Showing 36001 words to 39000 words out of 235422 words

Chapter 13 - GIDAN SARAUTA COMPLETE

Zeeneert   

06 Sep 2025

3483

dashi tabude littafin ta tashiga karatu batareda wani damuwa ba setakejin yau karatun nawani shiga sosaima.....
Can tana cikin karatun ne seta iso inda takasa ganewa, don haka takarasa gurin shi hoping that he might help ......
Yanajin sanda ta taso jiyayi kaman yatashi ya gudu don da alama zatazo tadameshine Kuma, yana cikin wannan tunanin ne tayi mishi sallama ansawa yayi azuciya kafin tace don Allah I've a question if you don't mind,I mean muna yin course daya and you're ahead of me may be ka iyamin bayani.....
Gyada mata Kai yayi alamar to batareda yadago yakalletaba,nan tashiga yimishi tambayar hartakai karshe,dan shiru yayi nadan dakiku yana tunani,he can explain it but shidai he cannot talk for that long bakinshi seyayi ciwo ai don haka seyadubeta yace"zanmiki bayani in written"....
Damamaki ta kalleshi sannan tace ta ina zangane suma ai in written dinne shiyasa banganeba kamun explaining don Allah tayi maganar tana dan make kafada,daukan littafinta dake kasa yayi yamika mata alamun tatashi tatafi inbata yardaba kenan,cikin sauri tace nayarda karubuta din,yiyayi kaman baijitaba seda yaja mata aji kafin yakarbi littafin yashiga rubutu cikin nutsuwa seda yacika paper biyu na long note duka dauke da bayanin sannan yamika mata yacigaba da karatunshi,kallon rubutun nashi takeyi gwanin ban sha'awa tunda take bata taba ganin handwriting din daya tafi da imanintaba irin wannan ba sannan cikin nutsuwa tamaida hankalinta kan rubutun tashiga karantawa aikuwa segashi tagane don bayani yayi mata sosai kaman yanda zaiyi mata bayani in magana zaiyi....

Seda takai karshe sannan tadauki pen dinta Itama tafara mishi rubutu...

" _Thank you *Mr Taciturn* ,nagane sosai fiyeda yanda inwani mai bayani da baki zaiyimini bayani.i must say you're very talented_"...

Mika mishi littafin tayi tana dan murmushi,littafin yafi minti uku agabanshi beko kalla ba seda tace"Yaya Almustapha!"...
Dagowa yayi yadubeta,nuna mishi littafin tayi da hannu sannan yamaida hankalinshi kan littafin yashiga karantawa sannan yadawo mata da littafin batareda yayi reply ba,murmushi kawai tayi tana dan satan kallonshi sannan ah ahankali ta furta"Mr Taciturn, tareda yin 'Yar dariya sannan tace and the name really suits him".....
Tana cikin wannan tunanin ne taji kaman abu ah gefenta cikin sauri ta kalli gefen nata kadangare tagani yayo kanta aikuwa datawani fasa ihu se kan Almustapha faduwa sukayi dukansu biyun yayinda tana kanshi ta kankameshi sosai ga hawaye nata shatata, lizard! Yaya Almustapha help me!....
Shikuwa tunda tafada jikinshi wani yar yaji kaman electric shock don haka yashiga kokarin tabuketa daga jikinshi amma ina tabi ta kankameshi shi da abun ya isheshine yace"get back to your senses, yatafi lizard din" ....
Dago kanta daga kirjinshi tayi cikeda tsoro sannan tasaukesu kanshi "are you serious yatafi",kasa karasa maganar tayi because she get lost in his dashing eyes gakuma heart dinta daya shiga beating so fast at thesame time,batasan metake ciki ba she just know that she's in another world,the world of Almustapha may be! wanda awannan lokacin zuciyarta takasa cemata takoma nata duniyar,duniyar da kowa ke cikinta sannan inda take din bai dace da'ita ba ah bangaren Almustapha ma hakane tunda yake kallon cikin idanunta yakejin wasu irin feelings dabai taba jiba ah rayuwarshi,a new feeling dabaisan ana jinshiba, feelings din daya kasa defining nashi duk kuwa da irin basira da kwakwalwar da Allah yabashi.shine yafara dawowa cikin trance dinshi har ya farga da condition din da suke ciki cikin sauri ya tureta tafadi gefe don tariga ta sassauta rikon datayi mishi already,tashi yayi cikin sauri kaman wani marar gaskiya sannan yadibi litattafan shi yabar gurin......
Itakuwa tunda yayi gefe da ita takasa tashi donkuwa wani irin kunya ne yakamata gakuma haushin kanta datakeji seda ta tabbatar yabar gurin sannan ta tashi tana salati da dafe kanta, sega hawaye kuma"meya kaiki Asma'u,kinason jama kanki bala'i ne komi,what were you thinking, why were you lost in his eyes wannan abun kunya damai yayi kama",sune abubuwan data shiga nanata ma kanta tafi awa tana zaune ah gurin takasa tashi kuma takasa cigaba da karatun she is just regretting what has just happened,what if he yayi taking advantage of her weakness yamata wani abun yazatayi,mezatacema iyayenta kuka tadingayi sosai kafin daga karshe tayanke ma kanta hukuncin fita harkar Almustapha dukda wata zuciyar na hanata yin haka sede this's the best solution,diban takardunta tayi tawuce gida batareda taje gidansu Zahra dinba because she's not in the mood kuma.....

