Showing 279001 words to 282000 words out of 364327 words
kira layikansa na nan qasar duka sun shiga,wanda abaya idan bai naija layinsa baya shiga saidai ta gwada na wata qasar,kai tsaye ta nufi samanshi,ta tura dakin ta shiga,neat dakin yake,saidai shima akwai cakuduwar wani qamshin bayan qamshinsa data sanshi da shi,wanda bata raba dayan biyu qamshin yarinyar ne,kishi ya lullubeta,wai ya akayi haka ne?,me yasa ta tafi har ta basu sararin cakufuwa danjuna haka cikin kwanciyar hankali,me yasa bata zauna ba ta daga musu hankali,kowa ya qeaci almustaphan idan zai iya,wanda tana da tabbas ita ke da nasara,sabida tana da gogewa da wayewar da zata iya aiwatar da haka,yanzun ma ai bata makara ba(a cewarta)sai ta ja qofar dakin ta rufe ta nufi nata dakin,komai yayi qura,bata jin zata iya amfani da dakin,dole ta samu ma'aikatan gidan su gyara mata,sabida haka ta koma dakin almustapha ta sake wanka ta shirya cikin wando wanda daga same yake a dame,daga qasa kuma wajen qafafun ya bude sosai,riga ta sanya spaghetti hand wadda ta dameta dai dai jikinta,gashinta ta taje ta daureshi,sannan ta janyo takalmanta masu tsini hade da igiy kamar zata tsokale idanun duniya ta daura,'yar hula ta samu ta sanya akanta wai din idon jama'a sannan ta feshe jikinta da turare ta sauko qasan tana fatan shigowar almustapha bada dadewa ba don daidaita tsakaninsu.
Gab da zata fice sukayi kacibus da fahariyya tana shigowa,baya suka ja suna wa juna kallon kallo,tsaf fahariyya ta qarewa kayan jikin su'ad kallo,tasan ko na wanne kamfani ne,bazau wuce armani ko D&C ba,don bata siyan kaya a kamfani mai arha,lallai almustapha ya tsaya mata fahariyyan ke rayawa a ranta,waskewa tayi
"Ai naga shigowarki nace bari na leqo mu gaisa,ban tsammaci zuwanki ma bikin ba"
"Bashi ne ya kawoni ba"
"Da alama kam,tunda na lura kaman ma bakisan mai gidan bai sashen ba" idanu tabi fahariyyan da shi
"Tun yaushe?" Ta tambayeta
"Jiya da dare sun fita shi da amaryarsa" wani qunci ya ziyarceta,ina ya dauketa suka tafi?,wato ma basu kwana gidan ba?,bai taba mata haka ba duk yadda bata qaunar zaman gidan
"Da kyau almustapha,ni almustapha zaiwa haka?"
"Ai kadan ma kika gani,matuqar baki sanya himma kin fiddata daga gidan ba,ni ga tawa nan ta zamarmin ciwon ido,bata haihuwa amma ta fini power da fada wajen mai gidan,sai kiyi kamar kinayi" ta fada tana juyawa ta fice,burin ta ya cika,dama so take ta tura mata takaici,ta kuma samu nasarar haka.
Da qyar su'ad ta iya jan qafarta ta fice saboda neman masu mata gyara,kishi da baqinciki ya cika mata zuciya,yaushe har tayi wannan saken da har wata ke watayawa da almustaphanta yadda taga dama?.
Duk da cinkoson masu wucewa gidajen amaren daurin auren hakan bai sanyashi tsaida motar waje ba,dai da ya dangana da oarking space wanda tuni ya yiwa drivansa waya yazo ya sameshi a nan ya kaishi inda za'a daura auren,kashe motar yayi ya jingina da kujerar yana dubanta qasa qasa,sai daya gaji don kanshi sannan ya bude bakinsa
"Kijr but,banson ki cika yawo cikin gidan,nan da awa daya nasan gidan zaya sake cika da mutane,ki zauna gu daya" kai ta kada tana mamakinshi,wannan tsananin da takatsantsan duka na meye?,hannunta ta dora zata bude qofar motar ya hangin gungun angwayen tafe cikin shigar babbar riga,hayaniyarsu nata tashi,bisa dukkan alamu yanzu zasu wuce wajen daurin auren ne
"Wait....." Ya gada yana miqewa daga jinginar da yayi,haka kawai ranshi ya baci daya hango alqasim a cikinsu,ita dinma ta ganshu ta gane kuma me yasa ya tsaidata,sai da suka wuce sannan yace
"Muje" ya furta yana cire belt dake daure a jikinsa,ya bude murfin motar itama ta bude ya zagayo suka daidaita kafada kana suka jera.
