Showing 45001 words to 48000 words out of 364327 words
ba wayarsa dake aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya sanyashi dagawa
"Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan na ji shigowarka",bazai iya tantance mai yaji ba,so yake ya rufeta da masifa amma sai ya kasa,maimakon haka sai ya bige da cewa
" ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi"gabanta ha fadi haushi ta turniqeta,kada fa ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu komai saura qiris tayi maganin abun
"Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata kishiya,ka taho ko nazo da kaina na tafi da kai"
"Ok gani nan" ya fadi da sauri tare da katse kiran,maida idanunsa yayi ga qofar toilet din,ya tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya marairaice
"Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi" ya fada yana juyawa.
Zamewa tayi tayi zaman dirshan saman tiles din bandakin sabon kuka na kubce mata wanda ta sanya tafin hannunta ta toshe bakinta don kada su jiyota,duk da cewa ita tace ya tafin bata yi tsammanin tafiyar tasa da gaggawa ba haka.
Ta jima tana kuka a ciki kafin ta lallashi kanta bayan tayi tilawar wasiyyoyin mahaifiyarta tun daga auren da aka qara mata na fari zuwa wannan da ya kasance na biyu.
Bata bar bayin ba sai da cikakkiyar alwala,ta koma daki ta sauya kayan bacci,doguwar riga ce har qasa mai taushi da kauri,hijabi ta dora saman riga ta shimfida abun sallaha ta tayar da sallah hawaye na layi kan kumatunta.
Yana shiga ta miqe ta taroshi cikin karairaya da yauqi,ta amshi ledar hannunsa ta ajjye kana ta rungumeshi,yaqe haqora kawai yake,ko daya bata burgeshi ba,alamu sun nuna babu kunya ko qwaya daya cikin idanunta,ko daya baiji dadin kasancewarta cikin jikinsa ba amma sai ya kasa cewa da ita komai,sai ya dinga dauko daren farkon sumayya da na fa'iza da nata yana hadawa,tuni lissafin ya wargaje don tako ina sun sha banban.
Biye yake da ita kawai sai ido da yake binta da shi,ita ta hada musu ruwa sukayi wanka sannan ta samo plate ta juye kazar a ciki,kusan ita ta dinga ciyar da shi ta kuma ci da kanta har suka kammala ta janyeshi gado don tuni ta dokanta,kusan ita ta gabatar da komai a maimakonshi,mamaki da haushi ke tuqeshi,gefe guda wani irin takaici wanda idan ya yunqura zaiyi magana sai yaji ya kasa cewa komai,data dubeshi kuma sai yaji komai ya wuce ya bar tasiri cikin ransa.
Kwana tayi zaune bayan ta gaji da yin sallolin,abinda bata taba zata zata iya ba,yaushe mukhtar ya sake zame mata wani na daban haka,ita kanta tana mamakin yadda ta koyi kishinsa har haka,sai da ta gabatar da sallar asuba taji idanunta sun soma nauyi da zugi,duk yadda taso ta yakice baccin amma bata samu nasara ba,haka yazo ya saceta cikin gaggawa ya kuma mata nauyi wanda hakan ya sanya ta gaza sanin meke wakana cikin gidan har misalin qarfe goma da rabi ma safe wanda ta farka a firgice.
Bandakin cikin dakinta ta shiga da yake bayan na corridor akwaai cikin daki,wanka tayi bayan ta wanke bakinta ta dawo cikin dakin,jikinta babu qwari ta shirya cikin atamfa doguwar riga wadda ta mata kyau,duk da bata jin qwarin jikinta amma tayi lite make up wadda ta dace da yanayinta,babu dauda ko qura a rea dinta sai dan kakkabe kakkabe kawai da tayi sannan ta fito don samawa kanta abinda zata ci koda ruwan zafi ne,don jinta take iska na yawo da ita tsabar babu komai a cikinta,ledar jiya mukhtar din ya bata ta dauka ta fice da ita.
Bata kula da su ba sai data shigo cikin falon sosai,mukhyat sanye da yadi mai taushi fari tas wanda ka yiwa aiki da zare ash,sai wandda idanunta suka sake sauka kanta wanda bata tantama itace zainab din.