****
Sanda su Sulaiman suka isa Abuja hotel yaje yakama mata daki sannan yace tahuta anan zeje yadawo,kallon shi tayi sannan tace Yaya Sulaiman anan zamuyita zama?....
Murmushi yayi sannan yadan jaa hancinta"little Angel na isa inbarki ah hotel,sokike Yaya Almustapha yayi raga raga dani kenan?"....
'Dan turo baki tayi sannan tace tonikam inazamuje,yar dariya yayi sannan yace you'll see kamun yaduba wristwatch din hannunshi"I've to go somewhere now innadawo zamuyi magana,in anyi knocking kitambaya waye kafin kibude kinji?"....
To kawai tace mishi kafin yafice yabar ta zaune tana karema dakin kallo,ko ina ah dakin yayi kyau very perfect! 'dan jan soft pillow din tayi takwanta tareda sakin murmushi dukda kuwa tana tsoron ranar komawan ta masarautar dakuma ranar gamuwanta da Magajiya,she never thought for once in her life zatabar cikin masarautar Zaria har ta fita wani gari talk more of ace hartazo Abuja,garin masu kudi dakuma masu kasar baki dayanta bata tashi mamaki bama seda Sulaiman din yadawo yadauketa suka tafi airport don jirginsu da dare zaitashi zuwa Indonesia dukda kuwa da private plane zasu tafi wanda yakasance na Mai Martaba ne kukan murna tashiga yi tareda rungume Yayan nata,I love you so much Yaya Sulaiman.yar dariya yayi and I hate you more little Angel,turo baki tayi sannan tace "hate Kuma?",dariya yakuma yi more than love kenan Sisto,to naji amma tonikam kafada ma su Amira ne, I'm getting worried about them ....
Jan hancinta yayi sannan yace "I told them kada kidamu"....
nanfa tashiga murna sanda suka shiga jirgin kuma tajuyo ta kalle shi with questioning look "mezamuje yi ah Indonesia?".....
Ah takaice yace"to meet a family"....
Gyada mai Kai tayi kawai batareda takuma cewa komaiba,shikuma jingina kanshi yayi dajikin kujera yana tunanin yasu Almustapha zasu Kare ah masarautar dukda kuwa yayita kiranshi ta numbern daya saya mishi tareda wayar amma akashe which means Almustaphan be kunna wayar bama kwata kwata numbern Mallam Hudu kuwa tunsafe yake Kira ah kashe don haka ya hakura besides indai Magajiya tasamu labarin yatafi da Afiya to tabbas su Almustaphan ma zasuji labari shiyasa bai wani damuba......
Afiya kuwa da jirgi yatashi lulawa sararin samaniya seda tayi kauyanci with the help of her Brother tasamu tazama stable
haka jirginsu yadaga zuwa Indonesia (su Afieeya mutan Indonesia).........
****
Koda Asma'u takoma gida setayi kokarin cooling kanta sabida batason Ummi tashiga yimata tambayoyi,seda tayi wanka sannan tawuce bangaren Mommy kaman yanda suka saba zama ah parlourn haka tasamesu anata hira sede babu Asiya cikinsu, gaida Mommy tayi sannan tashiga gaida yayun nata kowa ya ansa amma banda Mubaraq idanunta suka ciko da kwallah tace Yaya Mubaraq don Allah kadaina fushi dani.....
Dubanta yayi ganin hawayen sunfara zuba kaman famfo yace zonan....
Karasawa tayi gabanshi tareda samun guri tazauna,riko hannunta yayi "kekam bakya gajiya da kuka ne?".....
Sa hannu tayi tana goge kwallar dukda kuwa kara zuba suke non stop tace"to ai kaine kake fushi dani",wannan karan dariya duka yan parlourn sukayi ga yanda tayi maganar kafin Mommy tace"to Yaya Mubaraq yakamata adaina fushi da Ma'u hakanan".....
Dubanta yayi tareda dan Kai mata rankwashi"To kinci sa'a Mommy tashigan miki sabida haka nahakura",godiya tashigayi mashi yayinda yace "aini akan godiyar nan dama noodles kika shiga kika dafa mini don nayi kewan dafuwan indomie dinki"...
Cikin sauri tatashi tana "right away,yanzu zan dafa maka Yaya Mubaraq" su Sadiq, Musa da Aliyu ne suka ce muma zamuci Mata ah gidan Doctor Mukhtar....
Yar dariya tayi tareda jijjiga Kai, Hajja dake gefe tanajinsu tayi tsaki sannan ta tashi tashige ciki don aganinta bazata iya ganin kayan takaicin nan ba.....
Hadaddiyar indomie tadafa musu sannan tabaje musu shi ah parlour nanne takejin wai iyayen Mukhtar zasuzo cikin weekend neman aurenta na Aslam kuwa gobe ma zasuzo neman auren Asiya,haka kawai setaji gabanta nawani mugun faduwa yayinda duk wani walwalarta ta gushe don haka bata jima ah gurinsu bama tayi musu sallama takoma bangarensu..... .