A hankali ta daga kai ta dubeshi sanda ta hangi sa'ad na takowa,cak su'adan ta tsaya sannan ta canza direction zuwa inda suke,kanta ta daga ta dubi almustapha,sarai shima ya ganta,amma sai ta lura da cewa ko a jikinshi,ba wani yanayi nashi da ya sauya,hasalima hannunta da ya kama bai saki ba,suka ci gaba da takawa su'ad itama na takowa zuwa nahiyar da suke idanunta qur bisa kansu duka su biyun.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
8⃣9⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*
*la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*
_____________________________________
Ci gaba tayi da tunkararsu ba tare data dauke idonta daga garesu ba,tamkar zuciyarta zata fito waje saboda tsananin kishi,kamar ta kurma ihu ko zata ji sauqin abinda ke sukar zuciyarta,bata taba jin bala'i irin wannan ba arayuwarta,ashe a baya duka qaryar kishi take kan almustapha?,almustaphan nata ne riqe da hannun wata haka?,sun kuma jero suna tafiya kan bigire guda?,ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,shi sam baiyi zaton ganinta ba ma a wannan lokaci,sai da suka qaraso dab da juna sannan ya zame hannunshi daga na sumayyan ya dubeta
"Idan kika shiga bana so ki fito,bana son yawo ki zauna waje guda,nasan duka nan za'a dawo akwai walima da zasuyi" sai ta samu kanta da narke masa cikin wani irin salo
"Ina so naje wajen umman khalipha fa,tunda nazo ban shiga ba" girarsa ya dage salon ya matuqar qayatar da shi
"Ko zakin ba yanzu ba,idan na dawo zan sanar miki" kai ta gyada tana jifanshi da wani irin qayataccen murmushi daya sake narkar da shi
"Ok,to a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya" idanu ya lumshe addh'a ta masa dadi,qarakin murmushi ya subuce masa
"Amin,thanks" kai ta gyada tana juyawa cikin takunta na nutsuwa,baki daya idanuwa su'ad ta bita da shi,ji take kamar ta fincikota ta yarfa mata mari,ba'a tabacin fuskarta irin haka ba,a gabanta wata ke soyewa da mijinta?,ita dun da dukkan 'yammatan danginsa sunsan halinta sarai ko cikakken kallo bata so taga ka fiya masa yanzun zata ci miki mutunci?,saiga wata a gaban idanunta tana narkewa mijinta,ga sumayya kuwa sanda ta juya sai ta dinga jin wani abu na mintsininta cikin zuciya,sai taji kamar ta koma,me yasa ta barsu su biyun?,zuciyarta ta cunkushe,kallon data lura su'ad na mata bai dameta ba,qarfin gwiwar da bata taba jinsa kan kishiya ba wannan karon shi take ji,ba abinda zai sanyata taci gaba da barwa wasu matan mazanta,ta tabbata ko ba'a gaya mata ba babu zancan zaman arziqi tsakaninta da su'ad,ta santa tun ba yau ba,ta santa tun kafin miji ya hadasu,bata da kirki bata da mutunci,bata ganin girman kowa,a haka taci gaba da takawa zuciyarta dake cike da kishi na bata shawarar ta waiwaya amma ta daure zuciyarta ta hana kanta aiwatar da hakan.
