Showing 87001 words to 90000 words out of 364327 words
da ka kwanta da matarnan,lallau namiji d'an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina" ta fada tana dora hannu a ka tare da qarewa gadon nasa kallo,tsaye sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato badon ta kora yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole wasu matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa tayi ta dafa kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta
"Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi bane yanzu aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana third round ba" ta fada tana kewayeta tare da komawa bangaran gadon ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.
Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin irinta ba
"Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa ba,duk wanda yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane kurenki,saikin gane shayi ba komai bane face ruwa,sai na cusa miki baqinciki fiye da wanda kika cusa min" sai ta waiwaya inda lukman ke zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda aka saba sai ta ganshi zaune ko gezau
"Kai kuma tashi mu wuce dakina" ta fada a tsawace
"Ba inda zanje" ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan ransa yana qoqarin danneta,idanuwa ta zaro,jikinta ya soma bari,ba shakka alqadarinta gab yake da karyewa,kasa magana ma tayi sai kallonsa da takeyi
"A'ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa" a fusace ta waiwayo ta tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin da tayi taga taga zata fadi lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa tana murmushi kamar ba ita aka yiwa ba
"Babu komai,duk cikin haushi ne" qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin zubo mata,da hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya ta gani har ta gane ta soma samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura hankalinsa ya soma tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba jikin hajiya wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar duk da taji shigowar karima gidan.
Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta falon,islam suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa
"Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi,kuma tace ba zata dawo ba" wani matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido yana dubanta
"Tun yaushe?"
"Dazu,naje dakinka baka nan" duk sai sumayya taji babu dadi,kada dai abinda ya faru dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun yarinyar yana fadin
"Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da su suna dakinsu ina zato" amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi yarda ta kama hannuwanta haka suka tafi,koda ta shiga dakin suna zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji tausayinsu ta dinga jin babu dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai nuwaira kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu itama ta ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi kicin kicin taqi shiga sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci sannan ta musu addu'a ta bar dakin.
Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan ya sanyashi dagawa cikin hanzari yana cewa
"Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi kaya,yaji da girmanki da komai"
"Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma ka sanar da wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu cewa,ta bar murna karanta ya kama kura,babu inda zani ina nan dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi wallahi sai ta gwammace kida da karatu,don babu wata 'ya da zan bari ta shigarmin rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma wahal da kanka kace zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai randa na dawo da karan kaina,ina fata ka gane"qit ta datse kiran sai yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata yana amsa sallamar da sumayya tayi masa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
4⃣4⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*innal laha la yazlimu misqala zarrah*
*_haqiqa Allah baya zalunci daidai da qwayar zarra(ko qasa ma da abinda yafi qwayar zarra qanqanta)*_
_______________________________
Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da mamansu ne,ta dubi lukman
"Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam,kada a ja abun yayi nisa don Allah,yaran na buqatar mamarsu" kai ya kada baison gaya mata wani abu da zai daga mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura ta bar gidan sai yake jin kamar an zare masa wata qaya data tsaya masa a maqoshi
"To naji" kawai ya fada.
Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku yace kada ta sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata dawo,ai ta saba ba yau farau ba,hakan ya sanya ta tsuke bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada hankali sosai kan rashin dawowar mamansu ba.
Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan yayi dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya ta fara fuskantar matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke da ita,amma sai ta jure tayi amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara janye qananan,nuratu basma da syyada,islam ce kawai ta taqi biyuya,ta soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta tattarata ta watsar gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na annabawa da sahabbai,suna bala'in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu abubuwa da dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya ba,kamar alwala,sallah,sallama idan zasu shiga guri,addu'ar sanya kanya,addu'ar bacci da tashi daga bacci,addu'ar shiga bandaki data fitowa,addu'ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi sukeji,nuwaira tafi kowa murna takance
"Anty dama tuntuni kema 'yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar qur'ani ko?" Dariya takanyi tace
"To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah",tarbiyya take basu sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi fisabilillahi,don har ga Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da kakarsu na gwada mata qauna.
A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan kaga sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar son yara,abun ya yiwa hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da addu'ar kada Allah yasa karima dawo,don ita kanta yanzu anan bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta suje su kwana tare da ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin girmanta,ta bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a kwance,sau tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da nutsuwa ya samu sosai irin wadda bai taba samun irinta ba tunda ya fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai kuma yi fatan kasancewa da ita har qarshen rayuwarsa,hatta da mai gadi da mai aikin gidan sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu 'yanci.
Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam sun mance ma basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan tada zancanta shikenan an wuce gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu baki daya saboda haka nuwaira ta samu matsayinta na babba a gidan,a yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da bata isa ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau zasu daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah zai sashi a wuta,ta wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu yadda zasu gane haka ma aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun san wuta.
Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk wanu ilimi da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya yarje mata kan ta nema musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin karatunsu saboda haka ta yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka gama musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna suke da fara zuwa makarantar,idan suka dawo tare suke bitar dukka karatuttukansu,wani dadi hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin duhu sai da Allah ya kawo musu SUMAYYA HASKE.
*KUNDIN QADDARARTA*
Ya sake bude mata shafi ne daga lokacin da karima ta cika wata biyu da rabi da barin gidan,sauyin data fara gani daga lukman din,kusan tun bayan tafiyar karima sumayya ta dorashi kan ibada saboda gunewa faruwar wani abu,cikin sati gaba daya ta fuskanci ya zama mai son jiki da wata muguwar kasala,da qyar yake iya sallolinsa na farilla balle akai ga na nafila,idan qur'ani suka dauko zasuyi tilawa yadda suka saba sai ya soma gyangyadi daga nan sai bacci,idan sallar asuba ce kullum sai ya makara sai tayi da gaske,duk wani abu na ibada ya zama very lazy akansa,tun abun na bata mamaki har ya soma bata tsoro,hakan ya sanya ta samu hajiya da maganan,sam bata kowa komai ba tace sumayyan taci gaba da haquri da kuma qoqarin ci gaba da dorashi a hanya har ya daina,kuma itama zata yi masa fada
A hankali sai abun ya soma cin tura,hatta idan yana bacci bai da aiki sai kiran sunan karima,idan ya tashi kuwa washegari haka zai yini babu wannan walwalar sam.haka kawai yake jin rayuwarsa da zuciyarsa cikin takura da qunci,ji yake kamar yana cikin wata kurkuru,burinsa kawai yaga karima cikin gidan,saidai duk da haka bai taba furtawa sumayya ba.
*_Bayan sati d'aya_*
Bayan sallar isha'i ne dukkansu suna zaune a falom gidan banda hajiya dake bangarenta saboda yau da wuri ta kwanta,sumayya da nuratu da nuwaira na zaune tana koya musu aikin gida(assigment)da aka basu a makaranta,basma na saman kujera tana bacci tun sanda suka gama cin abincin dare,sai islam dake kwashe kwanukan da suka ci abinci da su tana shigarwa kitchen.
Lukman ne ya fito falon a gaggauce wanda tunda ya dawo daga kasuwa yana cikin daki bai fito ba sai yanzu,hannunsa riqe da dan mukulli,daya hannun nasa kuma riqe da hularsa,kana ganinsa kamar wanda aka jefo ko aka tunkudo,daga kai sumayya tayi tana dubansa sanda ya giftasu zai fice ganin bai cewa kowa komai ba
"Abban nuwaira" waiwayowa yayi yana dubanta tare da amsawa
"Ina zaka fita haka tara na dare?" Ta fada a marairaice
"Sorry airphort zani,yanzu zamu dawo" ya fadi yana ficewa da sauri jin wayarsa na ringing,kanta ta maida suka ci gaba da assigment din da yaran,hakanan taji gabanta na yawaita faduwa,hasbunallahu wa ni'imal wakil ta dinga maimaitawa,suna gamawa ta tattara yaran duka suka tafi dakinsu,sai da kowa ya sanya kayam baccinsa ya karanta addu'ar kwanciya bacci suka kwanta sannan ta rufo musu dakin ta koma nata dakin,alwala tayu tayi shafa'i da wutirinta sannan ta zauna ta karanta suratul mulk,har ta gama abinda take bata ji shigowarsa ba,saboda haka ta sanya hijabinta ta nufi bangaren hajiya.
A kashingide ta sameta riqe da carbi,ganin sumayyan ya sanyata zama tana murmushi
"Yanzu kuwa nake zancanki a zuciyata" itama murmushin take tana cewa
"Hajiya baki bacci ba?"
"Kin ganni nan wlh banyi ba,gabana ne yake ta faduwa sai na tuna dazu banyi waraddallahu ba,sai nake yinta yanzu (waraddallahul lazina kafaru bi gaizihim lam yanaluu khairaa,wa khafallahul mu'umininal qital,wa kanallahu qawiyyan aziza,ana karanta ta ne qafa dari bayan sallar asaba kariya daga dukkan kaidin wani maqiyi dake nufarka da shi in sha Allah)"
"Ai gwara hajiya" ta fada tana tunanin faduwar gaban da itama take ji tayi dai dai data hajiya kenan
"Ina lukman din kuma?"