Macace wadda kallo daya ta yi mata ta fuskanci ta girmesu ita da fa'iza baki daya,A qalla tayi shekaru ashirin ta takwas wanda hakan ke nuna ta girmi sumayyan da shekara goma tunda sai yanzu taje cikin shekararta ta goma sha tara,baqa ce zainab din amma ba baqi can ba,tana da cika wadda za'a iya kiranta qiba kai tsaye duk da wata mai yawa bace,bata daga cikin sahun kyawawa ko kadan amma zaiyi wuya kai tsaye ka kirata da mummuna saboda yanayin iya gogayya da iya salo,saidai tako ina sumayyan ta mata fintikau,abu daya zata iya nuna mata qwala qwalan idanu da suke zagayayyu suka fi na sumayya girma,sakamakon natan lumsassu ne ba kowanne lokaci kake iya gane girmansu ba,sanye take da material mai santsi wanda aka yiwa dinkin riga da skert,breakfast sukeyi wanda ya qunshi tea da soyayyen qwai da bread,sai kaji wanda ba tantama na jiya ne aka sake gasa su.
Shi ya soma ganinta lokacin da zainab ke qoqarin bashi naman a baki,sai ya goce wanda hakan ya janyo hankalin zainab din ta ankara da fitowar sumayyan,murmushi ya sakar mata yayin da itama tayi qoqarin maida masa martani
"Kin tashi kenan,na leqaki na taras kina bacci"
"Eh,ban jima ai da tashi ba" ta fada tana takowa gabansu
"Kinyi kyau sumy ta" ya fada yana sake dubanta wanda kalmar ba qaramin dukan qirjin zainab tayi ba,lokaci daya ranta yayi baqi,sumayyan ta yaga mata tako ina,kyau da quruciya,akwai alamun nutsuwa tattare da ita sosai,hakan ta kwana da sanin lamba daya ce ita cikin zuciyar mukhtar din,don ko darensu na jiya ya bata amsa,duk yadda taso rikitashi ban manta sumayyan ba ita yake kira.
"Na gode ango mijin amarya,da fatan kun tashi lafiya" ta fada wajen kaiwa matuqa gurin boye kishi da damuwarta,sai ta dubi zainab
"Amarya ina kwana ya kwanan baqunta"
"Lafiya ya kike"ta fada tana yatsina tare da qoqarin baiwa mukhtar tea
"Qalau" itama sumayyan ta fada cikin yanayin data amsa mata tare da motsa kafada kana ta nufi kitchen don kaucewa ci gaba da kallon abinda ke faruwa.
Alamu sun nuna iyaka na cikinsu ne abincin,batasan waye yayi ba,amaryar ko mijin amaryar,koma waye dama bata da buqata,sai ta dora tea kan gas da a yanzu shi mukhtar ya siya mata take amfani da shi,ta bude kazar ta sake mata sabon hadi na spices,ta duba dan madaidaicin ovean dinta ta soma kici kicin hadawa tare da duba hanyoyin da ake hadawar.
Cikin haka mukhtar din ya shigi kitchen din dauke da kwanukan da suka ci abincin zainab din na biye da shi,bata bi takan sumayyan ba ta nufi side dinta ta dire kayan,mukhtar ya dubu sumayyan
"Me za'a girka mana ne naga ana hada ovean"
"Ai baka da buqatar abinci na malam" ta fada cikin gatse,murmushi yayi yana kallonta,lallai sumayyan ta fara zama babbar mace,tunda har tafara banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Kafin ya furta komai muryar zainab ta ratsa kunnuwansu tana qwala masa kira cikin wani irin salo,tamkar an soketa a qirji amma saita basar,ya juya yana cewa da ita
"Ina zuwa"
"Banda buqatar dawowarka ma" ta fada kishi na cinta tana qoqarin danneshi.
Har ta kammala babu shi babu alamarsa,ta juye ta koma daki da abincinta zuciyarta na raunana,saboda wannan ne karo na farko data taba ganin sauyi daga gareshi har irin haka.
**** ***** ****
Cikin kwanakin wani amarci ta dinga gani cikin gidan wanda bata tsammata ba,baki daya kamar daukar mukhtar din akayi aka sauya mata shi,hutu ya dauka na fita kasuwa har na kwanaki bakwai,ko yaushe suna daki idan kaga fitowarsa salla ce zaya yi,saita wuni sur bata sanyashi cikin idanunta ba,abun na taba ranta saidai bata yarda ta fiya zurfafa lamarin cikin ranta,runda anty dije ta gaya mata dole zata iya ganin wasu sauye sauye duk son da yake mata,amarya kota buzuz ce sai an mata rawar qafa,to bare baya ga wannan babu wani sauyi da ta gani cikin ma'amalarsu shi da ita.
