Showing 354001 words to 357000 words out of 364327 words
tsakanin kaduwa,banda momy wadda ta zube a qasa ba tare data shirya ba,duk da cewa furuci daya ne yake sabo a wajenta
"Eh....doctor james shi ya saida min qoda ga wani mutumi,amma mahaifa ni da kaina na kai kaina aka cire min ita" rintse idanunsa almustapha yayi
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya dinga furtawa can qasan ranshi,bakinshi ne kadai ke motsawa
"Nayi tunanin cewa haihuwa bata da wata rana matuqar kana da kudi,na dauka abu mai kyau nayi tunda mommy ta juya tata mahaifar,almustapha,idan kaso ka yafemin idan kuma ba zaka iya ba duk daya nasan idan na mutu wuta zan tafi,amma dai ina roqonka ka yafemin" ta fada tana zubda qwalla,rasa me zaice yayi?,a wacce duniya yake ciki?,hannunta ne kawai riqe cikin nashi,hango sumayya tayi dake sharar qwalla
"Zo...zo kema" sautin kukanta ne ya dadu,firgici da tsoro na cikata,wacce iriyar duniya ce wannan muke ciki?,da qyar ta iya tashi a daddafe ta isa gaban gadon itama saitin kanta
"Duk naga abubuwan da kike a zamanki da almustapha,wanda a sannan wani abu ya kange zuciyata na kasa ganin kyawun hakan bare nayi koyi,wanda ina da tabbacin ko nice shi a wannan bigiren dole na soki,a baya laifinsa nake gani,amma a yanzu na tabbatar da cewa baida laifi ko kadan,banfa san kwanansa da tashinsa ba,bansan cinsa da shansa ba,bansan me yakeso da wanda ke qona ranshi ba,duka ba ruwana,kawai ya jiqani da kudi ya bani freedom shikenan,girki kadai nasan na taba yi masa wanda zai iya dan shiga sahun nuna kyautatawa bayan shi din tunda muke da shi ban taba nema na rasa ba wajensa,koda zan jera wata ina tambaya,don me ya samu mai masa dukka irin wannan kulawa hakan zai kasa sonta?,ki yafemi kema duk da ba lallai yafiyar taki ta amfane ni ba" kuka ta saka sosai,tana jin su'ad kamar 'yar uwarta,a iya zamanta da ita banda furuci ko kallo bata taba wani abu na cutarwa a gareta koma bayan wannan ba,akan me zata riqeta?,meye zainab karima da a'iza basuyi mata ba?,tamkar zata shide ta furta
"Ki daina fadin haka,ki daina yanke qauna daga rahamar Allah,kowanne bawa da kalar qaddarashi,bakisan rayuwar da nayi ba abaya wanda ban taba tunanin a yanzu zanyi rayuwa irin wannan ba,ki godewa Allah daya sanya kika gane kuskuren naki,duk wanda kuma ya yafe maka ta karbu har a wajen Allah,nikam bakiyimin komai ba,ba abinda kika yimin,na yafemiki ina roqon Allah ya baki lafiya,ki yafemin nima idan na taba bata miki koda da mugun kallo ne" murmushi ta saka
"Kina da zuciya mai kyau wanda na tabbatar da kece na ganki cikin ciwo irin haka ba lallai na tausaya miki har nayi miki kuka haka ba,baki taba yimin komai ba saboda ko yaushe kina takatsantsan da hakan,koda kin yimin ma ya wuce har bada.....ki riqe almustapha da kyau wallahi kun dace....ya hada duk wani hali mai kyau amma rashin samun tarbiyya ta gari daga iyaye na gari ya janyo min na kasa riqeshi har na mori rayuwa mai inganci....ki kawo min 'yan biyu na sake ganinsu,na tabbatar da ace na zauna nayi rayuwa mai kyau da tuni ni haifesu....ummi" ta kira ummi dake gefe,itana qarasowa tayi
"Duk cikin yaranki kinfison almustapha,amma kika yi haquri kika zuba min ido ina yiwa rayuwarshi yadda naga dama,kinso nunan hanya kaman yadda baba yayi amma na taka miki birki,a ranan na miki rashin kunya gatse gatse wanda ina da yaqinim baki gayawa kowa ba sai yanzu dani na fada,kiyi haquri ki yafemin ummi,ki nema min gafara wajen duk wanda na taba batawa" itama ummin share qwalla take,tana ajjiye mata ummulkhir da ummu kulsun gefanta tana dubansu su'ad din
"Ba wanda baya kuskure cikin rayuwarshi su'ad,ma'aiki yana cewa tabbas ba don kuna ainata zunubi ba da tuni Allah ya tafiyar daku ya halicci wadansu,kuskure siffa ce ta dan adam saidai mafi alkhairinsu sune masu tuba,na yafe miki har abada,Allah ya tashi kafadarki don ya ara miki daman a nan gaba"
"Na gode ummi" ta fada tana shafa kansu ummulkhair a hankali ta furta
"I love you my kids"ta fada tana jin qaunar kyawawan yaran har cikin zuciyarta.