Yatsan tsakiyarsa da babban yatsanta ya hada ya murza a fuskar su'ad din wadda tabi sumayya da kallo,kishi ke sukarta,sam bata gane ma sumayyan ba,saboda ba duka wanda yayi mata qaramin sani irin wanda su'ad din tayi mata bane zai iya tantanceta ba tashi guda,idanunta da suka kada ta dauke ta maida kan almustapha,shigar jikinsa kadai ta bata mamaki,bata taba ganinsa da manyan kaya ba tunda suke sai yau din,wani qyama da takaici ya kamata,ya auri 'yar nijeria arewa ta fara zuba masa duhun kai kenan,to wallahi bazata lamunta ba,wata babbar riga harda hula sai kace wani limami,bakinta na rawa cike da tsantsar kishi tace
"Almustapha?,ashe da gaske baka sona?" Shanyayyun idanunshin nan kawai ya zuba mata yana dubanta
"Almustapha ka dubi yadda kake nuna qauna da kulawa ga wata bayan ni,dama zaka iya aikata hakan?" Ci gaba yayi kawai da dubanta,karon farko da ya soma ganin aibun irin shigar da takeyi,cikin qasarsa gidansu kuma gidan iyayensa surukai a garesu,ba shakka ta nan shine babban mai laifi,amma sam bai gane illar hakan bane sai yanzu,tunu hawaye ya soma wanke mata fuska,sai ya saki hannayenshi ya sake matsowa inda take ya kama hannayenta,ya sani qwarai kishi abu ne mai zafi cikin zuciya,abu daya ne wanda zai janyo mata ta rasa dukkan wata dama daga gareshi shine taci gaba da hauka da tashin hankali
"Enought.....daga gani na sai kuka,ya isa" wani ratsawa wadan nan taqaitattun kalaman sukayi har cikin zuciyarta,sai kawai ta fada jikinsa rungumeshi tana sake sakin kukan,hakan bai dace ba saboda suna tsakar filin gidan,kowa ma na iya ganinsu a haka,dagata yayi daga jikinsa yana fadin
"Zan wuce ne wajen daurin aure kada na makara,ki koma ciki,but ki sauya kayan jikinki kafin na dawo zuwa atamfa lace ko shadda,coz akwai maza da zasu shigo da yawa bayan dawowar tamu bana son kowa ya sake zuwa ya ganki da wannan shigar,ya kamata ta zama tsakamin ke da ni ne kawai cikin gida,understand?"mamaki ya kusa kasheta,bai taba furta mata makamanciyar wannan maganar ba sai yau,me yake son maida ta ne,irin kidahumar matarsa?,taga sarai shigar jikinta,ta nannade kanta da wani material kamar gawa ba wajen shan iska,itakam ba zata iya ba
"sai na dawo ko?" Bata saba yi masa a dawo lafiya ba ko wata addu'a tun da can ma da ake zaman dadi bare yanzu,saboda haka har ya juya ya koma wajen motarsa driver ya bude masa ya shiga suka fice tana tsaye wajen,ashariya ta lailayo ta qunduma cikin harshen nasara,tana jin nemawa kanta 'yanci ya zama dole,ba zata taba lamunta ta zauna cikin irin wannan rayuwar ba,da wannan tunanin ta tattaka cikin sassarfa ta wuce nasu bangaren.
Wajen anty maamaa ta soma shiga ta gaidata,suja gaisa da dukka 'yan uwanta a mutunce ta musu Allah ya sanya alkhairi,cikin farinciki tare da yabawa suke amsawa,lokaci daya ta burgesu ta shiga ransh,don babu wanda su'ad ta taba duba da irin wannan sigar tsawon saninsu da ita,ta dan kashe wasu mintina masu dama kamin ta wuce wajen ummee.
Dukka 'yammatan yau na falonta,amira uwar daba na cikinsu anata sabga,tsokanarta suka shiga yi har ta rasa na karewa,amiran tace
"Ku dubarmin wannan mata,daga dawowar miji saiki tattara ki bishi,wai ku don Allah baku gajiya da zaman hotel?" Duka kan cinyarta sumayyan ta kai mata
"Baki da kunya fa,nu yayarki ce ko kin manta?"
"Tuba nake,Allah ya ja da ran babbar yaya" dariya duka suka saka,barkwancinsu abin sha'awa ne da burgewa,ta gaisa da kowa cikin fara'a da mutuntawa,eesha dake zaune tun shigiwar sumayyan gaba daya sauran fara'ar da tayi rara a fuskarta ta bace bat,kusan a wannan bigiren tafi kishin sumayya fiye da su'ad,saboda su'ad din kusan bata da wani amfani ko tasiri mai yawa cikin zuciya da rayuwar almustapha,babban abin tashinbhankali kuwa data gano wasu sabbin sauyi da halaye da duka almustaphan ua qaro matuqar yana tare da sumayya,itama eeshan bata dameta,ita a yadda taje ji yanzu ko kishiya bazata bari ta dameta ba,balle wata wadda batasan me ya hadata da uta ba,abinda ta sani dai kawai eeshan nada izza izgilanci da jin kai,tun daga sanda tazo gidansu a kano tun bikin amira,ita kuwa a rayuwarta zata iya mu'a mala da kowa tayi haquri da shi banda mutum mai wadan nan halayen,don bata ga abinda zara nuna mata ba,mutunci da rufin asiri dai dai bakin gwargwado Allah ya basu,to kuma name zata zubda mutunctakarta ta dan adam kota yarda a zubda mata?,amiran ita ta miqe don raka sumayyan sama wajen ummee,suna haurawa saman ta dubeta
"Kinsan wajen ummee mijinki ya gaji halinshi,miskilancin tsiya rashin son hayaniya,daga wajen anty mamaa fa ta dawo wai kanta ke ciwo tana daki kwance" harara ta watsawa amira
"Eh kam su ai sun huta,ba irinku ba akun kuturu" baki amira ta riqe
"Iyeee,wai yau ya man kike tarewa?"