*KUNDIN QADDARA TA*
Kwanaki uku take zaton zaya yiwa zainab din tunda bazawara ce,sai gashi ya shiga cikin kwana na hudu biyar shida har zuwa bakwai.
Ranar kwana na bakwai din a ranar zaya soma fita kasuwa,tana kwance dakinta bayan sha daya na safe taji sallamarsa,sai ta miqe ta zauna tana amsa masa,fuskarta babu yabo babu fallasa,gefanta ya samu ya zauna yana fadin
"Ranki ya dade kinyi wuyar gani" ido ta daga ta dubeshi,lallai ne wai ita za'a yiwa halin maza,magana yake gaya mata a fakaice koko yaya,duk da hakan sai ta dake ta kuma basar ta kaufa zancan ta hanyar fadin
"Ina kwana"
"Lafiya sumy ta,kinga na qarawa zainab kwana ko,kinga baquwace tace kuma tan tsorom zama ita daya" wani haushi ya taso ya turniqeta,budurwa ce zainab din ko yau ta fara zaman gidan aure,ko ko tsabagen rainin wayo ne,wadan nan kalaman takeson gayawa mukhtar din amma girmansa da take gani yasa ta gaza furtasu ta hadiye kayanta sai ta bige da cewa
"Ko,Allah sarki" daga yanayin da tayi maganar kawai ya tabbatar masa cewa ta inda zancansa ya shiga ta nan ya fice.
Kafin su sake cewa wani abu zainab din ta daga labulen dakin ta danno tana fadin
"Dear fito mana na rakaka,ina ta jira fa"
"Ai gani nan" ya fada yana fiddo kudin cefane daga aljihunsa,wani banzan kallo da sumayyan batasan ta iyashi ba sai yau ta jefawa zainab sannan ta miqe zata fice ta bar musu dakin,mukhtar yace
"Ina kuma zaki sumayya bamu gama magana ba"
"Baka shirya yin maganar da ni bane" ta fada tana shigewa toilet abinta ta soma daura alwalar sallar walhar da dama ita take shirib tashi tayi.
Tana jiyosu daga nan zainab din na gaya masa ya qyaleta yazo su tafi,yace a'a taje falo ta jirashi zaya fito yanzu,a bandakin ya cimmata ta gama alwalar tana gyara daurin kallabinta,fuska a hade cikin kakkaurar murya yace mata
"Wai wane irin hali kika koya sumayya wanda ban sanki da shi ba,wannan wannw irin wulaqanci ne ina miki magana kina tafiya gaban zainab salon ki koya mata yadda zata raina ni", tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,lallai a daki mutum a kuma hanashi kuka.
" ai tare muka siyi foam din makarantar koyon sabbin halaye ni da kai muka cike,muka kuma fara daukar darasi a ciki"sarai yaso ya fahimceta amma sai ya waske
"Wai duka sumayya don na qarawa zainab kwanaki kike wannan abun,yanzun ban isa da gidana ba kenan?"
"Isa kai,tunda gashi ka nuna salon taka isar" ta fada tana kashe famfo tare da qoqarin rabeshi ta wuce,sai ya janyota jikinsa ya matse gam,yasan kan abarsa take ya fara sauke mata fushinta,yayi nasara kam don itama bata bijire masa ba,don babu qarya tayi kewar mijinta sosai.
Ita ta fara zame jikinta sannan tace
"Ka gayawa matarka kada ta sake shigo kin daki kanta tsaye,sabida hakan ya sabawa dokar addinin musulunci idan ita din bata sani ba" sai ya lumshe ido ya dafe kai
"Oh sumayya harda mita ma sai da kika koya,to ayi haquri" daga nan sukayi sallama ya ajjiye mata kudin cefane duk da suna da komai.
Sosai zainab din ta qulu,ta fara lura sumayyan ta shalle zatonta,amma daga yau zata fara dasa bamabamanta cikin gidan,shanye komai tayi ta masa rakiya kamar ta hadeshu,duk yadda ya nuna jin dadinsa a fili amma zuciyarsa ta gaza karbar hakan,a boye ma Allah Allah yake ta koma ya samu ya fice daga gidan.
Da azahar ta shiga kitchen ta musu girkin rana,tana fitowa ta samu zainab din a falon zaune tana kallo,qafarta daya kan daya tana amsa waya,har sumayyan ta gifata ta taji ance
"Ke!" Da fari tayi zatan cikin wayarta ne sai taji ta sake cewa
"Ke dake nake magana sumayyata" waiwayowa tayi tana tsaye daga inda take
"Wai da ni kike?"