Alhj abdus samad dake dafe da kanshi wanda tuni hawaye suka wanke fuskarshi sharkaf ya matso ya kama hannunta bayan ummi ta debe yaran ya soma neman gafararta,ya tabbatarwa da kanshi cewa ba shakka yayi babban kuskure na sakaci da sanya ido a rayuwar da iyalinahi keyi a matsayinsa na uba,wanda yake mai kiwo ne za'a tambayeshi a kan abinda aka bashi kiwo
"na yafe maka daddy...amma ko nan gaba Allah ya azurtaka da wasu yaran ka kula da su,na tabbatara addininmu yana da tsari wajen bawa yaro tarbiyya kabi wannan tsarin,ina da yaqinim shi kadai ne ingantaccen tsari" hawayenshi ya dinga sharewa yana jera mata addu'a suna amsawa,wanda yana gamawa ya miqe ya fice,wata nadama na shigarsa,shi kansa sai a yanzu ya farga,meye amfanin dukiyar da yake yunqurin tarawa wadda ta hanashi tsayawa ya duba gidanshi da rayuwar da suke kai?,qememe su'ad din taqi yarda ta kalli mummyn ko tayi magana da ita,so take kawai ta ganta bata dakin,kaman wasa abun amma sai gashi ta birkice da gaske,tilas mummyn ta fita hannunta saman ka tana kuka.
Ranar baki daya sumayya ta dinga kula da su'ad din,sosai su'ad din taji dadj,don addu'o'i ta dinga tofa mata wajen da tace yana mata ciwo,duk inda ta mata addu'ar kuwa sai taji ya lafa sai kuma idan ya sake tasowa,qarfe shida na yamma almustapha yace su wauce masauki ya kaisu,qi sumayyan tayi tace a barta a nan,ummi tace bazai yiwu ba ga yara,duka duka kwansu talatin ko arba'in bata cika ba,duk da nauyin ummin da take ji amma hakan bai hanata sake roqarta ba,baba ne ya sanya baki su barta din,tunda dakin baida maraba da gida ba wata matsala bace,fuskar su'ad kawai zaka kalla kasan taji dadin hakan,sai ta saki murmushi,ranan kusan kwanan zaune sukai da su'ad din,tuni 'yan biyu sukayi barci,itakam tana zaune,tayi sallah ta zauna ta huta,duk motsin su'ad din tana ankare da shi,itama su'ad din idanunta na kan sumayya,sai yanayin nata ya dinga burgeta,sam batasan da wannan rayuwar ta yawan yin sallah ba,banda ma almustapha ya tsaya kanta a tsaye sallar ma ta farilla ojoro take mata,sai daga bisani ya sanyata ta gyara da qyar
"Zanso nima inyi sallahr nan haka,akwai lada ko?" Murmushi sumayya ta saki,tana jin tausayinta har cikin zuciyarta,kana kallonta kasan gagarumin ciwo ke cin jikinta,a haka ma akwai kulawa kenan
"Akwai lada mai tarin yawa,sallah tana kusantar da bawa zuwa ga ubangijinsa" kai ta kada
"To ya za'ayi ina son nayi nima,king tun isha'i ban sake ba"miqewa tayi ta iso gareta saboda ganin tana yunqurin gyara hannunta,a tausashe ta gyara mata tana cewa
"ba lallai sai sallah ba kadai zata kawo miki lada,ko jinya ma idan kanayi ai kankarar zunubi ce,idan kina so kina iyayin istigfari salatin annabi da sauransu kina daga kwance"
"Ok,kaman yaya?" Koya mata tayi,ta kama ta dinga yi,a hankali ta dinga jin sanyi da sauqi cikin jikinta da zuciyarta,ta dinga satar kallon sumayya sanda take shayar da ummulkhair tana sha'awar rayuwarta,ashe rayuwa mai dadi nutstsiyar rayuwa itace rayuwar da addinin musulunci ya tanada ya kuma koya mana?,lallai iyayenta sun yiwa rayuwarta babban gibi.