****
Magajiya ganin Sulaiman tunsafe be ziyarcetaba ta aika akira mata shi amma se akace mata bayanan yayi tafiyi, hankali tashe tace akira mata isah....
Jikina bari Isah yazo bangaren Magajiya,zubewa yayi gabanta tareda mika gaisuwa irinta sarauta,cikeda zafin rai tace dago ka kalleni!....
Dagowa yayi sannan tace meyene Talatu tazo tana fadamin bangane ba?.....
Cikin in Ina Isah yace "tazo duba Yarima dazu kan kina kiranshi shine nace mata yayi tafiya tun jiya da daddare".....
Kan uba shine abunda Magajiyan tafada sannan tace"kanason kacemin Yarima yayi kusan awa ashirin da hudu da barin masarautar nan amma nibanida labari?"....
Jijjiga Kai yayi alamar eh kafin yace ranki shi dade tafiyar gaggawa ne takamashi,tsaki tayi sannan tace au kamasan da hakan shine bakazo ka fadaba,shiru Isah yayi don ya lura ah garin kare Yariman yajaza ma kanshi,hakuri yashiga bata yayinda tace yatafi yabata guri zata dawo kanshi sanda takeda lokacinshi kafin tawuce bangaren Mai Martaba direct harya kwanta yana shirin bacci tashiga dakin,dubanta yayi ganin ranta ah bace yatashi yazauna...
"Magajiya lafiya?"....
Zama tayi bakin gadon kafin tace "yanzu fisabilillahi har Sulaiman yayi tafiya bawanda yayi tunanin ya fadamin?"....
Kallonta yayi cikeda mamaki sannan yace shidin bai fada miki bane?.....
Kai tsaye tace befadaminba nikam....
Tabe baki Mai Martaba yayi sannan yace to bansan dalilinsa nayin haka ba sede niyacemin ana nemanshi ah makaranta Kuma nabarshi yatafi zedawo ai kafin bikinsu,zare idanu Magajiya tayi sannan tace Mai Martaba kana nufin Sulaiman London yatafi?.....
Jijjiga mata kai yayi kafin tashiga salati,tsaki Mai Martaba yayi sannan yakoma yakwanta don yasan halin Magajiya da exaggerating akan abunda baikai yakawoba,yana kwancen yace inzaki kwantar da hankalinki gwanda kikwantar da hankalinki yafi bawai kitsaya kina tada zaune tsayeba kifita kibarmin daki bacci zanyi"...
Rai bace tatashi tafita tana masifa,haka adaren bayin ta dazasu tayata canza kaya zuwa na bacci seda sukasha fada da mazga don kuwa akansu tashiga huce haushi haka tadinga Kiran layin Sulaiman na London amma baya tafiya dakyar tasamu ta kwanta bacci.......
.....
Wuraren karfe biyun dare kowa yayi bacci ah masarautar se dogaraye dasuke gadi ne kawai,wata mata ce sanye da bakin kaya from head to toe tashigo dakin Magajiyan tawani hanya hannunta rikeda wuka cikin sanda tadingayin kusa da gadon Magajiyan, Magajiya dake shatata bacci tayi juyi kaman zata tashi yayinda matar dake lullube cikin bakin kayan tayi saurin buya kusa da gadon wanda karan saukanta kasa yasa Magajiya tashi,dube dube tashigayi ah dakinnata sede bataga kowaba don hasken harabar masarautar na dan hasko cikin dakin,komawa tayi ganin ba kowa tacigaba da baccinta seda matar ta tabbatar takoma takwanta sannan ta tashi takaraso jikin gadon wuka tadago tana niyar kaima Magajiyan dede lokacin Magajiya tabude idanunta sekuma ga Talatu ma tashigo don Itama daga dakinsu dake dab dana Magajiya su masu kula da ita taji kaman motsin mutum,wani irin ihu daga Magajiya har Talatun suka saki wanda yajanyo hankalin guards din, dasauri Matar kuma tabi ta hanyar data shigo dagudu sanda guards din suka shigo Talatu tanuna musu hanyar da Matar tabi kafin takaraso gurin Magajiya dake haki tana sharban hawaye shikenan dayanzu an harba da ita lahirafa........