"Akwai wata mai sunan ne bayanke a gidan nan,koma ki dauko min abinci na".
Baki ta sake tana kallonta cikin mamaki,ita kuma nata salon kenan,sai ta kada kai kawai tace
" idan kin damu ki shiga da kanki ki dauko"
"Ni kike gayawa wannan maganar,lallai yau zaki gane niba irin sauran kishiyoyinki bane,wallahi yau sai kin gane matsayina gun mukhtar" bata tsaya bi ta kanta ba tayi komawarta daki don tana da abunyi.
Lambar mukhtar ta soma laluba tana huci,yana tsaka da sallamar custumer yaga kiran nata,sai da yaji wani dumm cikin kansa da yaga sunar,ko kadan baiyi farinciki ba amma sai ya gaza share kiran
"Amarya bakya laifi,ya gidan"
"Gida ba lafiya ba,mukhtar na fuskanci ka auroni ne don matarka ta rainani"
"Ya salam,me ya faru me tayi miki?"
"Bazan hanaka sana'a ba kabari idan ka dawo kaji koma mene ne,amma wallahi idan baka dauki mataki ba bazan ci gaba da zama cikin gidan nan ba" sai yaji wata faduwar gaba da sauri yace
"Haba zainab ki daina fadar wannan maganar mana,mai rabu mu ai sai Allah,bari na kira ita sumayyan naji" da sauri ta katseshi don bata son ya mata fadan tun yanzu lamarin ya wuce ba tare data iza wutar tafi haka ba
"A'ah nidai ban saka ba,nace ka bari kawai ka dawo"
"To shikenan sai na dawo din" ya fadi yana sauke wayar,sam jikinsa bai bashi sumayyan zata aikata wani abu na rashin mutunci ga zaina din ba,amma sai ya samu kansa da yarda da duka magan ganun zainab din.
Tun shuda saura ta gama fesa kwalliya tare da bade jikinta da turarenta data tanada na musamman wanda ke hargitsa tunani da lissafin mukhtar ya dinga maida su ba dai dai ba.
Cikin izza da isa ta fito daga dakin nata hannunta dauke da jug na kwalba wanda ta cikashi da lemin zobo da cups dinsa,tana tafe tana murmushin tarkon data d'ana ta ratso ta falo don fita harabar gidan,so take mukhtar din ya fara karo da ita kafin kowa saboda abinda ta tsara ya tafi dai dai ba tare da mishkila ba,idanunta ne suka sauka kan sumayya tada tsume cikin tata kwalliyar,wani irin material ne mai santsi kamar yanayin shufom saidai ya fishi kauri da aka matsawa dinkin wata shegiyar gown wadda ta fidda duk wata qira tata,kalar pink(ruwan hoda) ne mai turuwa,tayi amfani da dankunne da siririyar sarqa fashion baqaqe,hakanan abun hannunta zuwa zobe,take farincikin dake ranta ya ja baya ta raina tata kwalliyar data hasko farar fata ta hadu da pink da baqi,kishi ya sake taso mata,ya zama lallai kota halin qaqa tayi rugu rugu da gwamnatin sumayyan cikin zuciyar mukhtar ya zama tata ke wannan tashen,ta yadda zata yaga yarinyar yadda taga dama,yarinyar na neman fin qarfin zatonta,don ba'a rufe awa ba taga yadda ta tashi hankalin gidan da qamshin girkin abincin dare,ranta na suya ta fuce fuuu wanda sumayya bata ma lura da ita ba sai ficewarta ta gani kamar guguwa.
_tofa,yanzu ake yinta,muje zuwa_
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
2⃣5⃣
____________________________
*wa tawakkal alal hayyul lazi la yamutu wasabbih bi hamdih*
_kayi tawakkali ka dogara da rayyayyen(Allah S W T)da baya mutuwa,kayi tasbihi/ka tsarkakeshi ka kuma gode masa_
____________________________
Guguwar dawowarta sumayya da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige dakinta.
Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda yake da alama da wani abu aka sanya cikin garwashin wuta,data lura sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanni qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa'izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.
Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo harabar gidan.
Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.
Fuskarta ta fadada da fara'a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar
"Wash" zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta dora da nata jawabin
"Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?" Mamaki fal zuciyar sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin kallo
"Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau yaushe zan huta daga