawa don yanadawowa daga rakiyar Na'im din daki yawuto yazo yakwanta sannan yashiga kiranta kan zaice mata tazo tasameshi ah dakinshi amma taki picking shiyasa yayi mata text shidinma taki reply
"but why?"......
"Wayar bata kusa da'ita komi?",kasa samun amsa yayi hakanan yana kallon screen din wayarshi dakyar ya'iya sake mata wani massage din.........

"Are you there?".....
"Inkinzo kinga massage dina come and meet me in my room"....

Shima tagani amma setayi ignoring ba ajimaba kuma seyashiga sake kiran layin shima kin dauka tayi bakaramin baci ran Almustapha yayi ba hakanan yana mamakin miyasa zataki daukan call dinshi,is she by any chance trying to make him divorce her tawannan hanyar komi?"..........
Kasa bama kansa ansa yayi don haka seyayi wurgi da phone din gefe tareda daukar pillow ya rungume,can jin kwanciyar batayi mashi ba seya tashi cidok yafice ah dakin yajima yana zagaye awajen sashinnasu wanda shikanshi besan zagayen na menene ba......
Dogarayen dake aiki ah harabar masarautar sunyi mamakin ganin yanda yaketa safa da marwa shikadai wannan dalilin yasa uku daga cikinsu suka karaso inda yake kafin sukayi kasa da kansu cikeda girmamawa....
"Barka da dare Yarima".....
Da mamaki yakallesu kafin rai bace yace"Yauwa", because shiko maganarma dasukamai jiyayi kaman yakamasu da duka koya huce takaicin dayakeji akansu,dakyar daya daga cikinsu yace"munga kanata yawo ne kai kadai shine mukazo muji ko lafiya"........
Shiru yayi don yama rasa abun cemusu,aranshi kuwa cewa yake "shikenan mutum bazai fito yasha iska ba sewani abu yafaru",cigaba da safa da marwan yayi batareda yasake bi takansu ba amma seyaga sunshiga binshi ah baya duk inda yayi,inya juya zaikoma ma saisu sake binshi ah baya, bakaramin kafula yayiba amma sebece musu komaiba sukuma they're just trying to protect him ne sunyi tunanin wani abune yafaru ganin basuda niyar daina binshi sekawai yakoma bangaren nasu da niyar komawa dakinshi amma haka kawai seya tsinci kanshi dason sake dubawa ko tana dakinta dukda rabi da kwatan zuciyar naraya mishi batanan din. Koda yasamu batanan seya tsinci kanshi da kwanciya ah dakin nata feeling so lonely,sake duba wayarshi yayi Incase kotamai reply amma shiru dakyar yasamu yayi bacci ranar.........

Da asuba ma yayi tunanin zata shigo dakin yin sallah amma shiru wannan dalilin yasashi ficewa masallaci jiki ah sanyaye,koda yadawo ma seda yasake duba dakin nata amma yanda yabarshi haka yake wani wawan ajiyan zuciya yayi yana mamakin kanshi da kanshi karatu kan tunda jimawa daman ta sallama zuwa shiyasa ma baisa ran ganinta agurin ba,ah daddafe yayi musu karatun kafin yawuce dakin shi yashiga shiri don fita tunda yanada ayyuka akanshi, bangaren Asma'u tunda yacigabada kiranta ajiyan seta sake kashe wayar ma baki dayanta tareda jefata cikin wordrobe din Hamidan sannan takoma takwanta tayi baccinta......

Na'im kullum seyazo yabama Hamida drugs 3times a day wanda duk seya tabbatar taci abinci sannan tasha maganin haka allurar dayake yimata ma,itakam haushin shi takeji don bakaramin takura take gani yakeyi mataba kuma kayan haushin ma tasamu saukin ma bazai bartaba still takura mata yake tasha maganin wai harsaita gamasha duka..........
Akwai ranar daya takura mata dasai taci abinci kafin zatasha maganin bayan kuma bata jimada ciba,wai ai ba'agabanshi taciba so he's not sure ko taci din so dole seta kara kafin tasha maganin..........
"To wai miyasa bazaka yarda naciba?"......
Jijjiga kai yayi yana"kema kinsani ai".......

Harara ta watsamai"makaryaciya nakoma kenan?".....
Ware hannunshi yayi alamun oho yana yar dariya kasa kasa......
Cikeda takaici tace"wai kai wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login