Sanda almustapha ya kawosu da safe sannan ummi tace ya dauketa ya kaita gida ta huta anjima sai ta dawo,ba musu ta amsa,kowa yaji dadin yadda yaga salama tattare da su'ad din,suna tafe cikin mota shiru,yana dauke da amatullah wadda ke barci yana wasa ya hannunta,yayi kewar yaran sosai,sai yaga kaman an qara musu girma da wani wayo,sosai kamanninsu ke fitowa da shi,zuciyarshi a cunkushe take matuqa,babban abinda ke gabanshi yanzu yadda zai cimma doctor james,duk da alhj abdus samad yace ya qyaleshi kaman yadda su'ad din tace ita ta jawa kanta,duk abinda mutum yayi kanshi,saidai sam zuciyarshi bata nutsu da haka ba,har suka isa dakin daya kama musu a hotel din wamda babban falo ne da dakuna uku a ciki baice komai ba,ya kwantar mata da yaran sannan ya miqe suka hada idanu,duk itama sai take jinta ba dadi
"Ki wanka ga abinci can,ina zuwa" ya fada yana juyawa,binsa tayi da kallo kawai tana kada kai,baki dayansu sun zama abun tausayi cikin qaramin lokaci har ita din.
Cikin kwana goma sha hudu sumayya ke kwana da su'ad din,zama suke cikin asibitin tamkar ya da qanwa,a nan ta koyawa su'ad din wasu abubuwan da take ganin ya kamata ace ta sani,sukan zauna suyi hira sosai da ita cikim sakewa kaman sun jima da soma mu'amala,jikin su'ad din da sauqi sosai,har takan iya zama sumayyan ta jinginata,ita ke gyara mata jikinta,ta bata abinci,ta daura mata alwala idan lokacin sallah yayi,tana yawan sanya sumayya ta jera mata amatullah da amatur rahman tayi ta magana da su kaman wasu manya
"Ki musu tarbiyya irin taki don Allah" hakan su'ad ke yawaita fada,murmushi sumayya keyi tace
"Tare zamuyi musu har ke,kema mamarsu ce"
"Zanso hakan" abinda takan fadi kenan wanda sumayyan ta kasa gane me hakan yake nufi.
Hatta almustapha yaga sauyi qwarai wajenta,da ya shigo takan gaidashi ko tayi masa sannu da zuwa,abinda bai taba gani ba,hakan ya masa dadi qwarai ua faranta masa,yakan zauna cikinsu ya bada wasu mintuna suyi hira su duka,duk da bai zama waje daya,ba wanda yasan inda yake zuwa daga shi sai Allahnshi,idan dare yayi yazo ya musu sallama shikenan sai gobe da safe.
Wani dare bayan kowa ya tafi ya barsu,yan biyu na saman gado cikin neat suna bacci su'ad ta kalli sumayya
"Wai baki kewar maan,naga ko sau daya baki taba binshi ba" murmushi ta saki
"Kin manta jinyarki nake,ladan kuma da ake samu wajen yin jinyar mara lafiya ba kadan bane" kai take gayadawa cikin gamsuwa,duk wani furuci da sumayyan zatayi akwai qaruwa a cikinsa
"Wai nikam rannan kaman naji kina min magana kan rayuwarki,bani labari mana?" Dariya ta saki tana kallonta
"Kina son ji ne?" Kai ta kada
"Eh idan babu takura,don na tabbatar zan samu wani darasi a ciki"
"To qara kunne biyu" dariya ta saka
"Na qara" a nutse sumayya ta warwarewa su'ad labarinta,gyada kai kawai take,jikinta yayi matuqar yin sanyi qwarai,wato akwai mutane shigenta ko irinta da yawa a duniya
"Gaskiya rayuwarki baki daya darasi ce,ke din ta daban ce" ta fada tana jinjinawa yadda sumayyan ta fuskanci rayuwa haka,gyaran murya sumayya tayi wanda ya janyo hankalin su'ad daga duniyar tunanin data tafi
"Nikam in roqi wata alfarma mana wajenki"murmushi tahi,ki roqa ko mene idan baifi qarfina ba
" so nake ki yafewa mommy,kada ki manta uwa uwa ce komai lalacewarta,na tabbatar soyayyar da take miki ce ta kaita ga kasa tasawatarwa da tsayawa kai da fata wajen ganin ta hanaki aikata abinda kike so matuqar ba dai dai bane,ta kuma doraki kan dai dai din,ba zaka taba iya biyansu abinda suka yi maka ba har abada"murmushi ta saki ta kamo hannun sumayya
"Mummy,ina son mummy sumayya,saidai yadda ta tarwatsa rayuwata ta kasa gyarata tana qona min rai a duk sanda na tuna hakan,na jima da yafe mata sumayya,na mata haka ne ko don gaba,duk da cewa ko a yau na tafi na barta ba zata sake samun wasu yaran ba,amma wannan ya isheta izinar da zata bawa 'yan baya labari"kai ta kada