Talatun ne tace"Uwargijiyata sannu?"...
Tureta Magajiya tayi tana goge kwallarta kafin tace kinga fuskarta ne?......
Jijjiga kai Talatu tayi kafin tace aa banganiba fuskarta ah rufe take,tsaki Magajiyan tayi sannan tace aida kinbita kin kamota yanzu ba lallai su sugantaba,Talatu datayi tsumu tsumu Kai akasa tace kiyi hakuri yayinda ah zuciyarta kuwa cewa take"aiko ciwon haukane yakamata batabi mace irin wannan da wuka sh hannunta ba",ana cikin hakane sega guards din sundawo Magajiya already ta lullube jikinta tana tsaye tace baku sameta ba?.....
Babban cikinsu ne yace ranki shi dade bamu gantaba wallahi sede munga kaman anbude wata tsohuwar kofa tacan baya inatunanin tanan tashigo, cikeda tashin hankali Magajiya tace to wacece haka take niyar hallakani ni Magajiya....
Shiru kowa yayi agurin,yayinda cikin sauri kuma Afiya tafado ma Magajiya ah rai,duban daya daga cikin guards din tayi sannan tace kaje kasa ah sanar da Mai Martaba abunda yake faruwa kukuma ku buyoni tayi gaba suka bi bayanta har zuwa gidan yari, Sarkin gidan yari daganin Magajiya nan take cikin shi yashiga dura ruwa,dubanshi tayi rai bace sannan tace kafito min da tsinannan yarinyarnan I know she's behind all this.....
Zare idanu Sarkin gidan yari yayi sannan yashiga kiran daya daga cikin dogarayen dake gadin cell din da akasa Afiya,cikin sauri dogarin yakaraso yana mika gaisuwa,Sarkin gidan yari yayi kaman baisan komai da al amarin barin Afiya gidan yari ba yace "Kai Habu kafito da yarinyar can",cikeda tashin hankali Habu yasauke kai kasa ranka shi dade ai Yarima yazo yatafi da ita tun jiya da dare mu munyi tunanin Hajiya ce tasakashi bekai ga rufe bakiba Magajiya takai mishi wani wawan mari"ninasaka shi kakeson kacemin komi,kokataba ganin inzanyi abu inasakashi?"....
Iye,shidai kanshi na kasa bece komaiba dukda kuwa yaji zafin abunda tayi mishi aikoba komai taduba girman shekarunshi tayi mishi afuwa sede ashe yamanta wacece Magajiyan,Matar da batasan mutunci dan Adam ba domin batadaukesu abakin komaiba.... suna cikin hakanne akashiga announcing Mai Martaba ya iso,sa hannu tayi kan lips dinta tana ma Sarkin gidan Yari nuni dayayi shiru kada yace komai sannan tayima Habun ma haka gyada mata Kai yayi......
Alokacin Kuma Mai Martaba yakaraso,meyake faruwa tambayar dayayi kenan...
Kicin kicin Magajiya tayi da fuska sannan tashiga bashi labari tun abunda yafaru na sa abinci ah guba dakuma nayau din sannan takarada"tunda akaso kaimin wukar yarinyar tayi nasarar guduwa shine nace barinazo gurin wannan din ko itace aikuwa inazuwa suka cemin tagudu daga gidan yari suma neman ta sukeyi"......