"Ya dan fita ne hajiya yara kuma sun kwanta saboda makaranta goben"
"Sannunki kedai sumayya,Allah yayi albarka" "amin hajiya"ta fada tana murmushi kanta a qasa,shiru ne ya biyo baya kafin su soma taba hira kadan kadan,ganin har sha daya na dare tayi ya sanyata yiwa hajiyan sallama ta koma sashenta.
Tana zaune har sha daya da rabi sannan taji muryar lukman,a hankali ta tashi ta leqa,shine a gaba janye da akwati daya hannun jaka,sai KARIMA dake biye da shi a baya,da sauri ta saki labulen ta koma da baya tana kiran sunayen Allah,sannu a hankali nutsuwa ta saukar mata,sai ta daura alwala ta kwanta,don jikinta na bata lukman ba zaya nemeta a yau ba.
Ilai kuwa bata sake jin motsinsa ko na karima ba har bacci yayi awon gaba da ita.
****** ******* *****
Washegari yadda suka saba haka tayi bata fasa ba,ita ta tashi yaran baki daya sukayi sallar asuba,sannan ta dafa ruwa mai zafi islam ta fara yi sannan nuwaira ta dinga yiwa qananan tana tura su islam na shiryasu ita kuma tayi daga qarshe,sumayya kuma na kitchen tana hada breakfast da wanda zasu tafi da shi makaranta,abinda dukka a da basu saba yi ba amma a yanzu ya zame musu jiki.
Sun shirya tsaf suna karyawa ya zagaya ta buga dakin karima don taga idan sun tashi ta tura yaran su gaida mamansu kan su wuce,saidai har ta gama bugunta ko tari bata ji anyi ba,abinda bata sani ba lukman na jin bugun,ya kuma san sumayyarsa ce,kamar ya zura a guje ya bude saidai ina sam bai isa ba,saboda bai samu umarni ba,tunda ta dawo a jiyan qasan zuciyarsa ke a cunkushe cike da baqinciki bacin rai da tsananin tsoronta,amma a fili tsantsar farinciki ne da tsananin biyayya bayyane a fuskar tasa,abinda zai baka mamaki tunda ta dawo bai taba kwatanta tambayarta inda ta tafi da aurensa a kanta ba kuma ba tare da izininsa ba har na tsawon wata biyu ba,a lokacin ma yana bandaki yana wanke mata tana son shiga wanka saidai ya hada qura a tsawon wata biyu da bata nan tunda ba wani ke shiga ba gun nata na a rufe ne.
Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu ma ya iso ta dubesu
" mamanku fa ta dawo jiya da daddare"ta tsammaci zata ga tsantsar farinciki a fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa,babu wani zumudi ko doki,nuwaira kuwa tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta rakasu suka fice sannan ta dawo ta gyara falo zuwa kitchen ta barwa mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta leqa bangaren hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata 'yan gyare gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi tayi ta karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata kewa,zuwa yanzu sum shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji babu dadi kasancewarta mai son yara.
Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai ba har sai da taji cikin taqama tana fadin
"Ina yara na" cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na cewa
"Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu" cikin harzuqa tace
"Eh wato suma an shige musu za'a shanyesu a rabani da su kenan?" Sai ta saki wani shu'umin murmushi tana kada kai
"Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma" ta fada tana yin gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi bayanta,kai ta jinjina bayan fitarsu
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" ta fada tana kada kai ganin hannun agogo nason komawa baya game da lamarin lukman din.
Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada hajiyan ma ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da aure,sosai hajiyan keji qarfin zuciyarta sam babu wani dar da taji balle taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda lallai idan kayi sakaci da addu'a babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da cewa akwai QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU'A.
Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata,baki ta saki tana kallon yadda suka sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira da islam,lallai sumayya ta sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu farraqu ba ita da au ta barsu suka shaqu haka,tana gani suka sauya kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna sanya hijabansu sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su kariman ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take
"Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama" nuratu ta fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta amma sai ta wayance da cewa
"Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga dawowarku daga boko ko hutawa bakuyi ba" islam ce ta maqe wuya tana cewa
"Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa ana wuceka a karatun" ido ta kuma zarowa mamki na sake kasheta,lallai sumayya tayi amfani da irin surkullensu ta rabata da yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa
"Don ubanki da ni kike jayayya,ku cire kayanku nace babu inda zaku" sumayya ce ta bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa
"Haba maman nuratu,meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa farincikin zuwan yaranki makaranta,ba girmanki bane" sai ta waiwaya ga yaran da sukayi carko carko suna kallon karimar
"Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura" da sauri suka fice kuwa daya bayan daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli sumayya
"Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na baki shi nake jira" tana gama fada ta fita
"Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin ubangiji nake nemawa rayuwata" ta fada tana gyara dakin yaran da suka bata