"naji,amma gobe ki furta mata cewa kin yafe mata,ki daina gudun ganinta don Allah" murmushi ta saka sumayya na sake shiga zuciyarta
"Naji in sha Allah zanyi,nasan tunda kika dage kan maganar kika gyaramin babu kyau abinda nake,zanso ace zan haihu da na sakawa 'yata sunanki" ta fada wani abu na taba zuciyarta,hawaye ya sauko saman fuskarta,goge mata sumayyan tayi tana cewa
"Ki daina kuka,ki godewa Allah da lafiyar da kike samu"
"Na gode" ta ce da sumayya
"Ba abun gode min,haqqina ne dama na kula dake din koba komai miji daya fa muke" murmushi suka sakarwa juna,ranar sunyi hira sosai da su'ad din har take gaya mata
"Naga amira na sonki,da fari haka nima ta soni,halina yasa ta gujeni,ki tayani bata haquri don na mata ba dai dai ba da yawa wanda yasa ta daina hulda da ni"
"Amira bata da riqo,kuma ke matar yayanta ce,na tabbatar komai ya wuce a wajenta,don kullum sai ta kirani ta tambayeni jikinki,abinda ya hanata tace na baki duk sanda ta kira kina bacci,ni kuma banson tada ke" murmushi ta saki don maganar ta mata dadi,sai da suka raba dare sosai sannan sumayya ta daura alwala ta tada sallah,ta baiwa su'ad carbi ita kuma taci gaba da azkar,sanda ta idar ta waiwaya sai taga carbin ya fadi hannun su'ad din,idanunta alumshe alamun bacci yayi awon gaba da ita.
*Bayan awanni uku*
Zaune take kawai a gabanta ta zuba mata ido tamkar mutum mutumi,sam kukan da yaran ke tsalawa bai shiga kunnuwanta bare tayi yunqurin daukarsu,dubanta kawai take lokavi bayan lokaci tana kiran sunanta,saidai babu wani alami dake nuna motsa bare ta amsa,tun kan ya qaraso dakin yake jiyo kukan yaran,hakan ya sanya ya qara sauri cikin hanzari ya isa qofar dakin ya bude ya tura,a kansu su biyun idanunsa suka sauka,sai ya sauya akalar tafiyar tasa daga wajen 'yan biyun zuwa inda su sumayyan ke zaune,kallo daya ya yiwa su'ad dake kwance gabanshi yayi mummunar faduwa,tamkar wanda aka bigewa gwiwoyinshi ya qarasa bakin gadon ya duba hannyenta zuwa saitin zuciyarta inda take aiki,abinda yaji ya tabbatar masa da cewa babu rai jikin su'ad din,duk da haka zuciyarshi ta kasa gasgata masa,take ya hautsina kayan aikin dake dakin,ya dinga gwaje gwaje,wanda yana tsaka da aikin abokinsa mai asibitin ya shigo dakin da niyyar duba mara lafiyan,kallo daya ya mata ya tabbatar ta mutu,hakan ya sanyashi janye almustaphan cikin harshensa na turanci yace
"Kayi haquri,ta rigamu gidan gaskiya man,Allah ya jiqanta" tuni sumayya ta qarasa rushewa da kukan dake cinta,suka hadu ita amatullah da amatur rahman suka gauraye dakin,baya almustapha yayi ya jingina da bangi yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
*bayan awa daya*
Dukkansu suna zaune a babban falon dake asibitin wanda na likitan ne ya basu su zauna,kowanne ka dubi fuskarsa cikin baqinciki take,hatta da mazan dauriya kawai suke,saidai almustapha bai iya daurewar ba,karon farko da suka soma ganin hawaye kan fuskarshi,abinda basu taba gani ba tsahon rayuwarshi da su,ummi ma hawaye take sharewa lokaci zuwa lokaci,yayin da sumayya ke kuka tuburan,idanunta da fuskarta gaba daya sun kumbura,yayin da fuskar ta hadu tayi jazur,ummi dake gefanta ita ke lallabata ta bawa yaran nono,tana shayar da su cikin hijabin tana kuka,ba shakka mutuwa kota wanda baka sami bane tana da ratsa jiki da sanya wani sabon imani a zuciyar dan adam,ballantana wadda ta sani sun zauna tare tsahon shekara nesa da juna,gab da zata tafin kuma sukayi zama irin na yaya da qanwa,yaushe zata manta haka?,haka mutuwa take,takan dauke mutum a sanda bai shirya ba hakanan masoyansa basuyi sallama da shi ba,sai mutuwar mukhtar ta fado mata,kukanta ya sake daduwa,wanda hakan ya sake karya zuciyar duka sauran,ba shakka sunga irin zaman da sukayi a tsakaninsu cikin sati uku kacal kafin ta mutu,haka suka dinga bata baki kafin su fara tattauna abinda ya zaunar da su din bayan an kai gawar su'ad mutuware.