Sarkin gida da Habu speecchless suka zama donkuwa sune sukasan komai tunda sauran lokacin da ake bayani duk attention dinsu yakoma ga tarban Mai Martaba da aka fadi isowanshi......
Mai Martaba ne yace ma guards din duk yanda akayi batabar masarautar ba may be tanacikin harabar gidan su rabu tako Ina ah nemeta,dogarin daya ga hanyar data fitan ne yazo gaba yayima Mai Martaba bayani.....
Cikeda mamaki Mai Martaba yace ikon Allah,to duk yanda akayi wacce tasan kan masarautar nan ne domin kofarcan bakowa yasan da'ita ba,anjima da daina anfani da ita tun kakanni.....
Magajiya ne tace"shekarunsu nawa acikin Masarautar nan ai babu inda basu saniba".....
Kallonta Mai Martaba yayi sannan yace kinada tabbacin ita dinne?.....
Ahankali tace "Mai Martaba inba itabane wanene zeyi yunkurin kasheni tunda ba ataba irin abunnan ba acikin Masarautar nan,babu wanda yataba kaimin hari se ita,to inko ba itan bace to wanda tasakata ne,cikeda takaici tace Kai itannema tunda dai gashi tayi escaping"........
Gyada kai Mai Martaba yayi sannan yace wannan binciken zamuyita gobe yanzu dare yayi,sannan yadubi Sarkin gidan yari yace yakira masa Sarkin sojoji babu bata lokaci segasu sundawo, Mai Martaba ne yace masa a sake tightening securities more especially ta bangaren Magajiya ......
Cikin sauri Magajiya tace itafa bazata koma dakintaba bin Mai Martaba zatayi inyaso ah sa securities din ah nashi bangaren.......
cewa yayi to kafin suka tafi,duk wannan abunda yake faruwa su Almustapha basu da labari tunda cikin darene abun yafaru abu dayane yabashi mamaki yau dayaje duba Afiya kwata kwata Sarkin gidan Yari yahanashi shiga.....
Washegari dasafe tafiyar gaggawa takama Mai Martaba zuwa sokkoto wanda hakan yabama Magajiya daman yin abunda tayi niyar aikatawa tun jiya don ita bazata tsaya har ah aikata lahira batareda tadauki matakiba kuma bazata tsaya jiran Mai Martaba ba.....
don haka shida waziri suna tafiya da tawagarsa zuwa sokkoto itama tasa aka kiramata wasu daga cikin dogarayen gidan sannan tace suje su tabbatar yau su Almustapha sunbar masarautar nan sannan kuma batason taji labarin yakoma kunnen waziri don kuwa zatayi musu abunda basu taba tsanmani ba,jikina bari duwawu na zikiri dogarayen sukayi gidan su Almustapha....
Amira na sharar tsakar gida taji anbangazo kofa,cikin sauri tadaga kai nan taga dogaraye sunkai goma batareda sun mata magana ba suka shiga dakin da Ummi ke kwance sannan suka fara diban kaya suna fita dashi waje,Kuka Amira tashigayi tana basu hakuri"wai miye hakan kukeyine?"...