"To ya ranki?" Ta fada tana juya idanu,suka sanya dariya baki daya,ran amira ya mata fes,burinsu ya cika,dangantakar da suke fatan ta qullu tsakanin sumayya da almustapha bisa dukkan alamu Allah ga qulla ta cikin ruwan sanyi.
Knocking suka yi mata ta basu umarnin shigowa,amira ke gabasai sumayya,tana zaune a dakin ita da qannenta biyu da yayarta,idanunta kan sumayya fuskarta qunshe da fara'a,yayin da kunya ta yiwa sumayya katutu,don ta tabbata tasan ba gidan suka kwana ita da almustapha ba,a ladabce ta qarasa ta duqa tana gaidasu suka amsa a sake,nabila qanwar ummee wadda itama babba ce don tana da yara samari ke tsokanar sumayya
"Har yau baku kai mana ziyara kano ba,duk da dama wannan sarkin hade gabas da yamman sai sallah sallah yake zuwa mana,saidai ki jisu suna waya da mai martaba,da alama ma baisan jikinsa ya motsa ba bai gaya masa da tuni kin ganshi ya tashi hankalin kowa" dariya suka sanya ummee tace
"So nake kafin ya koma i yayi qoqari ya kaisu baki daya ita da su'ad din,don ita dinma dudud zuwanta nawa?"
"A'ah kibar ta wannan,itakam tunda baquwa ce sai ya kaitan,idan tana da sha'awa da kanta zata ko tasa ya kaita" inji hajiya saudat yayar ummee,hira suke kadan kadan kafin su fice don komawa bangaren anty mamaa,tsabar hadin kai da fahimtar juna ya sanya duk sanda wani abu ya taso cikin gidan walau na hajiya mamaa ne kona hajiya kilishi wato ummee 'yan uwan kowaccensj basa qasa a gwiwa wajen zuwa,run daga kan matasa yammata zuwa manya,akwai hadin kai da fahintar juna mai yawa tsakaminsu,kowanne family sunsan kowanne,haka 'yamnatan kowanne vangare na mu'amala dana kowa,kasanceqar duk sha'ani za'a hadu,sai duka suka zama kamar family daya.
"Ina almustaphan ya shiga ne?" Akunyace ta amsa mata
"Ya wuce wajen daurin aure ne"
"To masha Allah" inji ummeen dadi yaja ratsata,
"Allah ya saka da alkhairi fa amiran umman khalipha,naji dadin yadda na fara ganin sauyi wajen almustapha,bama ni ba hatta da babansu,Allah ya qara miki juriya da qwarin gwiwa,naji labarin abokiyar zaman taki tazo,ina son inja hankalinki da don Allah kada ki biye mata da duk wautar da zata zo da shi,ki dauke kanki kiyi haquri da ita,idan kika fuskabci akwai abindabtake miki na cutarwa da ba zaki iya dauka ba,ki samu mijinku cikin salama ki sanar masa ya warware muku matsalar,kada ki soma yarda ki biye mata ku dinga abinda ba dai dai ba,kada ki yarda saboda ita ku dinga bata ran mijinku kinji"
"insha Allah ummee"
"Allah yayi miki albarja,ya akbarkaceku da zuriya dayyiba" addu'ar tayi mata nauyi,amira ce ta cafe
"Amin ummee,kai Allah dai ya nuna mana ranar,ummi da ido daya zaki bacci ina jin" ta fada cikin tsokana tana qyaqyata dariya,murmushi ya subucewa ummee
"Kinci gidanku,kin maidani kakarki ko?" Ta fada tana harararta,murmushi itama sumayya tayi,gwara da zancan ya tsaya nan kada ta hanata sukuni gaban ummeen.