Alhj abdus samad ne ya fara magana
"Zamu wuce nigeria da gawarta,bama gawarta ba har maman tata ma"
"Amma alhj kaji fa sunce ita khaulat ta samu stroke,haka zamu tafi da ita" cikin tsantsar baqinciki yana goge qwallarsa yace
"Daga rana irin ta yau professor na bar zaman qasar nan har abada,zamu koma qasarmu ta gado da zama,babu abinda na tsinta a zaman qasar nan banda baqinciki da tarwatsewar iyalina tunda har na kasa control dinsu,kowa yana vin gashin kanshi,Allah ya jiqanki su'adah ya gafarta miki" ya qarasa fada yana shafe sabbin hawayen da suka zubo masa da tafin hannunshi
"Hakan yayi,a mata suttura cikin dakin mijinta" inji ummi,da wannan shawarar suka soma neman izinin tafiya da gawar su'ad,cikin kwana biyu rak suka samu kasancewar abun na masu da shi ne.
Cikin dakinta dake abuja aka mata wanka aka shiryata,almustapha na tsugunne gaban gawarta yana mata addu'a,sosai yayi mata addu'a tare da jaddada yafiyarshi a gareta,sannan ya bawa sumayya guri,alhj abdus samad da duk wani makusancinta,inda aka turo mommy a keke,kuka ta saka ta soma magana,saidai maganar bata fita ba'a jin abinda take fada,sakamakon bakinta daya karkace tun faduwar data yi sanda tayi ido hudu da gawar sy'ad tana ihu tana ita daya ta mallaka ya zata yi mata haka,daga nan ta sume,bayan ta farfado kuma ta gamu da wannan cutar,sosai sumayya ta qunshe kanta a tsakanin qafafunta tana sakin kuka sanda aka dauki gawarta aka fice da ita zuwa gidanta na gaskiya,tabbas duk wanda yayi damara don duniya ya kwanceta,Allah ya bamu sa'ar tafiya,kasa mu riskeka sanda kake farinciki da mu ya Allah.
A nan gidan dake abuja suka zauna karbar makoki,kaf 'yan uwan sumayyan ba wanda baizo mata ba,haka yan uwa da abokan ariziqi suka dinga zirya,har eesha ba'a barta a baya ba,tazo jikinta cikin matuqat sanyi,tana tuna yadda suke takun saqa da su'ad din,tana tuna yadda su'ad ta dauki rayuwarta kusan dai dai da yadda itama take jin kanta,hakan ya qara mata mutuwar jiki,sai data dangana da sumayya tayi mata gaisuwa,sannan ta roqi gafararta kan abinda ta nata a baya,murmushi kawai tayi,mutuwa kadai ta ishi mai hankali aya,me ya mata zafi da zata tsaya saka wani mutum a ranta,itakam mantawa ma take da faruwar abin sai idan wani abu ya taso da zai tuna mata da hakan,tace ya wuce har abada,'yan biyu sun jima hannunta,sosai yaran suka shiga ranta,bul bul da su cikin tsafta gwanin sha'awa,duk da mamarsu na cikin alhini amma fes suke,don ummi ke sawa baba uwani ke kula da su akai akai,ba'a maidasu wajen sumayyan sai sun buqaci nono.
Kwanaki bakwai akayi kaman yadda al'ada tace kowa ya watse,aka fidda duk wani abu na su'ad din aka miqawa iyayenta,don almustapha cewa yayi ya yafe,bazai iya amsar komai nata ba,ranan mummy khaukat tayi kukan da bata taba makamancinsa ba,tayi nadamat da bata taba tsammanin akwai kamarta ba,ta dinga kallon sumayya tana son gode mata amma babu baki,iya jinyar su'ad kawai zuwa mutuwar nan ta karanci irin kyakkyawar zuciyar da take da ita,da