me muka Kuma, hakanan me muka tare muku acikin gidan nan,daya daga cikin dogarayen ne yakai mata maka sannan yace yauko kubar gidan ko muyi waje daku bayan mungama fidda tsunmokaranku,cika umarnin Magajiya mukeyi.......
Almustapha dake daki yanajinsu,amma ko gezau beyiba Amira data gama yimusu magiya ne taga basuma kulataba yasata yin dakin Almustapha tana kuka,Yaya Almustapha don Allah kafito kaga abunda sukeyi ah waje......
"Ahankali yace let them do their work,ihunki bazaisa subari ba".....
Sakan baki tayi tana kallon shi da mamaki don kuwa ranta yabaci,bedamuda tsayuwar datayi akanshiba sema tashi dayayi yafita ah dakin ah lokacin sukuma sungama tattare kayan se Ummi dake kwance kan katifa ne suna shirin shiga dakin yayi saurin shiga tareda rufo kofar yasa sakata zuciyarshi nayi mishi wani irin Kuna,he can let them do anything but bazai bari suyi disgracing mahaifiyarsa ba, ahankali yadinga takawa har ya Isa gabanta sannan ya tsuguna cikin sanya hawaye yagani ah idanunta yana zuba non stop,rimtse idanunshi yayi shima ahankali besan sanda shima hawayen yafara bin nashi kuncin ba he can be strong agaban kowa,he can hide his tears from anyone amma bazai iya taba boyema Ummi ba dukda kuwa halin datake ciki because the situation is so tough daya rasa inazaisa ransa......
Ahankali yadaura kanshi ah jikinta tareda rike hannunshi cikin nata,yanajin dogarayen na buga kofa kaman zasu ballah amma bai damu ba sema cikin kuka yace "Ummi get well soon,kitashi don Allah as you can see irin injustice da ake mana ah gidan mahaifin mu,Kara kankameta yayi yana kuka me tsuma zuciya"we really need you Ummi!we need your support"...
Sunfi 30 minutes ahaka yayinda dakyar ya iya sassauta kukan nashi don ayanzu kuwa har dogarayen sungaji da bugawa se Amira dake faman Kiran sunanshi tana cewa yabude kofar don Allah......


*Zeeneert*

Vote
Comment
Share!....
[3/23, 5:24 PM] >?p?: *GIDAN SARAUTA*

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 12*


Jiki ah sanyaye yatashi yabude kofar cikin sauri Amira dake kuka tashigo cikin dakin tana Yaya Almustapha inata buga kofa muyi mubar gurin don Allah nan suntafi fadama Magajiya abunda kayi kada tazo tasameka....
Kallonta kawai yayi don shi tunaninshi daya,inda zasuje tunda dai su ba kudiba bare wani gidan bare ace sukoma can.......
Duban Amira yayi sannan yace kishiga ciki and kirufe kofar taciki I'm coming, juyawa yayi zai tafi yayinda tana binshi da kallo,harya fita ah kofar seya dawo kuma yadubeta"karki bude kofar harsaina dawo"...
Gyada mishi kai tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login