Bata jima ba ta wuce bangarenta,sanda ta shiga babu kowa falon,sai ta shige dakinta ta ware lafayar dake jikinta,kitchen ta wuce kai tsaye ta soma tunanin me zata dafa mishi?,don tuni ta sani wajen ummee baicin abincin taro idan ana yi,yankewa tayi tayi masa jallop din couse,sai ta tanada masa wani abun shan,shine zata gama cikin sauri kafin su shigo,cikin qanqanin lokaci ta hada komai ta dora.
Cikin mintina ta kammala jallop din wadda ta wadata ta kayan lambu da kuma hanta wadatacciya a ciki,kammala komai tayi waje guda ta soma hada lemo,shima bai dauketa lokaci mai tsaho ba ta gama ta kammale komai waje daya ta soma gyara wajen.
Cikin takun isa da izza ta shigo kitchen din,ta sauya kaya kamar yadda ya umarceta,a yanzun tana sanye da fitted gown na wanu lace mai azabar kyau da tsada,saidai bata daura dankwalin ba,sam sumayyan bata ji shigowarta ba,sai takun takalmanta masu tsini wanda ke haduwa da tiles din wajen suna bada wani sauti,a hankali ta waiwayo ta dubeta,sai ta dauke kai taci gaba da aikinta ganin ta shigo mata ne ba tare da sallama ba,bata tsaya ko ina ba sai data ci birki a gaban sumayyan wadda ke wanke sink data kammala amfani da shi,wani kallon sama da qasa ta yiwa sumayyan cike da tsantsar raini wanda sumayyan bata ma san tana yi ba bare ya dameta,aikin gabanta kawai take ci gaba da yi,itakam bata hango komai tattare da ita ba banda kyau da take da shi,sai tsantsar duhun kai,idan banda haka meye hadinta da daura zani?,meye na shiga kitchen tamkar matan daa?
"Ke" ta ambata cikin gatsali,sam bata nuna ta san da ita take ba,hakan ya quleta
"You african women dake nake" nan ma tayi banza da ita taci gaba da dauraye wajen tana gogewa da qaramin towel dake hannunta,hannu ta dora kan kafadar sumayyan ta juyo da ita suna fuskantar juna,murmushi sumayyan ta saki sannan ta dora hannunta saman na su'ad din ta saukeshi daga kafadarta tana fadin
"Sallama ya kamata ki soma kafin shigarki waje a matsayinki na diyar musulmi" ta juya taci gaba da aikinta,wani abu ya tsaya mata,itama za'a koyawa abinda ya dace
"Banga dama ba kuma bazanyi na,domin bani da shamaki cikin shiga duka inda naso a cikin gidan nan,gida dai na mijina ne so mallakata ne,ba wanda ya isa hanani shiga duk inda naso a sanda naso" waiwayowa tayi ta sake saki mata murmushi,mata na baki mamaki a yawancin lokuta,wato su duka son kansu ya musu yawa ne?,babu zaman lafiya idan su suka sameka cikin gidanka kamar yadda babu zaman lafiya idan kai ka tadda su,saidai zuwa yanzu ta tsike ya kamata itama ta shiga a dama da ita
"Oh sorry fa,may be labarin shafa fatihar dake tsakanin sumayya da almustapha bai isa kunnenki ba,idan kuwa har ya isa kunnenki to ya kamata kisam cewa nima matarsa ce kamar yadda kike matarsa,so kinga kenan matsayinmu daga,babu wanda nima zaimin shamakin shiga inda nakeso,saidai ni nawa addinin ya gayamin duk inda zan shiga na nemi izinin mai mallakin wajen kafim shigar tawa,wannan kadai shi zai sanyani neman izini bawai don nima ba matar doctor mustapha bace" kalamanta sunyi matuqar qona mata rai,ita take kallon idanuwanta take gaya mata cewa itama matar almustapha ce,sai ta gyara tsaiwa fuskarta na sauya launi saboda kishi
"Anzo point din,dama abinda nazo na baki shawara kenan a kai,ina mai baki shawarar sawunki a likkafa ki fita rayuwar mustapha,ki tattara ya naki ya naki ki koma gidan ubanki tun baki gamu da tuggun kishiya ba" abun ma sai yaso baiwa sumayya dariya,ta matse towel din data gama wankewa bayan ta gama goge gogenta